Hudubar farko
Kiyaye hakkokin jama'a na
daga cikin abubuwa na tushe kuma na kat da shariar musulunci ta karfafa, sawaun
ta bangaren bata kariya ko kiyaye ta, na daga cikin abin da wasu mutane ke
sakaci da shi akwai baiwa masu hakki
hakkokinsu musamman bashi, wanda ke kan mutum na rance,na farashin wani abu da
ya saya ko rance da ya ranta, ko ladan wani dan kodago ya yi mishi aikin kodago,da
makamantarsu.
To abin da ya ke wajibi ga
musulmi ya yi kokarin sauke nauyin da ke kansa, ya biya abin da ke kansa na
hakkin 'yan uwansa Allah Madaukakin sarki ya ce :(kada
ku ci dukiyarku a tsakaninku ta hanyar barna).
Lalle abin da ya ke farilla
akan kowane musulmi na dole ya bada gabadayan hakkokin halittu, cikakke ba tare
da ya tawaye ba, na daga cikin bayyanannen laifi da zunubi mai girma akwai
sulalewa daga biyan basuka ko gujewa masu hakkin, da kin biyan bashin da
jinkirta shi sai gaba mai zuwa tare da halin biya, Annabi tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi ya ce :(zalunci ne
mawadaci ya jinkirta biyan bashi).Muslim ne ya rawaito.
Almadalu shine jinkirta biyan
hakki da ya dace a biya tare da halin biya da iko, amma ya ki biya akan lokacin
to ya aikata haramun ya kuma fada cikin zalunci ga ma'abota hakki na daga cikin halittu,
karshen zalunci hasara ne kuma abin kunya ne duniya da lahira.
Ya 'yan Uwa Musulmi!
Bashi al'amarinsa babba ne, shaninsa
mai girma ne a musulunci, sabo da haka ne Abu Huraira Allah kara yarda a gare
shi yace zaa zo ga Annabi da mammaci wanda akwai bashi a kansa sai ya ce :(Shin
ya bar abin da zaa biya bashinsa da shi? In an bada bayanin cewa ya bar abin biya sai ya mishi sallah,in ba
haka ba sai yace : ku yi sallah ga sahibinku,) Hadisin Bukhari da Muslim ne
suka rawaito.
To ya
kai wanda bai damuwa da biyan bashi, bai kulawada hakkin mai hakki, ka ji
tsoron Allah Ubangijinka !
Muslim ya rawaito a sahih na
shi daga Abdullahi dan Amr Allah kara yarda a gare shi ya ce : (Ana gafartawa dukkan shahidi sai wanda akwai bashi a
kansa)
Haka
kuma a gun nasa cewa wani mutum ya zo ga Annabi tsira da amincin Allah su
tabbata agare shi sai ya ce:ya Manzon Allah, shin yanzu in an kashe ni a
tafarkin Allah zaa gafarta min dukkan zunubai na? ya ce :E a halin kana mai
hakuri kana neman lada kana mai fiskanta ba mai juya baya ba, ban da bashi,
dazu Jibrilu ya fada min haka.)
To ya kai Musulmi ka sauke
hakkin wani da ke kanka, ka kiyaye jinkirta biyan bashin dukiyan mutane a halin
kana da kuduran biyanta, to ka gaggauta kafin wucewan lokaci,sanda zai zama ba
wani abu na hakkokin halittu sai daukan fansa da kyawawa ko munana, Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata agare shi
sai ya ce:( Duk wanda ya ke da wani hakki akansa na zaluncin dan uwansa game da
mutuncinsa ko wani abu to ya warware daga gare shi a yau kafin ya zama dinari
ko dirhami, in ya lasance yana da ayyukan kwarai sai a dauka daga gare shi
gwargwadon abin da ya zalunce shi, to idan bai da kyawawa sai a dauka daga
laifukan sahibin nasa sai a dora mishi).
Nasa'i
ya rawaito daga Muhammad dan Muhsin Allah kara yarda a gare shi ya ce"(Mun
kasance zaune a gurin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare
shi, sai ya daga kansa zuwa sama, sai ya sanya tafin hanunsa akan goshinsa,
sannan ya ce : (Tsarki ya tabbata ga Allah! Me aka saukar na tsanani? Sai sahabbai
suka yi shuru suka firgita da gari ya waye sai na tambaye shi ya Manzon Allah wani tsanani ne wanda ya sauka? Sai ya ce
: Na rantse da wanda rai na ya ke hanun shi , da ace wani
mutum za a kashe shi a tafarkin Allah sannan a raya shi sannan a kashe shi sannan a
raya shi , sannan a kashe shi alhali
akwai bashi akan shi to da ba zai shiga Aljanna ba har sai anbiya mishi wannan
bashin .)
YA DAN UWANA MUSULMI:
Ka kasance cikin himma na gaskiya wurin sauke nauyin
halittu kuma ka halarto da kyakkyawar
niyya a lokacin biya da cika
alkawari Manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata agare shi ya ce :- (Duk
wanda ya karbi dukiyan mutane da nufin
zai biya to Allah zai biya mishi ) buhari ne ya rawaito
Kai kuma mai bin bashi ka kasance mai rangwame mai saukin
hali mai kyauta , duk wanda ya kasance yana cikin matsanancin hali ka yi mishi
rangwame zuwa sanda zai samu , sabo da
fadin Allah madaukakin sarki :-( Idan ya kasance
matalauci ne to a jinkirta mishi
zuwa lokacin da Allah zai hore mishi )
Daga cikin ayuka masu falala akwai
; yin hakuri ga wanda bai samu ba
da yafewa wanda ya rasa , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya
ce:(Wani attajiri ya kasance yana bawa
mutane bashi idan ya ga wanda ya gagara biya sai ya ce wa yaran shi
ku yafe mishi ko muma Allah zai yafe mana
to kuma sai Allah ya yafe mishi ).
A ruwayar musulim Allah madaukakin sarki ya ce :-(Mu muka fi dacewa da hakan bisa gare shi to a yafe mishi ). Ya zo a hadisi kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce:(Duk wanda ya saukake wa wanda ke mawuyacin hali to Allah zai saukake mishi a duniya da
lahira ) Buhari da muslim ne suka
rawaito.
YA KAI DAN UWA MUSULMI:
To ka ribaci
ladannan mai girma da falala mai auki ta hanyar tausayawa wanda ya rasa
, kana mai jinkirtawa zuwa ga wani ajali ko kuma ta hanyar yin rangwami da kubuta
daga hakki wannan shi ne lada mafi girma
da sakayya mafi yalwa .
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi
ya ce:-( duk wanda ke son Allah ya tsiratar da shi daga bakin
ciki na ranar alkiyama to ya yayewa
matalauci ) Muslim ne ya rawaito
HUDUBA TA BIYU
Yana daga cikin abin da musulunci ya wajabta akwai cika
ladan mai kodago , Manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:-(ku
bawa mai aikin kodago ladan sa kafin zufan sa ya bushe) wasu malamai masu tantancewa sun ce hadisi
ne mai kyau .
To ya haramta a tawaye hakkin sa ko a rika cewa sai nan
gaba , kan haka ne ma Allah
madaukakin sarki ya ce:-(mutum uku ni ne zanyi musu da su ranar alkiyama sai ya ambata daga cikin su:- da mutumin da ya
dauki hayan dan kodago, ya nemi ya
cikata mishi ya nemi hakki daga gunshi
bai bashi ladan shi ba) Buhari ne ya
rawaito