الجمعة، 19 أبريل 2019

watan sha'aban shiri ne don ramadan


Tarjamar Hudubar Masllacin Annabi Na shaikh Abdullah bin Abdurrahman Albuaijan 14-8-1440AH/19/4/2019AD

Hudubar farko
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya halicci sammai da kasa, ya sanya duhu da haske, mai sauya ranaku da watanni, mai karar da shekaru da zamuna.
Ina gode masa ga dukkan al'amura,muddin iskar gabas da ta yamma na kadawa.
Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, bisa gaskiya da yakini. Ina adana ta ga Allah  ranar da rai bai mallaki wani abu ba ga wani rai, kuma al'amari a wannan rana na Allah ne.
Kuma na shaida Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne, ya isar da sako ya sauke.amana, ya yi jahadi a tafarkin Allah har yakini ya zo mishi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabban shi baki daya.
Bayan haka !Lalle Alkur'ani shine zance da magana mafi kyau,Addini a gurin Allah shine musulunci,Mafi alherin shiriya shine koyarwar Annabinmu Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,(Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku ku tsoraci wata rana da mahaifi ba zai fanshi danSa ba, ko shi da ya fanshi mahaifinSa da wani abu, lalle alkawarin Allah gaskiya ne kada rayuwar duniya ta rude ku, kada wani mai rudi game da Allah ya rude ku.)
     Ya Ku jama'ar musulmi!
Lalle Allah ya sanya lokuta tamkar wata ma'adana ce ga aiki, (To duk wanda ya yi wani aiki da ya kai kwayar zarra na alheri zai gan shi. To duk wanda ya yi wani aiki da ya kai kwayar zarra na sharri zai gan shi)
Wanda ya yi hasara shi ne wanda ya hasarar da lokuta mafi alheri, mahrumi shine wanda aka hana shi ribatar lokutan da'a, hakika Allah ya sanya zamani ya zama hanya ne ga muminai zuwa ga biyayya ga Ubangijinsu, hasara ce ga wasu mutane da zai zama gafala ne ga kawunan su, to ku raya kawunanku,ta hanyar yin biyayya ga Allah, domin zukata na rayuwa ne da ambaton Allah (Abin da ku ka gabatar na alheri don kawunanku zaku same shi a gurin Allah).
Ya ku bayin Allah!
Lalle zamani na da fifiko kan sashi bisa ranaku ko watanni ko sa'oi, mafi alherin abin da mutum zai raya shekarunsa da shi ya raya lokacinsa sune ayyuka masu falala da abin da zai kusanto da kai ga ubangiji, da aikata ayyukan alheri da da'a, Allah Madaukakin sarki ya ce : (kuma shine wanda ya sanya dare da yini akan mayewa ga wanda ya ke son ya yi tunani ko kuwa ya yi nufin ya gode,)
Ku saurara! Lalle kuna cikin wata mai girma wanda da yawa daga cikin mutane na gafala daga shi tir da gafala kason wadanda aka hana alheri,kayan hajan lalatatu,
Ku saurara! Lalle kuna cikin wata mai girma da ake daga ayyuka a cikinsa zuwa ga Ubangijin talikai, to ku cike karshensa da tuba, da ayyuka na kwarai,ko Allah zai bamu kyakkyawan karshe,
Ku saurara! Lalle kuna cikin wata mai girma da manzon Allah ke kokarin yin azumi a cikin shi.
An karbo daga Usama dan Zaid yace da Manzon Allah tsira amincin Allah su tabbata a gare shi, ban ga kana yawaita azumi a wani wata ba kamar yadda naga ka ke yawaita wa a wannan watan na sha'abana ba, sai yace :( Ai wannan wata ne da mutane ke gafala daga shi yana tsakanin rajab da ramadan kuma wata ne da ake daga ayyuka zuwa ga Ubangijin talikai to sai na so a daga ayyuka na ina mai azumi.
An karbo daga Aisha Allah kara yarda agare ta tace : Manzon Allah ya kasance yana azumi har muce ba zai sha ba, wani sa'i kuma yana sha har muce ba zai yi azumi ba,ban taba ganin manzon Allah ya cika wani wata  yana azumi ba sai ramadan ba watan da naga yana yawaita azumi acikin shi kamar  sha'aban,)Muslim ne ya rawaito
An karbo daga gare ta ta ce: ya kasance mafi soyuwan watanni a gurin manzon Allah da ya azumce shi shine sha'aban) Abu Dawuda ne ya rawaito shi a sunan nashi kuma Albani ya inganta shi.
Ya Ku jama'ar musulmi!
Lalle a daren  tsakiyan sha'aban Allah na da gafara da take game muminai amma ana haramtawa masu gaba da kiyayya da kullin juna da kafurai, An karbo daga Abu Musa Al'ash'ari Allah ya kara yarda a gare shi, yace :Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yace: (Lalle Allah na tsinkaya a tsakiyar daren sha'aban sai ya gafartawa dukkan halittun shi banda mushriki ko mai gaba da wani,)Ibnu Majah ne ya rawaito da waninsa,Ibnu Hibban da Albani sun inganta shi    
 Ku yafe ku yi rangwame  ku dauke kai ku tausayawa juna, ku yi afuwa, ku sada zumunci, kar ku yi hasada, kar ku yi munajasha, kar ku yi kiyayya kar ku juyawa juna baya, ku zama bayin Allah  'yan uwan juna.
 An karbo daga Abu huraira Allah ya kara yarda a gare shi, yace :Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yace: (Lalle ana bude kofofin Aljanna ranar litini da ranar Alhamis, sai a gafartawa dukkan bawan da bai hada Allah da wani face mutumin da akwai kiyayya da dan'uwan shi, sai ace : ku dakanci wadannan biyun har sai sun yi sulhu! ku dakanci wadannan biyun har sai sun yi sulhu! ku dakanci wadannan biyun har sai sun yi sulhu!) Muslim ne ya rawaito.
Ya ku bayin Allah!
Sha'aban sha gaban daya daga cikin rukunnen musulunci ne, shine Azumin watan ramadan da aka saukar da Alkur'ani a cikinsa.
To shi fage ne na sabo da koyo, da kimtsawa da shiryawa, da shigowan watan imani don fiskantar watan ramadan,
Sha'aban da ramadan kamar sunnoni ne na ratibi  ga sallolin farillah. Shi kamar wani gwaji ne don sabo da watan ramadan don rage wahalansa da nauyin sa da dandana zakin azumi da dadinsa sai mutum ya shiga azumin ramadana da kuzarinsa da karsashinsa.
 Ya Ku jama'ar musulmi!
Duk wanda akwai biyan azumin watan ramadana da ya gabata a kansa to ya gaggauta azumtarsa kafin shigowan watan ramadan, don jinkiri game da haka zai iya zama sababi daga cikin sabuba na sakaci,
An karbo daga Aisha Allah kara yarda a gare ta tace : Azumi na kasancewa a kai na ba na samun daman biyansa har sai sha'aban sabo da matsayin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,)
To ku gaggauta ayyukan alheri –Allah ya muku rahama- kafin ajali ya zo, (ku gaggauta  zuwa ga gafara daga Ubangijinku, da Aljanna wanda fadinta ya kai sammai da kasa an tanade shi ga masu takawa.)

 Huduba ta biyu.
Dukkan yabo ya tabbata ga Allah bisa kyautatawarsa godiya ta tabbata a gare shi bisa datarwarsa  da baiwarsa, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya, ina mai girmama shaninsa,na shaida Annabi Muhammad bawansa ne kuma Manzon sa ne, mai kira zuwa ga neman yardarsa, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabbansa da aminci tabbatacce mai yawa.
Ya ku musulmai!
Lalle Allah madaukakin sarki, ya farlanta azumin watan ramadan a wannan wata, wato ina nufin  sha'aban  a shekara ta uku bayan hijira: Manzon Allah ya yi azumi
Ramadan sau tara, sannan ya koma ga Ubangijinsa.
 Allah madaukakin sarki yace; (Ya ku wadanda suka yi imani An wajabta muku azumi kamar yadda aka wajabta shi ga wadanda suka gabace ku ko zaku ji tsoron Alla)
. Ranaku ne kididdigaggu to duk wanda ya ke maralafiya a cikinku ko yana matafiyi to gwargwadon abin da ya sha na daga kwanaki a wadansu kwanaki yana kansa. Fidiya yana kan wadanda ke da ikon yin azumi tare da wahala ita ce abincin miskinai, duk wanda ya yi tadauwa'i na alheri to ya fi alheri a gare shi, ku yi azumi shi ya fi amfani a gare ku, in kun kasance kun san hakan yafi ( watan ramadan shine wanda aka sauke Alkur'ani a cikinsa mai shiryar da mutane daga bata, ayoyi na shiriya mabayyana da rarrabewa tsakanin karya da gaskiya. Duka wanda ya ga wata daga cikin ku to ya azumce shi, wanda ya kasance mara lafiya ko a kan tafiya to gwargwadon abin da ya sha na kansa na wasu kwanaki, Allah na nufin sauki gare ku bai nufin tsanani gare ku, sabo da ku cika adadin kuma ku girmama Allah bisa shiryarwar da ya muku kuma don ku gode masa bisa wannan ni'ima,)
An karbo daga Abdullahi dan umar Allah ya kara yarda a gare shi, yace :Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yace: (Lalle An gina musulunci akan  abubuwa biyar :Bisa a bautawa Allah a kafurcewa waninsa, ya tsaida salla ya bada zakka da hajji dakin Allah da azumin ramadan )Muslim ne ya rawaito.
An karbo daga Abu huraira Allah ya kara yarda a gare shi, yace :Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yace: (wanda ya yi azumin ramadana yana mai imani da neman lada zaa gafarta masa abin da ya gabata na daga zunubansa kuma wanda ya yi tsayuwan dare na ramadan bisa imani da neman lada to zaa gafarta mishi dukkan abin da ya gabata na daga zunubansa) Bukhari ne ya rawaito
 Ya ku bayin Allah!
Ba abin da ya rage a wannan wata sai ranaku kididdigaggu, to ya dace ga musulmai da su shirya wa wannan wata,da su kimtsa masa, kuma su yi gaggawa  su yi tsere da rigegeniya bisa biyayya ga Allah . to sam barka ga wanda ya riski ramadan,barka da duk wanda aka datar da shi zuwa ga alheri da ayyukan kwarai, ya mai neman alheri ka fiskanto ya mai neman sharri ka gajarta,
To ku nuna wa Allah alheri daga kawunanku, don matsiyaci shine wanda aka haramta mishi biyayya  ga ubangijinsa, kuma lokutan alheri suka tsere mishi bai fadaku ba. Ya yiwa kansa barna har mutuwa ta shammace shi bai tuba daga zunubansa ba.  


   


الخميس، 4 أبريل 2019

Ni'imar Aminci da zaman lafiya



Hudubar Juma'a na Masallacin Annabi na shaikh Abdullah Dan Abdurrahman Al-Buaijan 15-7-1440 AH.

HUDUBAR FARKO :
  Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Madaukakin sarki,  muna gode mishi kuma muna neman taimakonsa ,  kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu , da munanan ayyukanmu , duk wanda Allah ya shiryar da shi babu mai batar da shi , duk wan da ya batar kuma babu mai shiryar da shi , na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bai da abokin tarayya,
Wanzuwa da kyakkyawan yabo nasa ne, Kaddartawa da hukuntawa na hanunsa, shi ke gudanar da al'amura daga kasa zuwa sama, yana aikata abin da ya so, ba za ku samu damar ku so abu ba sai idan Allah ya nufa.
 kuma na shaida Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne, ya isar da sako ya bada amana, yayi nasiha ga al'uma, ya yi jihadi a tafarkin Allah cancancin jihadi har yakini ya zo masa (Mutuwa) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa  da sahabbansa baki daya.
Bayan haka :
Lalle mafi alherin zance shine maganar Allah,  kuma mafi alherin shiryarwa shine shiryarwar Annabi Muhammad, kuma mafi sharrin al'amura sune fararrunta, kuma dukkan bidiah bata ne kuma dukkan bata na wuta,
Ya ku bayin Allah ina muku wasiyya da ni kai na da ku ji tsoron Allah, shine wasiyar Allah ga mutanen farko da na karshe, Allah Madaukakin sarki ya ce :(, haƙĩƙa, Mun yi wasiyya ga waɗanda aka bai wa Littãfi a gabãninku, da kũ, cewa ku bi Allah da taƙawa,) 
Allah Madaukakin sarki ya ce :
  ( Ya ku mutãne! Ku bi Ubangijinku da taƙawa Wanda Ya halitta ku daga rai guda, kuma Ya halitta, daga gare shi, matarsa, kuma Ya watsa daga gare su maza mãsu yawa da mãtã. Kuma ku bi Allah da taƙawa Wanda kuke rõƙon jũna da (sũnan), shi, da kuma zumunta . Lalle ne Allah Ya kasance, a kanku, Mai tsaro ne). 
Ya ku jama'ar musulmi!
Hakika Allah ya yalwata mana ni'imomi da ba zasu kididdigu ba,kuma ya bude mana kofofin  kyautarsa gare mu, kyautar da ba za ta kirgu ba, ya girmama mu da aminci da yalwa,da kwanciyar hankali da wadata, ya yi nesa da mu daga fitintinu da bala'i da musibu na tsautsayi da hasara, da falalar Allah tare da rikon mu da akidarmu da kokarin jagororinmu da malamanmu, Allah madaukakin sarki ya ce : ( Ku tuna a lõkacin da kuke kaɗan, waɗanda ake raunanarwã a cikin ƙasa kunã tsõron mutãne su cafe ku, sai Ya tattara ku (a wurin natsuwa, Maɗina), kuma Ya ƙarfafã ku da taimakonSa kuma Ya azurtã ku daga abũbuwa mãsu dãɗi; Tsammãninku, kunã gõdewa).
Zaman lafiya na daya daga cikin abubuwan da ke mikar da rayuwan mutum, da shi ake samun kwanciyar hankali da natsuwa,
Zaman lafiya na daga cikin hadafin da kowace al'uma ke nema.kuma ta yi amfani da duk wata hanya ko karfi da take da sh,
Zaman lafiya ni'ima ce da ba wanda ya san kimanta da girman muhimmancinta face wanda ya konu da wutan rashinta,
  Zaman lafiya ni'ima ce da rayuwa bai dadi in babu ita,haka ba natsuwa da tabbatuwa guri guda in an rasa ta, Manzo Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(Duk wanda ya wayi gari cikin aminci a gidansa da lafiya a jikinsa, yana da abincin wuninsa to tamkar an tattara masa duniya ne)
Lalle amincin rai da mutunci da dukiya na daga cikin  mafi girman ni'imomi,duk dan adam na bukatarsa, a dukkan zamani da wuri,don ya samu hutu da natsuwa,
Amma idan wutan fitina ta kunnu al'amura suka rikirkice, ya tsoracewa rai da mutunci da dukiya, kuma mutane suka farga daga tashin hankali na bala'i idanuwa suka karkace, zukata suka isa makogoro sabo da tsoro to a nan ne mutum zai yi nadama a lokacin da nadama ba zata yi amfani ba, sai ya yi da na sani game da sakaci da yayi game da aminci da ni'imomi.
Ku yi dubi da idanuwa  ga wasu al'umu da garuruwa, da sun kasance cikin alheri da nitsuwa, yayin da wutar fitina ta kunnu a cikinsu kasa ta yi musu kunci yanayi ya sauya ba daya daga cikinsu da ya samu kwanciyar hankali, to lalle cikin wannan akwai abin lura da waazi ga duk wani wanda akwai kwayar zarra na imani a zuciyarsa.
Hakika alkur'ani ya yi bayani daki daki kuma ya buga misalai mafi ban   kaye:(kuma Allah ya buga misalin wata alkarya ta kasance tana cikin aminci da natsuwa, arzikinta na zuwa mata da yalwa daga ko ina sai ta butulcewa ni'imomin Allah sai ya dandana musu azbar yunwa da tsoro sabo da abin da suka kasance suna aikatawa)
Ku dubi yanda Allah ya ni'imta wasu mutane ya kwarara musu ruwan ni'ima daga taskarsa amma suka juya baya sai bala'i ya sauka a gare su
(Lalle hakika akwai aya ga Saba'awa a cikin mazauninsu: gonakin lambu biyu, dama da hagu, "Ku ci daga arzikin Ubangijinku, kuma ku yi godiya gare shi. Gari mai dadin zama, da Ubangiji Mai gafara" sai suka bijire, sabo da haka muka saki malalin Arimi (Dam) a kan su, kuma muka musanya musu gonakinsu biyu da wadansu gonaki biyu masu 'ya'yan ita ce kadan: talakiya da goruba da wani abu na magarya kadan, wancan, da shi muka yi musu sakamako sabo da kafurcinsu.kuma lallai ba mu yi wa kowa irin wannan sakamako face kafurai. . Kuma Muka sanya, a tsakaninsu da tsakãnin  garũruwan da Muka Sanya albarka a cikinsu, waɗansu garũruwa mãsuganin jũna kuma Muka ƙaddara tafiya a cikinsu, "Ku yi tafiya a cikinsu, darũruwa da rãnaiku, kunã amintattu."  Sai suka ce: "Ya Ubangijinmu! Ka nĩsantar da tsakãnin tafiyõyinmu," kuma suka zãlunci kansu, sabõda haka Muka sanya su lãbãran hĩra kuma Muka kekkħce su kõwace, irin kekkħcewa. Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga dukan mai yawan haƙuri, mai yawan gõdiya). 

  .  Ya Ku Jama'ar musulmai!
Rudani da hayaniya ba su sa a cinma manufa sai dai fitintinu da bala'i, ba abin da zasu haifar face  tashin- tashina da rikici da hasara, mun gani kuru kuru abin da ya faru da wasu al'umu a da yawa daga cikin wasu garuruwa a sakamakon hakan.rayuka da dama da basu ci ba basu sha ba aka sarayar da su,!Dukiya adananna da yawa an lalata ta,aka keta mutuncin masu mutunci, jama'a da dama sun gudu, dangi da iyalai an tarwatsa su,wasu yara an maida su marayu,an rusa gidaje.
Lalle tada fitina  makauniyar kira ce da abokan gaba suka shirya ta, wawaye da maha'inta kuma suke tallata ta, mashirmata kuma suke biye mata.
Abin da yake wajibinmu shi ne mu yake ta, mu zama tsintsiya madaurinki daya a gaban duk wanda ke son yayi batanci gare mu ko raba kanmu,ko ya ke barazana ga zaman lafiyarmu,ko ya yi tawaye ga jagororinmu da shuwagabanninmu.
To ku yi riko da addininku, ku dunkule ku hade don fiskantan abokan gabanku, ku tsayu a kan tafarkinku.
Ku sani lalle Allah ya wajabta muku biyayya ga jagororinku, Allah Madaukakin sarki yace : (ya ku wadanda suka yi imani ku yi da'a ga Allah kuma ku yi da'a ga Manzon Allah, da ma'abota jagoranci daga cikinku),
To biyayya ga jagororinmu na daga cikin addininmu wanda shine kariya ga al'amarinmu, akwai kuma gyara ga duniyarmu da muke rayuwa a cikinta.
An karbo daga Irbad dan sariya Allah ya kara yarda a gare shi ya ce, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya mana sallar asuba sai ya juyo ya mana wani wazi mai ratsa jiki wanda zukata sun tsorata, idanuwa sun zubar da hawaye, sai muka ce ya Manzon Allah tamkar wannan wazi ne na ban kwana, to a mana wasiya, sai yace :(Ina muku wasiya da ku ji tsoron Allah ku ji ku bi ko da kuwa an dora muku jagorancin bawa ne dan habasha,to duk wanda ya rayu cikinku zai ga sabani mai yawa,to ku yi riko da sunna ta da sunnar kalifofi na shiryayyu wadanda aka shiryar da su,ku riko ta da hakoran cin tuwonku,na hore ku da ku nesaci fararrun abubuwa a addini don dukkan bidia bata ce)Hakim ne ya rawaito shi a Mustadrak.
Ku roki Allah tabbatuwa a kan addininku,ku kiyayi fitintinu, ku zama kuna tare da jagororinku,kuna komawa zuwa ga malamanku, ku hada kai don fiskantar makiyanku da duk wanda ke son ku samu matsala a zaman lafiyarku da hadin kanku,
Ina neman tsarin Allah daga sharrin shaidan abin jefewa. (Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi ɗã'a ga Allah, kuma ku yi ɗã'a ga ManzonSa, da ma'abũta al'amari daga cikinku.(3) Idan kun yi jãyayya a cikin wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da ManzonSa idan kun kasance kunã ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Wannan ne mafi alheri, kuma mafi kyau ga fassara).
Allah sa mini Albarka da ni da ku cikin Alkur'ani mai gairma, ya amfane ni da ku da abin da ke ciki na ayoyi da ambato mai hikima,
Ina fadin abin da kuke ji, ina neman gafarar Allah ni da ku da sauran musulmai daga dukkan zunubai, to ku nemi gafararSa don shi mai gafara ne Mai jinkai.

Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah da ya sako ni'imomi, ya tunkude azaba, ya sanya mu al'uma mafi alheri, ya cusa imani a cikin zukatanmu, ya sanya aminci da zaman lafiya a kasarmu, to godiya ta tabbata ga Allah a farko da karshe, hukunci nashi ne kuma gare shi zaku koma.
Ya ku bayin Allah!
Allah ya halicci mutane a mataki mataki, ya sanya fifiko a tsakaninsu cikin kudura da baiwa, ya sanya malamai magada Annabawa, ya daga matsayin su da darajojin su, wannan falala ne na Allah ya na bawa wanda ya so, ya shiryar da mutane ga komawa gare su da koyi da su,To su ne masu rikon ilimi da bada kariya ga  addini, da kiyaye mutunci, ya tabbata daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : (Adilai ne na kowane mamaya  Zasu dauki wannanan ilimi, zasu kore jirkitawan masu ketare iyaka, da cogen mabarnata, da tawilin jahilai) .
To idan fitina ta taso, bidi'o'i suka cakuda da sunna, wawayen mutane suka tsoma baki cikin al'amarin al'uma, gaskiya ta jirkita da bata, malami da jahili suka jirkice, abubuwa suka rincabe,to ku riki akidarku da gaske, ku aminta da malamanku da jagororinku, ku ji tsoron Allah akan kawunan ku da al'umarku, kar ku bi ko wani mai ihu, ku banbance tsakanin jerin gwanon kalmomi na gaba da na baya.
(Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun haɗu da wata ƙungiyar yãƙi, to, ku tabbata, kuma ku ambaci(2) Allah da yawa, tsammãninku kunã cin nasara.   . Kuma ku yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, kuma kada ku yi jãyayya har ku raunana kuma karfinku ya tafi, kuma ku yi haƙuri. Lalle ne Allah Yanã tãre da mãsu haƙuri.)

 Ya ku matasa...
Ku ne ruhin Al'uma kuma mahanganta , da ku ne zata rayu ta yi kyau, al'uma ta taso a birni da kauye,daku  ake karya logon batattu da mabarnata,
To ku kiyaye dukkan kiyayewa daga fitintinu, da kuma kai komo a cikinta da mara mata baya, to addinin ku na da wajibi da ya hau kanku to ku bada shi, magabatanku na da hakki a kanku to ku cika, kuma kasarku na da wajibi da ya doru a kanku to ku kiyaye shi, ku ji tsoron Allah ku sani zaku hadu da shi.
(Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku karɓa wa Allah, kuma ku karɓa wa Manzo, idan Ya kirãye ku zuwa ga abin da Yake rãyar da ku; Kuma ku sani cewa Allah Yanã shãmakacewa a tsakãnin mutum da zũciyarsa, kuma lalle ne Shĩ, a zuwa gare Shi ake tãra ku.
   Kuma ku ji tsõron fitina wadda bã ta sãmun waɗanda suka yi zãlunci daga gare ku keɓe, kuma ku sani, lalle ne Allah Mai tsananin uƙũba ne).
Bayan haka yaku jama'ar musulmai
 Musulmai gangan jiki ne guda kuma gini ne guda, ketare iyaka ga dayan su to ketare iyaka ne ga dukkaninsu, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yace :Misalin mumini cikin kaunarsu da son junansu da tausayawa juna tamkar jiki ne idan wani gaba na ciwo sai sauran gabbai su amsa da rashin barci da zazzabi). Muslim ne ya rawaito
   Lallai musibarku da musibar mu na ga abin da ya faru  na yaudara da taaddancin da a ka nufi 'yan uwanmu musulmai da zubar da jinin masallata da tsoratar da wadanda ke cikin aminci, da keta alfarmar dakin Allah,
Kuma ba su tuhumce su ba, fãce kawai domin sun yi ĩmãni da Allah, lalle musiba ce mai girma,babban abin firgitarwa ne, muna neman ladanta a gurin Allah, kuma abin da ke gun Allah ya fi alheri kuma ya fi wanzuwa.
To daga Allah muke kuma gare shi za mu koma, Allah kyautata ta'aziyyar 'yan uwan mu, ya girmama musibarsu, Allah ka yi gaggawan bawa marasa lafiyan cikinsu lafiya, Allah gafartawa matattu ya daga darajojinsu cikin madaukaka,
Ya Allah ka daukaka musulunci da musulmai