اسم
المترجم : أمين سعد عبد الله
اللغة :
الهوسا
التاؤيخ :
20-10-1441هـ
Hudubar farko
Ya ku musulmi!
Fadaka na daya daga cikin manyan abubuwa masu
kima, da kuma abu mafi tsarki da ya dace a dasa shi , ba aminci sai da shi babu zaman lafiya kuma sai da kulawa da
shi da bin shi ; fadaka; shi ne
kiyayewa daga duk wani abubuwa kanana da
fahimta mai zurfi an karbo daga Aisha
Allah ya kara yarda a gare ta ta ce :- Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce
gamae da saukar wahayi :- (Sai ya tafiyar da ni
da hankali na a halin na kiyaye abin da
ya fada ). A wani lafazi (sai na
kiyaye abin da ya ke fadi ) Buhari ne fito da shi
Katada Allah ya mi shi rahama ya ce
:- (Kunnuwa na ba za su ji wani abu ba face
zuciya na ta kiyaye shi ) fadakakkiya
ita ce wacce ta hankalci abin da yake
daga Allah madaukaki da kuma amfana da
abin da ta ji na daga littafin Allah da
sunnar Manzon sa tsira da amincin Allah
su tabbata a gare shi ya ce :-(Kunnuwa masu fadakuwa) ya kawo shi bisa ga
tankiri bai kawo shi a sigar jam'i ba
sabo da karancin masu kiyayewan da fadakuwa.
An karbo daga Zaid dan sabid Allah ya
kara yarda a gare shi ya ce :- na ji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana
cewa:- (Allah ya haskaka fiskan duk mutumin da ya
ji magana ta sai ya kiyaye ta ya fadaku
da ita sannan ya sadar da ita zuwa ga
wanda bai ji ta ba , sau da yawa wanda ke dauke da fakihu
alhali shi ba fakihi ba , sau da yawa
kuma wani kan dauki fikihu zuwa
ga wanda ya fi shi fahimta ) Tirmizi ne
ya rawaito).
Ramah Ramazi Allah ya mi shi rahama ya ce :- ( Sai Annabi ya bambance tsakanin mai nakalto sunna da
mai fadakuwa da ita ya yi nuni zuwa ga falalan mai fadakuwa a fadin shi , sau da yawa wani kan dauki fikihu amma
shi ba fakihi ba sau da yawa kuma wani
kan dauki fikihu zuwa ga wanda ya fi shi fikihu ).
Ya ku musulmi:
Jakar mutum ita ce :- zuciyarsa da hankalinsa
da suke tattaro iliminsa da kudurinsa da kimarsa da tunaninsa
da jinsa (na jiki), kar ka sanya a jakar ka sai abin da ya dace da addininka da hankalinka da dabi'unka .
Alheri wanzuwa yake ko da zamani ya
yi nisa sharri kuma shi ne kazanta mafi muni da ka kiyaye na guzuri .
Ubangijin mu ya ce:- game da
kafiraia masu girman kai (Kuma Allah shi ne mafi sanin abin da suke tarawa )
wato ya san abin da suke tattarowa su boye a cikin
zukatan su na kiyayya ga Manzon Allah da
muminai .
Abdullahi Dan Mas'ud Allah ya kara
yarda a gare shi ya ce :- (Lallai wadannan zukata
jaka ce, to, ku shagaltar da ita da Alkur'ani,
kar ku shagaltar da ita da wanin sa ko
wani abu wajen shi na buso da abin da ke
cikin shi ne,
harshen sa kuma na furta abin da ke zuciyar shi )
Abin da ke zuciya ya ki sai ya bayyana *** Kuma dukkan
kwano yana nason abin da ke cikin shi
ne
Wanda asalin shi bai kasance tsarkakke ba ***
To ba zai fitar da abu mai tsarki ba daga bakin shi.
Dukkan mutum aikin shi
na kama da shi *** kofi na kamshin abin da ke cikinsa ne.
Ya ku musulmi:
Ana samun fadaka ne ta hanyar ilimi
da natsuwa da fahimta da bincike tana karfafuwa kuma ta hanyar abota da masu
yalwan hankali wanda ya goge a harkar yau
da kullum ya san jiya da yau.
Hakika ance abin da ya rage ya isa mai bada labari game da abin da ya wuce, abin da suka jarraba ya isa abin lura ga masu hankula,
fadakuwa na karuwa ne ta hanyar
tambayan ma'abota ilimi da gogewa a
rayuwa da basira a al'amura da shekaru
da kuma sani.
An tambayi Dan Abbas Allah ya kara
yarda a gare su ya ce:- (D a harshe mai yawan
tambaya da zuciya mai yawan hankalta da
rayi wanda bai gajiya).
Fadakuwa na habaka
ne ta hanyar shawara da ma'abota hankula da basira da kuma tattaunawa da masu hikima da ma'abota hankula .
Mai hankali idan
al'amura suka rikice mi shi *** Sai ya hade al'amuran ta hanyar tattaunawa da kuma neman shawara
Amma ma'abota jahilci
yana fandarewa da ra'ayin shi*** Sai ka ganshi yana taran aradu da ka
Abin sani fadakuwa na iya karuwa kuma yana iya raguwa , hakika ance
musharaka cikin al'amura yana bawa mutum
goge , atisayi kuma yana daga ma'abocin shi zuwa ga
darajoji na kamala
Mai hankali fadakakke yana gane
nauyin da ke wuyansa, kuma yana
dubi zuwa ga karshen al'amura kafin su bayyana
ya kiyasta wani abu da makamancin shi
kuma ya dauki izina daga wanin sa
ya kiyaye daga sharri kafin ya same shi .
Mai basira ne da
karshen al'amura kai ka ce **** yana
dubi ne da ra'ayin sa na dai-dai zuwa ga
abin da ya ke aukuwa
Huzaifa Dan Yamani Allah ya kara
yarda a gare shi ya ce :- (Mutane sun kasance suna
tambayan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi akan alheri , ni kuma na kasance ina tambayan
shi game da sharri, tsoron
Mai hankali fadakakke yana kiyayewa daga abin da akwai kaskanci ko tawaya
kuma yana taka tsantsan cikin abin da akwai aibi akan shi , ko kuma akwai cutarwa ga wanin shi,
kuma yana tsarkaka daga abin da yake akwai kazanta , ya kuma kauce daga
abin kyama ya kuma kare kan shi daga
abin da bai dace ba, kyau da kawa daga
gare shi ya ke fitowa, alheri kuma daga gare shi ya ke gangarowa.
Ya ku musulmi:
Karancin fadakuwa musiba ce
da ta tsaya akan kwabri na jahilci,
da kuma raunin hankali da
wauta da karancin gogewa, kuma yin ko inkula na daga cikin
bala'in da ya ke kasancewa ra'ayi , ga wanda yake da iko ba ga wanda ya
ke kallo ba, ta yaya mutum zai musanta abinda ya ke hakika ne ya kuma gaskata abinda ya ke na bata ne ko
karairayi , ya maida abubuwan da suke
ana ji ana gani ya rasa rarrabewa , zane da layi suka rikirkice mi shi ya kasa rarrabe tsakanin zare da abawa da kuma tsakanin gaskiya da wasa da kuma abu mai kyau da mara kyau bai yi dubi ba zuwa ga karshen ala'amura , bai
gano girman hadarin ba kuma bai yi riko
da azama ba , bai dauki mataki na kariya da iyakancewa ba da farkawa
ba , ya bi son rai ya kosar da
zuciyan sa sha'awe-sha'awen sa ba tare
da yayi dubi zuwa ga makomar al'amura ba, to ta yaya zai zamana ya amsa kiran
mai nasiha ko ya damu da abin da yake cewa.
Na daga cikin musiba
zargin wanda ba zai gargadu ba*** dabga
zaluncin shi da kuma magana da wanda bai
fahimta
Ba wani abu ba ne
cuta sai dai ka ilmantar da wanda yake
jahili *** Shi kuma yana zato cikin jahilcin shi cewa ya fi ka sani
Ya ku musulmi:
Ku gyaru da ilimi , ku amsa kira da
fahimta ku ja damara da basira, ku sa rigar kariya da fadaka.
Fadakuwa abu ne na dole *** ba mai rabauta sai mai yi da
gaske
Tir da wanda ya san abu na gaske
kuma ya ki ya ki ya tafi akai , muna
jin radadi a yayin da muka ga wanda ya
ke jin koyarwa na kariya da kuma abubuwa
da aka yadawa na fadakarwa da dalilai
na shiryarwa da kuma tsari na kare kai
da ke fitowa daga bangaren jami'an tsaro
da jami'an lafiya musamman daga abin da ya shafi korona sai ya yi kunnen uwar shegu , kamar bai ji
ba ya rinka fiskantar su da izgilanci da ko inkula
ya doge yana mai sabawa da musu ya haifarwa kansa da iyayensa da 'ya'yansa da
iyalansa ya jawo bala'i da cuta ya raba
musu a tsakiyar gidansu ya bude mu su kofofinta ya dauke musu shamakinta , ya
rinka kuma kashewa mutane gwuiwa daga
bin matakan kariya , ya kuma yada tsakanin mutane cewa korona karya
ne da yaudara, ya makance daga dubannin
matattu da wadan da suka kamu, wadan da suka dandani daci da tsananin cutan .
Yana tinkaran dukkan kokari da
kasashe ke yi na iyakan cewa da yin galaba da yaduwan shi , to ku kiyaye daga
raunin hankali da raunin alkalami da magana
ku sake bitan hankula ku yi lura cikin tunanin da kuke yadawa da lafuzan
da kuke saka da abubuwa da kukle yadawa
, ku ji tsoron Allah cikin abin da kuke fadi , ku bar abin da ba ku iya kyautata
kada ku kusa cikin abin da ba ku sani ba , kar ku yi amfani da jahilci
wurin yakar ilimi da zato wurin yakini ,
da abin da yake na shirme da
karairayi wanda ba su da makama , ku kyautata
al'amarin ku , ku shiga taitayin ku, hakika ance .
Ra'ayi mai gudana da
idanuwan mutane na bacci***Ra'ayin da ya
kaddamar da takatsatsan baya jinkirta
azama. Ina fadan abin
da kuke ji kuma ina neman gafaran Allah kuma kuma ku nemi gafarar shi lallai
shi ya kasance ga masu yawan komawa
gare shi mai yawan gafara ne .
Huduba na biyu
Ya ku jama'ar musulmi :
Hakika abubuwan da suka faru na wannan yanayi da ake
ciki na korona da abubuwan da suka auku
ya bayyana bukatuwanmu zuwa ga sake gina
fadakarwa , ga 'ya'ya da kuma al'uma da mata da maza , da yawa mun gani na daga dajjalanci da karairayi
wanda suke amfani da wannan annoban
wurin cimma kazantattun manufofin
su da neman abin duniya walakantacce ,
wofantacce mai da'awan karyan da bayi da ilimin likitanci ko kuma ba yi da wani abu da zai taimaka mishi wajen tabbatar da
binciken ilimi mai zurfi , ba kuma na'ura
da zai yi amfani da shi wurin gano maganin korona , amma zai yi da'awan
ya gano maganin cutar korona , mutumin da yake likitanci na karya da yaranta da yaudara zai bada magani na
kwayar cuta da ta gagari center ta bincike na duniya. Shi mai kwadayin abin
duniya mai son handama, maras dabi'u masu kyau zai boye kayaki da sumbattoci da
kuma ababan tsabtace wuri da magungunan kashe koyoyin cuta , domin ya rinka
wasa da farashin su , da kuma
,mai yin algus da dabaru yana mai sana'anta magunguna na karya da da abubuwan kashe koyoyin cuta na boge wacce
ke iya yin illa wa lafiya kuma yakan
taba lafiyan jiki da mai karyan ilimi
rudadde , wanda yake bushewan ido da
bada fatawa da yin ijtihadi a cikin
abubuwa da suke sabbi, da matsaloli da suke da alaka da korona , yana mai fiskantar da mutane ta yanda za su
yi salla su tsarkaka su yi ibada alhali kuwa bai mallaki cancanci na ijtihadi
ba ko fatawa .
Za ka ga wawa
yana kaucewa duk wani abu na mutunci*** yana sauraron duk wani abu na wauta.
Ba mai aminta da masu wadannan
da'awar sai mara fadaka da ganewa da lafiyayyen hankali.
Ku ji tsoron Allah ya ku musulmi ku hanu ku kame kai daga abubuwan aibi da
laifi da abin kunya, ga Al-kur'ani da suna gaba gare ku, suna cike da hikima da
hukunce – hukunce da ka'idoji da wa'azuzzuka, da laduba da wadanda su ne
shugabannin ilmuka kuma mabubbuga ne na fahimta kuma hanya ce ta samun daukaka
da ake nema, to ku kiyaye su,ku yada su, da wahayi ne da fadaka hankula ke cika,
shakku da wahami ke gushewa.duhu ke yayewa,
Ku
farkar da zukata daga gafala ku
tuba daga zunubai da kusakurai, bala'i bai sauka sai da zunubi, ba a daukewa
sai da tuba, ku nemi saukar rahama da adu'a, duk wanda ya nuna talaucin shi
zuwa ga Allah to Allah ya wadata shi,
duk wanda ya nemi mafaka a wurin shi Allah sai ya daukaka shi duk wanda ya nemi
kariya daga gun shi sai Allah ya kare shi idan har bayan jirkicewa ne to sai
Allah ya bashi kwanciyar hankali idan bayan ruwan sama ne kuma sai ta yi fayau,
rana tana buya kuma tana hudowa , fure kan yankwane sannan kuma ya yi 'yaya ,
dukkan wani tsanani to zuwa ga sauki ,dukkan kuma wani wahala to zuwa ga
yayewa, ku yawaita kankan da kai da adu'a da fatan alheri.
Waka :
***duk wanda ya ke neman mafaka kuma
yana fata ***
annoba ya bayyana sai gashi matambayi ya zo
zuwa gare ka***
*** idan ka bada taimako to dukkan
bala'ai zai yaye ***
Idan ka kwarara to dukkan alheri zai
sauka ***
***idan ka yi rahama to dukkan cuta
zai katse ***
Idan ka warkar to dukkan cuta zai
sushe ***
*** kasa idan ta yi fari a shekara to
zai tafe ***
To wanene mai karanci a gare mu mai
yawan yawan kyauta mai yawn zubar da ruwan sama ***
*** idan annoba ya taho a kan
guiwansa a kwangwan nin mu ***
To wanene mai jin kai a gare mu ko
a'agajin gaggawa ***
*** idan ya yafe to Shi Mai karamci
Mai yalwa ***
Idan Ya yi hukunci to Shi ne mai
hukunci na a'adalci
Ku yi salati da sallama ga
Ahmad mai shiriya mai ceto ga
halittu.