HUDUBAR JUMA'A NA MASALLACIN ANNABI TARE DA SHAIKH ALIYU DAN ABDURRAHMAN AL, HUZAIFI NA 30/8/ 1438
Da sunan Allah mai
rahama mai jin kai
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Mabuwayi
mai yawan gafara yana halittan abin da ya so kuma ya zaba abin da ya so , mai
juya dare da rana lallai cikin haka akwai abun lura ga masu basira, ina kyautata yabo ga Ubangiji na kuma ina gode mishi ina tuba zuwa gare shi ina nemar
gafarar sa na shaida babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya tilo
mai rinjaye na shaida Annabin
mu kuma shugabanmu Muhammad bawansa ne
kuma Manzon sa ne zababbe ya Allah ka yi
dadin tsira da aminci da albarka bisa ga
bawanka kuma Manzon ka Muhammad da iyalansa
da sahabbansa masu biyayya .
Bayan haka ku ji tsoron
Allah Madaukaki ku mishi biyayya ba wanda
zai tsiyata ta hanyar yiwa Allah
da'a ,
haka kuma ba wanda zai rabauta ta hanyar sabawa Allah .
Ya ku bayin Allah !
Ku aminta da alkawarin
Allah bisa ga kyawawan ayyuka , ku yi
kokari don samun kyakkyawan karshe da
makoma to, Ubangijinku mai yawan godiya ne kuma masani
mawadaci ne kuma mai karamci yana
kira don a nemi kusanci zuwa gare shi
da abinda ya ke so , kuma shi mawadaci ne ga barin da'an bayi yana muku gargadi daga sabo a halin kuwa ba zai cutar da shi ba, wanda ya tsayu akan zunubai masu
halakarwa Allah madaukakin sarki ya ce
: ( Wanda ya yi aiki na kwarai to, don kansa
wanda ya yi munana to, (alhaki) a kansa Ubangijinka ba mai zalunci ba ne ga
bayi ).
Kuma Allah madaukakin sarki ya ce : ( Kuma duk wanda ya juya baya akan
diga-digansa to, ba zai cutar da Allah
da komai ba kuma Allah yana sakanyawa
masu godiya ).
Ku kasance ya ku mutane cikin tsoron azaban
Allah domin baya sauka ga wani face ya halaka shi , haka kuma baya kewaya wani
wanda ya gafala face ya azabtar da shi
ya tsiyata shi Allah madaukakin
sarki ya ce : ( Kuma wanda hushi na
ya sauka akansa to lallai ne ya fadi )
Abun mamaki ga mutumin da yake aiki don duniya
ya manta da lahira , to, duniya akan same ta ta hanyar aiki hakanan akan same ta ba ta hanyar aiki ba ga wanda ya gaza yin aikin, amma ita lahira da ni'imarta
ba a riskanta sai da aiki, Allah
madaukakin sarki ya ce :
( Kuma wancan ita
ce Aljannar wannan da aka
gadar da ku ita sabo da abin da
ku ka kasance kuna aikatawa).
Ya ku Musulmai :
Ga wani lokaci mai girma ya sauka a gare ku ,
kuma wata mai karamci ,
albarkatu na sauka a cikinta da alheri , kuma ana kankare zunubai a
cikinta watan ramadana wanda Allah ya
sanya mishi falala . An
karbo daga Abu Sa'id Allah ya kara mishi yarda ya ce: daga Annabi tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi ya ce : ( Jagoran watanni shi ne watan Ramadana mafi girman al'hurma kuma shi ne watan
zulhijja ) Albazzar ne ya rawaito shi .
Allah madaukakin sarki ya ce : ( watan
ramadana da aka saukar da alkur'ani a cikinta shiriya ne ga mutane da hujjoji
bayyanannu na shiriya da kuma rarrabewa ) lokaci na Ramadan lokaci ne mai albarka da Allah
ya tattaro a cikinsa ibadoji na azumi
tare da salla da zakka ga wanda ya ke yin
zakka a cikinsa , ga kuma karamin hajji
acikinta , wanda shi ne umra da kuma yawaita karatun Alkur'ani da nau'uka daban –daban na ambaton Allah da umarni da kyakkyawa da hani da mummuna da sauran ayuka na da'a ga wanda ya ke son
yawaita neman kusanci to, sabuba
na alherin cikin sa na da yawa kuma a bayyane suke sabuban sharri kuma a ramadana dan
kadanne , ana shiga tsakanin shaidanu da abin da suke so na barna da batar da Musulmi
da kange shi daga da'a. An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda
a gare shi daga Annabi tisra da amincin
Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Idan Ramadana ya zo ana bubbude kofofin
Aljanna a rurrufe kofofin jahannama a
daure shaidanu cikin mari ) Buhari ne ya rawaito da Muslim
Daga cikin nau'uka na
lada da ni'ima a cikin Aljanna, akwai irin nau'ukan da'a da ibada da suka
dace da su anan duniya , to dukkan da'a na da ladan shi kuma da ni'ima da ya dace da shi, Allah madaukakin
sarki ya ce: Ana ce musu ( Ku ci kuma
ku sha a cikin ni'ima sabo da abin da ku ka gabatar a cikin kwanukan da suka shige )
An karbo daga sahal Dan
Sa'ad Allah ya kara yarda a gare shi
ya ce : Daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbat a gare shi ya ce : ( A cikin aljanna a kwai kofan da ake kira
arrayanu za a kira masu azumi ta gun shi , duk wanda ya kasance acikin masu
azumi zai shige shi, wanda ya shige shi ba zai ji kishi ba har abada , ) Buhari ne ya rawaito shi
Mafi girman girmamawa ga wanda ya
shiga aljanna shi ne dubi zuwa ga fiskan Ubangiji mai girma wanda shi din sakayya ne ga kyautatawa da musulmi ya yi na bautawa Allah kamar yana
ganin shi , Allah Madaukakin sarki yace :( Wadanda suka kyautata yi suna da
abu mai kyau kuma suna da kari) Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a
gare shi ya fassara kari da kallo zuwa ga fiskar Allah Mai girma, kamar yadda
ya zo a hadisin salman Allah kara yarda a gare shi, wanda Muslim ya rawaito, To
sakayyar na daga irin jinsin aikin da mutum ya yi, kamar yadda nau'i na azaba
ma ya ta'allaka ne da irin sabo da aka yi, To cin itaciyar zakkumi da shan tafasasshen ruwa sakayya ne ga cin
riba da haram, da shan abubuwan maye da hodar iblis, kwarara ruwan zafi a kai
sakayya ne na girman kai da jiji da kai daga bin shariar Allah da kin jawuwa a
tafarkinsa, Allah Madaukakin sarki yace: ( Lalle
itaciyar zakkum. Ita ce abincin mai laifi. Kamar narkakken kwalta, yana tafasa
a cikin cikuna. Kamar tafasar ruwan zafi.ku kama shi sa'annan ku fizge shi zuwa
ga tsakiyar jahim. Sa'annan ku zuba a kansa daga azabar ruwan zafi. Ka dandana
lalle kai ne! kai ne mabuwayi mai girma ) to sakayya na daga ginsin
aiki a duniya da lahira.
Albishirinku ya ku
musulmai da albishirin manzon Allah ya yi ga sahabbansa game da ramadana domin
hakika yakasance yana musu albishir da shi a karshen sha'ban don su shirya, to
ku fiskanci wannan wata da dukkan alheri kuma ku mishi dukkan tattali, ku fiskance shi
da neman lada da farin ciki mai tsanani , Allah ya kai ku zuwa gareshi
Allah madaukakin sarki yace :(ka ce da falalar Allah da rahamansa sai su yi
farin ciki da wannan shi ne mafi alheri daga abin da suke tarawa ) ku
fiskance shi da tuba daga dukka zunubai don Allah ya goge muku abin da ya
gabata na daga zunubai da shi ku fiskance shi da maida abinda aka zalunta ga
ma'botansa don Ubangiginka ya kiyaye maka kyawawa ya kankare
maka munana ka tuna akwai ranar da zai zo ba zaka riski ramadan ba, ka kasance
mai shirya wa mutuwa da kuma musibunta, ka kiyaye azumin ka daga wasa da batsa da cin nama dayanku da annamimanci da magana
mara kyau da ayyukan sabo da kallo zuwa ga abubuwan da aka haramta ka kiyaye
zuciyarka daga munanan sake- sake, An
karbo daga Ibnu umar Allah ya kara yarda a gare su daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata
a ga re shi ya ce :( Ta iya yiyuwa wani mai azumin kason shi daga azumin sa
shine yunwa da kishin ruwa, ta iya yiwuwa wani mai tsayuwan dare rabonshi na
tsayuwansa shine hana idonshi barci ) Addabarani ya rawaito shi a cikin
littafinshi Alkabir, Imamu Al munziri ya
ce isnadin ba shi da laifi,
An karbo daga Abu
huraira Allah ya kara yarda a gare shi
ya ce:Manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi ya ce :(Duk wanda bai bar fadin karya ba da aiki
da shi to Allah bai da bukatan barin abincinsa da abin shan sa ) Bukhari ne ya rawaito da
Abu Dawuda da Tirmizi.
An karbo daga Abu Ubaida Allah ya kara yarda a
gare shi Annabi tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (Azumi garkuwa ne) wato kariya ne muddin
ba' keta shi ba )Nasa'I ne ya
rawaito da dabrani a Al-ausad ya kara da
:sai aka ce me ya ke keta ta sai ya ce da karya da cin naman wani ,
Musulmi yayi kokarin girmama ladan azumin shi ta hanyar yawaita ayyukan da'a da neman
kusanci a ramadan, na daga tilawan alkura'ani da yawan zikiri da istigfari da
yin salati ga Annabi tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi da sadaka da kyauta don neman yardan
Allah da nau'uka na kyautata wa kamar ilmantarwa da umarni da kyakkyawa da
kwadaitar wa zuwa gare shi da hani daga sharri da gargadi game da shi .don
yawan da'a tare da yin azumi, yana kara ladar azumi, wanda ya shayar da mai
azumi yana da lada kwatan kwacin ladansa ba tare da an tawaye wani abu ba na
daga ladansa ba.
kada ka yi sakaci ya kai musulmi game da sallan tarawihi da tsayuwan dare
musamman kokari na neman lailatul kadri
a goman karshe, azumin ramadana kankara
ne ga zunubai an karbo daga Abu Huraira Allah ya
kara yarda a gare shi ya ce manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(Duk
wanda ya yi azumin ramadana cikin imani da neman lada to za a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubansa )Buhari da Muslim ne suka rawaito.
An karbo daga Ubada dan Samit Allah ya kara
yarda a gare shi Annabi tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce game da lailatu al kadri (ku
neme shi a goman karshe wanda yayi tsayuwan shi yana mai imani da neman lada
sannan yayi dace da shi za a gafarta mishi abin da ya gabata na daga zunuban shi
da abin da ya jinkirta ) Ahmad ne ya rawaito da Addabarani a Al kabir.
Ka kirdadi salla cikin jam'i , kai musulmi Allah zai kiyaye bawa kuma ya jibinci
alamarin shi kuma ya datar da shi a
alamuran shi, wanda ya daidaitar da sallah to duniyarsa za ta tafi hakanan kuma
da
lahirarsa zai ji dadi a duniya jin
dadi irin na dabbobi sannan kuma a ce da shi ranar alkiyama shiga wuta tare da
masu shiga.Ya zo a hadisi wanda yayi sallar ishai acikin jama' kamar ya yi tsayuwan rabin dare ne, sannan kuma wanda yayi sallar asuba
acikin jama'a kamar wanda yayi tsayuwan
dare ne dukaninsa. )Muslim ne ya rawaito a hadisin Usmana dan affan Allah ya
kara masa yarda,
Na daga cikin abin da
ke girmama hasara kuma yake haramta wa bawa alheri yin azumi da barin
salla ko kuma barin wani sashi daga gare
ta.
Na daga cikin tafiyar
da rayuwa da bata shi kwana da hana ido barci akan wasa ko kuma bibiyan
yanar gizo na barna da kuma bin fina
finai masu cutarwa da zubar da mutunci
da bata tarbiyya da halaye,hasara da tabewa na girmama idan mutun ya rinka
shagaltuwa da wadannan abubuwa a wannan wata, daga ayyuka na alheri Allah
madaukakin sarki ya ce (ku yi gaggawa zuwa ga meman gafara daga ubangijinku
da wata aljanna wanda fadinta (daidaida ) sammai da kasa ne an yi tattalinta
domin masu takawa )*(wadanda suke ciyarwa a cikin sauki da tsanani kuma
suke masu hadiyewar fushi kuma masu yafewa mutane laifi ,kuma Allah yana son
masu kyautatawa ) Allah ya sa mini
albarka ni da ku a alkura'ni mai girma
Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya
sun tabbata ga Allah mai shiryarwa zuwa ga hanya madaidaiciya. Ma'aboci falala
mai girma, yana baiwarsa ga wanda ya so da falalarsa, ya kuma hana wanda ya so bisa adalcinsa, shi mabuwayi
ne Mai hikima ina kyawtata yabo ga ubangiji na kuma ina gode mishi ina mai tuba zuwa gare shi ina neman
gafararsa na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake ba shi
da abokin tarayya Mai iko kuma masani na shaida cewa Annabinmu kuma shugabanmu muhammad bawansa ne kuma manzonsa ne, ma'abocin sharia' mai haske da shiriya
mikakkiya ya Allah ka yi salati da sallama da albarka bisa ga bawanka kuma
manzonka muhammad da iyalansa da sahabbansa wanda suka siffantu da dukkan dabiu
na karamci.
Bayan haka :
Ku ji tsoron Allah yadda ya dace a ji
tsoronsa kuma kuyi riko da igiya mai karfi na musulunci, Ya ku bayin Allah ko sanya wa kowani zunubi tuba hakika masu tuba sun rabauta masu dogewa
a kan zunubai sun yi hasara Allah madaukaki
ya ce: (ku tuba zuwa ga Allah ya ku mu'minai
ko za ku za ku rabauta). wannan
wata lokaci ne na tuba kuma na daga cikin
mafi girman zunubai da ya wajaba
atuba daga gareshi akwai shan taba ka
tsarkake bakinka ya kai musulmi daga shan shi, ka tsarkake bakinka daga gare shi don ambaton
Allah da karatun alkura'ni ka dadada kamshinka ga salihai masu zama da kai da
mala'ku masu rubutu domin shan taba yana kusanto da shaidanu kuma yana lalata
jini kuma yana jawo cututtuka masu
halakarwa, kuma yana gajarta rayuwa, kuma
ka'idoji na shari' na haramta shi, ka sani ya kai musulmi ya wajaba ka kwana da niya tun daga dare, An karbo daga Hafsa
Allah ya kara yarda agareta daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agare
shi yace : ( wanda bai kulla niyarsaba tun daga dare na
azumi to babu azumi agareshi ) Abu dawda
da tirmizi da nasa'I da ibnu majah su ka
rawaito shi. Ya zo a hadisi dukk wanda ya sha azumi na ramadana ba tare da
uzuri ba ba zai iya biyansa ba ko da ya azumci zamani baki daya.To Allah ya
tsare mu. lalle Allah da mala'kunsa na yin salati ga Annabi ya ku wadanda suka
yi imani ku yi salati a gare shi da aminci tabbatacce .
جزاك الله خيرا
ردحذف