الجمعة، 17 نوفمبر 2017

BURI A RAYUWA

HUDUBAR MASALLACIN ANNABI TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI NA SHAIK ABDULBARI   ATHUBAITI NA 28- 2 1439.
     HUDUBAR FARKO :
BAYAN HAKA:
Allah  madaukakin sarki  ya hore wannan duniya mai fadi ya sanya ta  farfajiya na burace-buracen Dan adam wanda ba sa yankewa, mutane  wasu a cikinta  na gajarta buri wasu kuma na tsawaitawa  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :  ( Da dan adam ya kasance yana da kwari na dabino da ya yi fatan ya sake samun wani  kamar sa   sa'annan kuma ya sake samun  wani kamar sa har ma ya yi fatan ya  zama yana da  kwarurruka,   ba abin da yake cika cikin Dan adam sai turbaya )  Ibn Hibbana ya rawaito shi a sahihin shi.
                   Dukkan wani buri da ake fatan aikata aikin alheri  abun yabo ne, duk wani buri kuma da ake ja da abin da Allah ya kaddara  ko kuma  ayi fatan samun abin da ba zai yiwu ba to wannan abin zargi ne ,   shi buri yana nuni ne da irin abin da mutum ke dauke da shi a zuciyar sa  , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce  : (  Kuma rayi yana buri  kuma yakan yi sha'awa).   Akwai wanda yake wulgawa da burin sa  zuwa ga  izza da daukaka   wani kuma  kan jefa burin sa zuwa ga cikin rami .
                   Ma'abota himma  da azama  suna fadada burin su  kuma su kawata rayuwan su da shi  ga Umar Dan Khaddabi  yana zaune cikin  mutanen shi wata  rana sai ya ce da su  kowa ya fadi burinsa ,  sai wani mutumi ya ce : '' ina burin ace  wannan gidan gaba daya a cike da zinari na ciyar da shi a tafarkin   Allah   ''   ,  sai  ya sake cewa:   '' kowa ya fadi burinsa'' sai wani mutumi ya sake cewa : '' ina fata a ce wannan gidan  a cike yake da lu'u-lu'u  , da Zubarjadi ,  da Jauhari na ciyar da shi a tafarkin Allah kuma na  yi sadaka da shi ,  sannan sai Umar ya ce  : '' ku fadi burinku ''  sai suka ce :  '' to, kai me kake gani ya Amiral muminin ''  sai Umar ya ce : ''  Ina fata  da ace wannan gidan a cike yake da mazaje  irin su Abu Ubaida Dan Jarrah  da Mu'azu Dan Jabal da Salim  Maula Abi Huzaifa  da  Huzaifatu Dan Yaman .
                      Kyakkyawan buri na daga cikin kofofi ne na lada mai girma , Abu Kabshata Al anmari ya rawaito daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata  a gare shi cewa  ya  ambaci wasu mazaje guda hudu:  (  Mutumin da Allah ya bashi dukiya da ilimi yana aiki da  ilimin sa  a cikin dukiyar sa yana ciyar da ita  bisa hakkin ta , da kuma mutumin da Allah ya bashi ilimi bai bashi dukiya ba ,  to, sai yana cewa ina ma da ina da irin wannan  ( dukiyar) sai na yi aiki da ita kamar yanda  yake aiki da shi    Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : '' Duk ladan su iri daya ne da kuma mutumin da Allah ya bashi dukiya amma bai bashi ilimi ba sai yana ta kwamacala a cikin dukiyar tasa  yana ciyar da ita ba a cikin hakkinta ba , da kuma mutumin da Allah bai bashi ilimi ba bai bashi dukiya ba  to amma yana cewa ina ma da ina da irin dukiyar da wane yake da shi    na yi irin aikin da yake yi da shi  ,  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya ce : ''  Dukan su biyu suna daidai a alhaki '').  Ibn Maja ne ya  rawaito shi.
             Burace-burace shi kadan shi ba yi da kima matukar bai hadu da aiki na kwarai ba tare kuma da kyakkyawar niyya na gaskiya  , da kuma bin koyarwan Annabi  tare  da kuma juriya   Allah  madaukakin sarki ya ce : (  Ku yi gaggawa zuwa ga neman gafara daga  Ubangijin ku) shi burace-burace wani nau'I ne na addu'a wanda ke tabbatuwa idan an amsa shi,  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (  Idan dayan ku zai yi adu'a  to, ya roka da babban masaki , domin Ubangijin shi  yake tambaya) Haithami ya rawaito
Albani ya ce marawaita hadisan amintattu ne kuma marawata ne na sahihi.
        Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (  idan dayan ku zai yi buri to, ya yi dubi zuwa ga abin da zai burata  ,  domin bai sani ba me za a rubuta mishi na daga burin nasa   . Ahmad ne ya  rawaito  da isnadi ingantacce .
     Kamar yan da mai hankali ba zai yi fatan   fitintinu ba ko haduwa da makiya , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce  : (   kar ku yi fatan haduwa da makiya , ku roki Allah  samun sauki  idan kun hadu da su to ku yi hakuri ).
            Mus'ab da Urwa da Abdullahi dan Zubair da Abdullahi dan Umar suka hadu a Hijir ,  sai suka ce kowa ya ambaci burinsa , sai Abdullahi dan Zubair ya ce  ni buri na in samu kalifanci , Urwa kuma ya ce : '' ni kuwa buri na a dauki ilimi daga gare ni , shi kuma Mus'ab sai ya ce na ga na rike Mulkin iraki na hada tsakanin Aisha 'yar Dalha da sukaina 'yar Husain , shi kuma Abdullahi Dan Umar ya ce ni kuma buri na in samu gafara , dukkan su kuma sai suka samu abin da suka nema,  ta iya yiwuwa Ibn Umar din ma an gafarta mishi .
       Umar dan Abdul'aziz Allah ya mishi  rahama  ya kasance yana da himma madaukakiya  wanda kuma ya cimmata da falalan Allah  , ana kuma fatan dayan ma ya cimmata   yana cewa ina da rayi mai yawan shauki ya yi shaukin Fadimatu 'yar Abdulmalik  kuma na aure ta,  na yi shaukin zama gwamna kuma na zama,  na yi shaukin kalifanci(shugaban kasa)  kuma na riske ta , kuma na bukaci Aljanna kuma ina  fatan na same ta in Allah mai girma da daukaka ya so.''
       Musulunci na kira zuwa ga yin fatan alheri da yada fata nagari da rayuwa, ba ya kira zuwa ga mutuwa da abu mara kyau, bai dacewa da shi munanan fata da neman mutuwa ko da fitinu sun tsananta, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Kada dayanku ya yi fatan mutuwa sakamakon wani cuta da ya same shi, in har ba makawa sai ya yi to ya ce : Ya Allah ka raya ni muddin rayuwar  ta kasance alheri a gare ni, kuma ka kashe ni idan mutuwa ta fi alheri gare ni) Buhari da Muslim ne suka rawaito.           
         Yin fata nagari na nuni ne ga kyautata zaton bawa  ga Ubangijinsa, ya zo cikin Hadisin Kudsi  : ''  Ni ina gun da bawa na ya zace ni, to , ya zaci  duk abin da ya so game da ni '' ibn Hibbana ya rawaito shi   a sahihin sa .  Wato ni  ina da ikon  na aikata da bawa na  duk abin da ya zaci zan aikata da shi . To idan bawa ya kyautata zato ga Ubangijin sa , sai hakan ya juyo  cikin  Burin sa sai ya zame madaukaki  a kima da kuma manufa .
            Mai hankali  yana saka burace –buracen sa ne tare da ,  jin ni'imar Allah a gare shi ba tare da ya yi hasada ga 'yan uwan sa ba , ko fatan abin hanun su ba  . Allah madaukakin sarki ya ce :   (kuma kada ku yi burin abin da Allah ya fifita shashenku da shi a kan sashe.)
Musulmi na da masaniyar cewa cin ma buri na hanun Allah ne shi kadansa, sabo da haka ba zai yi raki ko yayi bakin ciki ba sabo da rasa cin ma burinsa da ya ke fata ba,  Alheri na cikin zabin Allah   da kuma godiyan bawa ga Ubangijin sa a ko wani hali Allah madaukakin sarki ya ce :  (Akwai fatar  cewa ku ki wani abu alhali  shi ne mafi alheri   a gare ku kuma akwai fatar cewa kuna son wani abu alhali kuwa shi ne mafi sharri a gare ku ,  kuma   Allah ne  yake sani kuma ku ba ku sani ba ) .
          Iblisu shi ne tushen burace-burace mara kan gado , kuma ya yi alkawarin  ya nitsar da bayin Allah cikin kogin burace –burace na karya  na  jin dadin gaggawa ( duniya ) da kuma sa'ada mara tabbas  kamar yanda yake kawatawa dan Adam mummunan aikin shi sai ya gan shi kyakkyawa  Allah madaukakin sarki ya ce : ( Kuma wanda ya riki shaidan majibinci baicin Allah , to , hakika ya yi hasara bayyananniya yana yi musu alkawari  kuma yana sanya musu guri alhali  shaidan baya yi musu wa'adin komai face  rudi .)
                               Idan burace-buracen mutum ya gajarta bisa ga kyala-kyalan duniya,  ya zama babu na lahira  to hakika ya kauce hanya ya bar tafarki mikakke  Allah madaukakin sarki ya ce : (  wanda  ya kasance yana nufin duniya     sai mu gaggauta abin da muka ga  dama ga wanda muka ga dama  a cikin ta sannan mu sanya jahannama gare shi   a lahira  ya shige shi abin zargi , abin korewa.  wanda yake nufin lahira da aikin sa  ya yi kokari ya aikata aiki irin nata   a gare ta alhali shi yana mai bada gaskiya ga Ubangiji ,  to, wadancannin ka  aikin su ya kasance abin godewa) .
                                   Wanda burace-buracen sa ke nitso a kogin mafarkai yana fadake ko yana bacci ba tare da wani aiki ba, ya kewaye jikin sa da kasala , to ba zai tsinkaya ba sai kawalwainiya, an karbo daga Anas Dan Malik Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce   : (  Mai wayo shi ne wan da ya yi wa  kan sa hisabi ya yi kuma aiki domin bayan mutuwa ,  shi kuma gajiyayye shi ne wanda ransa ya bi abin da ya ke so ya yi kuma gurace-gurace  a wurin  Allah ).
                        Wanda ya bi hanyoyin da aka haramta domin cimma burace-buracen sa ta  hanyar komawa  zuwa ga matsafa ,  ko 'yan  siddabaru , to hakika ya zalunci kansa Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Duk wanda ya je wurin boka ko matsafi ya yarda da abinda ya ce to, hakika ya kafurce da abin da aka saukarwa  Muhammadu ). Dabarani ne ya rawaito Ibn Hajar kuma ya hassana isnadin sa.
                  HUDUBA TA BIYU
A  cikin kaburbura wanda ake fara rayuwan barzaku  akan samu gurace-gurace masu tsananin kunci  , burin mumini a kabarin sa shi ne kiyama ta tsaya , sabo da irin abin da ya ke gani kuma yake sauraro  na daga ni'ima da farin ciki ,  amma  kafuri burin sa kada alkiyama ta tsaya sabo da abin da yake gani da daga azaba mai tsanani .
         Mamaci na fatan sake dawowa duniya  don riskan abin da ya tsere mishi na daga da'a  ya samu ya yi sallah ko da raka'a biyu  ne  Annabi ya wuce wani kabari sai ya ce : ( Wane ne ma'aboci wannan kabari ? sai suka ce wane ne , sai ya ce  : '' raka'a biyu ya fi soyuwa ga wannan  (mutumin kabarin ) akan duk sauran abin duniya) .    
        Matattu na  fatan komowa  duniya domin su yi sadaka  kuma su ambaci Allah  ko da da tasbihi guda ne , ko  da hailala guda ne ,  Allah madaukakin sarki ya ce : (  KU CIYAR DAGA ABIN DA MUKA AZURTA MUKU  TUN GABANIN MUTUWA BA TA ZO MUKU BA YA FARA CEWA UBANGIJINA DON ME BA KA JINKIRTA MINI BA  ZUWA AJALI MAKUSANCI IN YI SADAKA DA ZAKKA , DON NA KASANCE DAGA CIKIN  SALIHAI ) .
Burin  mai radadi wanda ba makawa daga gare su  , shi ne kiran hasara   ga 'yan wuta ranar alkiyama don shi kafuri mai sabo  a yayin da ya karbi littafin shi da hanun  hagu , kuma ya ga makomarsa  sai ya yi fatan ina ma da ya  kasance turbaya  Allah  madaukakin sarki ya  ce : (  wancannin ka shi ne rana ta gaskiya   wanda ya ga dama  zai riki komawa zuwa ga Ubangijin sa  .   Lalle ne mu mun yi mu ku gargadin azaba makusanciya  ranar da mutum ke dubi zuwa ga abin da hannayen sa suka aikata , kuma kafuri ya ce kaito na da dai na zama turbaya  ).
                   Mafi daukakan matsayi  a tafiya na buri shi ne abin da 'yan aljanna za su samu   na ni'iman burace-burace ,  kuma Ubangijin su mai kyauta yana  mai kyauta a gare su kuma yana musu kari da karamcin sa,  mafi karancin guri da ma'abota sa'ada shi ne wanda zai shiga aljanna  a karshe ,  ta kammala kuma ta adonta a gare shi sai Ubangiji ya ce mishi fadi burin ka  sai bawan ya yi ta buri , har iya kurewar burin sa sai Allah ya ce wa bawan na shi an baka abinda ka burata da kwatankwacin shi guda goma tare da shi.
       Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (  Idan 'yan aljanna sun shiga aljanna sai Allah madukakin sarki ya ce shin ko kuna sha'awan  wani abu na muku kari sai su ce ya Ubangijin mu shin  yanzu akwai  abun da  ya fi alherin fiye da  abinda ka bamu  sai ya ce e, yarda na ya fi  girma ).  
          TA TIKE
         
     


الجمعة، 3 نوفمبر 2017

SATAR DUKIYA A MUSULUNCI

 HUDUBAR MASALLACIN ANNABI TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI14-2-1439AH NA SHAIK SALAH  BIN  MUHAMMAD AL- BUDAIR
Ya ku musulmai!  dukiya ganima ce mai tafiya , kuma dukkan wani dukiya na saya da sayarwa ana kwadayin shi ana haba-haba da shi ana kwallafa rai a kan shi   'yan fashi da barayi na sa ido gare shi.
                 Shi barawo fasiki yana likimo da sa ido, da kirdadon  lokacin gafala  a duk lokacin da masu dakon dukiya suka gafala  daga dukiyan su ;  sai ya  lallabo ya  awon gaba da ita    a boye  mai mummunan dabi'a mara kima , kaskantacce mai bushewan ido, mai yawan zalunci mai afkawa hakkin wanin sa  , ba mai tsallake gidaje  da  aka katange su  ya keta alfarmar abin da aka adana , ya balle kwado , ko ya yanke aljihu,  ya keta hannayen riguna ya saci dabinai da shuki da 'ya'yan itace   daga ma'adanan su , ba mai yin haka sai fasiki, masharraci , barawo maha'inci ,mayaudari kazantacce , tsinanne bisa  harshen Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
                             An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya ce :  ( Allah ya tsinewa  barawo ya saci  kwai a yanke hanun shi  ya  saci igiya  a yanke hanun shi ) Buhari da Muslim ne suka rawaito
                                 Barawo fasiki an mishi alkawarin narkon azaba da ukuba.  An karbo daga Jabir Allah ya kara yarda a gare shi a Hadisin Kusufi ya ce:  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (  Ba wani abu da aka alkawarta mu ku shi face na gan shi cikin wannan sallar tawa  ,  hakika an zo da wuta , wannan kuma a yayin da kuka ga na dan ja baya , tsoro na kada harshenta ta taba ni ,  har na ga a cikin ta wani ma'aboci sanda  yana jan hanjin sa a cikin wuta ,  ya kasance yana yiwa Alhazai sata da sandan shi   idan an ankara sai ya ce sandar ce ta makale da kayan , in an gafala  sai ya wuce da shi .) Muslim ne ya rawaito
         Hanun barawo hanu ne mai kwace mai ketare iyaka ,  shari'a ya wajabta a yanke shi a raba shi da ita domin tsoratarwa da gargadi da kuma ukuba domin bada kariya ga dukiya  da kayan albarkatu da kadarori ,  Allah mai girma da daukaka ya ce : (Kuma  Barawo da barauniya  sai ku yanke hannuwan su , sakamakon abin da suka aikata  a kan azaba  daga Allah kuma Allah mabuwayi ne mai hikima )
 An karbo daga Dan Umar Allah ya kara yarda a gare shi  shi da mahaifin shi  ya ce : Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata ya yanke hanu a kan  garkuwan  da bai wuce dirhami uku ba ,)  BUHARI DA MUSLIM NE SUKA RAWAITO SHI
                         Malamai suka ce game da hanun barawo ;  ya yin da ( Hanun) ya kasance amintacce  sai ya kasance yana da kima amma lokacin da ya yi ha'inci sai ya walakanta , wanin su yana cewa  ; izza ta amana  tana da ban mamaki na tsada  da kuma sauki  *** ha'inci kuma ya kaskanta to  ka fahimci hikimar mahalicci
 YA BAWAN ALLAH :
Ka kame daga kiyayyanka kar ka kasance bawa ga shaidaninka , domin alhurmar dan uwanka Musulmi  kamar alhurmar kanka ne    haka nan kuma alhurman dukiyan shi kamar   alhurmar dukiyar ka  ne  kuma alhurman gidan shi da iyalan shi  kamar alhurmar gidanka ne da iyalan ka ne ,  shin za ka yarda wani ya  yi ta'addanci da dukiyar ka da  iyalan ka ne  da gidan ka   da iyalan ka  kamar yanda ka yi ta'addanci zuwa ga wani ?  to idan har baka yarda da hakan ga dukiyar ka ba ,  to mutane ma  baza su yarda da hakan ga dukiyar su ba .
YA BAWAN ALLAH :
 Ka tuna ranar bijirowa kuma ranar  azaba ka tuna ranar da za ka tsaya a gaban Ubangijin ka mai girma mai daukaka ,   ka tuna ranar da dukiya ba zai yi amfani ba ko wadata ,  ka tuna ranar dauri  da sarka da  ankwa.
           YA KU MUSULMAI:
 Kada dayan ku ya dauki dukiya ko kayan wani ba tare da izinin shi ba kankani ne ko mai yawa ,  An karbo daga Abdullahi Dan Umar Allah ya kara masa yarda shi da mahaifin shi,  ya ce : Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (  Kada dayanku ya tatsi nonon akuyan  wani  ba tare da izinin shi ba ,  shin  dayan ku na so a zo wurin shansa  a fasa ma'adanan ruwan sa?    Sabo da nonon awakin na su na adana musu abincin su ne  to, kar dayan ku ya tatsi nonon   wani sai da iziznin shi .) BUHARI DA MUSLIM NE SUKA RAWAITO
                            An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : wata rana muna tare da Annabi tsira da amincin Allah su  tabbata a gare shi   a halin tafiya sai muka ga  rakuma  an tirka ta  da wasu  kayoyin itace sai muka  tafi zuwa gare ta don  mu kama ta ,  sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare  shi  ya kira mu , sai muka dawo zuwa gare shi , sai ya ce : '' wannan rakumar na  mutanen  wani gida ne  na musulmai  shi ne  abincin su,  yanzu zai muku dadi  ku koma zuwa  ga sulken  ku  ku same shi ba komai  a cikin shi an tafi da shi?  shin  kuna ganin  hakan adalci ne ?  sai suka ce : '' A'a''  sai ya ce : '' to, ai shi ma wannan kamar haka ne .)  AHMAD NE DA IBNU MAJA' suka  rawaito shi
                    An karbo daga Abu Humaid Assa'idi  ya ce:  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (  Kada dayan ku ya dauki sandan dan uwan  shi ba tare da  yardan shi ba ). Wannan sabo da tsananin abin da Annabi ya haramta ne  na dukiyan musulmi bisa ga musulmi ) Ahmad ne da Ibn Hibban ya rawaito shi
                 To idan wannan akan kananan abubuwa ne wanda   basu taka kara sun karya ba  a gun ma'abotan shi kamar sanda  da makamantar ta,  to abin da ke sama da wannan shi ya fi  dacewa a yi gargadi a kan su .
                Duk wanda ya kwace kasan wanin sa bisa karfi ba tare da hakki ba , ko ya riki taki  a  na daga hanyan musulmi   ko zira'i ko kuma ya taba cikin dukiyar al'uma ba tare da hakki ba , to ya kai kansa ne  ga azaba mai tsanani  da kuma  ukuba mai karfi . An karbo daga Hakam dan Haris Assulami  Allah ya yarda da shi ya ce : Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata  a gare shi ya ce : (  Duk wanda ya dauki taki a hanyar musulmai zai zo ranar alkiyama yana dauke da shi , daga kassai guda bakwai ) Abu ya'ala ne ya rawaito shi
               An karbo daga Abu Humaid assa'idi ya ce : Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (   Wallahi dayan ku ba zai riki wani abu ba na hakkin wani ba tare da izinin shi ba face ya  hadu da Allah yana mai dauke da wannan abun  ranar alkiyama   to lalle zan san dayan ku da zai hadu da Allah yana dauke da rakumi yana  kuka ko saniya na kara  , ko akuya na kara ,   sannan ya daga hanun shi har a ka ga hasken hamatan shi , yana cewa ya Allah na isar da sako )  BUHARI NE YA RAWAITO
              An karbo daga Abu malik Al-Ashja'I Allah ya kara yarda  a gare shi ya ce :  Annabi  tsira da amincin Allah su tabbbata a gare shi ya ce : (     Mafi girman  sata   a wurin Allah shi ne satan zira'i  na kasa ,  za ka samu mutum biyu ne makwabta  a kasa ko a gida  ,  sai daya ya yanka zira'I  guda na daga  na dan'uwan shi  idan ya yanka za a nade shi da kassai bakawai ranar alkiyama )
           Idan barawo ya tuba daga sata da aikata laifi , to ,  Allah ya karbi tuban shi na abin da ke tsakaninsa da shi ,  amma dukiyan mutane dole ne ya mayar zuwa gare su , idan abin da a ka satan na nan  to ya  wajaba a maida shi zuwa ga mai shi ko kuma a bada wani abu da ke a madadin sa ko farashin sa da  yake dai-dai da shi , ko kuma a nemi yafiya daga gare shi.
  Allah ya kare ni da ku daga fadawa  zuwa ga cin abin da yake mai halakarwa ,  da abubuwa masu shigowa kazantattu  da kuma dukiyan haramun  ,  Allah ya kare ni da ku ya wadatar da mu da halal , domin shi mai kyauta ne mai karamci , ina neman gafarar Allah  kuma ku nemi gafarar sa  domin shi ya kasance mai yawan gafara ne   ga  masu komawa gare shi .
          HUDUBA TA BIYU
YA KU MUSULMAI :
       Wanda ya shiga daga cikin mu  - ya ku jama'ar Masulmai -  garin wadanda ba musulmai ba  da  alkawari da aminci, wato wannan biza da ake bada wa a gare shi don ya samu daman shiga  garin su to,  ya haramta ya ha'ince su , ko ya musu sata ko ya ketare iyaka gare su  ga amincin su da  rayukan su , da mutuncin su da kadarorin su , wanda ya saci wani abu na su to ya wajaba ya mayarwa masu shi sabo da dukiya ne katangagge .
                   Sabo da haka ne yayin da Annabi ya yi hijira zuwa  ga madina  ya umarci Aliyu da ya maida  ajiyan Quraishawa da ke gunsa , Ibn Sa'ad ya kawo a cikin littafin shi ADDABAKAT AL KUBRA  : cewa Aliyu dan Abi dalib Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : Yayin da Manzon Allah ya fita;  zuwa hijira  ya umarce ni da na tsaya bayan tafiyar sa don na sauke  ajiyan mutane da ke gun sa , Annabi ya zauna  a  Makka har shekaru sha uku tare da shi akwai musulmai bai taba yiwa wani umarni ba,   da ya kwace dukiyar mutane ko  ya je ya zubar da jini , ko ya keta mutunci , sannan Annabi ya yi hijira ya bar musulmai suna cikin rauni ko suna cikin buya a makka  bai  bada izini ga dayan su ba ya yi wani abu makamancin haka .
 Musulunci na umarni da cika alkawura da gaskiya wurin mu'amala , kuma yana hani da ha'inci da cin amana  da gaba da kiyayya.
  Allah ya sanya ni da ku cikin shiryayyu wadanda aka shiryar, ya kare mu daga hanyar masu ketare iyaka  batattu ,  ku yi salati da aminci bisa ga  Ahmad mai shiryarwa mai ceto ga bayi gaba daya .
 Ta tike