Hudubar farko
Dukkan yabo da godiya sun
tabbata ga Allah, tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin halittun Allah,
Bayan haka !
A kalmomi biyu na karshen
farkon sura da aka saukar a Alkur'ani Allah yana cewa:(Kuma
ka yi kujada ka kusanto ) an karbo daga Abu Huraira
Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : Manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi ya ce :-( lokacin da bawa ya fi kusanci da
Ubangijin shi shi ne a halin yana sujjada , to ku yawaita adu'a ) Muslim ne ya
rawaito
Sujada
shi ne mafi daukakan hali na bawa , a cikin shi ne mutum zai ji dadin rusunawa
mabuwayi mai girma da kuma kawa irin na kankan da kai ga mai rahama mai
jin kai , wasu lokuta ne na karamci da albarka
wanda ba su da iyaka .
Acikin sujada ne a ke jin dadin da baya
misaltuwa da yaye walwalan zuciya wanda ba alkalamin da zai iya iyakance shi yana
kaurar da musulmi daga kunci ,
zuwa ga yalwa mai fadi na
kasa cikin sararin samaniya sabo da haka ne (Aisha
Allah ya kara yarda a gare ta ta sifanta
tsayuwan daren Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da cewa;
yana sujjada guda da zai kai dayan ku ya
karanta aya hamsin kafin ya dago) Buhari ne ya
rawaito .
Sujada
na kara wani haske na imani daga
ma'abocin shi ya jefa wani walwala a zuciya da natsuwa ya bashi wani
gairmamawa , Allah madaukakin sarki ya ce :-(Muhammadu Manzon Allah ne , kuma wadan da suke tare da shi suna masu
tsanani ga kafurai masu tausayi a
junan su za ka gansu suna masu yawan
ruku'u da sujada suna neman falala daga
wurin Allah da yarda alamun su
na fiskan su na gurbin sujada )
Asujada
ne Ubangiji ke kasancewa kusa da wanda ya roke shi , Ubangiji mai tsarki yana kusa da wanda ya roke shi , mai amsawa ne ga wanda ya nemi ganawa da
shi mai badawa ne ga wanda yayi fata
gare shi duk wanda ya kusanci Allah to
lallai zai riski kyauta mafi yalwa daga Ubangijin shi, kuma ya samu matsayi
mafi
aminci da yakini da kariya mai karfi , Allah madaukakin sarki ya ce (To amma ( idan
mai mutuwan ya kasance daga makusanta
sai hutawa da kyakkyawan abinci
da aljanna mai ni'ima )
Makusantan
suna da Rauhun shi ne; hutu da
natsuwa da farin ciki da kuma annashawa
, Raihan shi ne suna da ya tattaro dukkan wani jin dadi na jiki
na daga abinci ne ko abin sha da
makamantan su , da (aljanna mai ni'ima) wanda a cikin ta akwai
abinda ido bai gani ba kuma kunne bai ji ba kuma bai halarto a tunanin wani dan
adam ba yana yiwa makusantan shi
albishir yayin halartowan mutuwan su da
wannan albishir din wanda rayuka ke kusa da su fire sabo da tsabar jin
dadi da farin jiki , (ka yi sujada kuma ka
kusanto )
A
ko wani sujada kana da daukaka na daraja
da kusanci na matsayi da kuma
kusanci na wuri Manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :- (Ba
wani bawa da zai yi sujada don Allah
face an rubuta mishi kyakkyawa da ita , an kankare mishi mummuna da ita an kuma daga darajar ku da ita ,
to ku yawaita yin sujada ) Ibn Maja ne ya rawaito da isnadi ingantacce
To
kyautan Allah bai karewa duk wanda ya
kusance shi sai ya saukar da shi bisa falalan sa daraja irin na Annabawa da siddikai da shahidai da salihai , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce
da Rabi'ata Dan Ka'ab Al-Aslami a lokacin da ya nemi kusanci da Manzon Allah a
aljanna sai ya ce da shi:-(
ka taimaka mini akan kanka da yawan
sujada) Muslim ne ya rawaito
(ka yi
sujada kuma ka kusanto ) a cikin sujada ne
alamomi na gaskatawa da imani ke bayyana alamomin yakini da mika wuya ke fitowa
fili , an karbo daga Aliyu dan Abi Dalib
Allah ya kara yarda a gare shi ya ce :- ya kasancen
daga cikin adu'o'in manzon
Allah tsira da amincin Allah su tabbata
a gare shi a sujadan sa Allahumma laka
sajadtu , Aya Allah don kai na yi sujada , wabika amantu , da kai ne kuma na yi
imani wa laka aslamtu, kuma da kai na
mika wuya , fiska ta ta yi sujada ga wanda ya halicce ta
ya sauwara ta ya tsagi jinta da ganin
ta tsarki ya tabbata ga Allah mafi kyaun
masu halitta )Muslim ne ya rawaito
(ka
yi sujada kuma ka kusanto ) lalle sujada na cikin ibada
wanda dukkan halitu suka yi tarayya suka tattaru a kanta (Kuma ga Allah abinda yake cikin sammai da kasa na dabba
da mala'iku suke yin sujada , kuma basu kangara . Suna tsoron Ubangijin su daga bisan su kuma
suna aikata abinda ake umarnin su )
Manzon
Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce ni ina ganin abinda
bakwa gani kuma ina jin abinda bakwa ji , sama ta yi kara kuma ta cancanci ta yi karan sabo
da babu wani bigirea na yatsu fa ce
mala'ika yana daure da fiffigen shi yana mai sujada ga Allah , wallahi da
kunsan abinda na sani da kunyi dariya
dan kadan kunyi kuka mai yawa . Da ba ku ji dadi da mata ba akan shimfidi da kun fita kwararo –kwararo kun yi kururuwa kuna kara
zuwa ga Allah ) Nasa'I da Ibn Maja ne suka rawaito da Ahmada.
1. (ka yi sujada kuma ka kusanto ) ka yi sujada kana mai rokon Ubangijin ka kana mai kiran
mahaliccin ka , kana mai kankan da kai
zuwa ga masoyin ka , kai din nan kana aljanna ne daga cikin aljannoni na duniya
, ka yi sujada sujudan mai tsoron Allah
a duk lokacin da ka ji ayoyin alkur'ani , bayanansa suka ratsa ma
zuciya.
Allah madaukakin sarki yana cewa (Kuma yana abun karatu
mun rarraba shi domin ka karanta shi ga mutane akan jinkiri, kuma mun sasaukar da shi sassaukarwa ka ce ku yi imani da shi ko kuwa kada
ku yi imani , lalle ne wadan da
aka baiwa ilimi
gabaninsa idan ana karatun sa
akan su suna
faduwa ga habobin su suna masu sujada )
(Kuma
suna cewa tsarki ya tabbata ga Ubangijinmu lallae ne wa'adin Ubangijin mu ya
kasance hakika abin aikatawa , kuma suna faduwa ga habobin su suna
kuka kuma yana
kara musu tsoro
)
(ka
yi sujada kuma ka kusanto ) kuma duk lokacin
da ka tuna jinkirin ayukan ka kuma ka ji zafin zunuban ka da gafalar ka ka rinka kwankwasa kofar tuba da neman
gafarar ka to Allah madaukaki yana cewa yana mai siffanta Annabin sa Dauda Amincin Allah ya tabbata a gare shi
(Dauda
ya tabbatar da cewa mun fitine shi ne, sabo da haka, ya nemi Ubangijin sa gafara kuma ya fadi yana mai sujada kuma ya mayar da al'amari ga Allah , sabo da
haka muka gafarta masa wancan . Kuma
lallai yana da wata kusantar daraja a
wurin mu da kyawun makoma )
(ka
yi sujada kuma ka kusanto ) Idan bakin ciki ya
tananta a gare ka , matsaltsalu sun kyawaye ka
ga fitintinu sun dame ka , to lalle sujada yayewa ne ga dukkan wani bakin ciki duk wanda zuciyar sa ya kuntata
mutane suka bata mishi rai to, ya yawaita salla da sujada da adu'a Allah madaukakin sarki ya ce :- ( Hakika mun sani cewa
zuciyan ka na kuntata sakamakon
abinda suke fadi to ka yi tasbihi da godiy a ga Ubangijin ka ka kasance cikin masu sujada )
Sujada na
kashe fushin Uabangiji mai rahama kuma
yana haifar da yardan sa tsarki ya tabbata ga Allah madaukaki :- Ya zo a sahihi ingantacce na Annabi tsira da aminci su tabbata a gare
shi (kan cewa idan mutane sun tsaya a
farfajiyan ranar alkiyama aka tafi neman
ceto
wurin Annabawa, har suka kai ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata
a gare shi,sai suka ce ya Muhammad ba ka ga halin da muke ciki ba? Ba ka ga
musibar da ta same mu ba? Sai yace "Da ma neman ceton tawa ce" sai Manzon
Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya tafi ya yi sujada a
karkashin Al'arshi, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,
yace : sai na nemi izinin Ubangiji na sai ya ban izini,shi na gode mi shi,da
wasu yabo da ba zan iya su yanzu ba, wanda Allah zai min ilhamar su, sai na
fadi ina mai sujada sai a ce ya Muhammad daga kanka, ka fada za a saurare ka,
ka roka zaa baka, ka nemi ceto za a baka.) Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Sai Allah ya sanya sujada a
matsayin ceto kuma tsani don fita daga azabar matattarar kiyama.
A duk lokacin da ka samu wasu
alheri da kyauta mai yawa daga Mai rahama to ka fadi ka yi sujada ga Allah don godiya bisa ni'imarsa.
An
karbo daga Abu bakrata yace a duk lokacin wani abu na farin ciki ya samu Annabi
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai ya fadi ya yi sujada ga Allah)Su
biyar suka rawaito banda Nasa'i
An
karbo daga Abdurrahman Bin Auf Allah ya
kara yarda a gare shi ya ce Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a
gare shi, ya yi sujada sai ya tsawaita sujadan sannan sai ya daga kansa sai ya
ce " Lalle Jibrilu ne ya zo ya mini albishir sai na yi sujada don godiya
ga Allah" Ahmad ne ya rawaito Hakim kuma ya inganta shi.
Huduba ta biyu
Bayan haka!
Mamakin da kyaun sauyawan
mutumin da zai kwankwadi dadin sujada a dararrakin ramadana da falalarsa,Allah Madaukakin sarkin yace :(Daga wani sashe na dare ka
yi masa sujada kuma ka masa tasbihi dare mai tsawo,)
Allah
Madaukakin sarkin yace :(Da wadanda suke kwana suna sujada da tsayuwan dare) Allah
Madaukakin sarkin yace (Shin wanda yake mai tawaliu tsawon dare yana mai sujada ku yana mai tsayuwa ga sallah
yana tsoron lahira kuma yana fatan rahamar Ubangijinsa(yana daidai da waninsa?)
Ya kai mai tsere zuwa ga
aikin alheri a ramadan, ka yi gaggawa a
tafiyarka zuwa ga ubangijinka.
Hasara dukkan hasara shine a
haramtawa bawa ni'imar sujada gaba ga Ubangiji.
Idan dan'adam
ya karanta sajada sai yayi sujada sai shaidan, sai shaidan ya kebe yana kuka yana cewa : ya bonenSa- A riwayar Abu kuraib "ya bone na"
An umarci dan Adam da sujada sai yayi to yana da Aljanna.
An umarce ni da sujada sai na ki to gashi zan shiga wanda)
Muslim ne ya rawaito
Duk wanda ya
yi girman kai bai yiwa Ubangiji sujada ba a duniya ba, to ba zai iya yin haka a lahira ba in an kiraye shi da
haka.
An karbo daga
Ada'u dan yasar daga Abu Said Allah ya kara yarda a gare shi yace :Na ji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata
a gare shi ya ce:UbangijinMu zai yaye kwabrinsa sai dukkan wani Mumini da
mumina, su yi sujada sai yasaura kawai
wanda ya kasance mai yin sujada don riya da neman a ji. Sai ya je don yayi
sujada sai bayansa ya zamza shinfida
guda).Bukhari ne ya rawaito