الجمعة، 27 سبتمبر 2019

NEMAN MAFAKA WURIN UBANGIJI DA TUNKUDE BALA'I


Hudubar Masallacin Annabi 28-1-1441AH na shaikh Husain Al-Assheikh.
HUDUBAR FARKO
Duniya ba ta tabbatuwa a hali guda, sai an samu wasu lokuta wani yanayi na kunci da bakinciki kan gitta wa mutum, har ma da bacin rai a wasu lokuta,sabo da wasu sabuba ta fiskoki mabanbanta.
To ku saurara ! lalle komawa zuwa ga Allah bisa gaskiya ita ce hanya guda kadai da zata kubutar ta kuma bada kariya daga dukkan bakinciki da bacin rai.tare da kankan da kai  ga Majibinci Allah Tabaraka wa Ta'ala.
Allah Madaukakin sarki ya ce :"kuma lalle ne, Hakika, muna sanin cewa lalle kai,kirjinka yana yin kunci game da abin da suke fada(na izgili). Sabo da haka ka yi tasbihi game da gode wa Ubangijinka, kuma ka kasance cikin masu sujada. Kuma ka bautawa Ubangijinka har mutuwa ta zo maka."
Biyayya ga Allah abu ne na farinciki kamar yadda Takawa kuma abu ne mai sanya annashawa da walwala,to ka lazimci da'a ga Ubangijinka zai yaye ma dukkan bakinciki da ka shiga ya cire maka duk wani kunci. Allah Madaukakin sarki ya ce :"Duk wanda ya ji tsoron Allah to zai sanya mishi mafita kuma ya azurta shi daga ta inda bai tsammani" Allah Mai tsarki da daukaka ya ce :"Lalle masu biyayya na cikin ni'ima"
Kuma wannan ni'imar ta hada da jin dadin zuciya da farincikinta a nan duniya.
Idan ka shiga kunci  ka fada cikin duhun bacin rai to ka lazimci littafin Allah ta hanyar karanta shi da lura da ma'anoninSa tare da amsa kiranSa da aiki da shi, domin haske ne da waraka daga dukkan wahalhalu. Allah Madaukakin sarki ya ce : "ya ku mutane hakika waazi ya zo muku daga Ubanginku da waraka daga abin da yake cikin kiraza da shiriya da rahama ga muminai"
 Allah Madaukakin sarki ya ce : "ka ce shi (Alkur'ani) shiriya ne da waraka ga wadanda suka yi imani"
To duk wanda ya lizimtawa kansa maganar UbangijinSa, hasken sa ya haskaka masa zuciya to zai yaye mar duk wani bakinciki da bacin rai.
Ya Dan'uwa na musulmi:
Idan bakinciki da bacin rai ya dame ka to ka marairaice gaba ga Ubangijinka, ka nuna bukatuwarka zuwa gare shi,ka kankan da kai zuwa ga Mahaliccinka ka rusuna da adu'a, Allah  Madaukakin sarki ya ce : "kuma da Ayyuba a sa'ad da ya yi kiran UbangijinSa, (yace,) lalle ni, cuta ta shafe ni, alhali kuwa kai ne mafi rahamar masu rahama.Sai muka amsa masa, sa'anan muka yaye mishi abin da ke gare shi na cuta, kuma muka kawo masa mutanensa da kwatankwacinsu tare da su, sabo da rahama daga wurinMu da tunatarwa ga masu ibada."
     ka kankan da kai zuwa ga Mai iko ga kowani abu kankan da kai na gaskiya ka roke shi da harshe da gabbai cikin khushu'i ciki da waje, tare da cikakken marairaicewa irin na bawa ga Mahaliccinsa, da bawa ga Majibincinsa, tare da sakankancewa ba tsira da mafaka sai a gare shi Allah  Madaukakin sarki ya ce : "kuma mai kifi a sa'ad da ya tafi yana mai fushi, sai yayi zaton cewa ba za mu kuntata masa ba, sai ya yi kira a cikin duffai cewa ,: Babu abin bautawa face kai. Tsarki ya tabbata a gare ka.Lalle ne ni, na kasance daga azzalumai.sai muka amsa masa, kuma muka tsiratar da shi daga bakin ciki, kamar haka ne muke tsiratar da masu imani."
 Ya tabbata a sunna kwadaitarwa bisa ga wannan Adu'a, kuma ba wani musulmi da zai roki Allah da shi face Allah ya amsa masa, kuma yana cikin adu'o'in yaye bakin ciki da kwaranye bala'i sabo da abin da ya kumsa na ma'ana mai girma na kadaita Allah da girmama shi ta tsarkake shi da bayyana gajartawa da gazawa,na dan-Adam  da zaluntar kai wajen cika alkawari na hakkokin Mahalicci tsarki ya tabbata a gare shi, ba wata ni'ima ga zuciya ko jin dadi ga rai face da cikar tauhidi da tsaida hakki na imani.
Sabo da haka ne ya zo a cikin Bukhari da Muslim Daga Abdullahi dan Abbas  Manzon Allah (tsira da amincin Alllah su tabbata a garshi) ya kasance yana yin wannan addu'ar a lokacinda yaji kansa a yanayin damuwa:
La ilaaha ill-Allaah al-‘Azeem ul-Haleem, Laa
ilaaha ill-Allaah Rabb il-‘arshil-‘azeem, Laa ilaaha
ill-Allaah Rabbis- samawaati wa Rabb il-ard wa
Rabbil-‘arsh il-kareem
Ma'ana :(Ba abin bautawa da gaskiya sai Allah Mai girma Mahakurci, Ba abin bautawa da gaskiya sai Allah Ubangijin Al'arshi Mai girma, Ba abin bautawa da gaskiya sai Allah Ubangijin sammai da kassai Ubangijin Al'arshi mai girma".

Na daga cikin Aduo'in yaye bakinciki da bacin rai wanda ya kumshi rusuna wa Allah  Mabuwayi da daukaka da tawassuli da sunayenSa kyawawa da sifofinSa Madaukaka  akwai : "Ba abin bautawa da gaskiya sai Allah Mahakurci Mai girma.Tsarki ya tabbata ga Allah,Albarka ta tabbata ga Ubangijin Al'arshi Mai girma. Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai."
Ya tabbata daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace :"Ba wata musiba da zata samu wani mutum sai ya ce :

"Ya Ubangiji ni Bawanka ne dan bawanka dan baiwarka, makwankwadar kaina tana hannunka, kuma duk abinda ka Hukunta akaina, kuma Adalci ne Hukuncinka a gareni, ina rokonka da dukkan suna da yake naka wanda ka kira kanka da shi, ko ka saukar da shi a cikin littafinka, ko ka sanar da wani daga cikin bayinka, ko ka fifita saninsa akankin kanka, kasanya Alkur'ani Kakar zuciya ta, da hasken zuciya ta, da kuma yayewar bakin ciki na, da tafiyar damuwa." Face Allah ya tafiyar masa da damuwarsa da bacin ransa ya sauya masa su da farinciki kamar yadda ya zo a nassin Hadisin sabo da haka Annabi yayi umarni da a koye shi (An ce ya Manzon Allah ba za mu koye shi ba sai ya ce : "Ya dace duk wanda ya ji ya koya"
  Na daga cikin adu'o'i  na neman tunkude bakinciki da bacin rai :
 "Ya Ubangiji lallai ni ina neman tsari da kai daga Bacin rai da kuma damuwa, da gajiyawa da Kasala, da rowa da tsoro, da dabaibayewar bashi da galabar Mutane''
Daga ciki akwai (Allah Ubangiji na ba zan hada ka da wani ba   .) daga ciki akwai ya hayyu ya kayyum ; ya rayayye tsayayye  ina neman agaji da rahamar ka.
Ya kai musulmi:

Na daga cikin sabuba mafi girma na farin ciki da jin dadi da walwala  da annashuwa ;  shi ne ka tsaya gaba ga Ubangijin ka  da sallan farilla ko nafila  a lokutan da ba na hani ba kana mai kushu'i  tare da marairaicewa da nuna bukatuwa  ga Ubangiji mabuwayi  kasaitacce  Allah Madaukakin sarki ya ce:- (Ku nemi taimako da hakuri da salla )

Buhari ya rawaito daga Ummu salama Allah ya kara yarda a gare ta  ta ce wata rana  Annabi  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya farka cikin dare   sai ya ce '' tsarki ya tabbata ga Allah , me aka saukar na fitintinu a wannan dare me aka bude na taskoki ? ku tada ma'abota dakuna  sau da yawa  wata za ta zama tana cikin tufafi a duniya amma a cikin tsiraici a lahira .)
 A wata ruwayan kuma (har su samu su yi salla)
Ibn Hajar ya ce;  a wannan hadisi  akwai mustahabbancin gaggautawa zuwa ga salla yayin da aka tsoraci wani sharri , a wurin Muslim kuma fadin sa   tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi (Idan dayan ku ya ga abin da ya tsana (a cikin bacci) to ya tashi ya yi sallah)  A kan haka aikin magabata ya kasance kamar yadda Ibnu Abbas da waninSa suka rawaito.

Huduba ta biyu

Ya ku Bayin Allah!

Kyautatawa da nau'ukanSa na da tasiri na ban mamaki wurin tunkude naui daban –daban na bala'i musamman sadaka. Allah madaukakin sarki ya ce:- (Allah na saka wa masu sadaka). Allah madaukakin sarki ya ce:- (Ku kyautata Allah na son masu kyautatawa).
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(Aikata ayyukan alheri na kare fadawa bala'i, sadakar boye na dushe fushin Ubangiji, sada zumunta na karan tsawon kwana.) Dabarani ya fito da shi a littafinsa Alkabir, Imamul Baihaki da Munziri suka ce isnadinsa hasan ne yana da hanyoyi masu yawa da zasu karfafe shi.
Ya 'yan Uwa a Musulunci:
Samun farinciki da walwala na cikin daa ga Allah da da'a ga ManzonSa  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da aiki na kwarai da gaggawa zuwa ga ayyukan alheri, da lizimtar wajibabbu, da sauran ayyukan da'a,
  Allah madaukakin sarki ya ce:- (wanda ya yi aiki na kwarai namiji ne ko mace a halin yana mumini to zamu raya shi daddadan rayuwa kuma mu saka masa da lada fiye da abin da suka kasance suna aikatawa.)


ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق