الجمعة، 1 مارس 2019

BIYAN BASHI A MUSULUNCI


Hudubar Masallacin Annabi na shaikh Husain Al- Asshaikh 24-6-1440
Hudubar farko
Kiyaye hakkokin jama'a na daga cikin abubuwa na tushe kuma na kat da shariar musulunci ta karfafa, sawaun ta bangaren bata kariya ko kiyaye ta, na daga cikin abin da wasu mutane ke sakaci da shi akwai baiwa  masu hakki hakkokinsu musamman bashi, wanda ke kan mutum na rance,na farashin wani abu da ya saya ko rance da ya ranta, ko ladan wani dan kodago ya yi mishi aikin kodago,da makamantarsu.
To abin da ya ke wajibi ga musulmi ya yi kokarin sauke nauyin da ke kansa, ya biya abin da ke kansa na hakkin 'yan uwansa Allah Madaukakin sarki ya ce :(kada ku ci dukiyarku a tsakaninku ta hanyar barna).
Lalle abin da ya ke farilla akan kowane musulmi na dole ya bada gabadayan hakkokin halittu, cikakke ba tare da ya tawaye ba, na daga cikin bayyanannen laifi da zunubi mai girma akwai sulalewa daga biyan basuka ko gujewa masu hakkin, da kin biyan bashin da jinkirta shi sai gaba mai zuwa tare da halin biya, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(zalunci ne mawadaci ya jinkirta biyan bashi).Muslim ne ya rawaito.
Almadalu shine jinkirta biyan hakki da ya dace a biya tare da halin biya da iko, amma ya ki biya akan lokacin to ya aikata haramun ya kuma fada cikin  zalunci  ga ma'abota hakki na daga cikin halittu, karshen zalunci hasara ne kuma abin kunya ne duniya da lahira.
Ya 'yan Uwa Musulmi!
Bashi al'amarinsa babba ne, shaninsa mai girma ne a musulunci, sabo da haka ne Abu Huraira Allah kara yarda a gare shi yace zaa zo ga Annabi da mammaci wanda akwai bashi a kansa  sai ya ce :(Shin ya bar abin da zaa biya bashinsa da shi? In an bada bayanin cewa  ya bar abin biya sai ya mishi sallah,in ba haka ba sai yace : ku yi sallah ga sahibinku,) Hadisin Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
    To ya kai wanda bai damuwa da biyan bashi, bai kulawada hakkin mai hakki, ka ji tsoron Allah Ubangijinka !
Muslim ya rawaito a sahih na shi daga Abdullahi dan Amr Allah kara yarda a gare shi ya ce : (Ana gafartawa dukkan shahidi sai wanda akwai bashi a kansa)
Haka kuma a gun nasa cewa wani mutum ya zo ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi sai ya ce:ya Manzon Allah, shin yanzu in an kashe ni a tafarkin Allah zaa gafarta min dukkan zunubai na? ya ce :E a halin kana mai hakuri kana neman lada kana mai fiskanta ba mai juya baya ba, ban da bashi, dazu Jibrilu ya fada min haka.)
To ya kai Musulmi ka sauke hakkin wani da ke kanka, ka kiyaye jinkirta biyan bashin dukiyan mutane a halin kana da kuduran biyanta, to ka gaggauta kafin wucewan lokaci,sanda zai zama ba wani abu na hakkokin halittu sai daukan fansa da kyawawa ko munana, Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata agare shi sai ya ce:( Duk wanda ya ke da wani hakki akansa na zaluncin dan uwansa game da mutuncinsa ko wani abu to ya warware daga gare shi a yau kafin ya zama dinari ko dirhami, in ya lasance yana da ayyukan kwarai sai a dauka daga gare shi gwargwadon abin da ya zalunce shi, to idan bai da kyawawa sai a dauka daga laifukan sahibin nasa sai a dora mishi).
Nasa'i ya rawaito daga Muhammad dan Muhsin Allah kara yarda a gare shi ya ce"(Mun kasance zaune a gurin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai ya daga kansa zuwa sama, sai ya sanya tafin hanunsa akan goshinsa, sannan ya ce : (Tsarki ya tabbata ga Allah! Me aka saukar na tsanani? Sai sahabbai suka yi shuru suka firgita da gari ya waye sai na tambaye shi ya Manzon Allah  wani tsanani ne wanda ya sauka? Sai ya ce :  Na rantse da wanda  rai na ya ke hanun shi , da ace wani mutum   za a kashe shi a tafarkin Allah  sannan a raya shi sannan a kashe shi sannan a raya shi , sannan  a kashe shi alhali akwai bashi akan shi to da ba zai shiga Aljanna ba har sai anbiya mishi wannan bashin .)
YA DAN UWANA MUSULMI:
Ka kasance cikin himma na gaskiya wurin sauke nauyin halittu  kuma ka halarto da kyakkyawar niyya  a lokacin biya da cika alkawari  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce :- (Duk wanda ya karbi dukiyan mutane  da nufin zai biya to Allah zai biya mishi ) buhari ne ya rawaito
Kai kuma mai bin bashi ka kasance mai rangwame mai saukin hali mai kyauta , duk wanda ya kasance yana cikin matsanancin hali ka yi mishi rangwame  zuwa sanda zai samu , sabo da fadin Allah madaukakin sarki :-( Idan  ya kasance  matalauci ne  to a jinkirta mishi zuwa  lokacin da Allah zai hore  mishi )
Daga cikin ayuka masu falala  akwai  ;  yin hakuri ga wanda bai samu ba da yafewa wanda ya rasa ,  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce:(Wani attajiri ya kasance yana bawa mutane bashi  idan ya ga  wanda ya gagara biya sai ya ce wa yaran shi ku yafe mishi ko muma Allah zai yafe mana  to kuma sai Allah ya yafe mishi ).
A ruwayar musulim Allah madaukakin sarki ya ce :-(Mu muka fi dacewa da hakan bisa gare shi   to a yafe mishi ). Ya zo a hadisi kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce:(Duk wanda ya saukake wa wanda ke mawuyacin hali  to Allah zai saukake mishi a duniya da lahira  ) Buhari da muslim ne suka rawaito.
  YA KAI   DAN UWA MUSULMI:
To ka ribaci    ladannan mai girma da falala mai auki ta hanyar tausayawa wanda ya rasa , kana mai  jinkirtawa  zuwa ga wani ajali   ko kuma ta hanyar yin rangwami da kubuta daga hakki  wannan shi ne lada mafi girma da sakayya mafi yalwa .
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:-( duk wanda  ke son Allah ya tsiratar da shi daga bakin ciki na ranar alkiyama  to ya yayewa matalauci     ) Muslim ne ya rawaito
HUDUBA TA BIYU
Yana daga cikin abin da musulunci ya wajabta akwai cika ladan mai kodago , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:-(ku bawa mai aikin kodago ladan sa kafin zufan sa ya bushe)  wasu malamai masu tantancewa sun ce hadisi ne  mai kyau .
To ya haramta a tawaye hakkin sa ko a rika cewa sai nan gaba , kan haka ne ma  Allah  madaukakin sarki  ya ce:-(mutum uku ni ne zanyi musu da su ranar alkiyama  sai ya ambata daga cikin su:- da mutumin da ya dauki hayan dan kodago,  ya nemi ya cikata mishi  ya nemi hakki daga gunshi bai bashi ladan shi ba)  Buhari ne ya rawaito


       

الجمعة، 8 فبراير 2019

RYUWAR DUNIYA A MAHANGAN MUSULUNCI


HUDUBAR MASALLACIN ANNABI NA SHAIKH ABDULLAH BIN ABDURRAHMAN         ALBUAIJAN 3/6/1440AH
Lalle Dukkan Yabo da godiya sun tabbata ga Allah muna gode mishi kuma muna neman taimakonsa kuma muna neman gafararsa , muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunan mu da munanan ayyukanmu, duk wanda Allah ya shiryar da shi babu mai batar da shi, kuma wanda Allah ya batar da shi babu mai shiryar da shi, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, shi ke da wanzuwa da kyakkyawan yabo, kaddartawa da hukuntawa na hanunsa, yana gudanar da al'amura daga sama zuwa kasa, yana aikata abin da ya so, ba za ku so ba sai abin da Allah ya halitta ya yarda.
 kuma na shaida Annabi Muhammad bawansa ne kuma manzonsa ne, ya isar da sako, ya sauke amana ya yi nasiha ga al'uma, ya yi jahadi a tafarkin Allah cancancin jahadi har mutuwa ta zo mishi, tsira da amincin Allah su tabbata agare shi da iyalansa da sahabbansa baki daya, bayan haka:
To lalle mafi alherin zance shine maganar Allah, kuma mafi kyan shiryarwa ita ce shiryarwar manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata agare shi, kuma mafi sharrin al'amura sune fararrun ta, kuma dukkan bidi'a bata ce kuma dukkan bata na wuta,
Ya ku bayin Allah ku ji tsoron Allah cikin abin da ya yi umarni, ku hanu daga abin da ya hana ya tsawatar,kuna dukkan karami da babba abin rubutawa ne,
(ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah cancancin tsoronsa kada ku mutu face kuna musulmai)

Ya ku jama'ar musulmai!
Allah ya kaddara abubuwan kaddarawa ya sanya musu lokaci, ya kuma kasa musu arziki, ya rubuta ga kowanne rabonsa na rabauta ko tsiyace wa, da rabon shi na ni'ima da yalwa da kuma tsanani da cuta, to duk wanda ya yarda zi samu yarda wanda ya fusata yana da fushi, dukkan komai da hukuncin Allah ne da kaddararsa.
 Ya ku bayin Allah ! hakika Allah ya rubuta arzikin bani-adam tun sunacikin mahaifa, idan mutum ya cika wata hudu acikin mahaifiyarsa, sai Allah ya turo masa mala'ika da aka wakiltawa kula da mahaifa sai ya busa masa rai da izinin Allah ya rubuta masa ajalinsa da aikinsa da arziki kuma shakiyyi ne ko sa'idi,
An karbo daga Abdullahi dan Mas’ud (R.A) yace manzon Allah (S.A.W) ya bamu labari, shi ne mai gaskiya abin gaskatawa yace: lallai kowanne dayanku ana tara halittarsa a cikin mahaifiyarsa, tsawon kwana arba’in yana maniyyi, sannan , ya canja ya zama gudan jinni kwatankwacin
wannan, sannan ya juya ya zama tsoka kwatankwacin haka sannan, ya juya ya zama tsoka kwatankwacin haka, sai a aiko
mala’ika ya busa masa rai, a umarce shi da rubuta kalmomi guda hudu: A rubuta arzikinsa da ajalinsa da a ayyukansa da kuma dan wuta ne ko aljanna na rantse da wanda babu wani abin bautawa da gaskiya face shi lallai dayanku zai yi aiki irin na ‘yan Aljanna har ya zamanto baa bin da ke tsakaninsa da
Aljanna sai zira’i daya sai rubutun can ya rigaye shi, yayi aiki irin na ‘yan wuta, sai ya shige ta, lallai dayannku zai yi aiki irin na ‘yan wuta har abin da ke tsakaninsa da ita bai wuce zira’i daya ba, sai littafi ya rigaye shi sai yayi aiki irin aikin yan aljanna sai a shige ta) Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Arziki abu ne da an riga an kasa shi, dukkan komai an yi shi ne da hukunci na Ubangiji da ajali sananne,to ku dai ku nemi halal,ku nemi taimakon Allah,wajen neman arziki, ku kuma kyautata zato ga Allah,domin mummunar zato abin zargi ne da bai da amfani, Allah na ga inda bawansa ya  kyautata zato a gare shi, to ya kai bawan Allah ka rika kyakkawan fata,ka yarda da kason da Allah ya diba maka, na hore ka da ka nesaci kwadayi da tsoro da handama, na hore ka da sakaci,   domin hakan wauta ne da almubazzaranci, idan musiba ta same ka kada kace da da ba don kaza ba, sai dai kace Haka Allah ya kaddara, kuma abin da ya so shi ya ke aikatawa.
Ya ku bayin Allah!
Allah shine mai bayarwa shi ne Mai azurtawa, hannayensa biyu a shinfide suke yana ciyarwa yadda ya so, taskokin sa ba su karewa, damarsa a cike take ciyarwa bata rage ta, mai yawan kyauta ne dare da wuni.
"An karbo daga Abu-zarri (رضي الله عنه). Yace, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace cikin abin da ya rawaito daga Ubangijinsa Mai tsarki da daukaka ya ce : Ya ku bayi na ! lalle na haramta zalunci wa kai na kuma na sanya shi haramun a tsakaninku, to kada ku yi zalunci,
Ya ku bayina! dukkaniku batattu ne, sai wanda na shiryar da shi; ku nemi shiryarwata; in shiryar da ku. Ya ku bayina! dukkaninku mayunwata ne sai wanda na ciyar da shi; sai ku nemi ciyarwata; in ciyar da ku. Ya ku bayina! kowanenku tsirara ya ke; babu tufafi sai wanda na tufatar da shi; sai ku nemi tufatarwata, in tufatar da ku. Ya ku bayina ! lallai kuna yin laifi dare da rana, ni kuma ina gafarta zunubai gabadaya; sai ku nemi gafarata; in yi muku gafara  ya ku bayi na ba ku kai abin da zaku cutar da ni ba balle ku iya cutar da ni, haka kuma ba ku kai abin da za ku iya amfanar da ni ba balle ku amfanar da ni, ya ku bayi na da a ce na farkonku da na karshenku da mutanenku da aljaninku zasu kasance da zuciyan mutum guda mafi tsoron Allah a cikinku, to hakan ba zai kara komai a mulki na ba, ya ku bayi na da ace na farkonku da na karshenku da mutanenku da aljaninku zasu kasance da zuciyan mutum guda mafi fajirci a cikinku da hakan ba zai rage komai ba a mulki na, , ya ku bayi na da a ce na farkonku da na karshenku da mutanenku da aljaninku zasu tsaya a kan wata kasa guda suka roke ni na kuma bawa kowa bukatansa da hakan ba zai rage wani abu na daga gare ni ba face kamar abin da allura zai rage in an sa cikin kogi, ya ku bayi na lallai ayyukan ku ne nake kididdige  muku na cika muku, to wanda ya samu alheri ya godewa Allah, wanda ya samu sabanin haka to kar ya zargi kowa sai kansa) " Muslim ya ruwaito shi.
Ya ku bayin Allah !
Lalle Allah ya dauki nauyin azurtawa,sai yace : (Ba wata dabba  a cikin kasa face ga Allah arzikinta ya ke kuma ya san matabbatarta da ma'azarta , duka suna cikin littafi bayyananne)  
Yana azurta jariri a cikin mahaifiyarsa da kifi a cikin ruwa, da macizai a cikin rami, Allah bai taba halittar wasu halittu ba ya sarayar  da su, da bawa zai gujewa arzikinsa da arzikin ya riske shi, (Allah na yalwata arziki ga wanda ya so daga cikin bayinsa kuma yakan kuntata wanda ya so).
Ya ku musulmai!
Allah kan jarrabi mutum da arziki don ya kyautata ya bo ya gode, ya kan kuntata  don jarabawa ba don ya manta ba   ko gazawa, to a nan sai ya lizimci hakuri.
Duk wanda talauci ta sauka gare shi sai ya kai kuka ga wanin Allah to ba zai toshe mishi talaucin sa ba, duk wanda ya nemi kame kai to Allah zai bashi kamewa, wanda ya nemi ya wadatu Allah zai wadata shi, wanda ya nemi ya zama mahakurci Allah zai maishe shi mahakurci,
To hakuri bisa talauci da tsanani da tsadar rayuwa da jarabawa abu ne na wajibi a sharia  kuma al'amari ne na larura na dole, Allah ya zargi ga hakan sai ya ce : (To shi mutum idan Ubangijinsa ya jarrabe shi ya karrama shi ya masa ni'ima sai yace Ubangiji na ya karramani, to amma idan ya jarrabce shi ya ya kuntta mishi arzikinsa sai ya ce Ubangiji na ya wulakanta ni)
Ya ku bayin Allah!
Tsoron Allah shine abu mai riba  mafi alheri ga bawa, shine mafita daga duk wani kunci da sharri, (Duk wanda ya ji tsoron Allah zai sanya mishi mafita kuma ya azurta shi daga ta inda bai zato).
Tsoron Allah shi ne taskar sammai da kasa,abin da ke gurin Allah ba a riskarsa da saba masa, (Kuma da lalle mutanen Alkaryu sun yi imani suka yi takawa da mun bude Albarkoki a kansu daga sama da kasa to amma sai suka karyata sai muka kama su da abin da suka kasance suna aikatawa)
      Allah ya sanya min albarka ni da ku a cikin Alkur'ani mai girma,kuma ya amfane ni da ku da abin da ke cikinsa na ayoyi da ambato mai hikima, ina fadin abin da kuke ji ina neman gafarar Allah mai girma, ga ni da ku daga dukkan zunubai, kuma ku nemi gafarar sa lalle shi Mai gafara ne Mai jinkai.
Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah,wanda ya halicci mutuwa da rayuwa don ya jarrabe ku  wanene ya fi kyan aiki, ya kuma sanya Albakiyatussalihatu ya zama mafi alheri a gurin Ubangijinka a lada da ku kyakkyawan fata, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabinmu Muhammad wanda ya fi tsarkin zance da aiki cikin halittu, da iyalansa da sahabbansa masu mutunci da falala da tabiai da wadanda suka bi su da kyautatawa har zuwa ranar sakayya.
Ya ku bayin Allah !
Aiki mabudi ne na kyakkyawan fata, mafi tsarkin abin nema shine sana'ar hanu, hannu mai mikawa ya fi hannu mai karba, kame kai ya fi alheri bisa roko, wanda ya wadatu daga waninsa ya daukaka kuma ya kare mutuncin kansa, Manzon Allah tsiran da amincincin Allah su tabbata a gare shi yace: Na rantse da wanda rai na ke hanunsa dayanku ya dauki igiyarsa ya je ya yi kirare ya dora a bayansa ya fi alheri a gare shi da ya zo ga mutum ya roke shi, sawa'un ya ba shi ko ya hana shi,) Bukhari ne ya rawaito.
Hakika Annabi Musa amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance yana kiwon dabobi ana biyansa, Annabin Allah Zakariyya ya kasance kafinta ne, Annabin Allah Dauda amincin Allah ya tabbata a gare shi ya kasance yana ci daga aikin hanunsa, Annabinmu Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana kiwon dabbobi na mutanen makka bisa wasu sulalla, ba wani abinci da mutum zai ci da ya fi alheri bisa aikin hanunsa, Aiki daukaka ne zaman banza kuma barna ne, (Shi, (Allah), Yã sanya muku ƙasa hõrarriya, sai ku tafi cikin sãsanninta, kuma ku ci daga arzikinSa, kuma zuwa gare shi ne tãshin yake)
 (Ku tafi a doron kasa ku nema daga falalar Allah)
  Ku dogara gare shi, to  duk wanda ya dogara a gare shi ya isan masa,     (Kuma kada ku yi bakinciki game da abin da ya tsere muku, kuma kada ku yi farinciki bisa abin da ya ba ku)
Ya ku musulmai!
Duniya mai karewa ne kuma mai gushewa ce, lalle gidan lahira ita ce gidan rayuwa, ba rayuwa kamar rayuwar lahira, Duniya jin dadi ne na rudi,mai saurin wucewa, mai saurin sanjawa, ba ta tabbatuwa a hali guda, ta fi tsananin juyawa a kan ranaku da dararraki, idan ta sauka a guri sai ta bata shi, in ta bayyana sai ta bada tsoro,sau da yawa takan sa mutum dariya kuma ta sa shi kuka, ta faranta kuma ta jiyar da ciwo, ta fiskanto ta kuma juya baya, ita ba wata aba ba ce sai farinciki da bakinciki, jin dadi ne na holewa da kuma juyayi, kuma walwala ne da annashwa,da bakinciki da bacin rai,kuma wargi ne da wasa, da kawa da alfahari da  tinkaho da yawa    (Ku sani cewa rãyuwar dũniya wãsã ɗai ce da shagala da ƙawa da alafahri a tsakãninku da gãsar wadãta ta dũkiya da ɗiya, kamar misãlin shũka wadda yabanyarta ta bãyar da sha'awa ga manõma, sa'an nan ta ƙħƙashe, har ka ganta tã zama rawaya sa'an nan ta kõma rauno. Kuma, alãmra akwai azãba mai tsanani da gãfara daga Allah da yarda. Kuma rãyuwar dũniya ba ta zama ba fãce ɗan jin dãɗin rũɗi kawai).
   Mutum bai da wani abu cikinta sai abin da ya gabatar ko ya ci ya karar, ko ya sanya tufafi har ya tsufar ya rididdige, ko ya yi sadaka ya shude, to ka kasance a duniya kamar wani bako ko mai ketare hanya, jin dadin rayuwar duniya dan kadan ne, lahira ta fi alheri ga wanda ya ji tsoron Allah, kuma ita ta fi alheri da wanzuwa, ka guji duniya Allah zai so ka, ka guji abin hanun mutane, sai mutane su so ka.
Bayan haka ya jama'ar musulmai!
To lalle duniya za ta kaura tana mai juya baya,lalle kuma lahira za ta fiskanto, kowacce na da 'ya'ya, to ku kasance daga 'ya'yan lahira, kar ku kasance daga yaran duniya, to lalle yau aiki ne ba hisabi, gobe kuma hisabi ne ba aiki.
To ka gaggauto zuwa ga Aljannar Adni,domin ita ce masaukanka na farko cikinta akwai shemomi,
ya kai mai saida wannan da raha kana mai gaggawa,
    kai ka ce baka sani bane aaha zaka sani.
To in baka sani ba ne to wannan musiba ce.
In ka kasance kana sane to musibar ta fi girma.
          

الجمعة، 25 يناير 2019

ALBISHIR A MUSULUNCI


Hudubar Masallacin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi na shaikh Abdulmuhsin Alkasim 19-5-1440
Hudubar farko
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, muna gode masa kuma muna neman taimakonsa
Muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu  da munanan ayyukanmu, duk wanda Allah ya shiryar babu mai batar da shi, wanda ya batar kuma babu mai shiryar da shi, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya,kuma na shaida Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa. Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabbansa da aminci tabbatacce mai yawa.
Bayan haka, ku ji tsoron Allah -ya ku bayin Allah- cancancin tsoronSa, don cikin tsoron Allah akwai karuwar  ni'ima da tunkude azaba.
Ya ku musulmai! Addinin musulunci addini ne na fidira yana kira zuwa ga kyakkyawan kuduri da kyawawan dabiu, da sifofi abin yabawa, yana lura da yanayin halin da mutum ke ciki, kuma ya faranta masa rai a yanzu, kuma ya kwadaitar da shi fatan alheri a nan gaba, da yi wa halittu albishir da abin da zai dadada musu rai, a matsayin bauta ga Allah da kusanci, Allah ya ce : (ka yi albishir ga muminai). Hakika Allah ya siffanta kanSa da hakan sai yace: (wancanninka shine abin da Allah ke albishir ga bayinSa)     sabo da girman matsayi irin na albishir a cikin zukata mala'iku ke zuwa da shi, Allah Mabuwayi da daukaka ya ce:(Hakika manzanninMu sun zo wa Ibrahim da bushara). Yin bushara ga bayin Allah muminai na daga cikin manufa na turo manzanni, Allah Madaukakin sarki ya ce :(Ba mu turo manzanni ba face masu albishir masu gargadi)
Isa amincin Allah su tabbata a gare shi ya zo da albishir sai Allah ya ce : (Kuma ina mai albishir da wani manzo da zai zo a bayana sunansa Ahmad)
Kuma yana cikin siffofi mafi kyau na mutanen farko, (A yayin da mai albishir ya zo sai ya jefa ta (rigar) akan fiskarsa sai ya koma mai gani)
Allah ya turo Annabinmu Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da bushara na falaloli da  gidajen aljanna masu ni'ima ga Al'umarsa,Allah madaukakin sarki ya ce : (Ba mu turo ka ba face mai albishir kuma mai gargadi)
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance mai yawan Albishir ne ga sahabbansa, dukiya ya zo mishi daga kasar Bahrain sai ya ce da su (Ku yi bushara da fatan alheri na abin da zai dadada muku rai) Bukhari da Muslim ne suka rawaito.  
Na daga cikin koyarwarsa ya kan tura masu da'awa ga sassa na duniya don su yi wa mutane bishara da ni'ima ta musulunci, sai yace da Mu'az dan Jabal da Abu Musa Allah kara yarda a gare su a yayi da ya tura su yaman :(ku saukaka kada ku tsananta, ku yi bushara kada ku kore mutane,) Bukhari da Muslim ne suka rawaito,
Hakika Allah ya bada labari cewa na daga cikin siffofin muminai albishir ga junansu, (kuma idan aka saukar da wata sura to daga cikinsu akwai wadanda suke cewa: wanene a cikin ku wannan sura ta kara masa imani? To amma wadanda suka yi imani, to ta kara musu imani, kuma su suna yin bushara (da ita).  Wato sashe na yi wa sashe albishir da baiwa da Allah ya yi musu.
A addinin musulunci akwai albishir masu yawa daya bayan daya  ga mabiyansa, bushara mafi girma ga wanda ya tabbatar da tauhidi (kuma wadan da suka nesanci shaidanu ga bauta musu kuma suka maida al'amari ga Allah,suna da bushara , To ka bayar da bushara ga bayi na)
To idan bawa ya tsayu a kan biyayya ga Allah da kadaita shi to yana da albishir da gidajen Aljanna na ni'ima, (Lalle wadannan da suka ce Ubangijinmu shine Allahm sa'annan suka daidaitu Mala'iku na sauka a gare su(lokacin zuwan ajalinsu) suna ce musu) kada ku ji tsoro kuma kada ku yi bakinciki, kuma ku yi bushara da aljanna.wanda kun kasance ana yi muku wa'adi da ita.
   Duk wanda ya hadu da Allah bai hada shi da wani to albishirinsa Aljanna ne, Mala'ika jibrilu amincin Allah ya tabbata a gare shi ya ce da Manzon Allah (ka yi albishir ga Al'umarka cewa Duk wanda ya mutu bai hada Allah da wani to zai shiga Aljanna.)Bukhari da muslim ne suka rawaito
To duk wanda ya bi Alkur'ani da sunna Allah na mishi albishir da gafara da lada mai girma, (kana yin gargadi kawai ga wanda ya bi Alkur'ani ne kuma ya ji tsoron Mai rahama a fake, to ka yi masa bishara da gafara da wani sakamako mai karamci ).
Tushen shiriya shine ilimin da ya hadu da aiki  Allah madaukakin sarki yace :(wadan da suke sauraron magana sa'annan su bi mafi kyaunta, wadancan sune Allah ya shiryar da su, kuma wadancan su ne masu hankali).
Kuma shi musulmi mai kankan da kai ga Ubangijinsa mai mika wuya ga umarninSa, mai tawaliu ga halittunSa zai samu bushara, Allah madaukakin sarki ya ce : (Kuma ka yi bushara ga masu kankantar da kai)   
Duk wanda wata musiba ta same shi sai ya maidawa Allah lamarin shi ya yi hakuri bisa ga abin da Allah ya hukunta ya kaddara, to yana da albishir daga Ubangijin talikai. Allah madaukakin sarki ya ce : (ka yi albishir ga masu hakuri wadan da idan musiba ta same su sai su ce :lalle ne mu daga Allah muke kuma gare shi za mu koma. Wadannan akwai kyakkyawan yabo daga ubangijinsu da wata rahama kuma wadannan su ne shiryayyu.)
Kyautayi ga Allah da halittunSa alheri ne a duniya da lahira Allah ya ce : (ka yi albishir ga masu kyautatawa).
Kuma muminai ana musu albishir da daddadan rayuwa da sakayya mai girma. Allah madaukakin sarki ya ce: (ka yi albishir ga muminai suna da wani falala mai girma daga Allah).
Na daga cikin falalarSa gare su yi musu bushara da abin da Allah ya alkawarta musu na gidajen Aljanna masu ni'ima da dukkan abin da suke fata a cikinta. Allah madaukakin sarki ya ce : (Wadanda suka yi imani kuma suka yi ayyukan kwarai  suna cikin fadamun aljanna suna abin da suke so, a wurin Ubangijinsu waccan fa ita ce falala mai girma. Wancan shi ne Allah ke bayar da bushara da shi ga bayinSa wadanda suka yi imani kuma suka aikata ayyuka na kwarai).
Bisharori masu yawa na bin juna cikin rayuwar duniya har bayan mutuwa. Allah madaukakin sarki ya ce : (To lalle masoyan Allah babu tsoro a gare su kuma ba bakinciki. Wadanda suka yi imani kuma suna jin tsoron Allah. Suna da bushara a cikin rayuwar duniya da ta lahira babu musanyawa ga kalmomin Allah, wancan shine babban rabo mai girma  ).
Idan mutuwa ta zowa mumini sai a mishi bushara da mafi daukakan masaukai Manzon Allah tsira amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(Mumini Idan mutuwa ta zo mishi zaa mishi albishir da yardar Allah da karamarSa sabo da haka ba wani abu da ya fi soyuwa a gare shi fiye da abin da ke gaba gare shi, sai ya so haduwa da Allah to Allah ma ya so haduwa da shi,) Bukhari ne ya rawaito.
Malaiku na cewa ka fita ya kai rai mai tsarki, ana maka albishir da hutawa da kyakkyawan abinci, da Ubangiji wanda ba zai yi fushi ba, sannan a haura da shi zuwa sama, sai a bude mishi sai a ce :wanene wannan sai su ce wane ne, sai a ce maraba da rai mai tsarki wanda ya kasance cikin jiki mai tsarki, ka shiga kana godiya,ana ma bushara da hutu da abinci, da Ubangiji ba zai yi fushi ba, ba zaa gushe ba ana fada mishi haka har a kai ga saman da Allah Mabuwayi da daukaka ke cikinta,)Ahmad ne ya rawaito.
   Idan kiyama ta tsaya bishara zata bayyana a fiskar muminai, Allah madaukakin sarki ya ce : (wasu fiskoki a wannan ranar masu haske ne, masu dariya masu bishara)
Suna da bushara a yanayi mafi tsanani, lokacin da mutane zasu kasance a kan siradi bisa jahannama, Allah mai tsarki da dauka ya ce : ( Rãnar da zã ka ga mũminai maza da mũminai mãtã haskensu nã tafiya a gaba gare su, da kuma dãma gare su. (Anã ce musu) "Bushãrarku a yau, ita ce gidajen Aljanna." Ruwa na gudãna daga ƙarƙashinsu sunã mãsu dawwama a cikinsu. Wannan, shĩ ne babban rabo maigirma. )
Idan sun shiga aljanna suna da sakayya mai yawa a wurin Ubangijinsu.(  kuma ka yi bushãra ga waɗanda suka yi ĩmãni da cewa: Lalle ne sunã da abin gabãtarwar gaskiya a wurin Ubangijinsu.)
Musulmi na so wa 'yan'uwansa abin da ya ke so wa kan sa, kuma yana kokari don ya faranta musu, bishara da alheri na cikin kofofi mafi sauki na ribatar zukata, idan wata ni'ima ta sabunta ga dan'uwanka na  addini ko duniya, to ka mishi Albishir da ita,kamar yadda mala'iku suka yi wa Annabi Ibrahim albishir da Isma'il Amincin Allah su tabbata a gare shi, Allah madaukakin sarki ya ce : (  Sai Muka yi masa bushãra da wani yãro mai haƙuri)
  Sun yi mishi bishara da Ishak Amincin Allah ya tabbata a gare shi Allah madaukakin sarki ya ce : ( Kuma Muka yi masa bushãraDa Is'hãƙa ya zama Annabi daga sãlihan mutãne.)
An yi albishir ga zakariyya da Da bayan ya yanke tsammani  (Allah Ya karɓa) "Yã zakariyya! Lalle ne Mũ, Munã yi maka bushãra da wani yãro, sunansa Yahaya. Ba Mu sanya masa wani takwara ba a gabãni).
 Wani Malaika ya sauka ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi wanda bai taba sauka ba :(Bushara gare ka da haske biyu da aka baka ba wani Annabi da aka bawa su kafin kai, fatiha da karshen suratul bakara ba za ka karanta su ba sai an baka su.)Muslim ne ya rawaito.
Na daga cikin koyarwarsa Manzon Allah su tabbata a gare shi,Albishir ga wanda wani bakinciki ya yaye a gare shi, ya ce da Aisha Allah kara yarda a gare ta: (Albishirinki ya A'isha, amma Allah ya barrantar dake)
Mace tagari mai biyayya ga mijinta sakayyarta Aljanna ne,Jibrilu amincin Allah su tabbata a gare shi ya sauka ga Annabi sai yace :(Ya Manzon Allah ga khadija nan tana zuwa da kwano acikin shi akwai miya ko abinci ko abin sha, to idan ta zo ma to ka isar mata da gaisuwa daga Ubangijinta kuma daga gare ni, kuma ka mata bushara da gida a Aljanna na Zinari ba hayaniya a ciki ko gajiya,)Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Kaifin hankali na ga rarrashin wanda halinsa ya kyautata idan wani abu ya dame shi sai a mishi bushara da fatan alheri, a farkon saukan wahayi ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai ya shiga gun khadija Allah kara yarda a gare ta sai ya ce da ita :(Hakika na tsoracewa kai na, sai ta ce da shi:, A'a albishir na rantse da Allah, Allah ba zai taba kunyata ka ba har abada). Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Duk wanda ya lazimci gaskiya ba tare da ketare iyaka ba, ko jafa'i to yana da bushara ta lada mai yawa, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (ku kirdadi daidai ku kusanto ku yi bishara) Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Allah na farinciki da tuban bawa sabo da falala da karamci irin nashi, kuma ranar da bawa zai tuba zuwa ga Allah shine mafi alherin ranaku a gare shi a duniya, sabo da abin da tuba ke janyowa ga bawa na maslaha a duniya da lahira, Ka'ab dan Malik bai halarci yakin tabuka  ba,Allah ya yarda a gare shi, shi da abokan nasa biyu ba tare da wani uzuri ba, sannan Allah ya karbi tubansu, sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana mai albishir ga ka'ab, sai yace : (Bushara a gare ka  da rana mafi alheri a gare ka tun daga randa mahaifiyarka ta haife ka),
Kuma duniya kan kuntata ga wanda ajalinsa ya kusato, amma kuma yana jin dadin kalamai masu dadi, da zai ji ta sabo da kusacin kaurarsu ga gidan lahira bai san ina ya nufa ba,  Mutuwa ta zo ga  Amru dan As, sai ya yi kuka mai tsawo, sai dansa na cewa : Ya baba na a se Annabi bai ma albishir da kaza ba)Muslim ne ya rawaito.
 Mafi girman abin da musulmi zai yi albishir da shi shi ne daukakan wannan addini da isan sa duk inda dare da rana ya isa,
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Yi wa wannan al'uma bishara  da daraja  da daukaka, da addini da nasara da samun mulki a doron kasa)Ahmad ne ya rawaito). Ahmad ne ya rawaito
Duk wanda aka mar albishir da alheri ya zama mustahabbi ne a gare shi da yayi wa Allah sujada na godiya, kuma ya saka wa wanda ya mishi albishir da abin da zai iya,Ka'ab dan Malik Allah ya kara yarda a gare shi ya ce  a hadisin kissarsa da sahibansa : (A yayi da ina zaune a halin da Allah ya ambata game da mu, hakika raina ya kuntata, kasa ta min kunci da duk fadinta, sai na ji mai yekuwa ya cika dutse da sautin sa yana cewa :ya ka'ab dan Malik Albishirinka, sai yace :sai na fadi ina mai sujada, sai na san cewa yayewan bakinciki ya zo, wasu masu albishir suka tafi ta gun sahibai na, wani mutun yayi gudu haye kan doki zuwa gare ni, wani mai   kokari daga kabilar Aslama ya hauro dutse to sautin nasa har ya fi  dokin sauri, yayin da wanda na ji sautin nasa ya iso sai ya min albishir,sai na tube tufafi na biyu na tufatantar da shi su sakayya ga albishir da ya yi min, Wallahi ban mallaki waninsu ba,sai na ari wasu tufafi biyu na sanya su, sai na tafi zuwa ga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ,sai ga mutane suna ta tara na tawaga tawaga suna mini barka da karbar tuba, suna cewa: Barkanka da tubar da Allah ya amsa ma).Bukhari da Muslim ne ya rawaito.
Bayan haka ya ku musulmai:
Ba wani addini da ya fi addinin musulunci kyau, don shi addini ne na farinciki da jindadi, yana  kwadaitarwa gurin cusa walwala ga al'uma, mafi dacewan mutane da alherin musulunci sune musulmai, Bushara tushe ne cikin kiran halittu zuwa ga addini, da kwadaitar da shi cikin zukatarsu.
Ina neman tsarin Allah daga sharrin shaidan abin jefewa,
 (Yã kai Annabi! Lalle Mũ Mun aike ka kanã mai shaida, kuma mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi. 
  Kuma mai kira zuwa ga Allah da izninSa, kuma fitila mai haskakãwa. 
  Kuma ka yi bushãra ga mũminai cħwa, sũnã da falala mai girma daga Allah.) 
 
Allah sa mini Albarka ni da ku cikin Alkur'ani mai girma.


Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah bisa kyautatawarsa, godiya ta tabbata agare shi bisa taufikinsa da datarwarsa, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, sabo da girmama sha'aninSa, kuma na shaida Annabinmu Muhammad bawanSa ne kuma Manzonsa ne,tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa da sahabbansa da karin  aminci tabbatace mai yawa.
Ya ku Musulmai:
Mafi girman mai albishir a musulunci shine Alkur'ani mai girma, dukkan shi shiryarwa ne da albishir Allah madaukakin sarki ya ce : ( kuma Mun saussaukar da Littãfi a gare ka dõmin yin bãyani ga dukkan kõme da shiriya da rahama da bushãra ga mãsu mĩƙa wuya (Musulmi). 
Kuma da Kyautata yabo ga wanda ya kyautata ba tare da ya nemi hakan ba, na daga cikin albishir na kusa ga mumini, an ce da Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,(bani labarin mutumin da yana aikata aikin alheri kuma mutane na yabonsa bisa haka, sai manzon Allah yace : Ai bushara ce ta mai gaugawa ga mumini.)Muslim ne ya rawaito.
Mafarki na kwarai na farantawa ba ya korewa kuma yana cikin masu bishara, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Ba abin da ya rage na annabtaka sai masu bushara, sai suka ce: menene masu bishara? Sai yace : Mafarki nagari,) Bukhari ne ya rawaito.
Allah na turo iska ne da bushara ta ruwan sama don ya farantawa mutane rai  kafin saukarsa da bayan saukarsa.
Kuma akwai daga ãyõyinSa, ya aika iskõki mãsu bãyar da bushãra)  
Daddadan lafazi na bishara ne da alheri, kuma yana cikin kyakkyawan fata, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Ba rabuwar cuta ko camfi kuma kyakkyawan fata na burge ni sai suka ce : menen kyakkyawan fata ? sai yace daddadar kalma).Bukhari da muslim ne ya rawaito.
Sannan ku sani lallai Allah ya yi muku umarni da salati da aminci bisa ga Annabinsa

الجمعة، 11 يناير 2019

ka yi kwadayin abin da zai amfane ka


Hudubar Masallacin Annabi na sheikh AbdulBari Assubaiti 5/5/1440 AH /11/1/2019
Hudubar Farko
Nasara a rayuwa abin nema ne ga kowane mutum,manufarsa da muradinsa samun walwala da sa'ida,rayuka da zukata na karkata zuwa gare su,hakika Annabi ya zayyana mana abubuwa uku na samun nasara da walwala a rayuwar duniya da lahira, a hadisi mai yawan fa'idoji da girman amfani,a fadinsa (ka yi kwadayin abin da zai amfane ka ka nemi taimakon Allah kar ka gajiya).
(ka yi kwadayin abin da zai amfane ka); ka yi kokarin samun manyan manufofi masu ma'ana da kyawawan dabi'u madaukaka,da ibadoji mafi daraja,ka sanya wa rayuwarka manufa,kar ka tafiyar da shekarunka kara zube ba tare da tabbatar da  wata babbar gaya da kake so ka cinma ba, (shin wanda ke tafiya a kife a kan fiskarsa ya fi zama a kan shiryuwa ko kuwa wanda ya ke tafiya mike a kan hanya madaidaiciya) ?
(ka yi kwadayin abin da zai amfane ka) :sabo da rayuwar gajeruwa ce, bayan samarta sai tsufa, ga lafiya na samun barazana daga cututtuka, Ibnu Mas'ud Allah kara yarda a gare shi ya ce : (Ba abin da nayi nadama a kansa kamar ace rana ta fadi ajali na ya ragu, aiki na bai karu ba a cikin shi,)
(A ranar nan mutum zai yi tunani, to ina fa tunanin yake a gare shi! Yana dinga cewa kaito na ina ma da na gabatar (da aikin kwarai) domin rayuwa ta).
Wanda ya yi kwadayin abin da zai amfane shi zai shagalta ne da abin da zai kawo riba a gare shi, da ganima mai tsada   da ayyuka da suka fi yawan lada kuma suka fi soyuwa ga Allah,  don haka ne ma sahabbai suke tambayan Annabi  mafi darajan ayyuka da daukaka  wani mutum ya ce :'' ya Manzon Allah menene musulunci ? sai Manzon Allah ya ce :- '' (Zuciyan ka ya mika wuya ga Allah  mabuwayi da daukaka  kuma Musulmai su kubuta daga harshen ka da hanunka) sai ya ce :-    a musulunci wani abu ne ya fi ? sai ya ce ''imani  sai ya ce : ; to meye imani ?   sai ya ce ka yi imani da Allah da mala'ikunsa da littatafansa da manzanninsa , da  tadawa  bayan mutuwa'' sai ya ce wani imani ne ya fi ?  sai ya ce '' hijira'' sai ya ce to menene hijira ?  sai ya ce ka kauracewa mummuna )
Na daga ciki fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi : (sallar jam'i ta fi sallar daidaiku da daraja (27) ashirin da bakwai)
Da fadinsa :(Dirhami guda ya riga dirhami dubu dari ).
wanda ya  yi kwadayin abin da zai amfane shi to zai kirdadi abin da gurbinsa zai wanzu,falalarsa ya dauwama a duniya, ya zarce zuwa rabauta a lahira, Allah Madaukakin sarki ya ce :(kuma a cikin su akwai mai cewa: ya Ubangijinmu ka bamu mai kyau a cikin duniya da mai kyau a lahira,kuma ka tsare mu daga azabar wuta. Wadannan suna da rabo daga abin da suka sana'anta, kuma Allah mai gaggawan sakamako da yawa ne.)
  Abin da ake nufi da kyakkyawa biyu shi ne ; ni'imar duniya da na lahira  musulmi mai lura  wanda ke kwadayin abin da zai amfane shi  zai fara ne da kan shi ya gyarata  , hakanan kuma zai wadatu  ga dukkan abin da bai shafe shi ba   Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :-  (yana daga cikin kyautatuwan musuluncin mutum  yabar abin da bai shafe shi ba ,.)
Duk wanda   ya bar abin da bai shafe shi ba ya shagalta da abin da ya shafe shi  to musuluncin shi zai kyautata  ,  ya kebanta don abubuwan da suka fi muhimmanci , ya kuma daukaka da ayukan shi   ya tsarkake ran shi da  da dabi'un shi da harshen shi  ya zama mai kula da rayin shi   , kuma  ya zama mai gadin halayen shi yana mu'amala da kan shi da gaskiya da adalci .
Shu'aibu Amincin Allah ya tabbata a gare shi ya ce  da mutanen shi :-( kuma ba ni nufin in saba muku zuwa ga abin da nake  hana ku daga gare shi  , ba ni nufin kome face gyara gwargwadon   da na sami dama  . kuma  muwafakata ba ta zama ba face ga Allah a gare shi na dogara kuma zuwa gare shi nake komawa da rusunawa).
Kwadayin abin da zai amafanar yana sa a fiskantar da karfi zuwa ga gini da habaka kasa  yana haifar da albarka a rayuwa  ya sanya aiki ya zauna da gindin shi ya kafu  Allah madaukakin sarki  ya ce :- ( Amma abin da ke amfanan mutane zai zauna a cikin kasa ).
 Kwadayin abin da zai amfanar yana bukatar a samu karfi  na  mu'amala  tare da  ababan jin dadi tare da bukatun rayi, don ba kowane abu da ake sha'awa ne mai amfani ba, kuma ba kowane abin ki ba ne mai cutarwa ba, sai da shi mutum mai hankali zai fifita amfani mai girma mai yawa akan amfani na yanzu dan kankani,Allah Madaukakin sarki yace :
(Aa ha ba haka ba kuna son mai gaggawar nan (Duniya) ne.kuna barin ta karshen(Lahira).
Kuma ya ce: (Akwai fatar cewa ku ki wani abu alhali shine mafi alheri a gare ku, kuma akwai fatar cewa kuna son wani abu alhali kuwa shine mafi sharri a gare ku, kuma Allah ne yake sani kuma ku ba ku sani ba.)
Abokantaka da wanda zai amfanar na daga cikin abubuwa na tilas a kwadayin abin da zai amfanar, domin dukkan aboki na koyi ne da aboki.akwai bambanci nesa ba kusa ba abota da kasalalle da mai basira da hangen nesa. Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : (Mutum na kan addinin abokinsa ne, to dayanku ya dubi wanda zai yi abota da shi,)
Annabi Muhammadu () yana cewa: - “Misalin aboki nagari da abokin banza, kamar misalin mai daukar turare ne da mai hura zuga-zugi, mai daukar turare ko dai ya shafa maka ko ka sayi turare a wurinsa ko kuma ka ji kamshi mai dadi a wurinsa, mai hura zuga- zugi kuma ko ya kona maka kaya ko ka ji wari a wurinsa” Bukhari ne ya rawaito
Idan abubuwan amfani suka taru ga musulmi to sai ya gaggauta zuwa ga aiki, don kowa an saukake mishi aikin da aka halicce shi dominsa,to abin da aka shar'anta ga ko wane mutum ya aikata abin da ya ke da ikon yi na daga alheri,kamar yadda Allah Madaukakin sarki yace :(ku ji tsoron Allah gwargwadon abin da ku ka sami iko)
Hakika ta kan iya kasancewa abin da bai fi falalan ba ka ke da iko akai fiye da abin da ya fi falala, kuma ka samu lada ta gun shi fiye da wanda ya fi falala, to abin da ya fi ga musulmi ya nemi abin da yafi amfani a gare shi, to a shaninsa wannan shi ya fi, ba wai zai nemi abin da ya fi fifikon falala na gabadaya ba,Idan mutum na da uzuri ko zai wuyata a gare shi yin abin da ya fi falala, to lalle Allah ya raba ayyuka kamar yadda ya raba arziki,
Duk yadda mutum ya kai da kwadayin ya samu abin da zai amfane shi to ba zai iya cinma manufarsa ba da burinsa ba face idan Allah ya taimake shi ya datar da shi ya yi mishi muwafaka (ka yi kwadayin abin da zai amfane ka ka nemi taimakon Allah) shine wanda tsarki ya tabbata a gare shi kuma ake neman taimako daga gare shi, wanda dukkan halittu ke neman mafaka a gare shi,bisa zabi ko larura,kowa na neman taimakonsa a halin tsanani ko sauki,da halin yelwa ko cuta, a ko yaushe mutum na cikin bukatan taimakon Allah, a dukkan halin da ya ke ciki,a dukkan al'amuran addininsa da na duniyarsa,to neman taimakon Allah da rokon shi agaji bisa yardarsa na daga cikin adua mafi amfani, kuma shine abin da harshen muminai ya fi nanatawa da karfafawa, raka'a bata cika a sallah muddin ba a ambace ta ba.(kai kadai muke bautawa kuma kai kade muke neman taimako)  
Manzon Allah  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : (Ina ma wasiyya ya kai Mu'az kar ka bar fadin wannan adu'a karshen kowace sallah,: (Allahumma a'inni ala zikrika wa shukrika wa husni ibadatika)ya Allah ka taimake ni bisa ambatonka da gode maka da kyautata bauta maka).
Al'istianatu Billah: shine bawa ya tabbatar kuma ya gamsu da raunin karfinsa da dabararsa, kuma karfi da dabara na Allah ne shi kadai Albarka da daukaka su tabbata a gare shi,sabo da bawa na da gazawa na cin gashin kan shi wurin janyo wa kan shi amfani ko tunkude wa kansa cutarwa. Ba mai taimaka mishi a maslaharsa ta duniya da lahira face Allah shi kadai, duk wanda Allah ya taimakawa to shine ya samu taimako,duk wanda Allah ya tabar da shi shine tababbe.to wannan shine tabbatar da Lahaula wala kuwwata illa billah  
(Kada ka gaza) sako ne na himmatuwa da tasowa a shiga fagen aiki, da bigire na kokari da kyauta da jajarcewa wajen tinkaran wahalhalu da fiskantar kalu bale, don raya kasa, Allah Madaukakin sarki yace : (shine ya kaga halittar ku daga kasa kuma ya sanya ku masu raya ta da zama a cikinta).

Huduba ta biyu
(Kada ka gaza) don mai gaza wa ya kayyade kansa da wani abu na kashe jiki,da dabaibaye tafiyarsa da wahami na  kasala, ya mika tunaninsa ga saka burace –burace, gazawa na bude aikin shaidan, kuma mabudi ne na dukkan sharri da fadinsa ina ma da kaza da kaza da na yi kaza, yana bijiro mishi da bakinciki da bacin rai,da tsoro da rowa, da taruwan bashi da finkarfin mazaje sabo da haka ne yana daga cikin aduar Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi:(Allahumma inni auzu bika minal hammi wal huzun, wa'ajzi walkasal walbukhli waljubn wadala'iddain wa galabatir rijal)      
Ya Allah ina neman tsarin ka daga bakinciki da bacin rai da gazawa da kasala da rowa da tsoro da yawan bashi, da galaba namazaje.
Wanda ya zauna tare da masu gazawa, to bashi da wata kima a cikin al'uma, kuma bai da tasiri a kasa, bai da matsayi a cikinAl'uma,wanda ya yi zaman kashe wando da rashin aikin yi, to ya fita daga insaniya (DanAdamtaka), Duk wanda ya saba da kasala ya karkata  zuwa hutu to kuwa zai rasa hutu, wannan hadisi ne maigirma ya tatttaro a dunkule dukkan hanyoyi na yin nasara, duk wanda yayi kwadayin abubuwa masu amfani to ya yi kokari acikinta ya bi sabubanta, ya nemi taimakon Ubangijinsa wurin samunta da cikan ta to hakan shi ne kamalarsa da dacen sa, to a duk lokacin daya daga cikin wadannan abubuwa uku suka tsere masa to alheri zai tsere masa dai dai gwargwadonta,
(ka yi kwadayin abin da zai amfane ka ka nemi taimakon Allah kar ka gajiya).