الجمعة، 24 أبريل 2020

WASU AYYUKA DA SUKE GUSAR DA BAKINCIKI




 
الوصف: cbc250ed-6a0e-4037-8d54-a9eb3d0a0577المترجم : أمين سعد عبد الله
التاريخ :24/8/1441هـ
اللغة : الهوسا
Hudubar Masallacin Annabi  24/8/1441AH  shaikh Abdulmuhsin Alkasim
Hudubar farko
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, muna gode maSa kuma muna neman taimakonSa,muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu  da munanan ayyukanmu, duk wanda Allah ya shiryar babu mai batar da shi, wanda ya batar kuma babu mai shiryar da shi, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke, ba shi da abokin tarayya, kuma na shaida Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne. tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabbansa da aminci tabbatacce mai yawa.
Bayan haka, ku ji tsoron Allah -ya ku bayin Allah- cancancin tsoronSa;  to ni'ima na cikin bin shiriya, tsiya kuwa na ga biyewa son rai.
       YA KU MUSULMAI:
Allah Mai tsarki yana da kyau da kuma daukaka a cikin sunayen shi da siffofin shi  da ayukan shi , ya halicci duniya ya kyautata abin da ya kirkira ya sanya wasu sunnoni da ba sa canzawa ko sauyawa , Allah Madaukakin sarki ya ce: (To ba za ka sami musanyawa ba ga  hanyar Allah,  kuma ba za ka sami  juyarwa ba ga hanyar Allah).

  Na daga cikin  sunnonin sa yana jarraban bayi da yalwa don su gode mishi  ya kuma jarrabe su da cuta don su juyo gare shi Allah Mai tsarki ya ce:- (Kuma muna jarraban ku da sharri da alheri domin fitina , kuma zuwa gare mu ake mayar da ku).
Hakika kuma an jarabci wasu al'umu da haka Allah Madaukakin sarki ya ce :- (Ko kuna zaton ku  shiga Aljanna kuma tun misalin wadan da suka wuce daga gabanin ku bai zo muku  ba wahaloli da cuta sun shafe su).
Ibn Kasir Allah ya mishi rahama ya ce :-''Su ne rashin lafiya da cututtuka da radadi  da musibu da tashin hankali  ''.
Sai Allah ya turawa Banu isara'ila  ruwan dufana ; fari,  da kwarkwata, da kwadi  da jini ayoyi ne daki-daki.
 Kuma Allah Mai izza da daukaka  yana bayyanawa bayinSa  kasaitanSa  da mulkinSa da karfinSa da kudurarSa  ga halittunSa da buwayarSa da jabarutinSa  a duniyarSa da kuma rinjayenSa da kuma haimanarSa ga  bayinSa , domin su girmama Shi kuma su kadaita Shi, su kankan da kai zuwa gare shi, sai Allah ya tunbuke dutse mai girma ya dora shi a saman banu isra'ila don su yi imani, Hasanul Basri Allah ya masa rahama ya ce : ''Yayi da suka ga dutsen  sai kowani mutum ya fadi ya yi sujada da saman giransa na hagu yana dubi da idonsa na dama ga dutsen tsoron kada ya fado a kansa"
Allah Madaukakin sarki ya ce:  (Kuma a lokacin da muka daukaka dutse sama da su kamar dai shi girgije ne, kuma suka tabatar mai faduwa ne gare su, (aka ce) ku karbi abin da muka baku da karfi, kuma ku tuna abin da ya ke a cikinsa ko za ku yi takawa)
Allah ya turo mala'ikan duwatsu  ga Annabinmu Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce da shi ya Muhammad  idan ka so sai na kifa musu duwatsun na biyu Akhshabain  wasu manyan duwatsu ne guda biyu a makka.  
Kuma Allah ya yi bayani game da saurin zartar da al'amarinsa a fadinSa;(UmarninSa idan ya yi nufin wani abu sai ya ce masa kawai "ka kasance" sai ya kasance (kamar yadda ya ke nufi)
Domin bayyana ajizanci irin na bani adam Allah ya kalubance su gabadayansu  da su halicci kwayan hatsi, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce Allah Mabuwayi da Daukaka ya ce : (To in zasu iya su halicci kwayar zarra ko su halicci kwayan hatsi ko sha'iri) Buhari da Muslim ne suka rawaito.
Da Allah ya so da ya turo musu wata aya da zata tilasta musu su yi imani da karfin tsiya  Allah Madaukakin sarki ya ce:  (Idan mun so zamu saukar a kansu da wata aya daga sama sai wuyayensu su yini sabo da ita suna masu kaskantar da kai).
Ibnu Juraij Allah ya masa rahama ya ce''Da Allah Ya so da ya nuna musu wani al'amari daga cikin al'amuranSa wanda bayan haka ba dayansu da zai iya saba masa a cikinsu"
  Allah ya yi wa bayinSa umarni da su rika yin tunani kan abin da yake faruwa a duniya kuma su yi lura da abubuwan da ke wakana, sai Mai tsarki ya ce : (kace Ku yi dubi ga abin da ke cikin sammai da kasa)
 Mumini yana daukan izina a ayoyi kuma ya wa'azantu da su, Allah Madaukakin sarki ya ce:  (wannan tafarki na ne mikakke hakika mun yi bayanin ayoyi daki –daki  ga mutane masu wa'azantuwa)
Kuma ya sakankance cewa dauraya ne a gare shi da daukaka daraja daga Allah, sai ya siffatu da wata ibada da ladanta ba iyaka.    
 Allah Madaukakin sarki ya ce:  (Kuma da sannu zamu jarabe ku da wani abu na tsoro da yunwa da tawaya na daga dukiya da rayuka da 'ya'yan itace to ka yi albishir ga masu hakuri. Wadanda idan musiba ta same su sai su ce : daga Allah muke kuma gare shi zamu koma. Wadannan suna da wani kyakkyawan ambato daga Ubangijinsu da rahama kuma wadannan su ne shiryayyu.)
Duk wanda yayi imani da hukuncin Allah da kaddararSa to Allah zai maida masa madadinsa da ya tsere masa a duniya, Allah Madaukakin sarki ya ce : ((Ba wata musiba da za ta samu  face da izinin Allah, kuma wanda ya yi imani da Allah Allah zai shiryar da zuciyarsa)
Ibnu kasir Allah ya masa rahama ya ce:''Duk wanda musiba ta same shi ya san cewa hukuncin Allah ne da kaddararsa, sai ya yi hakuri ya nemi ladansa a gurin Allah, ya mika wuya ga hukuncin Allah  to Allah zai shiryar da zuciyarsa, kuma ya musanya masa abin da ya rasa a duniya  da shiriya a zuciyarsa da yakini na gaskiya, kuma ya kan maye masa da abin da ya rasa ko ma abin da ya fi shi alheri.)
Mumini a duk juyawan zamani ko dai ya zama yana da lada bisa yalwa ko ya yi hakuri bisa ga abin da ya tsere na wani abin duniya na musiba ko jarabawa, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : (Mamaki da al'amarin mumini, lalle dukkan al'amarinsa alheri ne, haka bai kasancewa ga kowa sai mumini, idan abin farinciki ya same shi sai ya yi godiya sai hakan ya zama alheri a gare shi, in kuma cuta ce ta same shi sai ya yi hakuri hakan sai ya zama alheri a gare shi) Muslim ne ya rawaito.
Kyautata zato ga Allah cikin hikimarSa da gudanarwanSa da tausayinSa ga bayinSa da tausasawarSa gare su da rahamarSa bisa halin da suke ciki na cikin mafi girman sababi na dauke bala'i,  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace  : Allah Madaukakin sarki yace (Ni ina inda bawa na ya zace ni)Buhari da Muslim ne suka rawaito.
Kuma dogaro ga Allah da maida al'amari gare shi wajen kauda bakinciki abin lamuncewa ne. , Allah Madaukakin sarki ya ce : (Duk wanda ya dogara ga Allah to ya isan masa)
Imam Alkurdubi Allah ya masa rahama ya ce''wato wanda ya maida lamari gare shi zai isar masa duk abin da ya sha gabansa".
 Aikata sababi tare da dogaro ga Allah na daga cikin abin da sharia ta zo da shi : (Ya ku wadanda suka yi imani ku riki shirinku).
Na daga cikin manufofi na musulunci akwai kiyaye rai da nesatar da shi daga duk cuta mai rabuwa, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya ce:  (ka guje wa mai kuturta tamkar yadda zaka gujewa zaki) Ahmad ne ya rawaito.
Zaman gida a lokacin musiba da hadura shi ne hanyar kiyayewa da samun aminci, tururuwa ma ta gano haka (Ya ku  jama'ar tururuwa! Ku shiga gidajen ku kada Sulaimanu da rundunonin sa  su karkarya ku  alhali kuwa  su basu sani ba )
Ya dace ga musulmi a wannan halin da wanin sa  da ya raya lokacin sa da faragarsa  cikin  abin da zai amfane shi , kuma ya yawaita  nusar da iyalan shi da 'ya'yansa .
 Kuma duk wanda ayukan shi na kwarai suka gajarta sabo da wani uzuri,  to ladan sa na wurin Allah cikakke, kuma shi ma'aboci falala ne mai girma , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :- (Lallai a cikin madina akwai wasu mutane , ba wata tafiya da za ku yi  ko ku keta wani kori  face sun kasance tare da ku, sai suka ce  ya Manzon Allah ahali suna madina ? sai ya ce '' e, uzuri ne ya tsare  su'') BUHARI ne ya rawaito.
  Kankan da kai zuwa ga Allah da juyawa zuwa gare shi don neman mafaka   tare da bayyana rauni da kankan da kai a gare shi  abu ne da yake gusar da bala'i,   Allah Mai tsarki da daukaka yana cewa:- ( Ina ma da yayin da tsananin mu  ya zo musu sun  kankan da kai ).
Adu'a mabudi ne da ke canza yanayi  zuwa yanayi mafi kyau  Allah Madaukakin sarki ya ce :- (Kuma Ubangijin ku ya ce ku roke ni zan amsa muku ).
 Ita sadaka tana  kashe fushin Ubangiji Mai rahama da ita ne lada kan ribanyu  , kuma ake kankare kusakurai da laifuka  mai yin sadaka yana cikin aminci a duniya da lahira , Allah Madaukakin sarki ya ce :- (Wadanda suke ciyar da dukiyoyin su a dare da wuni  a sirrace da bayyane to, suna da ladan su a wurin Ubangijin su  babu tsoro a gare su ko bakin ciki).
Ciyarwa yana yaye  bakin ciki  yayin da wahayi ya saukawa Annabi farkon sauka sai ya cewa khadija Allah ya kara yarda a gare ta ( Hakika na jiwa kai na  tsoro , sai ta ce; a'a  wallahi Allah ba zai tozartar da kai ba har abada domin kai kana sada zumunci, kuma kana daukan nauyin gajiyayyu kana kuma taimakawa gaskiya a lokacin musiba , BUHARI ne ya rawaito
Amfanin ta na wucewa zuwa ga yaye bakin ciki na matattara (ranar alkiyama) , mai yin sadakan sai ya zama yana karkashin inuwar  sadakarsa ranar alkiyama, wanda ya boye sadakarsa ko da dan kadan ne to kuwa Allah zai karrama shi a wata inuwar  wacce ba inuwar sadakarsa ba , wato inuwar al'arshin Allah.   
Tuba zuwa ga Allah  da komawa zuwa gare shi tafarki ne  na Manzanni Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:- (Lallai ni ina  neman gafara ga Allah   na tuba zuwa gare shi  a rana sau saba'in) Buhari ne ya rawaito. 
     Kuma yawaita da'a  da tsoron Allah tafarki ne na samun sa'ida, Allah Madaukakin sarki ya ce:-
(Wanda ya ji tsoron Allah toAllah zai sanya mishi mafita ).
Ibn Abbas Allah ya kara musu yarda ya ce:- (Zai tsiratar da shi daga  bakin cikin duniya da lahira).
Idan hanyoyi suka yanke jarabawa suka tsanan ta  bayi suka ta'allaka da Ubangijinsu Allah,  sai Allah ya yaye bakinciki, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:- (Ubangijin mu ya yi dariya sabo da yanke tsammanin bayinSa   da kuma kusancin  tsananinSa ,-wato tsananin su na kusanci  tare da kusancin sanjawan halin su –Abu Razin Allah ya kara yarda a gare shi ya ce:- ''Na ce ya Manzon Allah  ashe Ubangiji ma yana dariya  ya ce '' E'' to ko ba za mu rasa alheri ba daga Ubangijin da yake dariya ). Ahmad ne ya rawaito.
Idan bakin ciki ya yaye ya wajaba ga bayi su kyautata yabo ga Allah su gode mishi su yi kyakkawan ambato a gare shi Allah Madaukakin sarki ya ce :- (Ku gode mini kada ku kafurce mini )
BAYAN HAKA YA KU MUSULMAI:
To Allah mai girma ne  ya iyakance dukkan komai , babu gujewa daga gare shi sai dai dawowa zuwa gare shi ,  kuma yana yarda ga bayin shi da su mishi da'a  kuma ya yi alkawarin bude alheru gare su daga sama da kasa muddin suka nemi mafaka a gare shi , (Da ace mutanen alkaryu za su yi imani su yi takawa  da mun bude musu albarkatu  a gare su daga sama da kasa  ) ba wanda zai amfane ka  koma bayan Allah (Idan Allah ya shafe ka da cuta  ba mai yayewa face shi , in kuma ya nufe ka da alheri to ba mai maida falalar Sa ).
Ka ta'allaku da  Shi ta hanyar  ayyukan da'a, ka girmama addininSa  kuma ka yawaita tilawar littafinSa   da kuma karanta sunnan  ManzonSa  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi   kuma ka yi riko da shari'arsa kuma ka yi farin cikin  da ita.
 Ina neman tsarin Allah daga sharin  shaidan abin jefewa
(Za mu nuna musu ayoyinMu a cikin sansani da kuma a cikin rayukansu, har ya bayyana a gare su cewa lalle (Alkur'ani) shi ne gaskiya , ashe, kuma  Ubangijin ka bai isa ba ,   ga cewa lallai shi halartacce akan ko wani abu ne).
Allah ya sa mini albarka ni da ku a cikin alkur'ani mai gairma.


HUDUBA TA BIYU
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah bisa kyautatawarsa, godiya ta tabbata a gare shi bisa datarwarSa da baiwarSa, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya, ina mai girmama sha'aninSa, na shaida Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne. Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabbansa da aminci tabbatacce mai kari.

Ya ku musulmai!
 Allah na saukar da cuta tare da sauki  to gashi watan alheri ta fuskanto,  tana kusa da ta  bude kofofin ta, a duk lokacin da jinjirin watan ta ya  haska sai ya hasko tare da  iskan alheri da kyakkyawan fata ,  Musulmai na  jiranta  rayukansu na  cike da albishir   zukatan su na cike da farin ciki da walwala, ramadana mafi alherin watannin shekara ,  Allah ya turo Manzon sa a cikinta ya saukar da littafinsa mai girma  acikin ta, kofofin sama  a bude suke kofofin jahannama a rufe suke , a cikin ta ne ake daure  shaidanu wunin ta na da falaloli daren ta na da albarka , a cikin ta akwai lailatulkadari wanda tafi wata dubu  alheri , wanda ya azumce ta kuma ya tsaya mata yana mai  imani  da kuma neman lada za a gafarta mishi abin da ya gabata na daga zunuban shi, yawaita ambaton Allah  yana daga cikin abu mafi alheri  da musulmai za su fiskanci  watan nasu da shi ,  da kuma neman gafararSa  da azama bisa ga ribatan sa'o'inta  ta hanyar biyayya da kyautatawa  da kuma fiskantar da'a da tilawar  Alkur'ani  da tsere a wurin aikin alheri a cikin ta , sa'annan ku sani  Allah yana umartan ku da salati da aminci ga AnnabinSa .       



    
    

    

السبت، 4 أبريل 2020

SUNNAR ALLAH A HALITTU


Hudubar masallacin Annabi na shaikh Abdulbari Bin Awad Assubaiti 10-8-1441AH/ 3-4-2020 AD
Hudubar farko:
AlKur'ani na da girma a cikin ayoyinsa, yana da karfi a nusarwansa cikin izinansa da wa'azuzzukansa yana haskaka basira kuma yana bayyana sunnonin Allah a duniya da rayuwa da kuma rayayyu, na daga cikin ayoyinSa fadin Allah Ta'ala (Allah ne Mahaliccin dukkan komai kuma wakili ne ga dukkan komai).
Allah tsarki ya tabbata Mahaliccin dukkan komai dukkan abin da ya ke motsi da motsawarsa haka nan dukkan abin da ya ke zaune gu guda da kuma zamantakansa, ba wani kwayan zarra a cikin sammai ko kasa face Allah ne Mahaliccinsa ba mahalicci koma bayan shi, ba kuma wani Ubangiji baicin Shi.
Yayin da musulmi ya ke karanta fadin Allah Madaukakin sarki (ka ce Allah shi ne Mahaliccin dukkan komai kuma shi ne guda daya Tilo Mai rinjaye)  zuciyarsa na samun natsuwa kuma ya rusuna ga kasaitar  Allah wanda dukkan wata kasaita ta ke zama ba komai ba gaba ga kasaitarSa.
Mutum musulmi ya na karanta fadin Allah Madaukakin sarki (Ya halicci dukkan komai kuma ya kaddarta shi kaddarawa) sai ya ga tafiyar duniya a cikin tsari mai zurfi, haka nan kuma a irin tsarin tafiyanta a kwai kyautatawa da kuma juyawan halayenta akwai kawatarwa da kuma ban kaye (lallai ko wani abu mun halicce shi da kaddara) Mahalicci ya yi duniya da abin da ya dace da ita sai ya kaddara ta kaddarawa ya kimtsawa dukkan wani halitta abin da ya halitta masa ya tabbatar da haka wa kanSa a fadinSa (shi ne wanda ya halitta kuma ya daidaita kuma ya kaddara ya shiyar), musulmai na karanta fadinSa (kuma Ubangijinka ya halicci abin da ya so kuma ya zaba) to mutum zai yi lura ta yaya halittan Allah suka kasance nau'uka daban daban na halittu da kuma iri daban daban na abubuwa da Allah ya halitta zai gani a ko wani kwayan halitta a kwai bambanci da waninsa na daga sauran halittu wurin sababin samuwansa da kuma kimansa da kuma ma'anansa, kuma fadin Allah Subhanahu Wa Ta'ala (Halittan Allah yanda ya ke kyautata dukkan komai, lallai shi Mai bada labari ne game da abin da ku ke aikatawa) wato ya kyautata dukkan komai da ya halitta ya kyautata shi kuma ya sa a cikinsa, akwai hikima na daga abin da ya sanya  .
Musulmai na jin fadin Allah (Ban halicci sammai da kasa ba da abin da ke tsakaninsu don wasa ba, ban haliccesu ba face da gaskiya sai dai mafiya yawan su ba su sani ba) sai ya gane cewa lallai Allah bai halicci duniya don wasa ba, bai kuma bar halittu haka kara zube ba, kuma abin da ke bayan wannan gudanarwa na ban kaye da kuma tafiyarwa wanda ya ke akwai hikima a ciki, akwai haduwa na lahira da sakayya Mai adalci yayin da musulmi zai yi lura da fadin Allah Madaukakin sarki (Allah wanda ya halicce ku sa'an nan ya azurta ku) zai samu natsuwa a zuciyarsa,  hakika Allah ya dauki nauyin azurta shi da yalwata shi daga taskarSa wacce ba ta karewa, da wannan yakinin ne ba zai fiskanci tambayan wani ba koma bayan Allah Madaukaki, musulmi yana sani a lokacin da ya ke karanta fadin Allah Madaukakin sarki (Lallai ne mun halicci mutun cikn wahala) lallai rayuwa tana haduwa da wasu abubuwa na wahalhalu gajiya na cakuduwa da ita jarabawowi na kewaye da ita sai ya kawata da imani mai zurfi da hakuri mai kyau Allah Madaukakin sarki ya ce (kuma lallai ne muna jarabar ku da wani abu na tsoro da yunwa da tawaya na daga dukiya da rayuka da 'ya'yan itace kuma ka yi bishara ga masu hakuri).
Na daga cikin abin da ya ke karfafa hakuri sakankancewan bawa cewa duk abin da ya same shi imma ya kasance kankara ne ga zunuban shi ko kuma sababi ne na ni'iman da ba a samu sai an bi gadan wahala da jarabawa sa'annan karshen ya zama abu ne mai kyau.
Musulmi na karanta fadin Allah Madaukakin sarki (wanda ya halicce ni sa'an nan  ya na shiryar da ni wanda shi ne ya ke ciyar da ni kuma ya ke shayar da ni, kuma idan na yi rashin lafiya shi ne ya ke warkar da ni, kuma wanda ya ke matar da ni sa'an nan ya rayar da ni , kuma wanda na ke kwadayin ya gafarta min kurakurai na a ranar sakamako). To sai ya tabbata a gare shi wannan ma'anan  ya samu natsuwa da kwanciyan hankali to Ubangijin shi yana ciyar da shi kuma ya na shayar da shi idan wani abu na rashin lafiya ya same shi, shi ya ke warakar da shi, idan ya roke shi bukata zai bashi, kamar kuma yanda musulmi ya sakankance cewa tunkude rashin lafiya da kawo waraka yana hanun Ubangijinsa majibincinsa .
Musulmi na karanta fadin Allah (Allah ne wanda ya halicce ku sa'an nan kuma ya ke kashe ku), zai sani sani da ba shakku cewa, lallai rayuwan duniya wata tasha ce kuma lallai za ta gushe duk tsawon wanzuwarta, kuma cewa shi din nan zai kaura a yau ko gobe, don ya hadu da Ubangijinsa.
 Musulmi kan karanta fadin Allah (An halicci dan adam da halin gaggawa, zan nuna muku ayoyi Na  sabo da haka kada ku memi yin gaggawa) sai ya san cewa abubuwa da suke faruwa da musibu lallai da ya yi a cikin halittunSa a ko wasu sha'anunnuka haka nan kuma abubuwan da ya boye akwai hikimomi masu zurfi, akwai na bayyane wasu kuma a boye ( kar ku zaci cewa sharri ne a gareku) a cikin abubuwa da ke faruwa da musibu musulmi kan karanta fadin Allah (lallai ne mutum an halicce shi mai ciwon kwadayi, idan sharri ya shafe shi ya kasa hakuri, kuma idan alheri ya shafe shi ya yi rowa , sai kawai masu yin salla ,wadanda suke, a kan sallar su su masu dawwama ne) sai ya ga siffofi na kwadayi da rashin hakuri tana galaba a kan shi ga wanda rashin lafiya ya sauka gare shi ko kuma wani talauci ya same shi ko kuma wata musiba ta sauka gare shi ya samu daman yin rowa da hanawa idan an bashi dukiya wadata  ko lafiya ta lullube shi da waraka amma Allah sai ya toge daga cikin haka wanda su ke bisa ga sallolin su suna masu dawwama, masu kiyaye salloli, su ne wadanda su ke samun sa'ida masu kiyayewa Allah na kiyaye su a cikin abubuwa da ke faruwa na musibu, musulmi ya kan tsiraita daga dabarar shi ko  karfin shi ya tabbatar da talaucin sa da bukatuwarsa zuwa ga Ubangijin shi da rashin wadatuwansa daga shi kyabtawan ido, a hakan ne Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ke fadin adu'o'i na bakin ciki (Ya Allah rahamarka mu ke fata kar ka kyale mu zuwa kan mu ko da kyabtawan ido ka gyara mini sha'ani na gaba dayan shi, ba abin bautawa da gaskiya sai kai).

Huduba ta biyu :
     A cikin wannan mawuyacin yanayi da duniya ta samu kanta sakamakon abin da wannan annoba mai saurin yaduwa ta haifar, duk wani mai hankali zai yaba da yadda mahukunta wannan kasa - masu son kawo tsari da matakan kariya ga rayuka da maslahohi - suka zama tsintsiya madaurin ki daya da talakawan su da suke wayayyu wadanda suka san ya kamata wajen bin dokoki da ka'idoji har zuwa wannan bakinciki da bala'in ya wuce, mu tsallake wannan tashin – tashina da matsanancin yanayi da falalar Allah da rahamarSa da tausayawarSa, haka kuma ana samun karin dankon zumuci ne da ke dauke da kambin sarauta ta gaskiyar komawa ga Allah da tuba.
A irin wannan yanayi na gamagarin annoba ya zama wajibi akan masu fada a ji da masu akwai  da su  ji nauyin da ke kansu na addini, mas'uliyyarsu da sakonsu a irin wannan yanayi da ake jarraba imani, a haka ne imani da 'yan uwantaka ke bayyana  don a saukakewa talakawa da miskinai da marayu radadin wannan musiba da yadda abubuwa suka ci tura ya jefa wasu ciki kuma bai gushe ba yana jefa wasu, ga wasu ayyuka sun tsaya, to a nan ne ake samun wasu ke tashi da hobbasa a bangaren tattalin arziki da dukiya da sanin ya kamata a bangaren zamantakewa da kula da ruhi da iyalai kowa ya yi gwargwadon fagensa da kwarewarsa a bigirensa ya bada nasa gudumawa iya gwargwadon himmarsa, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Duk wanda ya yayewa mumini wani bakinciki daga bakincikin duniya to shi ma Allah zai yaye mishi bakinciki daga bakincikin ranar alkiyama, wanda ya yalwatawa matalauci shi ma Allah zai yalwata masa a duniya da lahira, duk wanda ya rufa asirin musulmi to Allah zai rufa asirinsa a duniya da lahira, Allah na taimakon bawa muddin bawa na taimakon dan'uwansa). Muslim ne ya rawaito.