السبت، 28 يناير 2017

FALALAR GARIN MAKKAH NA SHAIKH ABDULMUHSIN ALKASIMI(HUDUBAR 23 Zulkida 1437

Hudubar Masallacin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi na 23/11/1437 Ah
Da sheikh  Abdulmuhsin Bin Muhammad Alkasim
Hudubar farko
     Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah muna gode masa kuma muna neman taimakonsa da gafararsa, kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu , duk wanda Allah ya shiryar da shi babu mai batar da shi, kuma wanda Allah ya batar da shi babu mai shiryar da shi, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah
Shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya, kuma na shaida Annabi Muhammad bawansa ne kuma manzonsa ne,tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da iyalansa da sahabbansa  da aminci tabbatace mai yawa.
Bayan haka:
 ku ji tsoron Allah ya ku bayin Allah yadda ya cancanci a ji tsoronshi, ku yi riko da igiya mai karfi na musulunci,
Ya ku musulmai!
Allah ya kebanta da halittawa, da gudanarwa da zabi, zabinsa na nuni ne ga rububiyyarsa  da dayantakarsa madaukaki,da cikar hikimarsa da iliminsa da ikonsa, Hakika  Allah madaukaki ya fifita tsakanin wurare da zatuttuka, da ayyuka da wattanni, da dararraki da ranaku.
Mafi alherin halittu shi ne Annnnabi muhammmad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kuma mafi alherin aiki shine kadaita Allah da bauta , mafi daraja daga cikin  watanni shine watan ramadan, kuma mafi daukakan  dare shi ne daren lailatul kadri, mafi alherin  rana shine ranar suka (Babbar sallah) kuma mafi alherin wuri a gun Allah kuma mafi soyuwa a gareshi shine makkah,Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: ( Wallahi lalle ke ce mafi  alherin kasar Allah kuma mafi soyuwar kasa a gun Allah madaukakin sarki kuma ba don an fitar da ni daga cikinki ba da ban fita ba) Ahmad ne ya rawaito shi ,
ita ce uwar alkaryu kuma waninta  na  biye mata ne, Allah ya rantse da ita, don  nuni ne zuwa ga girmanta sai yace :(Ubangiji na rantsuwa da wannan gari (Makka), tare da rantsuwa  ya kira shi da gari amintacce, sai ya ce; ( Da wannan gari amintacce).
Masallacin makka ne mafi daukaka cikin masallatayya, shi ne dakin farko mai albarka da aka sanya a doron kasa don shiryar da mutane, : ( kuma lalle ne daki na farko da aka aza domin mutane hakika shi ne wanda ke Bakka mai albarka kuma shiriya ga talikai) Ali Imran 95
Abu Zarri Allah kara yarda a gare shi yace:( ya manzon Allah: wani masalllaci ne aka  fara  aza shi  a doron kasa? Sai yace :( Masallacin ka'aba), sai nace  saannan sai wanne? Sai yace (masalllacin Aksa) Bukhari da muslim ne suka rawaito.
Allah ya shiryar da Annai  Ibrahim zuwa ga gina  dakin kaba,  a cikinta, Allah madaukakin sarki ya ce (Kuma a lokacin da muka iyakance wa Ibrahim wurin dakin ) Hajj 26
Sai ya daga shi da dansa Annabi Isma'ila, kuma khalilin Allah ya roki a jefa son Makka a  zukatan mutane da farin ciki lokacin zuwa gare shi sai ya ce (sai ka sanya zukata daga mutane ta dinga karkata izuwa garesu) ibrahim '37.
 Allah ya zabe ta domin mafi karamcin manzanninsa, a cikinta ne aka haifi Annabi muhmmad tsira da amincin Alla su tabbta a gare shi kuma acikinta ya taso kuma acikin ta aka turo shi, kuma a cikinta aka fara sauko da wahayi da alkur'ani, Manzon Allah ya  rayu a cikinta sama da shekaru hamsin, daga nan kira na musulunci ta taso, kuma a nan ne mafi alherin mutane bayan Annabawa wato sahabbai suka taso, daga nan ne aka yi tafiyan dare da shi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi zuwa ga masallacin Aksa.
Manzon Allah ya so shi so mai yawa, an kuma fitar da shi daga garin makkan a halin tilasci, yayin da  ya sauka madina ya kasance  yana adu'a (ya Allah ka jefa mana son madina kamar yadda ka sanya mana son makka ko sama da haka). Buhari da Muslim,ne suka rawaito shi . Gari ne mai aminci Annabi  Ibrahim yayi mar addua na neman aminci sai ya ce :  (ya ubangiji na ka sanya wannan gari amintacce ) Bakara 126
 Allah yayi ma garin baiwa  inda yake cewa, (Asai  basu ganin mun sanya harami amintacce kuma ana kaiwa mutane hari  a kewayenshi )Ankabut 67.
 Malam kurdubi Allah ya masa rahama yake cewa : " lalle makka bata gushe ba cikin aminci  kuma cikin alhurma daga masu dagun kai da girgizan kasa da kuma sauran abubuwa na fitintinu da ke sauka a kasa.
Duk wanda ya shiga Masallacinta zai samu aminci irin nata Allah (Mai tsarki da daukaka )yake cewa : ( Duk wanda ya shige shi  zai kasance  amintacce) Ali Imran 97.
 Allah ya sanya mata alhurma tun lokacinda ya halicci sammai da kasa, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce: (lallai Allah ya sanya ahurma wa makka tun randa ya halicci sammai da kasa, sai ta kasance tsararriya ce  da alhurman Allah har zuwa ranan Alkiyama) buhari ne ya rawaito.
  Annabi ibrahim shi ya bayyana wa halittu  alfarmarta kamar yadda manzon Allah Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,yake cewa: (lalle  Ibrahim  ya haramta garin makka) Bukhari da muslim suka rawaito.
Annabinmu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana girmamata, a ranan hudaibiyya yake cewa :( na rantse da wanda raina ke hanunshi baza su tambayeni wata kudda ba wanda suke girmama Alhurman Allah  a cikinta sai  na basu ita ) Bukhari ne ya rawaito
Na daga cikin Alhurmanta akwai cewa : Zubar da jini a cikinta ba tare da hakki ba ya fi muni da alfarma akan watan ta.
Manzon Allah Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce : (Baya halatta ga mutumin da yayi imani da Allah da ranan lahira da ya zubar da jini a cikinta) Bukhari da muslim ne suka rawaito.
Ba a tsorata mutanenta ta hanyan rike makami a cikinta manzon Allah Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce : ( Ba ya halatta ga dayanku ya riki makami a makka )muslim ne ya rawaito.
Haka dabbobi ma amintattu ne da amincin Allah a farfajiya ko fili, su kuma tsuntsaye suna masu tafiya ne cikin jeji )  kuma itatuwanta na kadawa da aminci ba a sare ta,  kuma baa tsintuwan batattun dukiya a  a cikinta kamar sauran garurruka  manzon Allah Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce :  (ba a tsinke danyen itaciyarta haka nan kuma ba a yanke bishiyarta sa'annan kuma ba a kora abin farawtarta haka nan kuma ba a tsintuwan abin tsintuwan cikinta sai ga wanda zai nemi me shi)Bukhari da muslim ne suka rawaito.
  Manzon Allah ya kamanta alhurman dukiyoyi da mutunci da kuma jini  saboda girman hurumcinta Allah Madaukakin sarki ya ce :  (lallai jininku da dukiyoyinku  da mutuncinku haramtacce ne a gareku kamar haramcin wannan rana naku a wannan gari naku kuma da wannan wata naku ) Buhari da muslim ne suka rawaito.
  wanda yayi niyyan aikata mummuna a cikinta Allah zai  azabtar da shi  Allah  Madaukakin sarki ya ce : (wanda yayi nufin aikata aikin  ilhadi  a cikinsa da  zalunci zamu dandana masa daga wata azaba mai radadi  ) Hajji 25

Dan masud  -Allah kara masa yarda – " ya ce : Da wani mutum zai yi nufin  ilhadi kuma yana garin Adan  Da Allah ya dandana masa azaba mai radadi ".  
kuma mai zalunci a cikinta shi ne wanda Allah yafi ki a cikin mutane,  Manzon Allah  (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ) ya ce : (wanda Allah ya fi ki a cikin   mutane   shi ne mai ilhadi  a harami ) Buhari ne ya rawaito.
Saboda girman alhurmanta mushriki baya taka kasanta,  sai  Allah ya ce : (lallai mushrikai masu najasa ne kar su kusanto masallacin harami)Tauba 28.
  kuma dujjal shine ya kafurce wa Allah yana fitinan mutane a addininsu,   sai Allah  ya hana shi  shiga makka da madina,Manzon Allah  (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi )  ya ce (Babu wani gari da dajjal baya takawa sai Makka da Madina )Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
  Allah ya kiyaye makka kuma zata cigaba da zama cikin kiyayewar  Allah, duk wanda ya nufe ta da mummuna  Allah zai  halaka shi, mutanen giwaye sun  nufe ta da sharri, sai  Alla ya kangesu kuma ya sanya su suka zama aya da darasi har zuwa ranar sakayya,
  wasu mutane zasu yaki garin ka'aba har sai idan sun kasance a wata sahara  sai  Allah ya kisfe na farkonsu har zuwa  na karshensu)  Bukhari ne ya rawaito. 
Kamar yadda Allah ya sanya aminci a cikinta, ya yi falala ga mutanenta da alhkairu da 'ya'yan itace, duk da cewa tana kwari ne a tsakanin duwatsu biyu wanda ba  shuki, duwatsu ne ke kewaye da ita ta kowani gefe, kasar da gu ne da zaa tsammaci yunwa, sai Ibrahim ya yi adua ga mutanenta da a azurta su da 'ya'yan itace, kamar yadda Allah ya azurta garuruwa masu ruwa, da shuki, sai yace :
(kuma ka azurta mutanenta da yayan itace )Bakara 126.
 sai Allah ya amsa da cewa ( shin bamu tabbatar musu da mallakr hurumi ba ya zama amintacce ana jawowa zuwa gare shi  'ya'yan itace  kowani irin bisa ga azurtawa daga garemu?)Kasas 57.
A'a ai Annabi  Ibrahim ya mata adduan albarka a cikin kwanon awunta da mudunta, wato cikin abin shanta da abincin ta,
Na daga cikin Adduar  Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce (ya Allah ka sanya a madina ribin Abinda ka sanya a makka na Albarka )Buhari da muslim ne suka rawaito.
Ya shayar da mutanen ta ruwan da ba irin shi a doron kasa, wanda mutane na fatan samun ko dan kadan ne daga gare shi. Ruwan zamzam ruwa ne mai albarka kuma abin ci ne Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : :( lallai ruwa ne mai albarka kuma abin sha ne mai dadano ) muslim ne ya rawaito  har ila yau waraka ne daga dukkan cuta manzon Allah Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce(zam zam abinci ne kuma abin sha ne waraka ne kuma ga cuta )  Muslim ne ya rawaito.
Malaika ya tsaga kirjin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya wanke shi da ruwan zamzam.) Bukhari ne ya rawaito
Samuwar arziki da kuma aminci  a cikinta abubuwa ne da za su sa a bauta wa Allah shi kadai,  Allah Madaukakin sarki ya ce: ( su bautawa ubangijin wannan gida (kaba)* wanda ya ciyar da su (ya hanasu daga yunwa kuma ya amintar da su daga wani tsoro )) kuraish 3-4
 Allah zai tunkude sharri daga mutanenta a dalilin girmama daki da suke yi a cikinta da kuma kadaita Allah,  Allah Madaukakin sarki ya ce : (Allah ya sanya ka'aba daki me alfarma rayuwa ga mutane ) Ma'ida 97.
Ibnu kasir ya ce : wato ze dauke musu mummuna sakamakon girmama fiskantanta,
 Makka gari ne mai albarka alherinta gamamme ne,  da na daga cikin Albarkanta ribanya sallah a cikinta don (sallar mutum a masallacin ka'aba ya fi sallah dubu dari a waninsa ) Ahmad ne ya rawaito,  yin dawafi a dakin ka'aba ibada ne kuma ba za a hana wani ba  daga cikin mutane  cikin dare ne ko wuni  Allah ya ce (kuma suyi dawafi a daki dadedde ) Hajj 29
wuraren nata alamomin  addini  ne  kuma wurarene na bauta ga musulmai, Allah ya wajabta  musu fiskantanta  kuma ya sanyata daya daga cikin rukunnan musulunci ,
matafiyi zuwa Masallacinta na samun lada,  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya ce : (ba a nika gari zuwa ga kowani masallaci sai  guda uku masallacin ka'aba da masallacin Manzon Allah da Masallacin aksa) Bukhari da muslim ne suka rawaito.
  Babu wani wuri a doron kasa da ake kewaya shi da sunan ibada sai dakin ka'aba haka kuma ba wani wuri a duniya da aka shar'anta sumbatan shi, sai  Hajarul – Aswad, da ke ka'aba,  rukunul  yamani na ka'aba  ake shafa wa.
 Allah ya sanya ka'aba wurin neman lada, da kuma wurin komawa  kuma da aminci  gare ta ne mutane ke cacarindo  shekara bayan shekara daga kowani sako mai zurfi,  rayuka na begensa kuma zuciya na kwadayin zuwa gare shi a duk lokacin da suka ziyarce ta sai begensu ya karu zuwa gareta.  Annabawa sun nufe shi , Annabi Musa da  Annabi  Yunus da Annabi Muhammad  sun yi hajji, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce; (kamar gani ina ganin Musa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) yana sauka daga tsakanin duwatsu ya na mai kakan da kai zuwa ga Allah da talbiya, kamar ina dubi zuwa ga yunusa dan matta Amincin Allah ya tabbata agare shi ya na kan jar taguwa a halin  yana mai talbiya) Muslim ne ya rawaito.        
Allah ya daukaka wannan daki ya jingina shi zuwa gare shi, kuma ya sanya shi wurin daukaka tauhidi da haskaka shi, ya yi umarni da a tsarka ke shi daga dukkan wani abu da zai kishiyanci hakan na daga gumaka da bauta musu, sai ya ce (ka tsarkake dakina don masu dawafi da masu tsayuwa da masu yawan ruku'u da sujada) Hajj 26
Ya sanya zuwa gare shi ya zama kankara ne ga zunubai da kusakurai da suka shude, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce : (wanda yayi hajji a wannan dakin kuma bai yi jimai ba, kuma bai yi  fasikanci ba  zai dawo kamar yadda mahaifiyarsa ta haife shi ) Bukhari da muslim ne suka rawaito.
  Allah bai  yarda  da wani lada  ga wanda ya ziyarci ka'aba ba koma bayan Aljanna ba,  Annabi Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce :( Daga umra zuwa wata umra kankara ne ga zunubai, aikin hajjin da aka yi da'a bai da sakamako sai aljanna ) Bukhari da muslim ne suka rawaito.
   kuma shi ne alkibila  na mutanen doron kasa baki daya,kuma dukkan musulmi na fiskantan shi sau da dama a kowani rana   Allah Madaukakin sarki ya ce : ( sai ka juya fiskarka wajen masallaci tsararre kuma inda duk kuka kasance to ku juyar da fuskokinku jiharsa)Bakara 144.
Wanda ya mutu cikin musulmai za'a fiskantar da kabarinsa zuwa gare shi.
 Ubangiji mai tsarki ya sanya masa alhurma   ba a fiskantan jihar shi yayin fitsari ko kuma ba haya,  Manzon Allah Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce : (kada ku fiskanci alkibila da bahaya ko bawali sai dai ku fiskanci gabas ko kuma yamma )Bukhari da Muslim ne suka  rawaito.
  zuwa gareshi ne ake kora  hadaya da kuma abin da za a nemi kusanci zuwa ga ubangiji  Allah Madaukakin sarki yake cewa : (sa'annan kuma wurin halatta ta zuwa ga dakin yantacce ne ) Hajj 33
A dakin kaba akwai ayoyi bayyanannu, lallai yana daga cikin ginin Ibrahim, akwai  Makama ibrahima, Amincin Allah ya tabbata a gare shi, Allah ya ya umarce mu da mu mu rike shi gurin sallah, a dakin Allah mai girma akwai Hajarul Aswad (ya sauko  daga Aljanna a halin ya fi nono fari,sai kusakuran bani adam ya bakanta shi) Ahmad ne ya rawaito shi.
shi dutse ne da baya amfanarwa ko kuma  cutarwa, kawai dai ana sumbatan shi domin bin sunna na  Annabi Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sayyidina Umar Allah ya kara masa yarda ya ce : (lallai ni na san kai dutse nebaka cutarwa kuma baka amfanarwa ba don na ga Annabin  Allah yana sumbattanka ba da ba zan sumbanceka ba ) Bukhari da Muslim suka rawaito.
A Masallacin ka'aba akwai Safa da Marwa,   suna daga cikin manyan alamomi na  ibada  wajibi ne a girmamasu a kai komo a tsakaninsu.
 A dakin Allah akwai zamzam,abin lura ne kuma aya ne cikin yawansa da albarkansa da amfaninsa.
Kuma Bayan Ya ku Musulmai:
Dakin Allah an gina shi ne don bautawa Allah shi kadan shi bashi da abokin tarayya,  yana daga cikin wuraren da ake karban tuba, kuma ake komawa zuwa ga Allah,
 ga  duk bawa ya nufi wannan masallaci na ka'aban yana mai kankan da kai da rusunawa ga Allah yana mai neman kusanci zuwa ga mai tsarki Madaukakin sarki don neman a yafe masa zunuban shi. Wajibi ne akan bayi su girmama dakin Allah, don  girmama abin da Allah ya girmama na daga cikin tsoron Allah, a cikin hakan akwai   gyaruwan  Musulmai a cikin addininsu da duniyansu.
Duk wanda yayi  hidima wa Masallatai biyu masu alfarma, da alhazai da masu umrah da masu ziyara, to sakayyansa fa yana wurin Allah ne mai girma,   dukkan Masallatan biyu Annabi ne ya gina su, kuma suna cikin guraren ibada a gurin Allah,
Ina neman tsarin Allah daga sharrin shaidan abin jefewa.
(Kace) An umarce ni in bautawa Ubangijin wannan gari, wanda ya mayar da shi Hurumi, kuma yana da dukkan kome. Kuma an umarce ni da na kasance cikin masu mika wuya.) Namli 91.
Allah mini albarka ni da ku cikin Alkur'ani mai girma, kuma ya amfanar da ni da ku da abin da ke cikin shi na ayoyi da ambato mai hikima, Ina fadin wannan bayanan nawa kuma ina neman gafarar Allah wa ni da ku da dukkan musulmai daga dukkan zunubai, ku nemi gafararsa don lalle shi mai gafara ne mai jinkai.
Huduba ta biyu
Dukkan yabo sun tabbata ga Allah  bisa kyautatawarsa, da kuma godiya bisa ga datarwan shi da baiwarsa, Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai bashi da abokin tarayya muna masu girmama sha'aninsa kuma na shaida lalle Annabinmu  Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa ne, tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi da iyalansa da sahabbansa kuma da tsira tabbatacciya mai yawa.
 ya ku musulmai:
A wannan gari mai albarka amintacce musulmai suna sauke hajjinsu suna masu tsiraituwa daga dukkan wasu abubuwa na duniya da kwadaye kwadayenta, suna mika kawunansu ga Allah kuma suna masu bauta mishi kuma suna neman a 'yanta su, tawhidi ya hadasu kuma kuma Imani ya tausasa zukatansu ya hada  su, suna masu bayyana da'a ga Allah madaukakin sarki  suna masu kankan da kai kuma suna jayuwa a tafarkin Allah, suna masu nuna talaucinsu ga Allah suna neman bukata a wurin shi kuma suna rokon Allah, kuma suna masu yawan ambaton Allah halin zaman gida ko tafiya.
A wurare na ayyukan ibada na aikin hajji akwai abin lura da kuma wa'azuzuka, dukkan mutane a wurin Allah daya suke,ma' aunin  shi ne tsoron Allah, haka nan kuma a wurin ihrami da kuma tattaruwan mutane akwai  tunatar da su, game tattaruwan da zasu yi a matattara wato ranar alkiyama, wanda za'a karbi nashi shine wanda ayyukansa ya kasance yayishi da ikhlasi don Allah bai cakuda shi da shirka ba, ko  riya ko rashin  bin sunnar Annabi, lokutan hajji na da tsada, kuma wanda ya samu dace shi ne wanda ya ribaci wannan lokutan ta hanyan yawaita ambaton Allah da kuma Ayyuka na kwarai.
Sa'annan ku sani lallai Allah ya umarce ku da salati da aminci ga Annabinsa , sai yace cikin
Alkur'ani : ( Lalle Allah da Mala'ikunsa suna salati ga Annabi, ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi da sallama tabbatacciya.) Ahzab 56.
Ya Allah ka yi salati da aminci da albarka bisa ga Annabinmu Muhammad, Ya Allah ka yarda da khalifofinsa shiryayyu, wadanda suka yi shude akan gaskiya kuma da ita suke hukunci: Abubakr, Umar, Usman, Ali, da sauran sahabbai baki daya, ka hada mu da su cikin kyautar ka da karamcinka ya mafi karamcin masu karamci.
Ya Allah ka daukaka musulunci da musulmai, ka kaskantar da shirka da mushrikai, ka ruguza makiya addini, ka sanya wannan gari cikin aminci da kwanciyar hankali da  yalwa da suran garuruwan musulmai.
Ya Allah duk wanda ya nufe mu ko ya nufi gidajenmu ko ya nufi musulmai da mummunar manufa to ka shagaltar da shi da kansa, ka sanya kaidinsa a makasansa, ka jefa tsoro cikin zuciyarsa ya mai karfi ya mabuwayi.
Ya Allah ka amintar da Alhazai da masu Umra, ya Allah ka sanya Hajjinsu karbabbe, aikinsu abin godiya, da aikinsu  karbabbe, ya maabocin daraja da karramawa, ya Allah ka gyara musu niyoyinsu da zuriyarsu, ka saukar musu da kwanciyar hankali da natsuwa, da khushu'I da kankan da kai gare ka ya Ubangijin talikai.
Ya Allah ka gyara halin musulmai a ko ina, ya Allah ka amintar da iyakokinmu, ya Allah ka karfafi zukatan sojojinmu, ya Allah ka datar da  jifansu, Ya Allah ka basu nasara mai karfi, ya ma'abocin daraja da daukaka.
Ya Allah ka datar da jagoranmu zuwa ga shiryarwarka, ka sanya aikinsa cikin yardarka.
Ya Allah ka datar da masu hidima ga Masallatayya biyu masu alfarma, ka daga ladansu, ka sanya su cikin masoyan bayinka, ya ma'abocin daraja da daukaka.
(Ya Ubangiji ka bamu kyakyawa a nan duniya da kyakkyawa a lahira kuma ka kare mu daga azaba na wuta.) Bakara 201
Ya ku bayin Allah: (Lalle Allah na yin umarni da adalci da kyautatawa da bai wa ma'abocin zumunta. Kuma yana hani ga alfahasha da abin da aka ki da zalunci, yana muku gargadi ko zaku waazantu). Nahl 90
Ku ambaci Allah mai girma da daukaka zai ambace ku, ku gode mishi bisa ni'imominsa zai kara muku, kuma ambaton Allah ya fi girma Allah ya san abin da ku ke aikatawa.

     


الخميس، 26 يناير 2017

ADU'A DA ROKON ALLAH (HUDUBAR MASALLACIN ANNABI DAGA SHAIKH ABDURRAHMAN ALHUZAIFI

Hudubar Juma'a a Masallacin Annabi  29/4/1438 AH na sheikh Aliyu dan Abdurrahman Alhuzaifi
Da sunan Allah Mai rahama Mai jinkai.
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin kasa da sama, Mai amsa adua,yana faran ni'imomi  kuma ya yaye mummuna kuma  ya yaye bala'i,
Ina kyautata yabo ga Ubangiji na kuma ina gode mishi kuma ina tuba zuwa gare shi, ina neman gafararsa, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, ma'abocin daukaka da girmame- girmame, Na shaida Annabinmu kuma shugabanmu Muhammad bawansa ne kuma Manzonsa ne,wanda aka turo shi da cikakkiyar sharia, mai haske,ya Allah ka ka yi dadin tsira da amincinci da albarka ga bawanka kuma Manzonka Muhammad da iyalansa da sahabbansa  masu fintikau a ayyukan da'a, da ayyuka biyaya abin yabawa,
Bayan haka, ku ji tsoron Allah hakkin jin tsoronsa, duk wanda ya yi riko da takawa sai Allah ya hada masa alheri a duniyarsa da lahirarsa,wanda ya nesanci takawa zai tsiyace a karshen al'amarinsa ko da duniya ta samu a gare shi.
 ya ku musulmai!
 Allah ya kaddara sabuba na dukkan alheri da walwala  a duniya da lahira, ya kuma kaddara sababi na dukkan sharri a gidajen biyu (Duniya da lahira).To duk wanda ya riki sabuban alheri da rabauta sai Allah ya lamunce masa gyaruwar  rayuwar duniyarsa kuma a lahira ya na da karshe mafi kyau, zai dauwama a Aljanna na nii'ma, yana mai rabauta ya yardar Ubangiji Mai jinkai, Allah Madaukakin sarki ya ce : (Shin kyautatawa na da wani sakamako? (aa) face kyautatawa.)
Dun wanda ya riki  sababin sharri zai girbe sharri sakamakon aikin sa a rayuwarsa da bayan mutuwarsa,  Allah Madaukakin sarki ya ce: ( Al'amarin bai zama gurace – guracenku ba ko na Ahlul kitabi ba ne, wanda ya aikata mummunan aiki za'a saka masa da shi, kuma ba zai samu wani masoyi ba baicin Allah, kuma ba zai samu mataimaki ba.)
Ku saurara ! na daga cikin sabuba na gyaruwa da gyara da rabauta da samun alheri mai yawa da tunkude tsautsayi da bala'i da dauke musiba da ta auku, da bakin ciki akwai adua da ikhlasi tare da halarto du zuciya da naci, domin Allah na son adua kuma yana umarni da shi, kuma adua na amfani ga abin da ya faru da wanda bai faru ba, Allah ya ce :( Kuma Ubangijinku ya ce : ku roke  ni zan amsa muku, lalle wadannan da ke kangara daga barin bauta mini zasu shiga jahannama suna kaskantattu)
Adu'a shi ne ibada kamar yadda ya ke a hadisin Annu'uman dan Bashir` daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : (Adua shi ne ibada)Abu Dauda ya rawaito da Tirmizi kuma yace Hadisi ne Hasan sahih.
An karbo daga Abu  Huraira :yace ;Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:( Ba wani abu da ya fi girma a gun Allah kamar adu'a,) Tirmizi da Ibnu Hibban a sahihinsa, da hakim kuma yace " isnadin sahihi ne".
Adua abu ne da aka kwadaitar a ko yaushe, shi ibada ne Allah na bada lada mafi girma, kuma abu ne da  ke tabbatar samun biyan bukatu gaba daya na kebe da na duka na Addini da na duniya, a rayuwar duniya da kuma bayan mutuwa, sabo da amfani mai girma ga adua  Allah ya shar'anta shi,a Ibadoji na farilla bisa wajabci ko mustahabbanci domin tausayawa daga Ubangijin mu da karamci da falala, don mu yi aiki da wannan sababin  da Allah ya koyar da mu, ba don ya koyar da mu adua ba, da ba mu shiryu zuwa gare shi ba, Allah yace ;(An sanar da ku abin da ba  ku sani ba ku ko iyayenku).
To godiya ta tabbata ga Allah, godiya mai yawa  da tsarki da albarka a cikin ta, kamar yadda Ubangijin mu ke so ya kuma yarda da ita.
Kuma bukatuwa na tsananta zuwa ga adua a ko yaushe, musamman a wannan zamani da fitintinu ke bayyaana da yawa da manya musibu masu halakarwa, da aukuwan abubuwan bakanta rai ga musulmai da fitowar kungiyoyi na bidi'a da ke rarraba kan musulmai, ta halatta jini da dukiya katangaggu, tare da neman kawo hautsaniya da rusa wurare, da barna a doron kasa, kuma suna jafa'i ga ilimi da ma'abotansa, kuma suna bada fatawa bisa jahilci da bata.ga taron dagin da makiya musulunci ke yi a kan shi, da kulla makirci ga Ma'abota imani,   da tozartarwa da haifar da rarraba da sabani tsakanin musulmai , ga irin cutarwar da ke riskar dukkan daidaiku da aka fitar daga gidajen su, bisa zalunci, kuma ya cutu ga rayuwa ta yi mishi zafi yana cikin tsananin bukata, ya shiga kunci na rayuwa, to a irin wannan mawuyacin hali ,  wanda wutanta ke kona musulmai  a garuruwan da ake fitintinu, ana cikin matsananciyar bukata ta adua.
Hakika Allah ya kyautata yabo  ga wadanda su ke rokon shi suna masu kankan da kai zuwa gare shi mabuwayi idan musiba ta auku a gare su, ko tsanani, Allah madaukakin sarki ya ce game da Iyaye biyu na Halittu( Adam da Hauwa) Amincin Allah ya tabbata a gare su.(Suka ce : ya ubangijinmu mun zalunci kanmu idan baka yi mana gafara ba ka jikanmu lalle za mu kasance daga cikin tababbu)
Allah yace: (kuma lalle ne zamu jarrabe ku da wani abu na tsoro da yunwa da tawaya na daga dukiya da rayuka da 'ya'yan itace kuma ka yi albishir ga masu hakuri. Su ne wadanda idan wata masifa ta same su sai su ce : lalle ne mu ga Allah muke kuma lalle ne mu masu komawa ne a gare shi. Wadannan akwai albarka a gare su daga Ubangijinsu da wata rahama, kuma wadannan su ne shiryayyu ).
Allah ya ce game da Yunus: ( sai ya yi kira cikin duffai cewa ba abin bautawa sai kai, tsarki ya tabbata a gare ka, lalle ne ni  na kasance cikin azzalumai.)
An karbo daga Sa'ad dan Abi Wakkas yace , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Aduar Zannun yayin da ya kira shi yana cikin kifi, ba wani mutum  musulmi da zai roki Allah da shi game da wata bukata sai an amsa masa) Ahmad da Tirmizi su ka rawaito da Hakim ya ce Isnadin ingantacce ne.
Ya yin da Annabi ya kira  kabilar sakif zuwa ga Musulunci sai suka ki karban da'wansa suka jefe shi da duwatsu sai ya roki ubangijin shi yana mai cewa: ( ya Allah gare ka na ke koka raunin rashin karfi na, da kuma rashin dabara ta, da kuma irin walakanci na mutane a gare ni, ''ya mafi jin kan masu jin kai, zuwa ga wa zaka bar ni ? zuwa ga na nesa da zai hade min fiska  ko zuwa ga makiyin da ka mallaka mishi al'mari na?, in har bai kasance akwai wani fushin ka ba a gare ni, to bani da damuwa, sai dai yafiyar ka nake so, wanda yafi yalwa a gare ni,  ina neman tsari da hasken   fiskarka wanda ka haskaka da shi duffai, kuma ka gyara al'mura na duniya da lahira, kada fushin ka ya hau kaina ko kuma azabarka ta hau kaina, Ina neman  yardar ka har sai ka yarda da ni, ba dabara ko karfi sai a gare ka )
Da addua ne ake fiskantan abubuwa masu tsanani  da kuma abubuwa na bakin ciki, idan dan adam bai iya tunkudesu ba.  
Daga Sauban  daga annabi (saw) ya ce :  '' Ba abinda ke maida kaddara sai addua ba abu me kara tsawon rayuwa sai biyayya lalle mutum akan haramta mishi arziki sakamakon zunubi da ya aikata shi '' ibn hibban ya rawaito a sahihinsa da hakim kuma ya ce isnadin shi ingantacce ne
An karbo daga dan umar (ra) daga manzon Allah (saw) ya ce : '' addua na amfani ga abinda ya auku da ma abinda bai auku ba, Ya wajaba a  gareku ya bayin Alla ku riki addua '' Tirmizi ne ya rawaito shi da Hakim.
An karbo daga Abu huraira Allah ya kara yarda a gare shi  ya ce:  ( Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi  ya ce : '' lallai Allah madaukakin sarki yana cewa Ni ina nan a yadda bawa na ya zace ni  kuma ina tare da shi idan ya roke ni ''  Bukhari da muslim ne suka rawaito ,   wannan kuma ya isa lada da falala kamar yanda Allah ya zargi masu barin Addua yayin saukan ukubobi da bayyanan fitintinu 
Allah madaukakin sarki ya ce : '' kuma lallai ne hakika muna kama su da azaba sai dai basu saukar da kai ba wa ubangijinsu kuma basu yin tawali'u '' 
Allah madaukakin sarki ya ce : '' Hakika mun aika zuwa ga Al'ummai daga  gabaninka kuma muka kama su da tsanani da cuta tsammaninsu zasu kankan da kai, to don me a lokacin da tsananinmu ya je musu basu yi tawali'u ba ?  kuma amma zukatansu sun kekashe kuma shaidan ya kawata musu abinda suka kasance suna aikatawa ''  kuma Allah ya ce:'' kuma ba mu aika wani annabi  a cikin wata alkarya ba face mun kama mutanen ta da azaba da cuta tsammaninsu suna yin kaskantar da kai ''  
Kuma barin addua a lokacin bakin ciki dogewa ne akan zunubai kuma da rena damkar Allah mai tsanani  Allah madaukakin sarki ya ce: lalla damkar ubangijinka mai tsanani ne kwarai ''
(Kuma kamar wancan ne Kamun Ubangijinka, idan ya kama alkaryoyi alhali kuwa suna masu zalunci , Lalle kamunSa mai radadi ne, mai tsanani)
            Kuma lallai shi addu'a sababi ne mai girma na saukar alkhairori da albarkoki, da tunkude sharri, ko dauke shi, daga mai yin addu'ar.
            Kuma yin addu'a shine sababin da ya fi karfi domin fita daga sharrin da ya auku, da mummunan yanayin da ake ciki,
 Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma da Ayyuba a lokacin da ya kirayi Ubangijinsa lallai ne Ni, cuta ta shafe ni, kuma kai ne mafi rahamar masu tausayi * Sai muka amsa masa, sa'annan muka kwaranye abinda ke a tare da shi na cuta, Kuma muka kawo masa iyalansa da kwatankwacinsu tare da su, saboda rahama daga gare mu, da tunatarwa ga masu ibada" [Suratul Anbiya'i: 83-84]. Kuma Allah (تعالى) yace:
"Ko, Wane ne ya ke amsawa mai bukata, idan ya roke shi, kuma ya kwaranye mummuna" [Suratun Nakml: 62]. Ai, Babu wani da yake aikata hakan, sai Allah (تعالى).
Kuma Allah (سبحانه) yace:
"Ka ce Wane ne yake tsirar da ku daga duffan tudu da ruwa, kuna rokonsa bisa ga kankan da kai, kuma a boye; Lallai ne idan ka tsiratar da mu daga wannan (masifa), zamu kasance masu godiya * Ka ce: Allah ne, yake tseratar da ku daga gare ta, da kuma dukan bakin ciki, Sa'annan sai ku kuma ku ci-gaba da yin shirka" [Suratul An'am: 62-63].
            Shi Musulmi wajibi ne akansa ya rika addu'a da kwadayin Allah (تعالى) ya gyara masa sha'anoninsa, gabadaya, yana mai daga bukatunsa zuwa ga UbangijinSa gabadayansu, ya rika rokonSa kowani abu. Kuma mafi girman abin nema shine aljannah, da kubuta daga aukawa wuta, Allah (تعالى) yana fada a cikin hadisin Kudusiy:
"Ya ku bayina! dukkaniku batattu ne, sai wanda na shiryar da shi; ku nemi shiryarwata; in shiryar da ku. Ya ku bayina! dukkaninku mayunwata ne sai wanda na ciyar da shi; sai ku nemi ciyarwata; in ciyar da ku. Ya ku bayina! kowanenku tsirara ya ke; babu tufafi sai wanda na tufatar da shi; sai ku nemi tufatarwata, in tufatar da ku. Ya ku bayina ! lallai kuna yin laifi dare da rana, ni kuma ina gafarta zunubai gabadaya; sai ku nemi gafarata; in yi muku gafara", Muslim ya ruwaito shi daga hadisin Abu-zarri (رضي الله عنه). Ma'anar hadisin kuma shine: Ku roke ni shiriya, da ciyarwa, da tufatarwa da gafara.
Kuma y azo a cikin hadisi cewa:
"Dayanku ya rika rokon UbangijinSa koda akan igiyar takalminsa ne (da ya tsinke), da gishirin abincinsa".
          Kuma dayawa, addu'a ta kan canza abin da yake gudana a tarihi daga sharri zuwa ga alheri, ko kuma daga abu mai kyau zuwa wanda yafi shi kyau, Allah (تعالى) yana cewa dangane da Babanmu annabi Ibrahim (عليه الصلاة والسلام):
"Ya Ubangijinmu! Ka aiko a cikinsu, wani manzo, daga gare su, yana karanta musu ayoyinka, kuma yana karantar da su wannan littafin da hikima, kuma yana tsarkake su, lallai ne kai, kai ne Mabuwayi Mai hikima" [Suratul Bakara: 129].
 Kuma an ruwaito daga Abu-Umamah (رضي الله عنه), yace: Na ce: Ya ma'aikin Allah! Menene farkon lamarinka? Sai yace: Ni addu'ar babana ne annabi Ibrahim, kuma busharar annabi Isah, Sai mamata ta gani a mafarki cewa wani haske ya fita daga gare ta, wanda har ya haskaka benayen kasar Sham", Ahmad ya ruwaito shi. 
Kuma saboda wannan addu'ar ta annabi Ibrahima; Musulmai suka kasance cikin alheri madawwami, kai, dukkan duniya ita ma wannan addu'ar ta shafe su.
   Haka, addu'ar da annabi Nuhu (عليه الصلاة والسلام) ita ma ta kasance alheri da tsira ga muminai masu tauhidi,  kuma sharri ga mushirkai da halaka.
            Haka addu'ar da annabi Isah (صلى الله عليه وسلم) zai yi; shi da sahabbansa wadanda za a killace su a jikin dutsen ADDUR, a karshen zamani itama zata kasance nasara ce ga muminai, sa'annan halaka ga YAJUJU da MAJUJU, wadanda suke kamar farar da za ta game dukkan kasa (duniya), Mafi sharrin halitta, masu tsananin barna da ketare iyaka da girman kai,  saboda Ya zo cikin hadisin Annawas dan Sam'an (رضي الله عنه) bayan annabi Isa ya kashe MASIHU AD-DAJJAL:
"Sai Allah (تعالى) yayi wahayi ga annabi Isah (صلى الله عليه وسلم) cewa: Lallai ni na fitar da wassu bayi, wadanda wani bashi da ikon yakarsu, Sai ka killace bayina a wajen dutsen Ad-dur. Sai Allah ya tayar da Ya'ajuju da ma'ajuju alhalin suna gaggawa daga kowani tudun kasa; Sai na farkonsu su shige ta jikin wani karamin teku na dabariya, sai su shanye dukkan ruwan da ke cikinsa, Sai na karshensu su zo shigewa sai su ce: Lallai wannan, da akwai ruwa a cikinsa, To, sai a killace annabin Allah Isah (صلى الله عليه وسلم)shi da sahabbansa; har sai ya kasance kan Saniya yafi alheri ga dayansu, fiye da dinari dari ga dayanku a yau, to daga nan, sai annabin Allah; Isah ya bayyanar da kwadayinsa shi da sahabbansa (رضي الله عنهم) wa Ubangijinsu madaukaki; ta hanyar rokonsa, Sai Allah (تعالى) ya saukar da tsutsotsi a wuyan Ya'ajuju da Ma'ajuju, sai su wayi gari sun mutu, kamar mutuwar rai guda daya. Sa'annan sai annabin Allah; Isah da sahabbansa su sauka kan kasa, saidai kuma ba za su sami daidai da taki daya ba, a doron kasa face gawar Ya'ajuju da ma'ajuju da warinsu ya cike shi; Sai annabin Allah; Isah ya bayyanar da kwadayinsa shida sahabbansa (رضي الله عنهم) wa Ubangijinsu madaukaki; ta hanyar rokonsa, Sai Allah (تعالى) ya turo da wassu tsuntsaye, wadanda suke kama da wuyan rakumi, sai su tattare su; su kai su, su jefa, a wurin da Allah (تعالى) ya nufa", Muslim ya ruwaito shi.

            Kuma addu'ar da annabi (صلى الله عليه وسلم) shugaban halitta,  yayi; shi da sahabbansa, a yakin badar, itama ta kasance wata nasara ce ga Musulunci, har abada, kuma tabewa ce, ga kafirci har abada; Allah (تعالى) yana cewa:
"A lokacin da kuke neman agajin Ubangijiku sai ya amsa muku; da cewa: lallai ne Ni zan taimaka muku da dubu daga cikin Mala'iku, a jere" [Suratul Anfal: 9]. Sai Annabi (صلى الله عليه وسلم) yayi ta yin addu'a, kuma ya nace, wajen yin addu'ar, har sai da mayafinsa ya fadi, A nan ne, Abubakar (رضي الله عنه) ya rungume shi, sa'annan ya ce:  Yadda kake yin magiya wa Ubangijinka, ya isa, ya ma'aikin Allah! Kuma lallai Allah zai cika maka abinda ya yi maka alkawari. Sai Annabi ya ce :Albishirinka ya Abubakar , ga Jibrilu Amincin Allah ya tabbata a gare shi,yana tunkude kura a kan hakwaransa, kuma mala'iku basu taba yaki da wani Annabi ba kafin shi, kuma an kebe shi da wannan sabo da cikan falalarsa  Amincin Allah su tabbata a gare shi,da karfin yakinin shi da halayen sahabbansa Allah ya kara yarda a gare su.

    Kuma lallai yin addu'ar taimakon gaskiya, da ruguje barna, yana daga nasiha ga Allah da littafinSa, da ManzonSa, da jagororin Musulmai, da kuma sauran Mutanensu.
            Kuma babu wanda zai guje wa yin addu'a, yana mai kaurace masa face wanda ya tozarta rabonsa a duniya da lahira, sa'annan ya tozarta abinda ya wajaba akansa na hakkin Musulunci da Musulmai. Ya zo a cikin hadisi cewa:
"Duk wanda bai himmatu da lamarin Musulmai ba to baya cikinsu".
            Kuma da a ce, za mu yi ta bibiyar fa'idojin addu'a da albarkokinsa, da alherorinsa, da sakamakonsa, dadada, kuma ababen mamaki, to da, ambaton hakan yayi tsayi. Saidai abinda muka riga muka yi ishara, a baya, ya isar.
           
            Kuma lallai addu'a yana da SHARRUDA, DA LADDUBA;
Kuma yana daga cikin sharrudan addu'a: Cin abinci na halal, da sanya tufar halal, Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace wasahabinsa Sa'ad dan Abiy-Wakkas (رضي الله عنه):
"Ka kyautata abincinka; sai a amsa maka addu'arka".
Kuma yana daga cikin sharrudansa: Riko da Sunnah, da kuma amsawa Allah (تعالى) ; ta hanyar aikata abubuwan da ya yi umurni, da nisantar abubuwan da yayi hani, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma idan bayina suka tambaye ka dangane da ni, ka ce: Lallai ni, a kusa nake, ina amsa addu'ar mai addu'a idan ya roke ni, Sai su nemi amsawata, kuma su yi Imani da ni, tsammaninsu za su shiryu" [Suratul Bakara:186]. Kuma Allah (تعالى) yace:
"Kuma yana amsawa wadannan da suka yi imani,  suka kuma aikata aiyukan kwarai, kuma yana kara musu sakamako daga falalarsa" [Suratush Shurah: 26].
 Mutumin da aka zalunce shi, shi kuma ana amsa masa, idan yayi addu'a; koda kuwa kafiri ne, ko dan bidi'a.
            Kuma yana daga cikin sharrudansa: Yin ikhlasi da halarto da zuciya, da yin naci, wa Allah, da yin gaskiya cikin neman mafaka, daga Ubangiji (تعالى), Allah ta'alah yana cewa:
"Sai ku roki Allah kuna masu tsarkake addini a gare shi, ko da kuwa kafirai sun ki" [Suratul gafir: 15].
Ya zo cikin hadisi cewa, "Allah baya karbar addu'a daga zuciya rafkananniya mai wargi".
            Kuma yana daga cikin sharrudansa: Kada ya yi, addu'a da sabo, ko yanke zumunta, kuma kada ya ketare iyaka, cikin addu'a.
            Kuma yana daga cikin sabbuban amsa addu'a: Yin yabo wa Allah (تعالى) da sunayensa mafiya kyau, da sifofinsa madaukaka, tare da yin salati wa annabi (صلى الله عليه وسلم); Ya zo cikin wani hadisi cewa; Lallai annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ji wani Mutum yana cewa:
"Ya Allah, lallai ne Ni ina rokonka , da shaidawata cewa babu abin bautawa da gaskiya sai kai, Makadaici, Wanda ake nufi da biyan bukata, wanda bai haifu ba, kuma ba a haife shi ba, kuma bashi da wani wanda yake daidai da shi, Sai yace: Lallai ne, ka roki Allah da sunanSa da yafi girma; wanda idan aka roke shi da shi ya kan bayar, idan kuma aka yi addu'a da shi, ya kan amsa", Abu-dawud ya ruwaito shi, da Attirmiziy, kuma yace: Hadisi ne mai kyau (hasan).
Da kuma Ibnu-Majah da Ibnu-Hibbana, da Alhakim, daga hadisin Buraidah (رضي الله عنه).
An kuma ruwaito daga Fadalah dan Ubaid  (رضي الله عنه), yace: Wata-rana Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana zaune, sai wani Mutum ya shigo yayi sallah, Sa'annan ya ce:
"Ya Allah, ka gafarta mini, ka yi mini rahama, Sai Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace: Ka yi gaggawa ya kai mai sallah, Idan ka zo sallah; sai ka zauna, to ka yi godiya wa Allah da abin da ya cancance shi, San'annan sai ka yi min salati, Sa'annan sai ka roki Allah", Ahmad ya ruwaito shi, da Abu-dawud, da Attirmiziy, kuma yace: Hadisi ne hasan.
A cikin wani hadisin kuma:
"Lallai addu'a yana rataye tsakanin sama da kasa har sai ya yi salati wa Annabi (صلى الله عليه وسلم)".
            Kuma yana daga cikin ladduban addu'a da sharrudan karbarsa: Kada ya yi gaggawar  neman amsawa, A'a yayi hakuri, Ya zo a cikin hadisi cewa:
"Za a amsa wa dayanku matukar bai yi gaggawa ba; yace: Na roka, na roka, amma ba a amsa mini ba", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi, daga hadisin Abu-hurairah (رضي الله عنه).
            Kuma lallai, dawwama kan addu'a (da yawaita yinsa), a tare da shi akwai amsawa, Ya zo cikin hadisi cewa:
"Babu wani Musulmi a bayan kasa, wanda zai roki Allah da wata addu'ar face, Allah ya bashi ita, ko kuma ya tunkude masa wani mummunan kwatankwacinta, matukar bai roki sabo, ko yanke zumunta ba. Sai wani Mutum yace: To, lallai za mu yawaita! Sai yace: Allah zai fi ku yawaitawa", Attirmiziy ya ruwaito shi, kuma yace: Hadisi ne, hasan sahih, kuma Alhakim ya ruwaito shi daga riwayar Abiy-Sa'id, sa'annan ya yi kari a cikinsa: Ko kuma, a ijiye masa kwatankwacin addu'arsa.
            Kuma ya dace, Musulmi ya yi kirdadon lokutan amsa addu'a, An ce wa Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم):
Wace addu'a ce, aka fi amsawa? Sai yace: "Ta karshe dare, da bayan sallolin farilla", Attirmiziy ya ruwaito shi, yace: Hadisi ne, hasan, daga hadisin Abiy-Umamah. Kuma ya zo cikin wani hadisin cewa:
"Ubangijinmu yana sauka zuwa ga saman duniya, a cikin daya bisu ukun dare na karshe; Sai ya ce: Wa zai yi roko sai na amsa masa, Wa zai tambaye ni sai na bashi, Wa zai nemi gafara ta sai na gafarta masa", Bukhariy ya ruwaito shi, da Muslim daga hadisin Abu-hurairah.
            Da kuma tsakanin kiran sallah da yin ikamah, Nan ma ba a mayar da addu'a: Ya zo cikin hadisi cewa:
"Lokacin da bawa yafi kasancewa kusa da UbangijinSa shine a lokacin sujjada; Sai ku yawaita addu'a", Muslim ya ruwaito shi daga hadisin Abu-hurairah.
            Da kuma lokacin ganin ka'abah, da lokacin saukan ruwa, da hali na bukatuwa, da bayan kammala alkur'ani gabadaya, da bayan yin sadaka.
            Ka yi mamakin girman rabauta, da nasara, da samun ladan Mutumin da ya killace zuciyarsa, ga Allah (تعالى); yana rokonSa, yana fatanSa, yana kuma dogara akanSa, yana neman taimakonSa.
            Da kuma tabewa, da girman shirka ko kafircin wanda yake rokon kabari, ko yake neman agaji daga Annabawa (عليهم الصلاة والسلام), da waliyyai, ko yake rokonsu koma bayan Allah (تعالى), ko yake daga bukatunsa zuwa ga wani mala'ika makusanci, ko wani annabi mursali; saboda Annabawan Allah (عليهم الصلاة والسلام) sun zo ne, don kiran Mutane, cewa su kebe Allah (تعالى) da yin roko a gare shi, sa'annan su kadaita shi da bauta shi kadai. Su kuma waliyyai an umurce mu da mu rika yin aiki irin nasu, sa'annan mu so, su, kuma aka hane mu, kan rokonsu, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma lallai masallatai na Allah ne, kada ku roki wani tare da Allah"[suratul Jinn: 18]. Kuma Allah (تعالى) ya ce:
"Kuma ka ce: Kawai ni, ina rokon Ubangijina ne, kuma ba zan tara kowa da shi ba" [Jinn: 20].       
Kuma wanda baya halarce, da matattu babu wani daga cikinsu da yake amsa addu'a; saboda addu'a babu mai amsa shi idan ba Allah Mabuwayi da daukaka ba, Allah (سبحانه) yana cewa:
"Kiran gaskiya nasa ne, Wadanda kuma suke rokon waninshi basa amsa musu da komai, face kamar mai shumfuda tafukansa zuwa ga ruwa domin ya kai ga bakinsa, kuma shi ba mai kaiwa gare shi ba ne, Kuma kiran kafirai (ga wanin Allah) bai zama ba, face a cikin bata" [Suratur Ra'ad: 14]. Kuma Allah (تعالى) yace:
"Babu wanda ya fi bata fiye da wanda ke rokon wanin Allah, wanda ba zai amsa masa ba, har ranar kiyama, alhalin (wadanda ake rokan) sun gafala da kiran masu kiran * Kuma idan aka tattara mutane, za su kasance abokan gaba a gare su, kuma za su kasance masu kafircewa ga bautan da suka yi a gare su" [Ahkaf: 5-6].
Kuma Allah (تعالى) yace, alhalin yana bada labarin aiyukanSa:
"Yana shigar da dare a cikin yini, kuma yana shigar da yini cikin dare, kuma ya hore wata da rana; kowannensu yana gudana zuwa ga ajali ambatacce. Wannan shine Allah Ubangijinku, mulki nasa ne, kuma wadanda kuke roka waninSa basa mallakar ko da fatar kwallon dabino * Idan kuka roke su, to ba za su ji kiranku ba, koda sun ji to ba za su amsa muku ba, kuma a ranar kiyama za su kafirce wa shirkarku, kuma babu mai baka labari, kamar wanda ya sani", [Fadir: 13-14].
            Kuma lallai Allah bai yi izinin a roki waninSa ba, duk irin kusancin da yake da shi, Allah (تعالى) yana cewa:
"Almasihu ya ce: Ya ku 'ya'yan Isra'ila, Ku bauta wa Allah; Ubangijina, kuma Ubangijinku; lallai ne duk wanda ya yi shirka da Allah to, lallai Allah ya haramta masa aljanna, kuma makomarsa itace wuta, kuma babu wasu mataimaka ga azzalumai" [Ma'idah: 72]. Kuma me tsarki da daukaka (Allah) ya ce ''kuma baya umurninku da ku riki mala'iku da annabawa iyayengiji . shin ze umarceku da kafirci ne bayan kun riga kun zama masu sallamawa (musulmi) .
Ya zo cikin hadisi cewa: "Wanda ya mutu alhalin yana rokon wani koma bayan Allah ya shiga wuta", Bukhariy ya ruwaito shi daga hadisin Abdullahi dan Mas'ud (رضي الله عنه).

            Ya kai Musulmi!!
            Wannan shine littafin Allah, da hadisan ManzonSa (صلى الله عليه وسلم) suna bayyana maka cewa, lallai ADDU'A shine BAUTA, kuma lallai Allah mabuwayi da daukaka shine kawai ya kebanta da addu'a, ba a yinsa sai ga Allah madaukaki, kuma duk wanda ya hada wani da Allah a cikin addu'a to wannan mushirki ne mai babbar shirka.
Kuma kada wani ya yi koyi da wani cikin bata da shirka; saboda shirka da kafirci basu auku a cikin 'ya'yan Adam ba face, da sababin takalidanci, da bin mutane batattu, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma shin wancan, shine mafi zama alheri ga liyafa, ko kuma itaciyar zakummi * Lallai Mu mun sanya ta fitina ga azzalumai * Lallai ita wata bishiya ce, wadda take fita daga asalin wutar jahima * Fudarta, kai kace kayukan shedanu ne * Lallai su hakika masu ci ne daga gare ta, sa'annan masu cika cikinsu ne daga gare ta * Sa'annan suna da wani gauraye a kanta, daga ruwan zafi * Sa'annan lallai makomarsu izuwa ga wutar jahimu take * Lallai su, sun iske Ubanninsu suna batattu *  Sai suka kasance akan gurabansu suke ta yin gaggawa" [As-safat: 62-70].
Kuma Allah (ta'alah) yana cewa:
"Kuma ku roki Ubangijinku da kankan da kai, da kuma a boye, Lallai ne shi, baya son masu ketare iyaka, kuma kada kuyi barna a cikin kasa bayan gyaranta kuma ku kirayeshi saboda tsoro da tsammani : lallai ne rahamar Allah makusanciya ce daga masu kyautatawa" [A'araf: 55].

            ALLAH YAYI MINI ALBARKA, NI DA KU A CIKIN ALKUR'ANI MAI GIRMA.

HUDUBA TA BIYU
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah Mai rahama, Mai jin kai, Mabuwayi Mai hikima, Ma'abucin sunaye da suka fi kyau, da sifofi madaukaka.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai yake bashi da abokin tarayya, Madaukakin da Yafi daukaka.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawansa ne manzonsa ne Zababbe.
Ya Allah ka yi dadin salati da sallama da albarka, ga bawanka kuma manzonka Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa Masu takawa.
Bayan haka:
Ku kiyaye dokokin Allah, sai ya gyara muku aikyukanku, sa'annan ya sanya ku daga cikin masu rabauta a yanzu, da kuma bayan komawa izuwa ga makoma.

Ya ku Bayin Allah!
            Ku kasance, masu bayyanar da kwadayi zuwa ga Allah, masu dawwamar da yin roko a gare shi (da yawaitawa); saboda Duk wanda ya roki Allah baya tabewa, wanda kuma ya yi fatan samun Allah ba a hana shi.
Umar Allah kara yarda a gare shi yace : Lalle ni ba na dorawa kai na damuwar amsa adua sai dai na kan damu da yin aduar, in har an min dacen yin adua to Allah ya lamunce amsa aduar.
Kuma kowani Mutum yana da bukatun da suke sabuntuwa, da ababen nema a kowani lokaci masu yawa; Don haka; Sai kowa ya roki UbangijinSa, duk abinda ya san alheri ne. kuma ya yi wa Musulmai da aka zalunta a addini adu'a, ya kuma nemi tsarin Allah daga  duk abinda ya san sharri ne.
Kuma mafi girman abin roko shine neman samun yardar Allah, da kuma aljannah.
Shi kuma mafi girman abin da ake neman tsari daga gare shi, shine wuta da sabubanta.
Kuma Mutum Musulmi ya yi naciyar rokon abinda ya dame shi, daga wajen Ubangijinsa; saboda Allah Mawadaci ne, Mai karimci, Abun godiya, Mai yawan baiwa, Mai girma, Mai iko, Allah madaukaki yana cewa:
"Ya ku bayina! Da, na-farkonku da na-karshenku, da mutanenku da aljanunku zasu tsaya a bigire daya, sai kowanne ya roke ni, sai in bada kowanne daya abinda ya roka; to ba zai rage komai daga cikin abinda ke wurina ba sai kamar gwargwadon abinda allura ta rage; idan aka tsoma ta a cikin ruwan teku", Muslim ya ruwaito shi/
 ya zo a hadisi :Wanda bai roki Allah ba zai yi fushi da shi,

            Kuma mustahabbi ne, Musulmi ya riki addu'oi masu gamewa, wadanda suka zo daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), kamar fadinsa madaukakin sarki:
"Ya Ubangijinmu ka bamu mai kyau a Duniya, a lahira ma mai kyau, ka kare mu daga azabar wuta" [Bakara: 201].
Da kuma misalin
"Ya Allah, lallai ne Ni ina rokonka aljanna da abinda ya kusantar zuwa gare ta na zance ko aiki, Kuma ina neman tsarinka daga wuta da kuma abinda ya kusantar zuwa gare ta na zance, ko aiki".

            Ya ku bayin Allah!
             "Lallai Allah da Mala'ikunSa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi domin amintarwa" [Ahzab: 56].