Hudubar Masallacin Annabi na sheikh Salah Dan Muhammad
AlBudair.29 zulhajji 1440AH
Hudubar Farko
Ya ku musulmai
Kokari zuwa
ga halaye na mutunci da kyawawan dabi'u dabi'a ce na masu juriya kuma al'ada ce
na masu kokari, ilimi shi ne daukaka mai daga darajan mai nemansa kuma aga
kiman ma'abocinsa a ido , duk wanda ya so ilimi to falalolin shi kuwa zai
kewaye shi abubuwan adonsa su sauka a farfajiyansa. Almuzani ya ce : "na ji shafi'I Allah ya yarda da shi yana cewa duk
wanda ya nemi ilimin alkura'ani to kimarsa za ta kara girma duk kuma wanda ya
yi nazarin ilimin fikihu matsayinsa zai yi kyau, duk wanda ya rubuta hadisi zai
zama yanada karfin hujja duk wanda ya yi nazari a ilimin lugga dabi'arsa za ta
tausasa, duk wanda yayi nazari a ilimin hisabi ra'ayin shi zai yawaita duk
wanda bai kare kansa ba to iliminsa ba zai mishi amfani ba" .
Al'umma na samun karfi ne ta hanyan ilimi ### hukunci a cikin zamani ana danganta shi ne
zuwa ga alkalami ###sau da yawa tokuba na zubar da jini #### alkaluma kuma na
zubo da hikimomi ###da mutane za su yi a'adalci ### da falala a tsakaninsu zata
kasance ne ### ta hanyar digon tawada ba
ta hanyar zubar da jini ba ### ka dukufa wurin neman ilimi #### za ka kai
kololuwa a matsayi ### a falala wanda
yana kumshe da daukaka da karamci.
ilimi a lokacin
fitina ya na baka kariya, a lokacinci
kadaici yana dauke ma kewa yana sanya daukaka a cikin iyalai
ya ku musulmai:
ga sabuwar
shekarar karatu ta kunno kai nan ba da jimawa ba za a bude makarantu da jami'o'i
za a karbi dalibai da kauna da maraba to saboda haka ga wasu wasiyyoyi ga
dalibai maza da dalibai mata game da wannan munasabar:
Ya kai dalibi
to ka koma makaranta tare da kwadayin karatu da farinciki da annashuwa da himma
da kokari ka cire mutuwan jiki da jin tawaya da sakaci da kasala .
samun daukaka na ga kokari ### rasawa kuma na ga
kasala ### to ka kafu za ka samu cimma
burinka nan kusa ### lallai matashi
wanda ya siffantu da himma irin na mutanen farko ### kuma bai saba rage zance
ko aiki ba duk wanda ya sarayarda himma to ba zai cimma bukatunsa ba ### duk
wanda ya yi jifa da kifiyoyi na ji ji da kai to ba zai samu ba .
Hakika mai
himma ma'aboci hankali za iya cimma gaci ta hanyar da'a ga himmarsa da kuma
sabawa son rai.
ya ku dalibai
: ku yi sammako ku gaggauto zuwa ga ajin karatu, na horeku da ku nesaci jinkiri da ja da baya domin a cikin sammako
akwai albarka da samun arziki da najahi da kuma dace, Tirmizi ya rawaito daga sakr dan gamidi Allah
ya kara yarda a gare shi ya ce : Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata
a gare shi ya ce (ya Allah ka sa albarka ga
alummata a cikin sammakonta , sai ya ce ya kuma kasance idan ya tura mayaka ko kuma runduna yana
turasu ne a farkon wuni sakru ya kasance mutun ne dan kasuwa ya kasance kuma
idan ya tura kasuwanci yana tura su ne da jijjifi sai ya zama hanshakin mai
kudi dukiyarsa ta yawaita)
Samun
albarkan rana baya tabbatuwa sai da riskan sallan asubahi domin lallai sallan
asubahi tamkar wata iska ce mai kamshi da wani yanayi mai dadi ku sammaka kuma
ku yi katanga da adu'oyi na neman kariya
da azkar da suka zo daga annabi wadanda suke jefa debe kewa a cikin rayi da
farin ciki a cikin zuciya su kara karfi da nashadi a jiki da kariya da kiyayewa
,duk wanda ya bawa ransa rabonta na more rayuwa da mutuwan jikin da sabo da
jinkiri da bacci daga barin aikin shi da makarantan shi da hissarsa na karatu
to hakika zai rasa manufarsa danashinar sa
zata yi girma, duk wanda ya yawaita kwanciya to zai rasa biyan bukata wanda ya
lizimci kasala to zai yi asaran fatarsa shi mutun sakali mai kasala yana rayuwa
ne matsiyaci zai zama yayi nesa amma duk wanda ya yi hakuri to zai rabauta, da hakuri ne ake bude kofofin
da suke rufe kuma ayi dace.
Baccin safiya
wato yin bacci baya sallar asuba ya halatta sai dai idan zai kai ga sarayar da
wajibi, kuma baccin kailula wato baccin azahar mustshabbi ne saboda hadisin Anas
Allah ya kara yarda a gare shi ya ce
manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (ku
yi baccin kailula saboda shaidanu basa yin baccin kailula ) abu nua'im
ne ya fitar dashi
saboda kailula yana maida nashadi ga kwakwalwa
da kuma jiki yana taimaka wa wurin bita da sauke nauyin da ya wajaba akan mutun
da kuzari da kuma karfi da nashadi.
ku kiyaye
kashe dare da hira domin yana haifar da wahala da kuma sa nauyin jiki kuma
bala'i ne da ke bata yanayi, mutun ya kasa sakewa ya kashe mishi kuzari ya jefa
mishi gajiya na zuciya da jiki kada ka
fi karfin idanunka ka hana shi barci idan barci ya zo, ka yi barci a farkon
dare ka hutar da idanuwanka biyu, kada ka cutar da iyayenka, a ko wani safiya sau da yawa mun ga wanda ya
sarayar da aikin shi ko ya bar karatun shi ko kuma yayi sakaci da iyayen shi da
iyalan shi sakamakon bata dare kan abin da ya ke na haram abun zargi tare da
wasu abokan banza masu batarwa masu lalatarwa. ya kai dalibi ka yi kwadayin samun
ladabi da tsabta da tsarkin zuciya da girmama malami da lazimtan tsari da kiyaye abin da aka dora ma
na karatu, da kiyaye wurin karatu da kuma abin da aka dora ma na karatu na
makaranta, ka ji tsoron Allah domin Allah ba abin da ke boyuwa a gare shi na zuciya ba wani kwayan zarra ko
kwayan hancin dibino da zai shiga wa Allah duhu, ka sanya ilim shi ne babban
tattalinka ladabi ya zama shi ne tufafinka ka kasance mafi cikan mutane ladabi,
mafi tsananinsu wurin kankan da kai, kuma ka zama ka fi su tsarkaka da kuma
addini ka zama ka fi su karancin shirme da kuma yawan fushi, ka abokanci
mutanen kwarai ka yi nesa daga mutanen sharri, kar ka kusance su kar ka aminta
da su kar ka yi cakudedeniya da su ko ka zauna da su, kada ka zauna zuwa ga
mutanen banza domin halayen wawaye yana raba
mafi sharrin mutane shi ne wanda bai damu mutane su gan shi ba yana
mummunan abu, duk wanda ya so yayi ababan mutunci to zai nesaci abubuwa na
haramun kar ka saki ganinka kada ka kafa ganinka zuwa ga waninka domin idanuwa tarkon
shaidan ne duk wanda ya saki ganin shi zai hadu da ajalin shi, na horeka kar ka
kai kanka wuraren abin tuhuma da abin da
zai haifar da shakku na horeka da kar ka yi abin daza ka zo kana bada uzuri ka
dauki izina daga waninka duk mutumin da luran shi ya yi yawa to kusakuren shi
za su karanta, lallai rabautacce mai samun sa'ada yana da abin wa'azi ga wanin shi
kuma yana mai daukan gogewa a matsayin abin da zai yi mishi hukunci abin da zai rika lura da shi, na gargade ka da
dukkan wani wasa wanda zai haifar da kiyayya ko ya zubar da kwarjini, ba daukaka shi ne a kyakkyawan tufafi ba sai
dai daukaka na nan ga ilimi ne da ladabi da addini, harshe waziri ne na mutun
idan baka iya fadan magana wanda ya ke na daidai ba to ka yi shuru daga abin da
yake ba daidai ba shi kanshi shi ne daidai, kada ka kasance cikin wanda ya ke
aibata wa sannan ya na yawaita zagi yana yawaita suka ga abokai kada ka bankado
laifukan mutane muddin sun boye sai Allah ya tona asirinka na daga laifuka, ka
ambaci kyawawan abin da ka gani a cikinsu a duk lokacin da aka ambace su kar ka aibata wani cikinsu a abin da kai ma
kana da shi kar ka yi abokantaka da mai kasala, Abubakar alkawarizmi ya na cewa
:" kar ka abokanci mai kasala a duk halayensa## sau da yawa mutun na
kwarai kan lalace sakamakon bacin wani## raban wawa zuwa ga mai wayo abu ne da
yake cikin sauri## baka ganin gaushi da ake dora shi a cikin toka shi ke nan
sai gaushin ya mutu ?
A tarbiyantar
da al'uma su taso kan kyawawan laduba wajibi ne da ya rataya ne a kan iyaye da
majibinta al'amura, wani daga cikin masu
hikima ya ce : "ku yi gaggawa ta hanyan ladabtar
da yaranku kafin shungulla su rarraba tsakaninku"
Ya ku dalibai
: ku yi gaugawa zuwa ga ilimi wanda dage
mishi ya dace agare ku, ku kiyayi
hayaniya da kuma gajiya da kosawa da kasawa da yankewa .
Ka nema kada ka yi hayaniya wurin neman, laifin dalibi shi
ne ya yi hayaniya ku nemi ilimi duk wanda ya nemi ilimi zai mikar da shi tun
yana karami kuma zai gabatar da shi idan ya girma.
Urwa dan
zubair ya ce :" 'ya'ya na 'ya'ya na ku nemi ilimi
in kun kasance kanana ba a bukatanku, to ya wuci ku zame manya ba za a wadatu da ku ba."
ku yi kwadayi
bisa makarantu domin makarantu su ne
wurin dashe, duk wanda darasi ya kwace mishi to dashe ya baci mishi, ku dimanci
kallo a cikin littafi kada ku gaji daga leke leke a littafi da bincike da
karatu da kuma daukan rubutu da bita da kuma mudarasa a tsakani da hadda.
Ibnul jauzi
Allah ya mishi rahama ya ce : da zan ce lallai ni din nan na tsinkayi littafi
littafi da ya kai mujalladi dubu ashirin kai dama sai na ce ma ya kasance ya fi
haka a lokacin da na ke nema,
Ya ku
dalibai kokari kokari a tsakanin
alkaluma da kuma litttatafai da tawada da abun rubutu har ku riski burinku,
wasunsu suka ce na yi kura shekara arba'in ban yi kailula ba ban kwanta ba face
littafi na dore akan kirji na an tambayi Imamu Ahmad bin Hanbal Allah ya mishi
rahama zuwa yaushe ne mutun zai nemi ilimi sai ya ce "tare
da kurtun tawada har zuwa akai shi makabarta" ya kai dalibi kasa
natsuwa da bi a hankali da kaifin hankali na horeka da kar kayi gaggawa a wurin
tafiya da hauka da nuna danyen kai da yaranta, wanda ke koro sharri ya jefa
mutun cikin nadama hakika wanda ya bi a tsanaki zai iya riskan hajarsa wanda ya
yi gaggawa kuma zai iya fadawa cikin kuskure, duk wanda ya yi amfani da wayar
salula a yayin da yake tuki to hakika ya kai kansa ga hatsarin mutuwa ya kai
kansa zuwa ga bakin halaka da abin da ya ke makruhi saboda waya yana dauke
hankali da ji ya sa mutun ya rasa kulawa da halartowa da hankali duk mutuninda
idonsa ya kafu akan waya ya saki kunnuwarsa ya sunkuyar da kansa da kafadunsa
ya shagalta da tattaunawa da ture ture da yada tagrida da ababan kallo a halin
yana tafiya to hakika ya zo da wani babban laifi da wani abin da aka ki, to ka
sanya tunanika ka tattaro da hankalinka zuwa ga inda ka nufa da abin da ka
fiskanta da tukinka idan wani abu ya zo ma na tunani ko na sada wani zumunci ta
wayarka to ka fita daga kan hanya ka tsaida abin hawanka to ka kare bukatarka
da wayarka ka kame kanka daga cutar da musulmai da kuma shi kanshi sharrinka
kafin wani abin ki ya faru har ya sanyaka ka yi bakinciki da nadama da hasara
da kaji radadi ka ce wayane ya mantar da ni ya makantar da ni ya shagaltar da
ni a wannan lokacin kuma nadama ba zata yi amfani ba bayan kafarka ta riga ta
zame.
Kuyi salati
da aminci bisa ga Ahmadu mai shiryarwa mai
mai ceto ga
halittu gaba daya .
Huduba ta biyu
Ya ku dalibai : girmama malami
fa wajibi ne mutunta shi da kimanta shi da kankan da kai a gare shi farilla ne na tilas, sanin falalan
ilimi da gode wa mai kyau aiki ne daga cikin abubuwa na kyawawan dabi'u masu
daraja dalibi na siffantuwa da ladabi a ajinsa hakama tare da abokan karatunsa
domin wannan shi ne girmama ilimi da kuma ma'abotansa Umar dan kaddabi Allah ya
kara yarda agareshui ya ce : (ku nemi ilimi kuma ku ilmantar da mutane shi ku nemi
ilimin mutuntawa da kuma nitsuwa ku yi tawaliu ga wanda kuka koya daga gareshi
da kuma wanda kuke koyarda shi kar ku kasance masu jiji da kai na daga malammai
shi malami yana cikin manyanmu ne abun girmamawa cikin manya kuma girmama manya
yana cikin abnda aka samo daga hadisi)
An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi daga Annabi tsira da amincin Allah
su tabbata a gare shi ya ce (Duk mutuminda bai tausaya wa karaminmu ba kuma bai san
kiman ko hakkin babbanmu ba to baya tare da mu)
Tashi don malami
ka girmamashi ###
malami ya
kusa ya zama manzo .
yanzu ka san wanda
yafi daukaka ###
fiye da wanda yake
gina kuma ya tada rayuka da hankula ?!.
tsarki ya tabbata
a gare ka mafi aherin masu ilmantarwa ### ka ilmantar da alkalami karnonin da
suka shude na farko
.ka fidda wannan
hankalin daga duhunsa ### ka shiryar da shi zuwa ga hanya na haske bayyananne .
katuro Annabi Musa
da attaura yana mai shiryarwa ### dan batulu kuma ya ilmantar da injila .
sai ka bubbugo da
mabubbuga na bayani ## sai ya shayar da hadisi kuma ya bada alkura'ani
(tanzila).
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق