الأربعاء، 23 ديسمبر 2020

SHI NE ALLAH

 

خطبة الشيخ  أحمد الطالب

المترجم : أمين سعد

اللغة : الهوسا

التاريخ : 4-5-1442هـ

 

 

HUDUBAR MASALLACIN ANNABI NA SHAIKH AHMAD –ADDALIB

4-5-1442AH 18-12-2020AD

 

HUDUBAR FARKO

Dukkan yabo  da godiya sun tabbata ga Allah  muna gode masa kuma muna neman taimkonSa kuma muna neman gafararSa, muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu, da munanan  ayukanmu duk wanda Allah y shiryar da shi babu mai batar da shi  kuma duk wanda ya batar da shi babu mai shiryar da shi .

Kuma na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah  shi  kadai yake bashi da abokin tarayya , kuma na shiada Annabi Muhammadu bawansa ne kum ManzonSa ne , kuma zababbenSa ne cikin halittunSa , kuma badadayinSa ne,  ya isar da sako kuma ya bada amana  ya yi nasiha wa al'uma  ya yaye bakin ciki ya yi jahadi don Allah cancancin jahadi ,  har mutuwa ta zo mi shi ,tsira da amincin Allah su tabbata agare shi  da iyalan gidansa tsarkaka  da kuma matayen sa  uwayen muminai da  sahabbansa  masu hasken hannaye  da kuma wanda ya bisu da kyautatawa zuwa ranar sakayya .

 BAYAN HAKA:

Lallai mafi gaskiyan zance shi ne littafin Allah , mafi alherin shiriya shi ne shiryarwan Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi , mafi sharrin al'amura kuma su ne fararrun ta , kuma  dukkan fararrun abu bidi'a ne dukkan bidi'a bata ne, dukkan bata na wuta .

Ya ku Muminai:

Lallai Allah ya kira ku ne da suna na imani ,  kuma ya kira ku da ku ji tsoronSa kuma ya umarce ku da ku yiwa kanku hisabi kafin  a yi muku hisabi, dubi zuwa ga  abin da kuka tanada mata kafin komawa , ya muku gargadi game da manta ta, da kuma  radadin hasarar ta  ya sanar da ku fifikon hali da za a shiga a ranar  komawa gare shi  , da girmar tasirin alkur'ani da an saukar da shi ga duwatsu , ya kuma sanar da ku da kamalar sunayenSa masu daraja da kaye .

 Shi ne Allah wanda  zukata  take bauta mi shi bisa kauna da  rusunawa  da tsoro,  da tsammani da kushu'i , da fata da kuma firgici .

Shi ne Mai gaskiya duk  abin da ke koma bayan shi bata ne, kuma mai gushewa, ba abin bautawa da gaskiya  sai shi, gani bai  iyakance shi,  tunani baya  riskan shi, sutura baya mishi shamaki, sirri baya boyuwa gare shi, da izinin shi ne falaki ya ke juyawa mai kewayawa, da hukuncinSa da hikimarSa dare kan saba da wuni..

Ma'aboci rahama mai yalwa mai dorewa, ya daidaita bisa mafi yalwan halittunSa.Da  mafi kyaun sunayen sa da mafi yalwan sifofinSa, (Mai rahama , Ya daidaita  a kan Al'arshi. Abin da ya ke a cikin sammai Nasa ne, da abin da ya ke  a cikin kasa  da abin da yake a tsakaninsu  da abin da ke karkashin  turbaya .

Kuma  idan  ka bayyana da  magana, to, lalle Shi, Yana sanin  asiri da mafi  boyuwa . Allah babu abin bautawa  face  Shi . Yana da sunaye  mafiya  kyau.)

RahamarSa ta yalwaci halittu wurin samarwa da tattalawa da taimakawa  da shiryarwa  da zabarsa ga waliyyanSa, halin shiryarwa da kuma datarwa  da tattalawa  har  ya kaisu ga matabbatar rahamarSa da ni'imar aljannarSa,  mulki mai zartuwa na iko a duniya da aikinSa ne da umarninSa , mamallakin sarakuna da abin da aka mallaka da malakuti da falakoki , yana bada mulki ga wanda ya so ya kwace ga wanda ya so ,  ya daukaka wanda ya so ya kaskantar da wanda ya so,  alheri na hanunSa, kuma shi yana da iko ga dukkan komai.

(UmarninSa, idan Ya yi nufin wani abu , sai Ya ce masa kawai, ''Ka kasance,'' sai yana kasancewa (kamar yadda Yake nufi).

Ya tsarkaka daga dukkan tawaya sabo da kamala , ya kubuta daga dukkan aibi  sabo da kyau ,  ya tsarkake abin da ya so sabo da albarka da daukakawa, ya amintar da wanda ya so bisa ga wanda ya so sabo da daukakawa da kaskantarwa.

 (makoma), shine amincin masu tsoro, kuma mafakan masu yankewa don ibada , ba aminci  Ya yi imani na da fadinSa cewa shine gaskiya Mai kasaita, kuma muminai sun yi imani da  shi bisa dadin rai a fadi da aiki, saura halittu kuma suna da'a  bisa tilas  a karshe ba zaman lafiya sai daga gare shi kuma zuwa gare shi,  rinjayin iko a ilimi da umarni  da shaidawa da karfin mulki  da amfanarwa da cutarwa  a sirrace da a bayysane duka na shi ne .

Ya buwaya bisa ga halittunSa wanda tsarki ya tabbata a gare shi  a karfi da kudura da galaba  da hani .

Ya karya  garkuwan halittu bisa umarninSa da haninSa a shari'a da kaddara  da karfin mulki , ya karya garkuwan su  ta karaya da talauci , da tsanani da cuta ,  bisa jin dadi da wadatarwa  da gamsarwa  da kuma saukakewa da taimakawa.

Shi ya fi komai girma da daukaka da daraja da sha'ani  da zati da sifa  da ayyuka  da iko, to ko wani abu kasa da shi ya ke karami ne abin renarwa  ya tsarkaka daga dukkan wani abokin tarayya , kuma ya daukaka ba wani abu kwatankwacinSa shi mai ji ne kuma  mai gani , ya yi halitta daga babu  sai ya bayyana  shi  ya halicci iska sai ya sanya mishi wuri  ya suranta a mahaifa sai ya rarrabe , ya kadaita da sunaye , wanda suka kai kololuwa wurin kyawu a lafazi da ma'ana  , ko wani abu ya yi tasbihi a gare shi  yana mai tsarkake shi  da dukkan harshe .

Allah ya buwaya daga makamanci  ko kini, ko kishiya da majibinci da mataimaki. Ya kyautata halitta a hukunci da hikima, shine Al hakku  kuma maganarSa gaskiya ce, hukuncinSa adalci ne alkalancinSa ne  mai rabewa (kat), babu kusakurai ko zamewa, ba wani abu da zai fita daga iliminSa na aiki ne ko fadi, Shi Mai hikima ne gwani.(Ya ku wadan da suka yi imani  ku ji tsoron Allah kuma rai ya dubi abin da ya gabatar domin gobe , kuma ku bi Allah da takawa . Lalle Allah  Mai kididdigewa ne ga  abin da  kuke aikatawa.

Kuma kada  ku kasance  kamar wadanda suka  manta  Allah,  Shi  kuma Ya mantar  da su rayukansu . Wadannan  su ne fasikai .

'Yan wuta da 'yan aljanna basu daidaita , 'yan aljanna su ne masu babban rabo.

 Da mun saukar wannan Alkur'ani akan dutse , da lallai ka ga dutsen yana mai tawali'u mai tsatssagewa sabo da tsoron Allah, kuma wadancan misalai muna bayyana su ne ga mutane da fatan za su yi tunani .

(Wanda ya saukar da Alkur'ani) Shi ne Allah wanda babu wani abin bautawa face shi masanin fake da bayyane , shi ne mai rahama mai jin kai .

Shi ne Allah wanda babu abin bautawa  face shi Mai mulki mai tsarki , aminci , Mai amintarwa Mai tsarewa Mabuwayi Mai tilastawa  Mai kamun kai , tsarki ya tabbata a gare shi daga abin da suke yi na shirki da shi.

Shi ne Allah mai halitta mai ginawa  Mai surantawa Yana da sunaye masu kyau , abin da ke a cikin sammai da kasa suna tsarkake shi, kuma shi ne mabuwayi  Mai hikima ).

Allah ya sa mini albarka ni da ku a cikin Alkur'ani mai girma , ya amfane ni da ku da abin da ke cikin shi na daga ayoyi da ambato mai hikima, ina fadin wannan maganar tawa  ina neman gafarar Allah wa ni kai na da ku da sauran musulmai daga dukkan zunubai , kuma ku nemi gafararSa , lallai shi mai gafara ne mai jin kai .

HUDUBA TA BIYU

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah  wanda ya isa, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi zababbe  da iyalansa da sahabbansan , da wanda suka bi sawunsu .

Bayan haka:

To ku ji tsoron Allah ya ku bayin Allah , lallai mafi alherin guzuri shi ne tsoron Allah, kuma ku yi riko da igiya mai karfi na musulunci .

Ku yi salati da aminci…. Ya ku bayin Allah  karshe da kuma adu'a.

 

       

 

 

  

     

   

 


 


 

 


 

 

 


 

 


 

 


 

 


 

 


 

 


 

 


 

 


 

 

 

الجمعة، 11 ديسمبر 2020

CUTAR DA MUSULMI

 

ترجمة

خطبة المسجد النبوي للشيخ حسين آل الشيخ

اللغة : الهوسا

المترجم : أمين سعد

التاريخ : 26/4/1442هـ

HUDUBAR MASALLACIN ANNABI NA SHAIKH HUSAIN AL-ASSHAIKH 26-4-1442AH 11-12-2021AD

 

HUDUBAR FARKO

 

Cutar da halittu   da sabbaba hakan ba tare da hakki ba  na daga cikin hanya mafi hadari ga mutum. Wannan ita ce hanya irin ta shaidanu tana tasowa daga sabani  da gaba da  rikici na kashe juna, tare da rasa ginshiki na rahama  da hali irin na tausayi, da jinkai.

Lalle cutar da bayi dabia ce mara kyau abin zargi ne da  ta tattaro sifofi daban daban  na laifi da abubuwa masu halakarwa.

Lalle sake linzami ga rai ya cutar da wasu  da harshe ne ko a aikace  bai fitowa sai daga masu raunin imani da biye ma son rai, wanda bata da rai mai yawan umarni da mummuna da alfahasha.

To ka kare kanka daga cutar da wani - ya kai musulmi - ka yi wa kanka gargadi daga halaka   zaka kubuta ka rabauta a duniya da lahira Allah Madaukakin Sarki yace :  (Wadannan  da suke cutar da muminai maza da mata ba da abin da suka aikata ba suke jifansu hakika sun lafta karya da zunubi mabayyani ga kansu)

Allah subhanahu yana cewa : ( Wanda ya aikata kuskure karami ko babba sannan ya dorawa wanin sa to hakika ya girba karya da zunubi mabayyani)

   Kuma Manzonmu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bayana littafin Ubangijinsa ya fassara shi yayi  bayanin wadannan ayoyi  daki – daki, ta hanya mutawatiri da aka karbo daga gare shi yana mai gargadi mai tsanani da jan hankali mai karfi bisa cutar da wani  da zaluntar su da musu shisshigi da wuce iyaka wajen cutar da su, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace :(Musulmi dan uwan musulmi ne ba zai zalunce shi ba ba zai rena shi ba ba zai  tabar da shi ba) Muslim ne ya rawaito.

Kuma ya fitar a hadisin hana zama a kan hanya Annabi  ya bayyana cewa (Na daga cikin hakkin hanya kamewa daga cutarwa)

 ya kai musulmi

ka kiyaye kyawawanka ka kare addininka, ka kame daga cutar da waninka, ka kasance kamar yadda Fudail Bin Iyad yace :(Ba ya halatta a gare ka ka cutar da kare ko alade ba tare da hakki ba, to ina ga halitta mafi daukaka )

Matsanancin hani ya tabbata daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi

Game da cutar da musulmi sai ya ce : (ya tawagan wadanda suka yi imani da harshensu a halin imani bai fantsama cikin zuciyarsu ba, to kar ku cutar da musulmai  kar ku aibata su kada ku bibiyi  al'aurarsu, to lallai wanda ya bibiyi al'aurar dan'uwansa musulmi to Allah zai bibiyi al'aurarsa, kuma duk wanda Allah ya bibiyi al'aurarsa to zai kunyata shi ko da kuwa a tsakiyar gidansa ne ) Tirmizi ne ya rawaito.

Katada yace :(Na hore ku da ku nesaci cutar da mumini domin Allah na kewaye da shi kuma yana iya yin fushi dominsa.)

Ya kai bawan Allah!

Ka kubutar da kanka daga cutarwa , ka hana kanka daga zalunci da ketare iyaka zaka kubuta daga  walakanta da halaka.

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Musulmi shine wanda musulmai suka kubuta daga sharrin harshensa da hanunsa) Buhari ne ya rawaito.

Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Duk wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira to kada ya cutar da makwabcinsa) Buhari ne ya rawaito. A gun muslim kuma (Ba zai shiga aljanna ba duk wanda makwabcinsa bai aminta da sharrinsa ba)  wato sharinsa da mugayen halinsa.

 

Ya  'yan uwa musulmi

 

A duniyar  yau akwai abin da ake cewa kafofin sadarwa ta sada zumunta,wanda wasu ke amfani da shi wajen cutar da musulmai da suka ga mahukuntansu da malamansu da daidaikunsu. Da al'umominsu  da maganganu na fajirci da yada jita –jita marasa kan gado. To masu yin wannan lalle su tuna cewa : Allah na dakon su a madakata, kuma lalle mizani ya hada da kyawawa da munana  to su kiyaye kada su je ga Ubangijinsu suna halin Muflisai wadanda suka shiga cikin rudani sun yanke tsammani, - muna rokon Allah afuwa da waraka-.

Lalle haramcin cutar da musulmi bai tsaya ga cutar da daidaiku ba, sai dai ya game da cutar da musulmai cikin maslahohinsu da ya shafi kowa da kowa.da abubuwan amfaninsu da ake tarayya kamar kayakin  al'uma mallakin gwamnati, na daga tushe na musulunci akwai (Ba cuta ba cutarwa).

   Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: (ku tsoraci abubuwa biyu masu janyo  tsinuwa : wanda ke bahaya a  hanyar mutane ko inuwar su).Muslim ne ya rawaito.

Dabarani ya fitar  da sanadi hasan daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace ; wanda ya cutar da musulmai a kan hanyar su to tsinuwa ta tabbata a gare shi).


 

Huduba ta biyu

Ya dan uwa musulmi !

Ka sabarwa kanka da kubuta daga cutar da halittu, ka tsarkake ta daga zaluntar wasu a zahiri da badini,  ka sani kubutar da rai daga shirka  da bidiah , da kullin zuci da hasada da kyashi da muzanta musulmai da zaluntansu na daga cikin sabuba na kubuta. Kuma sifa ce daga cikin sifofi na 'yan aljanna . Allah Madaukakin sarki ya ce game da khalilin sa Ibrahim in da ya roki Ubangijinsa game da abin da ya roki Ubangijinsa da shi,( kada ka kunyatar dani ranar da ake tashin mutane) kuma Allah ya ce (Mun fitar da abin da yake cikin kirzansu na daga keta, halin kasancewarsu  "yan uwa, suna kan gadaje suna kallon juna ).

 Hakika hadisai da yawa sun inganta wurin bayyana falalan lafiyan  zuciya  ga musulmai  daga gaba da kiyayya da nufin muzantawa, na daga ciki akwai mutumin na da ya zo daga cikin Ansarawa  wanda Annabi ya yi mar shaida da cewa dan aljanna ne, Abdullahi dan Amru Dan As ya bibiyi wannan mutumin har ya taho ya yi kwanaki uku a gidan mutumin, amma bai ga wani abu na daga kyawawan ayyukan shi ba irin su tsayuwan dare ba, face in ya tashi cikin dare daga makwancinsa sai ya ambaci Allah  yayi kabbara har zuwa ya tashi don sallar Asubahi, bai fadi wani abu ba face alheri, sannan Abdullahi ya bashi labarin abin da Annabi ya fada game da kissarsa, sai mutumin yace da shi game da ayyukansa shi bai yin wani abu face abin da ka gani sai dai ni ba na rike wani musulmi a cikin zuciya ta kuma bana hasada ga wani bisa wani alhairin da Allah ya bashi  saiAbdullahi ya ki cewa lale wanan itace wanda ta kai ka wanan matsayin da ba zamu iya ba.   

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 


 

 


 

 

 

السبت، 5 ديسمبر 2020

 

 

بسم الله الرحمن الرحيم

HUDUBAR FARKO

 

Yabo ya tabbata ga Allah; Ma'abucin buwaya da karamci, Wanda ya kagi halitta, Mai yalwar falala da ni'imomi, Ina yin yabo ga Ubangijina, kuma ina gode masa kan ni'imominSa wadanda muka sani, da kuma wadanda bamu sani ba.

Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya, sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya, Mafi girman buwaya da karamci,

kuma ina shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawansa ne Manzonsa, Wanda Allah ya bashi dunkulallun kalmomi (na jawami'ul kalim).

Ya Allah! ka yi dadin salati, da sallama da albarka ga bawanka kuma Manzonka; Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa, wadanda aka shiryatar da su ga hanyar da ta fi mikewa,

 

Bayan haka:

Sai ku yi takawar Allah Mabuwayi da daukaka, ta hanyar neman kusanci zuwa gare shi da aikata kyawawan ayyuka, da kuma nisantar ayyukan haramun, saboda babu mai tsira (a wurin Allah) face masu takawa, kuma babu mai tabewa ya yi hasara face masu bin soye-soyen zukata, da masu sakaci.

 

Ya ku, Musulmai… !!!

Ku yi hisabi ga kayukanku gabanin a muku hisabi, kuma ku farkar da zukatanku daga gafalarsu, kuma ku kame rayuka daga aukawa cikin dadi irin na haramun, kuma ku yi gaggawan tuba, gabanin saukowar ajali, da yankewar guri, da katsewan yin ayyuka, domin kuna ganin saurin tafiyar shekaru, da gaggawar tafiyar kwanaki.

Kuma babu komai a bayan wannan rayuwar face mutuwa, kuma babu komai a bayan mutuwa face shiga gidan ni'ima, ko gidan azaba mai radadi.

Kuma kamar yadda kuke aiki domin duniya mai karewa, to sai ku yi aiki domin lahira mai wanzuwa, Allah Ta'alah ya ce: "Kawai, kuna fifita rayuwa ce ta Duniya * alhalin Lahira itace mafi alheri kuma mafi wanzuwa" [A'alah: 16-17].

 

Ya ku, Musulmai… !!!

Ku rungumi littafin Ubangijinku, domin daukakarku da rabautarku da gyaruwar lamuranku, duka a cikinsa suke, kuma a cikinsa samun rabonku bayan mutuwarku yake, da kariyarku da tsirarku daga fitintinu wadanda suke yawaita duk lokacin da Kiyamah ta kara kusantowa, fitintinu wadanda suke da sarkakiya a farkon faruwarsu, sai kuma su bayyana su fito sarari a karshen lamuransu; don haka, babu wanda zai tsira daga fitintinu sai wanda yayi riko da Alkur'ani da Sunnah, kuma ya lazimci jama'ar Musulmai;

Sai ku yi tadabburi, ko nemi sanin ma'anar littafin Allah Mabuwayi da daukaka, kuma ku yi aiki da shi, sannan ku haddace abin da addini zai tsayu da shi, na sunnar Manzon Allah صلى الله عليه وسلم, kuma akida ta ingantu da shi, itama ibada ta samu kamala da shi, musamman hadisan da ma'anoninsu ya game hukunce-hukuncen Musulunci, wadanda suka kunshi falaloli, sai ku san ma'anoninsu, domin ku yi riko da su kuma ku yi aiki, domin wannan shine MANHAJIN MAGABATA NA KWARAI, wadanda Allah Ta'alah ya fada, akansu: "Masu rigayen farko daga Muhajirawa da Ansarawa, da wadanda suka bi su da kyautatawa, Allah ya yarda da su, kuma suma sun yarda da shi, kuma ya musu tanadin gidajen Aljannoni, koramu suna gudana a karkashinsu, suna masu dawwama a cikinsu har abada, wannan shine rabo mai girma" [Tauba: 100].

Kuma –a wannan matsaya- zan kawo hadisi daya daga cikin dunkulallun magana (Jawami'ul kalim), wanda ya wajaba kowane Musulmi namiji da Musulma suyi aiki da shi, a cikin kowane hali, kuma dole ne mazaje da mata su rika aiki da hadisin matukar akwai rai a cikin jikinsu, Wannan kuma shine, fadinSa –صلى الله عليه وسلم-: "Addini nasiha ne, addini nasiha ne, addini nasiha ne. Sai muka ce: Ga wa Ya Ma'aikin Allah? Ya ce: Ga Allah ne, da littafinSa, da ManzonSa, da kuma shugabannin Musulmai, da kuma sauran gama-garinsu", Muslim ya ruwaito shi, daga hadisin Tamim Ad-dariy (رضي الله عنه). Kuma wasu Maluma dayawa banda Muslim, suma sun ruwaito shi; daga cikin Maluman hadisi.

Kuma hadisi ne mai girman sha'ani, Imam Abu-dawud ya ce: "Fik-hu yana gudana akan hadisai guda biyar; hadisin halal a bayyane yake, haram a bayyane yake, da hadisin babu cuta babu cutarwa, da hadisin: dukkan ayyuka suna tare da niyyoyinsu, da hadisin: addini nasiha ne, da hadisin: Abin da na hane ku, ku nisance shi, wanda kuma na umarce ku, to ku zo da shi gwargwadon iko".

Kuma Alhafiz Abu-Nu'aimin ya ce: "Wannan hadisi ne da yake da sha'ani mai girma, Muhammadu bn Aslam Ad-duwsiy ya ambaci cewa, lallai hadisin addini nasiha ne, daya ne cikin kashi hudu na addini".

 

Yana daga cikin dalilan da suka nuna cewa; lallai wannan hadisin, wajibi ne ga kowane Musulmi namiji da kuma mace musulma, su yi aiki da shi, koyaushe, Lallai Allah Ta'alah ya dauke wasu ibadodi, ga wasu daga cikin Mutane, saboda wani uzuri, ko saboda wasu sababi, amma bai dauke yin nasiha ba, karkashin kowane uzuri, ko cikin kowane hali, Allah Ta'alah ya ce: "Babu kunci ga Maraunana, kuma babu laifi, ga majinyata, da wadanda basu samu abin da za su ciyar ba, matukar sun yi nasiha ga Allah da ManzonSa, kuma babu wata hanya (ta cutarwa) ga masu kyautatawa, Allah shine Mai yawan gafara, Mai jin-kai" [Tauba: 91].

Sai Allah ya bayyana cewa, ba za a yi uzuri ga wani Musulmi ba, kan yin watsi da nasiha, daidai da kyaftawar ido (koda yana da uzuri).

 

Sahabbai basu yi tambaya kan ma'anar nasiha ba, saboda sahabban sun san abin da kalmar take nuni akansa na ma'anonin addini mai fadi ta kowace fiska, domin hakikanin nasiha ya kunshi, martabobin addini uku na Musulunci da Imani da Ihsani.

Kawai abin da sahabbai suka tambaya, shine Ga wa ake nasihar, kuma wanene suka cancanceta?

 

Kuma asalin ma'anar nasiha, shine Tsamo abu ko cire shi daga abubuwan da suka shiga masa domin gurbata shi, a larabci ana cewa; Nasahal asala, wato ya tace zuma, idan Mutum ya tsaftace zumar daga kwansonsa.

 

Kuma MA'ANAR YIN NASIHA GA ALLAH TA'ALAH ya kunshi, Son Allah, da kan-kan-da-kai a gare shi, da rusuna masa, da mika-wuya ga shari'arsa, domin neman yardarSa da ladanSa, da kuma tsoron fushinSa da azabarSa, Allah Subhanahu ya ce: "Kawai masu imani da ayoyinmu, sune wadanda idan aka fadakar da su da ayoyin, sai su fadi suna masu sujada, kuma suna yin tasbihi game da gode wa Ubangijinsu, alhali ba su yin girman kai * sasanninsu suna nisantar wuraren kwanciya, suna kiran Ubangijinsu bisa ga tsoro da tsammani, kuma suna ciyarwa daga abin da muka azurta su" [Sajada: 15-16].

Kuma AllahTa'alah ya ce: "kuma Masu imani sune masu tsananin so ga Allah" [Bakara: 165].

Kuma Annabi صلى الله عليه وسلم  ya ce: "Ku so Allah daga dukkan zukatanku, saboda abin da yake ciyar da ku da shi, na ni'imomi".

 

        Kuma mafi girman nasiha ga Allah, itace bauta masa Subhanahu, ba tare an hada shi da abokin tarayya ba, cikin tsarkake niyyah, da aiki da Sunnah da bin shiriyar annabi Muhammadu صلى الله عليه وسلم, da kebance Ubangiji da na'ukan ibadodi dukkansu, kamar addu'a da neman taimako, agaji, da tawakkali, Allah Ta'alah ya ce: "Ka ce, lallai kawai ina rokon Ubangijina ne, ba zan masa shirki ko hada shi da kowa ba" [Jin: 20].

        Shi kuma Ubangiji Mabuwayi da daukaka ana masa bauta ne, saboda abin da yake da su na sifofin kamala da girma, da kuma yadda ya tsarkaka daga sisfofin tawaya (nakasa), da kuma saboda abin da Allah yake da su na ni'imomi ga halittunSa, da bukatuwan bayi zuwa ga rahamarSa; don haka: Ita ibada sababi ce na samun alherorin Allah, kuma sababi ce na tunkude sharrace-sharrace ga Mutum, a cikin rayuwarsa da kuma bayan mutuwarsa.

 

        Kuma nasiha ga Allah Tabaraka wa Ta'alah tana kasancewa ta hanyar tabbatar wa Allah abin da ya tabbatar wa kansa a cikin littafinSa, da kuma abin da ManzonSa ya tabbatar masa da su; na sunaye da sifofi, akan abin da magabata na-kwarai suka kasance akansa, Allah ya yarda da su, amin. An ruwaito daga Abu-Umamah رضي الله عنه daga Annabi صلى الله عليه وسلم, Allah Ta'alah ya ce: "Mafi soyuwan abin da bawana ya bauta min da shi, shine yin nasiha a gare ni", Ahmad ya ruwaito shi, da 'Dabaraniy a cikin mu'ujam kabir.

 

        Kuma ma'anar yin nasiha ga Manzon Allah صلى الله عليه وسلم itace: son annabi da darajanta shi da girmama sunnarsa, da aiki da umurninsa, da hanuwa da haninsa, da yin bauta wa Allah da shari'arsa, da bibiyar shiriyarsa, da gaskata labarunsa, da yada hadisansa, da yin da'awa zuwa ga addininsa, Allah Ta'alah ya ce: "Ka ce: Ku yi da'a ga Allah, kuma ku yi da'a ga Manzo, amma idan kuka bijire, to lallai akansa akwai abin da aka aza masa, kuma akanku akwai abin da aka aza muku, kuma idan kuka masa da'a zaku shiryatu" [Nur: 54].

 

Kuma ma'anar yin nasiha ga Littafin Allah Ta'alah itace: Girmama Alkur'ani mai karamci, da sonsa, da yin kokari wajen koyan karatunsa da karantar da shi, da neman sanin hukunce-hukuncensa, da yin tilawarsa tilawa ingantacciya, da yin aiki da umurnin Alkur'ani, da barin haninsa, da dawwama kan tilawarsa, da kiyaye harrufansa da iyakokinsa, da sanin tafsirinsa da ma'anoninsa, da abin da aka nufa da shi, da yin tunani cikinsa, da dabi'antuwa da shi, da yin raddi ga wadanda suka karkata wajen fahimtar Alkur'ani da sunnah, tare da ruguza barnace-barnacensu, da tsawatarwa akansu, Allah Subhanahu ya ce: "Lallai wannan Alkur'anin yana shiryatarwa zuwa ga hanyar da tafi kyawu" [Isra'i: 9].

 

Kuma ma'anar yin nasiha ga Shugabannin Musulmai itace: So musu alheri, da son su yi adalci, da yin farin-ciki idan aikinsu ya yi dace, da nisantar algus a gare su, da kin ha'intarsu, da kuma (uwa uba) kada Mutum ya yi fito-na-fito da su, ko ya taimaki makiya akansu, tare da taimaka musu cikin lamarin gaskiya, da yin biyayya a gare su cikin abin da ba sabo ba, da yin addu'ar dace a gare su, da addu'ar dacewa da gaskiya a cikin hukuncin da suke yi, An ruwaito daga Abu-hurairah (رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), ya ce: "Lallai Allah yana yarje muku abu uku, yana yarje muku, ku yi bauta a gare shi; kada ku hada shi da kowa, kuma ku yi riko da igiyar Allah gaba daya, kada ku rarraba, kuma rika nasiha ga wadanda Allah ya jibinta musu lamuranku", Muslim ya ruwaito shi.

Abdullahi bn Mas'ud رضي الله عنه ya ce: "Lallai abin da kuke kyama alhalin kan jama'a yana hade shine mafi alheri akan abin da kuke so, a halin rarrabuwa".

Kuma nasiha shine amincin zuciya

Kuma an ruwaito dagaabin da Jubair bn Mud'im, daga Annabi صلى الله عليه وسلم ya fada a cikin hudubarsa a masallacin Khaif (dake Minah): "Abu uku zuciyar Mutum Musulmi baya daukar kyashi akansu; Tsantsanta aiki ga Allah, da yin nasiha ga Majibinta lamura (shugabanni), da lazimtar jama'ar Musulmai", Ahmad ya ruwaito shi da Alhakim.

Kuma an ruwaito daga Ma'akil bn Yasar, daga Annabi صلى الله عليه وسلم ya ce: "Babu Mutumin da Allah zai bashi wani abin kiwo, sai bai kewaye su da nasiharsa ba, face ba zai shiga Aljannah ba", Bukhariy da Muslim da Ahmad suka ruwaito shi.

 

Ita kuma ma'anar nasiha ga dukkan Musulmai itace: Fadakar da su zuwa ga maslahohinsu, da ilmantar da su lamuran addininsu, da sitirce al'aurarsu, da kokarin toshe ko biya musu bukatu, da nisantar algus ko ha'intarsu, da nisantar yin hasada a gare su, da kyautata musu.

Nasiha sifa ce ta Annabawa da Manzanni Amincin Allah ya tabbata a gare su, Allah Ta'alah ya ce:( Hakika manzo ya zo muku daga cikinku mai jin nauyin abin da ya wahalar da ku, mai muku fatan alheri kuma mai tausayi da jinkai ne ga muminai)

Kuma yace game da Nuhu Amincin Allah ya tabbata a gare shi( Ina isar muku da sakon Ubangiji na kuma ina muku nasiha) Kuma yace game da Hudu Amincin Allah ya tabbata a gare shi( Ina isar muku da sakon Ubangiji na kuma ni a gare ku mai nasiha ne amintacce).

Kuma yace game da Salihu Amincin Allah ya tabbata a gare shi :( Hakika na isar muku da sakwannin Ubangiji na kuma na yi muku nasiha)

Nasiha sifa ce ta mumunai Allah Mai tsarki da daukaka ya ce game da muminin Alu Yasin : ( ya ku muta ne na: ku bi manzanni) (sai aka ce : ka shiga aljanna sai yace ina ma da mutane na sun sani)

Ibnu Abbas Allah ya yarda da shi ya ce :  ya yi nasiha ga mutanensa a halin yana raye da bayan ya mutu.

  Allah Ta'alah ya ce: "Lallai Muminai 'yan'uwan juna ne", [Hujurat: 10] " (Kuma ku yi riko da igiyar Allah gaba daya, kuma kada ku rarraba" [Ali-imrana: 103],

 

Allah ya yi mini albarka NI da KU, cikin alkur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abin da ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,      Na fadi abinda ku ke ji, kuma ina neman gafarar Allah Mai girma ga Ni da KU da sauran Musulmai daga kowani zunubi, Ku nemi gafararSa,    lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.


 

HUDUBA TA BIYU

        Yabo ya tabbata ga Allah Masanin abin da ya buya na gaibu, Mai jujjuya zukata, Mai yaye musibun da suka sauka da bakin ciki, Ina yin yabo ga Ubangijina kuma ina gode masa akan ni'imominSa gaba daya; wadanda suka gabata da wadanda zasu zo,

Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai yake bashi da abokin tarayya, Mai yawan gafarar zunubai,

Kuma ina shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawanSa ne ManzonSa zababbe,

Ya Allah ka kara salati da sallama da albarka ga bawanka kuma Manzonka Muhammadu, da iyalansa, da sahabbansa madaukaka, masu takawa.

 

Bayan haka … !!

Sai ku yi takawar Allah Ta'alah, a asirce, da kuma a bayyane, domin da takawa ne zaku samu mafi kololuwar daukaka, kuma ku rabautu da alkhairori a wannan rayuwar, da kuma bayan mutuwanku,

 

Ya ku Bayin Allah … !!

Ku yi tunani akan fadin Allah Ta'alah: "Kuma Muminai maza da mata, sashensu majibincin sashe ne, suna yin umurni da kyakkyawa, kuma suna hani da abin da ba a so, kuma suna tsayar da sallah, kuma suna bayar da zakka, kuma suna da'a ga Allah da ManzonSa, wadannan lallai Allah zai yi rahama a gare su, Lallai Allah Mabuwayi ne Mai hikima" [Tauba: 71]. A cikin wannan ayar akwai taimaka wa juna, da tallafar juna, da nasiha wa juna, da agaza wa juna, da 'yan'uwantaka, da jin-kai da rahama da kauna.

        Kuma an ruwaito daga Jarir bn Abdullahi, ya ce: "Na yi mubaya'a ga Manzon Allah صلى الله عليه وسلم akan tsayar da sallah, da bada zakka, da yin nasiha ga kowane Musulmi", Bukhariy da Muslim su ka ruwaito shi.

Kuma Abubakar Almuzaniy ya ce: "Abubakar رضي الله عنه bai fi sauran Sahabban Manzon Allah صلى الله عليه وسلم yawan azumi ko salla ba, saidai ya yi fice ne da wani abu da ya tabbatu a cikin zuciyarsa",

Ibnu-Ulayyah ya ce: "Abin da ya kasance a zuciyar Abubakar shine, soyayya don Allah Mabuwayi da daukaka, da yin nasiha ga halittarSa".

        Kuma an ruwaito daga Hakim bn Abiy-Yazid, daga Babansa, daga Annabi صلى الله عليه وسلم ya ce: "Idan dayanku ya nemi nasihar dan'uwansa, to ya masa nasiha", Ahmad ya ruwaito shi, da 'Dabaraniy a cikin mu'ujam kabir.

.

        Ya ku Bayin Allah… !!!

        "Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan Annabin, Ya ku wadanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da sallamar amintarwa" [Ahzab: 56].

Ya Allah! Ka yi salati da sallama wa Annabi Muhammadu,