الجمعة، 20 أبريل 2018

sha'aban wata ne na kimtsawa don ramadan


Hudubar juma'a  na Masallacin Annabi tare da sheikh Abdullah Bin Abdurrahman Albu'aijan 4-8-1439AH
Hudubar farko
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, wanda ya sanya jinjirin – wata  lokuta ne ga mutane da kuma sanin kidayan  zamani, shekaru da watanni , ya sanya dare da wuni  mayau ga wanda ya ke  nufin ya wa'azantu ko ya ke nufin  godiyar    ni'imar  Ubangiji  , na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya , ya sanya rana ya zama mai tsananin haske da wata kuma mai haske   na shaida Annabi Muhammadu bawan sa ne kuma Manzon sa ne  , ya turo shi da shiriya da addini na gaskiya , yana mai albishir da gargadi kuma mai kira  zuwa ga Allah da izinin shi da fitila mai haskakawa, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabban shi da aminci tabbatacce mai yawa .
            Bayan haka :
 Lallai zance mafi gaskiya shi ne littafin Allah , mafi kyan koyarwa shi ne koyarwar Annabi  mafi sharrin al'amura shi ne fararrun ta , kuma dukkan fararrun abu bidi'a ne  kuma dukkan bidi'a bata ne  kuma dukkan bata na wuta .
        Bayin Allah :
Ina muku wasiyya da ni kai na da tsoron Allah  mabuwayi da daukaka, domin ita ce wasiyyar mutanen farko  da na karshe  ( Hakika mun yi wasiyya ga wadan da aka bawa littafi  kafin ku da ma ku kanku da ku ji tsoron Allah ).
YA JAMA'AR MUSULMI:
Lallai  Allah na da  wasu yanki na  rahama  to ,  ku yi kokari ku same su  da wasu zamuna na alheri  to ku yi kokari ku same su  da kuma lokuta masu falala ku yi kwadayin riskan su, ga su sun  fiskanto  ku,  to ku fiskance su  ga su sun sauka gare ku to ku ribace su  domin su dinnan wasu lokuta ne kadan  da za su zo su wuce kamar kyabtawan ido,  kaito ga sarayar da rayuwa ga mutumin da  ya sarayar da ita, madalla  kuma da  wanda ya ribace ta  ya yi nasara da ita (Shi ne wanda ya sanya dare da rana mayau ga wanda  yake nufin  ya wa'azantu ko yake nufin godiyar ni'imar Ubangiji ).
                     Rajabu ya shude  to me  ka kaddamar a cikin shi  *** Ga kuma watan   sha'abanu mai albrka   
Ya kaiton wanda ya sarayar da lokuta bisa jahilci *** da alfarmar ta  ka farka  ka kuma kiyaye  albarkoki 
To da sannu  za ka rabu da jin dadi  cikin karfi *** mutuwa kuma  zai sanya ka a kana ki   ka bar gidan ka
Ka yi kokari  ka tuba daga kusakurai ***tuba irin na mai iklasi kuma ka sanya  abun riska
Bisa neman kubuta daga wutar jahima *** mafi alkairi ga ma'abota laifuka shi ne wanda ya yi kokari ya gyara.
YA KU BAYIN ALLAH
Hakika watan sha'abana ya sauka a gare ku, kuma yana cikin lokuta na da'a  da kuma lokuta masu falala,  ana neman alheri a cikin shi  ana daga ayyuka a cikin shi  da ayuka na kusanci , an karbo da Usama Dan Zaid Allah ya kara yarda a gare su da baban shi  ya ce : '' na ce ya  Manzon Allah  ban gan ka kana azumtar wani  wata daga cikin watanni ba kamar yanda  kake azumtar sha'aban''. Sai Manzon Allah ya ce  (Wannan wata ne da mutane ke gafala daga gare shi,  wanda ke tsakanin rajab da ramadana  shi ne watan da ake daga ayyuka a cikin shi  zuwa ga Ubangijin talikai , ina so  kuma a daga ayyuka na  ina mai azumi , an karbo daga Aisha Allah ya kara yarda a gare ta  ce : Manzon Allah ya kasance yana azumi har mu ce ba zai sha ruwa ba , kuma yana shan ruwa har mu ce ba zai yi azumi ba  ban ga Annabi ya cika azumin wani wata ba  sai ramadana  ban ganshi kuma yana yawaita azumi ba kamar yanda yake yawaitawa a sha'aban .
YA KU BAYIN ALLAH
Lalle watan sha'aban fage ne na kimtsawa da shiryawa don fiskantar ramadan, to shi rai na bukatar maimaci da a bi da shi mataki bayan mataki, da shimfida har ya saba da shi, haurawa zuwa sama na bukatar matakala da tsani, rayi kan kwace, jiki kan gaji  kuma mutum ya kosa daga ibada   sabo da ba abi da shi mataki -mataki ba sai ya rasa jin dadin ta  kuma ya rinka haduwa da tsananin ta , ta iya yiwuwa ma ya yanke daga  gare ta  ya kasa cigaba da ita  sai alheri mai yawa ya tsere mishi .
               Ya yin da sha'aban ya kasance  mukaddima  ne ga  ramadan  to ya dace ga musulmi ya dage a cikin ta  irin kokarin da zai yi a ramadan , matsayin azumin sha'abana ga ramadan kamar matsayin sunnonin farilla ne  ga  sallan farilla , azumtar shi na daga cikin shiri ne da kwadayi bisa ga  ramadana daya daga cikin rukunnan musulunci   kuma azumi  na  daga cikin ibadoji  da ake  neman kusanci da shi  da kuma  da'a  da ibada mafi girma,  an karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : '' Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: ''Allah madaukakin sarki ya ce : ( Dukkan aikin dan adam na shi ne sai azumi  lallai shi nawa ne kuma ni zan sakanya game da shi ).
          (Kuma azumi garkuwa ne  idan dayan ku na azumi  kada ya yi fasikanci   kada ya yi batsa  kada ya yi hayaniya   in wani ya zage shi  ko ya yi fada da shi ya ce ni mutum ne mai azumi .( Na  rantse da wanda ran muhammadu ke hanunsa   warin bakin mai azumi ya fi kamshi a wurin Allah a kan turaren almiski),  ( mai azumi na da farin ciki biyu ; farin ciki yayin shan ruwarsa da kuma  farin ciki yayin  haduwa da Ubangijinsa) .
   YA JAMA'AR  MUSULMI:
Kofofin alheri a bude suke, kuma Allah baya sarayar da ladan wanda ya kyautata aiki  ,ga aiyuka na da'a da suke saki waiwai  ba a kayyade su da zamani ko wuri ba,  nau'ukan ayyukan da'a   suna da yawa  kuma suna fin junan su  gwargwadon lokaci  sai dai  ba wasu ibadoji na da'a da aka kebance  su da watan  sha'aban  sai dai wata ne da ake daukaka ayukan shekara a cikin ta  kamar yanda ake daukaka ayukan mako     a litinin da alhamis  ya dace mutum ya yi kwadayin  ya cika ta , sabo da haka ne Manzon Allah yake  son  azumtar shi , kamar yanda ya ke son azumtar litinin da alhamis .
    Ya jama'ar Musulmi :
Lallai gafala wata cuta ce mai wuyan magani  kuma  abu ne na laifi wanda yake mai zunubi  yana  yanke sila tsakanin bawa da Ubangijin shi ba zai rinka jin wani laifin shi  ba   ko ya yanke daga  alhakin shi ba ,  ba zai tuba daga zunubin shi  ba  ba zai yi wani ma'arufi ba ko ya yi hani ga wani munkari ba   lokutan alheri na ta wuce shi da lokutan falala  alhali yana cikin bacci na gafala  baya farkawa  yana gani baya lura ana mishi wa'azi baya wa'azantuwa ana fadakar da shi baya fadakuwa  hakika Manzon Allah ya kwadaitar game da  azumin sha'aban sabo da gafalan da yawa daga cikin mutane game da shi  sai ya ce  : (  Wancan wani wata ne da mutane suke gafala game da shi  yana tsakanin rajab da ramadana ).
         Ya mai yiwa kan shi nasiha ka gajarta buri  kuma ka farka daga gafalan ka  ka yi shiri don hisabi  kafin zuwan ajali .
      Ina neman tsarin Allah daga shaidan  abin jefewa 
(Ka tsare kanka tare da wadan da suke bautawa Ubangijin su  safiya da maraice suna nufin  fuskan Allah da ibada  ta su  kada ka juyar da idanunka da barin abokantaka ta su , kana nufin kawar duniya   kada ka bi wadan da muka rafkanar da zuciyar sa da barin ambatonmu  ya bi son zuciyar sa  a cikin shirka  al'amarin sa ya kasance faifayi )
Allah ya sa mini albarka ni da ku  a cikin alku'ani
HUDUBA TA BIYU
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah , yabon da ya dace da daukakar sa  tsira da amincin Allah su tabbata  bisa ga  zababbe cikin Manzannin sa da Annabawan sa  da iyalan sa da sahabban sa  da mabiyan sa da masoyan sa   .
YA KU BAYIN ALLAH :
 Lallai Allah  bai halicci mutum ba  ya kara mishi a tsawon rayuwa face don ya yi kokari wajen yi mishi da'a kuma ya nesanci saba mishi Allah madaukakin sarki ya ce :(Ban halicci mutum da aljani ba sai don su bauta mini)  Hakika Allah ya fifita wasu sashi na lokuta ya kwaranya musu sauki  da albarkatu da alheri mai busowa, ya shar'anta wasu hukunce-hukunce da ayyuka da kuma da'a, kuma ya yi wa bayin sa izini da su nemi  alheri a cikinta, to ku nemi alheri a dukkan zamaninku,kuma ku kutsa don karbar rahamar Allah, lalle Allah Mabuwayi da daukaka,na da wani yanki na rahamarsa da ke samun wanda ya so da ita daga cikin bayinsa.
Ya Al'uma masu kadaita Allah!
Ku kiyaye akidarku   ku rike ta da  hakwaran cin tuwo   domin ita ce tushen tsiran ku,  ku yi riko da addinin ku da littafin ku da shiryarwan Annabin ku
 YA JAMA'AR MUSULMI :
 Lallai Shaidan makiyi ne a gare ku to,  ku rike shi makiyi  domin shi dinnan yana iya kokarin shi a lokutan alheri da falala don ya batar da mutane daga shiriya ya yi shamaki tsakanin su da yanki na rahama da gafara ya katange su daga da'an Ubangijin su kuma ya sanya alheri mai yawa ya tsere musu  , sai ya batar da wasu sashi na daga  mutane ta hanyar shubuhohi  kamar yanda yake batar da wasu sashi na su ta hanyar   sha'awe –sha'awe  , sai ya fitini wasu mutane ta hanyar bidi'o'i da fararrun abubuwa   ya sarayar musu  da dama na lokutan alheri  ta hanyar bidi'o'i da sha'awe-sha'awe.
 TO YA JAMA'AR MUSULMAI :
(Hakika kuna da abin koyi mai kyau daga Manzon Allah   ga wanda ya kasance yana fatan Allah da ranar lahira )
(kuma duk wanda ya yi wani aiki wanda ba umarnin mu a ciki to an maida mishi )
To ku yi riko da sunna to fa dukkan fararren abu bidi'a ne dukkan bidi'a bata ne kuma   dukkan bata na wuta.
YA KU BAYIN ALLAH :
Duk wanda yake da ramuwa na ramadana a kansa to ya gaggauta azumtar shi  kafin shigowar ramadana  domin lokacin ya matse,  to, wajibi ne ga dukkan musulmi ya gaggauta biya  , ku yi tsere wurin ayukan alheri  ku gaggauta wurin da'a ku yi gaggawa zuwa ga gafara daga Ubangijin ku  da aljanna fadint ya kai kasa da sammai .
                YA KU BAYIN ALLAH
Hakika lallai Allah ya saukar a gare ku mafi daraja cikin littatafai ya kuma aiko muku da mafi daraja cikin manzanni ya cika muku addini kuma ya yarda da shi a gare ku  ya bayyana shi akan dukkan addinai , ya cika ni'ima  sai ya ce :  (A yau na cika muku addininku kuma na cika muku ni'imata a gare ku , na yarda a gare da musulunci a matsayin  addini)
 Hakika mun yarda da Allah shi ne Ubangiji da musulunci shi ne addini  kuma Muhammadu shi ne Annabi kuma Manzo ,
 muna rokon Allah da ya tabbatar da mu da tabbataccen zance  a rayuwan duniya  da kuma lahira , kuma ya  nisantar da fitina daga gare mu na bayyane da na boye ,  kuma ya azurta mu da riko da sunna  kuma ya tunkude mana gafala da tabewa kuma ya datar da mu  a sha'abana kuma ya riskar da mu da ramadana.
 ya  Allah ka daukaka musulunci ga musulmai  

       
      


الجمعة، 6 أبريل 2018

NI'IMAR ALJANNA


Hudubar juma'a na Masallacin Annabi  tare da sheikh Salah bin Muhammad Albudair 20-7-1439 AH.
Hudubar farko:
Ya ku Musulmai ! Ajali na kusantowa, Burace –burace na karewa, duk wani tsani ya yanke, lokacin tafiya da kaura ya zo, ya raba mutum da iyalai da sadawa da su,
Ba na ganin akwai abin da zai sha gaqban mutuwa ya tsallake ta, *
                                                                              Mutuwa ta katse jin dadi ga mawadaci da talaka.
Ka yi dubi ga duniya da idon mai ban kwana, *
                                                                      Domin hakika tafiyar ta kusa lokacin ban kwana ya yi.
Lallai Masoyi abin fizgewa ne daga masoyansa, *
                                                                                          Mai gadi ko mai tsaro bai hana  mutuwa.
Ta yaya zai yi farin ciki da duniya da jin dadin cikinta?*
                                                            mutumin da ana kidanya masa lafuzansa da numfashinsa.
Dukkan wata gida –wata rana-abar rushewa ce *
                                                         Komin dadewarta bisa ginshikinta.

Ya ku musulmai!
Yayin da duniya ta kasance gida ce ta fitintinu da jarabawa to mutum zai dandani wahalar neman abin rayuwa ,da gwagwarmaya da bala'i da cututtuka da nau'uka na musibu, da cin karo da abubuwa masu hanun riga, da kawatarwa irin na shaidan, da ma'abota barna.
Mai kyauta da karamci Mai jinkai,Mai girma ya yi kira ga bayinsa muminai zuwa ga Aljannarsa  gidan karamcinsa  gidan aminci da ni'ima, kubutacciya daga bakin ciki da bacin rai, wanda babu matsaltsalu da tashin hankali da bala'I,(kuma Allah na kira zuwa gidan aminci)
Idan duniya ta ma kunci gabadayanta *** ka zama baka da wani masauki sananne.
To ka yi gaggauto zuwa ga Jannatu Adnin  domin ita dinnan *** Masaukan mu ne na farko kuma cikinta akwai shemomi
sai dai fursunonin yaki ne na Magauda (Makiya) abin mamaki ya jama'a *** shin ko za mu koma gidajenmu mu samu aminci?
Gida ce da ni'imarta bai karewa , bai  halakewa,gidan da akwai dukkan alheri cikinta har da kari, an tanade ta an kusanto da ita an kawata ta domin karramawa ga masu tsoron Allah, ba su jin tsoron wani abu a ciki na bakin ciki ko hayaniya da gajiya,ba su tsoron talauci ko bashi a cikinta,ko fitarwa ko katsewa ko karewa ba. (Ba zaa fitar da su daga cikinta ba).
Duk wanda ya shiga Aljanna ba zai samu wata damuwa ba, tufafinsa ba zai ridddige ya tsufa ba,haka samartansa ba zai tsufa ba, mai yekuwa zai kira su : (lalle za ku samu  lafiya a cikinta ba za ku yi rashin lafiya ba har abada, kuma ku rayu ba za ku mutu ba har abada, kuma ku zama matasa ba za ku tsufa ba har abada, lalle kuma za ku samu ni'ima ba za ku samu wata damuwa ba har abada, sai a ce : Ya ku 'yan Aljanna ku dawwama ba mutuwa har abada, ya ku 'yan wuta ! ku dawwama ba mutuwa,  a cikin Aljanna akwai abin da ido bai taba gani ba, kunne bai taba ji ba,zuciyar dan Adam bai taba hararo shi ba,).
(Mala'iku na shiga musu ta kowace kofa, Amincin Allah ya tabbata a gare ku sabo da hakurin da ku ka yi, madalla da gida mai kyakkyawan karshe).
Allah Mai girma!! Mala'iku na shigo musu,!! Mala'iku su zo musu,Mala'iku  su gaishe su, Mala'iku na taya su murna!!
(To amincin Allah ya tabbata a gare ku, kun ji dadi, ku shige ta kuna masu dawwama.)
Abin mamaki da girman wannan kusancin da girmamawa a gidan aminci.
Lalle Allah Madaukakin sarki zai ce ga 'yan Aljanna,  :( ya ku 'yan Aljanna ! sai su ce : Mun amsa kirarka kuma mun rusuna, sai yace : ko kun gamsu? Sai su ce :  ta yaya ba za mu gamsu ba bayan ka bamu abin da baka baiwa wani ba daga cikin halittunka,sai yace : zan baku abin da ya fi haka.sai su ce Ya Ubangiji me ne ne ya fi hakan?, Sai yace : zan sanya yarda ta a gare ku bayan haka ba zan yi fushi da ku ba har abada).
(Kuma yardar Allah ya fi girma)
Ya fi girma bisa Aljannar da koramanta ya fi girma akan benayenta da tufafinta da guzurinta.
Amma ganin Allah a Aljanna shi ne abin da masu jan damara su ke jan damara akan shi, masu yin munafasa da rige –rige ke tsere a kan shi, ya hana shi ga wadanda aka musu shamaki da Ubangijinsu, kuma aka kore su daga kofarsa, Allah Madaukakin sarki ya ce :(Wasu fiskoki a wannan rana suna mani'imta ne. masu dubi zuwa  ga Ubangijinsu) Al  kiyama 21-22
An karbo daga Abu Musa Allah kara yarda a gare shi yace : Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : Gonakai guda biyu na azurfa kwanukansu da abin da ke cikin su,da gonakai biyu na zinari  kwanukansu da abin da ke cikinsu, ba wani abu da yake tsanin mutanen da su ga Ubangijinsu  mai tsarki da daukaka face  rigar girmame –girmame a fiskarsa cikin Aljannar Adni) Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
An karbo daga Suhaibu daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :: Idan 'yan Aljanna sun shiga Aljanna Allah Madaukakin sarki zai ce : Ko kuna son wani abu na kara muku? Sai su ce : Allah ba ka haskaka fusakanmu ba ka shigar da mu Aljanna ba kuma ka tseratar da mu daga wuta? Yace sai ya yaye hijabin  sai su ji dadin da  ba a taba basu wani abu da ya fi soyuwa a gare su ba kamar ganin Ubangijinsu  ba Mabuwayi da Daukaka).Muslim ne ya rawaito.
Ibnul Kayyim Allah ya mishi rahama ya ce :  To wannan kenan in ka tambayi ranar kari daga Mabuwayi  Abin godiya, da ganin fiskarsa tsarkakakka daga misali ko kamanci, kamar yadda kake ganin rana lokacin azahar, da kuma wata a daren sha hudu, kamar yadda aka karbo daga mai gaskiya abin gaskatawa,ta hanyoyi  masu dumbin yawa, hakan na nan cikin sahihai da sunann da musnadai, na daga riwayar Jarir da Suhaibu da Anas da Abu Huraira da Abu Musa da Abu Sa'id , Ka saurari ranar da mai kira zai yi kira ? Ya 'yan Aljanna Ubangijinku  zai nemi ziyartarku,, to ku zo , don ziyartarshi,  sai su ce : mun ji mun bi,sai su taso zuwa ga ziyara suna gaggautowa  har lokacin da suka isa kwarinmai fadi  wanda aka sanya musu magama, suka hadu a can ba wani guda da mai kiran ya bari, Ubangiji Allah sai ya yi umarni da a kafa masa kujerar sarautarsa, sai aka kafa, su kuma aka kafa musu  minbarai na haske, da minbarai na lu'ulu'u, da minbarai na zubarjadi, da minbarai na zinari da minbarai na azurfa, mafi karancin daraja a  cikinsu ya zauna,-  duk da ba wani makaskanci cikinsu- bisa wata turbaya na almiski, kuma basu ganin nan kan kujera sun fi su samu kyauta,
Har zuwa lokacin da kowa ya natsu a mazauninsa hankali ya kwanta, sai mai kira ya yi kira,: ya 'yan Aljanna  lalle kuna da wani alkawari a gurin Allah da yake so ya cika muku! Sai su ce : Mene ne shi? Ase ba an haskaka fisakanmu ba,a ka nauyaya mizaninmu ba, aka shigar da mu Aljanna ba, aka nesatar da mu daga wuta ba? Suna cikin haka sai wani haske ya bayyana  wanda Aljanna ta haskaka da shi, sai suka daga kawunansu, sai ga Aljabbaru (kasaitacce) Girmansa ta kasaita, sunayensa sun tsarkaka, ya fuskanto su daga ta samansu,yace : (ya 'yan Aljanna amincin Allah ya tabbata a gare ku) Ba a amsa wannan gaisuwar da sama da fadin cewa : ya Allah kai ne aminci, daga gun ka aminci ya ke, albarka ta tabbata a gare ka,ya Ma'abocin girma da karamci,sai Ubangiji ya yi tajalli a gare su(Ya bayyana) Albarka da daukaka sun tabbata a gare shi, ya musu dariya yace :  Ya 'yan Aljanna ! sai ya zama farkon abin da zasu ji daga gare shi shine : Ina bayi na da suka yi min biyayya a fake bisa halin ba su ganni ba? To wannan ne ranar kari , sai su yi tarayya a kalma guda: Mun yarda to  ka yarda da mu, sai ya ce ya 'yan Aljanna in da ban yarda da ku ba da ba zan saukar da ku a Aljanna  ta ba. Sai yace : wannan ne ranar kari ku roke ni! Sai duk su yi tarayya a kan kalma guda: ka nuna mana fuskar ka mu yi dubi zuwa gare shi, sai Ubangiji  Allah Madaukakin sarki ya yaye shamaki, Daukaka ya tabbata a gare shi, sai ya yi tajalli a gare su, sai ya lullube su da haskensa, sai su manta da duk wata ni'ima da su ka taba gani, badon Allah ya hukunta ba za su kone ba da sun kone, ba wani da zai rage a wannan majlisar har sai ubangiji ya mar lacca kai tsaye, har ma ya ce ya wane ko kana tuna ranar kaza ka aikata kaza da kaza,? Yana tunatar da shi wasu sashi na ha'ince –ha'incen da ya yi a duniya, sai ya ce ya Ubangiji ba ka yafe mini ba? Sai yace ai da gafara tawa ce ka kai wannan matsayin taka da ka ke kai.
Allah Mai girma! Abin mamaki  da girman irin wannan ni'imar, abin mamaki da irin wannan karramawar, zasu ga Ubangijinsu a Aljanna,  za su ga Allah Ma'abocin girma da kyau da kamala, za su ga abin bautan da sun dade suna bauta masa, suna mishi tasbihi,da halala da kabbarori, suka yi mishi  sujada kuma suka girmama shi.
Wani irin dadi ne da jin dadi, wace irin ni'ima ce, wani irin rayuwa ce wani irin walwala ce,wani irin zabi ne, zasu ga Allah wanda duniya  bata yi dadi ba sai da ambatonsa,lahira ma bata yi dadi ba sai da yafiyarsa, haka ma Aljanna ma bata yi dadi ba sai da kallo zuwa gare shi, wayyo kwadayinmu zuwa gare shi, wayyo shaukinmu zuwa ga gidan ni'ima, wacce a cikinta masu kadaita Ubangiji zasu , zai yi tajalli a gare su ya bayyana, kuma yayi dariya agare su,ya fiskanta zuwa gare su, kuma yana bayyana ga 'yan Aljanna a kowace juma'a, cikin wata turbaya na Alkafur sai su kasance kusa da shi gwargwadon gaggawar su zuwa Juma'a a duniya,ba su kara dubi zuwa ga Ubangijinsu sai hakan ya kara musu karama.
Zaka ga fiskar Ubangiji  madalla da fiska da ke cike da kauna da daukaka.
Ya ku bayin Allah!
Wannan dadin labari ina ga dadin ganin?
Ya Allah muna rokon ka dadin dubi zuwa fiskar ka, da kwadayin haduwa da kai, ba cikin wata cuta ko cutarwa ba, ko wata fitina mai cutarwa ba.
Huduba ta biyu
Ya ku musulmai !
Ku kimtsa kayanku ku gaggauta morar rayuwarku  ku ribaci lokacin ku, to me ke baya ni'ima da jin dadi da kawar rayuwa da walwalarta face mutuwa da kare wa da rididdigewa,
Mutuwa kofa ce kuma dukkan mutane zasu shige ta
Me zan ji bayan wannan kofar me ke cikin gidan?
Gidan Aljanna ne na dawwama  muddin ka yi aiki da abin da zai yardar da Allah
In ka gaarta sai wuta, sune gidaje biyu mutane basu da wasu gidan in ba su ba.
To ka duba wa kanka wanne zaka zaba.     



الجمعة، 23 مارس 2018

KABARI MASAUKIN FARKO NE NA LAHIRA


Hudubar juma'a  na Masllacin Annabi na Shaikh Abdulbari Subaiti 6/7/1439 AH
Hudubar Farko:
Tafiyan Mutum a wannan rayuwa   masaukanta na sabunta , marhalolinta na jujjuyawa , yana rayuwa ne na wasu matakai a cikin mahaifiyar sa  sannan da wasu matakai a doron kasa , da wasu matakan kuma a cikin kasa har zuwa a tashe shi.
          Wannan tafiyan tana da tsawo a zahirinta  sai dai tana da saurin gushewa ,  kuma  tana da saurin karewa da tafiya,  to ita duniya ba gidan zama ba ne ga rayayye, mai hankali zai tuna irin jujjuyawa da take da shi  da saurin karewan shekaru,  sai ya ratsa jikin   zuciyan shi ta  tausasa .
           Masaukin da baya  yiwuwa ga ko wani matafiyi sai ya sauka gare shi  wata rana shi ne kabari   , kuma lallai  ya isa abin wa'azi a  gare shi , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya  ce : (Lallai kabari na da wata matsa  wanda da a ce dayan mu zai kubuta daga gareta  da  Sa'ad Dan Ma'azu ya kubuta daga gare ta ).
      An karbo  daga Amirul muminina  Usman Dan Affan  Allah ya kara yarda a gare shi ya kasance idan ya tsaya a wurin kabari  sai ya yi ta kuka har gemun shi ya jika da hawaye , sai a ka ce da shi  kana tuna aljanna da wuta amma ba ka kuka amma in ka tsaya a wurin kabari sai ka yi kuka    , sai ya ce na ji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa  : ( Kabari shi ne farkon masaukan lahira  idan mutum ya tsira daga gare shi to abin da zai biyo baya ya fi sauki  a gare shi, idan kuma bai tsira ba to abin da zai biyo baya ya fi tsanani a gare shi ).
                  Yana daga cikin rukunnan imani da ranar lahira akwai kudurtawa da hakikanin imani da kabari , imani da ni'iman kabari ga ma'abota da'a da kuma   azabar kabari ga  wadan da suka cancanta ma'abota sabo  da fajirci,  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Badon kada ku ki binne mamatan ku ba da na roki Allah ya jiyar da ku daga azabar kabari na daga abin da na ke ji ).
Ziyaran kabari don daukan izina da wa'azantuwa sunna ce kuma kusanci ne, wanda ya ziyarci kabari zai tuna wadannan matattu wadanda kakaninsa ne da iyayensa, sai ya sakankance cewa zai mutu a binne shi kamarsu, kuma zaa tambaye shi a kabarinsa, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :( ku ziyarci makabarta zai tunatar da ku lahira).
                      Idan an binne mutum a kabarin shi  iyalan shi da dukiyan shi suka bada baya farkon maziyartan shi su ne mala'iku guda  biyu su mishi jarabawa,  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (  Lallai idan an sanya mamaci a kabarinsa zai ji sautin takalman su lokacin da suke bada baya   idan ya kasance mumini ne sai salla ta kasance ta kansa azumi ta kasance ta damansa , zakka kuma ta hagunsa,  zai  kasance ayukan  da yake aikatawa na alheri  na daga sadaka da salla da ma'arufi da kyautatawa mutane a ta kafan sa , sai a zo ta kansa sai salla ta ce tanan ba gun shiga zai a je  ta daman sa sai azumi ya ce ta guna ba mashiga  sai a zo ta hagun sa sai zakka ta ce  ba wani mashiga ta guna  sai a zo ta bangaren kafafuwan sa  sai ayukan alkairi   na daga sadaka da  ihsani da kyautatawa mutane  su ce ba mashiga ta guna  sai  a ce da shi zauuna , sai ya zauna  sai a suranta mishi rana tana kusan faduwa  sai a ce da shi ko ka ga wannan  da ke fiskantar ku me za kace  game da shi  me za ka shaida kuma game da shi ? sai ya ce ku barni na yi salla , sai a ce da shi, ai za ka yi amma bamu labarin a bin da muka tambaye ka game da shi ,  ka ga mutumin nan da ke ta fiskar ka me za ka ce game da shi kuma wacce shaida za ka masa? Sai yace : Muhammad, ne, kuma na shaida shi           Manzon Allah ne, kuma yazo da gaskiya daga Allah  ,  sai a ce da shi : akan haka ka rayu, kuma a kan haka ka mutu , kuma a kan haka za a tashe ka in Allah ya yarda , sai a bude mishi kofofi n Aljanna  sai a ce da shi  nan ne masaukin ka a cikinta da abinda Allah ya tattala maka a ciki  sai ya kara jin kaimi da farin ciki  , sa'annan sai a bude mishi kofofin wuta  sai a ce da shi ka ga wannan  shi ne masaukin ka da abin da Allah ya tattala maka a ciki da ka saba mishi , sai ya kara kaimi da farin ciki  sannan sai a buda mishi a kabarin shi   zira'i  saba'in  a haskaka mishi ciki  a maida jikin shi kamar yanda aka fare shi , sai a sanya ruhinsa a cikin wani iska mai dadi  wato wani tsuntsu ne ke shawagi akan itaciyar aljanna  wannan shi ne fadin Allah madaukakin sarki  ( Allah yana tabbatar da   wadan da suka yi imani da magana tabbatacciya  a cikin rayuwar duniya   da cikin lahira kuma Allah yana batar da azzalumai ).      Lallai kafuri  in anzo ta fiskan shi ba za a samu komai ba , in anzo ta daman shi ba za a samu komai ba in anzo ta hagun shi ba za a samu komai ba sai a zo ta kafafuwan shi ba za a samu komai ba  sai a ce da shi zauna sai   ya  zauna  cikin tsoro  da firgici, sai a ce da shi  ba ka  ga wancan mutumin da ya kasance a cikin ku ba me za ka ce game da shi kuma wacce shaida za ka  yi akansa , sai ya ce wani mutumi?  Ba zai ma gane sunan shi ba  sai a ce da shi Muhammad      sai ya ce ban sani ba  na ji dai mutane suna cewa wani magana sai ni ma na fada  kamar yanda suka  ce, sai a ce da shi  a haka ka rayu kuma ahaka ka mutu kuma akan haka za a tada  in sha Allahu, sai a bude mishi kofa daga   cikin kofofin wuta sai a ce da shi wannan ne masaukin ka na daga wuta  da abin da Allah ya tanada maka na daga cikinta ,   sai ya kara bakin ciki da hasara  , sannan a bude mishi kofa daga cikin kofofin Aljanna   ace da shi, wannan masaukin ka ne a cikin ta da abin da Allah ya tattala maka  da ka mishi biyayya,  sai ya kara bakin ciki da hasara  sai kabarin shi  ya kuntata a gare shi  har  kasusuwan hakarkarin shi su shiga junan su.
               Wannan ita ce rayuwa ta kunci wanda Allah ya ambata ( To lallai ne rayuwa mai kunci ta tabbata  a gare shi ,  kuma muna tayar da shi a ranar kiyama yana makaho ) Dabarani ne ya rawaito da Ibn Hibban a sahihin sa .
       Mai hankali  zai shirya ne kafin mutuwa ya kimtsa wa kabarinsa don kansa,  ya raya ta, ta hanyar ayuka na kwarai  da imani  don ya kasance yana da dausayi daga cikin dausayin Aljanna Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Yana daga cikin abin da zai riski mumini   bayan mutuwan na daga aikin shi da kyawawan aikin sa ,    ilimi da ya ilmantar kuma  ya  yada shi   ,  da Da na kwarai da ya barshi , da Alkur'ani da ya gadar da shi ko masallaci da ya gina ,  ko kuma gida da ya gina na 'yan tafarki , ko korama  da ya buda ya gudana , ko sadaka da ya fitar daga dukiyar shi ,  a halin yana mai lafiya yana raye  zai riske shi  bayan mutuwar sa .'
     Wanda ke yawan  tuna mutuwa  zai raya kabarin sa da kyawawan ayuka, domin ya sani bisa yakini , lallai shi ya sani idan ya wayi gari ba zai yi yammaci ba  , idan kuma ya yi yammaci  ba zai jira wayan gari ba  sai ya yi gaggawa zuwa ga ibada kafin a yi shamaki tsakanin shi da ita , ga Amr  dan As  yana ganin mamaci an binne shi sai yayi sauri ya tafi masallaci ya yi salla raka'a biyu, sai aka ce da shi me ya sa ka yi haka ?,  sai ya ce makabarta ta tuna min fadin Allah ( Sai aka yi   shamaki  tsakanin su da abin da suke sha'awa  ).
     Sai na sha'awi salla kafin a yi shamaki tsakani na da ita , wanda yake son aboki a kabari wanda zai debe mishi kewa, ya haskaka mishi kabarin shi  ya tafiyar mishi da kadaici to ya riki Alkur'ani .
     Yana daga cikin sabuba na tsira   daga fitinan kabari da azabar sa, dauwama akan karanta suratul mulk, da aiki da abin da ta hukunta .  An  karbo daga Dan Mas'ud Allah ya yarda da shi ya ce :  (Za a zo wa mutum a cikin kabarinsa sai a zo  ga kafansa sai kafofin sa  su ce :   ba ku da wata dama ko kofa ta fuskar mu ya kasance yana tsayuwa da mu  ya karanta suratul mulk sannan sai a zo ta kirjin sa ko ta cikin sa ,  sai ya ce  ba ku da wata dama ta bangare  na a kan shi ya kasance da ni yake karanta suratul mulk  sannan a zo ta kasan sa sai ya ce  baku da wata kofa  akan shi game da ni ya kasance da ni yake karanta suratul mulk  ,  sai ya ce : ita ce  mai hani, tana hani  daga azaban kabari  tana cikin attaura suratul mulk   wanda ya karanta ta a dare to hakika ya yawaita kuma  tsawaita )  Hakim ne ya rawaito shi a mustadrak ya ce ingantacce ne amma(Bukhari da Muslim) basu fitar da shi ba  Albani  ya  inganta shi  
                 Istigfari ga muminai da musu adu'a zai tabbatar da al'amarin ka a kabari yayin tambaya  , Manzon Allah tsira  da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance in ya binne mamaci  sai ya tsaya gaba gare shi sai ya ce ku nemawa dan uwan ku gafara  kuma ku roka mishi tabbatuwa domin   yanzu za a tambaye shi  , mutanen kwarai na raya  kaburburan su ne ta hanyar lazimtar adu'o'i a ko wace salla, suna  neman tsari  daga fitinan  kabari , Annabi ya kasance yana adu'a Ya Allah ina neman tsarin ka daga azaban kabari da azabar wuta ,  da fitinar rayuwa da ta mutuwa,  da fitinan  masihuddajjal).

      HUDUBA NA BIYU
Musulmi mai hankali yana kiyaye wa daga guraren fitina da halaka,wanda ke lalata al'umarsa kuma ya fitine shi a kabarinsa, na daga ciki akwai yada karerayi da sadar da su, ya zo a hadisin Isra'i da Mi'iraji mai tsawo Jibrilu ya ce da Manzon Allah ( amma shi  mutumin da ka zo mi shi ana keta mukamukin sa  zuwa keyan sa ,  da hancin sa zuwa keyan sa da idanuwan sa  zuwa keyan sa , to lallai mutum ne yana wayan gari daga gidansa sai ya yi karyan da za ta bazu a duniya  ,  yana daga ciki kuma akwai cin riba da halatta shi    ya zo a hadisin isra'i da mi'i raji , amma mutumin da ka zo mi shi  yana iyo a korama yana hadiye duwatsu to  lallai shi maciyin riba  ne )  .
    Yana daga ciki mutumin da yake bacci ya bar sallan farilla da me kauracewa kur'ani , to a cikin hadisin isra'i da mi'iraji ( Amma mutumin da ka zo mishi yana dandaka kansa da dutse shi ne mutumin da yake daukan kur'ani ya yi watsi da shi , ya yi bacci kuma daga sallan farilla).
Yana daga cikin sabuba na azaban kabari yawo a tsakanin mutane da annamimanci da yin sake wurin tsarki , manzon Allah ya wuce wasu kaburbura  guda biyu sai ya ce :( Lallai su dinnan ana azabtar da su ne kuma ba akan wani abu mai girma ba ake azabtar da su, amma dayan su ya kasance ba ya tsarkaka daga fitsari, shi kuma dayan yana yawo da annamimanci).Sahihul Jami'i:  Albani.      
   

السبت، 17 مارس 2018

GARGADI A KAN ZUNUBAI DA SABON ALLAH


Hudubar Juma'a na Masallacin Annabi na shaikh Abdullah Dan Abdurrahman Al-Buaijan 21-6-1439 AH.

HUDUBAR FARKO :
  Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Madaukakin sarki,  muna gode mishi kuma muna neman taimakonsa ,  kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu , da munanan ayyukanmu , duk wanda Allah ya shiryar da shi babu mai batar da shi , duk wan da ya batar kuma babu mai shiryar da shi , na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya , kuma na shaida Annabi Muhammadu bawansa ne kuma Manzonsa ne, Allah ya turo shi don rahama ga  talikai, sai ya buda zukata, ya haskaka hankula da shi, ya buda makantattun idanuwa da shi, da kuraman kunnuwa, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa  da sahabbansa da aminci tabbatacce mai yawa har zuwa ranar sakayya .
Bayan haka :
Lalle da'a ita ce bin Allah sau da kafa  da biyayya ga Manzo, sabo kuma shi ne sabawa Allah da kirkiran bidio'i, mafi sharrin al'amura ita ce bidi'a da fararrun al'amura, da laifuka da abin da aka ki, mafi muninsu shine  sha'awe –sha'awe da shubuhohi.
Ku bi Allah cikin umarninsa , ku hanu game da abin da ya hane ku ya tsawatar,(ya ku wadanda suka yi imani ku bi Allah da takawa, a kan hakkin binsa da takawa, kuma kada ku mutu face kuna musulmai)
Ya ku bayin Allah!
Lalle Allah ya halicci mutum ya ba shi kyautan hankali da harshe,ya bashi sharia ya sanar da shi bayani, ya turo manzanni da hujjoji ya saukar da littafi da mizani, ya kaddara mutuwa da rayuwa, don ya gwada ku ya ga wanda ya fi kyan aiki .
Ya halicci mutum don ya mishi biyayya da zai haifar da yardarsa, ya hane shi ga  saba mishi da zai haifar da fushinsa, (To wanda ya aikata wani aiki gwargwadon nauyin zarra na alheri zai gan shi. kuma wanda aikatagwargwadon nauyin zarra na sharri zai gan shi ).
Ya sanya duniya gida na aiki da jarrabawa, ya rubuta mata karewa, gidan lahira kuma gidan hisabi da sakayya,ya rubuta mata dauwama da wanzuwa,(To wanda ya yi aiki na kwarai don kansa,wanda ya munana don kansa)
Ya tattalawa masu takawa  gidajen Aljanna, koramai na gudana daga karkashinsu,suna madauwama a cikinta har abada. Cikinta akwai abin da ido bai taba gani ba, kunne bai taba ji ba, bai kuma taba fadowa ga zuciyan wani dan 'adam ba, ya tanada, ya tanadawa kafurai wutan jahannama, ba ta ragewa kuma ba ta bari, mai nacewa ga jiki ce da kuna, suna masu zama a cikinta na wasu zamuna, ba su dandanar wani sani sanyi ko abin sha, face tafasasshen ruwa da rubabben jini, sakamako mai dacewa.
Kowani rai mai dandanar mutuwa ne, kuma ana cika muku ladanku ne a ranar Alkiyama, to wanda aka nesantar daga barin wuta kuma aka shigar da shi Aljanna to lalle ne ya tsira, kuma rayuwar duniya bata zama ba face jin dadin rudi.) Ali – Imran 185
Ya ku bayin Allah !
Lalle dan'adam ana jarraba shi da sha'awa da shubuhohi, yana tunkuduwa cikin jin dadi da hutu, ana jarabta shi da zunubai, da munanan laifuka, hakika makiyansa sun yi hayan masa da abokan fadansa, shaidan abokin tafiyansa ne kuma makiyinsa ne, makiyyinsa ne mai tsananin jayayya, ga rai mai yawan umarni da mummuna, kuma tana cikin jiki, ga gabbai masu musu ne kuma shaidu.
Hakika shaidan ya yi rantsuwa  ( sai ya ce :To ina rantsuwa  da buwayarka sai na batar da su gaba daya. Face bayinka tsarkakku daga gare su )Sad 82
Ya kuma bamu labari game da rai sai ya ce :    (Lalle rai mai yawan umarni ne da mummuna)Yusuf  52
Game da gabbai sai yace : ( A ranar da harsunansu zasu yi shaida akansu da hannayensu da kafafuwansu da abin da suka kasance suna aikatawa) Annur :24
(kuma suka cewa fatunsu don me kuka yi shaida akanmu? Suka ce Allah wanda ke sanya ko wani abu yayi furuci shi ne ya sanya mu mu yi furuci kuma shi ne ya halitta ku can da farko kuma zuwa gare shi za ake mayar da ku. Baku kasance kuna sani ba a boye cewa jin ku zai yi shaida a kan ku kuma ganinku zai yi,kuma fatunku zasu yi, kuma amma kun yi zaton Allah bai san abubuwa masu yawa daga abin da ku ke aikatawa ba,)
To shaidan na ingizawa zuwa ga sabo da laifuka masu halakarwa, rayi na umarni da munana da abin da aka ki, gabbai shaidu ne masu tabbatarwa, mai wayo shi ne wanda  ya yi wa kansa hisabi ya mata linzami don kar ya auka ga zunubai.
Ya ku musulmi!
Lalle aikata zunubai  da laifuka akwai cutuwa da kuma barna a ciki da ke haifar da fushin Allah da ukubarsa, da azabarsa, kuma yana janyo  saukar azabarsa da bala'insa. (kuma da yawa daga alkarya wadda ta yi tsaurin kai daga barin umarnin Ubangijinta da Manzanninsa, sai muka yi mata hisabi,hisabi mai tsanani, kuma muka azabtar da ita, azaba abar kyama. Sa'annan ta dandana masifar al'amarinta , kuma karshen al'amarinta ya kasance hasara. Allah ya musu tattalin wata azaba mai tsanani, sabo da haka ku bi Allah da takawa ya ma'abota hankula ).Dalak 8 -9.
To abin da ke faruwa ga musulmai na fitintunu da musibu  masu radadi da jarabawa da tsadan kaya da mulka irin na makiya, da fari da fako,da cututtuka da yunwa da bala'i  ba wani abu ya haifar da shi ba face sabon Allah da laifuka da zunubai, da abin ki.
Hakika Allah ya buga misali ga mai lura ya koro ayoyi ko akwai mai wa'azantuwa, ya bayyana  cewa zunubai da laifuka na daga mafi girman sabuba na gushewar ni'ima da saukar azaba, sai Allah ya ce :(kuma Allah ya buga misali, wata Alkariya ta kasance amintacciya natsatsiya  arzikinta yana je mata a wadace daga kowane wuri,sai ta kafurta da ni'imomin Allah sabo da haka Allah ya dandana mata tufafin yunwa da tsoro, sabo da abin da suka kasance suna sana'antawa, ). Annahl 112
To Abin mamaki ga  walakancin halitta a gun Allah Mabuwayi idan an saba umarninsa.
Ya ku bayin Allah!
Lalle hadarin sabo na girmama kuma ukubanta na kasaita da musibanta  idan aka wayi gari mutane sun saba da ita suna bayyana ta a fili jama'a na fito na fito da Allah, kuma dukkan al'uma na samun kubuta daga sabo banda masu bayyanawa, mutane ba za su halaka ba sai an basu hanzari akansu.
Ya ku bayin Allah!
Lalle bayyana sabo wani nau'i ne na watsi da hakkin Allah da bushewar  ido gare shi, da ja da mumunai da kara yawan masu sabo,da  kuma isar shi gurbin   sabon ne zuwa  ga wani,
Kuma da zamewa sababi na janyo su gare shi da kwadaitar da su, da kuma kasancewa  sababin sanya zunubai ga wanda bai yi inkari ba(hani ba). Duk wanda aka jarabce shi da wasu sabo to ya boye da boyewar da Allah ya mishi, kuma ya tuba zuwa ga Allah tuba na gaskiya.
Ya ku Musulmai!
 Lalle dogewa a kan zunubai  da sake jiki cikin aikin sabo, da dulmuya cikin laifuka da murna da su,da bushewan ido cikinta, da aminta daga makarkashiyar  Allah,da rena laifuka, abu ne da ke shelanta gafala da janyo fushin Allah, kuma sababi ne na tabewa da halaka, An karbo daga  Abdullahi dan Mas'ud Allah kara yarda a gare shi, yace : Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : ku kiyayi rena kananan laifuka, domin su ne ke taruwa  akan mutum har su halaka shi, lalle Annabi ya buga misali game da su yace kamar mutane ne suka sauka jeji sai lokacin dafa abincin su ya yi, sai mutum ya je ya kawo kirya, wani mutum ma ya dauko kirya,har suka hada taru mai yawa, sai suka hura wuta suka dafa abinda suka jefa a  ciki). Ahmad ne.
Musiba na girmama  ga mai laifin idan ya ga kananan zunubai abin renawa an kididdige su,sun habaka ,sai ya firgita ya  ce :(Kaitonmu mene ga wannan littafi ba ya barin karama kuma ba ya barin babba face ya kididdige ta,to kuma suka sami abin da suka aikata halarce, kuma ubangijinka ba ya zaluntar kowa.)
Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya  sun tabbata ga Allah da yake gafarta zunubai, ya suturce aibi, ya yaye bakin- ciki, yana shinfida hannayensa da dare ga masu laifin wuni don su su tuba,kuma yana shimfida hannayensa da rana ga masu laifin dare don su tuba su koma.
Ya ku bayin Allah! Ku ji tsoron Allah kada ku aikata zunubai kada ku rena shaninsu,  ku kankantar da su, ba abin da ya fi a gare ku, ku hadu da Allah da shi kamar karancin laifuka.
Ya jama'ar musulmi!
Lalle hadarin zunubai na kanzaga kuma yana tada hankali,bala'inta da musibanta  na girmama na tsoratarwa, idan ta zama abu sananne mutane suka  tabbatar da ita, baa umarni da kyakkyawa ko hani ga mummuna,  Allah Madaukakin sarki ya ce : An la'ani wadanda suka kafirta daga  banu Isra'ila, akan harshen Dauda da Isa da maryam, wannan kuwa sabo da sabawar da suka yi ne, kuma sun kasance suna ta'adi.sun kasance ba su hana juna daga abin ki, wanda suka aikata,hakika abin da suka kasance suna aikatawa ya munana.)
An karbo daga Abi bakra Allah ya kara yarda a gare shi ya ce ;Manzon Allah tsira da amincin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Lalle mutane idan sun ga munkari basu canja ba to suna kusa da Allah ya game su da azaba daga gare shi.).
Umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna na daga cikin dabia ta al'umar Muhammadu, kuma aminci ne daga saukar bala'i, kuma katanguwa daga  kaidin makiya da wawaye ,Allah Madaukakin sarki ya ce: Ku kasance, Allah ya yi umarni da shi ya kwadaitai a inda ya ce.(A cikinku a samu wata al'uma suna kira zuwa ga Alheri suna umarni da kyakkawa , suna hani da mummu ,  to lalle wadannan sune masu rabauta)
Ya Al'umar Muhammada ku yi umarni da kyakkya wa , ku hana munkari, Duk wanda , ya ga abinki to ya canza shi da hanunsa, idan ba zai iya ba to ya sanja shi da hannunsa,in ba zai iya ba da harshensa, idan bai iya ba da zuciyarsa, idan bai iya ba da zuciyarsa, wannan shine mafi raunin imani)
Ya ku bayin Allah!
Lalle ku din nan abin tambaya  ne  game da gidajenku da abin da aka ba ku kiwo,to ku ji tsoron Allah cikin 'ya'yanku da matayenku, ku sanar da su shariar Allah, kuma ku hana su fadawa ga abin da Allah ya haramta, ku tarbiyantar da su bisa halaye masu kyau da kyakkyawan dabiu, domin lalle zaa tambaye ku game da su gobe gaba ga Allah, kuma zasu zama shaidu akan ku, kuma zaa rubuta shaidar su kuma zaa tambaye su, a ranar da mai laifi zai yi fatan a fanshe shi daga azabar wannan rana da 'ya'yanan sa, da matarsa da dan'uwansa,  da danginsa da suke tattara shi,da wanda ke cikin duniya duka gaba daya sa'annan fansar ta sirar da shi.
Ku kula da abin da aka baku kiwo, kuma  (kada ku yaudari Allah, da Manzonsa, kuma ku yaudari amanoninku, alhali kuwa kuna sane. Kuma ku sani cew abin sani kawai dukiyoyinku da 'ya'yanku wata fitina ce, kuma lalle ne Allah a wurinsa akwai lada mai girma).
Ba wani mutum da Allah zai bashi kiwon wani abin kiwo,  ya zama ya zambace su, face Allah ya haramta Aljanna a gare shi.
Wanda ya yi kokari wurin gyaran mutanen gidansa, ya tsaida shariar Allah  a cikin abin da aka bashi kiwo,ya dasa musu imani a cikin zukatansu, zai kasance yana da lada kwatankwacin aikin da suka yi, ba tare da an tawaye wani abu na daga ladansu ba.
Ya tabbata daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya ce : (Idan dan'adam ya rasu ayyukansa zasu katse sai guda uku daga ciki akwai :Da na kwarai da  ya ke mishi adu'a ).
Ya jama'ar musulmai!
Lalle koyi da yammaci ya fadada, ya kutsa gidaje, da na'urori da hanyoyin sadarwa, sun rusa kyawawan halaye sun bata dabiu na kwarai , an wayi gari abin ki (MUNKARI) a jiya ya zama  shine  abin so (MA"ARUFI), abin da ya ke ma'arufi ne a jiya an wayi gari ana sifanta shi da ci-baya da rashi wayewa da fandarewa.
Abu Mas'ud Al'ansari ya shiga wa Huzaifa sai ya ce : ka mana wasiyya ya Baban Abdullahi, sai Huzaifa ya ce : Ase yakini bai zo ma ba? Sai yace : E ya zo, da buwayar Ubangiji na, sai yace : ka sani Bata hakikanin bata shine ka zama abin da ka ke ganinsa  a jiya mara kyau ya zama abu mai kyau, haka kuma abu da jiya ka ke gani mai kyau  to yau ya zama mara kyau , to na hore ka da juyawa,  addinin Allah daya ne.)           
  To ya ku bayin Allah ku riki sunna, Ina muku gargadi da fararrun abubuwa , domin dukkan fararren abu bidi'a ne, kuma dukkan bidi'a bata ne, kuma dukkan bata na wuta.
Ya Allah ka nuna mana gaskiya gaskiya ce ka bamu ikon bin ta, ka nuna mana karya karya ce ka ba mu ikon guje mata.
Ya Allah ka sanya mana son imani , ka kawata shi a zukatanmu, ka sa mu tsani kafurci da fasikanci da sabo,ka sanya mu cikin shiryayyu.
Ya Allah ka daukaka musulunci da musulmai,ka taimaki bayinka masu kadaita ka,
Allah ka sanya wannan gari cikin aminci da natsuwa, da sauran garuruwan musulmai,
Ya Allah ka kasance tare da masu rauni a garin suriya mai ruwa da itatuwa, ya Allah ka kare jininsu, ka suturce al'aurarsu, ka amintar da su daga tsoro.  Ya Allah ka musanya musu tsoron su da aminci, bayan rauninsu Allah ka basu nasara.
Ya Allah an zalunce su ka taimake su, ya Allah ka taimake su akan wanda ya zalunce su,
Ya Mai karfi  ya Mabuwayi.