الأربعاء، 25 سبتمبر 2019

Girman Allah da girmamawanSa ga bawanSa


Hudubar Masallacin Annabi 14-1-1441AH na shaikh Aliyu Bin Abdurrahman Alhuzaifi.
HUDUBAR FARKO
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Mabuwayi mai yawan gafara, yana juya dare akan wuni kuma yana juya yini a kan dare, lalle akwai abin lura a hakan ga masu basira,ina kyautata yabo ga Ubangiji na kuma ina gode mishi bisa ni'imominSa da ba mai iya kididdige su sai shi, daga wadanda muka sani da wadanda ba mu san su ba,sunayen Ubangijinmu sun tsarkaka, siffofinsa sun kasaita, ba abin bautawa da gaskiya sai Allah Tilo Mai rinjaye,na shaida Annabinmu shugabanmu Muhammad bawanSa ne kuma manzonSa ne mai Albishir da rahamar Allah da AljannarSa, mai gargadi da ukubar duniya da azabar wuta, ya Allah ka yi dadin tsira da aminci da albarka ga bawanka kuma Manzonka Muhammad da iyalansa da sahabbansa ma'abota biyayya. Bayan haka ku ji tsoron Allah Madaukaki ta hanyar neman yardarSa da tsoracewa fushinSa da ukubarSa,Allah Tsarki ya tabbata a gare shi yace " Kuma Ubangijinka yake halitta abin da ya so ya kuma zaba, zabi bai kasance na su ba, tsarki ya tabbata ga Allah Madaukaki daga  abin da suke yi na shirka"
Lalle Ubangiji Mabuwayi da daukaka ya halicci halittu da kudurarsa da iliminSa da hikimarSa da rahamarSa ya samar da wannan duniya da ake gani, ya sanya mata wani ajali da zata kare zuwa gare shi ba zata wuce shi ba,ya halicci wannan duniya da muke ciki tare da sababi, ya halicci abin da ke zamewa da sababi kuma shine ke halitta sababi da abin da ke kawo sababin: To duk abin da Allah ya so zai kasance duk abin da bai so ba kuma ba zai kasance ba.Allah Madaukakin sarki ya ce: Allah ne Mahaliccin dukkan komai kuma shine wakili akan kome. Shi ke da mabudan sammai da kasa kuma wadanda suka kafirta da ayoyin Allah, wadannan su ne masu hasara.     Kuma ya ce: "To shine da halittar kuma da umarnin Albarkar Allah Ubangijin halittu ta bayyana! ".
Mutum halitta ne daga cikin halittun Allah na ban mamaki, Allah ya hada mishi sifofi na ban al'ajabi, wdanda ke rarrabe ga wasu halittu da ba shi ba. Allah ya ce : "Lalle ne Mun halitta mutum a cikin mafi kyawon tsayuwa".Allah Madaukakin sarki ya ce: kuma a cikin rayukan ku (akwai ayoyi) kuma ba za ku duba ba?"
Ya kuma ce : "kuma akwai daga ayoyinSa ya halitta ku daga turbaya sai ga ku kun zama mutum kuna watsuwa" kuma Allah ya yi baiwa ga bani adam bisa karrama su sai yace "kuma Lalle ne Mun girmama 'yan Adam kuma muka dauke su a cikin kasa da teku kuma muka azurta su daga abubuwa masu dadi, kuma muka fifita su a kan mafiya yawa daga cikin wadanda muka halitta, fifitawa."
Kuma girmamawa da Allah ya yi wa bani Adam girmama wa ne na gaba daya ga mai biyayya da mai fajirci a nan duniya da ni'imomi, amma kebantacciyar girmama wa a lahira da yardarSa da Aljanna ta ni'ima ga muminai ne kawai, kafuri bai da rabo a lahira, kuma Ubangijinka ba ya zaluntar kowa, amma a lahira Ubangiji bai girmamawa sai ga wanda ya mishi biyayya cikin Mutane da Aljanu.
Ibnu Asakir ya rawaito daga Hadisin Anas dan Malik Allah ya kara yarda a gare shi"Daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace :(Lalle mala'iku sun ce : ya Ubangijinmu ka halicce mu ka halicci bani Adam sai ka sanya su suna cin abinci kuma suna shan abin sha,suna sanya tufafi kuma suna auren mata, kuma suna hawan dabbobi,suna barci suna hutawa, amma mu baka sanya mana wani abu na daga wannan ba, to ka sanya musu a duniya mu kuma ka sanya mana a lahira sai Allah Mabuwayi da daukaka ya ce: Ba zan sanya wanda na halita da hanu na na kuma busa mishi rayi na ba tamkar wadda na ce da shi kasance ! sai ya kasance"
akwai wani hadisin da zai karfafe shi daga hadisin Abdullahi dan Amr wanda Dabrani ya rawaito.
Na daga cikin ni'imomi masu girma da aka yi wa bani Adam akwai hore masa abubuwa masu amfani da maslahohi da ni'imomi, Allah Madaukakin sarki ya ce: "Ase baku ga yadda Allah ya hore muku abin da ke cikin sammai da kasa ba ya kuma yalwata muku ni'imominSa na zahiri da badini " Allah Madaukakin sarki ya ce: ya hore muku abin da ke cikin sammai da kasa baki daya, daga gare shi, lalle cikin haka akwai ayoyi ga mutanen da suke masu tunani."
  Hikima na yalwata ni'imomi ga bani Adam ita ce :don su mika wuya ta hanyar da'a ga Allah Madaukaki su kuma gode masa, kada kuma su hada shi da wani a cikin bauta, Allah Madaukakin sarki ya ce:"kamar wancan ne Allah ya ke cika ni'imarSa a gare ku ko zaku mika wuya.
Ibnu kasir Allah ya mishi rahama ya ce a tafsirinsa:"Ai haka zai sanya muku abin da zaku taimaki kanku cikin al'amuranku da abin da za ku bukace shi don ya zme muku abin da za agaza muku wurin bin Allah da bauta masa"
Allah bai yi nuni ga ambaton dan Adam ba tun da ya halicci Adam da hanunSa da abin da ya ke tsakanin marhala zuwa wata marhala na mutum  face don ya bayyana mishi nauyin da ke kan shi a wannan rayuwa ta duniya kuma ya sanar da shi aikin da ke kan shi, da hikimar da ya sa aka halitta shi, kuma an kallafa mishi umarni da hani kuma yana mai dauke da wannan sharia da kuma daukakaka na bautawa Ubangijinsa Allah Madaukakin sarki ya ce:   " yanzu mutum na zaton zaa bar shi haka kawai ne " Imamusshafi'I Allah ya mishi rahama yace : wato ba za a umarce shi ba ko a hana shi,
Allah Madaukakin sarki ya ce: " To kuna zaton cewa mun halicce ku don wasa ne kuma ba za ku dawo zuwa gare mu ba?
Na daga cikin abin da Allah ya tsara wannan duniya  da abin da ya halitta na sabuba da ke tasiri a samuwar wadannan abubuwa, lalle Allah ya bayyana mana daga cikin sunnoninSa a rayuwa cewa ayyukan dan Adam na inganta rayuwa ta yi dadi idan ayyukan sun yi kyau a nan duniya, haka kuma rayuwa kan baci idan ayyuka suka lalace, kuma ayyukan dan Adam na shiga har cikin dabbobi da tsirrai ya yi tasiri wurin gyaruwansu ko bacin su, bisa rahamar Allah da adalcinsa, don ya lazimtawa mutum da'a kuma ya kauracrwa abubuwan da aka haramta.   Allah Madaukakin sarki ya ce game da albarkar rayuwa da alherinta na ga kyautatuwan ayyukan mutum :- (Da mutanen  alkarya za su yi imani su yi takawa da mun bude mu su  albarkatu daga sama da kasa  sai dai sun karyata sai muka rike su da abin da suka kasance suna aikatawa )

Kuma Allah Madaukakin sarki ya ce :-  (Da ma'abota littafi za su yi imani  su yi takawa da mun kankare musu laifukan su  kuma da mun shigar da su aljanna na ni'ima .  Kuma da a ce sun tsaida attaura da linjila  da abin da aka saukar musu daga Ubangijin su  da sun ci daga saman su da kuma karkashin kafan su )
Kuma Alkur'ani shi ne abin da Allah ya saukar ga musulmai da ahlul kitabi  ba wanda  ya sanja shi sabo da kiyaye shi , kuma Allah Madaukakin sarki ya ce :- (Wadanda suka yi imani basu chakuda imanin su da zalunci ba wadannan suna da aminci kuma su ne shiryayyu)
Wato basu churkuda imanin su da shirka ba , kamar  inda annabin shi ya  fassara shi kuma Allah Madaukakin sarki ya ce :- (Ya ku wadan da suka yi imani in za ku taimaki Allah Allah zai gtaimake ku). Wato in za ku taimaki addinin Allah to zai taimake ku.
 Kuma Allah mabuwayi da daukaka ya ce :- ( Wadan da in mun basu matsayi a doron kasa sai su tsaida salla kuma su bada zakka su yi umarni da kyakkyawa su yi hani da mummuna  , kuma lallai akibar al'amura na wurin Allah ).
Ibn Kasir Allah  ya mishi rahama  ya ce a tafsiri  : ''Umar Dan Abdul-aziz ya yi huduba sai ya karaanta wannan aya sai ya ce : 'ku saurara wannan aya bata tsaya akan jagora kadai ba sai dai ta kunci shugaba da talakawa  a sai  ba zan baku labari ba  da abin da yake hakkin ku ne akan shugaba da kuma abin da ya ke hakkin shi ne akan ku:- na daga  ciki , shi ne ya rike ku da hakkokin Allah da ke kan ku  kuma ya karbi hakkokin wasun ku da ke kan wasu  kuma ya shirye ku zuwa ga abinda yake dacewa iya'iyawan shi  , to, ku kuma ya wajaba a gare Ku ,  ku mishi da'a'' . Afadin Allah (kuma lallai akibar al'amura na wurin Allah ).
Akwai aminci ga wanda ya tashi da wadannan al'amura guda hudu :  Na daga wani da kuma kaidi na makiya  kamar yanda Allah Madaukakin sarki ya ce:- (muddin kuka yi hakuri kuka yi takawa to kaidin su ba zai cutar da ku ba da wani abu  lallai Allah ya iyakance abin da suke aikatawa).
Kuma kamar yanda gyaruwan aikin mutum  yakan game da alheri  to haka namma yake shafi shi mai aikin shi kan shi ,  kamar yanda Allah Madaukakin sarki ya ce :- (Duk wanda ya yi aiki na kwarai  na miji ko mace a halin yana mumini to za mu raya shi rayuwa daddada  kuma za mu sakanya mu su  da ladan su da mafi kyaun abin da suka kasance suna aikatawa).
Ta daya bangaren kuma  da ke kishiyantan wannan  shi kan shi barna na aikin mutum yana cutar da shi kan shi mutum din   kuma ya shigar da shi  barnan a cikin rayuwa ,  Allah Madaukakin sarki ya ce :- (Da a ce gaskiya zai bi soye-soyen rayukan su da sammai da ksa sun   lalace da abin da ke cikin su )  

 Kuma Allah Madaukakin sarki ya ce:- (Barna ta bayyana a doron kasa da taiku  sakamakon abinda hannayen mutane ya aikata  don ya dandana musu wani sashi na abinda suka aikata  ko za su dawo ). Kuma Allah Madaukakin sarki ya ce :- (Duk wani abin da ya same ku na musiba to sakamakon abin da hannayen ku suka aikata ne  kuma yana yafiya ga mafi yawa)

To ka yi lura ya kai mutum halin wadannan da suka munana aiki  abin da ya sauka a gare su  Allah Madaukakin sarki ya ce :- (Sau dayawa muka halaka daga alkaryu wanda sun kasance azzalumai   bayan su muka tada wasu mutane daban)
An karbo daga Abdullahi Dan Umar  Allah ya kara yarda a gare su ya ce :-(  Abubuwa biyar na tare da wasu abub uwa biyar : Alfahasha ba zata bayyana ba a cikin mutane har kuma su bayyana ta karara  face annoba ta bayyana a cikin su da cututtuka irin wanda ba a samu ba daga wadanda suka gabace su.kuma muddin jagororinsu ba su yi hukunci da littafin Allah ba face Allah ya sanya yakinsu a tsakaninsu, kuma ba wasu mutane da zasu hana zakkan dukiyar su face an damke su da fari a kuma hana su ruwan sama ba don dabbobi da ba a saukar musu da ruwa ba, kuma zasu tawaye kilo ba face an rike su fari da zalunci shugaba, baza su warware alkawarin Allah da Manzo ba face Allah ya dora musu makiya akan su, su rika kwace wani sashi na abin da ke hanun su) Ibnu Maja ya rawaito

  Allah Madaukakin sarki ya ce :- (Kuma dan adam bai da wani abu sai abin da ya aikata . Kuma aikin sa da sannu za a gani ). Allah ya sa min albarka ni da ku a cikin alkur'ani mai girma

 HUDUBA TA BIYU
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah mabuwayi mai yawan gafara mai hakuri mai yawan godiya , ina kyautata yabo ga Ubangiji na kuma ina gode mishi  ina tuba zuwa gare shi kuma ina neman gafarar sa ,  to lallai godiya ta tabbata ga Ubangijina a duniya da lahira  bisa falalar sa  da baiwar sa cikin abin da muka sani da wadda ba mu sani  na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya masani da abinda ke cikin zukata  ,  na shaida Annabin mu kuma shugaban mu Muhammad    bawan sa ne kuma Manzon sa ne  wanda aka turo shi  da shiriya da haske Allah ka yi dadin tsira  da aminci da Albarka  bisa ga bawan ka kuma Manzon ka Muhammad  da iyalan sa da sahabban sa  wanda suka yi fintinkau zuwa ga dukkan aiki na da'a .

Bayan haka  ku ji tsoron Allah Madaukaki don ku riki tafarki  zuwa ga Allah wanda zai shigar da ku cikin aljannar sa  ku rabauta da yardan sa   ya kai dan adam yi dubi zuwa ga ni'imomin  Allah a gare ka  da ya ni'imtar kai wanda ba wanda ke da kudura na iyakance su sai Allah kuma ka tashi da godiya gare shi game da su  da zai kwace mafi karancin ni'ima to ba wanda ya isa ya dawo ma da ita sai shi  .
A cikin ni'imar Allah ba wani abu kankani   a halin kuma ga ka ya kai mutum ta hanyar daidaiton ka da gyaruwan ka  da yadawan ka ga alheri  da kuma kamewan ka daga sharri   za ka kasance ka taimaka wurin kiyaye muhallin ka na zama(matattara)  da kuma tseratar da kanka daga sharrace-sharrace , da ukubobi , ka sani lallai kai abin tambaya ne game da ayukan ka a rayuwar ka  da kuma bayan mutuwar ka   to ka yi dubi me za ka gayawa Ubangijin ka Allah Madaukakin sarki ya ce:- (Ya kai  mutum lallai ne kai mai aikin wahal da kai ne zuwa ga Ubangijin ka , wahala mai tsanani to, kai mai haduwa da shi ne.  To amma wanda aka baiwa littafin sa da damarsa .  To za a yi masa hisabi mai sauki . Kuma ya juya zuwa ga iyalan sa (a cikin aljanna) yana mai raha. Kuma amma wanda aka baiwa littafin sa daga wajen bayan sa .  To za shi dinga kiran halaka kuma ya shiga (wutar) sa'ira .

    
Ya zo a hadisi:- (Kafan bawa baza su gushe ba har sai an tambaye shi game da abubuwa guda hudu;  game da rayuwan sa   cikin abin da ya karar da su da samrtan sa   a cikin me ya tafiyar da , da dukiyar sa  daga ina ya same su kuma a me ya ciyar da su,    da kuma aikin sa  mai ya aiwatar da shi ).
Ka sani ya kai mutum lallai gidan ka da ke wanzuwa na dindindi ita ce take gaban ka bayan mutuwa, to dadi ya tabbata a gare ka in ka rayata da ayuka na kwarai  , kuma azaba ya tabbata a gare ka in ka yarda da wannan duniya taka ka manta lahirar ka ,  duniyar ka za ta juya ma baya ne in ka kaunace ta ko  ka ki ta , lahira kuma za ta fiskanto ka  bisa ga abin da ka kaddamar  kuma ita  ta har abada ce .

Ya ku bayin Allah ! lalle Allah da mala'ikunSa suna salati ga Annabi ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi da aminci tabbatacce.

 














   

ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق