الخميس، 25 مايو 2017

GODIYA GA ALLAH



Hudubar juma'a na masallacin Annabi tare da sheikh Salah Bin Muhammad Al Budair
16/sha'aban/ 1438 AH
Ya ku musulmai!
Godiya hanya ce ta kari da takawa da dace.
Rabiu dan Anas yace: lallai  Allah na ambaton wanda ya ambace shi kuma yana kari ga wanda ya gode mishi kuma yana azabtar da wanda ya kafurce mishi
Na gode maka lalle godiya wata igiyace ta takawa* kuma ba dukkan wanda ka yiwa ni'ma bane yake biya.
Allah madaukakin sarki yace (kuyi godewa ni'mar Allah in kun kasance shi kadai kuke bawtawa ) 
(ku godemini kada ku kafurce mini).
An karbo daga Mu'azu dan Jabal Allah yakara yarda a gare shi yace lalle manzon Allah yayi riko  da hanun shi sai yace ya Mu'azu  wallahi ni lalle ina sonka wallahi lalle ni ina sonka, sai yace ;ina ma wasiyya ya kai Mu'az kar ka bar fadin cewa bayan kowani sallah : ya Allah ka taimakeni bisa ambatonka da godiya a gare ka da kyautata bauta a gare ka) Abu dauda ne ya fitar da shi.
Dukkan yabo da godiya naka ne ya ubangiji sa'annan dukkan yabo naka ne muddin baki na furuci, falalarka ta kebance ni kuma ta game, daga gun ka ne gani da ji da dandano,  da shakan ga wuni ma haske ga dare mai duhu ga kuma dutse mai tudu da tsirrai wanda suke tsaye akan makyangamansu da wadanda suke akasin haka.
Yaku musulmai
Lalle ku kuna rayuwa a cikin aminci mai yawa da arziki mai yalwa da rayuwa na jin dadi da ci da sha, ga wasu a kewayenku matsanancin yunwa na kashe su ga mutuwa na bi ta kansu a kashe   akamasu amasayin bayi a riki matayensu kuyangi suna kuma fama da bala'i da annoba suna kuma fiskanta tsadan abinci ga kuma fitar da su da aka yi daga gidajensu ba abin da za kagani sai uwa cikin yunwa yara cikin  kuka ga alummu raunuka  ya illantasu to ku kiyaye wasa da ni'mar da Allah ya yi muku kar ni'man ya mantar da ku godiyan Allah a gare ku, ku  yi dubi da abin da Ubangijinku ya yalwata a gareku na daga ni'momi ku san hakkin shi ne mai muku ni'man
Ku kasan ce daga cikin wadanda suka jawu gare shi ta hanyar godiya bisa ga ni'imominsa,
Kar kuyi amfani da kyauta  da ya muku cikin saba masa kada shaidanu su rudekukada makiyanku su yaudareku da bata ,karku bayyana sabo bayan samuwan arziki da aminci da bayani da baiwa,ku kyautata muamala da ni'imomi, ku kiyaye ni'imomin da ke tare da ku, sai kuma ku nemi ni'imomin da kuka rasa ,ku nemi dawwamar kyautar Allah da karamcinsa ni'ima ba ta juya baya idan ta fiskanto, ba a dauke ta bayan ta sauka ba a dauke wata karama bayan an bada ta ,sai dai  kasancewarta kyauta da ba a gode ba ,ko sakamakon kusakurai da aka aikata kuma ita ni'ima idan an yi godiya sai ta tabbata, idan an butulce saita guje.
ya wanda ke tafiya akan koyin kafirci ya sanya kafarsa cikin tawagar matafiya na kafirci da fasikanci da sharri, abin da ya rudeka shine hakurin Allah sararawarsa harka juya baya da fiskanka ka yi watsi da hakkin Allah.
Ya kai dan' adam lallai ka gafala,  sai  kace ba zaka kare ba ko ba zaka halaka, ba ya wanda yayi sharri da dagawa da sabo da fasikanci da fajirci ,shin ko kana zaton kyautar bata halake ba ne, ko ni'imar ba a amsarta ne,dako da jinkiri da rashin gajiyawa ukuba ke diban ka, ka gajarta daga barnarka Allah bai taba kama mutane ba face a yayin da suke mayensu suka shagaltu cikin rudunsu da walwalansu, sau da yawa Allah kan bawa mutane arziki da yalwa da ni'ima, sai suka riki ni'imar Allah tamkar wani tsani ne da zasu haura su tsallaka zuwa ga saba mishi suka rike shi matakala zuwaga abin da Allah ya hana sai suka zaci wannan kyautar da ni'ima wata girmamawa ce da daukaka da darajanta su kan saura da fifitasu da zabansu basu san hakan ba wani abu bane sai daurin talala, sau barkatai akan yiwa wasu daurin talala ta hanyar ihsani, sau da yawa wani kan fitinu in an yabe shi, wani kuma ya rudu in Allah suturce shi bai tona masa asiri ba.
 Ya ku musulmi!
 ka kiyaye fadawa cikin sabon Allah da nuta a cikinsa, da kwankwada daga gare shi da yin sakaci gurin keta laduba, da yin karan tsaye ga tauhidi da sharia da addini, ku kiyaye daga mataimakan shaidan da abokansa dake kokarin batar da ku ta hanyar yaudara kuyi nesa da mummunar fahimtarsu da bataccen tafarkinsu, ku kauda kai daga kiranye kiranyesu, ku kaurace wa tawagarsu, ku wofantar da hanyarsu  ku shakala yinsu, kar kubi soye soyen rayu kansu da sha'awe sha'awensu, kar kuyi biyayya ga mai zunubi ko mai yawan sabo mai yawan kafurci, (kada ka bi wanda muka rabkanar da zuciyarsa ga barin  ambatonmu,alhali kuwa al'amarinsa ya kasance yin barna)
( ku kauda kai daga wanda ya juya bayadaga ambatommu bai nufin komai sai rayuwar duniya)
Makhlad dan Husain yace: An kasance ana cewa : (Godiya shi ne barin sabo)
Mai lura mai hankali yakan banbance tsakanin tsaki da tsakuwa, kuma ya rabe tsakanin zare da abawa domin rogo ba kitse bane.
Yaku musulmai!
 ku janyowa kanku kari ta hanyar  godiya daga kyauta kuyi nesa daga sifa ta butulci da afkawa ga sabo, kuyi nesa daga abin da aka haramta, kar kuyi sabuban da za su kai ku ga fadawa cikinta, don godiya ga Allah bisa ga ni'imominsa masu yawa  da ya baku, duk wanda ya tsallaka halall ya fada ga haram to ya ketare iyaka kuma yayi zalunci,
 Allah yace:(wadancan iyakokin Allah ne, sabo da haka kada ku ketare su, to duk wanda ke ketare iyakokin Allah wadan nan sune azzalumai)
 yaku musulmai ku kiyaye yin dabaru don bata hukunce- hukunce na sharia don ku isa zuwa ga abubuwa da aka haramta munana, don aikata hakan baya cikin aikin masu tauhidi masu godiya, aa yana cikin sifofi na fasikai batattu ) Al hiyal wato dabaru jam'i ne na dabara hanya ce ta boye da zata isar dakai ga manufa.
Imamun Nasafi yace acikin Al kafi daga Muhammad dan Alhasan yace: Baya cikin dabi'ar mumini gujewa hukunce- hukuncen Allah ta hanyar dabaru da zasu kai mutum ga bata gaskiya .
 Allah ya sanya ni da ku cikin masu godiya a halin yalwa ya tabbatar da mu akan addininsa  ba tare da baudewa ba .
HUDUBA TA BIYU:-
Ya ku Musulmai :  Yarda da kadan sifa ce ta masu godiya,  ba sa rena ni'imar Allah  ko da ta karanta,  a duk yayin da wani abu na al'amarin duniya ya wuyata a gare su,  sai su wadatu da abin da ya ke koma bayansa , kuma su yarda ,  hakika ya daukaka duk wanda ya yi wadatan zuci ,  kuma ya kaskanta duk wanda ya sa kwadayi,   daga cikin mutane akwai wanda baya yarda da abin da Allah ya kasa mishi na  arziki ,  za ka ganshi  yana fushi yana raki  yana kuma fatan abin da ke hanun wanin shi na daga matsayi da  dukiya da hali ,  

Yaro na neman girma  *   tsoho kuwa na neman  ya koma yaro
 Me zaman banza na neman aiki   *  Ma'abocin aiki kuma ya kosa
Ma'aboci dukiya kuma na cikin gajiya  *  Matalauci kuma na cikin wahala
Mai yara kuma na cikin bacin rai   *  mai neman su kuma gashinan ya jikkata
 Mutumin da aka yi galaba akan shi kuma yana cikin  tsiya  *  wanda  kuma ya yi nasara shi kuma bai da  hutu
Zai rika neman daukaka  cikin tsoron hasara   *  idan ya yi nasara da ita kuma  sai jikin sa ya mutu .
Arziki kaso ne daga Allah  wanda ya fito bisa hikima  da gudanarwa da ilimi game da halin bayi,  kada ku yi hasada, kada ku yi fatan abin da Allah ya fifita wasunku akan wasu da shi  , kada dayanku ya yi burin  dukiyan wanin shi  da iyalan shi,   ku roka mishi Allah albarka , kuma  ku roki Allah daga taskar sa da bata karewa , a cikin mutane akwai wanda yake rokan mutane don ya bunkasa dukiyan shi, zai rika bijiro musu a masallatayya da kuma wuraren tarurruka  ,   da kuma lokuta masu daraja  kamar juma'a  da ramadan,  watakila ma ya rike dan yaro  ya koya mishi kaskanci da roko  domin neman tausayin mutane   da kuma neman yawaita kyautan su .
An karbo daga Abu Huraira  Allah ya kara yarda a gare  shi ya ce :  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :''  Wanda ya roki mutane dukiyan su  don neman ya yi kudi  to hakika garwashin wuta yake rokan su  to ya roki dan kadan ko da yawa  '' . Muslim ne ya rawaito shi.
 Ya ku Musulmai :
 Almabazzaranci da dukiya  da ciyar da shi a gurin da ba hakkinsa ba   hakanan a wurin alfahari da neman suna,  da tinkaho  da shi   kishiyan godiya ne .
Mujahid ya ce:  da mutum zai ciyar da dukiyan shi gaba daya a cikin hakki , to, da bai zama  almabazzaranci ba  .
 Ciyar da abinci  falala ne mai girma  da kuma ciyar da masu azumi abincin buda baki   a Ramadan  kusanci ne mai daraja , kuma  ibada ne mai girma  da ya dace  duk wani  wanda ya yi dace   ya yi kwadayin ta,
 Muna gargadi game da barna cikin fadada  shinfidar cin abinci  ba tare da bukata ba      da zuba dabino da biredi da abinci ba tare da iyaka ba,  wanda karshe makomansu ya zama abin jefarwa a wurin tara shara , ku tuna 'yan uwanku talakawa da wadanda suke cikin jarabawa a kasar fari   , da tsananin talauci  da yunwa  da  yake -yake  .
Ku nemi abin da yake dai-dai, ku kusanto , ku yi bishara, kuma ku yi fatan alheri, lallai Allah baya sarayar da ladan wanda ya kyautata aiki,
 lalle Allah bai lalata ladan masu kyautatawa.            

MARABA DA RAMADAN

HUDUBAR  JUMA'A NA MASALLACIN  ANNABI TARE DA SHAIKH ALIYU DAN  ABDURRAHMAN AL, HUZAIFI  NA 30/8/ 1438
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai
  Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Mabuwayi mai yawan gafara yana halittan abin da ya so kuma ya zaba abin da ya so , mai juya dare da rana   lallai  cikin haka  akwai abun lura  ga masu basira, ina kyautata  yabo ga Ubangiji na kuma ina gode mishi  ina tuba zuwa gare shi  ina nemar   gafarar sa   na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya  tilo  mai rinjaye   na shaida Annabin mu  kuma shugabanmu Muhammad bawansa ne kuma Manzon sa ne zababbe  ya Allah ka yi dadin tsira da aminci da albarka  bisa ga bawanka kuma Manzon ka Muhammad da iyalansa  da sahabbansa masu biyayya .
Bayan haka ku ji tsoron Allah Madaukaki  ku mishi biyayya   ba wanda  zai tsiyata ta hanyar   yiwa Allah da'a  ,  haka kuma ba wanda zai rabauta ta hanyar sabawa Allah  .
 Ya ku bayin Allah !  
Ku aminta da alkawarin Allah   bisa ga kyawawan ayyuka , ku yi kokari  don samun kyakkyawan karshe da makoma   to,  Ubangijinku mai yawan godiya ne  kuma masani   mawadaci ne kuma mai karamci  yana kira don a nemi kusanci zuwa gare shi   da abinda  ya ke so ,  kuma shi mawadaci ne  ga barin da'an bayi   yana muku gargadi daga sabo  a halin kuwa ba zai cutar da shi ba,   wanda ya tsayu akan zunubai masu halakarwa  Allah madaukakin sarki ya ce :  (  Wanda ya yi aiki na kwarai to, don kansa wanda  ya yi munana to, (alhaki)  a kansa Ubangijinka ba mai zalunci ba ne ga bayi  ).
 Kuma Allah madaukakin sarki ya ce : (  Kuma duk wanda ya juya baya akan diga-digansa  to, ba zai cutar da Allah da komai ba  kuma Allah yana sakanyawa masu godiya  ).
 Ku kasance ya ku mutane cikin tsoron azaban Allah domin baya sauka ga wani face ya halaka shi , haka kuma baya kewaya wani wanda ya gafala face ya azabtar da shi   ya tsiyata shi  Allah madaukakin sarki ya ce :  ( Kuma wanda hushi na ya sauka akansa to lallai ne ya fadi )
 Abun mamaki ga mutumin da yake aiki don duniya ya manta da lahira , to, duniya akan same ta ta hanyar  aiki hakanan akan same ta ba ta hanyar  aiki ba ga wanda ya gaza yin aikin,  amma ita lahira da  ni'imarta   ba a riskanta sai da aiki,  Allah madaukakin sarki ya ce :
( Kuma wancan ita ce  Aljannar  wannan da aka  gadar da ku ita   sabo da abin da ku ka kasance kuna aikatawa).
Ya ku Musulmai :
 Ga wani lokaci mai girma ya sauka a gare ku , kuma wata  mai karamci  ,  albarkatu na sauka a cikinta da alheri , kuma ana kankare zunubai a cikinta  watan ramadana wanda Allah ya sanya mishi falala    . An karbo daga Abu Sa'id Allah ya kara mishi yarda ya  ce: daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Jagoran watanni shi ne watan Ramadana  mafi girman al'hurma kuma shi ne watan zulhijja ) Albazzar ne ya rawaito shi .
  Allah madaukakin sarki ya ce : ( watan ramadana da aka saukar da alkur'ani a cikinta shiriya ne ga mutane da hujjoji bayyanannu  na shiriya  da kuma rarrabewa )  lokaci na Ramadan lokaci ne mai albarka da Allah ya tattaro a cikinsa  ibadoji na azumi tare da salla da zakka  ga wanda ya ke yin zakka a cikinsa  , ga kuma karamin hajji acikinta , wanda  shi ne umra  da kuma yawaita karatun Alkur'ani da nau'uka  daban –daban    na ambaton Allah  da umarni da kyakkyawa da hani da mummuna    da sauran ayuka na da'a ga wanda ya ke son yawaita  neman  kusanci   to, sabuba na alherin cikin sa na da yawa kuma a bayyane suke  sabuban sharri kuma a ramadana dan kadanne  ,  ana shiga tsakanin shaidanu da  abin da suke so na barna  da batar da  Musulmi  da  kange shi daga da'a.  An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi daga Annabi  tisra da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya ce : (  Idan Ramadana ya zo ana bubbude kofofin Aljanna a rurrufe  kofofin jahannama a daure shaidanu cikin mari ) Buhari ne ya rawaito da  Muslim
Daga cikin nau'uka na lada da  ni'ima a cikin Aljanna,  akwai irin nau'ukan da'a da ibada da suka dace da su anan duniya    , to dukkan da'a na  da ladan shi kuma  da ni'ima da ya dace da shi, Allah madaukakin sarki ya ce: Ana ce musu ( Ku ci  kuma ku sha a cikin ni'ima sabo da abin da ku ka gabatar  a cikin kwanukan da suka shige )
An karbo daga sahal Dan Sa'ad  Allah ya kara yarda  a gare shi  ya ce : Daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbat a gare  shi ya ce : (  A cikin aljanna a kwai kofan da ake kira arrayanu za a kira masu azumi ta gun shi , duk wanda ya kasance acikin masu azumi zai shige shi, wanda ya shige shi ba zai ji kishi ba har abada ,  ) Buhari ne ya rawaito shi
  Mafi girman girmamawa ga wanda ya shiga aljanna shi ne dubi zuwa ga fiskan Ubangiji mai girma    wanda shi din sakayya ne ga kyautatawa  da musulmi ya yi na bautawa Allah kamar yana ganin shi , Allah Madaukakin sarki yace :( Wadanda suka kyautata yi suna da abu mai kyau kuma suna da kari) Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya fassara kari da kallo zuwa ga fiskar Allah Mai girma, kamar yadda ya zo a hadisin salman Allah kara yarda a gare shi, wanda Muslim ya rawaito, To sakayyar na daga irin jinsin aikin da mutum ya yi, kamar yadda nau'i na azaba ma ya ta'allaka ne da irin sabo da aka yi, To cin itaciyar zakkumi  da shan tafasasshen ruwa sakayya ne ga cin riba da haram, da shan abubuwan maye da hodar iblis, kwarara ruwan zafi a kai sakayya ne na girman kai da jiji da kai daga bin shariar Allah da kin jawuwa a tafarkinsa,   Allah Madaukakin sarki yace: ( Lalle itaciyar zakkum. Ita ce abincin mai laifi. Kamar narkakken kwalta, yana tafasa a cikin cikuna. Kamar tafasar ruwan zafi.ku kama shi sa'annan ku fizge shi zuwa ga tsakiyar jahim. Sa'annan ku zuba a kansa daga azabar ruwan zafi. Ka dandana lalle kai ne! kai ne mabuwayi mai girma ) to sakayya na daga ginsin aiki  a duniya da lahira.
Albishirinku ya ku musulmai da albishirin manzon Allah ya yi ga sahabbansa game da ramadana domin hakika yakasance yana musu albishir da shi a karshen sha'ban don su shirya, to ku fiskanci wannan wata da dukkan alheri  kuma ku mishi dukkan tattali, ku fiskance shi da neman lada da farin ciki mai tsanani , Allah ya kai ku zuwa gareshi Allah madaukakin sarki yace :(ka ce da falalar Allah da rahamansa sai su yi farin ciki da wannan shi ne mafi alheri daga abin da suke tarawa ) ku fiskance shi da tuba daga dukka zunubai don Allah ya goge muku abin da ya gabata na daga zunubai da shi ku fiskance shi da maida abinda aka zalunta ga ma'botansa  don  Ubangiginka ya kiyaye maka kyawawa ya kankare maka munana ka tuna akwai ranar da zai zo ba zaka riski ramadan ba, ka kasance mai shirya wa mutuwa da kuma  musibunta,  ka kiyaye azumin ka daga wasa da batsa  da cin nama dayanku da annamimanci da magana mara kyau da ayyukan sabo da kallo zuwa ga abubuwan da aka haramta ka kiyaye zuciyarka daga munanan sake- sake,  An karbo daga Ibnu umar Allah ya kara yarda a gare su  daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a ga re shi ya ce :( Ta iya yiyuwa wani mai azumin kason shi daga azumin sa shine yunwa da kishin ruwa, ta iya yiwuwa wani mai tsayuwan dare rabonshi na tsayuwansa shine hana idonshi barci ) Addabarani ya rawaito shi a cikin littafinshi Alkabir, Imamu Al munziri  ya ce isnadin ba shi da laifi,
An karbo daga Abu huraira  Allah ya kara yarda a gare shi ya ce:Manzon Allah tsira da  amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(Duk wanda bai bar fadin karya ba da aiki da shi to Allah bai da bukatan barin  abincinsa  da abin shan sa ) Bukhari ne ya rawaito da Abu Dawuda da Tirmizi.
 An karbo daga Abu Ubaida Allah ya kara yarda a gare shi Annabi tsira da  amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce  (Azumi garkuwa ne) wato kariya ne muddin ba' keta shi ba  )Nasa'I ne ya rawaito da dabrani a Al-ausad  ya kara da :sai aka ce me ya  ke keta ta  sai ya ce da karya da cin naman wani ,
Musulmi yayi kokarin  girmama ladan azumin shi  ta hanyar yawaita ayyukan da'a da neman kusanci a ramadan, na daga tilawan alkura'ani da yawan zikiri da istigfari da yin  salati ga Annabi  tsira da  amincin Allah su tabbata a gare shi da sadaka da kyauta don neman yardan Allah da nau'uka na kyautata wa kamar ilmantarwa da umarni da kyakkyawa da kwadaitar wa zuwa gare shi da hani daga sharri da gargadi game da shi .don yawan da'a tare da yin azumi, yana kara ladar azumi, wanda ya shayar da mai azumi yana da lada kwatan kwacin ladansa ba tare da an tawaye wani abu ba na daga ladansa ba.
 kada ka yi sakaci ya kai musulmi  game da sallan tarawihi da tsayuwan dare musamman kokari na neman lailatul  kadri a goman karshe,  azumin ramadana kankara ne ga zunubai  an karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce manzon Allah tsira da  amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(Duk wanda ya yi azumin ramadana cikin imani da neman lada to za a gafarta  masa abin da ya gabata daga zunubansa  )Buhari da Muslim ne suka rawaito.
  An karbo daga Ubada dan Samit Allah ya kara yarda a gare shi Annabi  tsira da  amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce game da lailatu al kadri (ku neme shi a goman karshe wanda yayi tsayuwan shi yana mai imani da neman lada sannan yayi dace da shi za a gafarta mishi abin da ya gabata na daga zunuban shi da abin da ya jinkirta ) Ahmad ne ya rawaito da Addabarani a Al kabir.
Ka kirdadi  salla cikin jam'i , kai musulmi  Allah zai kiyaye bawa kuma ya jibinci alamarin shi  kuma ya datar da shi a alamuran shi, wanda ya daidaitar da sallah to duniyarsa za ta tafi hakanan kuma  da  lahirarsa  zai ji dadi a duniya jin dadi irin na dabbobi sannan kuma a ce da shi ranar alkiyama shiga wuta tare da masu shiga.Ya zo a hadisi wanda yayi sallar ishai acikin jama' kamar  ya yi tsayuwan rabin  dare ne, sannan kuma wanda yayi sallar asuba acikin jama'a  kamar wanda yayi tsayuwan dare ne dukaninsa. )Muslim ne ya rawaito a hadisin Usmana dan affan Allah ya kara masa yarda,
Na daga cikin abin da ke girmama hasara kuma yake haramta wa bawa alheri yin azumi da barin salla  ko kuma barin wani sashi daga gare ta.
Na daga cikin tafiyar da rayuwa da bata shi  kwana  da hana ido barci akan wasa ko kuma bibiyan yanar gizo na  barna da kuma bin fina finai masu cutarwa  da zubar da mutunci da bata tarbiyya da halaye,hasara da tabewa na girmama idan mutun ya rinka shagaltuwa da wadannan abubuwa a wannan wata, daga ayyuka na alheri Allah madaukakin sarki ya ce (ku yi gaggawa zuwa ga meman gafara daga ubangijinku da wata aljanna wanda fadinta (daidaida ) sammai da kasa ne an yi tattalinta domin masu takawa )*(wadanda suke ciyarwa a cikin sauki da tsanani kuma suke masu hadiyewar fushi kuma masu yafewa mutane laifi ,kuma Allah yana son masu kyautatawa  ) Allah ya sa mini albarka ni da ku a alkura'ni mai girma   
Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah mai shiryarwa zuwa ga hanya madaidaiciya. Ma'aboci falala mai girma, yana baiwarsa ga wanda ya so da falalarsa, ya kuma  hana wanda ya so bisa adalcinsa, shi mabuwayi ne Mai hikima ina kyawtata yabo ga ubangiji na kuma ina gode mishi  ina mai tuba zuwa gare shi ina neman gafararsa na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya Mai iko kuma masani na shaida cewa    Annabinmu kuma shugabanmu  muhammad bawansa ne kuma manzonsa ne,  ma'abocin sharia' mai haske da shiriya mikakkiya ya Allah ka yi salati da sallama da albarka bisa ga bawanka kuma manzonka muhammad da iyalansa da sahabbansa wanda suka siffantu da dukkan dabiu na karamci.
Bayan haka :
    Ku ji tsoron Allah yadda ya dace a ji tsoronsa kuma kuyi riko da igiya mai karfi na musulunci, Ya ku bayin Allah  ko sanya wa kowani zunubi  tuba hakika masu tuba sun rabauta masu dogewa a kan zunubai sun  yi hasara Allah madaukaki ya ce: (ku tuba zuwa ga Allah ya ku mu'minai  ko za ku za ku rabauta).  wannan wata lokaci ne na tuba kuma na daga cikin  mafi girman zunubai da ya  wajaba atuba daga gareshi akwai shan taba  ka tsarkake bakinka ya kai musulmi daga shan shi,  ka tsarkake bakinka daga gare shi don ambaton Allah da karatun alkura'ni ka dadada kamshinka ga salihai masu zama da kai da mala'ku masu rubutu domin shan taba yana kusanto da shaidanu kuma yana lalata jini kuma yana jawo  cututtuka masu halakarwa, kuma yana gajarta rayuwa, kuma  ka'idoji na shari' na  haramta shi,  ka sani ya kai musulmi ya wajaba ka kwana  da niya tun daga dare, An karbo daga Hafsa Allah ya kara yarda agareta daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yace :  (  wanda bai kulla niyarsaba tun daga dare na azumi  to babu azumi agareshi ) Abu dawda da tirmizi da nasa'I  da ibnu majah su ka rawaito shi. Ya zo a hadisi dukk wanda ya sha azumi na ramadana ba tare da uzuri ba ba zai iya biyansa ba ko da ya azumci zamani baki daya.To Allah ya tsare mu. lalle Allah da mala'kunsa na yin salati ga Annabi ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi da aminci tabbatacce .