Hudubar masallacin
Annabi 6-shawwal 1438AH na sheikh
Abdullah bin Abdurrahman Albuaijan
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Alllah, wanda da ni'marsa ce
ayyuka na kwarai ke kammala, na shaida
babu abin bawtawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya,
Ubangijin kasa da sammai na shaida lalle Annabin mu Muhammadu bawansa ne kuma
manzonsane, shine mafi darajan wadanda su ka yi gaggawa zuwa ga alkin alheri,
Allah ka yi dadin tsira da aminci da albarka a
gare shi da iyalansa da sahabbansa masu tsoron Allah da ayyuka na kwarai.
Baya haka:
lalle mafi alherin
zance shine littafin Allah kuma mafi alherin koyarwa shine koyarwan Annabi muhammadu
tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, mafi sharrin al'amura shine fararrunsu dukkan
bidi' a kuma bata ce dukkan bata kuma yana wuta .
ya ku bayin Allah ina
muku wasiyya da ni kaina da tsoron Allah Mabuwayi da daukaka domin ita ce
wasiyyan Allah ga mutanen farko da na karshe (kuma lalle ne hakika mun yi
wasiyya daga wanda aka baiwa littafi a gabaninku da ku cewa kubi Allah da takawa)
ya jama'r musulmi:
cikin shudewan
zamanunnuka akwai abin lura mafi girma haka cikin jujjuyawar ranaku akwai gargadi mafi
girma (lalle ne a cikin sabawan dare da yini da abin da Allah ya halitta a cikin
sammai da kasa akwai ayoyi ga mutane wadanda su ke yin takawa).
Ya ku bayin Allah! hakika munyi bankwana da wata mai girma kamin
wasu yan kawana ki kadan kum wani lokaci ne mai girma daga cikin lokutan alheri
da albarka ya kasance yana cike da riba da kyawtuttuka da gafara da rahama
wanda ke ratsa zuciya ga idanuwa kuma na zubar da hawaye ga zukata sun rusunawa Ubangijinsu kuma suna cikin tsoro, da
gabbai sun himmatu suna fiskantan Allah da wurin ambaton shi kuma ana raya
masallatai da ambaton Allah da karatun alkura'ni ga natsuwa ta sauko kuma
rahama ta lullube.
Allah ya karrama mu da
azumi a wuninsa da abin da ya sawwaka na
tsayuwa a darensa, ya kuma datar
da mu a cikinsa da da yawa daga nau'uka
na da'a da ibadoji da zikiri da adduao'i da sadakoki, to dukkan yabo da
godiya da baiwa na Allah ne to muna godiya a gare shi bisa wadannan ni'momi
to ya Allah ka karba .
Ba wani abu bane face
wasu ranaku kididdigaggu da awowi iyakantattu da wasu 'yan lokuta da ke shudewa hakika gajiyansu da
wahalansu sun tafi saura ladarsu da ribarsu in Allah ya yarda .
Watan ramadana ya kare
kuma ya nade tabarmarsa wanda ya rabauta a cikinsa ya rabauta wanda aka
haramtawa kuma an haramta mishi Allah sarki wanene aka karbi aikin shi a cikin
mu yi mishi murna! kuma wanene aka maida mishi mu mishi jaje! .
Ya ku bayin Allah
Ibada na da tasiri a
halayen ma'abotanta Allah madaukakin sarki ya ce:
(lalle salla tana hani ga alfahasha da
munkari ).
Na daga cikin alamomin
karban ayyuka akawai gyaruwan halaye daga wani halin zuwa halin da yafi kyau (lalle da'a na shiryarwa zuwa ga aljanna )
Ta daya bangaren kuma
na daga cikin alamomin tsiya da kuma
rashin karban aiki akwai komawa baya zuwa ga munanan ayyuka bayan shudewan
ramadana da canjawan hali zuwa mafi muni
domin shi sabo sashinsa na jan sashi (madalla da aikata kyakkyawa bayan mummuna
don zata gogeta wanda yafi kyau kuma shine mutum ya aikata kyakkyawa bayan kyakyawa, mafi muni kuma aikata mummuna bayan kyakkyawa
domin zata shafe albarkanta kuma ta gogeta . zunubi guda daya bayan tuba yafi
muni akan zunubai da yawa kafin tuba,
juyawa zuwa ga munanan halaye yafi wuyan sha'ani akan cuta watakila ma ta halakar, roki
Allah tabbatuwa akan da'a har zuwa mutuwa , kuma mu nemi tsarinsa daga juyawan zukata da kuma lalacewa bayan gyaruwa, abin mamaki
da dabbancin kaskancin sabo bayan daukaka irin na da'a, abin mamaki kuma da
abkawa cikin talaucin kwadayi bayan wadatan zuci).
Ya ku musulmai
Lalle hanyoyin alheri
na da yawa ina masu binsa haka kuma kofofin nasa a bude suke ina masu
shigansu lalle gaskiya a bayyane take ba
mai baude wa daga gare ta sai halakakku,
to ku yi riko ya ku bayin Allah da kaso dagsa dukkan biyayya (ya ku wadanda suka yi imani ku yi rukui
kuma ku yi sujjada kuma ku bautawa ubangijinku kuma ku aikata alheri saboda ku
samu babban rabo )
Kuma lalle hakuri a kan
dimantan da'a da tsayuwa a kan tafarki da tabbatuwa na daga cikin mafi girman
ayyukan da'a, tabbatuwa da dogewa dalili ne na ikhlasi da
karban aiki , (mafi soyuwan ayyuka a wurin Allah su ne wadanda aka dawwama
a kansu )
(aikin manzon Allah
ya kasance dimamme )
To ku tabbatu akan da'a, ku tabbatu a kan da'a kuma
ku tsayu a kan biyayya, to ku tsayu a kan biyayya kuma ku dawwama a kan
ayyuka .
Ya ku bayin Allah !
Ku yi kwadayin karban
ayyuka kuma ku kiyayi talauci da gushewa ,lalle mafi girman hasara shine ka bawa waninka mafi girman abinda ka
samu na daga lada, to wannan shi ne talauci na gaskiya.
An karbo daga Abu Huraira
Allah ya kara masa yarda ya ce manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a
gare shi ya ce :( shin kun san wanene matalauci ? sai suka ce matalauci shine wanda bai da dirhami
ko kaya sai ya ce: matalauci daga alumma ta
shine wanda zai zo ranar alkiyama da salla da azumi da zakka, ya zo ya
zagi wannan kuma ya yi wa wannan kazafi kuma ya ci dukiyan wannan kuma ya zubar
da jinin wannan kuma ya daki wannan sai
abawa wannan daga ayyukan shi
kyawawa wannan ma daga ayyukan shi
kyawawa in ayyukansa kyawawa sun kare kafin a gama masa hisabi Sai a dauki
zunuban wannan sai a dora mishi sai a hurgashi cikin wuta )muslim ne ya
rawaito
Bayin Allah!
Kuma rena sabon Allah
da bushewar ido wurin keta alhurmarsa na daga cikin sababi mafi girma na
tsiyacewa da hasara da bata da tabewa,
an karbo daga Sauban Allah ya kara
yarda a gare shi cewa Manzon Allah tsira
da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Lallai zan san wasu mutane
acikin al'umata za su zo ranar alkiyama da ayuka misalin duwatsun Tihama
farare sai Allah ya maishe su tarwatsatssen kura , Sauban ya ce: ya Manzon Allah siffanta mana su
don kar mu kasance cikin su a halin ba mu sani ba , sai ya ce
ai su dinnan lalle 'yan uwan ku ne
kuma wadanda fatar ku iri daya, kuma suna riko cikin dare kamar yadda ku ke riko, sai dai su din wasu mutane ne da idan sun
kebanta da ababen da Allah ya haramta sai su keta alfarmarsa, sun kasance suna azumi kuma suna salla kuma
suna rikan wani lokaci cikin dare sai
dai basa murakabar Allah a lokacin
yalwa, to idan sun kebanta da abin da
Allah ya haramta sai su keta
alfarmarsu sai Allah ya ruguza ayukan su
( Kuma abin da ba su kasance suna zato ba daga Allah ya bayyana a gare su) .
Idan ka kadaita a wani zamanin wata rana to kar ka ce *
Na kadaita sai dai ka ce ina da mai mini murakaba
Kada ka zaci Allah
yana gafala na wani lokaci *
ko kuma
abin da ake boyewa yana fakuwa a gare shi.
ku saurara ku tsayu akan da'a wa Ubangijinku ku amsa kiransa ku bi umarnin sa a dukkan
matakan rayuwanku za ku samu rabauta da ganima da walwala da tsira (
Lalle ne wadan da suka ce '' Ubangijin mu Allah ne'' sa'annan
suka daidaitu to, babu wani tsoro a kan su , kuma baza su yi bakin ciki ba . to wadannan su ne ma'abota aljanna suna masu
dauwama a cikinta sakayyan abin da suka kasance suna aikatawa ).
HUDUBA NA BIYU
Lalle dukkan yabo da
godiya sun tabata ga Allah muna gode
mishi kuma muna neman taimakonsa , muna neman shiriyarsa , kuma muna neman
gafararsa , muna tuba zuwa gare shi , muna neman tsarin Allah daga kawunan mu
da kuma munanan ayukanmu wanda Allah ya
shiryar da shi ba mai batar da shi wanda
kuma Allah ya batar da shi babu mai
shiryar da shi , na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi
kadai yake bashi da abokin tarayya , na
shaida Annabi Muhammadu bawansa ne kuma
Manzon sa ne , tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa da
sahabansa , da wadanda suka bisu da kyautatawa har zuwa
ranar sakayya da aminci tabbatacce mai yawa.
Ya ku Musulmai
ku ji tsoron Allah ku gaggauta
ribatan ayukanku kafin karewar rayuwarku ku tabbatar da maganganun ku ta hanyar
ayukan ku domin lalle hakika rayuwar mutum
shi ne abinda ya tafiyar da shi a
cikin da'a wa Allah ,
lalle mai wayo shi ne wanda ya yi
hisabi da kansa ya yi aiki don bayan
mutuwarsa shi kuma wanda ya gajiya shi ne wanda ya bi son ran shi ya yi ta gurace
– gurace a wurin Allah .
Ya ku bayin Allah watanni dukkan su lokuta ne na ibada ko da sun
saba a wurin falala. rayuwa
dukkanin ta dama ce ta aiki da kuma da'a , ko wanne yana wayan gari yana mai saida kansa, wani ya 'yanta ta wani
kuma ya halakata , sannan kowa ana
saukake mishi abinda a ka halicce shi don shi .
To ya wanda ya cika a ramadana ya kyautata bisa mafi kyawun kyautatawa , maganganun shi
da ayukan shi suka kawata, to ka tabbatu kada ka canza a bayan shi a
cikin shauwal.
Ya wanda mutane suka tsere maka aka barka a baya mafi yawan rayuwa ya
tafi sai zanyi , bai yin ba , dama ta
Ramadan ta tsere maka baka ci riba ba , taho
, to, kofofin basu gushe ba suna bude ,
kuma tuba ana karbanta Allah
madaukakin sarki ya ce :( Ka ce , (Allah ya ce) '' ya ku bayi Na wadan da suka yi barna akan rayukansu ! kada ku yanke kauna daga rahamar Allah . Lallai Allah na gafarta
zunubai gaba daya . Lallai shi ,
shi ne mai gafara , mai jin kai .
Ya ku
jama'ar Musulmai :
Lallai na daga cikin hanyoyi na shiriya da kuma aikin
Musdafa tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi akwai azumtar azumi shida na watan shauwal, an karbo daga Abu Ayuba Al'ansari Allah ya
kara yarda a gare shi Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata gare shi
ya ce : ( Wanda ya yi azumin Ramadana ya bi
shi da guda shida a shauwal yana dai-dai
da ya yi azumin shekara)
Hakika Allah ya sanya lada goma ga kyakkyawa daya wato wata daya na da ladan watanni goma , ranaku shida kuma na bayan salla na da ribin
su sau goma wato kwana sittin wannan shi ne shekara guda cikakkiya .
Ba laifi , a yi azumin su a jere ko a rarrabe kada dayan ku yayiwa kanshi rowa na wannan kwanaki shidan ta iya yiwuwa a
rubuta shi cikin wadanda suka yi azumin shekara, lallai kuwa wannan babban ganima ce wanda ke
sa mutum yayi kokari don ya same shi.
Ya ku Musulmai :
Lallai abin da 'yan ta'adda suka
tashi da shi a cikin azumi kuma a
makka a kusa da ka'aba na daga cikin ayyuka na ta'addanci wanda shari'a da hankali duka zai kyamace
shi , basu kiyaye alfarmar Ramadana
ba ko alfarmar daki mai alhurma ba , ko
kuma alhurmar jinin muminai ba , ma su
azumi , lallai wannan na daga cikin kaidi na makiya musulunci da kuma bushewar ran mahara wanda suke aikin barna a doron kasa .
Lallai dakin na da Ubangijin da
zai kiyaye shi , hakika Allah yayi alkawarin narkon azaba ga wanda ya keta alhurmar sa, Allah ya ce :
(Lallai wadanda suka kafurta kuma suka taushe'' mutane'' daga hanyar Allah da masallaci mai
alhurma wanda muka sanya shi ga mutane alhali kuwa` mazauni a ciki da
bakauye dai-dai suke kuma wanda ya yi nufin karkatar da gaskiya a cikinsa da
zalunci za mu dandana masa daga wata
azaba mai radadi).
Allah ya kiyaye
shi daga dukkan mai ketare iyaka azzalumi , maha'inci , mai laifi ,
shaidani abin jefewa , mai girman kai la'imi (mai dakon mummunan abu) ya faru da musulunci , to, mugunyan musifa mai kewayewa ta tabbata akansa ,Allah ya
maida mishi kaidinsa a mokoshinsa , ya sanya mummunan shirinsa ya zama
halakarwa a gare shi , kuma Allah ya yanke karshensa .
Ya ku bayin Allah:
Lallai Allah mabuwayi da daukakaa ya umarce mu
da al'amari mai girma , ku saurara! Wanda shi ne salati da aminci ga Annabi mai
girma ya Allah ka yi dadin tsira da aminci da
albarka bisa ga shugabanmu
Annabin mu Muhammad.
Ya Allah ka yarda da kalifofi shiryayyu
Abubakar da Umar da Usman da Ali da
iyalai baki daya da wanda ya bi su da kyautatawa har zuwa ranar sakayya .
Ya Allah ka sanya mu cikin wadanda ka karbi
azuminsu da tsayuwansu da sauran ayukan
su .
Ya Allah ka maimaita mana Ramadan shekaru masu
yawa muna cikin lafiya da aminci da
imani .
Ya Allah ka tsawaita
rayuwarmu ka kyautata ayukanmu ka bamu
kyakkyawan karshe .
Ya Allah ka gyara
halayen Musulmai a ko ina ya Ubangijin
talikai .
Ya Allah ka kiyaye
shugabanmu kadimul haramaini sharifaini da kiyayewan ka ka ba shi kulawa da
kulawarka .
Ya Allah ka datar da mataimakin shi cikin abin
da kake so kuma ka yarda da shi , ka riki makwarkwadan su da da'a da takawa .
Ya Allah ka datar da su cikin abinda akwai
alheri ga Musulunci da musulmai , da
kuma abin da cikin shi a kwai gyaruwar gari da bayi .
Ya Allah ka azurta shi
da abokan sirri na kwarai, masu nasiha wanda za su nusar da su zuwa ga alheri kuma su taimaka
musu a kanshi , ya Ubangijin talikai.
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق