اسم
المترجم :أمين سعد
اللغة :
الهوسا
التاريخ 9/1/1442ه
Hudubar
masallacin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi na 9/1/1442 na
shaihk Abdul Bari dan Awad Alsubaiti
Hudubar farko:
Dukkan yabo da
godiya sun tabbata ga Allah, tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzon Allah
da iyalanSa da sahabbansa da wanda suka biyo su,,,,,, bayan haka:
wata
sura ce mai girma, - dukkan surorin Alkur'ani kuma na da girma- gajeruwa ce a
harufanta, amma tana da zurfin ma'ana a ma'anoninta, ta tattaro abubuwa da su
ke na dabi'u masu kyau ta kebanta da girma na falaloli tana daidai da daya bisa
ukun Alkur'ani , Allah Madaukakin sarki ya ce:(ka ce
: Allah Shi daya ne) (Allah wanda ake
komawa yayin bukata)(Bai haifa ba kuma ba
a haife Shi ba )(kuma bai da wani da ya ke kininSa), kul huwa
Allahu ahad, Allah : wannan sunan
shi ne sunan da yafi ko wanne cikin sunayen Allah kuma shi ne sunan da ya fi ko
wanne a wurin biyayya da kuma wurin tattarowa, Allah : shi ne suna mafi girma ,
shi ne abin ambato mafi daukaka , jalalarSa ta cika sammai bakwai da abin da ke
cikinsu kasaitarSa ta kewaye doron kasa da abin da ke kanta da abin da ke
karkashinta da kuma abin da ke cikinta sanin Allah tushe ne na dukkan ilimi,
kai shi ne sani mafi daukaka kuma mafi girma mafi kasaita Allah Madaukaki ya
ce:(Shi ne Allah a cikin sama kuma a kasa)
Babu
rayuwa ga zukata kuma babu farin ciki babu annashawa babu ni'ima babu debe kewa
face na cikin sanin Allah , Malik dan Dinar ya ce: ''Miskinan
gidan duniya sun fita daga gidan ba su dandani abu mafi dadi ba a cikinta sai
aka ce da shi , menene abu mafi dadi a cikinta? Sai ya ce: sanin Allah da
kaunarSa''
sani
ne wanda ke tabbatar da wuyaye a masaukai na bauta da kankan da kai da rusunawa
da kauna , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:(lallai Allah na da sunaye
casa'in da tara, dari ba daya duk wanda ya kiyaye su zai shiga aljanna),
duk wanda ya so Allah da sunayen Shi da siffofin Shi Allah zai kaunace shi idan
ya so shi kuma zai debe kewa tare da ambaton shi kuma zai yi shauki zuwa gare
shi kuma da zuwa haduwa da shi.
Gwargwadon
sanin mutum gwargwadon girmamawan shi ga Alla Mabuwayi da daukaka, matakan
mutane cikin bauta gwargwadon abin da ya dasu a cikin zukatan su ne na sanin Allah.
kamar yanda halayen mutane ya dara juna a
cikin salla da gwargwadon halartowan su da ma'anonin da sakon sanin Ubangiji.
Sanin
Allah na sanya bawa ya halarto da kasancewan Allah tare da shi a dukkan halayen
da ya ke ciki sai zuciyarsa ta samu natsuwa, ya samu kwanciyan hankali ya
dogara zuwa ga Allah dogaro na gaskiya kuma ya samu sakankancewa da Allah bisa
gaskiya ,Allah Madaukakin sarki ya ce: (wadanda suka
yi imani zukatansu na natsuwa da ambaton Allah ku saurara da ambaton Allah ne
zukata ke natsuwa).
Duk
wanda ya san Allah cancancin saninSa zai ji dadi a sujjadarsa zai yi sallah sai
ya yi kushu'i a tsayuwarsa da zamarsa kuma zai zama yayi yawo a malakutin sama
ko a malakutai yana mai lura yana mai tafakkuri wato tunani harshensa zai zama
yana furtawa da ''tsarki ya tabbata ga Allah… godiya ta tabbata ga Allah …Allah
mai girma… ba abin bautawa da gaskiya sai Allah…''
Sunan
Allah idan aka ambata a abin da ya ke dan kadan sai ya karu, idan aka ambata
shi yayin shiga tsoro sai tsoron ya gushe, idan lokacin bakin ciki ne sai bakin
cikin ya yaye, idan lokacin bacin rai da damuwa ne sai mutum ya samu farin ciki
da walwala, idan lokacin kunci ne sai mutum ya samu yalwa, duk wanda ya san
Allah zai ji kunyan Ubangiji ya same shi wurin da ya hane shi kuma ya rasa shi
a wurin da ya umarce shi saboda yana tuna kasaitar Allah (ka dogara ga Mabuwayi Mai rahama) (wanda ya ke ganinka a lokacinda ka ke tashi) (da kai komonka cikin masu sujjada) .
Idan
halarto da ma'anoni na sanin Ubangiji ya raunana to sai mabubbuga na imani ya
bushe kututturen dadin biyayya sai ya dushe zuciya sai ta kekashe mutum ya fada
cikin damuwa , damuwa ya yawaita a tare da shi ya rika shiga cikin tsoron abin
da zai fiskanto da kuma arziki
(ka ce: Allah daya ne):Shi ne guda daya wanda ba
Shi da makamanci ba wani wanda ya ke irin Shi a kudurarSa ne to Shi kadai ne a
SiffofinSa Shi daya ne a zatinSa Shi ne Mahalicci Mai azurtawa, Mi rayawa, Mai
kashewa Mamallaki, Mai sarrafa halittunSa yanda ya so, ba a neman agaji da
taimako da tsari sai zuwa gare Shi, Shi kadanShi .
(Allahussamad): Shi Samadu Shi ne wanda ya cika a siffofinsa wanda
dukkan halittu na bukatuwa zuwa gare Shi, wanda ya wadata daga dukkan kowa,
wanda baya mutuwa , ba ya gadarwa amma duk abin da ya ke na sama da kasa dukka
gadonSa ne wanda ba ya barci , ba ya mantuwa Shugaba wanda shugabancinSa ya
kammala ya cika Mai girma a iliminSa da hikimarSa da hakurinSa da kusurarSa da
buwayarSa da dukkan siffofinSa tsarki ya tabbata a gare Shi Madaukaki (Assamadu): Shi ne wanda halittu ke dumfara
yayin bukatu a bukatunsu kuma ya gamsar da su, sunan Allah (Assamadu): yana sanya bawa ya rika jin wani karfi da izza da wadatuwa daga dukkan
wani da ke koma bayan Allah Mabuwayi da daukaka sai ya sakankance ma'anar cewa
Allah din nan ya ishi bawanSa tofa domin assamadu yana jin ganawarsa yana ganin
wurinSa ko da dukk duniya ne suka tattaru dommi su cutar da shi ba za su iya
cutar da shi ba da wani abu face sai abin da Allah ya rubuta a gare shi .
(lam yalid wa lam yulad):
Shi ne rayayye wanda ba ya mutuwa Mai wanzuwa bayan karewan halittunSa Shi ne
mai tsarki wadatacce daga da'a, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata
a gare shi ya ke cewa : (Ba wani da ke mafi
hakuri bisa cutarwar da ya ji shi kamar Allah, lallai suna sanya miSha da'a
alhali kuwa yana azurta su kuma yana basu lafiya) .
(wa lam ya kun lahu kufwan ahad) ta yaya zai
kasance yanada kini alhali kuwa Shi ya halicci dukkan komai? , ya samar da
dukkan kowa Shi ya samar da kowa da kowa Shi ne babba Mai daukaka wanda Shi ne
yafi dukkan komai kuma mafi girma ga dukkan komai, an karbo daga Anas dan Malik
Allah ya kara yarda a gare shi ya ce: (wani mutumi daga cikin ansar ya kasance
yana jan mutane salla a masallacin kuba ya kasance a duk lokacin da ya fara
karatun sura yana farawa ne da ita a cikin sallan da ke musu, sai ya fara da (kul
huwa Allahu ahad) har ya kare da ita sannan ya karanta wata sura daban tare
da ita ya kasance yana yin haka a ko wace raka'a mutanensa suka mishi magana
sai suka ce kai kana bude salla da wannan suran sannan kuma ba ka ganin ita ta
isar maka ba sai ka karanta wata ba? ko dai ka karantata ko ka barta ka karanta
wata ,Sai ya ke cewa: ni ba zan barta ba, in kuna so na cigaba da limantanku ko
jagorantan ku a salla to sai na yi in kuma kun ki ba kwa so to sai na barku kuma suna ganin lallai shi ne ya fi su daraja,
sai suka ki waninsa ya musu limanci , yayinda suka zo wurin Manzon Allah tsira
da amincin Allah su tabbata a gare shi, su ka bashi labari da wannan labarin
sai ya ce: ya wane : mai ya hana ka ka aikata abin
da mutanenka ke umartanka da shi? Meyasa ka ke lizimtan karanta wannan sura a
ko wace raka'a? sai ya ce: ni ina kaunanta ne sai Manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi ya ce: kaunar da ka ke mata ta shigar da kai Aljanna)
Buhari ne ya rawaito .
Huduba ta biyu:
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya
ji wani mutum yana cewa : (Ya Allah ina rokonKa, lallai kai ne Allah Tilo,
wanda ake dumfara yayin bukata wanda bai haifa ba kuma ba a haife Shi ba, bai da wanda ya ke kininSa, Manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Hakika
ya roki Allah da sunan Shi mafi girma wanda idan an roke Shi da shi zai bada,
idan an yi adu'a da shi zai amsa) Ibnu Majah ya rawaito Albani ya inganta
shi
Manzon Allah
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: ((kul
huwallahu ahad) da(kul a'uzu ) guda
biyu a yayin da aka wayi gari da yayin da aka yi yammaci sau uku sun isar maka
ga dukkan komai) Abu Dauda ne ya rawato da isnadi ingantacce .
Gobe asabar ne ranan ashura, hakika Annabi tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi yana kirdadan wannan rana na ashura kuma ya ce: (lallai ina fatan Allah ya kankare zunubin shekaran da ta
gabata) Abu Dauda ne ya rawaito da isnadi ingantacce.