HUDUBAR MASALLACIN
ANNABI 25-1-1440 NA SHAIKH ABDULLAHI BIN ABDURRAHMAN AL-BUAIJAN
HUDUBAR FARKO
Dukkan yabo da godiya
sun tabbata ga wanda ya halicci zukata ya daidaita su, ya kimsa fajircewarsu da takawar su, kuma ya
wajabta rabauta ga tsarkake ta, hasara
ta tabbata ga wanda ya biye wa son
ransa.
Muna neman tsarin Allah
daga sharrin kawunan mu da munanan ayyukanmu, wanda Allah ya shiryar da shi babu
mai batar da shi, wanda ya batar da shi ba bu mai shiryar da shi,
Na shaida ba abin
bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya, dahir
kuma tabbas, kuma na shaida cewa Annabi Muhammad bawan sa ne kuma Manzonsa
ne,tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, aminci tabbatacce mai yawa,
Bayan haka, mafi
alherin zance shi ne maganar Allah,kuma mafi kyan shiryarwa shi ne koyarwar
Annabi Muhammad, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, mafi sharrin
al'amura sune fararrunta, kuma dukkan fararrun abubuwa bidi'a ne, kuma dukkan
bidi'a bata ce.
Ya ku bayin Allah !
ina muku wasiyya da ku ji tsoron Allah, da ku
yi wa kan ku hisabi, ( ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah kuma
rai ya yi dubi ga abin da ya kaddamar don gobe, ku ji tsoron Allah. Lalle Allah
masani ne ga abin da ku ke aikatawa ,) ALHASHR
18
Ya taron musulmi !
Lalle Allah ya hallici
mutum ya sanar da shi fasaha, ya bashi kyautan hankali da harshe, ya nusar da
shi hanyoyi biyu, ya bayyana mishi hanya
ko ya gode ko ya butulce.
Ya jarraba shi da
kiyayyar rayi da shaidan ya rubuta masa dace ko tabewa, ya sanya makomansa wuta ko aljanna.
Ya shar'anta sharia sabo da shi, ya saukar da littatafai
ya turo manzanni suna masu albishir masu
gargadi, cikin mutane akwai wanda ya amsa kira ya tsarkaku, duk wanda ya
tsarkaka to don kansa, daga cikin su akwai wanda ya juya baya ya ki ya warware,
wanda ya warware to don kansa.
Ya jama'ar musulmi!
Ku sani rai abokin gaba ne kuma mai umarni da
mummuna ne,mai yanke tsakani zukata da Ubangiji masanin gaibi.
Rai a dabi'arsa mai
kwadayi ne ga abin sha'awe sha'awe da son jin dadi, mai nawa ne gurin da'a da ayyukan alheri, rai abin hawan shaidan, ne
motarsa ne, kuma wasilarsa ne , kuma kayan alatonsa ne, ta hanyarsu ne ake masa
biyayya, kuma hujjarsa ne kuma katangarsa ne. (sai iblis ya fada yayin da
aka hukunta Al'amari Lalle Allah ya muku alkawari alkawarin gaskiya ni kuma na yi muku alkawari na karya na
saba muku, kuma ba ni da wani karfi akan
ku, sai dai na kira ku ne ku ka amsa min, kada ku zarge ni ku zargi kawunanku)
Ibrahim 22
Rai na yawan umarni da
mummuna, mai yawan karkata ga son rai (Amma wanda ya ji tsoron tsayuwa gaban
UbangijinSa ya hana kansa ga barin soye-soyen rai , to, lallai aljanna ita ce
makoma) kuma ya ce :-(Ase baka ga
wanda ya riki abin bautar sa son ransa ba kuma Allah ya batar da shi bisa ilimi
ya toshe jinsa da zuciyan sa ya sanya
rufi a ganin sa to wa zai shiryar da shi
bayan Allah ).
Rai
matattara ce ta alheri da sharri
Allah madaukakin sarki ya ce :-( Wanda a ka kiyashe shi kwadayin kan sa
wadancannin ka su ne hakikanin marabauta) al hashir aya 8 , kuma ya ce:- ( Lallai rayi mai yawan umarni ne da mummuna ) .
Ya ku bayin Allah ;
Lallai Allah yana yiwa zuciya ilhami na alheri
da na sharri , kamar yanda Allah madaukakin sarki ya ce :- ( Da rayukan dan
adam da wanda ya daidaita su . kuma ya kimtsa mata fajircin ta da tsoron Allah
) surah asshams aya 7-8 .
Kamar yanda Allah ya bawa mutum kyautan ji na
zahiri , to, haka kuma ya bashi kyautar rayi
wanda ita ce ta tattari basira na ciki
Allah madaukakin sarki ya ce :-( Bari ! shi
mutum malami ne a bisa kansa ko da zai
zo da hanzare-hanzaren sa )
Manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi nuni zuwa ga haka sai ya ce:- (Shi laifi shi ne abin da ya
sosa a zuciyan ka ka sani mutane su gane shi )
YA KU BAYIN ALLAH:
Lallai rayi na da bukatan
kulawa da sa ido da tarbiyantarwa da kuma tsarkakewa da bibiya sabo da haka ne annabi tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi ya ce da husaini dan munzir : - (Ka ce ya Allah ka
kimtsa mini shiriya ta ka kare ni
daga sharrin rayi na ) ya zo a cikin
khudubatul haja ( Muna neman tsarin
Allah daga sharrin kawunan mu ).
YA JAMA'AR MUSULMI:
Lallai hanyar kubuta
daga sharrin rayi shi ne a tsarkake ta a
bata kulawa a kuma bibkiye ta , kuma hakika Allah ya yi rantsuwa a cikin
littafin shi a wurare goma sha daya a jere
bisa ga rabautan wanda ya tsarkake ta ,
kuma da hasaran wanda ya turbude ta
sai ya ce :- (Allah ya yi
rantsuwa da rana da hasken walahan ta . Da wata
idan ya bi ta . Da wuni idan
ya bayyana rana . Da dare idan ya lullube ta. Da
sama da wanda ya gina ta. da kasa da wanda ya shimfida ta . Da rayukan dan adam da wanda ya daifdaita ta kuma ya kintsa mata fajircinta da tsoron
Allah. Hakika wanda ya tsarkake ta ya
rabauta. Hakika wanda ya turbude ta ya tabe.
Allah ya yiwa muminai baiwa da ni'ima
mafi girma sai ya ce : -( Hakika Allah ya yi baiwa bisa muminai da ya aiko Manzo a cikin su daga kawunan
su yana karanta ayoyin sa a gare su yana tsarkake su yana sanar da su alkur'ani
da hikima , hakika su sun kasance
gabanin aiko shi lallai suna cikin bata
mabayyani ).
Allah ya bada labari kan cewa tsarkake rayi wasila
ce na samun babban rabo da rabauta da
aljanna sai ya ce : -( Hakika wanda ya tsarkaka ya rabauta , ya ambaci
Ubangijin sa ya yi salla ).
Kuma ya ce :- (Amma wanda ya ji tsoron
tsayuwa gaban UbangijinSa ya hana kansa ga barin soye-soyen rai , to, lallai aljanna ita ce
makoma)
YA KU BAYIN ALLAH :
Lallai tsarkake rayuka bai samuwa sai da matsayi na ihsani :-
Kan ka bautawa Allah kamar kana
ganin shi , in kai baka ganin shi to shi yana ganin ka .
Baya samuwa sai da sabawa son rai da lazimtar tsoron Allah kuma bai samuwa sai da sabawa rayi mai umarni
da mummuna , da kyale abubuwa na jin
dadin rai da sha'awe-sha'awenta.
To duk mai ciyar da
rayi abin da take sha'awa
|
Tamkar mai ciyar da wuta
ne busasshen kirare
|
To duk wanda aka datar ya fi karfin zuciyar shi to ya
cinma manufa kuma ya habaka rayin sa. Wanda ya sake mata linzami sai ta wurga shi cikin hanyoyi na halaka.
Duk wanda ya kauracewa jin dadi zai cinma
manufa
|
Wanda ya dukufa akan
ababan jin dadi zai yi nadama
|
Daukakan rai na cikin
tunkude sha'awarta
|
Cikin samun abin da yake sha'awa akwai kaskanci na har abada
|
Kar ka shagalta sai
da abin da zai kawo ma daukaka
|
Kar ka yarda da
halaka ga rai mai tsada
|
YA KU JAMA'AR
MUSULMAI :
Jihadi shi ne kololuwan
tozo na musulunci farilla ne mafi
girma daga cikin farillai mafi
girman jihadi shi ne jihadin rai , ku sa
mata linzami game da abubuwan jin dadin ta , ku yaye ta daga sha'awe-sha'awen
ta , daukakan ta na daga cikin fin karfinta game da sha'awe-sha'awen ta, kaskancinta da walakantar ta na cikin bata
dama game da sha'awanta
Rayi kamar jariri yake wurin shan nono in an kyale shi sai ya girma
|
a kan haka in an yaye shi sai ya yayu
|
Ka yaki ranka da
shaidan ka saba musu
|
Idan sun maka nasiha to ka tuhume su
|
Kar ka yi biyayya gare su suna abokan jayayya ko hukunci
|
Domin kai dinnan
kasan kaidi irin na abokin jayayya da
kuma mai hukunci
|
Gaba irin na rayi
kwatankwacin gaba irin na shaidan ne
kuma hakika Allah ya gargade mu game da musu da'a a cikin alkur'ani ((Amma
wanda ya ji tsoron tsayuwa gaban UbangijinSa ya hana kansa ga barin soye-soyen rai , to, lallai aljanna ita ce
makoma).
Allah ya sa muku
albarka ni da ku a cikin alkur'ani.
HUDUBA TA BIYU
Dukkan yabo da godiya
sun tabbata ga Allah da ya halicci mutum
ya daidaita shi ya girmama shi ya fifita shi , ya kuma kalifantar da shi ya ba shi
aminci , kuma ya ba shi kiwo ya daga darajar shi kuma ya azurta shi kuma ya masa baiwa ya mar kyauta .
Tsira da amincin Allah
su tabbata ga wanda Allah ya zaba
Annabin mu Muhammad dan Abdullahi
da iyalan sa da sahabban sa da duk wanda ya bi tafarkin sa kuma ya bi
shiriyar sa .
YA JAMA'AR MUSULMI:
Rayi mai yawan umarni
ne da mummuna ita dinnan ta hada yawan
zalunci da kuma yawan jahilci, tana yin jiji da kai da kuma nuna girman
kai da kuma hasada da riya da fushi da kuma kwadayi ,
da handama da babakere, da rowa
da kankamo da tsoron talauci da kuma da sauran su na daga cututtuka.
Tsarkake ta
shi ne a cire mata wadan nan sifofin
.
Tsarkake rayi shi ne siffantuwa da kyawawan
dabi'u da kuma kyawawan halaye da laduba
irin na shari'a kamar kauna
da ikhlasi da hakuri da gaskiya
da kuma kankan da kai da tsoro da
fata da karamci da kyauta da tuba da
istigfari , da kuma tuna mutuwa da
karewa da juya baya ga duniya da fiskantar Allah madaukaki.
Tsarkake rayi
yana tabbatuwa ta hanyar sabawa son arai da rashin amsa bukatun ta , da
kuma yaye ta daga sha'awe-sha'awen ta
da jin dadin ta da kuma yi mata
inkari da zarginta Allah madaukakin sarki ya ce: - (Duk
wanda ya tsarkaka ya rabauta . Ya kuma ambaci sunan Ubangijin shi. Ya tsarkake
sunan Ubangijin shi mafi daukaka
)
YA KU BAYIN ALLAH :
Ku yi kokari wurin
tsarkake rayuka kafin mutuwar gaggawa
ta zo mu ku da kuma yin da na sani ,(Ranar
da ko wace rai take samun abin da ta aikata
na alheri abin halartarwa da abin
da ta aikata mummuna tana burin da
hakika akwai fage mai nisa ).
Ku yi kokari wurin tsarkake rayuka kafin
rayi ya zo ya ce ya hasara na bisa ga sakaci da na yi a sha'anin
Allah ko da kuwa na kasance cikin masu
yin isgilanci ko kuma ta ce ina ma
da Allah ya shiryar da ni da na kasance
cikin masu tsoron Allah , ko kuma ta ce
ya yin da ta ga azaba ina ma da ina da kome sai in kasance cikin masu
kyautatawa.
Ku yi kokari
wurin tsarkake rayuka kafin a
toshe baki ba zai iya yin furuci ba , shaidu za su tsaya abokan jayayya sune gabbai
kamar yanda Allah ya ce :- ( A yau ne muke yumkewa bakunan su , hannayen su za su yi mana zance
, kafafuwan su za su yi mana magana za
su shaida bisa ga abin da suka kasance
suna aikatawa)
(Ranar da muke tara
makiya Allah to su ana kora su (zuwa
wuta). Har yayin da suka zo mana sai
kunnuwan su da idanuwan su da fatun su suka shaida a gare su da abin da suka
kasance suna aikatawa , za su fada ga
fatun su don me kuka yi shaida a kanmu , sai suka ce Allah ne ya furtar da
mu wanda ya furtar da ko wani abu shi ne ya halicce ku marrar farko izuwa gare shi ake komawa da ku. Ba ku kasance kuna buya ga miyagun al'amura don kunnuwan ku da idanuwan ku da fatun ku su yi muku mummunar shaida ba,
kai dai kun yi zato ne ya yin buyan ku cewa
hakika Allah bai san yawanci daga abin da kuke aikatawa ba , abin da
kuke boyewa ba . Wancannin ku zaton ku wanda kuka zata ga
Ubangijin ku shi ne ya halakar da ku ku
ka zamanto daga cikin tababbu .
In sun
yi hakuri to wuta ne makomar su ,
in suka nemi a yarda da su to su basa daga cikin ababen yarda . )
Ku yi kokari wajen tsarkake rayi
kafun ranan da zai zame a cikin
shi ( Ranar da mutum zai gujewa dan uwan shi. Da uwar sa da Uban sa . Da matar sa da diyar sa . Ko wani mutum a
cikin su a wannan ranar yana da sha'ani
da zai shagalar da shi .
YA KU BAYIN ALLAH:
Mai wayo shi ne
wanda ya yiwa kan sa hisabi ya yi aiki
domin abin da zai zo bayan mutuwa , shi kuma gajiyayye shi ne wanda ranshi ya
bi abin da yake so , ya yi ta gurace-gurace a wurin Allah .
Ku yiwa kan ku hisabi kafin a yi muku
hisabi ku auna kafin a auna ku , lallai hakan ya fi saukin hisabi a gobe idan kuka yiwa kan ku hisabi a yau kuka yi ado
domin halartowa a wuri mafi girma , a wannan ranar ne za a kawo ku babu wani mai tsoro a cikin ku .
Wata rana Umar dan khaddab Allah ya yarda da shi ya shiga wani kango sai ya kebanta da ranshi
yana mata hisabi Anas dan Malik Allah ya
yarda da shi yana sa mishi ido daga nesa ta inda baya ganin shi , sai ya ji umar shugaban muminai yana cewa
sannu, sannu na rantse da Allah ya kai dan Khaddab ko dai ka ji tsoron Allah ko Allah ya azabtar
da kai .
Ku ji tsoron Allah ya ku bayin Allah , ku
sani fa zaku hadu da shi
Ya Allah zukatan mu ka
bata tsoron Allah
Ya Allah ka daukaka
musulunci ga musulmai .
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق