الجمعة، 11 ديسمبر 2020

CUTAR DA MUSULMI

 

ترجمة

خطبة المسجد النبوي للشيخ حسين آل الشيخ

اللغة : الهوسا

المترجم : أمين سعد

التاريخ : 26/4/1442هـ

HUDUBAR MASALLACIN ANNABI NA SHAIKH HUSAIN AL-ASSHAIKH 26-4-1442AH 11-12-2021AD

 

HUDUBAR FARKO

 

Cutar da halittu   da sabbaba hakan ba tare da hakki ba  na daga cikin hanya mafi hadari ga mutum. Wannan ita ce hanya irin ta shaidanu tana tasowa daga sabani  da gaba da  rikici na kashe juna, tare da rasa ginshiki na rahama  da hali irin na tausayi, da jinkai.

Lalle cutar da bayi dabia ce mara kyau abin zargi ne da  ta tattaro sifofi daban daban  na laifi da abubuwa masu halakarwa.

Lalle sake linzami ga rai ya cutar da wasu  da harshe ne ko a aikace  bai fitowa sai daga masu raunin imani da biye ma son rai, wanda bata da rai mai yawan umarni da mummuna da alfahasha.

To ka kare kanka daga cutar da wani - ya kai musulmi - ka yi wa kanka gargadi daga halaka   zaka kubuta ka rabauta a duniya da lahira Allah Madaukakin Sarki yace :  (Wadannan  da suke cutar da muminai maza da mata ba da abin da suka aikata ba suke jifansu hakika sun lafta karya da zunubi mabayyani ga kansu)

Allah subhanahu yana cewa : ( Wanda ya aikata kuskure karami ko babba sannan ya dorawa wanin sa to hakika ya girba karya da zunubi mabayyani)

   Kuma Manzonmu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bayana littafin Ubangijinsa ya fassara shi yayi  bayanin wadannan ayoyi  daki – daki, ta hanya mutawatiri da aka karbo daga gare shi yana mai gargadi mai tsanani da jan hankali mai karfi bisa cutar da wani  da zaluntar su da musu shisshigi da wuce iyaka wajen cutar da su, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace :(Musulmi dan uwan musulmi ne ba zai zalunce shi ba ba zai rena shi ba ba zai  tabar da shi ba) Muslim ne ya rawaito.

Kuma ya fitar a hadisin hana zama a kan hanya Annabi  ya bayyana cewa (Na daga cikin hakkin hanya kamewa daga cutarwa)

 ya kai musulmi

ka kiyaye kyawawanka ka kare addininka, ka kame daga cutar da waninka, ka kasance kamar yadda Fudail Bin Iyad yace :(Ba ya halatta a gare ka ka cutar da kare ko alade ba tare da hakki ba, to ina ga halitta mafi daukaka )

Matsanancin hani ya tabbata daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi

Game da cutar da musulmi sai ya ce : (ya tawagan wadanda suka yi imani da harshensu a halin imani bai fantsama cikin zuciyarsu ba, to kar ku cutar da musulmai  kar ku aibata su kada ku bibiyi  al'aurarsu, to lallai wanda ya bibiyi al'aurar dan'uwansa musulmi to Allah zai bibiyi al'aurarsa, kuma duk wanda Allah ya bibiyi al'aurarsa to zai kunyata shi ko da kuwa a tsakiyar gidansa ne ) Tirmizi ne ya rawaito.

Katada yace :(Na hore ku da ku nesaci cutar da mumini domin Allah na kewaye da shi kuma yana iya yin fushi dominsa.)

Ya kai bawan Allah!

Ka kubutar da kanka daga cutarwa , ka hana kanka daga zalunci da ketare iyaka zaka kubuta daga  walakanta da halaka.

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Musulmi shine wanda musulmai suka kubuta daga sharrin harshensa da hanunsa) Buhari ne ya rawaito.

Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Duk wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira to kada ya cutar da makwabcinsa) Buhari ne ya rawaito. A gun muslim kuma (Ba zai shiga aljanna ba duk wanda makwabcinsa bai aminta da sharrinsa ba)  wato sharinsa da mugayen halinsa.

 

Ya  'yan uwa musulmi

 

A duniyar  yau akwai abin da ake cewa kafofin sadarwa ta sada zumunta,wanda wasu ke amfani da shi wajen cutar da musulmai da suka ga mahukuntansu da malamansu da daidaikunsu. Da al'umominsu  da maganganu na fajirci da yada jita –jita marasa kan gado. To masu yin wannan lalle su tuna cewa : Allah na dakon su a madakata, kuma lalle mizani ya hada da kyawawa da munana  to su kiyaye kada su je ga Ubangijinsu suna halin Muflisai wadanda suka shiga cikin rudani sun yanke tsammani, - muna rokon Allah afuwa da waraka-.

Lalle haramcin cutar da musulmi bai tsaya ga cutar da daidaiku ba, sai dai ya game da cutar da musulmai cikin maslahohinsu da ya shafi kowa da kowa.da abubuwan amfaninsu da ake tarayya kamar kayakin  al'uma mallakin gwamnati, na daga tushe na musulunci akwai (Ba cuta ba cutarwa).

   Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: (ku tsoraci abubuwa biyu masu janyo  tsinuwa : wanda ke bahaya a  hanyar mutane ko inuwar su).Muslim ne ya rawaito.

Dabarani ya fitar  da sanadi hasan daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace ; wanda ya cutar da musulmai a kan hanyar su to tsinuwa ta tabbata a gare shi).


 

Huduba ta biyu

Ya dan uwa musulmi !

Ka sabarwa kanka da kubuta daga cutar da halittu, ka tsarkake ta daga zaluntar wasu a zahiri da badini,  ka sani kubutar da rai daga shirka  da bidiah , da kullin zuci da hasada da kyashi da muzanta musulmai da zaluntansu na daga cikin sabuba na kubuta. Kuma sifa ce daga cikin sifofi na 'yan aljanna . Allah Madaukakin sarki ya ce game da khalilin sa Ibrahim in da ya roki Ubangijinsa game da abin da ya roki Ubangijinsa da shi,( kada ka kunyatar dani ranar da ake tashin mutane) kuma Allah ya ce (Mun fitar da abin da yake cikin kirzansu na daga keta, halin kasancewarsu  "yan uwa, suna kan gadaje suna kallon juna ).

 Hakika hadisai da yawa sun inganta wurin bayyana falalan lafiyan  zuciya  ga musulmai  daga gaba da kiyayya da nufin muzantawa, na daga ciki akwai mutumin na da ya zo daga cikin Ansarawa  wanda Annabi ya yi mar shaida da cewa dan aljanna ne, Abdullahi dan Amru Dan As ya bibiyi wannan mutumin har ya taho ya yi kwanaki uku a gidan mutumin, amma bai ga wani abu na daga kyawawan ayyukan shi ba irin su tsayuwan dare ba, face in ya tashi cikin dare daga makwancinsa sai ya ambaci Allah  yayi kabbara har zuwa ya tashi don sallar Asubahi, bai fadi wani abu ba face alheri, sannan Abdullahi ya bashi labarin abin da Annabi ya fada game da kissarsa, sai mutumin yace da shi game da ayyukansa shi bai yin wani abu face abin da ka gani sai dai ni ba na rike wani musulmi a cikin zuciya ta kuma bana hasada ga wani bisa wani alhairin da Allah ya bashi  saiAbdullahi ya ki cewa lale wanan itace wanda ta kai ka wanan matsayin da ba zamu iya ba.   

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 


 

 


 

 

 

السبت، 5 ديسمبر 2020

 

 

بسم الله الرحمن الرحيم

HUDUBAR FARKO

 

Yabo ya tabbata ga Allah; Ma'abucin buwaya da karamci, Wanda ya kagi halitta, Mai yalwar falala da ni'imomi, Ina yin yabo ga Ubangijina, kuma ina gode masa kan ni'imominSa wadanda muka sani, da kuma wadanda bamu sani ba.

Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya, sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya, Mafi girman buwaya da karamci,

kuma ina shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawansa ne Manzonsa, Wanda Allah ya bashi dunkulallun kalmomi (na jawami'ul kalim).

Ya Allah! ka yi dadin salati, da sallama da albarka ga bawanka kuma Manzonka; Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa, wadanda aka shiryatar da su ga hanyar da ta fi mikewa,

 

Bayan haka:

Sai ku yi takawar Allah Mabuwayi da daukaka, ta hanyar neman kusanci zuwa gare shi da aikata kyawawan ayyuka, da kuma nisantar ayyukan haramun, saboda babu mai tsira (a wurin Allah) face masu takawa, kuma babu mai tabewa ya yi hasara face masu bin soye-soyen zukata, da masu sakaci.

 

Ya ku, Musulmai… !!!

Ku yi hisabi ga kayukanku gabanin a muku hisabi, kuma ku farkar da zukatanku daga gafalarsu, kuma ku kame rayuka daga aukawa cikin dadi irin na haramun, kuma ku yi gaggawan tuba, gabanin saukowar ajali, da yankewar guri, da katsewan yin ayyuka, domin kuna ganin saurin tafiyar shekaru, da gaggawar tafiyar kwanaki.

Kuma babu komai a bayan wannan rayuwar face mutuwa, kuma babu komai a bayan mutuwa face shiga gidan ni'ima, ko gidan azaba mai radadi.

Kuma kamar yadda kuke aiki domin duniya mai karewa, to sai ku yi aiki domin lahira mai wanzuwa, Allah Ta'alah ya ce: "Kawai, kuna fifita rayuwa ce ta Duniya * alhalin Lahira itace mafi alheri kuma mafi wanzuwa" [A'alah: 16-17].

 

Ya ku, Musulmai… !!!

Ku rungumi littafin Ubangijinku, domin daukakarku da rabautarku da gyaruwar lamuranku, duka a cikinsa suke, kuma a cikinsa samun rabonku bayan mutuwarku yake, da kariyarku da tsirarku daga fitintinu wadanda suke yawaita duk lokacin da Kiyamah ta kara kusantowa, fitintinu wadanda suke da sarkakiya a farkon faruwarsu, sai kuma su bayyana su fito sarari a karshen lamuransu; don haka, babu wanda zai tsira daga fitintinu sai wanda yayi riko da Alkur'ani da Sunnah, kuma ya lazimci jama'ar Musulmai;

Sai ku yi tadabburi, ko nemi sanin ma'anar littafin Allah Mabuwayi da daukaka, kuma ku yi aiki da shi, sannan ku haddace abin da addini zai tsayu da shi, na sunnar Manzon Allah صلى الله عليه وسلم, kuma akida ta ingantu da shi, itama ibada ta samu kamala da shi, musamman hadisan da ma'anoninsu ya game hukunce-hukuncen Musulunci, wadanda suka kunshi falaloli, sai ku san ma'anoninsu, domin ku yi riko da su kuma ku yi aiki, domin wannan shine MANHAJIN MAGABATA NA KWARAI, wadanda Allah Ta'alah ya fada, akansu: "Masu rigayen farko daga Muhajirawa da Ansarawa, da wadanda suka bi su da kyautatawa, Allah ya yarda da su, kuma suma sun yarda da shi, kuma ya musu tanadin gidajen Aljannoni, koramu suna gudana a karkashinsu, suna masu dawwama a cikinsu har abada, wannan shine rabo mai girma" [Tauba: 100].

Kuma –a wannan matsaya- zan kawo hadisi daya daga cikin dunkulallun magana (Jawami'ul kalim), wanda ya wajaba kowane Musulmi namiji da Musulma suyi aiki da shi, a cikin kowane hali, kuma dole ne mazaje da mata su rika aiki da hadisin matukar akwai rai a cikin jikinsu, Wannan kuma shine, fadinSa –صلى الله عليه وسلم-: "Addini nasiha ne, addini nasiha ne, addini nasiha ne. Sai muka ce: Ga wa Ya Ma'aikin Allah? Ya ce: Ga Allah ne, da littafinSa, da ManzonSa, da kuma shugabannin Musulmai, da kuma sauran gama-garinsu", Muslim ya ruwaito shi, daga hadisin Tamim Ad-dariy (رضي الله عنه). Kuma wasu Maluma dayawa banda Muslim, suma sun ruwaito shi; daga cikin Maluman hadisi.

Kuma hadisi ne mai girman sha'ani, Imam Abu-dawud ya ce: "Fik-hu yana gudana akan hadisai guda biyar; hadisin halal a bayyane yake, haram a bayyane yake, da hadisin babu cuta babu cutarwa, da hadisin: dukkan ayyuka suna tare da niyyoyinsu, da hadisin: addini nasiha ne, da hadisin: Abin da na hane ku, ku nisance shi, wanda kuma na umarce ku, to ku zo da shi gwargwadon iko".

Kuma Alhafiz Abu-Nu'aimin ya ce: "Wannan hadisi ne da yake da sha'ani mai girma, Muhammadu bn Aslam Ad-duwsiy ya ambaci cewa, lallai hadisin addini nasiha ne, daya ne cikin kashi hudu na addini".

 

Yana daga cikin dalilan da suka nuna cewa; lallai wannan hadisin, wajibi ne ga kowane Musulmi namiji da kuma mace musulma, su yi aiki da shi, koyaushe, Lallai Allah Ta'alah ya dauke wasu ibadodi, ga wasu daga cikin Mutane, saboda wani uzuri, ko saboda wasu sababi, amma bai dauke yin nasiha ba, karkashin kowane uzuri, ko cikin kowane hali, Allah Ta'alah ya ce: "Babu kunci ga Maraunana, kuma babu laifi, ga majinyata, da wadanda basu samu abin da za su ciyar ba, matukar sun yi nasiha ga Allah da ManzonSa, kuma babu wata hanya (ta cutarwa) ga masu kyautatawa, Allah shine Mai yawan gafara, Mai jin-kai" [Tauba: 91].

Sai Allah ya bayyana cewa, ba za a yi uzuri ga wani Musulmi ba, kan yin watsi da nasiha, daidai da kyaftawar ido (koda yana da uzuri).

 

Sahabbai basu yi tambaya kan ma'anar nasiha ba, saboda sahabban sun san abin da kalmar take nuni akansa na ma'anonin addini mai fadi ta kowace fiska, domin hakikanin nasiha ya kunshi, martabobin addini uku na Musulunci da Imani da Ihsani.

Kawai abin da sahabbai suka tambaya, shine Ga wa ake nasihar, kuma wanene suka cancanceta?

 

Kuma asalin ma'anar nasiha, shine Tsamo abu ko cire shi daga abubuwan da suka shiga masa domin gurbata shi, a larabci ana cewa; Nasahal asala, wato ya tace zuma, idan Mutum ya tsaftace zumar daga kwansonsa.

 

Kuma MA'ANAR YIN NASIHA GA ALLAH TA'ALAH ya kunshi, Son Allah, da kan-kan-da-kai a gare shi, da rusuna masa, da mika-wuya ga shari'arsa, domin neman yardarSa da ladanSa, da kuma tsoron fushinSa da azabarSa, Allah Subhanahu ya ce: "Kawai masu imani da ayoyinmu, sune wadanda idan aka fadakar da su da ayoyin, sai su fadi suna masu sujada, kuma suna yin tasbihi game da gode wa Ubangijinsu, alhali ba su yin girman kai * sasanninsu suna nisantar wuraren kwanciya, suna kiran Ubangijinsu bisa ga tsoro da tsammani, kuma suna ciyarwa daga abin da muka azurta su" [Sajada: 15-16].

Kuma AllahTa'alah ya ce: "kuma Masu imani sune masu tsananin so ga Allah" [Bakara: 165].

Kuma Annabi صلى الله عليه وسلم  ya ce: "Ku so Allah daga dukkan zukatanku, saboda abin da yake ciyar da ku da shi, na ni'imomi".

 

        Kuma mafi girman nasiha ga Allah, itace bauta masa Subhanahu, ba tare an hada shi da abokin tarayya ba, cikin tsarkake niyyah, da aiki da Sunnah da bin shiriyar annabi Muhammadu صلى الله عليه وسلم, da kebance Ubangiji da na'ukan ibadodi dukkansu, kamar addu'a da neman taimako, agaji, da tawakkali, Allah Ta'alah ya ce: "Ka ce, lallai kawai ina rokon Ubangijina ne, ba zan masa shirki ko hada shi da kowa ba" [Jin: 20].

        Shi kuma Ubangiji Mabuwayi da daukaka ana masa bauta ne, saboda abin da yake da su na sifofin kamala da girma, da kuma yadda ya tsarkaka daga sisfofin tawaya (nakasa), da kuma saboda abin da Allah yake da su na ni'imomi ga halittunSa, da bukatuwan bayi zuwa ga rahamarSa; don haka: Ita ibada sababi ce na samun alherorin Allah, kuma sababi ce na tunkude sharrace-sharrace ga Mutum, a cikin rayuwarsa da kuma bayan mutuwarsa.

 

        Kuma nasiha ga Allah Tabaraka wa Ta'alah tana kasancewa ta hanyar tabbatar wa Allah abin da ya tabbatar wa kansa a cikin littafinSa, da kuma abin da ManzonSa ya tabbatar masa da su; na sunaye da sifofi, akan abin da magabata na-kwarai suka kasance akansa, Allah ya yarda da su, amin. An ruwaito daga Abu-Umamah رضي الله عنه daga Annabi صلى الله عليه وسلم, Allah Ta'alah ya ce: "Mafi soyuwan abin da bawana ya bauta min da shi, shine yin nasiha a gare ni", Ahmad ya ruwaito shi, da 'Dabaraniy a cikin mu'ujam kabir.

 

        Kuma ma'anar yin nasiha ga Manzon Allah صلى الله عليه وسلم itace: son annabi da darajanta shi da girmama sunnarsa, da aiki da umurninsa, da hanuwa da haninsa, da yin bauta wa Allah da shari'arsa, da bibiyar shiriyarsa, da gaskata labarunsa, da yada hadisansa, da yin da'awa zuwa ga addininsa, Allah Ta'alah ya ce: "Ka ce: Ku yi da'a ga Allah, kuma ku yi da'a ga Manzo, amma idan kuka bijire, to lallai akansa akwai abin da aka aza masa, kuma akanku akwai abin da aka aza muku, kuma idan kuka masa da'a zaku shiryatu" [Nur: 54].

 

Kuma ma'anar yin nasiha ga Littafin Allah Ta'alah itace: Girmama Alkur'ani mai karamci, da sonsa, da yin kokari wajen koyan karatunsa da karantar da shi, da neman sanin hukunce-hukuncensa, da yin tilawarsa tilawa ingantacciya, da yin aiki da umurnin Alkur'ani, da barin haninsa, da dawwama kan tilawarsa, da kiyaye harrufansa da iyakokinsa, da sanin tafsirinsa da ma'anoninsa, da abin da aka nufa da shi, da yin tunani cikinsa, da dabi'antuwa da shi, da yin raddi ga wadanda suka karkata wajen fahimtar Alkur'ani da sunnah, tare da ruguza barnace-barnacensu, da tsawatarwa akansu, Allah Subhanahu ya ce: "Lallai wannan Alkur'anin yana shiryatarwa zuwa ga hanyar da tafi kyawu" [Isra'i: 9].

 

Kuma ma'anar yin nasiha ga Shugabannin Musulmai itace: So musu alheri, da son su yi adalci, da yin farin-ciki idan aikinsu ya yi dace, da nisantar algus a gare su, da kin ha'intarsu, da kuma (uwa uba) kada Mutum ya yi fito-na-fito da su, ko ya taimaki makiya akansu, tare da taimaka musu cikin lamarin gaskiya, da yin biyayya a gare su cikin abin da ba sabo ba, da yin addu'ar dace a gare su, da addu'ar dacewa da gaskiya a cikin hukuncin da suke yi, An ruwaito daga Abu-hurairah (رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), ya ce: "Lallai Allah yana yarje muku abu uku, yana yarje muku, ku yi bauta a gare shi; kada ku hada shi da kowa, kuma ku yi riko da igiyar Allah gaba daya, kada ku rarraba, kuma rika nasiha ga wadanda Allah ya jibinta musu lamuranku", Muslim ya ruwaito shi.

Abdullahi bn Mas'ud رضي الله عنه ya ce: "Lallai abin da kuke kyama alhalin kan jama'a yana hade shine mafi alheri akan abin da kuke so, a halin rarrabuwa".

Kuma nasiha shine amincin zuciya

Kuma an ruwaito dagaabin da Jubair bn Mud'im, daga Annabi صلى الله عليه وسلم ya fada a cikin hudubarsa a masallacin Khaif (dake Minah): "Abu uku zuciyar Mutum Musulmi baya daukar kyashi akansu; Tsantsanta aiki ga Allah, da yin nasiha ga Majibinta lamura (shugabanni), da lazimtar jama'ar Musulmai", Ahmad ya ruwaito shi da Alhakim.

Kuma an ruwaito daga Ma'akil bn Yasar, daga Annabi صلى الله عليه وسلم ya ce: "Babu Mutumin da Allah zai bashi wani abin kiwo, sai bai kewaye su da nasiharsa ba, face ba zai shiga Aljannah ba", Bukhariy da Muslim da Ahmad suka ruwaito shi.

 

Ita kuma ma'anar nasiha ga dukkan Musulmai itace: Fadakar da su zuwa ga maslahohinsu, da ilmantar da su lamuran addininsu, da sitirce al'aurarsu, da kokarin toshe ko biya musu bukatu, da nisantar algus ko ha'intarsu, da nisantar yin hasada a gare su, da kyautata musu.

Nasiha sifa ce ta Annabawa da Manzanni Amincin Allah ya tabbata a gare su, Allah Ta'alah ya ce:( Hakika manzo ya zo muku daga cikinku mai jin nauyin abin da ya wahalar da ku, mai muku fatan alheri kuma mai tausayi da jinkai ne ga muminai)

Kuma yace game da Nuhu Amincin Allah ya tabbata a gare shi( Ina isar muku da sakon Ubangiji na kuma ina muku nasiha) Kuma yace game da Hudu Amincin Allah ya tabbata a gare shi( Ina isar muku da sakon Ubangiji na kuma ni a gare ku mai nasiha ne amintacce).

Kuma yace game da Salihu Amincin Allah ya tabbata a gare shi :( Hakika na isar muku da sakwannin Ubangiji na kuma na yi muku nasiha)

Nasiha sifa ce ta mumunai Allah Mai tsarki da daukaka ya ce game da muminin Alu Yasin : ( ya ku muta ne na: ku bi manzanni) (sai aka ce : ka shiga aljanna sai yace ina ma da mutane na sun sani)

Ibnu Abbas Allah ya yarda da shi ya ce :  ya yi nasiha ga mutanensa a halin yana raye da bayan ya mutu.

  Allah Ta'alah ya ce: "Lallai Muminai 'yan'uwan juna ne", [Hujurat: 10] " (Kuma ku yi riko da igiyar Allah gaba daya, kuma kada ku rarraba" [Ali-imrana: 103],

 

Allah ya yi mini albarka NI da KU, cikin alkur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abin da ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,      Na fadi abinda ku ke ji, kuma ina neman gafarar Allah Mai girma ga Ni da KU da sauran Musulmai daga kowani zunubi, Ku nemi gafararSa,    lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.


 

HUDUBA TA BIYU

        Yabo ya tabbata ga Allah Masanin abin da ya buya na gaibu, Mai jujjuya zukata, Mai yaye musibun da suka sauka da bakin ciki, Ina yin yabo ga Ubangijina kuma ina gode masa akan ni'imominSa gaba daya; wadanda suka gabata da wadanda zasu zo,

Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai yake bashi da abokin tarayya, Mai yawan gafarar zunubai,

Kuma ina shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawanSa ne ManzonSa zababbe,

Ya Allah ka kara salati da sallama da albarka ga bawanka kuma Manzonka Muhammadu, da iyalansa, da sahabbansa madaukaka, masu takawa.

 

Bayan haka … !!

Sai ku yi takawar Allah Ta'alah, a asirce, da kuma a bayyane, domin da takawa ne zaku samu mafi kololuwar daukaka, kuma ku rabautu da alkhairori a wannan rayuwar, da kuma bayan mutuwanku,

 

Ya ku Bayin Allah … !!

Ku yi tunani akan fadin Allah Ta'alah: "Kuma Muminai maza da mata, sashensu majibincin sashe ne, suna yin umurni da kyakkyawa, kuma suna hani da abin da ba a so, kuma suna tsayar da sallah, kuma suna bayar da zakka, kuma suna da'a ga Allah da ManzonSa, wadannan lallai Allah zai yi rahama a gare su, Lallai Allah Mabuwayi ne Mai hikima" [Tauba: 71]. A cikin wannan ayar akwai taimaka wa juna, da tallafar juna, da nasiha wa juna, da agaza wa juna, da 'yan'uwantaka, da jin-kai da rahama da kauna.

        Kuma an ruwaito daga Jarir bn Abdullahi, ya ce: "Na yi mubaya'a ga Manzon Allah صلى الله عليه وسلم akan tsayar da sallah, da bada zakka, da yin nasiha ga kowane Musulmi", Bukhariy da Muslim su ka ruwaito shi.

Kuma Abubakar Almuzaniy ya ce: "Abubakar رضي الله عنه bai fi sauran Sahabban Manzon Allah صلى الله عليه وسلم yawan azumi ko salla ba, saidai ya yi fice ne da wani abu da ya tabbatu a cikin zuciyarsa",

Ibnu-Ulayyah ya ce: "Abin da ya kasance a zuciyar Abubakar shine, soyayya don Allah Mabuwayi da daukaka, da yin nasiha ga halittarSa".

        Kuma an ruwaito daga Hakim bn Abiy-Yazid, daga Babansa, daga Annabi صلى الله عليه وسلم ya ce: "Idan dayanku ya nemi nasihar dan'uwansa, to ya masa nasiha", Ahmad ya ruwaito shi, da 'Dabaraniy a cikin mu'ujam kabir.

.

        Ya ku Bayin Allah… !!!

        "Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan Annabin, Ya ku wadanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da sallamar amintarwa" [Ahzab: 56].

Ya Allah! Ka yi salati da sallama wa Annabi Muhammadu,

 

 


 


 

 


 

 

 


 

 


 

 


 

 


 

 


 

 


 

 


 

 


 

 

 

YAWO A GONAN ZUNUBAI

 ترجمة خطبة المسجد النبوي 

الخطيب الشيخ عبد الباري الثبيتي

المترجم : أمين سعد

اللغة : الهوسا

Hudubar Masallacin Annabi Na shaikh Abdul bari Bin Awad  Assubaiti

19/4/1442AH 4/12/2020Ac

Hudubar Farko

 

Da sunan Allah da godiya a gare shi nake farawa, tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzon Allah, Shiyarwar Manzon Allah shi ne mabubbuga na alheri, kuma da haske ne mai fantsama da kuma hasken rayuwa : yana tare da kai har a lokacin zamewa da kuskurewa, Buhari ya rawaito daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : lalle wani bawa ya aikata zunubi ko kuma yace ya yi wani zunubi,sai ya ce : ya Ubangiji na yi laifi ko kuma na aikata laifi, ko na aikata wani to ka gafarta mini, sai Ubangijinsa ya ce : ase bawa na ya san yana da Ubangiji yana gafarta zunubai kuma ya yi damka sabo da shi? na gafarta wa bawa na, sannan ya zauna na wani lokaci da Allah ya so sai ya sake aikata zunubi ko ya yi laifi sai ya ce ya Ubangiji na yi zunubi ko na aikata wani laifi to ka gafarta shi, sai ya ce : bawa na ya san yana da Ubangiji yana gafarta zunubi kuma yana damka da shi? na gafartawa bawa na, sai ya zauna na wani lokaci da Allah ya so sai ya  sake aikata zunubi ko ya yi laifi sai ya ce ya Ubangiji na yi zunubi ko na aikata wani laifi to ka gafarta shi a gare ni. Sai yace :Bawa na ya san yana da Ubangiji da yana gafarta zunubi kuma yana damka da shi? Na gafartawa bawa na har sau uku, to ya aikata abin da ya so,)

Wannan hadisi yana hakaito halin bawa game da zunubi da tsarin musulunci wurin gyara halin masu laifi- dukkan mu masu laifi ne – yana bude kofar fatan alheri da kofa ta alhini kamar yadda ake surantawa kowani mai laifi rahamar Allah da ta yalwaci dukkan komai da kyautarSa ga masoyanSa, da tausayinSa ga bayinSa.

Wannan hadisi na farawa ne da fadinsa (Lalle bawa ya yi zunubi)    musulunci na lura da yanayin rayi irin na mutum, wacce ta ke aukawa cikin zunubai, kuma kafa ta zame da ita bisa mantuwa ko wata shubuha ko sha'awa, a dalilin fizga irin na shaidan da batarwarsa: An karbo daga Abu Said daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, lalle iblis ya ce da Ubangijinsa Mabuwayi da Daukaka, na rantse da buwayarka da daukakarka bazan gushe ba ina batar da bani adama muddin rai na gangan jikinsu, sai UbangijinSa Mabuwayi da daukaka ya ce :Na rantse da buwaya ta da Daukaka ta ba zan gushe ba ina gafarta musu muddin suka nemi gafara ta.). Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : na rantse da wanda raina ke hanun shi, ba don kuna laifi ba da Allah ya tafiyar da ku sai ya zo da wasu mutane suna laifi kuma suna neman gafara sai ya gafarta musu.)

     (lalle wani bawa ya aikata zunubi sai yace ya Ubangiji na yi laifi) mutum ya yi ikirari da zunubinsa wannan wani jarumta ne, da nuna ya san lalle ya yi kuskure wannan kankan da kai ne da rusunawa, wannan shine matakin farko na gyaran zuciya da ladabtar da ita, Allah Madaukakin Sarki ya ce : (wasu sun yi furuci da laifukansu sun cakuda ayyuka na kwarai da wani mummuna, ana fatan Allah ya yafe musu lalle Allah Mai gafara ne Mai jinkai)

A cikin fadin Manzon Allah ga Aisha Allah ya kara yarda a gare ta (Lalle idan bawa ya yi furuci da zunubansa ya kuma tuba sai Allah ya karbi tubansa)

Musulmi na furuci da zunubansa a duniya ya tabbatar da su a lahira, to idan ya aikata haka sai a gafarta masa zunubansa da izinin Ubangijinsa, An karbo daga Abdullahi dan Umar Allah ya kara yarda a gare su, yace na ji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : (Lalle Allah na kusanto da mumini sai ya dora kariyarSa ya suturce shi. Shin ka san zunubi kaza? Shin ka san zunubi kaza? Sai ya ce : e ya Ubangiji, har zuwa lokacin da ya tabbatar da zunubansa ya fahimci cewa ya halaka, sai Allah ya ce na suturtata a gare ka a duniya to a yau na yafe ma ita, sai a bashi littafin shi na kyawawan ayyukansa).  

furuci da zunubai yana da lokacinsa idan ya wuce to sai ukubar zunubai ta sauka gare shi, Allah Madaukakin Sarki ya ce game da 'yan wuta  wadanda basu yi furuci da gajartawansu ba sai bayan sun dandani azabar wuta: (sai suka yi furuci da zunubansu to nesa ga 'yan wutar sa'ira).

  Musulunci ya nusar da musulmi zuwa ga ikirari da furuci da zunubai sai dai ya yi gargadi game da tonon asiri da yada kuskurensa bayan Allah ya suturce shi, Manzon Allah tsira da amincin Allah tsira da amincin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : (Dukkan al'uma ta na samun waraka sai masu bayyana sabo, na daga cikin bayyana sabo mutum ya yi wani aiki da dare bayan Allah ya suturta shi, sai ya ce ya wane na aikata kaza da kaza a halin ya kwanaUbangijinsa na suturta shi, sai ya wayi gari yana yaye suturawar Allah a gare shi.)

    

Na daga cikin falalan Allah a gare mu  suturtawan aibi da kiyaye anbato tsakanin halittu. Wani mutum  yace ga daya daga cikin magabata  : ya ya ka wayi gari? Sai yace : tsakanin ni'imomi biyu, ban sani ba wanne ta fi wani zunubai da Allah Mabuwayi da Daukaka ya suturta ta ba wani da zai iya aiba ta ni da su, da kauna da Allah ya jefa cikin zukatan bayi guri na ba zai iya riska ba, Bawa yana cewa na yi laifi ga raina na disan kunya sabo da ya saka da  kyauta mai kyau bisa sabo mummuna,  zuciyarsa na  fito da radadi sabo da nauyin zunubai da tsananin tsoron Allah, wannan yanayi da

Wannan wani Abu ne Mai ratsa jiki da yanayi na ruhi da ke rayye wanda hakan na karfafan imani kuma ya  kan janyo rahamar Ubangiji Mai rahama.

Komowa zuwa ga Allah bayan zunubi wata kyauta ce  daga Allah kuma raya makunnin shiriya ne bayan duhun sabo, Allah Madaukakin Sarki yace:

: ( Lallai wadanda suka ji tsoron Allah Idan wani yanki NA shaidan ya shafe su sai su tuna sai ga shi suna gani irin na basira).

Sau dayawa wani zunubin kan haifar da rayayyen zuciya ga ma'abocin shi da kankan da kai da rusunawa da kuma fiskantar Allah  da gaggawa wurin aikin alheri , sau dayawa sabo  kan haifar da tuba ga ma'abocinsa ,  tuba irin wanda ke daga matsayinsa  ya gyara halayensa , kuma ya kara imanin sa , kuma ya gyara rayuwarsa .

Ya zo a sunna  ingantacce cewa wani sahabi ya aikata wani zunubi mai girma sannan ya tuba  bayansa ,  tuban da  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce game da ita   (Hakika ya yi tuban da  da za a kasa ta tsakanin al'uma da ta ishe su ).

Ya zo a hadisi (Ya Ubangiji na aikata zunubi ka gafarta mini ), (Wanene ke gafarta zunubi   face Allah ):- shi ne wanda tsarki ya tabbata a gare shi ya ke cewa (Ka labartawa bayina lallai ni dinnan mai gafara ne  mai jin kai ) kuma mai cewa wanda ya aikata wani mummuna ko ya zalunci kansa to, zai samu Allah mai gafara kuma mai rahama) . Ya zo a hadisil kudusi .

 (Ya  ku bayi  na lallai ku kun kasance kuna kusakurai a cikin dare da yini  , kuma ni ina gafarta zunubai gaba daya  to ku nemi gafara na , sai in gafarta mu  ku). Ya zo a cikin hadisi (Ya Ubangiji na  na yi zunubi to ka gafarta mini ). To istigfari tarihi ne na Annabawa,  kuma abin nanatawa ne  a bakin salihai, kuma  shi dinnan magani ne na cututtuka ; yana gyaran rayi , ya tsarkake  ta kuma   ya shigar da kyawawa  , shi ne hasken da yake zuwa ga zunubai  sai ya halaka ta ya zo ga zukata marasa lafiya sai ya ingantata, ya zo ga rayuka masu nauyi sakamakon zunubai sai ya  mikar da shi, ya sanya rayuwa ta zama ado,  rayi kuma ya zamana mai sheki Allah Madaukakin sarki ya ce :- (Kuma ku nemi gafarar Ubangijin ku kuma ku tuba zuwa gare shi , zai jiyar da ku dadi,  jin dadi mai kyau zuwa wani lokaci abin ambato, kuma ya bawa ko wani ma'aboci falala falalarsa ) Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:- (Lallai ni ina  neman gafara  zuwa ga Allah kuma in tuba zuwa gare shi  sama da sau saba'in a wuni  ) ya zo  a hadisi  sai Ubangijin shi ya ce :- ( Ase bawa na ya san yana da Ubangiji mai gafarta zunubai , ? kuma yana damka da shi ? to na gafartawa bawana ) (na gafartawa bawa na) :- Kalmace da take kamar wani magani na yanke  wurin waraka bisa ga zukata masu tsoro , da kwarara natsuwa a cikin zukata  masu tsoro; kalma ce da Allah ke tabbatar da tsarkin jiki  da ita, da  kawar  zuciya   da walwala a rayuwa , kuma ta goge zunubanka  ta yaye zuciya  kuma ta saukake alhaki wanda bayanka  ke dauke da shi .

(Na gafartawa bawana ).Fa'ida ne wanda  ya san Ubangijin shi zai  fiskance shi,   ya ji tsoron mahaliccin shi kuma zubowan hawaye kamar tsani ne zuwa gare shi .

 (Na gafartawa bawa na ) Kalma ce  da ke wasa himma na muminai kuma ta karfafi azamar masu zunubai , ta hanyar gaggawa zuwa ga neman gafara da ribatar dama , da neman mafaka a wurin Allah , to zunubbai , suna da mai rahama kuma mai jin kai  zai goge ta , da Allah mai  tausayi da zai gafarta musu .

Wanda ya gafala daga neman gafara bayan aikata sabo , ko kuma bai haura don nemanta ba to  lallai ya wajaba ya tada idanuwan sa daga gyangyadin da yake yi  kuma ya rinka bibiyan  imaninsa , wannan alamace na mutuwar jin bawa na aikata sabo, Allah Madaukakin sarki ya ce :- (kar ku kasance kamar wadanda  suka manta da Allah sai ya mantar da su kawunansu, wadannan sune fasika).

        Mafi girman zunubai shine bawa ya manta cewa shi  yana cikin mantuwa wannan shi ne tarun bala'i , kuma wannan ita ce asara  mai mummunan karshe  Allah  ya yi gargadi ga wanda ya  zalunci kansa  ya bijirewa istigfari, sai yace :  ( Ase ba za su tuba zuwa ga Allah bakuma su nemi gafararSa lalle Allah Mai gafara ne kuma Mai jinkai)

(Allah yace :Na gafartawa bawana  sau uku ya aikata abin da ya so).fadinSa (ya aikata abin da ya so) ba ya nufin umarni ne da ya aikata sabo ba, sai dai ana nufin tun da ya kasance haka a ko yaushe ya yi zunubi zai tuba to  zunubin ba zai cutar da shi ba bayan  tuba, sabo da tuba na goge abin da ke kafinta, sai dai mutum ya kiyaye daga aikata sabo, sabo da yana da yakini bisa ga sabo amma bai da yakini bisa ga gafara, kuma  zain iya rasa dacen tuba.

Kiyayewa daga  zunubai wajibi ne ,; sau dayawa zunubi kan lalata zuciya  ya fusata Ubangiji , kuma ya bakanta hanya , kuma yakan sa saukar da ukuba a doron kasa, a debe albarkan , a kazanta fidira a rarraba dangi .

Yin ko inkula da sabo dabi'a ne abin zargi,   wofantar da halin mai zunubi abu ne mai yanke kauna da cire tsammani , Allah Madaukakin sarki ya ce :- (Ka ce  ya ku bayi na  wanda suka yi barna bisa kawunan su kar ku yanke kauna daga rahamar Allah , lallai Allah yana gafarta zunubai gaba daya , lallai shi mai gafara ne mai jin kai).

 

HUDUBA TA BIYU

Na daga cikin hakurin Allah  jinkirtawa mai laifi har ya tuba , idan ya koma kuma ya tuba Allah sai ya karbi tubansa , Allah baya gajiya sai dai ku ku gaji ; ya zo a hadisi , cewa:- Shugaban istigfari  shi ne ; bawa ya ce :- (Ya Allah kai ne Ubangiji na ba abin bautawa da gaskiya sai kai , ka halicce ni kuma ni bawanka ne , kuma ina bisa alkawarinka mai karfi da alkawarinka , iya- iyawa na, ina neman tsarinka bisa ga sharrin abin da na aikata , ina komowa a gare ka da ni'imominKa da ke gare ni , kuma ina komowa gare ka da zunubi na –wato yana furuci da shi to, ka gafarta min lallai ba mai gafarta zunubai  sai kai .