HUDUBAR JUMA'A A
MASALLACIN ANNABI NA SHAIK
HUSAINI AL-ASSHAIKH 30-1-1439 AH
HUDUBAR FARKO
Na daga cikin abu mafi tsada a gun masu
hankali akwai son garin da aka haife su cikinta suka rayu suka ci daga albarkatun
da Allah ya sanya cikinta.
Lalle wannan wani abu
ne da shariar musulunci ta tabbatar da ita, kuma ta iyakance ta da kulawa da
wasu hakkoki da wajibabbu don kulawa da
maslahar addini da duniya gaba daya.
Hakika son kasa da rai
abu ne da ke hade kamar yadda kur'ani ya siffanta su, Allah Madaukakin sarki ya
ce : (Kuma da dai lalle mu mun wajabta musu cewa "Ku kashe kanku ko ku
fita daga gidajenku" da ba za su aikata shi ba sai kadan daga gare su)
Kuma Allah Madaukakin
sarki yace : (Allah ba ya hana ku daga wadan da basu yake ku ba sabo da addini basu fitar da ku daga gidajen ku ba ga ku
kyautata musu ku yi musu adalci.)
Ibnul Arabi ya na magana kan kissar Musa Amincin Allah ya tabbata a gare
shi da komowa ga iyalansa sai yace :
" A dawo wa ga kasa akwai wabcewa daga gumurzu da tsallake rijiya da
baya da samun kwanciyan hankali.
Batun son kasa da
kaunar gida ya sa Annabi ke cewa Makka
yayin kaurarsa a halin bakin ciki
da nuna tsananin kauna :(Abin mamaki da dadin ka (garin Makka) da
soyuwarka gare ni! ba don mutanen garin
sun kore ni ba da ba zan zauna a waninka ba.) Tirmizi ne ya rawaito.
Haka kuma yayin da
Allah ya nufe shi da kauratowa , ya wayi gari Madina ya zama garinsa wurin
rayuwar sa sakonsa ya haskaka garin sai
ya ce : (Ya Allah ka sanya mana kaunar Madina kamar yadda ka sanya kaunar Makka
a gare mu ko fiye da haka.)Bukhari ne ya rawaito.
A cikin siffanta
zababbun halittu bayan Manzanni Allah
Madaukakin Sarki ya bayyana halin sahabbai da suka yi hijira daga garin Makka
zuwa Madina sai ya ce : ( Ku yi mamaki ) Ga matalauta masu hijira
wadanda aka fitar daga gidajensu da dukiyoyinsu, suna neman falala daga Allah
da yardarsa, kuma suna taimakon Allah da Manzonsa, wadannan su ne masu
gaskiya.)
Ya ku Musulmi!
Na daga cikin ni'ima mafi girma ga bawa
samun zaman lafiya a garinsa cikin aminci tare da iyalansa, yana mai bautawa
Ubangijinsa, ya na biyayya ga Mahaliccinsa, Manzon Allah tsira da amincin Allah
su tabbata a gare shi ya ce : ("Wanda ya wayi-gari a cikinku da aminci
ga ransa, ko a cikin jama'arsa da iyalansa da dukiyarsa, ya wayi-gari da lafiya
a cikin jikinsa, ya wayi-gari a wurinsa akwai abincin yininsa, to kamar an hada
masa duniya ne gabadayanta".
Ya ku Musulmai ! Lalle son kasa a musulunci na
nufin kiyaye mutuncin kasar da kyawawan dabiu da tsarkakan ginshikanta, wato
yana nufin taimakekeniya gurin janyo dukkan alheri da gyaran kasa da mutanenta,
da tunkude dukkan wata barna da wahala ga kasar da mazaunanta, Allah Madaukakin
sarki ya ce : (Ku ma ku taimaki juna a kan aikin kwarai da takawa).
Lalle son kasa na nufin
ko wani daidaiku ya rayu da 'yan uwansa cikin kauna da soyayya da tausayi da
jinkai, don amsa kiran Allah madaukaki (Lalle
muminai 'yan uwan juna ne) da kuma fadin Allah mai tsarki (kuma mumunai
maza da mumunai mata sashensu majibincin sashe ne , suna umurni da alheri
kuma suna hani daga abin da ba a so kuma suna tsayar da salla kuma suna
bayar da zakka kuma suna da'a ga Allah da manzonsa wadannan Allah zai yi musu
rahama .) kuma manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a
gareshi ya ce :( Misalin Muminai cikin
kaunar juna, da tausayin juna da tausasawa juna, kamar Misalin jiki daya ne.
Idan wani sashin jiki babu lafiya sai sauran jikin su kama zazzabi da kasa
barci).
Lalle kauna ne da ke sanya wasiya da biyayya da tsoron Allah da yin nasiha da juna cikin abin da akwai alheri ga kasa
da raya ta. Allah Madaukakin sarki ya ce : ( Lalle mutum na cikin hasara.
Sai wadanda suka yi imani kuma suka yi aiki na kwarai kuma suka yi suka yi wa
juna wasiyya da bin gaskiya, kuma suka yi wasiya wa juna da yin hakuri)
Manzon Allah tsira
da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Addini nasiha ce, ya fade ta
har sau uku, sai muka ce: ga wa nene ya Manzon Allah? Sai yace : Nasiha ga
Allah da Manzonsa da littafinsa da jagorin musulmai da sauran jamaa)
Lalle shanin son kasa
abu ne da ke sanya bada kariya ga kasar da abubuwan cikinta masu kima, kowa
gwargwadon karfinsa da yadda zai iya kuma gwargwadon nauyin da ke kansa. Zuwa ga wannan ne alkur'ani ke nu ni a fadin sa Allah mabuwayi da daukaka:
( Sai suka ce mai zai hana mu yi yaki a tafarkin Allah a halin an fitar da
mu da 'yayanmu daga gidajenmu ?)
Kuma zuwa gare shi ne
fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi na cewa : ( Duk wanda aka kashe shi yana kokarin kare dukiyar
shi to, shi shahidi ne)
Wannan shi ne son kasa wanda ke lizimtawa
daidaikun al'uman da su shirya su tari
duk wani shirin da zai taba dukiyar kasa
da maslahohinta na addini da na duniya ,
ya kuma sosa amincinta da zaman lafiyanta , Manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Duk wanda ya ga abin ki , to,
ya canza shi da hanunsa , to, idan ba zai iya ba to, da harshen sa , to, idan bai iya ba da zuciyar sa ).
Ba makawa
yana daga cikin abubuwa da aka ki
akwai shirya makirci don taba akidar kasar da amincin ta
da zaman lafiyanta ko kuma a taba
dukiyanta da albarkatunta ,
son da Musulmi ya ke
yiwa kasan sa yana sanya shi ya lizimci kiyaye dukkan wani kadarorin kasar sa
da albarkatu kuma ya yi kokari domin samun aminci cikin abubuwan da yake samu
kamar yanda ya ke son abubuwa da yake na maslahar kansa, da amfanin sa na karan
kansa , :Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :( Imanin dayanku ba zai cika ba har sai ya so
wa dan uwan sa abinda ya so wa kansa )
YA 'YAN UWA MUSULMAI :
Yana daga cikin abinda
yake nuna kauna ga kasa a musulunci ko wani daidaiku a cikin mutanen ta su kame
daga cutar da ita , da kuma mazaunanta ,
ya zo a cikin sunna ingancecciya na daga cikin hakkokin hanya a
gusar da kazanta daga gare ta, ya zo a hadisai ingantattu daga
Manzon Allah tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi game da sanya kazanta
a farfajiyan mutane ko kan hanya ko wurin harkokin su, to Musulmi a na bukatar da ya
kasance a cikin garin sa da iyalan
sa kamar yanda Annabi ya yi nusar a
fadin sa :( Musulmi shi ne wanda musulmai suka kubuta
daga sharrin harshen sa da na hanunsa)
YA KU MUSULMAI:
Na
daga cikin hakkoki na kasa da mutanen ta
a kan daidaiku, da su kiyaye daga
ha'intar kasan da kuma 'ya'yanta , da kuma ita al'umar kanta , lallai na
daga cikin mafi munin sifa na
ha'inci a kwai ribatar dama da ma'aikata
su ke yi da masu matsayi don maslahan kan su , su fifita maslahar kan su akan
maslahar al'uma , na daga cikin mafi munin barna akwai barnatar da dukiya ,
wanda shari'a ta zo da hani mai karfi akan hakan
Allah madaukakin sarki ya ce :( Duk wanda
ya ci gululi zai je da abinda ya ci na
gululin a ranar kiyama )
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a
gare shi ya ce : ( Lalle wasu mutane
suna kutsawa a cikin dukiyar Allah ba tare da hakki ba , to, su na da
wuta a ranar alkiyama )
YA KU MUSULMAI:
Daga cikin hakkokin kasa a kanmu akwai
taimakekeniya tare da jagorori da Allah
ya basu rikon wannan kasa , tare da gudanar da ita kasar, a yi
gaskiya a gare su a bayyane da boye ,
kuma mu san cewa yi musu biyayya a abin da ba sabon Allah ba wajibi ne
daga wajibabbu na shari'a. Kuma mu yi kwadayin hada kayin al'umarta da dunkulewar
ta , ko wanne ya zama a shirye yake don kare kasar sa daga dukkan wani makirci da ake shiryawa kasa , da kuma
dukkan hanyoyi da za su iya taba amincin ta da kuma amanarta .
HUDUBA TA BIYU
Tunda ya tabbata cewa
son kasa abu ne na dabi'a wacce shari'a ta tabbatar da shi to ta yaya
kuma kasar da ta tattaro masallatai biyu masu alfarma a cikin ta da kuma dakuna masu daraja lalle wannan shi ne kasa mai tsarki wanda a
ka gina ta akan musulunci, a manhajanta da
kuma kundin tsarin mulkin ta bisa akida na tauhidi ciki da waje , alkalan ta na
hukunci na shari'a , kotunan ta na
hukunci da shari'a mai tsarki , gari ne da ma'abotanta sun rayu a kan sunna da girmamata , da kuma kore
bidi'a da 'yan kanzaginta .
To ya wajaba ga mutanen
ta a hali suna samun irin wadannan ni'ima mai yawa da su yi taimakekeniya bisa ga aminci da zaman lafiya , kuma su yi
kwanton dukkan wani mai son rusa kasa , ko kuma son mai da
dabi'unta irin na yammacin turai musamman a irin wannan mawuyacin
yanayi , wanda wata guguwa ke
girgiza duniya gaba daya .
Ku kiyaye Allah ya kula
ku bisa tabbatuwa cikin aminci, ya kuma bawa garin ku kariya , daga wadannan fitintinu masu yawa.
Ku kiyaye dukkan wasu kiraye –kiraye na sharri
da barna da kuma hanyoyin da zai kawo rarrabuwar kai da raba
tsakani .
Ku
kiyaye ya matasa na wannan gari bisa
abin da wannan gari ta saba, na tafiya a kan manhaji na sunna bayyananne
tacecce, tsarkakekken da baya ketare iyaka ko wuce gona da iri , ba a san shi da wani manhaji ba na bidi'a ,
ko wani fandararren tunani , na daga cikin abin da zai sabawa abin da aka gina wannan gari a kai na kyawawan dabi'u na Musulunci , da halaye na
shari'a , da kuma manhaja da mutane suka rayu a kai tsintsiya madaurin ki daya
,kuna masu taimakekeniya akan dukkan
wani alheri , masu haduwa akan abu mai
amfani ga maslaha ga kasa da kuma bayi ,
irin taimakekeniya na gaskiya tare da iklasi ga
jagororin ta . Don cimma kyawawan manufofi da ake fata , kuma a tunkude
duk barna da ake hasashe, kar ku canza abinda Allah ya ni'imta ku da shi har Allah
ya canza muku yanayin ku , kamar yanda Allah madaukakin sarki ya ce : ( Kuma Allah ya buga misali wata Alkarya ta
kasance amintacciya natsatssiya
arzikinta yana je mata a wadace daga ko wani wuri sai ta kafurta da ni'imomin
Allah , sabo da haka Allah ya dandana mata tufafin yunwa da tsoro sabo da abin
da suka kasance suna sana'antawa ).