الخميس، 25 مايو 2017

MARABA DA RAMADAN

HUDUBAR  JUMA'A NA MASALLACIN  ANNABI TARE DA SHAIKH ALIYU DAN  ABDURRAHMAN AL, HUZAIFI  NA 30/8/ 1438
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai
  Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Mabuwayi mai yawan gafara yana halittan abin da ya so kuma ya zaba abin da ya so , mai juya dare da rana   lallai  cikin haka  akwai abun lura  ga masu basira, ina kyautata  yabo ga Ubangiji na kuma ina gode mishi  ina tuba zuwa gare shi  ina nemar   gafarar sa   na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya  tilo  mai rinjaye   na shaida Annabin mu  kuma shugabanmu Muhammad bawansa ne kuma Manzon sa ne zababbe  ya Allah ka yi dadin tsira da aminci da albarka  bisa ga bawanka kuma Manzon ka Muhammad da iyalansa  da sahabbansa masu biyayya .
Bayan haka ku ji tsoron Allah Madaukaki  ku mishi biyayya   ba wanda  zai tsiyata ta hanyar   yiwa Allah da'a  ,  haka kuma ba wanda zai rabauta ta hanyar sabawa Allah  .
 Ya ku bayin Allah !  
Ku aminta da alkawarin Allah   bisa ga kyawawan ayyuka , ku yi kokari  don samun kyakkyawan karshe da makoma   to,  Ubangijinku mai yawan godiya ne  kuma masani   mawadaci ne kuma mai karamci  yana kira don a nemi kusanci zuwa gare shi   da abinda  ya ke so ,  kuma shi mawadaci ne  ga barin da'an bayi   yana muku gargadi daga sabo  a halin kuwa ba zai cutar da shi ba,   wanda ya tsayu akan zunubai masu halakarwa  Allah madaukakin sarki ya ce :  (  Wanda ya yi aiki na kwarai to, don kansa wanda  ya yi munana to, (alhaki)  a kansa Ubangijinka ba mai zalunci ba ne ga bayi  ).
 Kuma Allah madaukakin sarki ya ce : (  Kuma duk wanda ya juya baya akan diga-digansa  to, ba zai cutar da Allah da komai ba  kuma Allah yana sakanyawa masu godiya  ).
 Ku kasance ya ku mutane cikin tsoron azaban Allah domin baya sauka ga wani face ya halaka shi , haka kuma baya kewaya wani wanda ya gafala face ya azabtar da shi   ya tsiyata shi  Allah madaukakin sarki ya ce :  ( Kuma wanda hushi na ya sauka akansa to lallai ne ya fadi )
 Abun mamaki ga mutumin da yake aiki don duniya ya manta da lahira , to, duniya akan same ta ta hanyar  aiki hakanan akan same ta ba ta hanyar  aiki ba ga wanda ya gaza yin aikin,  amma ita lahira da  ni'imarta   ba a riskanta sai da aiki,  Allah madaukakin sarki ya ce :
( Kuma wancan ita ce  Aljannar  wannan da aka  gadar da ku ita   sabo da abin da ku ka kasance kuna aikatawa).
Ya ku Musulmai :
 Ga wani lokaci mai girma ya sauka a gare ku , kuma wata  mai karamci  ,  albarkatu na sauka a cikinta da alheri , kuma ana kankare zunubai a cikinta  watan ramadana wanda Allah ya sanya mishi falala    . An karbo daga Abu Sa'id Allah ya kara mishi yarda ya  ce: daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Jagoran watanni shi ne watan Ramadana  mafi girman al'hurma kuma shi ne watan zulhijja ) Albazzar ne ya rawaito shi .
  Allah madaukakin sarki ya ce : ( watan ramadana da aka saukar da alkur'ani a cikinta shiriya ne ga mutane da hujjoji bayyanannu  na shiriya  da kuma rarrabewa )  lokaci na Ramadan lokaci ne mai albarka da Allah ya tattaro a cikinsa  ibadoji na azumi tare da salla da zakka  ga wanda ya ke yin zakka a cikinsa  , ga kuma karamin hajji acikinta , wanda  shi ne umra  da kuma yawaita karatun Alkur'ani da nau'uka  daban –daban    na ambaton Allah  da umarni da kyakkyawa da hani da mummuna    da sauran ayuka na da'a ga wanda ya ke son yawaita  neman  kusanci   to, sabuba na alherin cikin sa na da yawa kuma a bayyane suke  sabuban sharri kuma a ramadana dan kadanne  ,  ana shiga tsakanin shaidanu da  abin da suke so na barna  da batar da  Musulmi  da  kange shi daga da'a.  An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi daga Annabi  tisra da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya ce : (  Idan Ramadana ya zo ana bubbude kofofin Aljanna a rurrufe  kofofin jahannama a daure shaidanu cikin mari ) Buhari ne ya rawaito da  Muslim
Daga cikin nau'uka na lada da  ni'ima a cikin Aljanna,  akwai irin nau'ukan da'a da ibada da suka dace da su anan duniya    , to dukkan da'a na  da ladan shi kuma  da ni'ima da ya dace da shi, Allah madaukakin sarki ya ce: Ana ce musu ( Ku ci  kuma ku sha a cikin ni'ima sabo da abin da ku ka gabatar  a cikin kwanukan da suka shige )
An karbo daga sahal Dan Sa'ad  Allah ya kara yarda  a gare shi  ya ce : Daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbat a gare  shi ya ce : (  A cikin aljanna a kwai kofan da ake kira arrayanu za a kira masu azumi ta gun shi , duk wanda ya kasance acikin masu azumi zai shige shi, wanda ya shige shi ba zai ji kishi ba har abada ,  ) Buhari ne ya rawaito shi
  Mafi girman girmamawa ga wanda ya shiga aljanna shi ne dubi zuwa ga fiskan Ubangiji mai girma    wanda shi din sakayya ne ga kyautatawa  da musulmi ya yi na bautawa Allah kamar yana ganin shi , Allah Madaukakin sarki yace :( Wadanda suka kyautata yi suna da abu mai kyau kuma suna da kari) Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya fassara kari da kallo zuwa ga fiskar Allah Mai girma, kamar yadda ya zo a hadisin salman Allah kara yarda a gare shi, wanda Muslim ya rawaito, To sakayyar na daga irin jinsin aikin da mutum ya yi, kamar yadda nau'i na azaba ma ya ta'allaka ne da irin sabo da aka yi, To cin itaciyar zakkumi  da shan tafasasshen ruwa sakayya ne ga cin riba da haram, da shan abubuwan maye da hodar iblis, kwarara ruwan zafi a kai sakayya ne na girman kai da jiji da kai daga bin shariar Allah da kin jawuwa a tafarkinsa,   Allah Madaukakin sarki yace: ( Lalle itaciyar zakkum. Ita ce abincin mai laifi. Kamar narkakken kwalta, yana tafasa a cikin cikuna. Kamar tafasar ruwan zafi.ku kama shi sa'annan ku fizge shi zuwa ga tsakiyar jahim. Sa'annan ku zuba a kansa daga azabar ruwan zafi. Ka dandana lalle kai ne! kai ne mabuwayi mai girma ) to sakayya na daga ginsin aiki  a duniya da lahira.
Albishirinku ya ku musulmai da albishirin manzon Allah ya yi ga sahabbansa game da ramadana domin hakika yakasance yana musu albishir da shi a karshen sha'ban don su shirya, to ku fiskanci wannan wata da dukkan alheri  kuma ku mishi dukkan tattali, ku fiskance shi da neman lada da farin ciki mai tsanani , Allah ya kai ku zuwa gareshi Allah madaukakin sarki yace :(ka ce da falalar Allah da rahamansa sai su yi farin ciki da wannan shi ne mafi alheri daga abin da suke tarawa ) ku fiskance shi da tuba daga dukka zunubai don Allah ya goge muku abin da ya gabata na daga zunubai da shi ku fiskance shi da maida abinda aka zalunta ga ma'botansa  don  Ubangiginka ya kiyaye maka kyawawa ya kankare maka munana ka tuna akwai ranar da zai zo ba zaka riski ramadan ba, ka kasance mai shirya wa mutuwa da kuma  musibunta,  ka kiyaye azumin ka daga wasa da batsa  da cin nama dayanku da annamimanci da magana mara kyau da ayyukan sabo da kallo zuwa ga abubuwan da aka haramta ka kiyaye zuciyarka daga munanan sake- sake,  An karbo daga Ibnu umar Allah ya kara yarda a gare su  daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a ga re shi ya ce :( Ta iya yiyuwa wani mai azumin kason shi daga azumin sa shine yunwa da kishin ruwa, ta iya yiwuwa wani mai tsayuwan dare rabonshi na tsayuwansa shine hana idonshi barci ) Addabarani ya rawaito shi a cikin littafinshi Alkabir, Imamu Al munziri  ya ce isnadin ba shi da laifi,
An karbo daga Abu huraira  Allah ya kara yarda a gare shi ya ce:Manzon Allah tsira da  amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(Duk wanda bai bar fadin karya ba da aiki da shi to Allah bai da bukatan barin  abincinsa  da abin shan sa ) Bukhari ne ya rawaito da Abu Dawuda da Tirmizi.
 An karbo daga Abu Ubaida Allah ya kara yarda a gare shi Annabi tsira da  amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce  (Azumi garkuwa ne) wato kariya ne muddin ba' keta shi ba  )Nasa'I ne ya rawaito da dabrani a Al-ausad  ya kara da :sai aka ce me ya  ke keta ta  sai ya ce da karya da cin naman wani ,
Musulmi yayi kokarin  girmama ladan azumin shi  ta hanyar yawaita ayyukan da'a da neman kusanci a ramadan, na daga tilawan alkura'ani da yawan zikiri da istigfari da yin  salati ga Annabi  tsira da  amincin Allah su tabbata a gare shi da sadaka da kyauta don neman yardan Allah da nau'uka na kyautata wa kamar ilmantarwa da umarni da kyakkyawa da kwadaitar wa zuwa gare shi da hani daga sharri da gargadi game da shi .don yawan da'a tare da yin azumi, yana kara ladar azumi, wanda ya shayar da mai azumi yana da lada kwatan kwacin ladansa ba tare da an tawaye wani abu ba na daga ladansa ba.
 kada ka yi sakaci ya kai musulmi  game da sallan tarawihi da tsayuwan dare musamman kokari na neman lailatul  kadri a goman karshe,  azumin ramadana kankara ne ga zunubai  an karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce manzon Allah tsira da  amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(Duk wanda ya yi azumin ramadana cikin imani da neman lada to za a gafarta  masa abin da ya gabata daga zunubansa  )Buhari da Muslim ne suka rawaito.
  An karbo daga Ubada dan Samit Allah ya kara yarda a gare shi Annabi  tsira da  amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce game da lailatu al kadri (ku neme shi a goman karshe wanda yayi tsayuwan shi yana mai imani da neman lada sannan yayi dace da shi za a gafarta mishi abin da ya gabata na daga zunuban shi da abin da ya jinkirta ) Ahmad ne ya rawaito da Addabarani a Al kabir.
Ka kirdadi  salla cikin jam'i , kai musulmi  Allah zai kiyaye bawa kuma ya jibinci alamarin shi  kuma ya datar da shi a alamuran shi, wanda ya daidaitar da sallah to duniyarsa za ta tafi hakanan kuma  da  lahirarsa  zai ji dadi a duniya jin dadi irin na dabbobi sannan kuma a ce da shi ranar alkiyama shiga wuta tare da masu shiga.Ya zo a hadisi wanda yayi sallar ishai acikin jama' kamar  ya yi tsayuwan rabin  dare ne, sannan kuma wanda yayi sallar asuba acikin jama'a  kamar wanda yayi tsayuwan dare ne dukaninsa. )Muslim ne ya rawaito a hadisin Usmana dan affan Allah ya kara masa yarda,
Na daga cikin abin da ke girmama hasara kuma yake haramta wa bawa alheri yin azumi da barin salla  ko kuma barin wani sashi daga gare ta.
Na daga cikin tafiyar da rayuwa da bata shi  kwana  da hana ido barci akan wasa ko kuma bibiyan yanar gizo na  barna da kuma bin fina finai masu cutarwa  da zubar da mutunci da bata tarbiyya da halaye,hasara da tabewa na girmama idan mutun ya rinka shagaltuwa da wadannan abubuwa a wannan wata, daga ayyuka na alheri Allah madaukakin sarki ya ce (ku yi gaggawa zuwa ga meman gafara daga ubangijinku da wata aljanna wanda fadinta (daidaida ) sammai da kasa ne an yi tattalinta domin masu takawa )*(wadanda suke ciyarwa a cikin sauki da tsanani kuma suke masu hadiyewar fushi kuma masu yafewa mutane laifi ,kuma Allah yana son masu kyautatawa  ) Allah ya sa mini albarka ni da ku a alkura'ni mai girma   
Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah mai shiryarwa zuwa ga hanya madaidaiciya. Ma'aboci falala mai girma, yana baiwarsa ga wanda ya so da falalarsa, ya kuma  hana wanda ya so bisa adalcinsa, shi mabuwayi ne Mai hikima ina kyawtata yabo ga ubangiji na kuma ina gode mishi  ina mai tuba zuwa gare shi ina neman gafararsa na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya Mai iko kuma masani na shaida cewa    Annabinmu kuma shugabanmu  muhammad bawansa ne kuma manzonsa ne,  ma'abocin sharia' mai haske da shiriya mikakkiya ya Allah ka yi salati da sallama da albarka bisa ga bawanka kuma manzonka muhammad da iyalansa da sahabbansa wanda suka siffantu da dukkan dabiu na karamci.
Bayan haka :
    Ku ji tsoron Allah yadda ya dace a ji tsoronsa kuma kuyi riko da igiya mai karfi na musulunci, Ya ku bayin Allah  ko sanya wa kowani zunubi  tuba hakika masu tuba sun rabauta masu dogewa a kan zunubai sun  yi hasara Allah madaukaki ya ce: (ku tuba zuwa ga Allah ya ku mu'minai  ko za ku za ku rabauta).  wannan wata lokaci ne na tuba kuma na daga cikin  mafi girman zunubai da ya  wajaba atuba daga gareshi akwai shan taba  ka tsarkake bakinka ya kai musulmi daga shan shi,  ka tsarkake bakinka daga gare shi don ambaton Allah da karatun alkura'ni ka dadada kamshinka ga salihai masu zama da kai da mala'ku masu rubutu domin shan taba yana kusanto da shaidanu kuma yana lalata jini kuma yana jawo  cututtuka masu halakarwa, kuma yana gajarta rayuwa, kuma  ka'idoji na shari' na  haramta shi,  ka sani ya kai musulmi ya wajaba ka kwana  da niya tun daga dare, An karbo daga Hafsa Allah ya kara yarda agareta daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yace :  (  wanda bai kulla niyarsaba tun daga dare na azumi  to babu azumi agareshi ) Abu dawda da tirmizi da nasa'I  da ibnu majah su ka rawaito shi. Ya zo a hadisi dukk wanda ya sha azumi na ramadana ba tare da uzuri ba ba zai iya biyansa ba ko da ya azumci zamani baki daya.To Allah ya tsare mu. lalle Allah da mala'kunsa na yin salati ga Annabi ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi da aminci tabbatacce .
  


هناك تعليق واحد: