الجمعة، 25 مايو 2018

Ma'anar azumi da abubuwan lura da ya kumsa.


Hudubar Juma'a na  Masallacin Annabi na shaikh Muhammad Salah Al-Budair 9-9-1439AH
Ya ku masu azumi … farkon ramadana ya shude, har mun doshi na gomansa,
To a gaggauta a yi hanzari a yi kukan kura a dage, ku yi tsere cikin watanku kafin ya nade darensa  da tabarmarsa, ku gaggauci ramadana kafin ya tafi, ku ribace shi kafin ya shude,
Ya ku masu azumi !
Abin mamaki ga wanda zai riski ramadana azuminsa bai gyara shi ba, tsayuwansa bai girgiza shi ba, ranakunsa bai sanja  shi ba!
Abin mamaki ga mutumin da zai riski ramadana kuma yana kwadayin Aljanna da gafara da 'yantawa daga wuta amma ya sarayar da shi cikin  wasanni da da abubuwan da aka hana da haramtattu,
Ya kaiton wanda alherin ramadan ya tsere mishi!  ya hasaran wanda ya sarayar da watan ramadan!
An karbo daga Abu huraira Allah kara yarda a gare shi ya ce Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce  (Hancin shi ya  dongwali kasa; mutumin da aka ambace ni bai yi min salati ba, Hancin shi ya  dongwali kasa duk mutumin da ramadana ya shiga har ya fita ba a gafarta masa ba,hancinsa ya dangwali kasa wanda ya riski iyayensa biyu sun girma   basu shigar da shi  Aljanna ba) Tirmizi ne ya rawaito.
Ya wanda ke tambaya game da kurar hanya da tankaden gari da hadiyar nyawu ko suna bata azumi ko aa? Ya kai mai kiyaye kananan abubuwa  kuma ka yi sakaci a abubuwa masu girma! to ka kiyaye daga manyan zunubai  na alfahasha da laifuka, ka kiyaye daga cin dukiyan dan'uwanka musulmi, da cin mutuncin shi, da zambatan shi da zaluntarsa, da yaudararsa da mishi dabara.
Shin ko ya yi azumi mutumin  da ya kame daga ci ko sha a wunin ramadana alhali bai daina sakaci da yaransa ba ya barsu gurin matarsa da ya saka ba tare da kyautatawa ko tausayi ba ko tambaya game da su ko ciyarwa ba?
Shin ko ta yi azumi wacce ta haramta wa yaranta ganin mahaifinsu da ya sake ta ko ziyartarsa, ta karfafe su gun keta zarafin mahaifi da kuma fasikanci,?
Shin ya yi azumi mutumin da ya hana yaransa ganin mahaifiyarsu  da ya sake ta wacce ba dadi ga rayuwarsu sai da shinshinan  kamshinta, da ganin fiskanta da jin duminta irin na tausayi.
Shin ya yi azumi mutumin da ya kaurace wa matarsa ya kyale ta abar  zalunta an tauye hakkinta ratayayya ita ba mata ba kuma ba a sake ta ba.
Shin ya yi azumi wanda ya ci zarafin iyayen shi ya kaurace musu ya musu dagun kai, ya kuntata don yi musu hidima, in an tambaye shi yayi rowa, in an zarge shi sai ya yi wauta, in an sa rai game da shi sai ya basar, in an neme shi sai ya faku, bai amsawa sai da nuna isa, bai bayarwa sai don tsoro, bai san wani abu ba face " sai nan gaba".
Shin ya yi azumi kenan mutumin da ya yi bacci ya bar sallan farilla? Ko lokacin salla ya fita bai yi azahar da la'asar ba sai a bayan lokacinsu?  Kuma ya saba kan haka a cikin watan ramadan gaba daya.
Shin ya yi azumi mutumin da ya cinye  dukiyar gado na 'yan uwansa  maza da mata, ya yi fashin dukiyan marayu da miskinai, yayi sama da fadi da dukiyan wakafi, da hurumin masu hakki?
E, ya yi azumi da yake na sauke nauyin wajibi amma azumin da ke cakude da karya da alhaki da zalunci, wanda ke hade da manyan zunubai da laifuka masu girma.
Watakila ladan  azumin nasa ba zai kai  nauyin alhakin zaluncin sa ba da laifin sa .
 Ku ji tsoron Allah ya ku  wadan da suka rike baki daga abubuwan da suke  karya azumi da masu bata su  yayin azumi,  ku ka kuma  aikata abin da ya wajaba ga  musulmi   ya nisance shi    kuma ya haramta a gare shi ya aikata su  ko yaushe  .
 Yi salla irin sallan mai fata da tsoro*** Kafin ka yi azumi ka yi  azumi daga dukkan alfasha
 An karbo daga Jabir Allah ya kara yarda a gare shi y ce :( Idan ka yi azumi   to jinka da ganin ka da harshen ka su ma su yi azumi daga  karya da laifi  kada ka cutar da hadimin ka   ya zamana a gare ka akwai girmamawa da  natsuwa a wunin azumin kar ka sanya wunin da ka ke shan ruwa  daya da wunin da kake azumin)  .
An karbo daga hafsa  'yar Sirin ta ce : ( Azumi  garkuwa ce muddin mai ita bai ketata ba ; ketata shine yi da  wani).
  An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce :  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Wanda bai bar fadin karya ba da aiki da ita  to Allah bai bukatar sa  da ya bar abincinsa da abin shan sa ) Buhari ne ya rawaito .
 Ya wanda ya kame daga ci ko sha  a yinin  ramadana  to ka kame daga zalunci da haramun  ka kuma kame daga fin karfin mai rauni da karbe hakkin sa ba tare da yardan sa ba .
 Ya wanda ya yi azumi daga ci *** ina ma a ce ka yi azumi daga zalunci
Ko azumi zai yi amfani ga wanda ya yi zalunci *** cikin sa na cike da laifuka
Idan har bai kasance game da ji na a kwai kurumcewa ba  a idanuwana akwai rintsawa ***  a furuci na akwai  kamewa 
 To kaso na game da azumi na kawai shi ne yunwa da kishir ruwa*** ko da na ce ni na yi azumi to ba fa azumin na yi ba .
Allah ya sanya ni da ku cikin wadan da suka yi azumin ramadana  suka kiyaye shi  ba su gurbata ayukan su ba da kyautatawan su ba  da zunubai,  ina  fadin abin da kuke ji kuma ina neman gafarar Allah , to ku nemi gafarar sa  lallai shi ya kasance  ga masu komawa gare shi mai yawan gafara ne.
 Huduba ta biyu
 Ya ku musulmai :
  Wannan lokaci ne na komawa ga Allah  wannan ruwa ne na wanka mai sanyi da kuma sha .
 Ya wanda zunubai ya daure shi, ya wadan da ayukan ababan kunya suka  kulle shi , wannan wata ne da ake kwance daurarre mai sabo,
Ya wanda ya saba  da zunubai da laifuka  , ya wanda ya wayi gari ya sammaka cikin kurakuran shi yana mai nadama   ka tuba  gaba gare ka  ga bukatar ka da kuma riba , Allah yana so ya  yi kyauta da kuma  rahama  , kuma ya yi afuwa ga masu tuba   don falala daga gare shi da kuma karamci .
 Dadi ya tabbata ga wanda ya wanke zunuban shi  a cikin ramadana  da tuba  ya dawo daga kusa kuran shi kafin kwacewan lokaci.       


الجمعة، 18 مايو 2018

FALALAR AZUMIN RAMADAN


Hudubar Masllacin Annabi 2-Ramadan -1439AH
Hudubar Farko:
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Madaukakin sarki,  muna gode mishi kuma muna neman taimakonsa ,  kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu , da munanan ayyukanmu , duk wanda Allah ya shiryar da shi babu mai batar da shi , duk wan da ya batar kuma babu mai shiryar da shi , na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya , kuma na shaida Annabi Muhammadu bawansa ne kuma Manzonsa ne, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa da sahabbansa  da aminci tabbatacce mai yawa,
Bayan haka ku ji tsoron Allah - ya ku bayin Allah - hakkin tsoronsa, ku yi riko da igiya mai karfi na musulunci.
Ya ku musulmai!
Ranaku da dararraki na tafiya cikin sauri, shekara na nade watanninsa daya bayan daya, a cikin haka Masu bauta  kuma suna komawa ne ga Allah, ba da jimawa ba zasu je su riski ayyukansu,
Na daga falalar Allah da karamcinsa ya  zaba musu zamuna da lokuta na da'a, ya zabi wasu ranaku da dararraki da wasu sa'o'I don kara kaimin kwadayin ibada da kimtsawa, masu munafasa kuma suna tsere gurin ayyukan alheri , a duk lokacin da jinjirin watan ramadan ya bullo sai ya buso mana wasu kyauta masu albarka, sai musulmai su fiskance shi zuciyarsu na cike da farinciki da annashawa,  zai iya yiwuwa wani sa'a na karbar aiki ya riski bawa  sai ya kai wasu darajoji na yarda da walwala.
Wata  mafi daraja da tsarkaka ta sauka gare mu,lokaci ne mai girma Allah ya kebance ta da karramawa da daukakawa,sai ya turo manzonsa a cikinta ya saukar da littafinsa, ya farlanta azumtanta,  sa'o'inta na da albarka, duk lokutanta ana raya su da alheri ne, alheru na bibiyan juna a cikinta, albarka na gamewa a cikinta, wata ne na ihsani da sadaka zamani ne na neman gafara da kankaran zunubai,  wuninta azumi ne darenta tsayuwa ake yi, ana raya ta da Alkur'ani, ana bude kofofin Aljanna a cikinta, ana rufe kofofin wuta,ana daure shaidanu da mari a cikinta, akwai dare a cikinta  da yafi wata dubu alheri, duk wanda aka hana alherin cikinta to lalle katangagge ne daga samun alheri.
Ramadana fage ne mai yalwa don tsere cikin aikin da'a, kyauta ne na gyaran zuciya daga dauda da matsaltsalu,wata ne mai karamci ana ribanya ayyuka a ciki, ana kankare kusakurai a ciki da laifuka, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:(salloli biyar da juma;a zuwa wata juma'a  da ramadan zuwa wani ramadan na kankare abin da ke tsakaninsu muddin an nesaci manyan zunubai) Muslim ne ya rawaito
A cikin watan ne musulmai ke sauke nauyin daya daga cikin rukunan musulunci, kuma wani abu ne na bayyane da ke nuna girman wannan addini, da kuma hada kan musulmai, a nan ne fadin Allah Madaukaki sarki ya ke bayyana  (Lalle wannan al'umarku ce guda daya kuma nine Ubangijinku ku bauta min)
  Ribatan lokutan alheri  budi ne daga Allah ga wanda ya so daga cikin bayinsa,a cikin ramadan na ne tushen Ibadoji  mafi girma ke gamewa  ga salihan bayi.
Salla sadarwa ne tsakanin bawa da Ubangijinsa,ba ta rabuwa da musulmi a dukkanin rayuwarsa, sallar mutum cikin jam'i  farilla ne tana daidai da sallar mutum a gidan shi da kasuwan shi sau ashirin da bakwai, ya dace da musulmi  ya nemi taimako da salla bisa azumin shi , kuma ya zama yana da kaso mafi girma na salla a darensa, To (wanda ya yi tsayuwan dare na ramadana cikin imani da neman lada an gafarta masa abin da ya gabata na daga zunuban shi) Bukhari da Muslim ne suka rawaito
(Wanda ya yi tsayuwan dare tare da limami har ya tafi to an rubuta masa tsayuwan dare)Tirmizi ne ya rawaito.
Zakka da sadaka tsarkaka ne ga dukiya da habaka, wadata ne ga zuciya da tsarkakuwa tasirinta a bayyane yake ga zuciya da dukiya  da yara, mai tunkude bala'i  mai janyo  yalwa, wanda ya yi kyauta  ga bayin Allah, Allah zai yi mishi kyauta, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :  Allah Madaukakin sarki ya ce ya kai dan Adam ! ka ciyar zan ciyar da kai.)Bukhari da Muslim suka rawaito
Dukkan mutum yana inuwar mutuwarsa ne ranar Alkiyama, to ku yi sadaka da da dan kadan ne, ka  dadawa rai da ita, ka taimaki maragalihu,  (Duk wanda ya ciyar da mai azumi yana da kwatankwacin ladan shi)
Kuma yana daga cikin koyarwarsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi akwai  ciyarwa da kyauta, yana bayar da kyauta irin kyautan wanda bai tsoron talauci, in ya zo bada kyauta sai ya yalwata, in ya bada sai yawaita. Ba ya maida mai tambaya, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ,ba a taba tambayarsa wani abu ba face ya bada,
Manzon Allah ya fi kyauda a cikin ramadana, ya kasance a cikinsa mai kyauta kamar iska mai kaiwa ga kowa.
Azumi shi ne ibada mafi girma a wannan wata  mai falala, Musulmai na guzurin takawa a cikinsa, Allah Madaukakin sarki ya ce : (Ya ku wadanda suka yi imani an wajabta muku azumi kamar yadda aka wajabtawa wadanda suka gabace ku ko zaku ji tsoron Allah)
Ladansa ba iyaka ko kididdiga, Allah ya ce a hadisul kudsi : (Dukkan aikin dan adam na shi ne sai azumi  don shi nawa ne ni zan saka game da shi)Bukhari da muslim ne suka rawaito.
(Wanda ya yi azumin ramadana cikin imani da neman lada daga Allah  an gafarta masa abin da ya gabata na daga zunubansa)Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Azumi na shamaki tsakanin ma'abocinsa da sharri da zunubai, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi (Azumi garkuwa ne)Tirmizi ne ya rawaito
Ba abin da ya fi  wani  ya  nemi taimako da shi bisa takawa da kiyaye dokokin Allah da nesatan abubuwan da Allah ya haramta  kamar  azumi, Ibnul kayyim Allah ya mishi rahama  ya ce : ( Amfaninsa ya fi karfin iyakancewa  yana da tasiri na ban mamaki  wurin kiyaye lafiya.)
A lahira zai yi ceto ga ma'abotansa, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Azumi da Alkur'ani suna ceto ga bawa a ranar Alkiyama sai azumi yace ya Ubangiji na hana shi abinci  da sha'awarsa a wuni to ka cece shi don ni, sai Alkur'ani ya ce : Na hana shi barci da dare to ka bani cetonsa,  yace sai a basu cetonsa.Ahmad ne ya rawaito.
Na daga cikin ayyuka na kwarai da ake ribata akwai umra , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : (Umra a ramadan na daidai da hajji)Bukhari da Muslim ne suka rawaito
Kur'ani maganar Allah ne kuma hujjarsa  ne a kan bayinsa, shi ne mabubbuga na hikima, mu'ujiza ce na sakon manzanci, babu hanya zuwa ga Allah sai ta gun shi, babu tsira gare mu ba tare da shi ba, haske ne  na basira da kuma gani  wanda ya kusance shi zai samu  daukaka  wanda yayi riko da shi zai samu buwaya   tilawar sa lada ne da shiriya, bitar sa kuma ilimi ne da tabbatuwa  aiki da shi   kariya ne da aminci  ilmantar da  shi  da kira zuwa gare shi kambina a kawunan masu biyayya  ,   a ramadana  ana karfafa yawaita karanta shi  da tadabburi da neman iliminsa  da kuma ilmantar da shi da aiki da shi  da kuma bin koyarwar sa  a cikin shi ne ya sauka , Allah madaukakin sarki ya ce: ( watan ramadana da a ka saukar da alkur'ani a cikin ta  shiriya ne ga mutane da  bayyanannu na daga shiriya da rarraabewa).Jibrilu amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana bitan alkur'ani tare da Annabinmu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sau daya a kowace  shekara ,   a shekarar da ya rasu a cikinta  ya yi bita tare da shi  sau biyu   tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi .
    Addu'a ibada ce kuma kusanci ce , wata ganima ce da ba tare  da  wahala ba  kuma riba ce wanda babu asara a cikin ta , yana  janyo sauki kuma makiyi ne ga dukkan wani bala'I  ba wanda zai halaka muddin yana adu'a,  da shi ne bawa yake riskan burin shi ya samu bukatar sa  , sau da yawa yakan  kusanto da abin da yake nesa  kuma sau da yawa yakan saukake abu  mai wahala sau da yawa kuma yakan yaye bakin ciki  mafi karbuwan adu'a shi ne wanda aka yi shi  a cikin karshen dare , idan bawa ya marairaice a gaban Ubangijin shi  , sai Allah ya  amsa mishi bukatar sa ,  idan rayi ta ji yunwa sai zuciya ta tausasa ta kwanta  mai azumi ba a maida adu'ar sa har zuwa lokacin buda baki  Ibn Rajab Allah ya mishi rahama  ya ce : (   Mai azumi a daren sa da yinin sa yana cikin ibada ne  , ana  amsa adu'ar sa  a azumin sa haka kuma yayin buda bakin sa  , to shi a wunin sa yana azumi kuma yana mai hakuri  a daren sa kuma  mai ciyarwa ne kuma mai godiya )
Wanda ya yi gamon-katar shi ne wanda ya kwankwasa kofar sama, ya sanya wa kansa a wadannan ranaku da dararraki wani abin adana.
Ambaton Allah ibada ce mai girma mai sauki,duk wanda ya ambaci Allah to Allah zai ambace shi, bawa idan bai shagaltar da harshensa ba da anbaton Allah ba to kuwa zai shagaltar da shi da magana mara amfani da na sabo.
Addini muamala ne, mafi  cancanta ihsaninka cikinn halittu shi ne wanda Allah ya gwama hakkinsu  da na shi, Iyaye biyu Aljannaka ne kuma wutar ka ne, su suka fi cancanta ka kyautata musu cikin mutane, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata  a gare shi,ya ce : (Hancinsa ya dumbuli kasa ! Hancinsa ya dumbuli kasa! Hancinsa ya dumbuli kasa! Sai aka ce da shi wane ne? wanda ya riski iyayensa biyu sun girma ko daya daga cikinsu ko su biyun   bai shiga Aljanna ba),Muslim ne ya rawaito.
(zumunci na hade ne da Al'arshi ne tana cewa ya Allah duk wanda ya sada ni ka sada misi, wanda ya yanke min ka yanke mishi)Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
(wanda zai burge shi da a yalwata mishi a arzikinsa,  a jinkirta masa a bayansa to ya sada zumuncinsa) Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Na daga cikin cikan daa  a kiyaye su daga dukkan abin da zai tawaye su ko ya warware su
Mai azumi ya fi tsananin son ya kiyaye ibadarsa da azuminsa daga abin da zai keta alfarmansa ko ya bata shi, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( a ranar da dayanku yake azumi to kada  yayi batsa, kada ya yi hayaniya, idan wani ya zage shi ko ya nemi fada da shi,  to yace ni mutum ne, mai azumi ne  )  Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Na daga cikin koyarwar magabata Allah ya musu rahama idan sun yi azumi sai su zauna a masllaci sai su ce : Mu kiyaye azuminmu kar mu ci naman wani, Ahmad Allah ya mishi rahama ya ce : Ya dace ga mai azumi da ya bibiyi azuminsa ya bashi kulawa tun daga harshensa  kada ya yi musu, ya dace ga mai azumi idan ya yi azumi ya kiyaye jinsa da ganinsa   da harshen sa da dukkan  gabbansa , kada ya sanya ranar azumin sa kamar ranar shan ruwan sa , 
Bayan haka ya ku musulmai :
 To lallai biyayya bata kasancewa cikakkiya  kuma bata tsayawa akan kwabrinta  da kuma gun da ya dace sai tare da kauna wanda za ta kai ma'abocinta zuwa ga ikilasi  da gaskiya  wanda ke haifar da kekkewar bin sunna , aiki baya kasancewa na kusanci har sai tushen shi  da ma'ingizan shi ya kasance imani ne ba al'ada ba da son rai , ba kuma neman suna ko yi don riya ba   kuma har sai ya kasance manufar sa  shi ne neman lada gun Allah da kuma yardar sa  idan imani ya hadu da neman lada a aiki to nan ne karbuwa yake tabbatuwa da kuma gafara .
         INA NEMAN TSARIN ALLAH DAGA SHAIDAN ABIN JEFEWA
(Ku yi gaggawa zuwa ga gafara daga Ubangijin ku da aljanna  da  fadinta  sammai da kassai  antanajeta ga masu tsoron Allah ).
Allah ya sa mini albarka ni da ku a cikin al'kur'ani mai girma


HUDUBA TA BIYU
Dukkan yabo da godiya sun tabbata  ga Allah bisa ga kyautatawan sa  godiya ta tabbata a gare shi bisa ga datarwansa   da kuma baiwarsa  na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya  ina mai girmama sha'anin sa  , kuma na shaida Annabinmu Muhahammadu bawan sa ne kuma Manzon sa ne  tsira da amincin Allah su tabbata  a gare shi  da iyalan shi da sahabban shi da aminci tabbatacce mai kari .
  YA KU MUSULMAI :
Duniya za ta kare da jin dadin ta da kuma bakin cikin ta shekaru za su kare da   tsawon su da gajertan su  kowa ya je ya hadu da Ubangijin su to a wannan lokacin ne fa dukiya ba zai yi amfani ba ko 'ya'ya face wanda ya zo wa Allah da zuciya  lafiyayyiya  , to ku fiskanci watan ku da tuba na gaskiya  , kuma ku kulla azama bisa ga ribatanta da kuma raya lokutan ta da biyayya , rayuwan duniya ba wani abu ba ne face wasu numfashi  kididdigaggu da kuma ajali  iyakantacce  , ku ribaci lokuta masu daraja   ku sani  kuma ku yi fata kuma ku yi bushara  , hasararru su ne wadanda suka riski ramadana ba a gafarta musu ba , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :  (Hancin shi ya  dongwali kasa duk mutumin da ramadana ya shiga har ya fita kafin a gafarta masa ) Tirmizi ne ya rawaito
 (Duk wanda bai bar fadin karya ba da kuma aiki da shi to ba ruwan Allah da ya bar abin cin sha da ruwan shan sa ) Bukhari da Muslim suka rawaito .
Mafi girman abin da zai gyara zuciya shi ne ambaton Allah da kuma lizimtar alkur'ani mai girma, da tsayuwan dare,  da zama da mutanen kwari .
Sannan ku sani ; lallai Allah ya umarce ku da salati da aminci ga Annabin sa ………
  

الجمعة، 4 مايو 2018

SURATUL MA'UN (AKIDA DA HALAYYA)


Hudubar Juma'a  a Masallacin Annabi tare da shaikh Abdulbari dan Awad Assubaiti 18-8-1439 AH
Allah ya saukar da littafinsa mai girma don shiryar da Dan-Adam , surorinsa haske ne, ayoyinsa fayyacewa ne, kuma ruwan marmaro  ne da bai  fakewa, mashayan ruwa ne da bai bushewa, ko gurbacewa, wanda ke cikin damuwa da bakin ciki in ya fiskance shi zai samu warakarsa cikinsa, haka wanda ke cikin bacin rai in ya koma masa zai samu  abin da zai rarrashe shi a cikinsa ya bashi annashawa.
Na daga cikin gwalagwalai masu tsada da ban kaye da ke cikin Alkur'ani akwai suratul ma'uni,
( Bamu labarin wanda yake karyatawa da ranar sakamako.
Shi ne wanda yake ingije maraya.
Ba ya kwadaitarwa bisa ga ciyar da miskini.
To azaba ta tabbata ga masallatan nan.
Wadan da suke rabkana ga barin sallarsu.
Wadan da suke riya kuma suke hana agaji.) Alma'un 1-6
Sura ce mai girma tsarin gininta ta bayyana auratayya mai karfi da ke tsakani kuduri da halayya,
Wanda ke karyata ranar sakayya shi ne mai karyata ladan Allah da ukubarsa, kuma ya karyata hisabi, imani da ranar lahira bai zauna da gindin shi ba a cikin zuciyarsa, mummunar kuduri na kai ga lalacewan aiki, lalacewan aiki alama ne na lalacewan kuduri.
Me yasa aka sifanta shi da mai karyata sakayya, sabo da yana karyata addini ne, sabo da a rayuwansa bai yi wani abu da ke hukunta yana yin addini ba kamar ya tabbatar da haka da harshensa kuma zuciyarsa ta gaskata,sai dai bai aiwatar da jikinsa ba abin da addini ya kumsa  na halayya da dabi'un addini ba, da bada hakki na imani da ke kansa ba, da bin tafarkin alkur'ani, kuma kowa ya sani imani fadi ne da harshe da gaskata wa da zuciya da aiki da gabbai.
Wanda imaninsa da hisabi da sakayya  ya yi rauni  to shi ne mai karyata addini, wanda zuciyarsa ta kekashe ta dunkule ta bushe, na daga cikin sifarsa yana ingije maraya ya walakanta shi ya cutar da shi, shi bai iya da imaninsa mai rauni da ya kyautata  rayuwarsa da halinsa, ya tsoraci mummunar aiki,
To ina kimar addini idan tasirinsa bai bayyana ba a halaye da dabi'u ba?
To ina hakikanin imani idan bai sa mutum ya yi laakari da waninsa ba har ya yi mishi alheri ba da aikata ihsani da ciyar da miskini kai da kwadaitarwa bisa ciyar da miskini, ko da a ce abin da Allah ya nema a yi abu ne na abin duniya to yin shi alama ne imani.
Imani da tadawa da sakayya shi ne  zai ja ka zuwa ga gaskiya, wanda zai dasa fiskantar ayyukan kwarai har ya zama mishi jiki, idan ya taso a kai, ba zai mishi wahala ba zai tsarkaka  ba tare da wani nauyi ba.
Kekashewar zuciya na kaiwa zuwa ga gafala da karyata addini, maganin haka na cikin hadisin mafificin halitta,Manzon halitta  Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, lokacin da wani mutum ya koka mishi bushewar zuciyarsa sai ya ce: Ka shafa kan maraya ka ciyar da miskini) Albani ya rawaito cikin sahih Attargib wattarhib.
A fadin Allah : (ba su kwadaitarwa bisa ga ciyar da miskini) akwai nuni ga cewa musulmi ana so ya kwadaitar da waninsa wurin yin ihsani, hakan kuma ba zai sauke nauyin da ke kansa ba aikata alheri ga masu rauni na daga marayu da miskinai gajiyayyu tare da kiyaye mutuncinsu da  yin nesa daga karya zukatansu, Allah Madaukakin sarki ya ce : (Magana kyakkyawa da gafara ya fi alheri kan sadaka da gori ke binta)
Mafi suran ihsani shi ne taimaka  musu da kayan masrufi da zai taimaka musu don tafiyar da rayuwarsu, da samar musu da hanyoyi na  aiki ga zauna gari banza daga cikinsu da tattala su da shirya su da samar musu da kayan aiki.
(To azaba ta tabbata ga masallatan nan). Na daga cikin sifofinsu suna yin salla ne na jeka na yika,ba tare da aikata abin da sallar ta kumsa ba,ta wofinta daga hakikanin manufarta.rukunanta kuma a tawaye. Wani mutum ya shiga masallaci ya yi sallah a halin Annabi na zaune a gefe, sai ya zo yayi mar sallama sai Annabi ya ce: ( Je ka sake sallah don ba salla ka yi ba.) Bukhari ne ya rawaito.
Wanda ya yi lura da halin wadanda basu taimakawa marayu kuma basu ciyar da miskini, suna zamba kuma suna karya, kuma suna saba alkawari, kuma suna zalunci zai samu suna rabkana ga barin sallarsu.
Duk wanda ya tawaye sallarsa to sai ya fi tawaye  duk wani abu  komabayanta.
Idan ibada ta rasa ma'anarta  sai ta zama kawai motsa jiki ne da ba karfafan imani ko gyaran hali, sai tasirinta ya raunana a rayuwa, nassoshin kur'ani da hadisi sun bayyana hikimar shar'anta ibadoji  da kuma manufofinta da tasirinta a rayuwar mutane, kuma wasu makarantu ne na tarbiyya, Allah Madaukakin sarki ya ce : (ka tsaida sallah don sallah na hana alfahasha da munkari)
Allah ya ce game da azumi (ya ku wadanda suka yi imani an wajabta muku azumi kamar yadda aka wajabtawa wadanda suka gaba ce ku ko zaku ji tsoron Allah)
Manzon Allah tsira da amincin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Duk wanda bai bar fadin karya ba da aiki da ita to  Allah bai da bukatar ya bar abincinsa da abin shansa) Bukhari ne ya rawaito.
Allah ya ce : Karbi sadaka daga dukiyoyinsu ka tsarkake su da ita ka kwalle su daga tsatsar zunubai).
Yace game da Hajji : (Namanta ba ya tarar da Ubangiji ko jininta sai dai tsarkakar niyya ce take samunsa daga gare ku) Hajj  37
Sallah ita ce karshen abin da zaa  rasa na daga addini, idan  ta tawaya to addini gaba daya ya tawaya, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(za a kwance igiyar riko na musulunci gaba gaba, a duk lokacin da wata igiya ta kwance sai mutane su riki wacce ke bi mata, wacce zata fara warwarewa ita ce hukunci na karshe ko ita ce sallah)     
  Ingantacce ne Albani ya rawaito shi cikin Attargib Wattarhib kuma yana da wani hadisi da zai karfafe shi a matsayin shahid.
Idan an datar da bawa  gurin yaki da musibar  rabkanuwa daga barin ibada to suratul Ma'un zata tunatar da shi game da gyaran zuciyarsa daga riya  da fadin Allah (Wadan da suke riya) wato masu yin riya a cikin sallah da waninta :ta hanyar aikata abu da yin shi ba don Allah ba,sai don neman yardar mutane, Riya na daga cikin manyan zunubai na zuciya, yana rusa aiki ya hana shi samun karbuwa a gurin Allah. Na daga cikin abin da ayar ke nuni gare shi muna fahimtar niyyar da ta cakuda da riya na sauya aiki nagari ya koma sabo, wanda ma'abocinta ya cancanci bone. Allah Madaukakin sarki ya ce :   
(To azaba ta tabbata ga masallatan nan.
Wadan da suke rabkana ga barin sallarsu.
Wadan da suke riya).
Haka nan ne zuciyar da ta rasa ikhlasi maganar ta ba ta da kimai, ibada ba zata yi wani tasiri ba a halayenta, kuma ba zaa karbi aikinta ba, ba tsarkaka ga ruhinta.
Na daga cikin mabudi mafi girma na nasara : a datar da bawa ga jan ragamar sha'awarsa ta riya ya ja mata linzami, kuma ya mika wuyarsa ga Allah, ya yi ikhlasi a aikinsa, niyyarsa kuma ya fiskance shi da ita, ya tace ta daga neman wata ganima, ko sha'awa ko matsayi ko dukiya, ko suna, ko samun matsayi cikin zukatar mutane, ko neman yabonsu, ko gudun zargi a gare su, Allah Madaukakin sarki na cewa a hadisin Alkudusi: (ni ne mafi wadatuwa daga abokan tarayya, duk wanda ya yi wani aiki ya hada ni da wani a ciki to na bar shi abokin tarayyar tasa) Muslim ne ya rawaito.
Huduba ta biyu
Karshen aya ta wannan sura na nuni ga muhimmanci halye na gari ga al'uma, ta hana zamewa kankamo, Allah Madaukakin sarki ya ce : ( kuma suke hana agaji.) wato suna hana bada aron abin da mutane suke arawa junansu, cikin abin da ba a saba hana wa ba a al'adance.
Wadannan  basu kyautata bautan Ubangijinsu ba, basu kuma kyautatawa halittunsa ba, ta hanyan bada aron abin da zaa amfana da shi  a taimaka da shi, tare da wanzuwar  abin a komo da shi ga mai shi,  to wadanna n mutanen  sun fi kusa da hana bada zakka da abubuwa na neman kusanci sama da wani abu,   
( Bamu labarin wanda yake karyatawa da ranar sakamako.
Shi ne wanda yake ingije maraya.
Ba ya kwadaitarwa bisa ga ciyar da miskini.
To azaba ta tabbata ga masallatan nan.
Wadan da suke rabkana ga barin sallarsu.
Wadan da suke riya kuma suke hana agaji.) Alma'un 1-6