الأحد، 10 يناير 2021

GARGADI GAME DA TASHIN ALKIYAMA

 

 

 
الوصف: cbc250ed-6a0e-4037-8d54-a9eb3d0a0577                                                                                                                           

ترجمة خطبة الشيخ أحمد بن طالب

المترجم : أمين سعد

اللغة : الهوسا

التاريخ :24-5-1442هـ

 

Hudubar Masallacin Annabi, shaikh Ahmad Bin Dalib

24-5-1442 AH 8-1-2021AD

HUDUBAR FARKO

Dukkan yabo  da godiya sun tabbata ga Allah  muna gode masa kuma muna neman taimkonSa kuma muna neman gafararSa, muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu, da munanan  ayukanmu duk wanda Allah y shiryar da shi babu mai batar da shi  kuma duk wanda ya batar da shi babu mai shiryar da shi .

Kuma na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah ba shi  kadai yake bashi da abokin tarayya , kuma na shiada Annabi Muhammadu bawansa ne kum ManzonSa ne , kuma zababbenSa ne cikin halittunSa, kuma badadayinSa ne,  ya isar da sako kuma ya bada amana  ya yi nasiha wa al'uma  ya yaye bakin ciki ya yi jahadi don Allah cancancin jahadi ,  har mutuwa ta zo mi shi ,tsira da amincin Allah su tabbata agare shi  da iyalan gidansa tsarkaka  da kuma matayen sa  uwayen muminai da  sahabbansa  masu hasken hannaye  da kuma wanda ya bisu da kyautatawa zuwa ranar sakayya .

 BAYAN HAKA:

Lallai mafi gaskiyan zance shi ne littafin Allah , mafi alherin shiriya shi ne shiryarwan Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi , mafi sharrin al'amura kuma su ne fararrun ta, kuma  dukkan fararrun abu bidi'a ne dukkan bidi'a bata ne, dukkan bata na wuta.

Ya ku mutane!

Ku yi wa kanku hisabi kafin a yi muku hisabi, kuma ku auna ayyukan ku kafin a aunaku,   

To, idan an yi busa a cikin kaho, busa daya.
14; Kuma aka dauki kasa da duwatsu, kuma aka nika su nikawa daya.
15; A ran nan, mai aukuwa za ta auku.
16; Kuma sama za ta tsage, domin ita a ran nan, mai rauni ce.
17; Kuma mala´iku (su bayyana) a kan sasanninta, kuma wasu (mala´iku) takwas na dauke da Al´arshin Ubangijinka, a sama da su, a wannan ranar.
18; A ranar nan za a bijira ku (domin hisabi), babu wani rai, mai boyewa, daga cikinku, wanda zai iya boyewa.
19; To, amma wanda aka bai wa littafinsa a damansa, sai ya ce wa (makusantansa), "Ku karba, ku karanta littafina."
20; "Lalle ne ni, na tabbata cewa ni mai haduwa da hisabina ne."
21; Saboda haka, shi yana cikin wata rayuwa yardadda.
22; A cikin Aljanna madaukakiya.
23; Nunannun ´ya´yan itacenta makusanta ne (ga mai son diba),
24; (Ana ce musu) "Ku ci, kuma ku sha a cikin ni´ima, saboda abin da kuka gabatar a cikin kwanukan da suka shige."
25; Kuma wanda aka bai wa littafinsa ga hagunsa, sai ya ce: "Kaitona, ba a kawo mini littafina ba!"
26; "Kuma ban san abin da (ke sakamakon) hisabina ba!"
27; "In da dai ita, ta kasance mai halaka ni gaba daya ce!
28; "Dukiyata ba ta wadatar da ni ba!"
29; "ikona ya bace mini!"
30; (Sai a ce wa mala´iku) "Ku kama shi, sa´an nan ku sanya shi a cikin kukumi."
31; "Sa´an nan, a cikin Jahim, ku kona shi."
32; "Sa´an nan, acikin sarka, tsawonta zira´i saba´in, sai ku sanya shi."
33; "Lalle ne, shi ya kasance ba ya yin imani da Allah, Mai girma!"
34; "Kuma ba ya kwadaitarwa ga (bayar da) abincin matalauci!"
35; "Saboda haka, a yau, a nan, ba ya da masoyi."
36; "Kuma babu wani abinci, sai daga (itacen) gislin."
37; "Babu mai cin sa sai masu ganganci."

Ranar sakayya da idon yakini, da kuma kamunga, da fayyacewa da nesatan juna,

"Aranar da zaku juya kuna masu bada baya (gudane) ba ku da wani mai tsaro a daga Allah, kuma wanda Allah ya batar to ba shi da wani mai shiryarwa)

(Baku da wata mafaka a ranar nan kuma baku iya yin wani musu)


1. Idan aka girgiza ƙasa, girgizawarta.
2. Kuma ƙasa ta fitar da kayanta, masu nauyi.
3. Kuma mutum ya ce « Mẽ neya same ta? »
4. A rãnar nan, zã ta faɗi lãbãrinta.
5. cewa Ubangijinka Ya yi umurni zuwa gare ta.
6. A rãnar nan mutane za su fito dabam- dabam domin a nuna musu ayyukansu.
7. To, wanda ya aikata ( wani aiki ) gwargwadon nauyin zarra, na alheri, zai gan shi.
8. Kuma wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarra na sharri, zai gan shi.

 (Shin, bã ya da sanin lõkacin da aka tõne abin da yake cikin kaburbura.

Aka bayyana abin da yake cikin zukata, lalle ne Ubangijinsu game da su a ranar nan Mai kididdigewa ne)

 

Mai kwankwasar (zukata da tsoro )   Me ne mai kwankwasr      kuma mai  ya sanar da kai abin da aki ce wa mai  kwansar     ranar da mutane za su kasance kamar ya yan fari masu watswa kuma duwatsu za su kasance kamar gashin sufin da aka sabe        to ama wanda ma aunrsa su kai naauyi     to shi ya na cekn wata rayuwa yardadda     kuma ama wanda ma aunarsa babu nauyi       to uwarsa hawiya ce  kuma mai ya sanar da kai me ne ita?     Wata wuta ce mai zafi     

 

Alfahari da yawan dangi  ya shagaltar da ko da ga ibada mai amfaninku har kuka ziyar ce kaburbura       A aha nan gaba za ku sani       sa an nan tabas za ko sani     hkika da kuna da sani sani nan yakini      lalle ne da kuna da ganin jhim       sa an nan lalle ne za ku ganta da edanu bayyane        sa an nan lalle ne za atambaye ku a  ranar nan labarin ni imar da aka yi muku   

 

Awanan ranar Allaha zai dunkule kasa  ya nade sammai da damanSa  sai ya ce nini me mulki ina masarautar kasan?

 

10; Lalle wadanda suka kafirta, ana kiran su, "Hakika, kin Allah (a gare ku) shi ne mafi girma daga kinku ga kanku a lokacin da ake kiran ku zuwa ga imani, sai kuna ta kafircewa."
11; Suka ce: "Ya Ubangijinmu! Ka matar da mu sau biyu, kuma Ka rayar da mu sau biyu, saboda haka mun yarda da laifuffukan mu. To, shin, akwai wata hanya zuwa ga fita?"
12; Wancan sababinsa, lalle (shi ne) idan an kirayi Allah Shi kadai, sai ku kafirta, kuma idan aka yi shirki game da Shi, sai ku yi imani. To, hukuncin fa, na Allah Madaukaki, Mai girma ne.
13; Shi ne Wanda ke nuna muku ayoyinSa, kuma Ya saukar da arziki daga sama saboda ku, kuma babu mai yin tunani face mai mayar da al´amari ga Allah.
14; Saboda haka ku kirayi Allah, kuna masu tsarkake addini a gare Shi, kuma ko da kafirai sun ki.
15 ; Mai daukaka darajoji (domin muminai), Mai Al´arshi, Yana jefa ruhi daga al´amarinSa a kan wanda Ya so daga bayinSa, domin ya yi gargadi kan ranar gamuwa.
16; Ranar da suke bayyanannu, babu wani abu daga gare su wanda yake iya boyuwa ga Allah. "Mulki ga wa ya ke a yau?" Yana ga Allah, Makadaici, Mai tilastawa.
17; Yau ana saka wa kowane rai a game da abin da ya aikata, babu zalunci a yau. Lalle Allah Mai gaggawar hisabi ne.
18; Kuma ka yi musu gargadi kan ranar (Sa´a) makusanciya, a lokacin da zukata suke masu cika da bakin ciki, ga makosansu. Babu wani masoyi ga azzalumai, kuma babu wani mai ceto da za a yi wa da´a (ga cetonsu).
19; (Allah) Ya san yaudarar idanu da abin da kiraza ke boyewa.
20; Kuma Allah Shi ke yin hukunci da gaskiya, wadannan da kuke kira, waninSa,ba su yin hukunci da kome. Lalle Allah, Shi ne Mai ji, Mai gani.
21; Ashe, ba su yi tafiya ba, a cikin kasa, domin su duba ga yadda akibar wadanda suka kasance a gabaninsu ta zama? Sun kasance su ne mafi tsananin karfi daga gare su, da kufaifan aiki a cikin kasa, sai Allah Ya kama su da laifuffukansu. Kuma ba su da wani mai tsarewa daga Allah.
22; Wancan sababinsa, domin su Manzanninsu sun kasance suna zuwa gare su da hujjoji bayyanannu, sai suka kafirta, sai Allah Ya kama su. Lalle Shi Mai karfi ne, Mai tsananin azaba.

42; "Kuma kada ka yi zaton Allah Mai shagala ne daga abin da azzalumai suke aikatawa. Abin sani kawai, Yana jinkirta musu ne zuwa ga wani wuni, wanda idanuwa suke fita turu-turu a cikinsa."
43; "Suna masu gaggawa, masu daukaka kawunansu zuwa sama kiftawar ganinsu ba ta komawa gare su. Kuma zukatansu wofintattu."
44; Kuma ka yi gargadi ga mutane ga ranar da azaba take je musu, sai wadanda suka yi zalunci su ce: "Ya Ubangijinmu! Ka yi mana jinkiri zuwa ga wani ajali makusanci, mu karba wa kiranKa, kuma mu bi Manzanni."(Allah Ya ce musu) "Ashe, ba ku kasance kun yi rantsuwa ba daga gabani, cewa ba ku da wata gushewa?
45; "Kuma kuka zauna a cikin gidajen wadanda suka zalunci kansu, kuma ya bayyana a gare ku yadda Muka aikata game da su, kuma Muka buga muku misalai."
46; Kuma lalle sun yi makirci irin makircinSu kuma a wurin Allah makircinsu, yake, kuma lalle ne makircinsu ya kasance, hakika, duwatsu suna gushewa saboda shi.
47; Saboda haka, kada ka karfafa zaton Allah Mai saba wa´adinSa ne ga ManzanninSa. Lalle ne Allah ne Mabuwayi, Ma´abucin azabar ramuwa.
48; A ranar da ake musanya kasa ba kasar nan ba, da sammai kuma su bayyana ga Allah Makadaici, Mai tankwasawa.
49; Kuma kana ganin masu laifi, a ranar nan, suna wadanda aka yi wa ciri daidai a cikin maruruwa.
50; Rigunansu daga farar wuta ne, kuma wuta ta rufe fuskokinsu.
51; Domin Allah Ya saka wa kowane rai da abin da ya tsuwurwurta. Lalle ne, Allah Mai gaggawar hisabi ne.
52; Wannan iyarwa ce ga mutane, kuma domin a yi musu gargadi da shi, kuma domin su sani cewa, abin sani kawai, shi ne abin bautawa guda. Kuma domin masu hankali su rika tunawa.


     
Allah ya sa mini albarka ni da ku.

 


Huduba ta biyu

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Tilo Marinjayi, Mabuwayi Mai gafara Mai juya dare da rana da kuma rana a kan dare, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi zababbe da iyalansa tsarkaka da muhajirai da ansar,da sauran sahabbai ma'abota biyayya, da wanda ya bi hanyar su ya haskaka da hasken su,

Bayan haka Ya ku mutane ku bi Ubangi-jinku (Ya ku mutane ku bi Ubangi-jinku da takawa lalle ne girgizar kasa ta tsayuwar Sa,a wata aba ce mai girma       Aranar da kuke ganin ta du –kan mai shayar da mama tana sha-gala daga a da ta shayar, kuma dukan mai ciki tana haihuwar  cikinta  kuma kana ganin mutane suna masu maye alhali kuwa su ba masu maye ba amma azabar Allah ce mai tsanani)

Ku yi salati da sallama ya ku bayin Allah!

 

الأربعاء، 23 ديسمبر 2020

SHI NE ALLAH

 

خطبة الشيخ  أحمد الطالب

المترجم : أمين سعد

اللغة : الهوسا

التاريخ : 4-5-1442هـ

 

 

HUDUBAR MASALLACIN ANNABI NA SHAIKH AHMAD –ADDALIB

4-5-1442AH 18-12-2020AD

 

HUDUBAR FARKO

Dukkan yabo  da godiya sun tabbata ga Allah  muna gode masa kuma muna neman taimkonSa kuma muna neman gafararSa, muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu, da munanan  ayukanmu duk wanda Allah y shiryar da shi babu mai batar da shi  kuma duk wanda ya batar da shi babu mai shiryar da shi .

Kuma na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah  shi  kadai yake bashi da abokin tarayya , kuma na shiada Annabi Muhammadu bawansa ne kum ManzonSa ne , kuma zababbenSa ne cikin halittunSa , kuma badadayinSa ne,  ya isar da sako kuma ya bada amana  ya yi nasiha wa al'uma  ya yaye bakin ciki ya yi jahadi don Allah cancancin jahadi ,  har mutuwa ta zo mi shi ,tsira da amincin Allah su tabbata agare shi  da iyalan gidansa tsarkaka  da kuma matayen sa  uwayen muminai da  sahabbansa  masu hasken hannaye  da kuma wanda ya bisu da kyautatawa zuwa ranar sakayya .

 BAYAN HAKA:

Lallai mafi gaskiyan zance shi ne littafin Allah , mafi alherin shiriya shi ne shiryarwan Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi , mafi sharrin al'amura kuma su ne fararrun ta , kuma  dukkan fararrun abu bidi'a ne dukkan bidi'a bata ne, dukkan bata na wuta .

Ya ku Muminai:

Lallai Allah ya kira ku ne da suna na imani ,  kuma ya kira ku da ku ji tsoronSa kuma ya umarce ku da ku yiwa kanku hisabi kafin  a yi muku hisabi, dubi zuwa ga  abin da kuka tanada mata kafin komawa , ya muku gargadi game da manta ta, da kuma  radadin hasarar ta  ya sanar da ku fifikon hali da za a shiga a ranar  komawa gare shi  , da girmar tasirin alkur'ani da an saukar da shi ga duwatsu , ya kuma sanar da ku da kamalar sunayenSa masu daraja da kaye .

 Shi ne Allah wanda  zukata  take bauta mi shi bisa kauna da  rusunawa  da tsoro,  da tsammani da kushu'i , da fata da kuma firgici .

Shi ne Mai gaskiya duk  abin da ke koma bayan shi bata ne, kuma mai gushewa, ba abin bautawa da gaskiya  sai shi, gani bai  iyakance shi,  tunani baya  riskan shi, sutura baya mishi shamaki, sirri baya boyuwa gare shi, da izinin shi ne falaki ya ke juyawa mai kewayawa, da hukuncinSa da hikimarSa dare kan saba da wuni..

Ma'aboci rahama mai yalwa mai dorewa, ya daidaita bisa mafi yalwan halittunSa.Da  mafi kyaun sunayen sa da mafi yalwan sifofinSa, (Mai rahama , Ya daidaita  a kan Al'arshi. Abin da ya ke a cikin sammai Nasa ne, da abin da ya ke  a cikin kasa  da abin da yake a tsakaninsu  da abin da ke karkashin  turbaya .

Kuma  idan  ka bayyana da  magana, to, lalle Shi, Yana sanin  asiri da mafi  boyuwa . Allah babu abin bautawa  face  Shi . Yana da sunaye  mafiya  kyau.)

RahamarSa ta yalwaci halittu wurin samarwa da tattalawa da taimakawa  da shiryarwa  da zabarsa ga waliyyanSa, halin shiryarwa da kuma datarwa  da tattalawa  har  ya kaisu ga matabbatar rahamarSa da ni'imar aljannarSa,  mulki mai zartuwa na iko a duniya da aikinSa ne da umarninSa , mamallakin sarakuna da abin da aka mallaka da malakuti da falakoki , yana bada mulki ga wanda ya so ya kwace ga wanda ya so ,  ya daukaka wanda ya so ya kaskantar da wanda ya so,  alheri na hanunSa, kuma shi yana da iko ga dukkan komai.

(UmarninSa, idan Ya yi nufin wani abu , sai Ya ce masa kawai, ''Ka kasance,'' sai yana kasancewa (kamar yadda Yake nufi).

Ya tsarkaka daga dukkan tawaya sabo da kamala , ya kubuta daga dukkan aibi  sabo da kyau ,  ya tsarkake abin da ya so sabo da albarka da daukakawa, ya amintar da wanda ya so bisa ga wanda ya so sabo da daukakawa da kaskantarwa.

 (makoma), shine amincin masu tsoro, kuma mafakan masu yankewa don ibada , ba aminci  Ya yi imani na da fadinSa cewa shine gaskiya Mai kasaita, kuma muminai sun yi imani da  shi bisa dadin rai a fadi da aiki, saura halittu kuma suna da'a  bisa tilas  a karshe ba zaman lafiya sai daga gare shi kuma zuwa gare shi,  rinjayin iko a ilimi da umarni  da shaidawa da karfin mulki  da amfanarwa da cutarwa  a sirrace da a bayysane duka na shi ne .

Ya buwaya bisa ga halittunSa wanda tsarki ya tabbata a gare shi  a karfi da kudura da galaba  da hani .

Ya karya  garkuwan halittu bisa umarninSa da haninSa a shari'a da kaddara  da karfin mulki , ya karya garkuwan su  ta karaya da talauci , da tsanani da cuta ,  bisa jin dadi da wadatarwa  da gamsarwa  da kuma saukakewa da taimakawa.

Shi ya fi komai girma da daukaka da daraja da sha'ani  da zati da sifa  da ayyuka  da iko, to ko wani abu kasa da shi ya ke karami ne abin renarwa  ya tsarkaka daga dukkan wani abokin tarayya , kuma ya daukaka ba wani abu kwatankwacinSa shi mai ji ne kuma  mai gani , ya yi halitta daga babu  sai ya bayyana  shi  ya halicci iska sai ya sanya mishi wuri  ya suranta a mahaifa sai ya rarrabe , ya kadaita da sunaye , wanda suka kai kololuwa wurin kyawu a lafazi da ma'ana  , ko wani abu ya yi tasbihi a gare shi  yana mai tsarkake shi  da dukkan harshe .

Allah ya buwaya daga makamanci  ko kini, ko kishiya da majibinci da mataimaki. Ya kyautata halitta a hukunci da hikima, shine Al hakku  kuma maganarSa gaskiya ce, hukuncinSa adalci ne alkalancinSa ne  mai rabewa (kat), babu kusakurai ko zamewa, ba wani abu da zai fita daga iliminSa na aiki ne ko fadi, Shi Mai hikima ne gwani.(Ya ku wadan da suka yi imani  ku ji tsoron Allah kuma rai ya dubi abin da ya gabatar domin gobe , kuma ku bi Allah da takawa . Lalle Allah  Mai kididdigewa ne ga  abin da  kuke aikatawa.

Kuma kada  ku kasance  kamar wadanda suka  manta  Allah,  Shi  kuma Ya mantar  da su rayukansu . Wadannan  su ne fasikai .

'Yan wuta da 'yan aljanna basu daidaita , 'yan aljanna su ne masu babban rabo.

 Da mun saukar wannan Alkur'ani akan dutse , da lallai ka ga dutsen yana mai tawali'u mai tsatssagewa sabo da tsoron Allah, kuma wadancan misalai muna bayyana su ne ga mutane da fatan za su yi tunani .

(Wanda ya saukar da Alkur'ani) Shi ne Allah wanda babu wani abin bautawa face shi masanin fake da bayyane , shi ne mai rahama mai jin kai .

Shi ne Allah wanda babu abin bautawa  face shi Mai mulki mai tsarki , aminci , Mai amintarwa Mai tsarewa Mabuwayi Mai tilastawa  Mai kamun kai , tsarki ya tabbata a gare shi daga abin da suke yi na shirki da shi.

Shi ne Allah mai halitta mai ginawa  Mai surantawa Yana da sunaye masu kyau , abin da ke a cikin sammai da kasa suna tsarkake shi, kuma shi ne mabuwayi  Mai hikima ).

Allah ya sa mini albarka ni da ku a cikin Alkur'ani mai girma , ya amfane ni da ku da abin da ke cikin shi na daga ayoyi da ambato mai hikima, ina fadin wannan maganar tawa  ina neman gafarar Allah wa ni kai na da ku da sauran musulmai daga dukkan zunubai , kuma ku nemi gafararSa , lallai shi mai gafara ne mai jin kai .

HUDUBA TA BIYU

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah  wanda ya isa, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi zababbe  da iyalansa da sahabbansan , da wanda suka bi sawunsu .

Bayan haka:

To ku ji tsoron Allah ya ku bayin Allah , lallai mafi alherin guzuri shi ne tsoron Allah, kuma ku yi riko da igiya mai karfi na musulunci .

Ku yi salati da aminci…. Ya ku bayin Allah  karshe da kuma adu'a.