Hudubar Juma'a a Masallacin Annabi 19-11-1438AH sheikh Abdullah bin Abdurrahman
Albuaijan
Dukkan yabo da godiya
sun tabbata ga Allah da ya raba halaye a tsakaninku kamar yadda ya kasa arziki
a tsakaninku ya sanya kyakyawan hali shine ma'uni na fifiko a tsakaninku na shaida babu abin bautawa da gaskiya
sai Allah shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya yana da kyawawan sunaye da
kuma siffofi madaukaka.
Na shaida Annabi Muhammadu
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi bawansa ne kuma Manzonsa ne, ya
isar da sako, kuma ya sauke amana, ya yi nasiha wa alumma, ya yi jahadi don
Allah yadda ya dace a yi jahadi har lokacin da mutuwa ta zo mishi .
Ya Allah ka yi dadin
tsira da aminci a gare shi da iyalansa da sahabbansa da wanda ya bi shiryarwarsa ya kuma yi riko da sunnarsa har zuwa ranar
sakayya.
Ya ku bayin Allah ku ji
tsoron Allah, Mabuwayi da daukaka,domin takawa daukaka ne a nan duniya kuma
guzuri ne a lahira.
(ya ku wadanda suka
yi imani! In kun ji tsoron Allah zai sanya muku mararraba kuma ya kankare
kananan zunubanku kuma ya gafarta muku. Kuma Allah ne Ma'abucin falala Mai
girma)
Lalle duk da sabawan
harshen su da launin su ko da kuwa sun kasance daga Uba guda,to su kamar ma'adinai ne (da ake
tonowa a kasa) wani na da fifiko kan wani haka wani nau'in ya dara wani, sabo
da dabiu ne maauni na kyawawan halaye, kuma shi ne mizani na al'umu, kuma tsani
zuwa ga daukaka, da kaiwa kololuwa, Manzon Allah ya yi gaskiya da ya ce :(Lalle
zababbun ku su ne mafi kyan halaye a cikinku) Bukhari ne ya rawaito.
Ya ku bayin Allah !
Lalle addinin da muke dangantuwa gare shi addini ne na kyawawan dabiu. Kuma AnnabinMu
Muhammad an turo shi ne don ya cika kyawawan dabiu, kuma biyu bisa ukun
farfajiya na duniyan musulmai sun karbi musulunci ne ta hanyar kyawawan dabiu.
kunya ne sarkin halaye nagari kuma, ba sabani
kan kunya ne abu mafi kyau da ado a cikin kyawawan dabiu,
ya
ku bayin Allah kunya ita ce tushen
kyawawan dabiu'kuma ita ce mabubbugan kyawawan halaye dukk wata falala ta boyu
a cikin kunya wanda ya siffantu da ita
musuluncinsa ya yi kyau, haka nan kuma dabiu'.
Ita za ta daukaka mutum ta sa ya yi nesa daga sabo domin jin kunyan ubangijin shi
dabia' ce mai daraja wanda ke haifar da aikata dukkan wani aiki mai kyaw ya
hana mutun aikata aiki dukkan mara kyaw yasa mutun ya yi nesa daga dukk
wani aiki na kunya muna na da kuma ya yi
nesa da abubuwa na minkari lalle shi din nan dalili ne da ke nuna girman hali da
tsarkakan zuciya ga mutun kunya na tunkude mutun daga aikata aikin ashshakuma kuma ya kare mai
mutuncin shi ya dasa mishi kame kai a zuciyan shi shi kama wani ma'dini ne mai tsada wanda ba mai siffantuwa da shi sai
zukatanda suke na ayaba kuma kaman wani ado ne na annabawa an karbo daga abu
masu'd Allah ya kara mishi yarda ya ce:
manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce''Na daga
cikin abinda mutane suka riska na maganganun Annabawan farko akawai " in baka ji kunya ba to ka aikata
abin da ka so ) Bukhari ne ya rawaito
kunya
alami ne na musulunci ko wani addini yanada wasu dabiu'
Na daga cikin dabi'u
na musulunci akwai kunya,Ibnu maja ya rawaito kuma Albani ya
inganta shi a cikin sahihuhu aljami
Imani yanki saba'in da dori ne kuma kunya daya daga cikin yanki ne na imani muslim ne ya rawaito
Manzon Allah ya wuce wani mutumi yana zargin
dan uwan shi sabo da yawan kunya sai ya ke cewa lalle kai din nan kana
jin kunya sai yana cewa har kaman hakan ya maka illa sai manzon Allah tsira
da amincin Allah su tabbata a gareshi yake cewa kyale shi domin lalle kunya na
daga cikin imani kuma babu imani ga wanda ba yi da kunya Bukhari ne ya rawaito
Kuma na daga cikin
sirri ya ku bayin Allah da ke sanya kunya ta zama a cikin imani saboda dukkan imani da kunya sun
kasance suna kira ne zuwa ga alheri kuma suna kusantarwa zuwa gare shi kuma
suna tunkudarwa daga sharri kuma suna nesatarwa
daga gareshi kunya kofa ne daga cikin
kofofin alheri.
An karbo daga Imran
dan Husain Allah ya kara yarda a gare shi ya ce Annabi tsira da amicin Allah su
tabbata a gare shi ya ce (Ita kunya bata kawo wani abu sai alheri ) kuma ya ce
(kunya alherine dukkaninta ) muslim ne ya rawaito
Ya ku bayin Allah
hakika manzon Allah ya tattaro dukkan siffofi
na mutanen farko da na karshe ya siffantu da dukkan sifa mafi daukaka da
daraja har Allah ma ya ke ce da shi (lalle kai din nan kana kan dabiu' masu
girma).
Manzon Allah ya kasance mafi jin kunya a kan budurwa da ta ke
cikin kafunta idan yaga wani abu da ya ki sai
a ga kin a fuskar shi ta hanyan kunya
ya lullubeshi
ya ku musulmai lalle kunya daya daga cikin
surori ne da darajoji mafi kololuwa a wurin Allah ta inda za ka ji kunyan a
ganka wurinda ya haneka hakika kuma shi ya halicceka kuma ya daidaita ka kana
jin kunyan ka yi amfani da ni'marsa da ya baka wurin saba mishi , Manzon Allah
ya kwadaitar bisa ga kunya kuma cewa kunya daga Allah ne sai ya ce (ku ji kunya
ya ku bayin Allah yanda ya dace a ji kunya sai suka ce ya manzon Allah dukkan
mu muna jin kunya Ahamdu llillahi sai ya ce ba shi a ke nufi ba ana nufin jin
kunya daga Allah yanda ya dace da cancancin
jin kunyarsa) wato kayi ya kiyaye abunda ya tattara ciki ya kiyaye
abinda ya kumsa kuma a tuna mutuwa da karewa duk wanda ya nufi lahira zai bar
kawan rayuwan duniya wanda ya yi haka to hakika ya ji kunyan Allah bisa
cancancin kunyarsa ) Hakim ne a
mustadrak ya rawaito kuma ya inganta shi zahabi ya mar muwafaka kunya daga
malayiku masu daraja da kuma masu kiyayewa masu rubutu da su shaida a gareka wato
daga dama da hagu suna zaune ba abin da zai ambata ko ya furta na fadi face akwai mai kulawa tare da shi kunya na mutane
shi ne ka keta dokan Allah da ya suturta a gare ka ka bayyana sabo a gabansu
Annabi ya ce dukkan alummana ana basu lafiya suna kubuta sai wadanda su ke masu
bayyana sabo kunya daga rayi daga gabbai domin su din nan sune zasu zama shaida
a gareka sun yi musu da kai ranar alkiyama Allah ya ce ( ranarda harsunansu za su shaida musu da hannayensu da
kafafuwansu da abinda suka kasance suna aikatawa a wannan ranar ne Allah zai
cika musu addininsu na gaskiya kuma su san cewa lalle Allah shi ne gaskiya kuma
bayyananne )
HUDUBA TA BIYU
Dukkan yabo da godiya
sun tabbata ga Allah mai kunya kuma mai suturcewa ya sanya daga cikin dabiu'
masu daraja da kuma ya cika kyawawan dabiu' ta hanyan turo mai albishir kuma
mai gargadi wato fitila mai haskakawa annabin mu muhammad tsira da amincin
Allah su tabbata a gareshi da aminci tabbatacce mai yawa ya ku musulmai lalle
muna rayuwa acikin wata marhala na halaye wanda suke na kunci muna karshen
zamani wanda wadan nan munanan dabiun sun yi rinjaye kuma sun yawaita shubuhohi
dabin soye soyen rayuka sun yadu abunda da ya kasance a jiya sanennen abune a yau ya zama shi ne abin ki abunda kuma ya kasance abin ki a jiya
ya zama shi ne abin so abinda aka saba da shi munanan dabi' sun sulale su shigo
cikin gidaje ta hanyoyin nau'urorin sadarwa na zamani a wannan yanayi gashi ana
fiskantanmu to ya wajaba mu tarbiyyantar
da masu tasowa kuma mu katangesu da akida na musulunci kyawawan dabiu' daga
Allah ne kuma su din nan katanga ne daga cikin katanga wanda suke masu bada
kariya kuma da aminci ga tarbiyya da tsarkake zukata da kuma murakaban Allah .
Ya ke musulma ya ke yar
uwata mai daraja lalle kunya ko da ya kasance abu ne da ake nema a hakkin maza
sai de kuma ya fi wajabta a kan hakkin mata a bangarenta yafi karfi domin lalle
matanda ta ke bautawa Allah da kyawawan
dabiu'nta tana neman lada kuma tana jin tsoron ukubarsa lalle kunya na daga cikin kyawawan dabiu' na
addini kuma da ake tada mutane a kansu wanda ke lullube mace a cikin kafunta da
shi tana ci tana sha kuma tana tufata shi kuma ta ke kai komo fita ta tafi tare
da shi lalle kunya ga mace musulma shine hanun jarinta kuma kuma shi ne
daukakanta kuma shi ke kiyaye karamarta kunya na janyo wa ya mace aminci da
kuma daukaka da kuma kawa dalili ne kuma na nuna cewa ita kamemmiya ce haka nan
kuma wani katanga ne mai katangewa mai karfi ya ke musulma Allah ya yi nuni a
cikin littafinsa da kunya mace a kissan musa alaihi assalam ayayinda ya zo diba
daga ruwan madyana ta inda wata mace
daya daga cikin diyar shua'ibu ta zana mana mana siffa daga cikin siffofi na
kunya na daga ciki abinda annabi musa ya yi la'kari da shi na irin kame kanta
da kunyanta da rashin cakudedeniyansu da mutane sai ya shayar da su Allah
madaukakin sarki ya ce game da annabi musa (kuma a lokacin da ya isa mashayar madyana
ya sami wata jam'ar mutane suna shayarwa kuma a bayansu ya sami wadansu mata
biyu suna korar (tumakinsu ).ya ce menene sha'ninku ? su ka ce ba za mu iya shayarwa
ba sai makiyaya sun fitakuma uban mu tsoho ne mai daraja ) (sai ya shayar da su
)
Shi kunya da kame wana
daga cikin abubuwa ne na kunya kuma alamane na musulma kuma dalili ne na kyakyawan tarbiyya ayan nan mai
girma ta nuna mana misali daga cikin kyawawan dabiu shi wato kunya da kuma
nitsuwa a dukkan kai komo da zance Allah
ya yabi daya daga cikinsu , lokacin da
ta dawo gare shi , sabo da abin da ta siffantu da shi na kunya, ba ta yi wani
rangaji ko kwarkwasa ba , ba ta bayyana kwalliyanta ba kuma bata rausaya murya ba, ( sai dayansu ta je masa tana tafiya akan jin kunya ta ce: Ubana yana
kiran ka domin ya sakanya maka ladan abin da ka shayar )
YA KE MUSULMA :
Ga mahaifiyarki kuma
abin koyin ki Aisha uwar muminai tana buga misali mafi kaye game da kunya , don
ta kasance tana jin kunya har ma ta suturce daga rayayye da matacce , tana cewa :- na kasance na kan shiga dakin da
aka binne Manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata agare shi tare da Abubakar a cikin shi, ba tare da tufafi ba
, sai nake cewa wannan miji na
ne wannan kuma mahaifi na , to
a yayin da aka binne Umar wallahi ban shiga dakin ba face da tufafi na a daure
a kai na sabo da kunya da nake ji na Umar .
Kuma ta kasance idan ta zo daura da
mahaya a halin tana ihrami sai ta sake jalbabinta a kan fiskanta .
Kuma ta kasance tana
dawafi a dakin ka'aba kamar yanda ya zo a cikin littafi mai inganci ba ta cakudaidainiya da su , a yayin da wata
'yar gidan ta take cewa da ita , na yi dawafi bakwai a dakin ka'aba kuma na
taba rukuni sau biyu ko uku sai Aisha ta ce, kar Allah ya baki lada , kina
tuttunkude maza, ase ba za ki yi kabbara ba kawai ki wuce .
YA KE MUSULMA :
Hijabin mace da kamun
kanta na cikin addininta kuma yana cikin kyawawan halayen ta , to, idan har fidiranta ya juya ,
ta shakala yin addinin ta sai ta yada kwarjallenta , ta yi wurgi da mayafinta ,
ta bayyana adonta wuraren da za ta sa a
fitinu da ita , tofa ta yi hasarar addinin ta kuma ta sarayar da amananta , an
karbo daga Abu Huraira ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a
gare shi ya ce: (nau'I biyu na mutane suna cikin 'yan wuta ban gansu , sai ya
ambata daga cikin su , Matayen da suke sanya sutura amma suna cikin tsiraici ,
suna kuma jan hankalin mutane , masu karkatarwa ne kuma karkatattu, kayukan su
kamar tozon rakumi , wanda suka karkace ,
ba za su shiga Aljanna ba ba za ma su ji kamshin ta ba , kuma a hali
kamshinta a na jin shi tun daga tafiyan kaza da kaza ).
YA KU MUSULMAI :
(Dukkan ku masu kiwo
ne , kuma dukkan ku abun tambaya ne bisa ga kiwonsu , na miji me kiwo ne akan iyalan gidan shi kuma abin
tambaya ne game da su , haka ma mace mai kiwo ne a kan gidan mijinta
da kuma 'ya'yan shi , kuma ita abin
tambaya ne game da su , ku saurara !
dukkan ku masu kiwo ne kuma dukkanin ku abin tambaya ne bisa ga kiwon da aka ba
ku) Muslim ne ya rawaito
Ya
Allah ina rokonka kunya da zai tsare ni daga saba maka ,
Ya Allah ka shiryar da
mu bisa ga mafi kyan halaye ba mai shiryarwa
zuwa gare su sai kai , ka tunkude mana munanansu daga gare mu , domin ba mai tunkude munanan daga gare mu sai kai.
Ya Allah muna rokon ka shiriya da takawa da
kame kai da wadata .
Ya Allah ka daukaka Musulunci ga musulmai ka
kaskantar da shirka da mushrikai, ka taimaki bayinka masu Tauhidi ,
jazakallahu cair allah ya karama malam lafya
ردحذفjazakallahu cair allah ya karama malam lafya
ردحذف