Hudubar Masallacin Annabi na 27 /10/ 1438 AH na shaik Husain bin Abdul'aziz
Al- As shaikh
Hutu da kwanciyan
hankali da natsuwa da walwala abin nema
ne ga ko wani dan adam, shine abin da mutun ke kokarin cimma, ya ke kuma
gasa wurin neman su , ku saurara! lalle al'amarin dukk iya kokarin da mutun
yayi ta ko wace hanya na kyala-k yalen
duniya da kuma sha'we sha'wenta don ya
kai ga wannan ba zai kai gare ta ba.
Lalle dalili na hakika na samun
daddadan rayuwa ta hanyoyi daban daban yana boye a cikin abin da Allah
ya fada a fadinsa : (wanda
ya yi aiki na kawarai na daga na miji ko mace
yana mumini to zamu raya shi rayuwa na jin dadi kuma mu sakanya mishi da mafi kyan abin da
suka kasance suna aikatawa )
Lalle shine imani da
Allah Mai girma da daukaka, wanda ya kumshi mika wuya ga Allah da biyayya na karshe wanda babu shirka a ciki,
wanda ya ke sanya mutun ya samu sa'ida da walwala na ciki da na
waje, ya samu natsuwa da walwala ta zuci
koda wani abu ya same shi na cuta da tsanani, to zuciyarsa tana cikin ni'ma kuma tana cikin annashuwa da
fara' a da farin ciki irin na imani da Allah da sanin Allah da kaunarsa da kuma
komawa zuwa gare shi da dogaro a gare shi
Allah madaukakin sarki ya ce : (wanda ya yi imani da Allah to Allah
zai shiryar da zuciyarsa )
Manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :( Mamaki na ke yi da al'amarin
mumini, al'amarin shi duka alheri ne, idan cuta ta same shi sai ya yi hakuri
hakan sai ya zama alheri a gareshi , idan kuma yalwa ta same shi sai ya gode wa
Allah hakan sai ya zama alheri a gare shi ) Muslim ne ya rawaito
Lalle wannan shi ne imani wanda ke sa mutun ya yi murna da abin da aka bashi a wannan rayuwa ta duniya,
yana mai yarda da abin da Allah azurta shi da shi, yana mai gamsuwa da abin da
Allah ya ba shi.
Manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Duk wanda ya wayi gari cikin ku
yana mai aminci a iyalan sa da lafiya a jikinsa kuma yana da abin da zai
ci na wuninsa to kai ka ce an tattaro
mishi duniya ne gaba dayanta ) Tirmizi da Ibnu Majah ne suka rawaito.
Manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce : ( Hakika ya rabauta wanda ya mika
wuya kuma ya wadatu da abin da Allah ya ba shi) muslim ne ya rawaito
Daya daga cikin salihan
bayi yake cewa : ( Wallahi mu muna cikin
sa'adan da da ace 'ya'yan sarakuna sun san irin wannan, da sun yake mu da
takuba wurin nemanta) wani kuma ya ke
cewa : (wasu lokuta kan zo min, wanda na
ke cewa idan dai 'yan aljanna suna cikinta
to lalle suna cikin jin dadi .
Ya ku musulmai!
A cikin zukata akwai tarwatsa
ba abin da ke hade ta sai fiskantar Allah Madaukakin sarki, haka nan akwai kewa
ba abin da ke debe ta sai shagaltuwa da Allah. Haka kuma akwai bacin rai ba
abin da ke kauda shi sai farin ciki da tauhidinsa da sanins,a sha'ninsa ya daukaka,
da gaskiyan yi mishi kuma biyayya a cikinta akwai wutar hasara da ta ke ci babu
abinda ya ke kasheta sai yarda da umarninsa da haninsa da hukuncinsa da
kaddaransa, kuma a cikinta akwai talaucin da babu abin da ke tunkude ta sai sonsa da
komawa zuwa gareshi da dimantan ambatonsa .
Allah Madaukakin sarki
ya ce (To da ambaton Allah zukata su ke natsuwa.)
Manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce :(ya bilal ka sanya mana hutu ta hanyar ita(sallah) . Abu Dawuda ne ya rawaito da
isnadi sahihi
Manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (kuma an sanya min sanyin idona a sallah ) Nasa'i ne ya
rawaito .
To duk wanda yake son
sa'ada mai dimanta da cikakkiyan jin
dadi da karshe kyakyawa to ya wajaba a
gare shi a bayyane da boye ya saisaita
kanshi da bin umarnin Allah subhanahu wa ta'la da kuma rayuwa cikin yi wa Allah
biyayya sh'aninsa ya daukaka Allah subhanahu wa ta'ala ya ce:(lalle ne masu
da'a ga Allah dahir suna cikin ni'ima).
Ka kiyaye ya kai
musulmi sabawa Allah karshenta hasara ce da tabewa, Ibnul kayyim yake cewa
:((lallai bawa idan ya sabawa Allah sai Allah ya sallada mishi mayaka guda biyu
ba zasu rabu da shi ba har sai ya tuba zuwa ga Allah na farkon (bakin ciki)na
biyu (bacin rai) Allah madaukakin sarki yace (kuma duk wanda ya bijire daga ambato na (Alkur 'ani) to lallai ne rayuwa mai
kunci ta tabbata agareshi )
To yakai musulmi ka
damfara zuciyarka ga Allah , kuma ka kyautata zato ga Ubangijinka, ka kasance
bawa tsarkakakke mai takawa zaka kasance cikin walwala da dadin rai.
(Shin fa wanda Allah
ya bude kirjinsa domin musulunci sa'annan shi yana kan haske daga Ubangijinsa
(zai zama kamar waninsa?)
Allah ya ce : (
Domin haka wanda Allah ya yi nufin ya shiryar da shi sai ya bude kirjinsa domin
musulunci, kuma wanda ya yi nufin ya batar da shi, sai ya sanya kirjinsa mai
kunci matsattse kamar dai yana haurawa ne a cikin sama
Huduba ta biyu
Katangagge shine wanda aka katange zuciyarsa daga
Ubangijinsa , kamamme shi ne wanda son zuciyarsa ta kame shi, mai bakin ciki
shi ne wanda ya jefa kansa cikin sabo, mai bacin rai shi ne wanda ya dulmuyar
da ransa cikin duhun halaka na saba wa sharia. Wasu Arifai suka ce : Miskinan
duniya sun fita daga cikinta basu dandani abu mafi dadi ba a cikinta, sai suka
ce : wani abu ne ? sai yace : Kaunar Allah da debe kewa tare da shi da kwadayin
haduwa da shi da fiskantarsa da bijirewa duk wani abu koma bayansa.
Allah Madaukakin sarki ya ce : ( Lalle ne,
wadanda suka ce Ubangijinmu Allah ne, sa'anan suka daidaitu,to babu wani tsoro
a kansu , kuma ba za su yi bakin ciki.)
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق