الجمعة، 30 نوفمبر 2018

Hakkokin Musulmi akan Musulmi


Hudubar Masallacin Annabi na sheikh AbdulBari Assubaiti 22/3/1440 Ah 30/11/18Ac
Hudubar Farko:
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga Manzon Allah da iyalansa da sahabbansa da wanda ya bi su,Bayan haka.

A wani hali da aka samu kai a ciki na ababan shagaltarwa da hanyoyi da zasu yi awon gaba da mutum na harkan abin duniya,sai a samu musulmi ya gafala daga wasu hakkoki da gina alaka ta zamantakewa, wani kan manta ko share tunanin dawowa kan tafarkin gyara tsarin rayuwar shi da kyautata alakarsa, shekaru na tafiya ranakun rayuwa na shudewa, ana dada samun rata da yin nesa da juna, sai rayuwa ta zama ba dankon zumunci, a rasa  tausayin juna.
Musulunci ya bada kulawa ga alaka ta zamantakewa, kuma ya sanya lada mai kwadaitarwa da janyowa da gaggawa zuwa gare ta.don a samu hadewar zukata da karfafa zumunta,da amsa bukatun juna, kuma al'uma zata dabiantu da kyawawan halaye da nagartattun ayyuka, sai mizani ya nauyaya, a daga darajojin mutum, idan an bada hakkoki alaka ta yi kyau, sai al'uma ta zama ta dunkule ta yi karfi.  
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Hakkin Musulmi akan Musulmi shida ne,sai aka ce da shi menene su ya manzon Allah? Sai ya ce : Idan ka hadu da shi ka mishi sallama, idan ya gayyace ka to ka amsa mishi idan ya nemi nasiha to ka yi mishi, idan ya yi atishawa ya godewa Allah to kace da shi  yarhamukallah (Allah ya maka rahama), idan ya yi rashin lafiya ka ziyarce shi, idan ya rasu to ga bi jana'izarsa.
Hadisi ne mai girma da ke bude sarari na kusantar juna da kauna, kuma hakan zai bada sabon rayuwa, Allah Madaukakin sarki ya ce :( Kuma ya sanya soyayya a tsakanin zukatansu, da ka ciyar da abin da ke cikin  kasa gaba daya da baka sanya soyayya a tsakanin zukatansu ba,kuma amma Allah ya sanya soyayya a tsakanin zukatansu lalle shi ne Mabuwayi mai hikima).Anfal 63

Farkon hakkokin musulmi bisa musulmi kalma ce ta kauna da hadinkai, gaisuwa ta 'yan Aljanna ita ce Assalam, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Ba za ku shiga Aljanna ba har sai kun yi imani, ba za ku yi imani ba sai kun kaunaci junanku, ashe ba zan nusar da ku ga abin da in kun aika shi zaku kaunaci junanku? To ku yada sallama a tsakaninku)
Sallama mabudi ne na kauna zuwa ga zuciya, kuma mabudi ne na neman izini ga kowace kofa, yana kawo albarka da habaka da kari a rayuwa.
 Allah Madaukakin sarki ya ce : (To idan kun shiga wasu gidaje, ku yi sallama a kan kawunanku,gaisuwa daga gurin Allah mai albarka mai dadi).
      Sallama sako ne na aminci,kuma alama ce na ma'abota imani,wanda ya san ma'anarsa da matsayinsa, yayi rayuwarsa ta hakika ya san falalarsa,to zuciyarsa zata tsarkaka dabiunsa zasu gyaru, Al'umarsa zata daukaka a addinance kuma a duniyance.
Allah Madaukakin sarki ya ce : (Da shi Allah yana shiryar da wanda ya bi yardarSa, zuwa ga hanyoyin aminci, kuma yana fitar da su daga duffai zuwa ga haske da izininSa,kuma yana shiryar da su zuwa ga hanya madaidaiciya.)
Na daga cikin hakkokin musulmi bisa dan uwansa musulmi akwai amsa gayyatarsa, ya halarci walimarsa ya dadada zuciyarsa. Da taya shi farinciki, kuma gayyaceceniya ga juna na haifar da kauna da hadinkai. Kaiwa juna ziyara da haduwa yana haifar da kauna, a cikin wannan yanayi akan samu warwarewan rikici, masu hankali na kauda kai bisa suka da zargi sai dankon zumunci ya kara karfi, rashin jituwa ya kau,
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Idan an gayyaci dayanku zuwa ga abinci to ya amsa,idan ya so ya ci idan bai so ba ya bari).
Kimar walima ba ana auna shi ba ne da girman abin da aka ciyar ba ko yawan abin da aka kashe ba, sai dai kawai don akyautata manufa ta 'yan uwantaka da sada zumunci tsakanin musulmai, amma yin almubazzaranci a cikin walima ba abin a yaba ba ne, don sharia bata yadda da haka ba, kuma yana cire albarka,
Allah Madaukakin sarki ya ce : (ku ci ku sha amma kada ku yi barna lalle shi  bai son mabarnata)Aaraf 31
Hakki na uku cikin hakkokin musulmi shi ne ka yi wa dan'uwanka  nasiha, cikin lumana da tausasawa, nasiha sako ne  na kauna daga musulmi zuwa ga dan'uwansa,sabo da yana son sa ya ke masa fata na dukkan alheri, kuma yake tsorace masa dukkan sharri. Mai nasiha na da matsayi madaukaki a addini, da daraja ta kololuwa ranar da mutane zasu tsaya gaba ga ubangijin talikai, a lokacin da mai nasiha zai yi nasiha to shi mai gaskiya zai buda kirjinsa don nasihar ya kuma saurare ta da zuciyarsa, kuma ta karbe ta da daukakawa ba zai maida ta ba, sabo da wani mummunan zato da ya ke yi wa mai nasihan,ko wata fassara da ba daidai ba,
Hakika sarkin muminai Umar Allah kara yarda a gare shi ya ce;( Allah ya yi rahama ga duk wani mutumin da ya nusar da mu ga laifukanmu).
Akwai banbanci nesa ba kusa ba tsakanin mutumin da zai yi nasiha yana mai kauna mai nusarwa mai tausayi yana nasiha tare da suturcewa, da wanda zai yi lullubi nasihar ya maida ta mayafi, sabo da wani abu mara kyau a zuci, da zarar ya ci karo da wani abu, sai ya rika bin gajartawa na 'yan uwansa ya yi ta yabazawa, ya rika yada laifukan abokan zamansa, sai ya rika aibata shi ya soki  wannan ya tuhumi wancan, ya taba mutuncin wadancan,
Hakki na hudu shi ne idan ya yi atishawa ya godewa Allah to ace da shi  yarhamukallah, kowa na jin dadin a yi mishi adua, yana kuma fatan karin rahama, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Aduar mutum ga dan'uwan shi musulmi a boye karbabbiya ce An wakilta wani mala'ika ta kansa a duk lokacin da ya yi wa dan'uwansa adua ta alheri sai Mala'ikan da aka wakilta ya ce :Amin,  kai ma Allah ya baka kwatankwacinsa).
Atishawa ni'iama ce daga Ubangiji ga bawa wacce ta cancanci a gode a yaba, a cikin cewa Yarhamukallahu da adua gare shi da ambaton Allah akwai fusata shaidan da kuma tunkude shi, umarni da aka yi ga mai atishawa da ya yi adua ga mai sauraronsa, da shi kuma da zai mishi adua da gafara da shiryuwa  da gyaruwan shani, wanda ke nufin komi nashi ya yi kyau ya daidaita.
Na daga cikin hakkokin musulmi a kan musulmi akwai ziyartar shi a halin bai da lafiya, sabo da maralafiya yana fama da jiki, watakila ma rashin lafiyan kan iya kai wa makwanni ko watanni, bai iya runtsa ido ko ya samu kwanciyar hankali, yana kururuwa yana jujjuyawa sabo da radadi da zafin ciwo, yana neman aduar da Allah zai tabbatar mishi da sauki da ita,kuma darajarsa ta dagu dalilinta, yana bukatar ziyara da za ta rage mishi zafi da kalma wacce za ta debe mishi kewa na daga bakinciki da yake fama, da shafa na tausayawa da zai ji yana kusa da 'yan uwansa, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Duk wanda ya je dubiya ga mara lafiyan da ajalinsa bai zo ba, sai ya fadi (As'alullaha Rabbal Arshil Azim an yashfiyaka) ina rokon Allah ubangijin Al'arshi mai girma da ya baka lafiya, har sau bakwai face sai Allah ya bashi lafiya.
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Allah Mabuwayi da Daukaka zai ce a ranar alkiyama : Ya wane na yi rashin lafiya baka ziyarce ni ba, sai yace :Ta yaya zan ziyarce ka kana Ubangijin talikai, sai yace baka san bawa na wane ya yi rashin lafiya ba ba ka ziyarce shi ba? Da ka ziyarce shi da ka same ni a gun shi)
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Duk wanda ya ziyarci mara lafiya to yana cikin dausayin AlJanna sai aka ce mene ne dausayin Aljanna  sai ya ce :abin anfani na aljanna)
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Duk wanda ya ziyarci maralafiya, ko ya ziyarci wani dan'uwansa don Allah, sai mai kira ya kira shi: ka tsarkaka takunka ma ta tsarkaka,kuma ka riki masauki a aljanna)
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Duk wanda ya ziyarci maralafiya bai zai gushe ba cikin rahama har sai ya zauna, idan ya zauna sai ya tsunduma ciki.)
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Ba wani mutum musulmi da zai ziyarci musulmi face Allah ya turo malaiku dubu saba'in suna nema masa gafara a kowace sa'a ce ta wuni har sai ya yi yammaci,kuma a kowane lokaci ne na dare har gari ya waye,)

Huduba ta biyu:
Yayin da muka yi lura da hakkoki da nau'ukansu da manufofinsu : za mu sani bisa yakini cewa hakkin musulmi akan dan'uwan shi abu ne mai ci gaba har zuwa mutuwarsa,ku zai zarce har bayan mutuwarsa: da bin jana'izarsa, da yi mishi adua, a cikin haka akwai girmama shi da daukaka shaninsa,da kimanta matsayinsa,kamar yadda waki'in alkawari tsakanin muminai  ke fassarawa, wannan shine abin da kullin 'yan uwantaka ke hukuntawa.
Abin mamaki da girman wannan addini na musulunci, abin mamaki da gamewar manhajarsa, abin mamaki da kyan ni'imarsa da garabasarsa, Addini ne da ya daukaka zaukin bawa da kawarsa, kuma ya tsarkake ayyukan bawa da zancensa, ya tsarawa musulmi abubuwa na sirrinsa da na bayyane.
Idan mutum musulmi ya mutu zaa wanke shi a sa mishi likkafani a mishi salla a mishi adua a raka shi zuwa kabarinsa,a binne shi da kasarsa, kuma ana kula da kaburbura kada wani abu na walakanci ya same su,
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Duk wanda ya bi jana'izan musulmi yana mai imani da neman lada ya kasance tare da shi har aka masa salla aka gama binne wa to zai koma da lada kiradi biyu,ko wani kiradi ya kai kwatankwacin Dutsen Uhudu.)

Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Duk wanda ya wanke musulmi ya kuma rufa mishi asiri to shi ma Allah zai suturce shi daga zunubai, wanda ya yi mishi likkafani Allah zai tufatar da shi tufafin sundusi(Alhariri).

Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Idan kun zo yi wa mamaci salla to ku kebance adua gare shi).
An karbo daga zaidu dan Sabit Allah kara yarda a gare shi yace :( Mun fita tare da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yayin da ya iso Baki'a sai ga wani sabon kabari sai ya tambaya game da shi, sai suka ce wance ce, yace: sai ya gane ta, sai yace :Me ya sa baku sanar da ni ba? Sai suka ce : ka kasance kana baccin kailula kuma kana azumi sai mu ka ji nauyin kada mu cutar da kai, sai ya ce : kada ku yi haka, kada wani daga cikin ku ya rasu face kun sanar da ni muddin ina tsakaninku, domin salla ta a gare shi rahama ce,sai ya zo kabarin sai muka yi sahu a bayansa sai ya yi mar kabbarori guda hudu).
Dukkan al'umar da take bada hakkoki don da'a ga  Allah  da koyi da sunnan Manzon Allah, to  zata dunkule ta yi karfi mazajenta kuma zasu samu daukaka, haka kuma duk makiyi mai musu dakon sharri ba zai samu kofa ba da zai jefa musu sharri ba ko dama da zai wargaza tsakaninsu ba, ko ya datse kauna da ke tsakanin 'ya'yan al'umar ba.     
Allah Madaukakin sarki ya ce : (Wadanda suka zo bayansu suna cewa ya Ubangijinmu ka gafarta mana da 'yanuwanmu  wadanda suka gabace mu da imani, kar ka sanya wani kulli a cikin zukatanmu game da wadanda suka yi imani, ya Ubangijinmu lalle kai Mai tausayi ne mai jinkai).           

السبت، 17 نوفمبر 2018

HARSHE DA ILLOLIN SHI


HUDUBAR MASALLACIN ANNABI TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA  A GARE SHI 8-3-1440 NA SHAIK ABDALLAH BIN ABDURRAHMAN ALBU'AIJAN
HUDUBAR FARKO
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya halicci mutum  ya fifita shi, ya bashi hankali ,  wanda da shi ne ake gane abu  sannan kuma shari'a take hawa kan mutum,  ya horar da shi kuma ya bashi kyautan harshe wanda da shi ne ake iya magana   da bayani  ya kuma sanar da shi  ,  tsarki ya tabbata  ga wanda   ya yi shi kuma ya daidai ta shi      kuma albarkar Allah ta bayyana,Mafi kyawun masu halittawa .
   Na  shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya   , kuma na shaida  Annabi Muhammadu bawan sa ne kuma Manzon sa ne    kuma ya turo shi da shiriya da addini na gaskiya  yana mai shaida kuma da albishir da gargadi   sai ya zo da gaskiya  ya kuma yi gaskiya tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ,  da iyalan sa da sahabban sa da aminci tabbatacce mai yawa  
BAYAN HAKA:
      To  lallai  mafi alherin zance shi ne maganan Allah   mafi alherin shiriya  kuma  shi ne shiryarwar Muhammadu dan Abdullahi  ,  kuma dukkan bidi'a bata ne kuma dukkan bata yana wuta .
      YA KU BAYIN ALLAH !
  Ina muku wasiyya da ni kai na da jin tsoron Allah ,  shi ne wasiyyar Allah ga mutanen farko da na karshe   (Hakika mun yi wasiyya ga wadan da aka bawa littafi gabannin ku da ku kan ku da ku ji tsoron Allah )
   YA JAMA'AR MUSULMI:
          Suka irin na harshe  yana shiga da zurfi  kuma yana da tasiri matsananci  da ke tsayawa a zuciya .   
Suka irin na mashi yana iya warkewa  *** Amma suka irin na  harshe bai warkewa
    Harshe   na'ura ne na bayyana magana da fasaha kuma   shi  ke  fassara  abin da ke zuciya  sifan shi dan karami ne amma  sukan shi na da girma  biyayya gare shi  abu ne mai girma  da laifin shi abu ne mai girma da shi ne kafurci ke bayyana  ko imani  wanda kuma su dinnan su ne makura na da'a da sabo ,  yana da fage mai fadi a alheri , kamar yanda  yake da    da makamancin shi wurin girma na sharri,  da shi ne  ake yada tuhume-tuhume    ake kuma kazafi  ga mata katangaggu gafalallu muminai , da shi ne kuma fitintinu da rikece-rikece ke aukuwa  kuma da shi ne boyayyun abubuwa ke bayyana  , kuma  da shi ne ake halatta abubuwa dake masu alfarma ,  kuma ake shuka fitintinu da gaba da bakin ciki da hasara cikin zukata  , da shi ne kuma ake zagi kuma ake yaface  ake annamimanci kuma da zunde, da yada jita-jita  kuma da tsinuwa da cin nama da  kazafi da alfasha da kuma maganar banza, da batsa da suka , bai gajiya da motsi , kuma bai raguwa sabo da magana, amma kuma dukkan haka abu ne kiyayye , adananne, kuma zaa yi wa mutum hisabi game da su ranan da zaa yi narkon azaba. (Baya lafazi da wata magana face a  like da shi akwai mai tsaro halartacce )  (Wata rana Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya rike harshen sa sai ya ce :- ya Mu'az ka kiyayi wannan!  sai Mu'az ya ce : wai shin ana kama mu da abin da muke furtawa?  sai Annabi ya ce : Mahaifiyar ka ta yi wabin ka   ya kai Mu'az  shin akwai abin da yake kifar da mutane cikin wuta a bisa fuskokin su  ko hancin su  face abin da harsunan su ke girbe musu .
   (An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi  kan cewa  ya ji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa :- '' Lallai bawa yana fadin magana ta kalma  da zata shigar da shi cikin wuta  ta kai shi nesa da ya fi nisan tsakanin  gabaci da yammaci)
         
(An karbo daga Anas Allah ya kara yarda a gare shi ya ce :- wani yaro ya yi shahada a cikin mu ranar Uhud sai a ka samu  wani dutse a daure a cikin shi sabo da  yunwa  sai mahaifiyarsa ta share masa turbaya a fiskan shi ta kuma ce: ''  Ina maka murna ya dana da Aljanna  sai manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce wa ya sanar da ke  watakila ko yana yin zance cikin abin da bai shafe shi ba '')     
 Wata rana Ibnu Mas'ud ya hau kan dutsen safa sai ya rike harshensa sai  yace : (ya harshe ka fadi alheri za ka samu riba, ka kame daga fadan sharri zaka kubuta,tun kafin ka yi nadama.sannan sai ya ce : (na ji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa : Mafi yawan kusakuran dan'adam  na samuwa ne daga harshensa).
Ya ku bayin Allah!
Ya ishi mutum laifi ya rena dan'uwansa musulmi, dukkan musulmi haramun ne jininsa da dukiyansa da mutuncinsa gurin  musulmi ,
Lallai   ambaton musulmi ga dan uwan shi da wani abu da baya so,  a yana halarce   zagi ne da suka  a baya nan kuma  in ya yi sukan a jikinsa ne ko addininsa  ko duniyarsa  ko cikin halittan sa ko dabi'un sa ko  dukiyarsa ko dansa  ko matarsa  ko tufafinsa  ko harkarsa  duka daya ne sawa'un da lafazi ya yi ko nuni  ko da wata alama ko da rubutu  ko hikaya,   to duka wannan in har yana tattare da shi giba  ne,  idan kuma babu tare da shi giba ne da zalunci da karya da kage .
  YA KU BAYIN ALLAH:
Cin kudin ruwa (RIBA) yana da kofofi saba'in da   biyu mafi karancin sa shi ne   mutum ya yi zina da mahaifiyar sa  dirhami  na riba  ya fi zina sau talatin da shida  lallai  kuma riban da ya fi ko wanne     lallai  kuma riban da ya fi ko wanne shi ne ka  kutsa cikin cin mutuncin dan uwanka musulmi ba tare da hakki  ba  .
     YA KU JAMA'AR MUSULMAI:
Lallai mafi girman laifuka na harshe da musibarsa  da ragar sa  da tarkon sa ;  shi ne yada jita-jita wanda  suke na karya    da  tsegumi  dabab-daban,   da saka karerayi na banza  da cire yarda tsakanin musulmai har a samu mummunan zato tsakanin su, da rashin jituwa  zai bata 'yan uwantaka dake tsakanin su  sai su rarrabu,  hadin kansu ya wargaje su rasa aminci .
 Sau nawa ne jita-jita   take fadawa akan wadan da suka barranta ta sa su cikin  damuwa  sau da yawa tana rusa manya   sau da yawa kuma tana katse  zumunci ,  sau dayawa tana haifar da manyan laifuka   , sau dayawa  takan rabe alaka da abokantaka  kuma sau da yawa tana rusa  al'uma    sau da yawa ta rusa iyalai ta raba tsakanin masoya  sau da yawa ta sa hasaran dukiya  kuma ta sarayar da  lokaci ,  kuma sau dayawa ta bakanta zukata   sau dayawa ta bakanta zuciya kuma ta kuntata  rayi  ta  haifar da hasara,  sau da yawa  jita-jita  ta wargaza tafiyar  wasu mutane.
     Hakika Allah madaukakin sarki ya ce :- ( Ya ku wadan da suka yi imani   ku  nisanci mafiya yawan  zato   lallai sashin zato laifi ne )
(Ya ku wadan da suka yi imani idan fasiki ya zo muku da wani babban labari  to ku nemi bayani domin kada ku cuci wadansu mutane a cikin jahilci,  sabo da haka  ku wayi gari akan abin da kuka aikata kuna masu nadama )    
An karbo daga Abdullahi dan Umar ya ce na ji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gage shi  yana cewa  (Duk mutumin da ya ambaci wani mumini da abin da babu shi tare  da  shi  , Allah zai bashi masauki na  RIDGATUL KHABAL  shi ne wuri mai matsanancin  tabo da diwa na  'yan wuta )
(An karbo daga sahal  dan Mu'az daga mahaifin shi  Allah ya kara yarda a gare su  ya ce:  Daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce duk mutumin da ya jefi wani musulmi  da wani abu don ya bata shi   Allah zai tsare shi akan gadan jahannama ` har sai ya fita daga abin da ya ambata ).
     YA KU JAMA'AR MUSULMAI:
Lallai Allah ya haramta taba mutuncin Musulmai kamar yadda ya haramta  jininsu da dukiyoyinsu  sai dai ma ya shar'anta bada kariya  ga mutuncin su  ta hanyar amfani   da rai  da dukiya  lallai   taba mutuncin musulmi  ta hanyar  jita –jita  da yada   ta a sarari  da kuma  da tallata ta  ta hanyar amfani  da jefa  shakku da  zato  da kirkira   da karya da kage da   fadin zur da  da izgilanci  da yada guba da fitintinu  ta hanyoyin sadarwa  da kuma kafafen  sadarwa   dukkan hakan na daga cikin cin mutunci wadda aka hana   kuma yana cikin manyan laifuka masu halakarwa  da fitintinu masu batarwa  ya wajaba ga ko wani musulmi ya kiyayi irin wadan nan.
 An karbo daga Abu Darda Allah ya kara yarda a gare shi ya jingina shi zuwa ga manzon Allah ya ce :- (Duk wanda ya yada wata kalma mara kyau game da musulmi  don ya bata shi da ita a duniya  to ya zama hakki  a kan Allah da ya narkar da shi  a wuta har sai ya kawo  abunda ke zartar da ita ).
Ku saurara; duk wanda ya yada alfasha  kamar wanda ya fare ta ne kuma yana da alhakinta da alhakin wanda ya nakalto  ta daga gare shi har  zuwa karshenta.
  (An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare  shi ya ce : Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:  ya ishi mutum  karya  da ya bada  labarin duk abin da ya ji  muslim ne ya  rawaito.
Ina neman tsarin Allah daga sharrin shaidan abin jefewa
(A lokacin  da kuke marabarsa  da harsunan ku  kuma kuna cewa  da bakunan ku  abin da ba ku da wani ilimi game da shi ,  kuma kuna zaton sa mai sauki ,  alhali kuwa,  shi a wurin Allah  , babba ne )

HUDUBA TA BIYU
Dukkan  yabo  da godiya sun tabbata ga ga Allah  wanda  ya  kare jini da mutunci da dukiya   ta hanyar addininsa  kuma ya yi alkawarin narkon azaba ga  wanda ya  ketare iyaka akan su   da ayyuka ne ko da fadi,  ya sanya muminai  'yan uwan juna ya shuka soyayya da kauna a tsakanin su  .
  YA JAMA'AR MUSULMAI :
 Lallai keta alfarma da kuma bibiyan  al'aura yana daga cikin manyan  musibu da kuma jarabawa  da kuma matsanancin fitintinu  da mafi girman abin ki  daga cikin abin da yake haifar da shi  shi ne raunin imani a zukuta.
  An karbo daga Abi Barza Al-aslami   Allah ya kara yarda a gare shi ya ce Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :-  ( Ya tawagar wadan da suka yi imani da harshe alhali imanin bai shiga cikin zuciyarsu ba!   kada ku ci naman musulmai , kada ku bibiyi al'auransu   ,  domin duk wanda ke bibiyan al'auran su Allah ma zai bibiyi al'auransa  , wanda Allah ya bibiyi  al'auransa to zai kunyata shi har a cikin gidansa ) Ahmad ne ya rawaito.
          To ku kare mutuncinku ku kiyaye harsunanku.
Ya ku bayin Allah!
Lalle musulmi na da alfarma mai girma wacce shari'a ta bata kariya kuma ta kiyaye ta,   kuma ya yi narkon azaba ga wanda ya mata ta'addanci, baya dacewa ga musulmi da ya ci zarafin ta  ko kuma ya yi kokari wurin   keta alfarmarta .
  Abdullahi dan Umar ya dubi kaba wata ran sai ya ce :- '' Abun mamaki da irin girman ki abin mamaki da irin girman  alhurmar ki amma kuma mumini  alfarmar shi ya fi girma a wurin Allah  akan ki   ''
 An karbo daga abi bakarata Allah ya kara yarda a gare shi ya ce :- Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya  yi mana khuduba ranar   sallan laiha sai ya ce :  ko kun san wani yini ne yau? sai muka ce Allah da Manzon sa ne suka  fi sani. sai ya yi shuru , har muka zaci cewa zai sanja mishi suna ne.  sai ya ce a she wannan ba ranar babban salla ba ne ? sai muka ce ,  e, haka ne , sai ya ce wani wata ne wannan?, sai muka ce Allah da Manzonsa ne suka fi sani  , sai ya yi shuru har muka zaci zai sanja mishi suna ne sai ya ce: -  ashe ba zulhijja ba ne ? ,  sai muka ce: e, haka ne,  sai ya ce wani gari ne wannan? Sai muka ce: Allah da  Manzon sa ne suka fi sani.  sai ya yi shuru har muka zaci zai sanja mishi suna ne sai ya ce: ase ba gari mai alfarma ba ne?,  sai muka ce e, haka ne.    sai ya ce lallai jinannakin ku da dukiyoyin ku da mutuncin ku  haramun ne a gare ku kamar alfarmar wannan wunin na ku  a  cikin wannan wata na ku a wannan garin  na ku har zuwa ranar da  za ku hadu da Ubangijin ku , ku saurara shin na isar da sako?  sai suka ce e, sai ya ce: ya Allah ka shaida  . To wanda yake halarce ya isar ga wanda baya nan  sau da yawa wanda ake isarwa  sai ya fi kiyayewa akan wanda  ya ji.  kar ku koma kafurai a bayana   sashin ku na dukan wuyan sashi ) Buhari ne ya rawaito

BAYIN ALLAH :
Lallai nisantar abubuwan da aka haramta kuma aka yi hani a kai ana fifita shi da ayyukan da'a na kwarai da kyawawa da ayyuka na gari , lallai wanda aka yiwa wasoso shi ne wanda zai yi kokari yayi aiki kuma ya tattara   sai dai shi din nan wawa ne, yana almubazzarantar da abin da ya tattaro.
  An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi  ya ce: Manzon Allah tsira da  amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : -ko kun san wane ne muflis  sai suka ce  '' Muflis a cikin mu shi ne wanda ba yi da dirhami ko  kuma wani abu na jin dadi  sai ya ce : - (; Lallai muflis  a cikin al'uma ta shi ne  wanda zai zo  ranar alkiyama da salla da azumi da zakka  zai zo ya zagi wancan , ya yi kazafi ga wancan   ya ci dukiyan wancan , ya zubar da jinin wancan  ya duki wancan  , sai a bawa wannan daga kyawawansa shi ma wancan a bashi daga kyawawan sa  to idan kyawawan sa sun kare  kafin a kare hukuncin abin da ke kanshi  nasu,  sai a dauko daga kusakuran su  a  dora mishi sannan sai a jefa shi a wuta )    
 YA KU JAMA'AR MUSULMAI :
Lallai Gamammiyar daular larabawa ta kasar saudiya  gari mai masallatai biyu masu alfarma kuma masaukar wahayi , kuma alkiblar musulmai ,  kuma abin son zukatan su  Allah ya zabe ta   don ta zama wurin da addinin shi zai taso   kuma mimbarin  da'awa zuwa gare shi  ,  kuma makoma ne na masu kadaita Allah , hasken musulunci  ya  yadu daga nan ginshiki na  adalci ya kafu  da aminci da ilimi da imani  ta rungumi  duk  wanda ya zo gare ta cikin musulmai  irin rungumar da uwa take yiwa dan ta tare da tausayi  to Allah ya sakawa jagororin ta da sakayya mafi alheri .
 Ku saurara lallai  tsegumi  da yada  jita-jita da abubuwan takaici, wanda mahassada ke rurawa, masu kulli a zuci game da wannan kasa  mai albarka su yayata shi,lalle ba wani abu ba ne sai fitintinu da matsanancin yaki da makiya addininnmu suke kunnawa, masu dakon wani mummunan abu ya faru ga al'umarmu, to muna kankan da kai zuwa ga Allah muke neman tunkude sharrinsu da shi ka mana maganinsu,
Ya Allah ka kiyaye mana wannan gari da kiyayewanka, ka bata kulawa da kulawarka,
Ya Allah ka sanya ta cikin aminci da natsuwa, da sauran garuruwan musulmai, ya Ubangijin talikai.
Ya Allah ka daukaka musulunci da musulmai.   

السبت، 3 نوفمبر 2018

KWANCIYAR HANKALI A MUSULUNCI


HUDUBAR MASALLACIN ANNABI NA SHAIKH ABDULMUHSIN ALKASIM 24 -2-1440AH
HUDUBAR FARKO :
  Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Madaukakin sarki  muna gode mishi kuma muna neman taimakonsa , muna neman gafarar sa  , kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu , da munanan ayyukanmu , duk wanda Allah ya shiryar da shi babu mai batar da shi , duk wan da ya batar kuma babu mai shiryar da shi , na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya , kuma na shaida Annabi Muhammadu bawansa ne kuma Manzonsa ne, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa  da sahabbansa da aminci tabbatacce mai yawa .
Bayan haka:
Ku ji tsoron Allah - ya ku bayin Allah – cancancin tsoronSa da shi ne ake neman ni'imomi  kuma ake tunkude azaba.
Ya ku musulmai!
Duniya gidan jarrabawa ne da gwaji, an dabi'antar da ita bisa gurbata da da kuma wahala,mutum zai yi kokari a cikinta tare da wahala Allah Madaukakin sarki ya ce : ( Hakika mun haliccin mutum cikin wahala)
Rayuwar mutum a duniya kadan ne, bai da wani abu a rayuwarsa sai abin da ya tsarkaka,
Kuma hutu da gushewar bakin ciki da bacin rai abin nema ne ga kowani dan –adam, da haka ne zaa samu daddadan rayuwa, da morewa na jin dadi.
Dukkan halittu na cigiyar walwala da jin dadin rayuwa kuma suna nemanta, Asalin sa'ida shi ne yelwatar zuciya, da samun kwanciyar hankali, idan Allah ya nufi bawa da alheri zai fadada kirjinsa babu wata  ni'ima mafi daukaka da ta kai ta, ita ce sababi  mafi girma na shiriya da ni'ima mafi daukaka, Ibnul Kayyim Allah ya mishi rahama ya ce : (kamar yadda yalwar zuciya take sababi na shiriya to kuwa asali ne na dukkan ni'ima da Alheri)
Sabo da girman wannan ni'imar ne Annabi Musa ya roki UbangijinSa  Allah ya mishi baiwar wannan a farko lokacin da ya tura shi zuwa ga Fir'auna sai ya ce : (Ya Ubangiji na ka bude Min kirji na)
Allah ya fara kirgo ni'imarsa da shi ga Annabi sai ya ce : (  shin bamu bude kirjinka ba ne).
Allah ya sanya shi sababi na dukkan komi a duk lokacin da abu ya yi girma to sabuban shi sai su  yawaita,samun shi ya saukaka,mafi cikan sabuba da kamalarta shi ne wanda sharia ta yi nuni gare ta ta  shiryar,   Babu abin da ya fi buda kirji kamar sanin Allah da sunayenSa da sifofinSa da kadaita shi da bauta,-tsarki ya tabbata a gare shi, gwargwadon haka da karfinSa gwargwadon  budewar zuciyarsa da samun sawabarsa, Ibnu Hazmi Allah ya kara yarda a gare shi ya ce " Na yi tunani game da ayyukan bayi sai naga duka suna neman  abu guda ne,ko da kuwa hanyoyinsu ya sha banban gurin samun shi amma gaba daya na ga suna yi ne don tunkude bakinciki da bacin rai daga kawunansu,ban ga hanya ba cikin hanyoyi da zai kai gare shi,- watakila wasun su ma suna kai wa ga akasin haka ne –sai da fiskantar Allah shi kadai da fifita neman yardarsa akan duk wani abu da ke kishiyantarsa, bawa bai da abin da ya fi wannan hanya kuma yafi sadarwa zuwa ga walwala da jin dadi kamarsa".
Mafi kamalan  halittu  a dukkan wata sifa da ke sanya walwala da jin dadi shi ne Annabin mu Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kuma mafi koyi da shi cikin mutane shi ya fi samun cikakken natsuwa da budewan kirji da jin dadi da samun ni'ima.
Mafi girman abin da ake samun walwala da jin dadi shi ne imani da aiki na kwarai, da su ne zuciya da gabbai ke gyaruwa, da daidaituwar ciki da waje,da shi ne ake samun daddadan rayuwa da walwala na har abada, Allah Madaukakin sarki ya ce  : (wanda ya yi aiki na gari na miji ko mace alhali yana mumini lalle zamu raya shi rayuwa daddada ) AL Nahl :97
Ba abin da ya fi sa walwala da jin dadi da kwanciyar hankali kamar kaunar Allah da komawa gare shi da jin dadin bauta masa, Shaikhul Islam Allah kara ya rahamce shi ya ce : (Idan baka jin dadin aiki a cikin zuciyarka ba da kwanciyar hankali to ka tuhumi zuciyarka don kuwa lalle Allah Mai girma  Mai yawan godiya ne )  
Zabin Allah ga mutum ya fi zabinsa ga kansa, Allah shi ya fi tausayawa bayi akan kansu, wanda yayi imani da kaddara  na alherin sa da sharrinsa zai samu kwanciyar hankali da budewar kirji,Allah Madaukakin sarki ya ce : ( Wanda ya yi imani da Allah zai shiryar da zuciyarsa)  Alkama Allah ya mishi rahama  ya ce :(shi ne muminin da musiba zata same shi sai ya san daga Allah ne sai ya yarda ya mika wuya)
Bayi suna kai komo  ne a rayuwarsu a tsakanin sauki da tsanani  ba wanda ya isa ya fita daga dayan biyun ko ta kaka, samun walwala cikin hukuncin Allah da godiya a halin yalwa da hakuri a halin kunci  ko cuta Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : Mamaki da al'amarin mumini, lalle al'amarinsa duka alheri ne a gare shi, ba wanda ke da haka sai mumini, in yalwa ko  sauki ya same shi sai ya yi godiya, sai ya kasance alheri a gare shi, idan tsanani ya same shi sai yayi hakuri sai ya zama alheri gare shi.) Muslim ne ya rawaito.
Abin da Allah ya hukunta wa bawansa shi ya fi alheri gare shi, ya yin da Allah ya jarrabi Maryam da haihuwar yaro ba tare da Uba ba sai ya ce da ita : (To ki ci ki sha ki sanyaya idanuwanki)
Wanda yayi imani da gamuwa da Allah da ladarSa sai ransa ya ta' allaka da Maifalala akan abin da bai kai shi falala ba,sai abin da aka alkawarta masa ya rarrashe shi daga abin da aka rasa  shi,  da wannan ne duniyarsa  da lahirarsa zasu  gyaru,
Kyautata zato ga Allah na cikin ibadoji da ke haifar da aminci da walwala ma'abocinta, baw na da abin da ya zata game da Ubangijinsa in alheri ya samu alheri in kuma  sharri ya samu sharri, Allah Madaukakin sarki ya ce a hadisin Alkudsi : (Ni ina gun da bawa na ya zace ni) Bukhari da Muslim suka rawaito.
Fatan nagari na kawo budewar kirji da kwanciyar hankali,kuma yana daga cikin  kyautata zato ga Allah Madaukaki.
Mabudan al'amura da ragamarsu na hanun Allah ne shi kadan shi, yana juya zukata yadda ya so wurin baci ko gyaruwa ko kunci ko kwanciyar hankali da walwala, da jin dadi ko tashin hankali, to dogaro ga wanda hakan ke hanunshi da maida al'amari zuwa gare shi da aminta da shi wajibi ne a sharia, kuma garkuwa ce ga ma'abotanta, Allah Madaukakin sarki ya ce : (Duk wanda ya dogara ga Allah to Allah ne ma'ishinsa)
To arzikin bayi a hanun Allah ya ke ba wani rayi  da zai mutu sai ya kammala  cinye  arzikinsa to ka yarda  ka gamsu ka ji dadi da abin da Allah ya baka na kasonka,
Duk wanda ya koma zuwa ga Allah to Allah zai taimake shi ya shige mishi gaba ya isan mishi,Allah Madaukakin sarki ya ce: ( Wadan da mutane suka ce da su Lalle mutanen sun muku gangami ku tsorace su, sai  hakan ya kara musu imani kuma suka ce ;Allah ne Ma'ishinmu kuma madallah da abin dogaro. Sai suka juya da ni'ima daga  Allah da falala, ba mummunar  abu  da ya shafe su kuma suka bi yardar Allah Allah ma'aboci falala ne mai girma ).
Duk wanda ya yi kwadayin samun  sa'ida da walwala da kwanciyar hankali to ya kwankwasa kofar Mai karamci to lalle Allah na kusa da wanda ya roke shi, kuma bai tabar da wanda ya yi fata daga gare shi, da adua ne al'amuran duniya da lahira ke gyaruwa, na daga cikin adu'o'in Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi (Ya Allah ka gyara min addini na wanda shi ne kariya ga al'amari na, ka gyara min duniya ta wacce cikinta rayuwa ta  take, ka gyara min lahira ta wacce gare ta zan koma ka sanya rayuwa gare ni kari ne ga dukkan alheri , ka sanya mutuwa ta zama hutu gare ni daga dukkan sharri)Muslim ne ya rawaito.
Ambaton Allah na da tasiri na ban al'ajabi wurin samar da kwanciyar hankali walwala da natsuwar zuciya da gusar da bakin ciki da bacin rai Allah ya ce : (wadanda suka bada gaskiya zuciyarsu take natsuwa da ambaton Allah, to da ambaton Allah zukata ke natsuwa,)
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance  yana cewa yayin bakin ciki : (   "La ilaha illallahul-Azimul-Halim. La ilaha illallahu Rabbul-'Arshil-'Azim. La ilaha illallahu Rabbus-samawati, wa Rabbul-ardi, wa Rabbul-'Arshil- Karim.) Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Maigirma mai hakuri .ba abin bautawa da gaskiya sai Allah ubangijin Al'arshi mai girma, Ba abin bautawa da gaskiya sai Allah ubangijin sammai kuma Ubangijin  kasa  kuma Ubangijin Al'arshi mai girma)  Bukhari ne ya rawaito
Bukhari ne ya rawaito
Mafi  falalan zikiri shine Alkur'ani mai girma shi ne maganar Allah  akwai shiriya tattare da shi da waraka, Allah Madaukakin sarki ya ce : (Ya ku mutane hakika gargadi ya zo muku daga Ubangijinku da waraka  ga abin da ke cikin kiraza da shiriya  da jinkai ga muminai )
Mafi cancantan  wadanda zasu samu  walwalar zuciya da kwanciyar hankali a halittu sune mahaddatan Alkur'ani, Allah Madaukakin sarki ya ce : (Taha. Bamu saukar da Alkur'ani gare ka don ka wahala ba )   
A Tasbihi da Tahmidi  da yawan sujada  da dimantan biyayya  akwai samun annashwa da kwanciyar hankali, da tafiyar da bakinciki da kunci,  Allah Madaukakin sarki ya ce : (Hakika mun san lalle kirjinka na kuntata  sabo da abin da suke fada. To sai ka yi tasbihi da godiyar Ubangijinka kasance cikin masu sujada . ka bautawa Ubangijinka har mutuwa  ta zo ma.)
Da lazimtar tsoron Allah akan samu yayewan bakin ciki da tafiyar  da bacin rai, Allah Madaukakin sarki ya ce : (Duk wanda ya ji tsoron Allah zai sanya mishi mafita ) kuma da ita ne akan samu saukin abubuwa Allah Madaukakin sarki ya ce : (Duk wanda ya ji tsoron Allah zai sanya mishi sauki cikin lamuransa)  
Sallah haske ne ga ma'abocinta  kuma tana taimakawa  wurin samar da kwanciyar hankali da natsuwa da tafiyar da bakin ciki Allah Madaukakin sarki ya ce : (ku nemi taimako da hakuri  sallah)
Na daga cikin koyarwan shi Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi idan wani abu matsananci ya  dame shi sai ya  bazama zuwa ga sallah.) Abu Dauda ne ya rawaito.
Idan bawa ya bude wuninsa da sallah sai sauran wunin nasa ya yi kyau, to duk wanda ya yi sallar asuba yana cikin kariyar Allah, wanda ya yi ta tare da nafilarta Allah zai isan masa karshen wuninsa, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Lalle Allah yana cewa ya Dan-Adam : kar ka gaza yin raka'a hudu a farkon wuni to zan kare ka karshensa)Ahmad ne ya rawaito.
Ilimin da aka gado daga Allah da manzonsa tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi  idan ya hadu da aiki yana sanya kwanciyar hankali da walwala har zuciyar ta fadada ta fi duniya fadi, ma'abota ilimin kuma zasu fi kowa kwanciyar hankali cikin mutane da walwala da fadin kirji da jin dadin rayuwa, kuma mafi kyan mutane dabi'u.
A duk lokacin da ilimin bawa ya karu to zai dada samun kwanciyan hankali da walwala a zuciyarsa , Allah Madaukakin sarki ya ce : (Shin kuma wanda ya kasance matacce  sa'annan muka rayar da shi kuma muka sanya wani haske dominsa, yana tafiya da shi yana zama kamar wanda misalinsa yana cikin duffai, shi kuma ba mai fita ba daga gare su?)
Ibnul kayyim ya ce game da shaikhul Islam : "Ban ga wanda ya fi shi jin dadin rayuwa ba duk da matsatsi da yake ciki da rashin wadata na abin duniya,sai dai ma kishiyan hakan, tare da daure shi da ake yi da tsoratarwa da tursasawa, amma duk da haka yana cikin wanda ya fi mutane jin dadin rayuwa  ya fi su fadin kirji da kwanciyar hankali, da karfin hali da dadin rai ga fiskarsa cike da fara'a da walwala ta ni'ima."
Kyautatawa mutane alheri ne bai kawo wani abu sai alheri, ba za ka taba ganin mutum mai karamci mai kyautata wa mutane ba face shine mafi kwanciyar hankali cikin mutane, kuma mafi zama cikin dadin rai a mutane  kuma mafi ni'imar zuciyarsa  a cikinsu, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Misali marowaci da mai sadaka, kamar mutane biyu ne ke sanye da sulken yaki ya takure hannayensu zuwa nononsu da hakarkarinsu  a duk lokacin da mai sadaka ya yi  sadaka sai  silken ya dada fadada  har ya suturce shi  zuwa yatsun shi yana share gurbin sa, amma shi munafuki a duk lokacin da ya nufi sadaka sai sulken ya kuntata  ko wani da'ira na sarkan  ya manne a gurbin shi.) Muslim ne ya rawaito.
Wanda ya muamalanci mutane don Allah ya huta  domin ba zai nemi tsinkayan  yabo  ko kuma  nadaman suka ba  halin shi tamkar misalin fadin Allah ne . ( Tamkar fadin Allah  madaukakin sarki ne :-   Lallai mu muna ciyar da ku ne  ,  don neman yardan Allah  ba ma bukatan sakayya ko godiya daga gare ku  ).
Hakan na dada karfafa a wurin mu'amala da  makusanta  da  kuma wanda ke da karfin alaka da su .
 Hakika za ka ga abin da ba ka so daga wasu mutane ,  to, mai hankali  bazai tawaye kyautatawan su ba sabo da tawaya  da ya fito daga gare su  ko ka yanke musu zumunci sabo da gajartawa  da haka ne mutum zai rayu  cikin tsanakin shi  da kwanciyan hankali  a ko wani hali  , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : - (Kar mumini ya tsani mumina –wato: kar ya ki ta – idan ya tsani wani hali daga gareta to zai yarda da wani halin) Muslim ne ya rawaito
A cikin zama da salihai da ma'abota ilimi da addini  akwai wani abu na debe kewa da samun walwala  kuma a nan ne mutum ke samun ilimi da hikima  zuciyar sa ta tsarkaka  ya zama mai kyau a cikin abokan sa  wanda ya koma zuwa ga ma'abota shawara da hankali  cikin al'amuran sa  zai samu kwanciyar hankali da waraka na zuciya  abinda ya rikice mishi zai gushe  Allah madaukakin sarki ya ce :-(Idan wani al'amari ya zo musu  na aminci ko tsoro sai su yada shi , dama sun maida shi  zuwa ga Manzon Allah  da jagororin su  ma'abota ra'ayi a cikin su  da wadan da suke tsinkayo fahimta ko hukunci  da sun san shi daga cikin su ).
Kiyayyan shaidan da dan adam baya yankewa   cikin yin neman tsari daga shaidan akwai koran wasuwasin na shi  dake jirkita   kwanciyar hankalin dewa daga cikin mutane ,  musulunci  na kwakwari don samar da sabuban   da za su kwantar da hankali su haifar da walwala ga musulmi tun lokacin da ya tashi daga baci shaidan na aiki don akasin haka  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Lallai shaidan yana   kulli  uku  a karshen kayin dayan ku  idan ya yi barci  yana buga ko wani daya daga cikin kullin  kana da  dare mai tsawo , ka kwanta   to idanya tashi ya ambaci Allah sai kulli guda ya warware in ya yi alwala sai kulli guda ya warware idan ya yi salla sai kulli guda ya warware  sai ya wayi gari mai kuzari  cikin tsarkakakken rayi   idan baiyi haka ba sai ya wayi gari yana da kazantaccen rayi mai kasala    ) Buhari da muslim ne suka rawaito
Kuma karfin mumini tushe ne mai girma   na samun  warakan zuciya  da walwala  ba zai biyewa abubuwa na wahami ba  zai kuma saki jiki don bakin ciki ba ko ya samu rauni  a gaban abubuwa na ki  sai dai ma zuciyan shi na kafe  yana kuma  tare da yakini da sakankancewa   cewa   lallai tare da  wahala akwai sauki   idan bawa ya halarto da falalar Allah  da ni'imar sa a gare shi hakan sai ya haifar masa  da  sabon godiya  da zai kwantar mishi  da hankali   kuma   ya sanya mishi walwala  .
Kuma wadatar zuci tushe ne na arziki,    kuma yana daga cikin mafi amfanin abin da ake yin magani da shi na zukata , abinda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya nusar zuwa gare  shi a fadin sa (ku yi dubi zuwa ga wanda ke kasa da ku kar ku yi dubi zuwa ga wanda ke sama da ku  don hakan shi ya fi dacewa  da kar ku raina ni'imar Allah  a gare ku)Buhari da muslim ne suka rawaito shi
Wanda ya tattara zuciyar sa  a bisa wunin sa da lokacin sa  zuciyan shi za ta natsu ba zai yi bakin ciki ba cikin abin da ya shude  ba zai bata rai ba cikin abin da yake fiskantowa   to abinda ya shude ba zai dawo ba  . Abu mai fiskantowa kuma gaibi ne rubutacce na daga cikin adu'o'in shi Manzon Allaha tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi   akwai ;;;( Ya Allah ina neman  tsarin ka daga  sharrin bakin ciki da bacin rai)  . Buhari ne ya rawaito
           Rashin amfana da  lokaci  tushe ne na bakin ciki da bacin rai  ,    wanda ya raya lokacin shi da aiki na kwarai ko ilimi mai amfani  wannan duka zai tafi daga gare shi, abunda ya tattaro walwala da sa'ada na cikin   neman taimakon Allah bisa ga abin da zai amfanar  da yin nesa da abin da zai sanya rauni ga bawa  ko ya raunana  zuciyar sa    da  karfin sa  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :-( Ka yi kwadayi bisa ga abin da zai amfane ka  ka nemi taimakon Allah , idan wani abu ya same ka kar ka  ce ba don na yi kaza-da kaza ba da kaza zai kasance domin lau tana bude aikin  shaidan )Muslim ne ya rawaito .
      Zunubai kofa ce  da musibu ke zuwa  ta gunta  ga bayi ,  da abin da ake sakawa mai laifi   da ita na daga bakin ciki da bacin rai da kunci    na zuci da kekasan zuciya  don ya zama ukuba na duniya  kafin na lahira  mafita daga haka shi ne yin nesa  daga sabo  da tuba zuwa ga Allah don ya warware  wurin kuncin  da  fadaduwan zuciya  haka nan kuma a wurin kadaici ya sanya debe kewa  .
     Tsarkake zuciya daga cututtukan sa yana kawo yayewan zuciya  ta samu walwala  yana kuma fadada shi  yana daga cikin adu'ar mumini  (Kada ka sanya kulli a cikin zukatan mu game da wadan da suka yi imani  ya Uabangijin mu lallai kai mai tausayi ne mai jin kai) bisa ga wannan sifa 'yan aljanna suke kasancewa Allah madaukakin sarki ya ce:-   (Muka  ci re daga cikin kirajen su  na kulli  kwaramai yana gudana a karkashin su kuma suka ce dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah   wanda ya shiryar da mu  zuwa ga wannan  ba mu kasance da  mu shiryu ba ba don Allah ya shiryar da mu ba  )
                BAYAN HAKA:
YA KU MUSULMAI:-
  To shi musulunci tushe ne na dukkan alheri   kuma  masdari ne na  dukkan samun sa 'ida da walwala   ma'abotan shi suna cikin aljanna  na gaggawa da ni'ima da baya yankewa  Allah madaukakin sarki ya ce :-(Wanda suyka kyautata a nan duniya da kyakkyawa suna  da kyakkyawa kuma  gidan lahira ya fi alheri  madalla da gidan masu tsoron Allah )
  Duk wanda ya san  shakawa irin na  jahiliyya da ma'abotan shi  zai san falala na ni'imar musulunci  da ma'abotan sa ba abin da zai  isar mishi sai godewa Allah bisa ga  hakan ,  da kuma riko da addinin sa da alfahari da shi  da tabbatuwa a kan shi da kiran halittu zuwa gare shi.
 Ina neman tsarin Allah daga shaidan abin jefewa 
Duk wanda Allah ya nufi ya shirye shi zai fadada zuciyar shi don musulunci,  wanda kuma ya nufi ya batar da shi zai sanya kirjin sa a kuntace cikin kunci  kai ka ce  yana haurawa ne  cikin sama  haka ne Allah yake sanya kazanta ga wadan da ba sa imani  ya Allah ka sanya albarka gare ni da ku a alkur'ani mai girma .
 HUDUBA NA BIYU
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah    bisa kyutatawan sa   da godiya a  gare shi bisa datarwarsa  da baiwar sa  na shaida  ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya  ina mai girmama sha'anin sa kuma na shaida Annabi Muhammadu bawan sa ne kuma Manzon sa ne   tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabban shi da amincin tabbatacce mai yawa da aminci mai kari .

YA KU  MUSULMAI:-
Allah ya yalwata kasar saudiya da ni'imomi masu yawa wanda ya fi ko wanne a cikin su shi ne ni'imar musulunci  da yaduwar shi  da kuma raya masallatai biyu masu alfarma da musu hidima da girmama wanda suka fiskanto su da bugawa da yada alkur'ani mai girma  a cikin sararin duniya  da bawa musulmai kulawa da musu hidima   a al'amuran su da yin hukunci da shari'ar Allah a kasar sa  kuma  ya sanya ta alkibla na musulmai , kuma zuciyar duniyar musulunci tare da abin da ya ni'imta a gare su na daga aminci da zaman lafiya da yalwa na rayu da jin dadin shi da kuma hadin kan jama'anta   da dunkulewan su  dukkan hakan da wanin sa  a falalan Allah ne  shi kadan shi  da kuma datarwa da Allah ya yiwa jagororin  ta   suka sanya abu na farko mafi muhimmanci  tun daga kafa wannan daula na musulunci tabbatar da kadaita Allah da bin Annabin sa  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  da hidima wa musulmai da yada ilimi na shari'a   wanda aka ciro shi  daga  littafi da sunna  da kuma bin sawun magabata na wannan al'uma  kuma duk yanda abu ya caccanza  da sautukan  wadan da suka saba mana  ba abinda zai karawa wannan kasa face  riko da musulunci da haduwa a kan kalma  tsakanin mabiya da jagororin su.
 Ya wajaba ga musulmai su kau da kai daga  wasu   jefe –jefe   da   jita-jitan masu  tada zaune tsaye  da rashin sauraro zuwa gare su   da shagaltuwa da abin da zai amfanar  . 
 Sannan ku sani lallai Allah na umartan ku da salati da aminci ga Annabin shi sai ya ce  a cikin littafin shi mafi hikima da  saukar :- (Lallai Allah da mala'iku suna salati ga Annabi  ya ku wadan da suka yi imani ku yi salati a gare shi  da aminci tabbatacce )