الجمعة، 4 سبتمبر 2020

KA JI TSORON ALLAH A KO INA KA KE

 

اسم المترجم :أمين سعد

اللغة : الهوسا

التاريخ 16/1/1442ه

Hudubar masallacin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi na 16/1/1442 na shaihk Husaini Al -Asshaikh

 

Hudubar farko:

An karbo daga Mua'azu dan Jabal Allah ya kara yarda a gare shi daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:(ka ji tsoron Allah a duk inda ka ke, kuma ka bi mummuna da kyakkyawa sai ta goge ta, ka mua'amalanci mutane da kyakkyawar dabia'a) Ahmad ne ya rawaito da Tirmizi kuma ya ce hadisi ne hasan, kuma da yawa daga cikin malamai sun inganta shi lallai hadisi ne mai girma da ya kumshi wasiyya mai girma wanda ya ke masu jumloli masu girma da ka'idoji muhimmai Ibnu hajar alhaisami ya ke cewa: wannan hadisi ne da ya tattaro sauran hukunce hukunce na shari'a wasun su sun ambace shi da uwar sunna ,aiki da shi ya kan kawo walwalan gidan duniya da na lahira da rabauta a cikin su:

Tushe na farko : akwai tabbatar da takawa ga Allah Mabuwayi da daukaka ta hanyan lizimtan umarnoni da da'a da kuma nisatan sabo da laifuka a bayyane da kuma boye .

Lallai wasiyya ce da ta kan sa bawa duk inda ya ke ya lizimci kiyaye dokokin Allah kuma ya yi nesa daga abubuwa na laifi da abubuwa da su ke muharramai , yana mai daidaito a kan tafarki mekakke yana mai kulawa da shi a cikin dukkan sha'ani Allah Madaukakin sarki ya ce :(ku ji tsoron Allah kuma ku sani lallai Allah yana ganin abin da ku ke aikatawa)

Kuma Allah Madaukakin sarki ya ke cewa(ku ji tsoron rananda za ku koma zuwa ga Allah sa'an nan a cikawa ko wace rayi abunda ta kasance ta ke aikatawa ba za ayi zalunce ku ba).

Ibnu Abbas da Sa'id dan Jubair suka ce: wannan wasiyyar Allah ce ga bayinSa a a'aya ta karshe da ta sauka a cikin alkur'ani , kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:(ka kiyaye Allah sai ya kiyayeka). Lallai aiki da wannan asali yana hukunta samun rabauta mai girma da kuma lada mai daraja.

Ya zo cikin sahihain wato Bukhari da Muslim cewa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Mutane bakwai Allah na musu inuwa a cikin inuwarSa ranar da ba wata inuwa sai inuwarSa, kuma ya ambaci a cikinsu da mutumin da mace ma'abociya matsayi da kyawu ta neme shi sai ya ce lallai ni ina tsoron Allah Ubangijin talikai)

Tushe na biyu: biyar da kyakkyawa bayan mummuna, ita kyakkyawa kalma ce da ta tattaro dukkan abin da zai kusantar zuwa ga Allah Mabuwayi Mai daukaka, mafi girman kyawawan abin da su ke tunkude munana shi ne tuba da gaske da kuma neman gafara ta gaskiya da kuma komawa zuwa ga Allah komawa ta gaskiya,

 Imamu Ahmad ya rawaito daga Abu zarri ya ce : Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (wani ya ce: ya Manzan Allah ka mini wasiyya sai ya ce: idan ka yi aiki mummuna to ka biyo ta da kyakkyawa sai ta goge ta ,sai ya ce: ya Manzan Allah na daga cikin kyawawa (la ilaha illallah)?sai ya ce ita ce mafificiya a cikin kyawawa).

Aikata ayyukan alhairi yana  kankare zunubbai da suka shude Allah Mabuwayi da daukaka ya ce:(kuma ka tsaida sallah a gefe guda biyu na gini da wani yanki na daga dare lallai ne ayyukan kwarai suna kore munanan ayyuka).

Allah Madaukakin sarki ya ce:(idan za ku nesaci manyan zunubai to za Mu kankare muku laifuka (kanana)), yazo a sahihu muslim (salloli guda biyar da kuma juma'a zuwa juma'a da ramadana zuwa ramadan suna masu kankare zunubban da ke tsakaninsu muddin aka nesaci manyan zunubai).

Tushe na uku: mu'amalantar halittu da kyawawan dabi'u da kuma kyawawan halaye da kuma tafarki wanda ya ke mai kyau wannan kuma ta hanyan dadadawa halittu da sake musu fiska da yalwata ayyukan ma'arufi gare su da kuma kamewa daga cutar da su, asali shi ne ka yardarwa dan uwanka abin da ka yarda wa kanka na daga maganganu kyawawa da ayyuka kyawawa da muamala na mutunci,Allah Madaukakin sarki ya fada yana mai yabo ga ManzonSa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi (lallai kana kan wasu dabi'u masu girma)  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (mafi cikan mumini imani shi ne wanda ya fi su kyakkyawan hali) Tirmizi ya rawaito kuma ya ce hadisi ne hasan sahihi,Ibnu hibban da hakim sun inganta shi , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:(lallai mumini yana riskan darajan mai azumi da mai tsayuwa ta hanyan kyawawan halayensa) Abu dauda ne ya rawaito kuma Ibnu hibban ya inganta shi.

Ka yi kokari ya kai dan uwana musulmi a rayuwanka ka kasance cikin ma'abota kyawawan hali kuma masu bin abu buwa na yardan Allah wannan shi ne aiki mai girma a wurin Allah kai  Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kidanya haka ma cikin da'a  mai sadarwa zuwa ga aljannan alkuld.

An tambayi Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi menene biyayya kuma da laifi? Sai ya ke cewa:(Biyayya: ita ce kyakkyawan hali, shi kuma laifi shi ne abin da ya sosa cikin zuciyarka kuma ka kyamaci mutane su tsinkaye shi) Muslim ne ya rawaito.

Hakika an tambaye shi kuma game da yawan abin da ke shigarwa aljanna sai ya ce (tsoron Allah da kyakkyawan hali) Tirmizi ne ya rawaito kuma ya ce hadisi ne hasan sahihi , Ibnu hibban ingantashi

Ku tabbatar - Allah ya muku rahama- wadannan ginshikai masu girma ku lizimce su wadannan ka'idoji masu girma za ku samu rabauta ku samu walwala da nasara a duniya da lahira .

 

Huduba ta biyu:

  

Na daga cikin kyawawa wadanda su ke goge laifuka shi ne akwai kyautata wa mutane ta fiskoki daban daban, Allah Madaukakin sarki ya ce (ku kyautata lallai Allah yana son masu kyautatawa) ,

 An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce: wani mutumi ya ce ya Manzon Allah : lallai wance tana yawaita  sallolinta da sadakanta da azuminta sai dai kawai tana cutar da makwabciyarta da harshenta sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (tana wuta) , sai aka ce ya Manzon Allah lallai wance ana ambaton karancin  azuminta da sallan ta kuma tana yin sadaka da  wani yanki na cukui amma bata cutar da makwabtanta , sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (tana cikin gidan aljanna) Ahmad ne da Bazzar suka rawaito da Ibnu hibban a cikin sahihansu da hakim kuma ya ce hadisin sahihi ne isnadinsa da kuma wasu sashi na daga malaman hadisi sun ingantashi.

الجمعة، 28 أغسطس 2020

DAGA SHIRYARWAR SURATUL IKHLAS

 

اسم المترجم :أمين سعد

اللغة : الهوسا

التاريخ 9/1/1442ه

Hudubar masallacin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi na 9/1/1442 na shaihk Abdul Bari dan Awad Alsubaiti

 

Hudubar farko:

 Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzon Allah da iyalanSa da sahabbansa da wanda suka biyo su,,,,,, bayan haka:

wata sura ce mai girma, - dukkan surorin Alkur'ani kuma na da girma- gajeruwa ce a harufanta, amma tana da zurfin ma'ana a ma'anoninta, ta tattaro abubuwa da su ke na dabi'u masu kyau ta kebanta da girma na falaloli tana daidai da daya bisa ukun Alkur'ani , Allah Madaukakin sarki ya ce:(ka ce : Allah Shi daya ne) (Allah wanda ake komawa yayin bukata)(Bai haifa ba kuma ba a haife Shi ba )(kuma bai da wani da ya ke kininSa), kul huwa Allahu ahad,  Allah : wannan sunan shi ne sunan da yafi ko wanne cikin sunayen Allah kuma shi ne sunan da ya fi ko wanne a wurin biyayya da kuma wurin tattarowa, Allah : shi ne suna mafi girma , shi ne abin ambato mafi daukaka , jalalarSa ta cika sammai bakwai da abin da ke cikinsu kasaitarSa ta kewaye doron kasa da abin da ke kanta da abin da ke karkashinta da kuma abin da ke cikinta sanin Allah tushe ne na dukkan ilimi, kai shi ne sani mafi daukaka kuma mafi girma mafi kasaita Allah Madaukaki ya ce:(Shi ne Allah a cikin sama kuma a kasa)

Babu rayuwa ga zukata kuma babu farin ciki babu annashawa babu ni'ima babu debe kewa face na cikin sanin Allah , Malik dan Dinar ya ce: ''Miskinan gidan duniya sun fita daga gidan ba su dandani abu mafi dadi ba a cikinta sai aka ce da shi , menene abu mafi dadi a cikinta? Sai ya ce: sanin Allah da kaunarSa''

sani ne wanda ke tabbatar da wuyaye a masaukai na bauta da kankan da kai da rusunawa da kauna , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:(lallai Allah na da sunaye  casa'in da tara, dari ba daya duk wanda ya kiyaye su zai shiga aljanna), duk wanda ya so Allah da sunayen Shi da siffofin Shi Allah zai kaunace shi idan ya so shi kuma zai debe kewa tare da ambaton shi kuma zai yi shauki zuwa gare shi kuma da zuwa haduwa da shi.

Gwargwadon sanin mutum gwargwadon girmamawan shi ga Alla Mabuwayi da daukaka, matakan mutane cikin bauta gwargwadon abin da ya dasu a cikin zukatan su ne na sanin Allah.

 kamar yanda halayen mutane ya dara juna a cikin salla da gwargwadon halartowan su da ma'anonin da sakon sanin Ubangiji.

Sanin Allah na sanya bawa ya halarto da kasancewan Allah tare da shi a dukkan halayen da ya ke ciki sai zuciyarsa ta samu natsuwa, ya samu kwanciyan hankali ya dogara zuwa ga Allah dogaro na gaskiya kuma ya samu sakankancewa da Allah bisa gaskiya ,Allah Madaukakin sarki ya ce: (wadanda suka yi imani zukatansu na natsuwa da ambaton Allah ku saurara da ambaton Allah ne zukata ke natsuwa).

Duk wanda ya san Allah cancancin saninSa zai ji dadi a sujjadarsa zai yi sallah sai ya yi kushu'i a tsayuwarsa da zamarsa kuma zai zama yayi yawo a malakutin sama ko a malakutai yana mai lura yana mai tafakkuri wato tunani harshensa zai zama yana furtawa da ''tsarki ya tabbata ga Allah… godiya ta tabbata ga Allah …Allah mai girma… ba abin bautawa da gaskiya sai Allah…''

Sunan Allah idan aka ambata a abin da ya ke dan kadan sai ya karu, idan aka ambata shi yayin shiga tsoro sai tsoron ya gushe, idan lokacin bakin ciki ne sai bakin cikin ya yaye, idan lokacin bacin rai da damuwa ne sai mutum ya samu farin ciki da walwala, idan lokacin kunci ne sai mutum ya samu yalwa, duk wanda ya san Allah zai ji kunyan Ubangiji ya same shi wurin da ya hane shi kuma ya rasa shi a wurin da ya umarce shi saboda yana tuna kasaitar Allah (ka dogara ga Mabuwayi Mai rahama) (wanda ya ke ganinka a lokacinda ka ke tashi) (da kai komonka cikin masu sujjada) .

Idan halarto da ma'anoni na sanin Ubangiji ya raunana to sai mabubbuga na imani ya bushe kututturen dadin biyayya sai ya dushe zuciya sai ta kekashe mutum ya fada cikin damuwa , damuwa ya yawaita a tare da shi ya rika shiga cikin tsoron abin da zai fiskanto da kuma arziki

(ka ce: Allah daya ne):Shi ne guda daya wanda ba Shi da makamanci ba wani wanda ya ke irin Shi a kudurarSa ne to Shi kadai ne a SiffofinSa Shi daya ne a zatinSa Shi ne Mahalicci Mai azurtawa, Mi rayawa, Mai kashewa Mamallaki, Mai sarrafa halittunSa yanda ya so, ba a neman agaji da taimako da tsari sai zuwa gare Shi, Shi kadanShi .

(Allahussamad): Shi Samadu Shi ne wanda ya cika a siffofinsa wanda dukkan halittu na bukatuwa zuwa gare Shi, wanda ya wadata daga dukkan kowa, wanda baya mutuwa , ba ya gadarwa amma duk abin da ya ke na sama da kasa dukka gadonSa ne wanda ba ya barci , ba ya mantuwa Shugaba wanda shugabancinSa ya kammala ya cika Mai girma a iliminSa da hikimarSa da hakurinSa da kusurarSa da buwayarSa da dukkan siffofinSa tsarki ya tabbata a gare Shi Madaukaki (Assamadu): Shi ne wanda halittu ke dumfara yayin bukatu a bukatunsu kuma ya gamsar da su, sunan Allah (Assamadu): yana sanya bawa ya rika jin wani karfi da izza da wadatuwa daga dukkan wani da ke koma bayan Allah Mabuwayi da daukaka sai ya sakankance ma'anar cewa Allah din nan ya ishi bawanSa tofa domin assamadu yana jin ganawarsa yana ganin wurinSa ko da dukk duniya ne suka tattaru dommi su cutar da shi ba za su iya cutar da shi ba da wani abu face sai abin da Allah ya rubuta a gare shi .

(lam yalid wa lam yulad): Shi ne rayayye wanda ba ya mutuwa Mai wanzuwa bayan karewan halittunSa Shi ne mai tsarki wadatacce daga da'a, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ke cewa : (Ba wani da ke mafi hakuri bisa cutarwar da ya ji shi kamar Allah, lallai suna sanya miSha da'a alhali kuwa yana azurta su kuma yana basu lafiya) .

(wa lam ya kun lahu kufwan ahad) ta yaya zai kasance yanada kini alhali kuwa Shi ya halicci dukkan komai? , ya samar da dukkan kowa Shi ya samar da kowa da kowa Shi ne babba Mai daukaka wanda Shi ne yafi dukkan komai kuma mafi girma ga dukkan komai, an karbo daga Anas dan Malik Allah ya kara yarda a gare shi ya ce: (wani mutumi daga cikin ansar ya kasance yana jan mutane salla a masallacin kuba ya kasance a duk lokacin da ya fara karatun sura yana farawa ne da ita a cikin sallan da ke musu, sai ya fara da (kul huwa Allahu ahad) har ya kare da ita sannan ya karanta wata sura daban tare da ita ya kasance yana yin haka a ko wace raka'a mutanensa suka mishi magana sai suka ce kai kana bude salla da wannan suran sannan kuma ba ka ganin ita ta isar maka ba sai ka karanta wata ba? ko dai ka karantata ko ka barta ka karanta wata ,Sai ya ke cewa: ni ba zan barta ba, in kuna so na cigaba da limantanku ko jagorantan ku a salla to sai na yi in kuma kun ki ba kwa so to sai na barku  kuma suna ganin lallai shi ne ya fi su daraja, sai suka ki waninsa ya musu limanci , yayinda suka zo wurin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, su ka bashi labari da wannan labarin sai ya ce: ya wane : mai ya hana ka ka aikata abin da mutanenka ke umartanka da shi? Meyasa ka ke lizimtan karanta wannan sura a ko wace raka'a? sai ya ce: ni ina kaunanta ne sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: kaunar da ka ke mata ta shigar da kai Aljanna) Buhari ne ya rawaito .

Huduba ta biyu:

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ji wani mutum yana cewa : (Ya Allah ina rokonKa, lallai kai ne Allah Tilo, wanda ake dumfara yayin bukata wanda bai haifa ba kuma ba a haife Shi ba, bai  da wanda ya ke kininSa, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Hakika ya roki Allah da sunan Shi mafi girma wanda idan an roke Shi da shi zai bada, idan an yi adu'a da shi zai amsa) Ibnu Majah ya rawaito Albani ya inganta shi

  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya ce: ((kul huwallahu ahad) da(kul a'uzu ) guda biyu a yayin da aka wayi gari da yayin da aka yi yammaci sau uku sun isar maka ga dukkan komai) Abu Dauda ne ya rawato da isnadi ingantacce .

Gobe asabar ne  ranan ashura, hakika Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana kirdadan wannan rana na ashura kuma ya ce: (lallai ina fatan Allah ya kankare zunubin shekaran da ta gabata) Abu Dauda ne ya rawaito da isnadi ingantacce.     

 

الجمعة، 21 أغسطس 2020

Lura

 

اسم المترجم :أمين سعد

اللغة : الهوسا

التاريخ 2/1/1442هـ

Hudubar masallacin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi na 2/1/1442 na shaihk Ali dan Abdurrahman Alhuzaifi

 

Hudubar farko

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Masanin gaibi Mai juya zukata Mai yawan gafarta zunubai, kyautata yabo ga Ubangiji na kuma ina gode mishi bisa ni'imominSa da wani bai iya kididdige su  in ba shi ba,  na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, da mulki da godiya na shi ne kuma mai iko ne ga dukkan komai, na shaida Annabinmu kuma shugabanmu Muhammad bawanSa ne, kuma manzonSa ne mai albishir mai gargadi, ya Allah ka yi dadin tsira da aminci da albarka, bisa ga bawanka Muhammad da iyalansa da shabbansa wadanda Allah ya jibince su to madalla da Majibinci kuma madalla da Mataimaki.

Bayan haka, ku ji tsoron Allah Mai tsarki a boyenku da bayyanenku, domin ya jibinci lamuranku ya kuma gyara muku halayenku, Takawa ita ce tafarkin mutanen kwarai masu rabauta  rasa ta kuma shi ne bayyananniyar hasara .

 YA KU BAYIN ALLAH

Ku kasance daga ma'abota basira da imani, ku bi tafarkin ma'abota hankula  da kyautatawa, ma'abota hankula su ne wadanda  hankulan su ke lafiyayye mikakke, masu lafiyayyan fidira  su ne wadan da suke amfana da wahayi kuma suke fahimtar abin da Allah ya saukar,  bisa muradin Allah da kuma muradin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  suna aiki da maganar Allah domin fatar lada kuma suna tsoron ukubarSa   .

Allah Madaukakin sarki ya ce :-(Kuma wadan da suka  nisanci dagutu da su bauta masa suka koma zuwa ga Allah, su na da kyakkyawan bishara, to, ka yi albishir ga bayi Na, wadanda suke jin magana kuma su bi mafi kyau daga ciki, wadan nan su ne wadan da Allah ya shiryar da su kuma wadan nan su ne ma'abota hankula ).

Lura na daga cikin ayyukan masu hankali masu basira, na daga cikin ayyuka na basira kuma da gwanancewa  shi ne ; lura yana shiryarwa zuwa  ga rabauta da tsirata daga abubuwa dake halakarwa, kuma yana datar da ma'abotan shi zuwa aiki na kwarai  ya nusar da  ma'abotan shi  zuwa ga tafarkin mutane  na gari  masu neman gyara  karshen shi kuma yakan koma ne zuwa ga alheri,  wanda aka haramta mishi lura to wa'azi ma ba zai amfane shi ba, zai fada kuma cikin halaka kuma zai bi sha'awe -sha'awen ransa  zai bi tafarkin mabarnata kuma ya zama ya yi nadama.

Lura shi ne kaura daga hali na mushahada ko hali da ya shude wanda yake akwai ukuba da azaba zuwa hali mai kyau  abin a yaba a hankalce da a shar'ance, ta hanyar nisatar sabuban ukuba da kuma azaba, ko kuma kaura daga tarihin salihan bayi da abin da Allah ya karrama su da shi na aiki da ayyukan su da kuma bin  sawun su ko kuma tuntuntuni  cikin dabi'un halittu da sanin sirrin da ke ciki da sifofin su ,  da hikiman da ya sa mahaliccin su ya halicce su,  da kebantar da shi da tauhidi da da'a ga Allah  tabaraka wa ta'ala.

Hakika Allah Mabuwayi da daukaka ya halicci halittu  ya sanyawa duniya wata sunnan da take tafiya a kai, sai ya sanya biyayya  sababi ne na dukkan alheri a nan duniya  da lahira, ya sanya kuma saba mishi sababi ne  na dukkan sharri a duniya da lahira .

Shin akwai wanda za ka ga ya tsiyace sabo da biyayya wa Allah  ko kuwa za ka samu wanda ya samu rabauta sabo da sabon Allah, hakika Allah ya bamu kissa tsarki ya tabbata a gare shi  a cikin littafinSa  kuma Manzon Allah ma tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kissanta mana , daga kissoshi na halayen Annabawa da Manzanni da muminai da abin da ke ciki na abin lura, da abin koyi ga wanda ke bayan su, da kuma tsirata daga ukubobi,  da rabauta da dukkan alhairu  wanda a cikin shi za ka samu kyakkyawan karshe,  da wanda a cikin su akwai akiba mafi kyau da kuma darajoji  Allah Madaukakin sarki ya ce :-    

(Hakika a cikin kissoshin su ya kasance akwai abin lura  ga ma'abota hankula ).

Ba zance ne na kage ba, sai dai gaskatawa ne ga abin da ya gabata  da kuma bayani daki-daki na dukkan  komai  da shiryarwa da rahama ga mutane masu imani .)

Allah Madaukakin sarki ya ce:- (Sa'annan muka tseratar da ManzanninMu da wadan da suka yi imani  hakanan ne ya kasance hakki a gare mu da mu tsiratar da muminai).

Allah Mai tsarki ya fadi game da masu karyatawa ( Ya ce suka yi makirci muma muka mai da musu makircin su a halin ba su sani ba, to ka dubi karshen makircin su yanda ya kasance;   shi ne Mun rusa  su da mutanen su baki daya  wadancan gidajen su ne ba komai  sakamakon zalunci da suka yi lallai  a cikin wannan akwai abin lura ga mutane  da suka gane,  muka tsiratar da wadan da suka yi imani kuma sun kasance suna tsoron Allah).

 

Yayin da Allah ya bamu kissoshi masu yawa  na daga Annabawa amincin Allah ya tabbata a gare su a cikin suratul Al-shu'ara sai ya rufe kissan  bayan tsiratan Manzanni da muminai tare da su sai ya rufe kissan da fadinSa  (Lallai a cikin haka akwai abin lura amma mafi yawan su  ba su kasance suna  muminai ba•  lallai Ubangijinka shi Mabuwayi ne kuma mai jin kai.)

Ibnu Kasir Allah ya mishi rahama yake cewa  '' Lallai a cikin haka akwai aya, wato a wannan kissa din da abin da ke cikin ta na ban mamaki  da kuma nasara da karfafan bayin Allah muminai,  ta hanyar dalilai da hujjoji na yanke da kuma hikima wanda takai kololuwa".

Lallai Ubangijinku shi ne Mabuwayi ai Madaukaki da ya buwaya daga dukkan komai, kuma mai yin galaba akan abun kuma ya rinjaye shi, ga rahama kuma wato ga halittun sa baya gaggawa da  ukuba ga wanda ya saba mishi sai dai yana saurara mishi ya jinkirta mishi  sannan ya damke shi damka irin na Mabuwayi Mai iko.

 

 Sa'id bin Jubair ya ke cewa Allah Mai jin kai ne ga wanda ya  tuba zuwa gare shi  kuma ya komo zuwa gare shi , maganar ta tike.

 A fadin Allah Madaukakin sarki a kissan mutanen ludu  tsira da amincin Allah su tabbata a gare su.

 

(Lallai a cikin haka akwai ayoyi ga masu hankula).  Katada ya ke cewa ;  masu hankula ana nufin masu lura Albagawi shi ya ambata shi a cikin tafsirinsa ba masu amfana da abubuwan da ke faruwa na tarihi da hikimomi da ke ciki na yanayi face  wadanda suke  masu lura masu tunani  wadan da suke koyi da ma'abota na kwarai da mutane na gargaru,  masu neman gyara  suna kyale mutanen barna  da masu kawo barna, amma wanda baya lura baya wa'azantuwa baya muhasaba wa kanshi baya aiki don lahiransa, addinin sa baya hana shi hankalin shi baya hana shi yin abu mara kyau da laifuka to, wannan kamar dabba  ya ke,  Allah Madaukakin sarki ya ce:- ( Ko kana zaton cewa mafiya yawan su suna ji ne ko suna hankaltuwa ,  a'a  su dinnan ba komai ba ne  sai kamar dabbobi ne, kai sun fi ma dabbobi bata).

Ya zo a cikin Hadisi daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  (Lallai mumini idan ya yi rashin lafiya ciwo ya same shi sannan ya mutu  zai kasance kaffara ne a gare shi game da zunuban shi cikin abin da ya shude idan ya bashi lafiya sai ya kasance kaffara ne  cikin abin da ya shude da kuma wa'azi ga abin da ya fiskanto lallai munafukai idan dayan su ya yi rashin lafiya sannan aka warkar da shi to sai ya kasance kamar rakumi ne da iyalan shi suka kunce shi sannan suka sake shi  bai san sabo da me aka sake shi ba,  bai san kuma sabo da me aka kunce shi ba Nasa'i ne ya rawaito).

 

Allah bai ambaci tarihin Annabawa ba da Manzanni da cikamakinsu Annabinmu Muhammad ba face don mu yi lura da tarihin nasu,  mu yi  koyi da shiryarwar su da halayen su mu bi tafarkin su hakika kuma Allah ya umarci Annabin mu Muhammad da ya yi koyi da su  sai yake cewa  wadannan su ne Allah ya shiryar to ka yi koyi da shiryarwar su Allah Madaukakin sarki ya ce :-(To ka yi hakuri kamar yanda ma'abota  azama suka yi hakuri na daga Manzanni)

 Allah Madaukakin sarki ya ce game da muminin Yasin  (Ya ku mutanena ku bi manzanni ku bi wanda bazai tambaye ku lada ba kuma su dinnan suna shiryarwa ne)

Cikamakinsu Annabinmu Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, wanda da shi ne Allah ya goge sauran shario'i gaba daya,ya turo shi da mafi kamalan addini da sharia ta har abada, kuma Allah ya dauki nauyin duk mutumin da ya yi riko da koyarwarsa da zai rayu  rayuwa daddada a duniya da lahira, kuma zai shigar da shi gidan aminci tare da mafi alherin halittanSa,  Allah Madaukakin sarki ya ce:(Duk wanda ya ke wa Allah da Manzo biyayya to wadannan suna tare da wadanda Allah ya yi wa ni'ima na daga Annabawa da siddikai da shahidai da salihan bayi, to madalla da wadannan abokan zama).

To wani irin karramawa ne ya fi wannan? Wani irin daukaka ne da zai yi kusa da wannan matsayi? Kuma kamar yadda Allah ya kissanta mana kissoshin Annabawa amincin Allah ya tabbata a gare su, da wadanda suka yi imani da su don mu yi koyi ne da su ne mu bi tafarkin tsira tare da su, kuma mu yi lura da tarihin rayuwarsu, mu san irin halin da suka shiga, kamar yadda ya bamu labarin wadanda suka karyata su, da wadanda suka ja da gaskiya suka yi girman kai daga binsu, wadanda suka fifita rayuwar duniya akan lahira, masu bin soye-soyen rayukansu da abubuwan jin dadin duniya, don mu yi lura da ukubar da aka musu, kuma mu dauki izina da abin da ya faru da su na walakancin duniya da azabar lahira, don mu kiyaye kanmu daga tsinuwar Allah da ta tabbata a kan su,   Allah Madaukakin sarki ya ce:(Da Adawa da samudawa alhali kuwa lalle alamun azaba sun bayyana a gare su daga gidajensu, kuma shaidan ya kawata musu ayyukansu, sabo da haka ya kange su daga hanyar Allah, kuma sun kasance masu basira. Kuma Karuna da Fir'auna da Hamana, kuma lalle Musa ya je musu da hujjoji, sai suka yi girman kai a cikin kasa, kuma basu kasance masu tserewa ba. Saboda haka kowannensu mun kama shi da laifinsa: wato daga cikinsu akwai wanda muka aiki iskar tsakuwa a kansa, kuma daga cikinsu akwai wanda tsawa ta kama, kuma daga cikinsu akwai wanda muka birkice kasa da shi, kuma daga cikinsu akwai wanda muka nutsar. Ba ya yiwuwa ga Allah ya zalunce su, amma sun kasance kansu suke zalunta.

 Allah Madaukakin sarki ya ce:(kowannensu ya karyata Manzanni sai Kyacewa ta tabbata).

  Allah Madaukakin sarki ya ce game da kissar Banu nadir :(To ku yi lura fa ya ma'abota basirori)

Tarihin Manzanni amincin Allah ya tabbata a gare su tare da masu karyata su, masu saba wa Allah da ManzonSa abu ne da mutane suka san shi, al'umar karshe sun san shi daga al'umar da farko, kuma yana cikin hujjojin Allah mafi girma ga halittunSa wurin karfafar gaskiya da ma'abotarta, sanin tauhidi da kira zuwa gare shi da taimakawa masu kadaita Allah, haka kuma hujja ne wurin rusa karya (bata) da shirka da yin gargadi game da shi, da ukubobi na mushrikai masu bijirewa, kuma tarihi shine bigere ko mahallin lura da daukan izina ga daidaiku da iyalai da dabakoki da al'umu da ma kasashe, duk wanda ya amfana da shi zai tsira, wanda bai amfana da shi ba kuma sunnar Allah zata bi ta kan shi sai ya samu tawaya, Allah Madaukakin sarki ya ce:(Sunnar Allah wacce hakika ta shude cikin bayinSa kuma kafurai sun yi hasara a wancanninka).

 Amma shi lura da dabiun halittu da binciko hikimomin da ke cikinsu da sifofinsu, da tunani game da farar da halittarsu to gayarsa da babbar manufarsa shine kadaita Allah  Mabuwayi da Daukaka da bauta masa da masa biyayya, wanda ya kadaita da halitta shine abin bauta da gaskiya Allah Madaukakin Sarki ya ce : (kuma lalle ne kuna da abin lura a cikin dabbobin ni'ima muna shayar da ku daga abin da yake a cikin cikunansu daga tsakanin tukar tumbi da jini, nono tsantsa mai saukin hadiya ga masu sha.)

    Allah Madaukakin Sarki ya ce : (kuma Allah yana juyar da dare da yini, lalle ne a cikin wannan akwai abin lura ga masu basira).

Allah Madaukakin Sarki ya ce : (ka ce ku dubi abin da ya ke cikin sammai da kasa, kuma ayoyi da gargadi basu wadatarwa ga wadanda basu yin imani).

    Lalle tunani cikin halittun Allah ibada ne ga musulmi, daukan izina ga wadannan halittu kuma yana kara imani ga musulmi da tabbatuwar yakini, Allah Madaukakin Sarki ya ce : (Lalle ne a cikin sammai da kasa akwai ayoyi ga masu imani).

To tunani da lura na tabbatar da mai shakku, kuma yana raya zukata, yana haskaka basira, yana daidaita halaye da dabiu, kamar yadda bijirewa tunani kan kekasar da zukata, kuma yana haifar da gafala, yana jan ragama zuwa ga nadama ya kuma jefa mutum cikin sabon Allah.   

   Daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi yace lalle Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a lokacin da ya yi isra'i ya ce : ( Yayin da na sauko saman duniya sai na dubi kasa da ni sai ga  wani irin iska da sauti da hayaki, sai nace : menene wannan ya kai jibrilu? Sai yace wadannan shaidanu ne suke kona wuta a idon dan adam wai don kar yayi tunani cikin mulkin sammai da kasa, ba don haka ba da sun ga abin al'ajabi).Ahmad ne ya rawaito.

Allah Madaukakin Sarki ya ce : (Lalle ne wadanda suka ji tsoron Allah idan wani tashin hankali daga shaidan ya shafe su, sai su tuna Allah sai ga su sun zama masu basira. Kuma 'yan'uwansu shaidanu suna taimakonsu cikin bata Sannan basu gajartawa.)

Allah ya sa min albarka ni da ku cikin Alkur'ani mai girma.

Huduba ta biyu

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah,  wanda ya haskaka zukatan masoyanSa da Alkur'ani, ya kuma haskaka basirarsu da Imani, ya kawata ayyukansu da kyautatawa, ina kyautata yabo ga Ubangiji na kuma ina gode masa, bisa ni'imominSa da ba mai iya iyakance su in ba shi ba, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bai da abokin tarayya, Mulki da godiya na shi ne, Mai jinkai Mai rahama, kuma na shaida Annabinmu kuma shugabanmu Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, wanda aka kebantar da shi da dunkulallun kalmomi gamammu da cikan bayani, Allah ka yi dadin tsira da aminci bisa ga bawanKa kuma ManzonKa Muhammad da iyalan shi da sahabban shi da wadanda suka biyo su da kyautatawa, bayan haka:

To ku ji tsoron Allah Madaukakin sarki zai gafarta muku ya tattaro muku alheri a rayuwarku da bayan mutuwarku.

Yaku bayin Allah! Ku yi wa kanku hisabi kafin a muku hisabi, dayanku ya yi dubi zuwa ga akibar al'amura, da karewar ajali duk wanda luransa ya yawaita to kura-kuransa zasu karanta, wanda ya kiyaye sabawa Allah da laifuka to zai rayu cikin aminci, kuma za a datar da shi zuwa ga kyakkyawan karshe, mai rabauta shine wanda ya wa'azantu da waninsa, hasararre shine wanda da shi waninsa ya wa'azantu.

Hakika Allah Madaukakin sarki ya zargi wadanda suka bi son ransu ba su yi lura ba, basu wa'azantu da labarai da suka zo musu ba, Allah Madaukakin Sarki ya ce : (kuma suka karyata suka bi soye- soyen rayukansu, alhali kowani al'amari tabbatacce ne. Hakika labarai ya zo musu wanda cikinsa akwai abin gargadi)

  Ku saurara ! lalle Allah Madaukakin sarki yana da wasu sunnoni a rayuwa wurin sakayya da lada ko ukuba, wanda ya nemi ja da yin Allah sai sunnar rayuwa ta nesatar da shi ya dunkufe  ya fado ya kaskanta, Allah Madaukakin Sarki ya ce : (Hanyar Allah ga wadanda suka shude kafin nan kuma ba za ka samu sauyi ba ga hanyar Allah).   

Ya zo a hadisi :(ku yawaita ambaton mai katse jin dadi mutuwa).

Wanda ya tuna mutuwa aikinsa zai yi kyau, wanda ya manta mutuwa aikinsa zai munana.

Ya ku bayin Allah! (Lalle Allah da Mala'ikunSa suna salati ga Annabi yaku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi da aminci tabbatacce).

To ku yi salati da aminci ga shugaban mutanen farko da na karshe kuma shugaban manzanni.

 

الجمعة، 7 أغسطس 2020

YI WA KAI HISABI

 

 

اسم المترجم : أمين سعد عبد الله

اللغة : الهوسا

التاريخ : 17-12-1441هـ

Hudubar Juma'a a masallacin Annabi na Shaikh Abdul Muhsin  Al kasim 17-12-1441AH /  7-8-2020AD

 

Hudubar farko:

  Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Madaukakin sarki  muna gode mishi kuma muna neman taimakonsa, muna neman gafararSa, kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu, da munanan ayyukanmu, duk wanda Allah ya shiryar da shi babu mai batar da shi , duk wanda ya batar kuma babu mai shiryar da shi, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya, kuma na shaida Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa  da sahabbansa da aminci tabbatacce mai yawa.

Bayan haka: ku ji tsoron Allah-

Ya ku bayin Allah,- cancancin tsoronSa, takawa ita ce mafi alherin abin ribata kuma kyauta mafi yawa.

Ya ku musulmi!

Na daga cikin juyawan watanni da shekaru ga bayi na daga cikin ni'imomin Allah masu yawa ga bayi, Allah Mai tsarki ya ce ; (Kuma ya hore muku rana da wata suna madawwama biyu, kuma ya hore muku dare da wuni. Kuma ya baku dukkan abin da kuka roke shi, kuma idan kun kidaya ni'imar Allah ba za ku lissafe ta ba. Lalle ne mutum, hakika, mai yawan zalunci ne mai yawan kafurci)

Allah ya tsawatar ga duk wanda bai ribaci lokacinsa ba  da abin da zai amfanar da  shi a lahira Allah mai tsarki ya ce:- (Ase bamu baku tsawon rayuwa ba  wanda ya ci ace  mai wa'azantuwa ya wa'azantu? Kuma ga mai gargadi ya zo muku)

  kuma ni'imomi biyu idan mutum bai ribace su ba yayi asara  kuma zai yi nadama game da su.

 Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :-( Ni'imomi guda biyu mutane suna asara a cikin su, su ne ; lafiya da kuma lokaci ) Buhari ne ya rawaito

Allah ya yi  rantsuwa a ayoyi da dama  a cikin littafinSa  da wani yanki na lokaci na daga dare da yini da  alfijir da asubahi da la'sar  da walaha, hakika ga shi muna kusa da bankwana da shekara wacce ta tattaro wani abu na rayuwarmu,  muna bankwana da ayyukan mu a cikinta, wanda za a shimfida su a ranar taro  a gaba gare mu,  abin mamaki da irin saurin abin da ya shude  ya tafi,  kuma abin mamaki da girman abin da ya tattaro .

Dararraki da ranaku wasu taska ne na ayyuka  kuma matakai ne na rayuwa  na shekaru  ana tsofar da abin da ya ke sabo  a kusantar da abin da ya ke nesa  ranaku na shudewa ga shekaru suna tafiya  al'uma  suna bin bayan juna ,  bisa tafiya zuwa ga lahira  wannan na fiskantowa wancan kuma na juyawa,  wannan na samun lafiya wani kuma na samun cuta,  duka zuwa ga Allah za su koma.  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :- (Dukkan mutane suna wayan gari akwai mai saida kanshi, to, sai ya 'yantata  ko kuma ya  halaka ta ) Muslim ne ya rawaito

A cikin zamani  akwai wasu radadi da ke juyawa farin ciki, akwai kuma  farin ciki da ke juyawa bakin ciki  ranaku na wucewa ga ma'abotanta , kaman shekaru , shekaru kuma na wucewa ga ma'abotanta kamar ranaku mai hankali shi ne wanda ya riki wannan a matsayin abin lura, kuma abin wa'azantuwa  Allah Madaukakin sarki ya ce :-(Allah na juya dare da yini  lallai a hakan akwai abin lura ga masu basira ) Shekara  kan tafi  da abin da ke cikinta  abin da bayi suka aikata a cikinta na ayyuka,  za a bijiro  musu da ayyukansu , (Ana bawa mutum labari game da abin da ya kaddamar ko ya jinkirta a wannan ranar) Ka yi dubi zuwa ga takardun  ranakun ka da suka shude  wani abu ne ka adanawa kanka  a ciki don lahiran ka?  Ka kebanta da kanka ka  mata hisabi, hisabi  amintacce  wanda akwai  matsi a ciki,  Maimun dan Mihran - Allah ya mishi rahama- ya ce :-(Bawa ba zai zama mi takawa ba har sai ya kasance  yana mai tsanani ga rayinsa fiye da aboki ga abokin shi).

 Dare da yini na wucewa ne don su  nesatar daga duniya  su kusantar zuwa lahira, madalla da bawan da ya amfana da rayuwarsa  ya tsaya tare da ransa tsayawa na hisabi da kuma zargi yana gyara tafiyarsa  kuma yana riskan kusakuransa,  yakan bude shafi da daddare  na daga abin da ya aikata a wuninsa ,  idan ya kasance abubuwa ne masu kyau sai ya  doge a kan su,  idan kuma ya kasance ayyuka ne na zargi sai ya tuba daga gare su  sabo da shi matafiyi ne tafiyan da ba komawa 

 Abu Hatim Dan Hibban - Allah ya mishi rahama - ya ce:- ( Mafifitan masu hankali matsayi su ne wadan da suka dimanci  yiwa kansu muhasaba .

Tsinkaya bisa ga  aibobi na rayi   da kuma abubuwan da suke   tawaya gare ta   da laifukanta zai mata linzami daga zalunci, bawa ya san kan shi kuma ya san makomar shi zuwa ga kabari  yana haifar mishi da kankan da kai da kuma bautawa Allah,  ba zai yi alfahari da aikinsa ba duk yanda abu ya girmama,  ba zai kuma raina zunubai ba komin kankantan su.

 Abu Darda Allah ya kara yarda a gare shi yana cewa :- '' Mutum ba zai zama  cikakken fakihi ba  har sai ya kama mutane  da  laifi a hakkin Allah  , sa'annan kuma ya koma zuwa ga kanshi  sai ya kasance ya fi mata tsanani.

Idan ka zauna da mutane  ka kasance mai wa'azi ga zuciyarka ,  domin halittu suna murakaban zahirin ka ne , Allah  kuma yana murakaban badinin ka ,  duk wanda badinin sa ya yi kyau  ta hanyar murakaba da ikhlasi  to Allah sai ya zayyana zahirin shi  da kyau da rabauta.

Sanin hakkin Allah da  girman falalarSa da baiwarSa  da tuna yawan ni'imominSa  yana kira zuwa ga Allah ,  yana sa mutum kuma ya gane gajartawarsa wurin  godewa ni'imomin Allah  kuma  lallai  ya san cewa babu tsira sai da komawa zuwa gare shi,  ya dace a mishi da'a ba za a saba mishi ba  a gode mi shi ba za a butulce mishi ba.

Ibnul  Kayyim Allah ya mishi rahama ya ke cewa:- '' Farkon muhasaba shi ne mutum ya yi kiyasi tsakanin ni'imarSa mabuwayi da kuma  laifukansa  a wannan lokacin ne zai bayyana mishi lallai akwai banbanci  kuma ya san cewa lallai  ba don wani abu na afuwar Allah da rahamar sa ba  da halaka za a fada da kuma  musiba, nemar laifukan rayi yana  tsarkake ta  kuma ya gyara ta Allah Madaukakin sarki ya ce:-(Hakika wanda ya tsarkake ta ya rabauta, hakika kuma yayi asara wanda ya turbude ta )  

Malik dan Dinar ya ce :-''Allah ya yi rahama wa bawan da ya ke  cewa ransa  ase ke ba ma'abociya kaza-da – kaza ba?  Ase ba ke ce mai kaza-da-kaza ba?  Sannan sai ya sa mata linzami sannan ya sa mata birki  sannan ya lizimtar da ita da littafin Ubangijinta  sai ya kasance shi ne mai jan  ragamar ta .

Ba wani mai nisata wanda zai nisanci Allah  face sai da gafalarsa da mantuwarsa daga muhasabar sa ga Allah , Allah Madaukakin sarki ya ce (Lallai sun kasance ba su fatan hisabi)  wanda ya fada cikin munanan ayyuka  kuma ya dogara bisa  afuwar Allah da rahamarSa to hakika  ya yaudari kan sa lallai  mai karamci baya fuskantar ayyuka munana  (Ya kai mutum me ya rude ka game da Ubangijin ka Mai karamci )?  

Ibn Kasir Allah ya mishi rahama ya ce:-  (Me ya rude ka ya kai dan Adam  game da Ubangijin ka wanda ya ke mai karamci wato mai girma har ma  ka je zuwa ga saba mishi  ka fiskance shi da abin da bai dace ba ).

 Hisabi yana yin sauki ga mutanen da  suka yiwa kansu hisabi tun a duniya kuma ya kan yi tsauri ga mutanen da  suka riki wannan al'amari ba tare da muhasaba ba.

 Hasanul-Basari Allah ya mishi rahama ya ce :- '' (Baya dacewa ga mumini  face da ya rika yiwa kan shi zargi  yana mata mu'ataba  sai ya ce da ita me kike nufi da  kalma ta, me kike nufi da abinci na, amma fajiri zai shude ne  zai tafi ne  da kafansa baya zargin kansa, shi kuma mumini  yana mai tsayuwa a kansa yana mata hisabi).

Allah Madaukakin sarki ya ce :-(Lallai ne  wadanda suka yi takawa idan wani tashin hankali daga shaidan ya shafe su,  sai su tuna  (Allah)  sai ga su ,  sun zama  masu basira .

Taka-tsantsan  wurin afkawa cikin kuskure  da barin zunubai shi ne  ya fi sauki akan  neman tuba  kuma da zargin rayi bisa ga gajartawa cikin  da'a  domin ranaku a gare ka basu dauwama  kuma ba ka sani ba yaushe  ne  za ka kaura daga duniya  kuma ka yiwa kan ka magana  menene  kika gabatar a ranakun da su ka shude  kuma  wani shiri kike yi don ranaku masu fiskantowa?

Umar Dan Khaddabi Allah ya kara yarda a gare shi ya ce:- '' Ku yiwa kan ku hisabi  kafin a yi muku hisabi  ku aunata kafin a auna ku

  ka rika bibiyan ranka  a farkon  ko wani rana  wurin kiyaye sallolin nan guda biyar  a masallatayya cikin jam'i  tare da musulmai  kana neman guzuri na ilimi mai amfani tare da kai-komo wurin yada shi  da kuma ilmantar da shi  da kiyaye harshen ka daga abubuwan da suke muharramai da karya da rada  da batsa da alfasha  kuma ka kasance kana da tsantseni cikin abin da ka ke ci da abin da kake sha,  ka nisaci abin da baya halatta  ka yi kwadayin biyayya wa iyaye  ka sada zumunci,   ka yawaita ma'arufi da makusanta da na nesa  ka tsarkake zuciyan ka daga hasada  da gaba da kiyayya  ka kiyaye daga aukawa cikin mutuncin musulmai  ka yi kokari wurin tashi da wato  sha'ira na umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna  da bada hakkokin yara kuma da iyali  bisa ga fiskan da ya dace  mafi kamala  ka rintse idanuwan ka daga kallon abin da ya ke muharramai  sawa'un a hanyoyi ne ko wanin su.

 To dare da wuni  suna  nesantarwa ne daga duniya kuma suna kusantarwa ne zuwa ga lahira, madalla da bawan da ya amfana  da rayuwarsa  dukkan wayan gari  rana na faduwa  yana maka gargadi ne cewa fa wani  abu na shekarunka ya ragu  mai hankali shi ne wanda ya wa'azantu a jiyansa ya yi kokari a yau dinsa  ya shirya don gobensa  ka dauki mataki  na shiri  domin  tafiyan da take gaban ka, yi guzuri domin tafiyan ta kusanto ,  mafi alherin guzuri shi ne wanda a ka hada da tsoron Allah,  mafi darajan mutane a wurin Allah  shi ne wanda ya fi su tsoron shi .

 

Ina neman tsarin Allah daga sharrin shaidan abin jefewa

(Ya ku wadan da suka yi imani ku ji tsoron Allah kuma rayi ta yi dubi zuwa ga abin da  ta gabatar  don gobe . ku ji tsoron Allah lallai Allah Mai bada labarin abin  kuke aikatawa ne).

Allah ya sa mini albarka ni da ku a cikin Alkur'ani mai girma.

 


 

HUDUBA TA BIYU

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah bisa  kyautatawanSa,  godiya ta tabbata gare shi bisa  datarwanSa  da baiwanSa, na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya  ina mai girmama sha'aninSa na shaida Annabi Muhammad bawanSa ne kuma Manzon sa ne  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabban shi da aminci tabbatacce mai kari .

Ya ku musulmi:-

 Shekarun dan adam a nan duniya na rayuwarsa su ne  kasonsa, idan ya kyautata ribatarsu a nan duniya  cikin abin da zai amfane shi a gidan lahira to ya ci riba a kasuwancinsa, to idan kuma ya munanta ribatan su ya yawaita sabo da laifuka to ya yi hasara a kasuwancinsa, mai dace shi ne wanda ya yi hisabi wa kansa kafin Allah ya masa, ya ribaci lokacinsa ya san maganinsa daga cutarsa, bai yi sake ba har a yi mishi sakiya, alheri na cikin da'a sharri kuma na cikin sabo.

Rayuwa fage ne mai fadi na kyawawan ayyuka, jinkirta aiki da cewa sai nan gaba bai haifar da wani abu sai nadama, tuba na goge kuskure, mai samun walwala shine wanda ya adana ayyuka na kwarai a tsawon rayuwarsa. Shakiyyi shine wanda gabbansa suka shaide shi da munanan laifukansa.

To ku kiyaye ranakun rayuwanku kafin ku kadaita a kabarinku, ku ribaci ranakun rayuwarku kafin kwacewar lokaci, ku girmama masaukinku na sabon rayuwa da da'a.

Sannan ku sani Allah ya umarce ku da salati da aminci ga AnnabinSa.    

 

الجمعة، 31 يوليو 2020

FALALAN GOMAN FARKO NA ZULHAJJI 2

 

اسم المترجم : أمين سعد عبد الله

اللغة : الهوسا

التاريخ : 3-12-1441هـ

Hudubar Juma'a a masallacin Annabi na Shaikh Abdul Muhsin  Al kasim 3-12-1441AH / 24-7-2020AD

 

Hudubar farko:

  Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Madaukakin sarki  muna gode mishi kuma muna neman taimakonsa , muna neman gafarar sa, kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu , da munanan ayyukanmu , duk wanda Allah ya shiryar da shi babu mai batar da shi , duk wan da ya batar kuma babu mai shiryar da shi, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya, kuma na shaida Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa  da sahabbansa da aminci tabbatacce mai yawa.

 

Bayan haka: ku ji tsoron Allah-

Ya ku bayin Allah,- cancancin tsoronSa, ku yi murakabarSa a boye da bayyane.

Ya ku musulmi!

Allah na zaba a cikin halittun shi wanda ya so  kuma ( Ubangijinka na halittan abin da ya so kuma ya zaba) sai ya zabi manzanni  daga cikin mala'iku, da mutane, ya zabi ambatonSa daga cikin magana, kuma ya zabi dakunanSa daga doron kasa. Ya zabi ramadana da watanni masu alfarma daga cikin watanni, Jahiliyya sun kasance suna kari a kwanaki ta jinkirta don bin son rai, azuminsu bai zama a lokacinsa ba, hajjinsu kuma ba a kan lokacinsa ba, kuma Allah ya yi mana falala da turo Annabinmu Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kuma ga zamani ya zagayo kamar yadda ya ke, hajjinsa ya kasance a zulhajji, ya fada a cikin hudubarsa : Lalle zamani ya kewayo kamar yadda ya saba a sifarsa tun randa Allah ya halicci sammai da kasa)Buhari da Muslim.

         Sai adadi ya cika kidaya ya inganta al'amari ya koma bisa yadda ya gabata a littafin Allah a farko.

Fifiko tsakanin dararraki da ranaku na kira ne zuwa ga ribatan alherin da ke cikinsu, kuma Annabinmu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kwadaitar bisa ribatar ni'imomi da za su gushe ba makawa, sai ya ce : (Ka Ribaci Abubuwa Biyar Kafin Zuwan Biyar : Ka Ribaci Ƙuruciyarka Kafin Tsufanka, Ka Ribaci Lafiyarka Kafin Rashin Lafiyarka,Ka Ribaci Wadatarka Kafin Talaucinka, "Ka Ribaci Lokacinka Kafin Zuwan Shagula, Ka Ribaci Rayuwarka Kafin Mutuwarka) Nasa'i ne ya rawaito.  

Ga goman zulhijja ya shigo mana Allah ya yi rantsuwa da dararrakin su sai ya ce (ina rantsuwa da Alfajir)(da dararraki goma) , su ne ranakun Allah masu alhuruma , kuma cikamakin watanni sanannu wanda Allah ya ce game da su, (Hajji watanni ne sanannu).

Wuninsu ya fi daraja akan wunin goman karshe na Ramadan , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (mafificin ranakun duniya su ne ranaku goma) Ibnu Hibban ya rawaito,

falalan goman Zulhijja ya samu ne sakamakon tattaruwan manya manyan ibadoji a cikinta na daga salla – da azumi – da sadaka – da hajji – wanda hakan baya samuwa a waninta.

kuma dukkan ayyuka na kwarai a cikinta ya fi soyuwa zuwa ga Allah na daga irin wannan aikin idan ya faru a waninta.

Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Ba wasu ranaku wanda ayyukan alheri a cikin su ya fi soyuwa ga Allah irin wadannan ranaku)  wato yana nufin ranaku goma, sai suka ce ya Manzon Allah ko da jihadi a tafarkin Allah?  Sai ya ce: (ko da jihadi a tafarkin Allah sai dai mutumin da ya fita da rayinsa da dukiyarsa bai dawo ba da wani abu na daga wannan) Abu Dawuda ne ya rawaito asalinsa na Bukari.

Ibnu Rajab Allah ya kara yarda a gare shi ya ce '' kuma wannan hadisi yana nuni da cewa aiki na kwarai a wannan kwanaki goma ya fi soyuwa  ga Allah akan aiki a sauran kwanakin duniyaba tare da toge wani abu ba daga cikin su ''

Magabata Allah ya musu rahama sun kasance suna kokarin ayyuka na kwarai a cikin su '' Sa'id binu jubair Allah ya mishi rahama ya kasance idan goman farko na Zulhijja ya shigoya ya kan yi kokarin da ba za a'a iya ba ''

Na daga cikin falalan Allah da karamcin Sa Ya sanya  nau'uka na da'a daban daban a ciki na daga cikin abin da aka shar'anta akwai yawaita ambaton Allah , Allah subhanahu wa Ta'ala ya ke ce:(kuma su ambaci sunan Allah a ranaku sanannu) Ibnu Abbas Allah ya kara yarda a gare shi, shi da mahaifin shi ya ce:<< wadan nan kwanaki goman>> ambaton shi Allah Subhanahu wa Ta'ala a ciki na daga cikin ibadodi na kusanci Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce; (Ba wata rana da tafi girma da soyuwa wurin Allah aiki a cikin su a wurin Allah irin ranaku goma to ku yawaita a cikin su halala da kabarori Da kuma godiya wa Allah) Ahmad ne ya rawaito,

 Imam Annawawi Allah ya mishi rahama ya ce:<< mustahabbi ne yawaita  zikiri a wadannan goma kari akan su, mustahabbi ne na daga haka a ranar arfa fiye da sauran kwanaki goman, mafificin zikiri karatun littafin Allah shi ne shiriya kuma da haske bayyananne >>

Kabbarori wanda suke na saki wzaiwai ba kaidi a dukkan lokaci yana cikin manyan alamomi a watan zulhijja Ibnu Umar da Abu huraira Allah ya kara yarda a gare su sun kasance suna fita kasuwa a cikin ranakun nan guda goma suna kabarbari mutane suna kabbara da kabarbarin su , an shar'anta yin kabbara mai kaidi karshen salloli tun daga asuban ranar arfa ga alhazai da wasun su shehul islam Allah ya mishi rahama ya ce mafi ingancin zantuka a cikin kabarbari wanda jamhurin magabata suka yi da fukaha'u da sahabbai da limamai shi ne ayi kabbaran tun daga asuban asuban arfa har zuwa karshen ranakun attashrik karshen ko wani sallah.

Na daga cikin abin da ya ke mustahabbi a ranaku goma azumtan su, rana na tara shi ya fi dacewa a cikinta , Imam Annawawi- Allah ya mishi rahama- ya ce '' lallai mustahabbi ne mustahabbanci mai karfi '' .

Yin sadaka aiki ne na kwarai wanda ya ke yaye bakinciki ya ke tafiyar da bacin rai , mafi alheri  ta kasance a lokacin bukata da kuma lokaci mafi daukaka na zamani.

Tuba matsayinta a addini na da girma da daukaka domin ita ce sababi na samun rabauta da kuma samun sa'ada, Allah ya wajabta ta ga dukkan al'umma daga dukkan zunubbai. , sai ya ke ce ga wanda ya yi da'awan mata da da ga Allah (ase ba za su tuba zuwa ga Allah ba su nemi gafaran Shi ?) kuma ya ce ga muminai (ku tuba zuwa ga Allah gaba daya ya ku muminai ko za ku samu rabauta) , Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana rokon Allah a wuni so dari , kuma ya tuba zuwa gare Shi , Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ke cewa: (ya ku mutane ku tuba zuwa ga Allah domin ni ina tuba zuwa ga Allah sau dari a wuni) Bukari da muslim suka rawaito , mu muka fi dacewa da bukatuwa zuwa ga tuba , mafi alherin ranaku ga bawa shi ne ranan da ya tuba , Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce da Ka'ab binu Malik Allah ya kara yarda a gare shi (Albishirinka da mafi alherin rana albishirinka da mafi alherin ranan da ya zo a gareka tunda mahaifiyarka ta haife ka) Bukari da Muslim ne suka rawaito .

Abin mamaki da kyan tuba mutun zai tuba a mafi kyan ranaku zuwa ga Allah duk wanda ya yi gaskiya a tuban sa to darajarsa zata daukaka Allah zai canja mishi munanan shi ya maida su kyawawa .

A cikin ranaku goma na Zulhijja ana nufan dakin Allah da aikin haji daya daga cikin rukunnan musulunci kuma ginshikan shi masu girma Allah Subhanahu wa ta'ala ya ke cewa (Allah ya wajabta fiskantan daki  ga mutane duk wanda ya samu iko na zuwa) , wanda ya gaza yin hajji saboda wani uzuri to shima yana  tarayya da alhazai a cikin lada idan ya gaskata niya, ta iya yuyuwa ma mutumin da ya tafi da zuciyarsa sai ya riga wanda ya tafi da jikinsa .

A goman farko na Zulhijja akwai ranar arfa azumtansa yana kankare zunuban shekara guda da kuma shekara mai zuwa (Ba wata rana da Allah ya fi yawaita 'yanta bayi daga wuta kamar ranan arfa) Muslim ne ya rawaito.

A ciki ne akwai ranan suka mafi alherin ranaku na yanka kuma shi ne mafi bayyana kuma shi ne mafi yawan tara jama'a shi ne ake cewa yaumulhajjil akbar (ranan hajji mai girma) Allah Madaukakin Sarki ya ce: ( shelantawa daga Allah da ManzonSa zuwa ga mutane ranan hajji mafi girma) .

Shi ne mafi girman ranaku a wurin Allah Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:(lallai mafi girman ranaku a wurin Allah shi ne ranan suka sa'an nan kuma sai ranan sha daya) Abu dauda ne ya rawaito.

Kuma daya daga cikin I'idi ne na musulmai , rana ne na farin ciki da annashawa ta hanyan sauke wani rukuni daga cikin rukunnan musulunci, wasu mutane suna gafala tare da farin ciki daga ambaton Allah to ya kasance ambato a wannan ranaku yana da daraja , Allah subhanahu wa Ta'ala ya ce:(ku ambaci Allah a cikin ranaku kididdigaggu) – wato sune ranakun nan na Tashrik - , Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(Ranakun Tashrik ranaku ne na ci da sha da ambaton Allah) Muslim ne ya rawaito.

Ibnu Hajir Allah ya mishi rahama ya ce: '' Ya tabbata falalan wadan nan ranaku goma , saboda haka wadan nan ranaku na ayyamuttashrik falalan su ya tabbata ''

A cikin ranakun suka akwai ibada ta dukiya da kudi kuma ita ce mafi soyuwar ayyuka zuwa ga Allah, Allah ya hada su da sallah sai ya ce:(ka yi salla ga Ubangijinka kuma ka yi suka) , Allah ya kwadaitar bisa ga ikhlasi a wurin suka, kuma ya kasance Allah aka nufa a ciki Shi kadai ba alfahari ko riya ko kuma neman a ji ko kuma ya zama kwai tsurar al'ada ce, Allah subhanahu wa Ta'ala ya ce :(naman shi baya riskan Allah ko jinin su saide tsoron Allah ne ya ke riskan Shi) kuma << Annabi ya yi laiha da raguna biyu masu fari da baaki a kahgon su ya yanka su da hanun shi >> Bukari da Muslim ne suka rawaito. ''al'amlah '' (shi ne baki wanda saman shi akwai fari) "al'akran"( kuma shi ne mai kaho) , babu laifi mutun ya yi bashi don ya yi laiha kuma ya nemi mayuwa a wurin Allah kada ya rika zambo sakamakon tsadanta , domin ladan ta wurin Allah yana da girma duk wanda ya nufi ya yi laiha to ya haramta a gare shi a cikin ranaku goman nan da ya dauke wani abu na daga gashin shi ko farcen shi , Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ke cewa (Duk wanda ya kasance yanada abun yanka zai yanka to idan jinjirin watan zulhijjah ya kama to kada ya dauki wani abu na daga gashin shi ko kkuma kumban shi har sai ya yi laiha) Muslim ne ya rawaito.

Bayan haka ya ku musulmai:

Wanda ya samu sa'ida shi ne wanda ya ribaci lokutan nan na watannin nan da ranakun nan da sa'o'in nan ya kusanci Allah Majibincin shi da abin da ya ke na ayyukan da'a , ya wuci wani abu ya riske shi na wannan alheru ya samu sa'ada wanda zai aminta da su bayan haka daga wuta da abin da ke ciki na daga alheru kuma ya rabauta da aljanna wanda fadinta ya kai sammai da kasa .

Ina meman tsarin Allah daga shaidan abin jifa

(Ku yi gaggawa zuwa ga Uban gijin ku da aljannah wanda fadinta ya kai sama da kasa an tanadeta ga wanda suka yi imani da Allah da ManzanninSa wannan falala ne na Allah ya kan bada shi ga wanda ya so Allah Ma'aboci falala ne Mai girma).

Allah Ya sa mini albarka ni da ku a cikin alkur'ani mai girma. 

 

Huduba ta biyu :

   

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah bisa kyautatawanSa dodiya a gare Shi bisa datarwan shi da baiwan Sa na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai Ya ke ba Shi da abokin tarayya ina mai girmama Sha'aninSa , na shaida Annabin mu Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da sahabbansa da aminci tabbatacce mai kari.

Ya ku musulmai:

Addinin musulunci addini ne mai girma da an gina shi akan janyo maslahohi da kuma tunkude barna saboda wata hikima da Allah ya ke nufi da ita, ya shafawa mutane a doron kasa gabacin kasa da yammacinta da wata annoba wanda ba a taba irinta ba a tarihin doron kasa ko da sau daya kuma da boyuwarta da yaduwarta da gazawan samo maganinta wanda yana kama wanda ya kiyaye daga gareta a wani lokaci kuma ya kuskure da umarnin Allah wanda ake zaton zai kamu da ita.

 Hakika Allah ya kebance wannan gari (Alharamain Ashsharifain) da wasu darajoji kuma ya daukaka darajan jagororinta ta hanyan hidima da kuma kaunan su ga musulmai a dukkan doron kasa da kuma tsorace musu  abin da zai faru gare su na daga cutuwa, saboda haka ne jagororinta suka dauki matakai na hana yaduwar wannan cuta na annoba domin fatan gushewarta ba tare da an samu cakudayyan mutane ba sashin su ga sashi musamman a hajji tunda ana tafiya ne zuwa gare shi kuma ana zuwa a dawo yana karuwa a garuruwa, sai suka maida karin alhazai zuwa ga shekara mai fiskantowa domin fatan alheri da neman yayewan Allah da rahamarSa, Allah ya saka musu da alheri bisa ga musulunci da musumai.

Allah Subhanahu wa Ta'ala Ya siffantu da falala da karamci da rahama na daga wanda ya nufi hajji ya gazara yi to za a rubuta mishi ladan shi Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (lallai a cikin Madina akwai wasu mutane da baza ku yi wasu tafiya ba ko ku yanka wani kwari ba face sun kasance tare da ku) sai suka ce ya Manzon Allah : alhali suna Madina sai ya ce:(iye, uzuri ne ya tsare su) Bukari ne ya rawaito .

Sannan ku sani Allah Ya umarce ku da salati da  aminci ga AnnabinSa.