الجمعة، 23 فبراير 2018

KUNYA ALHERI NE DUKA


Hudubar Masallacin Annabi  na shaikh AbdulMuhsin Alkasim  7-6-1439AH
HUDUBAR FARKO :
  Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Madaukakin sarki  muna gode mishi kuma muna neman taimakonsa , muna neman gafarar sa  , kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu , da munanan ayyukanmu , duk wanda Allah ya shiryar da shi babu mai batar da shi , duk wan da ya batar kuma babu mai shiryar da shi , na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya , kuma na shaida Annabi Muhammadu bawansa ne kuma Manzonsa ne, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa  da sahabbansa da aminci tabbatacce mai yawa .
Bayan haka

Ku ji tsoron Allah - ya ku bayin Allah – ku yi riko da igiya mai karfi na musulunci .
Mabudin bautawa Allah da sirrin bauta masa na ga sanin sunayen Allah ne da sifofinsa.to sunayensa  Madaukaki duk kyawawa ne, sifofinsa duk Madaukaka ne.  Yana da  wata sifa ta bauta na musamman ga dukkan suna da sifa  tsarki ya tabbata a gare shi , yana daga cikin  abin da ke haifar da shi  da kuma abin da ya kumsa,  Allah yana son sunayensa da sifofinsa kuma  yana son bayyana alamomin su ga halittunsa , sai ya umarci bayinsa da su roke shi da su,  Allah Madaukakin sarki ya ce: (Kuma  Allah yana da sunaye masu kyau , sai ku roke shi da   su ). Kuma mafi soyuwan halitta zuwa ga Allah  shi ne wanda ya siffantu da sifofin da Allah ke kauna ,  wanda ya bautawa Allah da sifofin shi zai kusantu  zuwa ga rahamarsa , wanda ya kiyaye sunayen sa  zai saukar da shi a aljannarsa  daga cikin sunayen Allah   akwai ALHAYIYU wato mai kunya  kuma daga cikin sifofin sa akwai kunya ,  kuma Allah ya siffanta kan shi da ita   sai ya ce : (Lallai ne Allah ba ya jin kunyar ya bayyana wani misali,  kowane iri ne, sauro da  abin da yake  bisa gare shi ) .
  Manzon sa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya ambace shi sai ya ce :( Lallai Allah mabuwayi da daukaka  mai kunya ne , kuma marufin asiri ne  yana son kunya da  suturcewa ) Abu Dauda ne ya rawaito .   Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :( Lallai Ubangijin ku mai girma da daukaka Makunyaci ne, kuma mai karamci ne , yana jin kunyar bawansa  idan ya daga hannayensa biyu zuwa gare shi ya dawo da su haka banza ).Abu Dauda ne ya rawaito shi
             Ibn Alkayyim Allah ya mishi rahama ya ce : '' Kunyan Ubangiji Madaukakin sarki ga bawansa, abu ne da fahimta ba zai riske shi ba , hankali kuma ba zai gano yadda yake ba, domin shi wani kunya ne na karamci  da kyautatawa  da kuma kyauta da daukaka ''.
             Mafi girman kyawawan halaye cikin halittu kuma mafi daukakansu da kuma mafi girma a daraja da kima kuma mafi  yawan amfani; shi ne kunya , wata dabi'a ce  wadda ke sa  abar duk wani munanan dabi'u  kuma yana hana yin sakaci  a cikin hakkin  ma'abocin hakki , tushen sa da asalin  maddarsa daga rayuwa ne ,  kuma bisa iya gorgodon rayuwar zuciya  iya kasancewar kunaya a cikin ta  a duk lokacin da zuciya  ta fi rayuwa , sai kunya ta fi cika a cikinta   da karfi  kunya bata  gushe ba  al'amarin ta tabbatacciya ce , kuma amfani da  ita  wajibi ne tun  zamanin Annabawan  farko ,  kuma ba wani  Annabi face   ya kirayi al'umar sa zuwa gare ta kuma an turo shi da ita  ba a goge ta ba cikin abubuwan da a ka goge na shari'o'insu , kuma  ba a canza ta ba cikin abubuwan da ake canzawa , sabo da wannan al'amari  da ya bayyana karara  na daidai ne  an sanshi  kuma  falalar shi ya bayyana  dukkan hankula sun yi taraiyya bisa ga kyanta , duk wanda wannan ya kasance shi ne sifansa  bai  halatta a goge shi ko a canza shi ba, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Lallai yana daga cikin  abin da mutane suka riska  na maganan Annabawa  shi ne idan baka ji kunya ba ka aikata abin da ka ga dama ) Buhari ne ya rawaito
      Mafificin halittu ya siffantu da ita kuma Allah ya kyautata yabo ga ma'abotanta   to kuma mala'iku ma sun siffantu  da ita  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata  gare shi ya ce game da Usman : ( Ase ba zan ji kunyar mutumin da mala'iku suke jin kunyar sa ba ), Muslim ne ya rawaito  , Annabawa an san su a cikin mutanen su da haka,   halittu za su nemi ceto ranar alkiyama da Adamu da Nuhu Alaihimassalam , sai ko wannen su ya tuna zunuban shi sai ya ji kunya )  Musa amincin Allah ya tabbata a gare shi makunyaci ne , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya ce : ( Lallai Musa  ya kasance  mutum ne makunyaci  mai yawan suturcewa  ba a ganin wani abu na daga fatar jikin shi sabo da irin kunyar sa ), Buhari ne ya rawaito
      Annabinmu Muhammadu  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana da kaso mafi tsoka na daga kunya,  sabo da haka yakan  yi jirwayi da kamar wanka,  baya yin karara,   akan gane  kunyar sa daga fuskarsa,  Abu Sa'id Al khudri ya ce:  '' Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ( Ya kasance   mafi tsananin kunya  fiye da budurwar  da take cikin haudajin ta , kuma ya kasance idan ya tsani wani abu mukan gane a fuskar sa) Buhari da Muslim ne suka rawaito  shi 
       Ya kai ya komo a daren mi'iraji  tsakanin Musa da Ubangijinsa yana rokon a sassauta game da sha'anin sallah har zuwa lokacin da ya ce : " ( Hakika na ji kunyar Ubangiji na ") ,  a yayin da ya shiga da Zainab 'yar Jahash,  an kira mutane   don hakan, sai suka ci abinci suka fita  sai ya rage wasu mutane uku suna ta hira a dakin  sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ji kunyar ya ce  mu su wani abu ,  sai ya fita ya bar su  a dakin, sai Allah Mabuwayi da daukaka ya saukar da : (Ya ku wadanda suka yi imani kada ku shiga gidajen Annabi  face fa idan anyi izini a gare ku zuwa ga wani abinci ,   ba da kun tsaya jiran nunar sa ba , kuma amma idan  an kira ku, to , ku shiga   sa'annan idan kun ci, to ku watse , kuma ba da kun tsaya kuna masu hira da wani labari ba ,  lallai wannan  yana cutar da Annanbi,  to yana jin kunyar ku , alhali kuwa Allah baya jin kunya daga gaskiya) Ahzab 53  Buhari da Muslim ne suka rawaito
            Kuma Usman Allah ya yarda da shi ya zama abin buga  misali a  akunya cikin sahabbai,  watarana  ya shigo ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  sai  Manzon Allah ya zauna ya daidaita tufafin shi   sai aka tambaye shi game da haka sai ya ce : ( Lallai Usman mutum ne makunyaci  na ji tsoron kada na mishi izini a wannan yanayi ya ki isowa zuwa gare ni , cikin bukatar sa ) Muslim ne ya rawaito .
         Mace an halicce ta bisa kunya  , kuma kunya ce adon ta  kuma kariya ne a gare ta da aminci   Aisha Allah ya kara yarda a gare ta ta ce " Ya Manzon Allah  ai ita budurwa tana jin kunya sai ya ce yardan ta –da auren - ai shi ne yin shurun ta  " Buhari ne ya rawaito
      'yar ma'abocin madyana  tazo  kunya na lullube da ita ta suturce fiskanta da hanunnta da kuma tufafin ta Allah madaukakin sarki ya ce : ( Dayan su sai ta zo tana tafiya bisa kunya  sai tace lalle mahaifi na na kiranka don ya saka maka abin da ka yi na shayar da mu)   .Kuma Aisha uwar muminai  Allah ya yarda da ita,  kunya ya kaita da ta suturce kanta  a cikin dakinta sabo da Umar  Allah ya yarda da shi   bayan an binne shi ( a  dakin ta ) Allah ya kara yarda  a gare ta, ta ce: "Na  kasance ina shiga  daki na   wanda aka binne  Manzon Allah a cikinsa da mahaifi na sai na cire tufafi na,  sai na ce ai wannan mijina ne, wannan kuma mahaifina  ne , to amma a lokacin da aka binne Umar tare da su   to wallahi ban shiga dakin ba face sai ina daure da tufafi na  a jiki na sabo da kunyar umar  )Ahmad ne ya rawaito .
          Kuma ga wata mace da ta yi hakuri bisa jarabawa   amma bata yarda da cire rigar kunya  ba , sai sakayyar ta  ya kasance aljanna :  Abdullahi Dan Abbas Allah ya kara yarda a gare su shi da mahaifin shi ya ce ga  Ada Dan Abi Rabah  Allah ya mishi rahama ya ce : " Ase   ba zan nuna maka mata 'yar aljanna ba ? sai na ce e;  sai ya ce : " wannan bakar matar  ta zo ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  sai ta ce : "   Lallai ni  ina da cutar  farfadiya  har nakan  yaye daga tufafi na,  to ka roka min Allah  ya raba ni da ita,  sai ya ce in kin so ki yi hakuri kina da aljanna  in kuma kin so in roka miki Allah ya baki lafiya " sai ta ce : "zan  yi hakuri,  sai dai nakan yi tsiraici , to ka rokamini  Allah kada na rinka yin tsiraici  sai ya roka mata Allah" ) Buhari da Muslim ne suka rawaito
       Kuma tana cikin dabi'u masu daraja wanda har mutanen jahiliyya ma sun wanzu a kan ta, Abu Sufyan Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : " a yayin nan da Hiraklu ya tambaye shi game da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,  kuma a lokacin yana kafurci : (Wallahi ba don kunya ba a wannan ranar kar mutane na su taba kama ni da karya a wannan ranar da na yi mishi karya , a lokacin da ya tambaye ni game da  shi, amma sai dai na ji kunya kar a same ni da karya sai na fada mishi  gaskiya).
      Da kunya ne a ke samun walwala   a riski kuma sabubanta, dukkan  ta alheri ne  , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Kunya alheri ne dukanta  ko kuma ya  ce  kunya  dukkan ta alheri ne )Muslim ne ya rawaito
      Karshen ma'abocinta alheri ne    har abada  kuma ba zai hadu da nadama ba har abada   , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  yana cewa : ( Kunya bata kawo wani abu sai alheri). Muslim ne ya rawaito
      Ibn Kayyim Allah ya mishi rahama ya ce :" kunya wani sinadari ne na rayuwar zuciya kuma ita ce tushen dukkan alheri ,  rasa ta kuma rasa alheri ne gaba dayan shi  )
Yana daga cikin mafi girman alherin da ke cikin ta akwai sabarwa rayi  da kyawawan dabi'u da kuma nisantar munanan dabi'u , idan kunayar mutum ta tsananta sai a kare mutuncin sa kuma sai a binne laifukansa a kuma yada kyawawansa.
          Yana daga cikin  akidar ahlussunna waljama'a ; cewa imani fadi ne  da kudiri da aiki,  kunya wani yanki ne daga gare shi   Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata  a gare shi ya ce:( Imani yanki ne sittin da dori kuma kunya wani yanki ne na imani )    Buhari da Muslim ne suka rawaito shi .
 Ibn Hibban Allah ya mishi rahama ya ce :"kunya  na daga cikin imani kuma mumini na aljanna, ba za a  zare kunya daga wani ba face an zare imanin shi  ".
       Manzon Allah ya wuce wani mutum yana zargin dan uwansa game da  kunya, yana cewa : " Lallai kai kana jin kunya  har kamar yana cewa  da shi  ya kai ma yana cutar da kai , sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :( kyale shi, lallai  kunya na daga cikin imani) . Buhari da muslim ne suka rawaito
      Ba ukubar da Allah zai yi ga zuciya da tafi a kwashe kunya daga gare ta, Ibn Umar Allah ya kara musu yarda  ya ce : " Lallai kunya da imani an hada su tare  idan an dauke dayan su sai a dauke dayan ma "  .
       Kunya da'a ce da ke janyo wasu biyayya  da za su kai  ma'abocinta zuwa ga tsentseni wanda kuma ya barta to zai aikata abin da yake kishiyan haka , Umar Allah  ya kara yarda a gare shi ya ce: " wanda kunyar sa ta karanta to tsentseninsa zai karanta, wanda tsantsenin sa ya karanta zuciyar sa ta mutu.
       Kunya na daga cikin abu mafi girma da ke  shiga tsakanin mutum  da  aikata sabo , makunyaci na  katse ayyukan sabo da kunya kamar yanda imani ke katse sabo,  idan an tube kunya daga bawa to sai ya zama ba abin da  ya rage da zai hana shi aikata munanan abubuwa   da kuma halaye marasa kyau,  sai ya zama kamar bai da imani,  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :( Idan  mutum bai ji kunya ba to ya aikata abin da ya so). Buhari  ne ya rawaito
                  Ibn Abdulbar Allah ya mishi rahama ya ce : " Duk wanda bai da kunyan da zai katange shi daga abin da Allah ya haramta , to daya ne a gare shi aikata aikin karamin zunubi da babba,   a cikin hadisin akwai gargadi da narkon azaba game da karancin  kunya "
 Zunubai na raunana kunya daga bawa har ma ya tafi gaba daya daga gare shi ,  ya zamana ba zai dame shi ba don mutane sun san halin shi ko suka gane abin da ya ke aikatawa , kai hakika ma yakan bada labari bisa halin shi da munanan  ayukan shi .
                 A kunya akwai ado da kawa ga ma'abocinta   Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Batsa baya shiga cikin komai sai ya bata shi kunya kuma baya shiga cikin komai sai ya kawata shi – wato ya adonta shi )  Tirmizi ne ya rawaito shi
                  Kunya na kira zuwa ga izzar rayi da kare ta , ba zai tambayi mutane wani abu ba ko da ya bukaci hakan , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Ba miskini shi ne wanda ya ke kai komo a kan loma daya ko biyu ba, sai dai miskini shi ne wanda ba yi da wadata kuma yana kunya, ko kuma baya tambayan mutane bisa naciya ) Buhari da Muslim ne suka rawaito.
                Kunya kamar wani adireshi ne na kyakkyawan dabi'a da ladabi.  Annabi  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya tambaya : ( Game da itaciyar da take kama da musulmi , sai Ibn Umar Allah ya yarda da su ya ce : ( sai ya fado a zuciya ta cewa bishiyar dabino ne sai na ga Abubakar da Umar ba su yi magana ba, sai   na ji nauyin  na yi magana. a wani lafazin kuma ya ce : " sai na ji kunya ) Buhari da muslim ne suka rawaito .
         Mutum ana sakanya mishi da irin aikin da ya yi,  na daga cikin amfanin kunya da kyakkyawan sakayyan ta Allah na  jin kunyan  ma'abotanta  , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: ( Amma dayan sai ya ji kunya sai Allah ya ji kunyar sa ) Buhari da Muslim ne suka rawaito 
           Tushen kunya kuma shi ne a ji kunyar Allah madaukaki, ta yanda kar ya gan ka  a inda  ya hane ka,  kar ya rasa ka kuma a in da ya umarce ka ,    Allah ne ya fi cancanta da a ji kunyar sa Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: ( Ku ji kunyar Allah cancantar kunyar sa) Tirmizi ne ya rawaito  
    Kunyar  Allah shi ne Allah ya jefa wani haske a zuciya da zai sa ya rinka ganin Allah gaba gare shi lokacin da yake shi kadai ko a cikin jama'a,  jin kunyan Allah  na tabbatuwa ne  ta hanyar tsinkayar baiwar sa da girman ni'imominsa tare da halarto da laifuka na rayi tare da gazawanta , kuma da sanin cewa yana tsinkayan abin da yake na  sirri da wanda ya fi boyuwa: ((Allah) Ya san yaudarar idanu da abin da kiraza ke boyewa) sura Al-Gafir aya 19  Allah madukakin sarki ya ce : (  Suna neman boyewa daga mutane  kuma ba sa neman boyewa daga Allah  alhali kuwa shi yana tare da su ).
 Idan bawa ya san cewa Allah madaukakin sarki yana kallon shi ;  kuma cewa  yana   gaban idon sa ne kuma yana jin sa  kuma  ya kasance mai jin kunya to sai ya ji kunyar kada ya kutsa zuwa ga  abin da zai fusata  shi  tare da mutum akwai mala'ikun  da ba sa rabuwa da shi yana daga cikin karrama su ka ji kunyar su (  Lalle ne a kanku  hakika akwai  matsara . masu daraja marubuta . Suna sanin abin da kuke aikatawa )  .
      Ibnul  Kayyim  Allah ya mishi rahama ya ce : " Ai ku  ji kunyan wadannan matsara din ku karrama su   ku ga kimar su   , ku ji nauyin su ganku  kuna aikata abin da ku ke jin kunyar wasun ku su ga kuna aikatawa ". 
            Jin kunyan mutane yana haifar da mutunci da kyawawan dabi'u  kai ko da ma a ce  mutum musulmi   bai samu wani Abu daga dan uwan shi ba sai kunyar  sa da zai hana shi aikata  sabo to ya isar mishi, wannan wani  alheri ne da zai taimakawa ma'abocin shi bisa jin kunyar Allah , to duk wanda baya kunyar mutane  to baya kunyar Allah , haka kuma duk wanda   ya zauna da ma'abota kunya , kunyar shi za ta sabunta   .
         Wanda ya fi dacewa mutum ya girmama shi ne kansa , duk mutumin da ya aikata wani aiki a sirrace  wanda ake jin kunyar aikata shi a  bayyane to bai kimanta kan sa ba,  wanda ya ji kunyar mutane bai ji kunyar kansa ba  to kansa ta fi walakantuwa a gunshi fiye da wanin shi  wanda ya ji kunyan wani kuma ya ji kunyar kansa bai ji kunyar Allah ba to baisan Ubangijin sa ba,  wanda  kunya ya lullube masa tufafin shi to mutane ba za su ga aibin shi ba.
   Bayan haka ya ku Musulmai   to musulunci addini ne na kyawawan halaye da  kyawawan dabi'u , ya tattaro daga halayya mafi kyansu   da sifofi kuma mafi daukakan su  ba wani alheri face ya yi umarni da shi , ba wani sharri kuma face ya yi gargadi game da shi,  to wajibi ne gare mu muyi riko da shi  kuma muyi alfahari da shi  kuma mu kira  mutane zuwa ga shi , jin kunyar Allah shi ne ta hanyar bin umarninsa  da kuma nisantar saba mishi .
       INA NEMAN TSARIN ALLAH DAGA SHARRIN  SHAIDAN  ABIN  JEFEWA
(Kuma wane ne ya fi  kyau ga addini daga wanda  ya sallama fuskar sa ga Allah alhali kuwa yana mai kyautatawa kuma ya bi akidar Ibrahim yana mai karkata ga gaskiya )
 Allah ya sa mini albarka ni da ku cikin alkur'ani mai girma,  kuma Allah ya amfane ni da ku da abinda yake cikin sa na daga ayoyi da ambato mai hikima , ina fadin wannan magana tawa kuma ina mai neman gafarar  Allah  da ni da ku da dukkan musulmai  daga dukkan zunubai ku nemi  gafarar shi lallai shi mai gafara ne mai jin kai
 HUDUBA TA BIYU 
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah bisa kyautatawan sa  , godiya ta tabbata a gare shi bisa  datarwar sa da baiwarsa na shaida  ba abin bautawa da gaskiya  sai Allah shi kadai yake bashi da  abokin tarayya   muna mai girmama sha 'anin sa,  na shaida Annabinmu Muhammad bawan sa ne kuma mManzon sa ne tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan sa da sahabbansa  da aminci tabbatacce mai yawa ,
 Ya ku Musulmai   :
  Kunyan da yake abin yabawa a maganan Annabi  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ita ce   wannan dabi'ar  da ke sanya mutum ya aikata kyakkyawan abu ya bar mummuna amma rauni da gazawa, Wanda ke sa gajartawa a wani abu na daga hakkokin Allah, ko hakkokin bayinsa,wannan ba su da alaka da kunya a wani abu, in ya hana ma'abocinsa wani alheri to bai zama abin a yaba ba. Aisha Allah ya kara yarda a gare ta ta ce : (Madalla da matayen Ansar kunya bai hana su neman fahimtar addininsu ba) Muslim ne ya rawaito.
Babu kunya cikin neman sanin addini, wanda ya bar ilimi don kunya to zai zauna cikin jahilci har abada ya hana kansa alheri.
Mujahid Allah ya masa rahama ya ce :  ( Mai kunya ko Mai girman kai ba zai samu ilimi ba)
Kuma ku sani Allah na umartanku da salati da aminci ga Annabinsa    
           ( lalle Allah da malaikunsa suna salati ga Annabi ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi da aminci tabbatacce.)  
               
  










































السبت، 10 فبراير 2018

TARBIYANTARWA DA KAUNA

Hudubar Masallacin Annabi  na shaikh Abdulbari subaiti 23-5- 1439 AH
Hudubar farko
Musulunci na raya tashi da nauyin mas'uliyya a cikin zuciyar musulmi: mafi girman mas'uliyya shine kula da yara da tarbiyantar da su bisa turba da ginshiki na  addini da kyawawan halaye, wanda addini ne mabubbuga na duk wasu halaye na mutunci, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :( Dukkan ku Makiyaya ne, kuma zaa tambayi kowannenku abin da aka ba shi kiwo) Bukhari ne ya rawaito.
Idan tarbiya ta yi rauni zaa wayi gari  damuwar wanda  ake tarbiyantarwa  da tunanin shi  kawai  yadda zai kashe  yunwarsa  da kosar da sha'awarsa, yana tafiya duk inda zai kai shi ga holewa da morewa na jin dadin rayuwa. Allah Madaukakin sarki ya ce : (Lalle ne Allah na shigar da wadanda suka yi imani kuma suka aikata ayyukan  kwarai a gidajen Aljanna, kogunan ruwa na gudana  daga karkashinsu, kuma wadanda suka kafirta, suna jin dan dadi (a duniya)  kuma suna ci kamar yadda dabbobi ke ci, kuma wuta ita ce mazauni a gare su.) Muhammad:12
Abin da ya fi karfin tasiri a tarbiya ita ce zuciya, idan ta gyaru to sauran jiki ya gyaru, to idan ya lalace to sauran jiki ma ya baci, (Domin lalle ne idanun basu makanta, amma zukata wadanda ke a cikin kiraza su ke makanta.)   Al-Hajj 46
     Idan zuciya ta gyaru ta yi kyau sai hankula su nuna su kuma rayuwa ta haskaka jiki, gabbai kuma su rusuna, Allah Madaukaki ya ce : ( shin lokaci bai yi ba ga wadanda suka yi imani  zukatansu su yi tawalui ga ambaton Allah da abin da ya sauka daga gaskiya.) Al-Hadid:16
Lalle ba makawa kauna  wani tushe ne mai asali daga koyarwar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, shi ne zancen  ruhi kuma sako ne daga zuciya zuwa zuciya, gurin tarbiyya da gyara. Kuma hakika Allah ya kimtsa zukatan iyaye biyu bisa son 'ya'ya da suke bawa tarbiya, Usama Dan Zaid na cewa Manzon Allah ya kasance yana dauka na ya zaunar da ni akan cinyarsa ya kuma zaunar da Hasan kan daya cinyar sai ya game su sannan ya ce : (ya Allah ka tausaya musu ni ma ina tausaya musu) Bukhari ya rawaito, a wata riwayar : (ya Allah lalle ni ina son su to ya Allah  ka so su) Tirmizi ne ya rawaito da isnadi ingantacce.
Na daga cikin alamomin tarbiyantarwa na bayyane  da kauna akwai sumbatar yara da manna su a jiki, Manzon Allah ya sumbaci Hasan a tare da shi akwai Akra Bin Al-Habis zaune sai yace :Ina da yara goma amma ban taba sumbatarsu ba sai Manzon Allah ya ce : (Duk wanda ba ya tausayawa to ba zaa tausaya masa ba,Tirmizi ne ya rawaito da isnadi ingantacce,
Manzon Allah ya kasance yana cikin huduba ga sahabbansa sai ga Hasan da Husaini sun zo suna sanye da tufafi jajaye suna tafiya suna faduwa, sai Annabi ya sauka daga kan minbari ya daga su ya dora su kan hannayensa,sannan ya ce Allah ya yi gaskiya (Dukiyoyinku da 'ya'yanku fitina dai ne) na  kalli yarannan biyu kanana suna tafiya suna faduwa sai na gaza hakuri na yanke zance na na daga su. Tirmizi da Nasa'I ne suka rawaito da isnadi ingantacce.
Manzon Allah ya kasance yana raha da yara kuma yana musu tawali'u, tare da la'akari da abin da ya kebance su, yace da dayansu (kai mai kunnuwa biyu.) Nasa'I ne ya rawaito da isnadi ingantacce. Yana cewa ga wani yaron kuma :( Ya Baban Umair menene labarin kanarin ka)?Bukhari da Muslim ne suka rawaito.       
 Kada iyaye biyu su manta cewa na daga cikin abu mafi girma da amfani  da tasiri a hanyoyi na tarbiya da kauna a aikace akwai lazimtar  adu'a ta shiryuwa da datarwa da gyaruwa da kariya ga wanda ake tarbiyantarwa, to bayin Mai rahama cewa suke yi a aduarsu : (Ya Ubangijinmu ! ka bamu sanyin idanu daga matanmu da zuriyarmu) Al-Furkan 74
Ga Annabi Zakariyya yana cewa : (sai ka ba ni wani mataimaki daga wajenka, ya gaje ni kuma ya yi gado daga gidan yakubu, kuma ka sanya shi yardajje ya Ubangiji!) Maryam 5-6
Ga Annabi Ibrahim yana cewa :  (Ya Ubangiji ka ba ni (abokin zama) daga salihan mutane)Assaffat 100 (Ya Ubangiji ka sanya ni mai tsayar da sallah  kuma daga zuriyyata).Ibrahim :40
Amma yi musu mummunar adu'a hani ya zo kan hakan, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace :(kada ku yi mummunar adu'a a kanku, kuma kada ku yi mummunar adu'a ga  'ya'yanku, kuma kada ku yi mummunar adu'a ga dukiyarku, domin kar ku yi muwafaka da lokacin amsawa  sai a amsa muku) Muslim ne ya rawaito
Abin nkoyi mai kyau wani tushe ne na tarbiya, kuma haske ne na tsarkaka, Allah Madaukakin sarki ya ce : (Ka ce: idan kun kasance kuna son Allah to ku bi ni, Allah ya so ku, kuma ya gafarta muku zunubanku, kuma Allah Mai gafara ne Mai jin kai).Al-Imran :31
 Kuma abu ne da bai buya cewa kwaikwayo da koyi na da tasirin da ya fi fadi da karatu da  sauraro,
Sabo da muhimmancin koyi ne ma da hadarin da ke tattare da shi Allah ya ke cewa :(Ya ku wadanda  suka yi imani! Don me ku ke fadin abin da ba ku aikatawa? Ya girma ga zama abin kyama a wurin Allah. Ku fadi abin da ba ku aikatawa). Assaf : 2-3  
Kauna na wanzuwa da karfafuwa da dawwama har a lokacin zamewa (kuskure) da gajartawa, wannan ita ce koyarwar Manzon Allah , hakika wani mutum ya zo mishi sai ya ce: ya Manzon Allah na halaka ! sai ya ce : (Me ke gare ka?) sai ya ce : na aukawa mata ta a halin ina azumi, sai manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace :(Ko kana da wuyaye da za ka 'yanta? Sai ya ce : A'a. sai yace :(To za ka iya yin azumin wata biyu a jere?) sai yace :A'a. sai ya ce :(To zaka iya samun ciyar da miskinai sittin ?) sai ya ce :A'a). sai manzon Allah ya dan zauna jim kadan muna halin haka sai i aka  kawo wa Annabi  kwando  a cikin shi akwai dabino, kwando wata tasa ce ta awu   sai ya ce ina mai tambaya? Sai yace : Ga ni sai Manzon Allah ya ce karbi wannan ka yi sadaka  da shi, sai ya ce : ga wanda ya fi ni talauci ya Manzon Allah? To na rantse da Allah! ai duk  kewayen madina a tsakanin duwatsunta biyu ba mutan gidan da  suka  kai iyalan gida na  bukata.sai Annabi yayi dariya har fikarsa suka bayyana sai yace : ka ciyar da shi ga iyalanka).Bukhari ne ya rawaito.
A yanayi na kauna mai tarbiyantarwa ba zai shakala yin amfani da hikima da kyakkyawan fadakarwa da tausasa zance, da saukin hali, tare da nesatan amfani da karfi da suka da walakantarwa,  Allah Madaukakin sarki ya ce: (Ka yi kira  zuwa ga hanyar Ubangijinka da hikima da wa'azi mai kyau, kuma ka yi jayayya da su da magana wadda take mafi kyau.)ANNAHL -125
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : Lalle Allah Mai sauki ne,kuma yana son saukakawa, kuma ta hanyar sauki ya kan bada abin da bai bada shi ta hanyar karfi ko waninsa.) Muslim ne ya rawaito.
Ya ce da balaraben kauyen da ya yi fitsari a masallaci: (ku kyale shi, ku kwarara bokitin ruwa ko guga guda a kan fitsarin  nashi abin sani kawai an turo ku ne kuna masu sauki baa turo ku kuna masu tsanani ba).Bukhari ne ya rawaito.
Kamar yadda girmama wadda ake tarbiyantarwa da yi mishi maraba da nuna haba-haba da shi, koyarwa ne na Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. A'isha Allah kara yarda a gare ta ta ce : Fadima ta fiskanto tana tafiya, tafiyarta irin na Annabi sai Annabi yace : (Maraba da 'ya ta )sannan ya zaunar da ita a damansa ko hagunsa) Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Jiki na da gudumawa da yake bada wa gurin tarbiyyantarwa da kauna; kamar murmushi da fara'a ta gaskiya, da shafa irin na shauki, da kalmomin kwantar da hankali, da tausayawa irin na zuci.
Mai bada tarbiya ba zai yi sakaci da dama da ya samu ba na halrtowar hankali zuwa gare shi face ya dasa kyawawan dabiu ba tare da kankantar da hankalin yaro ba ko renarwa.
An karbo daga Abdullahi dan Abbas Allah kara yarda a gare shi da mahaifin shi yace : wata rana na kasance a bayan Annabi sai ya ce: ya kai yaro zan sanar da kai wasu kalmomi: ka kiyaye Allah zai kiyaye ka,ka kiyaye Allah za ka same shi a gaba gare ka)Tirmizi ne ya rawaito da isnadi ingantacce.
Tarbiyantarwa da kauna na bukatar yanayi  da iyalai zasu game su dukule,su so juna , ta inda zasu samu farinciki da  walwala su yi wasa da bai sabawa shariar wannan addini ba, Aisha Allah kara yarda a gare ta tana cewa :Na kasance a wata tafiya tare da Annabi  sai muka yi tsere  da shi sai na yi galaba a kan shi,da kafafuwa ta,a yayin da na yi jiki muka sake tsere da shi sai ya yi galaba a kai na, sai ya ce : (To da wannan ni ma na rama wancan galaba da aka yi a kai na.)Abu Dawuda ya rawaito da isnadi ingantacce.
An karbo daga gare –Allah kara yarda a gare ta- ta tace: (na ga Manzon Allah a kofar daki na ga habashawa suna wasa a masallaci Annabi ya kare ni da mayafinsa ina kallon wasar tasu.)Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Tarbiyantarwa da kauna na bukatar kulawa da adalci wajen bayyana kauna ga yara, sai ya fadada  so da ya ke musu ya game su  gabadayansu ba tare da wariya ba,
Yayin da Annabi yusuf ya yi mafarki (lalle ne ni na ga taurari goma sha daya, da rana da wata na gan su suna masu sujada a gare ni) sai mahaifinsa Annabi  Yakub  -Amincin Allah ya tabbata a gare shi - ya ce da shi : (ya karamin da na! kada ka labarta mafarkinka ga 'yan uwanka har su kulla maka wani  kaidi,  lalle shaidan ga mutum makiyi ne  bayyananne.) yusuf 4 &5
Manzon Allah ya ki ya shaida kyautar da wani mahaifi ya bawa daya daga cikin 'ya'yansa yace : (Ni ba zan yi shaida na zalunci ba). Bukhari ne ya rawaito.
Tarbiyantarwa ta hanyar kauna da kosar da zukata da sosa mata inda ya ke mata kaikayi shiryarwa ne na Annabi kuma bukata ce aka halicci mutum a kanta,kuma ya fi karfi ta bangaren  'ya'ya mata Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Wanda aka jarabce shi   da wani abu na daga wannan 'ya'ya  matan , sai ya kyautata musu to za su kasance  kariya a gare shi daga wuta) buhari da muslim ne suka rawaito  lafazin na Buhari ne ,  : kyautatawa ga 'ya'ya mata ta hanyar koyar da su da  tada su akan kamun  kai, da nesantar da su daga abin da Allah ya haramta , na daga tsiraici da bayyana jiki   .
                 Da dora yara maza a tafarki tsayayya  na aiki mai amfani , da kuma  shirye-shirye na aikin alheri wanda zai daga manufar su  ya kuma  kare su daga fadawa  cikin abubuwa marasa muhimmanci  da yawon banza.
       Yana daga cikin abin da ke warware tarbiyantarwa da kauna ; akwai shagwabantar  da yara  ta hanyar amsa musu duk  abin da suka nema  da abubuwan  kwadaye-kwadayen  su da kuma yin sakaci ta bangaren ladabtar da su da gyara musu kusakuran su : to jajarcewa wani lokaci yana cikin kauna ,: musgunawa uwa a gaban 'ya'ya yana toshe kofar soyayya  amma bayyana zunubai da fandarewa da iyaye za su yi a gaban 'ya'yan su to hanya ne mai rusa tarbiya Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (  ya isa zunubi ga mutum da ya sarayar da  wanda yake ciyarwa ) Abu Dauda da Ahmad suka rawaito da isnadi ingantacce  .
           HUDUBA TA BIYU
Hakika hanyoyin tasiri na zamani sun habaka , kuma sun haifar da wani sanje- sanje na tushe  a tunani da fahimta da dabi'u, har a ka wayi gari suna  gogayya  da  gudumawar da iyaye suke bayarwa na tarbiyan 'ya'yayen su ,: to  a nan ne muhimmancin tarbiyantarwa  da kauna zata bayyana, da kuma bashi mafaka  da kuma  gina gada mai karfi na aminci  da sabunta salo,  da shuka kyawawan dabi'u da zaburantar da himmar kafafen ilmantarwa da tarbiyantarwa , don tashi da sakonnin su   wurin kiyaye   madosan al'uma da fatanta nan gaba , da kuma kiyaye arzikin kasa , ta hanyar bada kariya ga ginshiki na addini da kuma dabi'u  da bada kulawa ga matasa ,  da kuma  abin da suke burin zama nan gaba  da kuma kiyaye radadin su da damuwan su .
Allah Madaukakin sarki ya ce : ( Ya ku wadan da suka yi imani ku karewa kan ku da iyalan ku wata  wuta makamashinta  mutane da duwatsu ne.  


                 
   


الجمعة، 26 يناير 2018

NEMAN ILIMI DA LADUBARSA

Hudubar Juma'a na Masallacin Annabi na shaikh Abdullah Dan Abdurrahman Al-Buaijan 9-5-1439 AH.
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, wanda ya ilmantar da alkalami, ya sanar da mutum abin da bai sani ba,ina kyautata yabo a gare shi  bisa ni'imominsa,ina kuma  gode mishi bisa abin da ya mana na falaloli da karamci.
Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bai da abokin tarayya, na shaida Annabi Muhammad shine cikamakin Annabawansa da Manzanninsa, Allah ya zabe shi a kan sauran al'umu, ya turo shi don tausayawa ga talikai zuwa ga larabawa da ajamawa, ya isar da sako, ya sauke amana ya yi jahadi a tafarkin Allah hakkin jahadi har mutuwa ta zo mishi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,da iyalan shi da sahabbansa da duk wanda ya bi su da kyautatawa har zuwa ranar sakayya.
Bayan haka, Lalle Alkur'ani shine zance mafi kyau, Addini a wurin Allah shine Musulunci,mafi alherin shiryarwa shine shiryarwar Annabinmu Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ( Ya ku mutane ! ku bautawa Allah Ubangijin ku da takawa ,  kuma ku ji tsoron wani yini, ranar da wani mahaifi baya sakawa dansa  da komai ko wani da ya sakawa mahaifin sa da komai  lallai wa'adin Allah gaskiya ne  , sabo da haka kada rayuwar duniya ta rude ku  kuma kada marudin nan ya rude ku  game da Allah ) .
    YA KU BAYIN ALLAH !
Hakika Allah ya zabi dan adam  domin ya sanya shi kalifa a doron kasa  ya bashi ilimi  wanda yana ta'alluki ne da aiki da kuma daukaka  , ya kuma bashi hankali  wanda ya ta'allaka ne da takalifi  Allah Madaukakin sarki  ya ce : (  kuma a lokacin da Ubangijinka ya ce ga mala'iku  lallai ne ni mai sanya wani halifa ne a cikin kasa:  suka ce,  ashe za ka sanya a cikin ta wanda zai yi barna  kuma ya zubar da jini  alhali kuwa mu muna yi maka tasbihi game da gode maka , kuma muna tsarkakewa  gare ka  ya ce : lallai ne ni  na san abin da ba ku sani ba )
      Sannan ya bayyana cewa ilimin nan yana ta'allake ne da falala da daukaka sai ya ce :
 ( Kuma ya sanar da Adam sunaye dukkan su sa'annan kuma ya gitta su a kan mala'iku sa'annan ya ce :  to ku gaya mini sunayen wadannan idan kun kasance masu gaskiya)
 suka ce  tsarki ya tabbata a gare ka ! ba bu sani a gare mu face abin da ka sanar da mu , lallai ne kai, kai ne masani mai hikima .  Ya ce : ya Adam ! ka gaya musu sunayen su  : '' to alokacin da ya gaya musu sunayen su , (Allah) ya ce :  ashe ban ce muku  ba lallai ni ina sane da gaibin sammai da kasa ( kuma ina sane da abin da kuke bayyanawa da abin da kuka kasance kuna aikatawa)
        Sai Allah ya fifita mutum bisa da yawa daga cikin halittun sa  a dalilin ni'ima ta ilimi da hankali ,  ya kuma dora taklifi a kan haka .
        YA JAMA'AR MUSULMI!
Dalibai maza da mata za su fiskanci sabon fasali na karatu a wannan  ranaku,  to madalla da wanda ya dage ya yi kokari  ya ja damara cikin aikin alheri to zai samu sa'ada , to lallai  ilimi shi ne ginshikin addini  kuma da shi ne mutum zai san addinin shi  kuma da shi ne  mutum zai iya sanin yadda zai yiwa Ubangijin shi da'a ,  kuma farkon  umarnin da mala'ika jibrilu ya zo da shi  daga wurin Allah zuwa  ga Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  shi ne ;  umarni da neman ilimi  , kuma farkon ayan da ta sauka a Alkur'ani shi ne;  ( yi karatu).
    An karbo daga Aisha  , Allah ya kara yarda a gare ta  ta ce : (  Farkon abin da   aka   fara wahayi wa Manzon Allah shi ne mafarki  na gaskiya  a cikin bacci , ya kasance baya ganin wani abu a cikin bacci  face abin ya bayyana kamar hasken  safiya  sannan sai aka kwadaitar a gare shi yin khalwa , ya kasance yakan tafi kogon hira ya kebanta yana ta bauta a ciki na wasu dararraki  masu adadi  kafin ya dawo zuwa ga iyalan shi ya sake samun guzuri  , har zuwa lokacin da gaskiya ta  zo mishi , mala'ika Jibrilu ya sauka a gare shi a halin yana kogon hira sai mala'ika ya zo mishi sai ya ce :  yi karatu , ya ce : ( ni ba mai karatu ba ne ) sai ya ce : sai ya kama ni ya matse ni  har na ji wahala sannan ya  sake ni  sai ya ce yi karatu :  sai na ce: ( ni ba mai karatu ba ne )  sai ya sake kama ni ya matse ni a karo na biyu har na ji ba dadi sannan ya sake ni , sai ya ce yi karatu : sai na ce : ( ni ba mai karatu ba ne) sai ya kama ni ya matse ni a karo na uku har na ji jiki , sannan ya sake ni sai ya ce : yi karatu da sunan Ubangijin ka  wanda ya yi halitta, ya halitta mutum daga  gudan jini,  ka yi karatu  kuma Ubangijinka shi ne mafi karamci ,  wanda ya sanar da (mutum ) game da alkalami  ya sanar da mutum abin da bai sani ba ).
       Ya ku bayin Allah hakika  Alkur'ani ya kwadaitar bisa ga neman ilimi, Allah bai umarci  Annabin shi ba da ya roke shi karin wani abu ba sai  ilimi , ( kuma ka ce ya Ubangiji ka kara min ilimi )
       Kuma ya koda matsayi irin na malamai  sai ya ce :  ( Malamai kawai ke tsoron Allah a cikin bayin sa).
        Kuma Allah ya hada su da kansa da mala'ikunsa cikin shaidawa  da  kadaitakarsa,  Allah madaukakin sarki ya ce : ( Allah ya shaida cewa : Lalle ne babu abin bautawa face  shi , kuma mala'iku  da ma'abuta ilmi sun shaida ,  Yana tsaye  da adalci , babu abin bautawa  face shi , mabuwayi , mai hikima ).
Kuma Allah ya yi nuni bisa kimansu sai ya ce: ( Ka  ce  ashe , wadanda suka sani , suna daidaita  da wadanda ba su sani ba ?).       
Kuma ya yi umarni da komawa gare su yace :(To ku tambayi ma'abota ilimi in kun kasance baku sani ba).
Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya kwadaitar game da shi ya bayyana cewa alama ne na alheri (Wanda Allah ya nufe shi da  alheri zai fahimtar da shi addini).
  Yace : (Wanda ya kama hanya ta neman ilimi Allah zai saukake mishi hanya ta shiga Aljanna)
To ku bawa ilimi wani kaso na daga lokutanku,kuma ku kwadaitar da yaranku bisa kokari da jajarcewa wajen nemansa.domin shi ne hanya mafi dacewa ta tarbiya, kuma mafi tabbatuwar  yakini  wurin tsarkake zuciya.kuma ya fi kawo amintuwa daga fitintinu, kuma yake kawo tabbatuwa  da tsayuwa yayin  jarabawa, yafi kawo hakuri yayin musiba,kuma yana cikin kyawawa mafi daraja da aikin lada mafi girma na neman kusanci ga Allah, da samun daraja mafi daukaka.
Ya ku Musulmai!
Duk wanda Allah ya nufe shi da alheri zai sanar da shi addini, mafi alheri cikinku a lokacin jahiliyya sune mafi alherinku a lokacin musulunci in sun yi ilimi,kuma malamai sune magada Annabawa.
Shagaltuwa da ilimi na cikin Bakiyatussalihat da sadaka mai gudana bayan mutuwa,  da  samun lada mai dorewa bayan wafati,
An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : Idan mutum ya rasu ayyukansa zasu katse sai guda uku: Sadaka mai gudana, ko ilimi da ake amfana da shi, ko da na kwarai da yake mishi adu'a)
Sai dai fa ilimi na bukatar hakuri da lokaci da kokari da juriya, da bada kai,  gwargwadon wahalar  da aka sha gwargwadon yadda zaa  cinma manufa,da biyan bukata.
Neman ilimi na bukatar ikhlasi a niyya da azama ta gaskiya, da tsarkake zuciya,  da tsiraituwa daga duk  abin da zai kawo cikas ko kashe jiki,  to lalle duk wanda ya riki filo aboki ba shi ba riskan matsayi (Yaro bata dare ka yi suna).
(kuma Ba ya kasancewa ga muminai su fita zuwa yaki gaba daya. Saboda haka don mene ne wata jama'a daga kowane bangare daga gare su ba ta fita (zuwa neman ilimi ba) domin su nemi ilimi ga fahimtar addini kuma domin su yi gargadi ga mutanensu idan sun koma zuwa gare su, tsammaninsu, suna yin sauna? ).
Mai neman ilimi na bukatar laduba na shari'a a cikin nemansa  har ya zama abin koyi abin buga misali mai kyau, kuma ya zama ahali na karbar wannan sako, kuma cikin adilai na wannan Al'uma.
 Ya inganta daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, (wadanda zasu karbi wannan ilimi cikin mamaya sune adilan cikinsu, suna kore karkatarwar masu ketare iyaka da da'awar mabarnata da tawilin jahilai).
Bayan haka ya ku bayin Allah! dukkan ilmuka masu amfani an shar'anta nemansu, sawa'un tushensu Alkur'ani ne da sunna: kamar ilimin addini, na akida da tafsiri da hadisi da fikihu da wasunsu, ko tushensu ya samu asali ne daga sanin yau da kullum (Gogewa da gwaji) da dubi ga duniya da rayuwa kamar ilimin likitanci ko ilimin da ke nazari kan haske da sauti ko (kimiyya da fasaha), da waninsu.
, to duk wanda ya kyautata niyyarsa wajen nemansu ina fatan fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi : (Wanda ya kama hanya ta neman ilimi Allah zai saukake mishi hanya ta shiga Aljanna) ya game da shi.
Ina neman tsarin Allah daga sharrin shaidan abin jefewa
Shine wanda ya aika a cikin mabiya  al'adu wani Manzo daga gare  su yana karanta ayoyinsa a gare su kuma yana tsarkake su, kuma yana sanar da su littafin da hikimar sa ko da yake sun  kasance daga gabaninsa suna cikin bata bayyananna . Da wadansu mutane daga  gare su, basu ida riskuwa da su ba.alhali kuwa shine Mabuwayi Maihikima.
 
Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, godiyar da ta dace da daukakarsa, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai yake bai da abokin tarayya, cikin girmansa da kamalarsa, na shaida Annabi Muhammad bawansa ne kuma Manzonsa ne, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,da iyalan shi da sahabbansa da aminci tabbatacce mai yawa, har zuwa ranar sakayya.
Ya ku bayin Allah!
Lalle ilimi na da jakunkuna da ke adana shi, da masu tsaro da ke bada kariya a gare shi, da mazaje da ke daukanshi da shehunai da ke mishi hidima, ta hanyarsu ne yake tafiya ya yadu a duniya da kokarinsu.
Ya ku al'uma!
Lalle malami yana wakiltar Annabawa ne a ayyukansu na tarbiyantarwa da ilmantarwa, ya ke tashi da hidima don samar da al'uma masu tasowa nan gaba,kuma ya dasawa yara masu tasowa na wannan al'uma iri na kyakkyawan rayuwa da walwala na duniya da lahira,to lalle ya dace da a girmama shi a kimanta shi kuma ya dace da a mutunta shi, haka kuma a dauke kai game da kananan laifukansu a yafe masa kurakuransa.
Ya ku Malamai da masu bada tarbiya maza da mata.
Ku kasance abin koyi mai kyau ku siffantu da ilimi da ladubansa, to ku manya ne a idon dalibanku, daliban na sha'awan kwaikwayon ku da koyi da ku, to ku zama abin koyi nagari don Allah ku zame abin koyi nakwarai, idan kun bayyana musu kyan gaskiya to ku kasance cikin masu gaskiya, idan kun umarce su da hakuri to ku  zama cikin masu hakuri,
Fara da kanka ka hanu daga zalunci irin na rai   ***
idan ka hanu to kai ne mai hikima
To a nan ne zaa karbi abin da ka ke fadi a yi koyi * **
da ilimi daga gare ka, ilmantarwan ya yi amfani
Kar ka yi hani ga wani hali kuma ka aikata irin shi***
Babban laifi ne a gare ka in ka yi haka.
Ya ku Malamai!
Nauyin da ke kanku na da girma, amanar da ke wuyanku babba ce. 'ya'yan wannan al'uma amana ne a kan ku, kuma an bada ajiyar wannan al'uma a hannunku, abin da ake hanga na gabanta ya taallaka ne da nauyin da ke kanku. Ku ji tsoron Allah game da kiwon da aka baku, ku ji tsoron Allah game da kiwon da aka baku! (Dukkan ku masu kiwo ne kuma abin tambaya ne bisa kiwon da aka baku,).
To in kun kyautata to kun kyautatawa kanku ne, kuma haka ake zata muku,to kuwa kuna da falala mai girma a gurin Allah, in kun muzguna to kun muzgunawa kanku da al'umarku ne.
Ya ku dalibai zababbu 'ya'ya ga malamai masu biyayya!
Ku kasa kunnuwanku  ku saurara, wannan zance ne da ya kebance ku, daga mai tausaya muku kuma masoyinku:
Lalle girmama malami da kimanta shi ladabi ne na sharia kuma halaye ne na wajibi, kuma nasara ne na ilimi da na tarbiyya. A tafiyar Annabin Allah Musa da khidr Amincin Allah ya tabbata a gare su a kwai abin lura da wa'azi  da tunatarwa,
(yace shin ba zan bi ka ba don ka sanar da ni daga abin da aka sanar da kai na shiriya?). sai malamin ya maida mishi amsa da : (Lalle ne kai ba za ka iya yin hakuri tare da ni ba, kuma ya ya za ka yi hakuri da abin da baka kewaye sani da shi ba ga jarrabawa ).sai musa ya zanta mishi cewa ya san hakkin malami da wahala irin na neman ilimi,  (yace : zaka same ni in Allah ya so mai hakuri, kuma ba zan saba maka ba ga wani umarni).
Lalle falalar malami na da girma, kokarinsa da kyautarsa hakki ne da ba zaa saka masa ba sai da alheri, to na hore ku da ku kiyaye kar ku musu rashin ladabi, domin alama ce ta lalacewar tarbiya, da fandarewan dabiu, da hali mara fasali,  ba mai yarda da shi sai dan iska.
Kuna da abin koyi  mai kyau daga magabata, ga Rabi'u almajirin imamusshafi'I Allah ya jikansu da rahama, yana cewa : Ban iya bushewan ido ba na sha ruwa a gaban Imamusshafi'i yana kallo na sabo da kwarjininsa.
Ku girmama malamanku, kowa ku san matsayin shi, ku bawa kowani mai hakki hakkinsa, Allah ya datar da ku, ya azurta ku da ilimi mai amfani, da aiki na gari.
Ya Allah ka daukaka musulunci da musulmai.             


            

الجمعة، 12 يناير 2018

MUTUWA GA MUTUM

  HUDUBAR  JUMA'A  NA MASALLACIN ANNABI TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI  NA SHAIKH SALAH AL-BUDAIR  NA  25-4-1439 H
HUDUBAR FARKO
Yaku musulmai babu dauwama a  duniya  da za a yi fata  ko  wanzuwa  da za a bida
  mutane ba wani abu ba ne face mai tafiya da kuma dan mai tafiya ***zamani kuma ba wani abu ba ne sai shudewan yini da dare.
Mutuwa kuma ba wani abu ba ne sai abu ne  mai sauka kuma makusanci *** rayi kuma ba wani abu ba ne  fa ce  abin da ake nesa da haihuwar sa kuma mutuwa ke kusantowa ga zukata sai ta fita.

Kaito ya mutuwa  ba ta da dauke kafa idan muddar da  aka  diba ma rayi  ta  kai makurar sa*** sa'oi  za su mika ka ga wani  sashi na daga  lokaci   zuwa wani lokaci wanda babu wani  lokaci bayan shi .

   Abin mamaki  ga saurin ranaku cikin tafiyar su  za ta zo ta wuce mu kuma ta zo ta tafi da mu,  a ko wani rana   akwai buri wanda yana yin nesa,  manufansa daga lokaci da ya kusanto  .
      Ina wanda  suka  kasance  kafin mu ina  su ke *** Ina mutanen da  suka  kasance  kyawawa kuma masu  yin kawa .
Lalle  zamani ya biyo ta kansu  ya  karar da wani  adadi daga  cikin su ***Sa'annan muma yana zuwa kanmu .
Sau da yawa muna ganin mutum mamaci   bayan da ya kasance a raye***  ba da jimawa ba za a gane mana abin da muka ganewa wasu   .
Me ya same mu ne muke amin ta da mutuwa*** kai ka ce  ba za mu ganta  ta  zo  zuwa gare mu ba .
     Ya gafalalle ya wanda ya sha'afa  ko kun manta cewa mu 'yan adam ne  kaddara na kewaye da mu kuma mu dinnan muna cikin tafiya ne,  wanda za mu tafi zuwa kaburbura  , mutuwa  za ta hada da mu , tashin alkiyama zai tattaro da mu ,    to har zuwa yaushe ne za mu wa'azantu mu daina , to har sai zuwa yaushe ne kunnen ka zai kiyaye fadakarwan mai fadakarwa  ,  ga  zuciyar ka kuma baya tausasa sabo  da  mai zargi .
     Ase lokaci bai yi ba da zuciya za ta ji tsoro ***  To kuma ina kokarin ? a cikin gyangyadi muke ne ko kuma zuciyar ta sandare?  To ka farka   dan uwa na kuma  ka kiyaye  kar ka kwanta .
 Kwanciya za ka yi ya rudadde  bayan ga wuta ana kara kunna  ta *** zafin ta ba a kahse shi haka nan kuma gaushinta baya mutuwa.
Annabi ya kasance  amma bai dauwama ba ga al'umar sa *** Da Allah ya dauwamar da wani halitta kafin shi  , to , da shi ya dauwama .
Mutuwa  acikin mu tana da wasu masu wanda ba sa kuskurewa *** wan da kifiya ta tsere mishi a yau to fa gobe  ba  zata   tsere mishi ba  .
Allah madaukakin sarki ya ce : ( Kuma ba mu sanya dawwama   ga wani mutum ba a gabanin ka  . Shin to idan ka mutu to su ne madauwama ?  ,  ko wani rai mai dandanan mutuwa ne kuma muna jarraba ku da sharri da alheri domin fitina , kuma  zuwa gare mu ake mayar da ku  ) AYA 34-35 Al-Anbiya
     Ina wadanda muka yi mu'amala da su na tsawon lokaci muka saba da  su, ina wadanda mu ka karkata zuwa gare su da kauna da tausayawa ,?   Sau da yawa mun rintse idanuwan mu( mun yi kuka )   sabo da masoyanmu,  mutum nawa ne masu izza  mu ka binne  muka tafi kuma muka bar su   sau da yawa muna binne makusanci mu kwantar da shi  a cikin kabari ba za mu tsaya ba ?  shin ko mutuwa na tausayawa mara lafiya daga cikin mu sabo da raunin halin shi? Shin  ta bar wani  mai nema   (dan kasuwa)  sabo da 'ya'yan shi?  Shin ta saurarawa   ma'aboci iyalai sabo da iyalan shi ? .
    Ya bawan Allah  a ko wani rana akwai abun lura bayan abun lura *** Acikin mutuwa kuma akwai abu mai hani  da ka kasance  cikin wan da suke  hanuwa .
                                                                                                         Tohar zuwa yaushe? To har zuwa yaushe ? * wai kai yaushe ne za ka ji gargadi  kuma  ka ji tsoro.
                                                                                                Zuwa yaushe ne  za ka  dena cigaba da dogewa da ruduwa da gafala *** Sau da yawa  haka  ne  bacci  to yaushe ne ranar   farkawa.
                                                                                          Rayuwa ta saraya a wani lokaci  da za ka iya sayan cikin kasa da sama *** wani irin  bata abu mai karewa za ka saye shi  cikin  wauta   
                                                                                       Ka saida  fushi da yarda  *** sannan ka saida  aljanna  kuma da  wuta .
                                                     Yanzu kai masoyi ne ga rayin ka ko kuma makiyi ne gare shi *** to lalle kai kana jefa ta ga dukkan musibu .
                                                                     Hakika ka saida ta  cikin araha –ina mai ma bakin ciki***  wanda ta kasance ba abu ne da yake na tabbas ba a gare ta.
                                                                 A yau kana aikata abin da ka keso kuma da  abin da  ka ke sha'awa *** a gobe kuma  za ka mutu kuma a dauke alkaluma .
                                                             Mai laifi na zama fasiki ta hanyar aikata babban laifi *** haka nan kuma idan ya doge a kan kananan laifuka.
                                                                 Mutum ba zai fita daga imani ba*** sabo da ya aikata                      manyan laifuka na sabo   .
                          Kuma ya wajaba  a gare shi da ya tuba*** daga dukkan abin da zai  janyo mishi   zunubai .
  Allah madaukakin sarki ya ce : (  Kuma ku tuba zuwa ga Allah guda daya , ya ku muminai ko za ku samu babban rabo).
   (Lalle Allah na shimfida hanun shi da da dare don masu laifin wuni su tuba , kuma yana shimfida  hanun shi da wuni don masu laifin  dare su tuba har rana ta bulla daga yammacinta ).
 Ina neman gafarar Allah daga  zunubi na  da barna ta ***  lalle ni ko da na kasance ana boye min laifuka na to fa mai yawan laifi ne
                                                                 Ba wani sabo da  raina za ta janyo mi ni*** face na samu kai  na a tsakanin haske da duhu .
                                                             Hakika ina mamaki   bisa gafala ta  da kuma shammata ta***  a halin mutuwa zai kira ni gobe na amsa  
                                       Hakika na yi mamaki  na tsawon aminta daga mutuwa ta *** kuma gata zuwa gare  ni za ta sadado ta fisge ni.
                                                            Na sabawa Allah a wuni na da dare na *** cikin sabo na  saki jiki bone ya tabbata  a gare ni idan har aka haramta mi n Aljanna Adin .
                                                               Kuma bone  a gare ni muddin na shiga wuta kuma bone ya tabbata a gare ni.
 Allah madaukakin sarki ya ce : (  Ka ce ya bayi na wadan da suka yi barna a kan rayukan su !  kada ku yanke kauna daga rahamar Allah , lalle Allah na gafar ta zunubai  gaba daya  lalle shi mai gafara ne mai jin kai )
 HUDUBA NA BIYU
Ya ku musulmai Addini shi ne uwar kudin ku  kuma shi ne daukakan hali da makoma.
  duk wata  karaya addini na gyara ta*** amma karayan addini ba abin da zai gyara ta.
                           Dukkan wasu musibu idan sun bayyana suna da  sauki ko sun ko sun  girmama*** sabanin musiban da zai sami mutum a addinin shi.
Ga ruwan fitintinu na ambaliya  yana dukan juna, ga kasa cike da hanyoyi na macizai da kunamu da abubuwa masu cutarwa a cikin duwatsu na sanda.
 Duniya cike take da fitina da bala'i to ku shirya hakuri don bala'i,
An karbo daga Huzaifa Allah kara yarda a gare shi yace : Ya Manzon Allah lalle mun kasance muna cikin sharri sai Allah ya tafiyar da shi ya kawo mana alheri ta hanunka, to shin bayan wannan alherin ko akwai wani sharri? Sai ya ce : E,sai ya ce to menene shi? Yace wasu fitina kamar yankin duhun dare, sashi na bin sashe, zasu zo a rikice kamar fiskar shanu,baku fayyace wannan daga wancan.) Ahmad ne ya rawaito.
(Allah kara yarda a gare shi yace : fitina ba ta cutar da kai muddin ka san addininka  lallai ita fitina  idan gaskiya da bata suka rikirkice maka ka kasa sanin wadda zaka bi to   wannan ita ce fitina ) Ibn Abi Shaiba ne ya fitar da shi
    Allah ya kara yarda a gare shi ya ce '' Idan dayan ku ya so ya san  cewa fitina ta same shi ko bata same shi ba to ya yi dubi :  to in ya kasance abin da ya ke ganin shi a da haram ya koma yanan ganin shi halal , to, fitina ta same shi,  ko kuma abin da a da yake ganin shi halal ya koma yana ganin shi haram to, nan ma fitina ta same shi '' Hakim ne ya fito da shi
  Ma'ana ra'ayin mutum ya sanja  zuwa son rai da sha'awa .
   Malik Dan Anas yana cewa: "  duk lokacin da wani mutum ya zo mana mafi jayayya yana so mu maida abin da Jibrilu ya zo mana da shi  zuwa ga manzon Allah  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi"  .
       Yanzu zan zauna a bayan kasusuwa na  sun girgiza *** Ahalin mutuwa ta kasance ta fi kusa zuwa gare ni.
                                     Ina jayayya ga dukkan wani  mai cin karo mai yawan musu ***  na sanya addinin shi ya zamana abin da zai taba mini addini na .
                                   Na bar abin da na sani sabo da ra'ayin wani   na   a   hali  kuma  ilimi  na  yakini   ba daidai  yake da ra'ayin wani ba.
                                 Ni ban zame mai shiga cikin husuma ba *** wacce  za ta tunkude daga hagu zuwa dama.
                                      Kuma hakika an  sunnan ta mana wasu sunnoni   tsayayyu*** Wanda  zai sanya lahani ga dukkan wani  kofa  ko  kuma   wani  lokaci.
                 Gaskiya  ta kasance  bata boyuwa  *** tana bayyana  a  goshi kamar    yanda   safiya   ke   bayyana .
                                   Tafarkin jahamu bai kasance ya zamana  madadi a gare mu ba***  bisa  tafarkin  Dan Aminata  amintacce    .
       An karbo daga Abdullahi dan Dailami ya ce : (    Lallai farkon tafiyan addini shi ne barin sunna  ,   addini zai tafi sunna bayan sunna  ,  kamar yan da  igiya  ke tafiya gaba  bayan  gaba .
    Abubakar Siddik Allah ya yarda da shi ya ce : '' Ban kasance mai barin wani abu da Annabi ya kasance yana aikatawa ba  face sai na yi aiki da shi  , kuma lallai ni ina tsoron  na bar wani  abu daga umarnin sa ya zama na karkace ''.
       Ku  tabbata ya ku bayin Allah  akan  littafi  da sunna  da shari'a  da addini  da kuma dabi'u da halaye kyawawa  ku kiyaye masu batarwa,   masu tada fitina ,  ku kiyaye su kar su  fitine ku daga  wani sashi na daga abin da Allah ya saukar  a gare ka .
Ya  Allah muna rokon ka tabbatuwa  akan al'amari da kuma  azama bisa shiriya.