الإخلاص
وإحضار النية في الأمور كلها
عن عُمَرَ بْن الْخَطَّابِ رضي الله عنه، قال:
سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ، يَقُولُ:
إِنَّمَا الأَعْمَالُ بِالنِّيَّاتِ، وَإِنَّمَا لكل
امْرِئٍ مَا نَوَى، فَمَنْ كَانَتْ هِجْرَتُهُ إِلَى اللَّهِ وَرَسُولِهِ
فَهِجْرَتُهُ إِلَى اللَّهِ وَرَسُولِهِ، وَمَنْ كَانَتْ هِجْرَتُه لدُنْيَا
يُصِيبُهَا، أَوِ امْرَأَةٍ يَنْكِحُهَا فَهِجْرَتُهُ إِلَى مَا هَاجَرَ إِلَيْه.
أخرجه البخاري [1] ومسلم [1907]
HADISI NA FARKO: IKHLASI DA HALARTO DA NIYYA CIKIN
LAMURAN ADDINI GABAXAYANSU
An ruwaito daga Umar dan Alkhaddabi –Allah ya qara yarda a gare shi- ya
ce:
Na ji Manzon Allah –sallal lahu alaihi wa sallama- yana cewa:
Dukkan
aiyuka suna tare da niyya, kuma lallai kowane mutum yana samun sakamakon abinda
yayi niyya;
Wanda
hijirarsa ta kasance saboda Allah ne da Manzonsa, sakamakon hijirarsa tana ga Allah da
Manzonsa.
Wanda
kuma hijirarsa ta kasance saboda wata duniya ce da zai same ta, ko don wata
matar da zai aure ta, to sakamakon hijirarsa yana ga abinda yayi hijira dominsa.
Bukhariy [1], da Muslim [1907] su ka ruwaito shi.
FA'IDODI DAGA HADISIN
(1) Yin niyya, ga kowani aiki, da ikhlasi sharaxi ne
daga sharruxan karvar aikin.
(2)
Aiyukan masu hankali balagaggu (mukallafai), babu
makawa sai an yi musu niyya, saboda babu aikin da za a yi sakayya akansa face,
face an yi shi da niyya.
(3) Wajabcin ikhlasin niyya ga Allah shi kaxai, a cikin
dukkan aiyuka da zantuka.
(4) Baya halatta ga mutum ya nufi aikata wani aiki
gabanin sanin hukuncinsa, saboda ingantar aiki tana kasancewa ne da niyya, ita
kuma niyyar aikata abu bata inganta sai bayan sanin hukuncinsa.
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق