Ni'imomin Allah ga bayinSa suna da yawa ba za'a
iya iyakance su ba,mai dunbin yawa ne da ba za a iya kwalkwale su ba, suna
bibiyan juna basu karewa :Allah Madaukakin Sarki ya ce : (Allah ne wanda ya halicci sammai da kasa, kuma ya saukar da
ruwa daga sama sa'anan ya fitar game da shi daga 'ya'yan itace, arziki domin ku, kuma ya hore jirgin ruwa yayi gudu a
cikin teku da umarninSa, kuma ya hore muku koguna.kuma ya hore muku rana da wata
suna madawwama biyu, kuma ya hore muku dare da wuni. Kuma ya baku dukkan abin
da ku ka roke shi, kuma idan kun kidaya ni'imar Allah ba za ku lissafe ta ba,
lalle ne mutum hakika mai yawan zalunci ne mai yawan kafurci ).
Samuwan abubuwa masu amfani da tunkude cutarwa da ma dukkan alheri da bawa yake samu
ni'ima ce daga Allah zuwa gare shi ; na ilimi da imani da aiki da zuriya da
masauki da abin hawa da walwala da nasara Allah Madaukakin sarki ya ce (kuma abin da ya ke a gare ku na ni'ima to daga Allah ne)
kuma lura da abin da ya ke kewaye da mu yana kaimu ga jin niimar Allah , Allah
madaukakin sarki ya ce (To mutum ya duba zuwa ga
abincinsa) kuma ya ce (To mutum ya duba daga me aka halicce shi).
Muminai na dubi ga ni'imar Allah na ciki da na
waje: hakan sai ya kara musu imani ya kusanto da su ga Ubangijinsu suna masu
ikirari da baiwarsa da alherinSa da falalarSa a gare su, Allah madukakin sarki
ya ce : (suna yin gori gare ka don sun musulunta,
kace kada ku yi gorin kun musulunta a kai na, Aa Allah ne ke yi muku gori domin
ya shiryar da ku ga imani, idan kun kasance masu gaskiya.)
Mumini da kaifin hankalinsa da nunan tunaninsa;
na dubi ga ni'imomin Allah da ke kewaye da shi, Allah madaukakin sarki ya ce
yana mai sifanta halin muminin da zai karbi aikinsa
: (Har a lokacin da ya kai ga mafi karfinsa,kuma ya kai shekara arba'in yace ya
Ubangiji na! ka kange ni, domin in godewa ni'imarka, wadda ka ni'imta a kaina,
da kuma a kan mahaifa na biyu, kuma domin in aikata aikin kwarai, wanda ka ke
yarda da shi)
Idan zuciyar bawa ta cika da imani; ni'ima ta godiya ga ni'imar sai ta
tabbatu a gare shi, sai kai komonsa su
gyaru halayensa su tsarkaka,sai ya yi dace, Allah madaukakin sarki ya ce yana
mai gori ga bayinSa: (kuma Allah ya soyar da imani a
gare ku, kuma ya kawata shi a cikin zukatanku, kuma ya kyamatar da kafirci da
fasikanci da sabo zuwa gare ku, wadannan sune shiryayyu. Bisa ga Falala daga
Allah da ni'ima, kuma Allah Masani ne Mai hikima).
Ikirari da ni'imar Allah na daga cikin abin da
ke hukunta tuna ni'imomin Allah, da kuma jingina su ga wanda ya bada su - daukaka
ya tabbata a gare shi,- wanda ke dakon ni'imomi to ba zai gushe ba yana tuna
mai bada su, wanda shi ne Allah Madaukaki
Mai ni'imtarwa da dukkan ni'imomi wadanda muke jujjuyawa a cikinta,
Yin ikirari da ni'imar Allah shine mabudin
dukkan Alheri, zai sanya harshen mumini yana furta (Dukkan
yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Mai mulki ranar sakayya)
a tsawon wuninsa da darensa.
Idan musulmi ya tabbatar da ni'imar Allah a kan
sa, ya yi ikirari da falolin UbangijinSa da ke kewaye da shi,; to lalle zai yi
amfani da wadannan ni'imomin wurin neman yardar Allah Madaukaki, ga Annabi
Sulaiman Amincin Allah ya tabbata a gare shi yana rokon UbangijinSa; (ya Ubangiji ka cusa mini in gode wa ni'imarka, wadda ka
ni'imta ta a gare ni, da kuma ga mahaifana biyu, kuma in aikata aiki na kwarai,
wanda kake yarda da shi, kuma ka shigar da ni sabo da rahamarka a cikin bayinka
salihai,)
Ga Annabi musa abokin maganar Allah yana kulla
alkawari ga Ubangijinsa ; ( Yace Ya Ubangiji! Domin abin da ka ni'imta shi a kai na saboda
haka ba zan kasance mai taimako ga masu laifi ba)
Idan musulmi ya tabbatar da ni'imar Allah a kan
sa, to zai bayyana wadannan ni'imomin ne halin yana mai godiya da yabo, ba yana
mai alfahari da girman kai ba, Allah madukakin sarki ya ce: (kuma amma ni'imar Ubangijinka sai ka fada
(domin godiya). Wato ka labarta wa mutane abin da Allah ya ma na
ni'ima kana mai girmama wa ga Mai ni'imtarwan.
Ya zo a hadisi (
Idan Allah ya yi ni'ima ga bawa to yana so ya ga gurbin ni'iman a gare shi).Baihaki
ya rawaito da isnadi hasan.
An karbo daga Abul Ahwas Aufu dan
malik dan Nadlah daga Babansa yace :( Na zo ga Manzon Allah a halin ina wani
yanayi na tufafi mara fasali, sai ya ce : kana da dukiya? Sai na ce :E, sai
yace daga wani irin dukiya? Sai na ce : daga dukkan nau'i Allah ya bani; na
daga rakuma da bayi da dabbobi, sai yace : To idan Allah ya baka dukiya ta aga
hakan tare da kai).Ibnu Hibban ya rawaito a sahihinsa
Idan ni'imomi sun tattaru ga rayuwar
bawa ;to fa wani albishir ne na alheri ga ma'abocinsu muddin ya fahimci
hakkinsu da ke kan shi kuma ya sauke wajibi, kuma ya sarrafa su ta hanyar da ke
nuna godiya da bauta ga Allah.Amma wanda ya rudu da kansa ya yi jiji da kai da
abin da Allah ya bashi na ni'ima har ma ya jinginta ta ga kansa kamar yadda
Allah ya ambata a kur'ani bisa harshen Fir'auna yayin da ya ke cewa : (kuma Fir'auna ya yi kira a cikin mutanensa, yace : ya
mutane na! ashe mulkin masar ba a gare ni yake ba? Kuma wadannan koguna suna
gudana daga karkashi na? ashe ba ku gani ba)
Haka ma
Karuna yace( An bani shi akan wani ilimi wanda yake
gare ni kawai)
To irin wannan ni'imar ce take juyawa azaba
alherinta ya zama sharri samunta ya zama bala'i.
Mafi girman godiya ita ce gaggauta wa zuwa ga
ibada Allah yace (A'a Allah kadai zaka bauta wa kuma
kasance cikin masu godiya).
To kuma idan bawa ya yi kokari wurin bautawa
Ubangijinsa yana mai godiya a gare shi bisa ni'imominsa, to lallai sakayyarsa a
gurin Allah na daga cikin irin aikin da ya yi. Allah Madaukakin sarki ya ce : (Lalle wannan ya kasance sakayya a gare ku, lalle aikin ku ya
kasance abin godewa).
Bawa ba zai iya sauke nauyin godiyan ni'immomi
ba duk yadda ya yi kokari , ya isan mishi ya yi kokari ya samu yardan Allah
Madaukaki! Ya samu ya yi godiya na gabadaya da godiya na musamman, a duk
lokacin da ni'ima ta sake samuwa sai ya sake mata sabuwar godiya. Ya zo a hadisi Manzon Allah tsira da amincin Allah su
tabbata agare shi ya ce (wanda ya ce idan ya wayi gari; Ya Allah abin da ya
wayi gari da ni na ni'ima ko wani daga cikin halittunka to daga gareka ne yake
kai kadanka baka da abokin tarayya kuma dukkan yabo da godiya naka ne to hakika
ya sauke nauyin godiya na wannan rana, wanda ya ce idan ya yi yammaci Ya Allah
duk abin da ya yi yammaci da ni na ni'ima ko daya daga cikin halittunka to daga
gareka yake kai kadanka baka da abokin tarayya, to yabo da godiya ya tabbata
agreka to hakika ya sauke nauyin godiya na wannan dare).
kuma (An karbo daga Rifaa dan Rafi' Azzuraki ya ce mun kasance
wata rana muna salla a bayan Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare
shi ya yin da ya daga kansa daga ruku'u kuma ya ce :Allah ya amsa ga wadanda
suka gode mishi sai wani mutum a bayan shi ya ce:Ubangijinmu godiya ta tabbata
gareka ,godiya mai yawa tsarkakakkiya mai albarka a cikinta yayinda Manzon
Allah ya idar da sallah sai ya ce: wanene yayi magana dazu? sai wanan mutumi ya
ce nine ya manzon Allah! sai manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare
shi ya ce hakika naga mala'iku talatin da dori suna rige rige waye zai fara
rubuta ta )Hakim ne ya rawaito da ibnu hibba da isnadi ingantacce
Musulmi zai yi gaggawa zuwa kofan adu'a yana
rokon Ubangijinsa da ya mishi ilhama na godiya, domin ya kankare tawaya da
nakasa, ababin niimomi (kuma ka samu masu godiya
bisa niimarka masu kuma kyawtata yabo da ita agare ka to ka karbe ta ka cikata
agare mu )Ibnu Hibban ne ya rawaito.
Amma wanda idonsa ya makance daga
ganin ni'imomin Allah to hakika wannan ya fada
rabon shaidan da waswasinsa da makircinsa, kura'ani ya hakaito hakan
daga gare shi (saannan zan zo musu daga gaba garesu
kuma daga baya garesu kuma daga damansu da kuma hagunsu ba za ka samu mafiya
yawansu ba suna masu godiya)
Musulmi na gafala daga riskan ni'imomin
Allah a gare shi yana mai rainata ma a
lokacin da ya ga abin da ke hanun wasu na ni'imomi.
A cikin sahihu muslim daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce :Manzon
Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(ku yi dubi zuwa ga
na kasa da ku kar kuyi dubi zuwa ga wanda ya ke sama da ku domin haka ya fi
dacewa don kar ku rena niimar Allah a gare ku.
Na daga cikin munanta ladabi ga Allah dulmuya cikin ni'imomi da manta Mai yin
ni'imar da kuma zurfafa wa cikin farin ciki da manta Mai yaye bakin ciki da bacin rai, Allah Madaukakin sarki ya ce (kamar wancan ne Allah ya ke cika niimarsa a kanku tsammaninku
kuna mika wuya )
(To idan sun juya to abin da
ya wajaba a kanka shi ne isarwa bayyananniya) (suna sanin niimar Allah sa'annan
kuma suna musantawa kuma mafi yawansu kafirai ne )kuma ya ce: (kuma wanda ya musanya
niimar Allah bayan ta zo mishi to lalle ne Allah mai tsananin ukuba ne).
Huduba
ta biyu
Mai hankali ya na kiyaye amfani da ni'imomin Allah ba tare da ya yi sakaci da
hakkin Allah a ciki ba da bauta da
godiya, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (Idan ka ga Allah yana
baiwa bawa abin da ya ke so alhali shi kuma bawan yana saba mishi to lalle
hakan a gareshi daurin talala ne sannan sai aka yayeta da wannan ayan(saannan kuma A lokacin da
suka manta abin da aka tunatar da su da shi sai muka bude a kansu kofofin
dukkan kome har a lokacin da suka yi farinciki da abin da aka basu, muka kama
su kwasam, sai gasu sun yi tsuru- tsuru, sai aka katse karshen mutanen,wadan da
suka yi zalunci, kuma godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai ) Ahmad da Baihaki ne
suka rawaito Albani ya inganta shi.
Kuma musulmi na sanya bautarsa a
hade da abin da ya ke riska na ni'ima, idan an bashi ni'ima sai ya yarda in an
dauke sai ya yi fushi, to wannan sifa ce abin zargi,
Allah Madaukakin sarki ya ce (kuma cikin mutane akwai mai bauta wa Allah bisa gefe,
sa'annan idan wani alheri ya same shi sai ya natsu da shi, kuma idan wata
fitina ta same shi sai ya juya baya akan fuskarsa ya yi hasarar duniya da
lahira.
An karbo daga
Abdullahi dan Abbas Allah kara yarda a gare su, yace: (kuma cikin
mutane akwai mai bauta wa Allah bisa gefe,) Mutum
ne zai zo Madina idan matarsa ta haifi da dokin sa ya haihu sai ya ce : wannan
Addini ne mai kyau, idan matarsa bata haihu ba dokin sa bai haihu ba sai ya ce
: wannan mummunan addini ne).