Hudubar Juma'a na
Masallacin Annabi na shaikh Abdullah Dan Abdurrahman Al-Buaijan 9-5-1439 AH.
Dukkan yabo da godiya
sun tabbata ga Allah, Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, wanda ya
ilmantar da alkalami, ya sanar da mutum abin da bai sani ba,ina kyautata yabo a
gare shi bisa ni'imominsa,ina kuma gode mishi bisa abin da ya mana na falaloli
da karamci.
Na shaida ba abin
bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bai da abokin tarayya, na shaida
Annabi Muhammad shine cikamakin Annabawansa da Manzanninsa, Allah ya zabe shi a
kan sauran al'umu, ya turo shi don tausayawa ga talikai zuwa ga larabawa da
ajamawa, ya isar da sako, ya sauke amana ya yi jahadi a tafarkin Allah hakkin
jahadi har mutuwa ta zo mishi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,da
iyalan shi da sahabbansa da duk wanda ya bi su da kyautatawa har zuwa ranar
sakayya.
Bayan haka, Lalle
Alkur'ani shine zance mafi kyau, Addini a wurin Allah shine Musulunci,mafi
alherin shiryarwa shine shiryarwar Annabinmu Muhammad tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi ( Ya ku mutane ! ku bautawa Allah Ubangijin ku da takawa
, kuma ku ji tsoron wani yini, ranar da
wani mahaifi baya sakawa dansa da komai
ko wani da ya sakawa mahaifin sa da komai
lallai wa'adin Allah gaskiya ne ,
sabo da haka kada rayuwar duniya ta rude ku
kuma kada marudin nan ya rude ku
game da Allah ) .
YA KU BAYIN ALLAH !
Hakika Allah ya zabi
dan adam domin ya sanya shi kalifa a
doron kasa ya bashi ilimi wanda yana ta'alluki ne da aiki da kuma
daukaka , ya kuma bashi hankali wanda ya ta'allaka ne da takalifi Allah Madaukakin sarki ya ce : (
kuma a lokacin da Ubangijinka ya ce ga mala'iku lallai ne ni mai sanya wani halifa ne a cikin
kasa: suka ce, ashe za ka sanya a cikin ta wanda zai yi
barna kuma ya zubar da jini alhali kuwa mu muna yi maka tasbihi game da
gode maka , kuma muna tsarkakewa gare
ka ya ce : lallai ne ni na san abin da ba ku sani ba )
Sannan
ya bayyana cewa ilimin nan yana ta'allake ne da falala da daukaka sai ya ce :
( Kuma ya sanar da Adam sunaye dukkan
su sa'annan kuma ya gitta su a kan mala'iku sa'annan ya ce : to ku gaya mini sunayen wadannan idan kun
kasance masu gaskiya)
suka ce tsarki ya tabbata a gare ka ! ba bu sani a
gare mu face abin da ka sanar da mu , lallai ne kai, kai ne masani mai hikima
. Ya ce : ya Adam ! ka gaya musu sunayen
su : '' to alokacin da ya gaya musu
sunayen su , (Allah) ya ce : ashe ban ce
muku ba lallai ni ina sane da gaibin
sammai da kasa ( kuma ina sane da abin da kuke bayyanawa da abin da kuka
kasance kuna aikatawa)
Sai Allah ya fifita
mutum bisa da yawa daga cikin halittun sa
a dalilin ni'ima ta ilimi da hankali ,
ya kuma dora taklifi a kan haka .
YA JAMA'AR MUSULMI!
Dalibai maza da mata za su fiskanci sabon fasali na karatu a wannan ranaku,
to madalla da wanda ya dage ya yi kokari
ya ja damara cikin aikin alheri to zai samu sa'ada , to lallai ilimi shi ne ginshikin addini kuma da shi ne mutum zai san addinin shi kuma da shi ne mutum zai iya sanin yadda zai yiwa Ubangijin
shi da'a , kuma farkon umarnin da mala'ika jibrilu ya zo da shi daga wurin Allah zuwa ga Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi shi ne ; umarni da neman ilimi , kuma farkon ayan da ta sauka a Alkur'ani
shi ne; ( yi karatu).
An karbo daga Aisha , Allah ya kara yarda a gare ta ta ce : ( Farkon abin da aka
fara wahayi wa Manzon Allah shi ne mafarki na gaskiya
a cikin bacci , ya kasance baya ganin wani abu a cikin bacci face abin ya bayyana kamar hasken safiya
sannan sai aka kwadaitar a gare shi yin khalwa , ya kasance yakan tafi
kogon hira ya kebanta yana ta bauta a ciki na wasu dararraki masu adadi
kafin ya dawo zuwa ga iyalan shi ya sake samun guzuri , har zuwa lokacin da gaskiya ta zo mishi , mala'ika Jibrilu ya sauka a gare
shi a halin yana kogon hira sai mala'ika ya zo mishi sai ya ce : yi karatu , ya ce : ( ni ba mai karatu ba ne
) sai ya ce : sai ya kama ni ya matse ni
har na ji wahala sannan ya sake
ni sai ya ce yi karatu : sai na ce: ( ni ba mai karatu ba ne ) sai ya sake kama ni ya matse ni a karo na
biyu har na ji ba dadi sannan ya sake ni , sai ya ce yi karatu : sai na ce : (
ni ba mai karatu ba ne) sai ya kama ni ya matse ni a karo na uku har na ji jiki
, sannan ya sake ni sai ya ce : yi karatu da sunan Ubangijin ka wanda ya yi halitta, ya halitta mutum
daga gudan jini, ka yi karatu
kuma Ubangijinka shi ne mafi karamci ,
wanda ya sanar da (mutum ) game da alkalami ya sanar da mutum abin da bai sani ba ).
Ya ku bayin Allah hakika Alkur'ani ya kwadaitar bisa ga neman ilimi,
Allah bai umarci Annabin shi ba da ya
roke shi karin wani abu ba sai ilimi , (
kuma ka ce ya Ubangiji ka kara min ilimi )
Kuma ya koda matsayi irin
na malamai sai ya ce : ( Malamai kawai ke tsoron Allah a cikin
bayin sa).
Kuma Allah ya hada su da
kansa da mala'ikunsa cikin shaidawa da kadaitakarsa, Allah madaukakin sarki ya ce : ( Allah ya
shaida cewa : Lalle ne babu abin bautawa face
shi , kuma mala'iku da ma'abuta
ilmi sun shaida , Yana tsaye da adalci , babu abin bautawa face shi , mabuwayi , mai hikima ).
Kuma Allah ya yi nuni bisa kimansu sai ya ce: ( Ka ce ashe , wadanda suka sani , suna daidaita da wadanda ba su sani ba ?).
Kuma ya yi umarni da komawa gare su yace :(To ku tambayi ma'abota
ilimi in kun kasance baku sani ba).
Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kwadaitar game da shi ya bayyana cewa alama
ne na alheri (Wanda Allah ya nufe shi da alheri zai fahimtar da shi addini).
Yace : (Wanda
ya kama hanya ta neman ilimi Allah zai saukake mishi hanya ta shiga Aljanna)
To ku bawa ilimi wani
kaso na daga lokutanku,kuma ku kwadaitar da yaranku bisa kokari da jajarcewa wajen
nemansa.domin shi ne hanya mafi dacewa ta tarbiya, kuma mafi tabbatuwar yakini
wurin tsarkake zuciya.kuma ya fi kawo amintuwa daga fitintinu, kuma yake
kawo tabbatuwa da tsayuwa yayin jarabawa, yafi kawo hakuri yayin musiba,kuma
yana cikin kyawawa mafi daraja da aikin lada mafi girma na neman kusanci ga
Allah, da samun daraja mafi daukaka.
Ya ku Musulmai!
Duk wanda Allah ya nufe
shi da alheri zai sanar da shi addini, mafi alheri cikinku a lokacin jahiliyya
sune mafi alherinku a lokacin musulunci in sun yi ilimi,kuma malamai sune
magada Annabawa.
Shagaltuwa da ilimi na
cikin Bakiyatussalihat da sadaka mai gudana bayan mutuwa, da
samun lada mai dorewa bayan wafati,
An karbo daga Abu
Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce, Manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi ya ce : Idan mutum ya rasu ayyukansa zasu katse sai
guda uku: Sadaka mai gudana, ko ilimi da ake amfana da shi, ko da na kwarai da
yake mishi adu'a)
Sai dai fa ilimi na
bukatar hakuri da lokaci da kokari da juriya, da bada kai, gwargwadon wahalar da aka sha gwargwadon yadda zaa cinma manufa,da biyan bukata.
Neman ilimi na bukatar
ikhlasi a niyya da azama ta gaskiya, da tsarkake zuciya, da tsiraituwa daga duk abin da zai kawo cikas ko kashe jiki, to lalle duk wanda ya riki filo aboki ba shi
ba riskan matsayi (Yaro bata dare ka yi suna).
(kuma Ba ya
kasancewa ga muminai su fita zuwa yaki gaba daya. Saboda haka don mene ne wata
jama'a daga kowane bangare daga gare su ba ta fita (zuwa neman ilimi ba) domin
su nemi ilimi ga fahimtar addini kuma domin su yi gargadi ga mutanensu idan sun
koma zuwa gare su, tsammaninsu, suna yin sauna? ).
Mai neman ilimi na
bukatar laduba na shari'a a cikin nemansa
har ya zama abin koyi abin buga misali mai kyau, kuma ya zama ahali na
karbar wannan sako, kuma cikin adilai na wannan Al'uma.
Ya inganta daga Annabi tsira da amincin Allah
su tabbata a gare shi, (wadanda zasu karbi wannan ilimi cikin mamaya sune
adilan cikinsu, suna kore karkatarwar masu ketare iyaka da da'awar mabarnata da
tawilin jahilai).
Bayan haka ya ku bayin Allah! dukkan ilmuka masu amfani an shar'anta
nemansu, sawa'un tushensu Alkur'ani ne da sunna: kamar ilimin addini, na akida
da tafsiri da hadisi da fikihu da wasunsu, ko tushensu ya samu asali ne daga
sanin yau da kullum (Gogewa da gwaji) da dubi ga duniya da rayuwa kamar ilimin
likitanci ko ilimin da ke nazari kan haske da sauti ko (kimiyya da fasaha), da
waninsu.
, to duk wanda ya
kyautata niyyarsa wajen nemansu ina fatan fadin Annabi tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi : (Wanda
ya kama hanya ta neman ilimi Allah zai saukake mishi hanya ta shiga Aljanna) ya
game da shi.
Ina neman tsarin
Allah daga sharrin shaidan abin jefewa
Shine wanda ya aika
a cikin mabiya al'adu wani Manzo daga
gare su yana karanta ayoyinsa a gare su
kuma yana tsarkake su, kuma yana sanar da su littafin da hikimar sa ko da yake sun
kasance daga gabaninsa suna cikin bata
bayyananna . Da wadansu mutane daga gare
su, basu ida riskuwa da su ba.alhali kuwa shine Mabuwayi Maihikima.
Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya
sun tabbata ga Allah, godiyar da ta dace da daukakarsa, na shaida ba
abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai yake bai da abokin tarayya, cikin
girmansa da kamalarsa, na shaida Annabi Muhammad bawansa ne kuma Manzonsa
ne, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,da iyalan shi da
sahabbansa da aminci tabbatacce mai yawa, har zuwa ranar sakayya.
Ya ku bayin Allah!
Lalle ilimi na da
jakunkuna da ke adana shi, da masu tsaro da ke bada kariya a gare shi, da
mazaje da ke daukanshi da shehunai da ke mishi hidima, ta hanyarsu ne yake tafiya
ya yadu a duniya da kokarinsu.
Ya ku al'uma!
Lalle malami yana
wakiltar Annabawa ne a ayyukansu na tarbiyantarwa da ilmantarwa, ya ke tashi da
hidima don samar da al'uma masu tasowa nan gaba,kuma ya dasawa yara masu tasowa
na wannan al'uma iri na kyakkyawan rayuwa da walwala na duniya da lahira,to
lalle ya dace da a girmama shi a kimanta shi kuma ya dace da a mutunta shi,
haka kuma a dauke kai game da kananan laifukansu a yafe masa kurakuransa.
Ya ku Malamai da
masu bada tarbiya maza da mata.
Ku kasance abin koyi
mai kyau ku siffantu da ilimi da ladubansa, to ku manya ne a idon dalibanku,
daliban na sha'awan kwaikwayon ku da koyi da ku, to ku zama abin koyi nagari
don Allah ku zame abin koyi nakwarai, idan kun bayyana musu kyan gaskiya to ku
kasance cikin masu gaskiya, idan kun umarce su da hakuri to ku zama cikin masu hakuri,
Fara
da kanka ka hanu daga zalunci irin na rai
***
idan
ka hanu to kai ne mai hikima
To
a nan ne zaa karbi abin da ka ke fadi a yi koyi * **
da
ilimi daga gare ka, ilmantarwan ya yi amfani
Kar
ka yi hani ga wani hali kuma ka aikata irin shi***
Babban
laifi ne a gare ka in ka yi haka.
Ya ku Malamai!
Nauyin da ke kanku na
da girma, amanar da ke wuyanku babba ce. 'ya'yan wannan al'uma amana ne a kan
ku, kuma an bada ajiyar wannan al'uma a hannunku, abin da ake hanga na gabanta
ya taallaka ne da nauyin da ke kanku. Ku ji tsoron Allah game da kiwon da aka
baku, ku ji tsoron Allah game da kiwon da aka baku! (Dukkan ku masu kiwo ne
kuma abin tambaya ne bisa kiwon da aka baku,).
To in kun kyautata to
kun kyautatawa kanku ne, kuma haka ake zata muku,to kuwa kuna da falala mai
girma a gurin Allah, in kun muzguna to kun muzgunawa kanku da al'umarku ne.
Ya ku dalibai
zababbu 'ya'ya ga malamai masu biyayya!
Ku kasa kunnuwanku ku saurara, wannan zance ne da ya kebance ku,
daga mai tausaya muku kuma masoyinku:
Lalle girmama malami da
kimanta shi ladabi ne na sharia kuma halaye ne na wajibi, kuma nasara ne na
ilimi da na tarbiyya. A tafiyar Annabin Allah Musa da khidr Amincin Allah ya
tabbata a gare su a kwai abin lura da wa'azi
da tunatarwa,
(yace shin ba zan bi
ka ba don ka sanar da ni daga abin da aka sanar da kai na shiriya?). sai malamin ya maida mishi amsa da :
(Lalle ne kai ba za ka iya yin hakuri tare da ni ba, kuma ya ya za ka yi
hakuri da abin da baka kewaye sani da shi ba ga jarrabawa ).sai musa ya
zanta mishi cewa ya san hakkin malami da wahala irin na neman ilimi, (yace : zaka same ni in Allah ya so mai
hakuri, kuma ba zan saba maka ba ga wani umarni).
Lalle falalar malami na
da girma, kokarinsa da kyautarsa hakki ne da ba zaa saka masa ba sai da alheri,
to na hore ku da ku kiyaye kar ku musu rashin ladabi, domin alama ce ta
lalacewar tarbiya, da fandarewan dabiu, da hali mara fasali, ba mai yarda da shi sai dan iska.
Kuna da abin koyi mai kyau daga magabata, ga Rabi'u almajirin
imamusshafi'I Allah ya jikansu da rahama, yana cewa : Ban iya bushewan ido ba
na sha ruwa a gaban Imamusshafi'i yana kallo na sabo da kwarjininsa.
Ku girmama malamanku,
kowa ku san matsayin shi, ku bawa kowani mai hakki hakkinsa, Allah ya datar da
ku, ya azurta ku da ilimi mai amfani, da aiki na gari.
Ya Allah ka daukaka
musulunci da musulmai.