HUDUBAR
FARKO
Duniya ba ta tabbatuwa a hali
guda, sai an samu wasu lokuta wani yanayi na kunci da bakinciki kan gitta wa
mutum, har ma da bacin rai a wasu lokuta,sabo da wasu sabuba ta fiskoki
mabanbanta.
To ku saurara ! lalle komawa
zuwa ga Allah bisa gaskiya ita ce hanya guda kadai da zata kubutar ta kuma bada
kariya daga dukkan bakinciki da bacin rai.tare da kankan da kai ga Majibinci Allah Tabaraka wa Ta'ala.
Allah Madaukakin sarki ya ce :"kuma lalle ne, Hakika, muna sanin cewa lalle
kai,kirjinka yana yin kunci game da abin da suke fada(na izgili). Sabo da haka
ka yi tasbihi game da gode wa Ubangijinka, kuma ka kasance cikin masu sujada.
Kuma ka bautawa Ubangijinka har mutuwa ta zo maka."
Biyayya ga Allah abu ne na
farinciki kamar yadda Takawa kuma abu ne mai sanya annashawa da walwala,to ka
lazimci da'a ga Ubangijinka zai yaye ma dukkan bakinciki da ka shiga ya cire
maka duk wani kunci. Allah Madaukakin sarki ya ce :"Duk
wanda ya ji tsoron Allah to zai sanya mishi mafita kuma ya azurta shi daga ta
inda bai tsammani" Allah Mai tsarki da daukaka ya ce :"Lalle masu biyayya na cikin ni'ima"
Kuma wannan ni'imar ta hada da
jin dadin zuciya da farincikinta a nan duniya.
Idan ka shiga kunci ka fada cikin duhun bacin rai to ka lazimci
littafin Allah ta hanyar karanta shi da lura da ma'anoninSa tare da amsa
kiranSa da aiki da shi, domin haske ne da waraka daga dukkan wahalhalu. Allah
Madaukakin sarki ya ce : "ya ku mutane hakika
waazi ya zo muku daga Ubanginku da waraka daga abin da yake cikin kiraza da
shiriya da rahama ga muminai"
Allah Madaukakin sarki ya ce : "ka ce shi (Alkur'ani) shiriya ne da waraka ga wadanda
suka yi imani"
To duk wanda ya lizimtawa
kansa maganar UbangijinSa, hasken sa ya haskaka masa zuciya to zai yaye mar duk
wani bakinciki da bacin rai.
Ya Dan'uwa na musulmi:
Idan bakinciki da bacin rai ya
dame ka to ka marairaice gaba ga Ubangijinka, ka nuna bukatuwarka zuwa gare
shi,ka kankan da kai zuwa ga Mahaliccinka ka rusuna da adu'a, Allah Madaukakin sarki ya ce : "kuma da Ayyuba a sa'ad da ya yi kiran UbangijinSa,
(yace,) lalle ni, cuta ta shafe ni, alhali kuwa kai ne mafi rahamar masu
rahama.Sai muka amsa masa, sa'anan muka yaye mishi abin da ke gare shi na cuta,
kuma muka kawo masa mutanensa da kwatankwacinsu tare da su, sabo da rahama daga
wurinMu da tunatarwa ga masu ibada."
ka kankan da kai zuwa ga Mai iko ga kowani abu
kankan da kai na gaskiya ka roke shi da harshe da gabbai cikin khushu'i ciki da
waje, tare da cikakken marairaicewa irin na bawa ga Mahaliccinsa, da bawa ga
Majibincinsa, tare da sakankancewa ba tsira da mafaka sai a gare shi Allah Madaukakin sarki ya ce : "kuma mai kifi a sa'ad da ya tafi yana mai fushi, sai
yayi zaton cewa ba za mu kuntata masa ba, sai ya yi kira a cikin duffai cewa ,:
Babu abin bautawa face kai. Tsarki ya tabbata a gare ka.Lalle ne ni, na kasance
daga azzalumai.sai muka amsa masa, kuma muka tsiratar da shi daga bakin ciki, kamar
haka ne muke tsiratar da masu imani."
Ya tabbata a sunna kwadaitarwa bisa
ga wannan Adu'a, kuma ba wani musulmi da zai roki Allah da shi face Allah ya
amsa masa, kuma yana cikin adu'o'in yaye bakin ciki da kwaranye bala'i sabo da
abin da ya kumsa na ma'ana mai girma na kadaita Allah da girmama shi ta
tsarkake shi da bayyana gajartawa da gazawa,na dan-Adam da zaluntar kai wajen cika alkawari na
hakkokin Mahalicci tsarki ya tabbata a gare shi, ba wata ni'ima ga zuciya ko
jin dadi ga rai face da cikar tauhidi da tsaida hakki na imani.
Sabo da haka ne ya zo a cikin Bukhari da Muslim Daga Abdullahi dan Abbas
Manzon Allah
(tsira da amincin Alllah su tabbata a
garshi) ya kasance yana yin wannan addu'ar a lokacinda yaji kansa a yanayin damuwa:
La ilaaha
ill-Allaah al-‘Azeem ul-Haleem, Laa
ilaaha ill-Allaah Rabb il-‘arshil-‘azeem, Laa ilaaha
ill-Allaah Rabbis- samawaati wa Rabb il-ard wa
Rabbil-‘arsh il-kareem
ilaaha ill-Allaah Rabb il-‘arshil-‘azeem, Laa ilaaha
ill-Allaah Rabbis- samawaati wa Rabb il-ard wa
Rabbil-‘arsh il-kareem
Ma'ana
:(Ba abin bautawa da gaskiya sai Allah Mai girma Mahakurci, Ba abin bautawa da
gaskiya sai Allah Ubangijin Al'arshi Mai girma, Ba abin bautawa da gaskiya sai
Allah Ubangijin sammai da kassai Ubangijin Al'arshi mai girma".
Na daga cikin Aduo'in yaye
bakinciki da bacin rai wanda ya kumshi rusuna wa Allah Mabuwayi da daukaka da tawassuli da sunayenSa
kyawawa da sifofinSa Madaukaka akwai : "Ba abin bautawa da gaskiya sai Allah Mahakurci Mai
girma.Tsarki ya tabbata ga Allah,Albarka ta tabbata ga Ubangijin Al'arshi Mai
girma. Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai."
Ya tabbata daga Annabi tsira
da amincin Allah su tabbata a gare shi yace :"Ba wata musiba da zata samu wani mutum sai ya ce :
"Ya Ubangiji ni Bawanka ne dan
bawanka dan baiwarka, makwankwadar kaina tana hannunka, kuma duk abinda ka
Hukunta akaina, kuma Adalci ne Hukuncinka a gareni, ina rokonka da dukkan suna
da yake naka wanda ka kira kanka da shi, ko ka saukar da shi a cikin
littafinka, ko ka sanar da wani daga cikin bayinka, ko ka fifita saninsa
akankin kanka, kasanya Alkur'ani Kakar zuciya ta, da hasken zuciya ta, da kuma
yayewar bakin ciki na, da tafiyar damuwa." Face Allah ya tafiyar masa da
damuwarsa da bacin ransa ya sauya masa su da farinciki kamar yadda ya zo a nassin Hadisin sabo da haka
Annabi yayi umarni da a koye shi (An ce ya
Manzon Allah ba za mu koye shi ba sai ya ce : "Ya dace duk wanda ya ji ya
koya"
Na daga cikin adu'o'i na neman tunkude bakinciki da bacin rai :
"Ya Ubangiji lallai ni ina neman tsari da kai daga Bacin
rai da kuma damuwa, da gajiyawa da Kasala, da rowa da tsoro, da dabaibayewar
bashi da galabar Mutane''
Daga ciki akwai (Allah Ubangiji
na ba zan hada ka da wani ba .) daga
ciki akwai ya hayyu ya kayyum ; ya rayayye tsayayye ina neman agaji da rahamar ka.
Ya kai musulmi:
Na daga cikin sabuba mafi girma na farin ciki
da jin dadi da walwala da annashuwa ; shi ne ka tsaya gaba ga Ubangijin ka da sallan farilla ko nafila a lokutan da ba na hani ba kana mai kushu'i tare da marairaicewa da nuna bukatuwa ga Ubangiji mabuwayi kasaitacce
Allah Madaukakin sarki ya ce:- (Ku nemi taimako da hakuri da
salla )
Buhari ya rawaito daga Ummu salama Allah ya kara yarda a gare ta ta ce wata rana Annabi
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya farka cikin dare sai ya ce '' tsarki ya tabbata ga Allah , me
aka saukar na fitintinu a wannan dare me aka bude na taskoki ? ku tada ma'abota dakuna
sau da yawa wata za ta zama tana
cikin tufafi a duniya amma a cikin tsiraici a lahira .)
A wata ruwayan kuma (har su samu su yi salla)
Ibn Hajar ya ce; a wannan hadisi akwai mustahabbancin gaggautawa zuwa ga salla
yayin da aka tsoraci wani sharri , a wurin Muslim kuma fadin sa tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi (Idan dayan ku ya ga abin da ya tsana (a cikin
bacci) to ya tashi ya yi sallah) A kan haka aikin magabata ya kasance kamar
yadda Ibnu Abbas da waninSa suka rawaito.
Huduba ta biyu
Ya ku Bayin Allah!
Kyautatawa da nau'ukanSa na da tasiri na ban mamaki wurin tunkude naui
daban –daban na bala'i musamman sadaka. Allah madaukakin sarki ya ce:-
(Allah
na saka wa masu sadaka). Allah madaukakin sarki ya ce:- (Ku kyautata
Allah na son masu kyautatawa).
Manzon Allah tsira
da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(Aikata ayyukan alheri na kare
fadawa bala'i, sadakar boye na dushe fushin Ubangiji, sada zumunta na karan
tsawon kwana.) Dabarani ya fito da shi a littafinsa Alkabir, Imamul Baihaki da Munziri suka
ce isnadinsa hasan ne yana da hanyoyi masu yawa da zasu karfafe shi.
Ya
'yan Uwa a Musulunci:
Samun
farinciki da walwala na cikin daa ga Allah da da'a ga ManzonSa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,
da aiki na kwarai da gaggawa zuwa ga ayyukan alheri, da lizimtar wajibabbu, da
sauran ayyukan da'a,
Allah
madaukakin sarki ya ce:- (wanda ya yi aiki na kwarai namiji ne ko mace a halin yana
mumini to zamu raya shi daddadan rayuwa kuma mu saka masa da lada fiye da abin
da suka kasance suna aikatawa.)