بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Yabo ya
tabbata ga Allah; Ma'abucin buwaya da karamci, Wanda ya kagi halitta, Mai
yalwar falala da ni'imomi, Ina yin yabo ga Ubangijina, kuma ina gode masa kan
ni'imominSa wadanda muka sani, da kuma wadanda bamu sani ba.
Ina
shaidawa babu abin bautawa da gaskiya, sai Allah shi kadai yake bashi da abokin
tarayya, Mafi girman buwaya da karamci,
kuma ina
shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawansa ne Manzonsa, Wanda Allah ya bashi
dunkulallun kalmomi (na jawami'ul kalim).
Ya Allah!
ka yi dadin salati, da sallama da albarka ga bawanka kuma Manzonka; Muhammadu,
da iyalansa da sahabbansa, wadanda aka shiryatar da su ga hanyar da ta fi
mikewa,
Bayan haka:
Sai
ku yi takawar Allah Mabuwayi da daukaka, ta hanyar neman kusanci zuwa gare shi
da aikata kyawawan ayyuka, da kuma nisantar ayyukan haramun, saboda babu mai
tsira (a wurin Allah) face masu takawa, kuma babu mai tabewa ya yi hasara face
masu bin soye-soyen zukata, da masu sakaci.
Ya ku, Musulmai… !!!
Ku yi hisabi ga kayukanku gabanin a muku hisabi, kuma ku farkar da
zukatanku daga gafalarsu, kuma ku kame rayuka daga aukawa cikin dadi irin na
haramun, kuma ku yi gaggawan tuba, gabanin saukowar ajali, da yankewar guri, da
katsewan yin ayyuka, domin kuna ganin saurin tafiyar shekaru, da gaggawar
tafiyar kwanaki.
Kuma babu
komai a bayan wannan rayuwar face mutuwa, kuma babu komai a bayan mutuwa face
shiga gidan ni'ima, ko gidan azaba mai radadi.
Kuma kamar
yadda kuke aiki domin duniya mai karewa, to sai ku yi aiki domin lahira mai
wanzuwa, Allah Ta'alah ya ce: "Kawai, kuna
fifita rayuwa ce ta Duniya * alhalin Lahira itace mafi alheri kuma mafi wanzuwa"
[A'alah: 16-17].
Ya ku, Musulmai… !!!
Ku rungumi
littafin Ubangijinku, domin daukakarku da rabautarku da gyaruwar lamuranku,
duka a cikinsa suke, kuma a cikinsa samun rabonku bayan mutuwarku yake, da
kariyarku da tsirarku daga fitintinu wadanda suke yawaita duk lokacin da
Kiyamah ta kara kusantowa, fitintinu wadanda suke da sarkakiya a farkon
faruwarsu, sai kuma su bayyana su fito sarari a karshen lamuransu; don haka,
babu wanda zai tsira daga fitintinu sai wanda yayi riko da Alkur'ani da Sunnah,
kuma ya lazimci jama'ar Musulmai;
Sai ku yi
tadabburi, ko nemi sanin ma'anar littafin Allah Mabuwayi da daukaka, kuma ku yi
aiki da shi, sannan ku haddace abin da addini zai tsayu da shi, na sunnar
Manzon Allah صلى الله عليه وسلم, kuma akida ta ingantu da shi, itama ibada ta samu kamala da
shi, musamman hadisan da ma'anoninsu ya game hukunce-hukuncen Musulunci,
wadanda suka kunshi falaloli, sai ku san ma'anoninsu, domin ku yi riko da su
kuma ku yi aiki, domin wannan shine MANHAJIN MAGABATA NA KWARAI, wadanda Allah
Ta'alah ya fada, akansu: "Masu rigayen farko
daga Muhajirawa da Ansarawa, da wadanda suka bi su da kyautatawa, Allah ya
yarda da su, kuma suma sun yarda da shi, kuma ya musu tanadin gidajen
Aljannoni, koramu suna gudana a karkashinsu, suna masu dawwama a cikinsu har
abada, wannan shine rabo mai girma" [Tauba: 100].
Kuma –a
wannan matsaya- zan kawo hadisi daya daga cikin dunkulallun magana (Jawami'ul
kalim), wanda ya wajaba kowane Musulmi namiji da Musulma suyi aiki da shi, a
cikin kowane hali, kuma dole ne mazaje da mata su rika aiki da hadisin matukar
akwai rai a cikin jikinsu, Wannan kuma shine, fadinSa –صلى الله عليه وسلم-: "Addini
nasiha ne, addini nasiha ne, addini nasiha ne. Sai muka ce: Ga wa Ya Ma'aikin
Allah? Ya ce: Ga Allah ne, da littafinSa, da ManzonSa, da kuma shugabannin
Musulmai, da kuma sauran gama-garinsu", Muslim ya ruwaito shi,
daga hadisin Tamim Ad-dariy (رضي الله عنه). Kuma wasu Maluma dayawa banda Muslim, suma sun ruwaito shi;
daga cikin Maluman hadisi.
Kuma hadisi
ne mai girman sha'ani, Imam Abu-dawud ya ce: "Fik-hu
yana gudana akan hadisai guda biyar; hadisin halal a bayyane yake, haram a
bayyane yake, da hadisin babu cuta babu cutarwa, da hadisin: dukkan ayyuka suna
tare da niyyoyinsu, da hadisin: addini nasiha ne, da hadisin: Abin da na hane
ku, ku nisance shi, wanda kuma na umarce ku, to ku zo da shi gwargwadon iko".
Kuma
Alhafiz Abu-Nu'aimin ya ce: "Wannan hadisi ne
da yake da sha'ani mai girma, Muhammadu bn Aslam Ad-duwsiy ya ambaci cewa,
lallai hadisin addini nasiha ne, daya ne cikin kashi hudu na addini".
Yana daga
cikin dalilan da suka nuna cewa; lallai wannan hadisin, wajibi ne ga kowane
Musulmi namiji da kuma mace musulma, su yi aiki da shi, koyaushe, Lallai Allah
Ta'alah ya dauke wasu ibadodi, ga wasu daga cikin Mutane, saboda wani uzuri, ko
saboda wasu sababi, amma bai dauke yin nasiha ba, karkashin kowane uzuri, ko
cikin kowane hali, Allah Ta'alah ya ce: "Babu
kunci ga Maraunana, kuma babu laifi, ga majinyata, da wadanda basu samu abin da
za su ciyar ba, matukar sun yi nasiha ga Allah da ManzonSa, kuma babu wata
hanya (ta cutarwa) ga masu kyautatawa, Allah shine Mai yawan gafara, Mai
jin-kai" [Tauba: 91].
Sai Allah
ya bayyana cewa, ba za a yi uzuri ga wani Musulmi ba, kan yin watsi da nasiha,
daidai da kyaftawar ido (koda yana da uzuri).
Sahabbai
basu yi tambaya kan ma'anar nasiha ba, saboda sahabban sun san abin
da kalmar take nuni akansa na ma'anonin addini mai fadi ta kowace fiska, domin
hakikanin nasiha ya kunshi, martabobin addini uku na Musulunci
da Imani da Ihsani.
Kawai abin
da sahabbai suka tambaya, shine Ga wa ake nasihar, kuma wanene suka
cancanceta?
Kuma asalin
ma'anar nasiha, shine Tsamo abu ko cire shi daga abubuwan da suka
shiga masa domin gurbata shi, a larabci ana cewa; Nasahal asala, wato ya tace
zuma, idan Mutum ya tsaftace zumar daga kwansonsa.
Kuma MA'ANAR YIN NASIHA GA ALLAH TA'ALAH ya kunshi, Son Allah, da kan-kan-da-kai a gare shi, da
rusuna masa, da mika-wuya ga shari'arsa, domin neman yardarSa da ladanSa, da
kuma tsoron fushinSa da azabarSa, Allah Subhanahu ya ce: "Kawai masu imani da ayoyinmu, sune wadanda idan aka fadakar
da su da ayoyin, sai su fadi suna masu sujada, kuma suna yin tasbihi game da
gode wa Ubangijinsu, alhali ba su yin girman kai * sasanninsu suna nisantar
wuraren kwanciya, suna kiran Ubangijinsu bisa ga tsoro da tsammani, kuma suna
ciyarwa daga abin da muka azurta su" [Sajada: 15-16].
Kuma
AllahTa'alah ya ce: "kuma Masu imani sune masu
tsananin so ga Allah" [Bakara: 165].
Kuma
Annabi صلى
الله عليه وسلم ya ce: "Ku so Allah
daga dukkan zukatanku, saboda abin da yake ciyar da ku da shi, na ni'imomi".
Kuma
mafi girman nasiha ga Allah, itace bauta masa Subhanahu, ba tare an hada
shi da abokin tarayya ba, cikin tsarkake niyyah, da aiki da Sunnah da bin
shiriyar annabi Muhammadu صلى الله عليه وسلم, da kebance Ubangiji da na'ukan ibadodi
dukkansu, kamar addu'a da neman taimako, agaji, da tawakkali, Allah Ta'alah ya
ce: "Ka ce, lallai kawai ina rokon Ubangijina
ne, ba zan masa shirki ko hada shi da kowa ba" [Jin: 20].
Shi
kuma Ubangiji Mabuwayi da daukaka ana masa bauta ne, saboda abin da yake da su
na sifofin kamala da girma, da kuma yadda ya tsarkaka daga sisfofin tawaya
(nakasa), da kuma saboda abin da Allah yake da su na ni'imomi ga halittunSa, da
bukatuwan bayi zuwa ga rahamarSa; don haka: Ita ibada sababi ce na samun
alherorin Allah, kuma sababi ce na tunkude sharrace-sharrace ga Mutum, a cikin
rayuwarsa da kuma bayan mutuwarsa.
Kuma nasiha
ga Allah Tabaraka wa Ta'alah tana kasancewa ta hanyar tabbatar wa
Allah abin da ya tabbatar wa kansa a cikin littafinSa, da kuma abin da ManzonSa
ya tabbatar masa da su; na sunaye da sifofi, akan abin da magabata na-kwarai
suka kasance akansa, Allah ya yarda da su, amin. An ruwaito daga
Abu-Umamah رضي الله عنه daga Annabi صلى الله عليه وسلم, Allah Ta'alah ya ce: "Mafi soyuwan abin da bawana ya bauta min
da shi, shine yin nasiha a gare ni", Ahmad ya ruwaito shi, da
'Dabaraniy a cikin mu'ujam kabir.
Kuma ma'anar yin nasiha ga Manzon Allah صلى الله عليه وسلم itace: son annabi
da darajanta shi da girmama sunnarsa, da aiki da umurninsa, da hanuwa da
haninsa, da yin bauta wa Allah da shari'arsa, da bibiyar shiriyarsa, da gaskata
labarunsa, da yada hadisansa, da yin da'awa zuwa ga addininsa, Allah Ta'alah ya
ce: "Ka ce: Ku yi da'a ga Allah, kuma ku yi
da'a ga Manzo, amma idan kuka bijire, to lallai akansa akwai abin da aka aza
masa, kuma akanku akwai abin da aka aza muku, kuma idan kuka masa da'a zaku
shiryatu" [Nur: 54].
Kuma ma'anar yin nasiha ga Littafin Allah Ta'alah itace: Girmama Alkur'ani
mai karamci, da sonsa, da yin kokari wajen koyan karatunsa da karantar da shi,
da neman sanin hukunce-hukuncensa, da yin tilawarsa tilawa ingantacciya, da yin
aiki da umurnin Alkur'ani, da barin haninsa, da dawwama kan tilawarsa, da kiyaye
harrufansa da iyakokinsa, da sanin tafsirinsa da ma'anoninsa, da abin da aka
nufa da shi, da yin tunani cikinsa, da dabi'antuwa da shi, da yin raddi ga
wadanda suka karkata wajen fahimtar Alkur'ani da sunnah, tare da ruguza
barnace-barnacensu, da tsawatarwa akansu, Allah Subhanahu ya ce: "Lallai wannan Alkur'anin yana shiryatarwa zuwa ga hanyar da
tafi kyawu" [Isra'i: 9].
Kuma ma'anar yin nasiha ga Shugabannin Musulmai itace: So musu alheri,
da son su yi adalci, da yin farin-ciki idan aikinsu ya yi dace, da nisantar
algus a gare su, da kin ha'intarsu, da kuma (uwa uba) kada Mutum ya yi
fito-na-fito da su, ko ya taimaki makiya akansu, tare da taimaka musu cikin
lamarin gaskiya, da yin biyayya a gare su cikin abin da ba sabo ba, da yin
addu'ar dace a gare su, da addu'ar dacewa da gaskiya a cikin hukuncin da suke
yi, An ruwaito daga Abu-hurairah (رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), ya ce: "Lallai
Allah yana yarje muku abu uku, yana yarje muku, ku yi bauta a gare shi; kada ku
hada shi da kowa, kuma ku yi riko da igiyar Allah gaba daya, kada ku rarraba,
kuma rika nasiha ga wadanda Allah ya jibinta musu lamuranku",
Muslim ya ruwaito shi.
Abdullahi
bn Mas'ud رضي الله عنه ya ce: "Lallai abin da
kuke kyama alhalin kan jama'a yana hade shine mafi alheri akan abin da kuke so,
a halin rarrabuwa".
Kuma nasiha
shine amincin zuciya
Kuma an
ruwaito dagaabin da Jubair bn Mud'im, daga Annabi صلى الله عليه وسلم ya fada a cikin hudubarsa a
masallacin Khaif (dake Minah): "Abu uku
zuciyar Mutum Musulmi baya daukar kyashi akansu; Tsantsanta aiki ga Allah, da
yin nasiha ga Majibinta lamura (shugabanni), da lazimtar jama'ar Musulmai",
Ahmad ya ruwaito shi da Alhakim.
Kuma an
ruwaito daga Ma'akil bn Yasar, daga Annabi صلى الله عليه وسلم ya ce: "Babu Mutumin da Allah zai bashi wani abin kiwo, sai bai
kewaye su da nasiharsa ba, face ba zai shiga Aljannah ba", Bukhariy da Muslim da Ahmad suka ruwaito
shi.
Ita kuma ma'anar nasiha ga dukkan Musulmai itace: Fadakar da su
zuwa ga maslahohinsu, da ilmantar da su lamuran addininsu, da sitirce
al'aurarsu, da kokarin toshe ko biya musu bukatu, da nisantar algus ko
ha'intarsu, da nisantar yin hasada a gare su, da kyautata musu.
Nasiha sifa
ce ta Annabawa da Manzanni Amincin Allah ya tabbata a gare su, Allah Ta'alah ya
ce:( Hakika manzo ya zo muku daga cikinku mai jin
nauyin abin da ya wahalar da ku, mai muku fatan alheri kuma mai tausayi da
jinkai ne ga muminai)
Kuma yace
game da Nuhu Amincin Allah ya tabbata a gare shi(
Ina isar muku da sakon Ubangiji na kuma ina muku nasiha) Kuma yace
game da Hudu Amincin Allah ya tabbata a gare shi(
Ina isar muku da sakon Ubangiji na kuma ni a gare ku mai nasiha ne amintacce).
Kuma yace
game da Salihu Amincin Allah ya tabbata a gare shi :( Hakika na isar muku da sakwannin Ubangiji na kuma na yi muku nasiha)
Nasiha sifa
ce ta mumunai Allah Mai tsarki da daukaka ya ce game da muminin Alu Yasin
: ( ya ku muta ne na: ku bi manzanni) (sai aka ce :
ka shiga aljanna sai yace ina ma da mutane na sun sani)
Ibnu Abbas
Allah ya yarda da shi ya ce : ya yi
nasiha ga mutanensa a halin yana raye da bayan ya mutu.
Allah
Ta'alah ya ce: "Lallai Muminai 'yan'uwan juna
ne", [Hujurat: 10] " (Kuma ku
yi riko da igiyar Allah gaba daya, kuma kada ku rarraba"
[Ali-imrana: 103],
Allah ya yi
mini albarka NI da KU, cikin alkur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da
KU da abin da ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai
hikima, Na fadi abinda ku ke ji, kuma ina
neman gafarar Allah Mai girma ga Ni da KU da sauran Musulmai daga kowani
zunubi, Ku nemi gafararSa, lallai shi Mai gafara ne Mai
rahama.
HUDUBA
TA BIYU
Yabo
ya tabbata ga Allah Masanin abin da ya buya na gaibu, Mai jujjuya zukata, Mai
yaye musibun da suka sauka da bakin ciki, Ina yin yabo ga Ubangijina kuma ina
gode masa akan ni'imominSa gaba daya; wadanda suka gabata da wadanda zasu zo,
Kuma ina
shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai yake bashi da abokin
tarayya, Mai yawan gafarar zunubai,
Kuma ina
shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawanSa ne ManzonSa zababbe,
Ya Allah ka
kara salati da sallama da albarka ga bawanka kuma Manzonka Muhammadu, da
iyalansa, da sahabbansa madaukaka, masu takawa.
Bayan haka … !!
Sai ku yi
takawar Allah Ta'alah, a asirce, da kuma a bayyane, domin da takawa ne zaku
samu mafi kololuwar daukaka, kuma ku rabautu da alkhairori a wannan rayuwar, da
kuma bayan mutuwanku,
Ya ku Bayin Allah … !!
Ku yi
tunani akan fadin Allah Ta'alah: "Kuma Muminai
maza da mata, sashensu majibincin sashe ne, suna yin umurni da kyakkyawa, kuma
suna hani da abin da ba a so, kuma suna tsayar da sallah, kuma suna bayar da
zakka, kuma suna da'a ga Allah da ManzonSa, wadannan lallai Allah zai yi rahama
a gare su, Lallai Allah Mabuwayi ne Mai hikima" [Tauba: 71]. A
cikin wannan ayar akwai taimaka wa juna, da tallafar juna, da nasiha wa juna,
da agaza wa juna, da 'yan'uwantaka, da jin-kai da rahama da kauna.
Kuma
an ruwaito daga Jarir bn Abdullahi, ya ce: "Na
yi mubaya'a ga Manzon Allah صلى الله عليه وسلم akan tsayar da sallah, da bada zakka, da yin nasiha ga
kowane Musulmi",
Bukhariy da Muslim su ka ruwaito shi.
Kuma
Abubakar Almuzaniy ya ce: "Abubakar رضي الله عنه bai
fi sauran Sahabban Manzon Allah صلى الله عليه وسلم yawan
azumi ko salla ba, saidai ya yi fice ne da wani abu da ya tabbatu a cikin
zuciyarsa",
Ibnu-Ulayyah
ya ce: "Abin da ya kasance a zuciyar Abubakar
shine, soyayya don Allah Mabuwayi da daukaka, da yin nasiha ga halittarSa".
Kuma
an ruwaito daga Hakim bn Abiy-Yazid, daga Babansa, daga Annabi صلى الله عليه وسلم ya ce: "Idan dayanku ya nemi nasihar dan'uwansa, to ya masa nasiha",
Ahmad ya ruwaito shi, da 'Dabaraniy a cikin mu'ujam kabir.
.
Ya ku Bayin Allah… !!!
"Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan
Annabin, Ya ku wadanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da sallamar amintarwa"
[Ahzab: 56].
Ya
Allah! Ka
yi salati da sallama wa Annabi Muhammadu,