الجمعة، 26 يناير 2018

NEMAN ILIMI DA LADUBARSA

Hudubar Juma'a na Masallacin Annabi na shaikh Abdullah Dan Abdurrahman Al-Buaijan 9-5-1439 AH.
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, wanda ya ilmantar da alkalami, ya sanar da mutum abin da bai sani ba,ina kyautata yabo a gare shi  bisa ni'imominsa,ina kuma  gode mishi bisa abin da ya mana na falaloli da karamci.
Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bai da abokin tarayya, na shaida Annabi Muhammad shine cikamakin Annabawansa da Manzanninsa, Allah ya zabe shi a kan sauran al'umu, ya turo shi don tausayawa ga talikai zuwa ga larabawa da ajamawa, ya isar da sako, ya sauke amana ya yi jahadi a tafarkin Allah hakkin jahadi har mutuwa ta zo mishi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,da iyalan shi da sahabbansa da duk wanda ya bi su da kyautatawa har zuwa ranar sakayya.
Bayan haka, Lalle Alkur'ani shine zance mafi kyau, Addini a wurin Allah shine Musulunci,mafi alherin shiryarwa shine shiryarwar Annabinmu Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ( Ya ku mutane ! ku bautawa Allah Ubangijin ku da takawa ,  kuma ku ji tsoron wani yini, ranar da wani mahaifi baya sakawa dansa  da komai ko wani da ya sakawa mahaifin sa da komai  lallai wa'adin Allah gaskiya ne  , sabo da haka kada rayuwar duniya ta rude ku  kuma kada marudin nan ya rude ku  game da Allah ) .
    YA KU BAYIN ALLAH !
Hakika Allah ya zabi dan adam  domin ya sanya shi kalifa a doron kasa  ya bashi ilimi  wanda yana ta'alluki ne da aiki da kuma daukaka  , ya kuma bashi hankali  wanda ya ta'allaka ne da takalifi  Allah Madaukakin sarki  ya ce : (  kuma a lokacin da Ubangijinka ya ce ga mala'iku  lallai ne ni mai sanya wani halifa ne a cikin kasa:  suka ce,  ashe za ka sanya a cikin ta wanda zai yi barna  kuma ya zubar da jini  alhali kuwa mu muna yi maka tasbihi game da gode maka , kuma muna tsarkakewa  gare ka  ya ce : lallai ne ni  na san abin da ba ku sani ba )
      Sannan ya bayyana cewa ilimin nan yana ta'allake ne da falala da daukaka sai ya ce :
 ( Kuma ya sanar da Adam sunaye dukkan su sa'annan kuma ya gitta su a kan mala'iku sa'annan ya ce :  to ku gaya mini sunayen wadannan idan kun kasance masu gaskiya)
 suka ce  tsarki ya tabbata a gare ka ! ba bu sani a gare mu face abin da ka sanar da mu , lallai ne kai, kai ne masani mai hikima .  Ya ce : ya Adam ! ka gaya musu sunayen su  : '' to alokacin da ya gaya musu sunayen su , (Allah) ya ce :  ashe ban ce muku  ba lallai ni ina sane da gaibin sammai da kasa ( kuma ina sane da abin da kuke bayyanawa da abin da kuka kasance kuna aikatawa)
        Sai Allah ya fifita mutum bisa da yawa daga cikin halittun sa  a dalilin ni'ima ta ilimi da hankali ,  ya kuma dora taklifi a kan haka .
        YA JAMA'AR MUSULMI!
Dalibai maza da mata za su fiskanci sabon fasali na karatu a wannan  ranaku,  to madalla da wanda ya dage ya yi kokari  ya ja damara cikin aikin alheri to zai samu sa'ada , to lallai  ilimi shi ne ginshikin addini  kuma da shi ne mutum zai san addinin shi  kuma da shi ne  mutum zai iya sanin yadda zai yiwa Ubangijin shi da'a ,  kuma farkon  umarnin da mala'ika jibrilu ya zo da shi  daga wurin Allah zuwa  ga Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  shi ne ;  umarni da neman ilimi  , kuma farkon ayan da ta sauka a Alkur'ani shi ne;  ( yi karatu).
    An karbo daga Aisha  , Allah ya kara yarda a gare ta  ta ce : (  Farkon abin da   aka   fara wahayi wa Manzon Allah shi ne mafarki  na gaskiya  a cikin bacci , ya kasance baya ganin wani abu a cikin bacci  face abin ya bayyana kamar hasken  safiya  sannan sai aka kwadaitar a gare shi yin khalwa , ya kasance yakan tafi kogon hira ya kebanta yana ta bauta a ciki na wasu dararraki  masu adadi  kafin ya dawo zuwa ga iyalan shi ya sake samun guzuri  , har zuwa lokacin da gaskiya ta  zo mishi , mala'ika Jibrilu ya sauka a gare shi a halin yana kogon hira sai mala'ika ya zo mishi sai ya ce :  yi karatu , ya ce : ( ni ba mai karatu ba ne ) sai ya ce : sai ya kama ni ya matse ni  har na ji wahala sannan ya  sake ni  sai ya ce yi karatu :  sai na ce: ( ni ba mai karatu ba ne )  sai ya sake kama ni ya matse ni a karo na biyu har na ji ba dadi sannan ya sake ni , sai ya ce yi karatu : sai na ce : ( ni ba mai karatu ba ne) sai ya kama ni ya matse ni a karo na uku har na ji jiki , sannan ya sake ni sai ya ce : yi karatu da sunan Ubangijin ka  wanda ya yi halitta, ya halitta mutum daga  gudan jini,  ka yi karatu  kuma Ubangijinka shi ne mafi karamci ,  wanda ya sanar da (mutum ) game da alkalami  ya sanar da mutum abin da bai sani ba ).
       Ya ku bayin Allah hakika  Alkur'ani ya kwadaitar bisa ga neman ilimi, Allah bai umarci  Annabin shi ba da ya roke shi karin wani abu ba sai  ilimi , ( kuma ka ce ya Ubangiji ka kara min ilimi )
       Kuma ya koda matsayi irin na malamai  sai ya ce :  ( Malamai kawai ke tsoron Allah a cikin bayin sa).
        Kuma Allah ya hada su da kansa da mala'ikunsa cikin shaidawa  da  kadaitakarsa,  Allah madaukakin sarki ya ce : ( Allah ya shaida cewa : Lalle ne babu abin bautawa face  shi , kuma mala'iku  da ma'abuta ilmi sun shaida ,  Yana tsaye  da adalci , babu abin bautawa  face shi , mabuwayi , mai hikima ).
Kuma Allah ya yi nuni bisa kimansu sai ya ce: ( Ka  ce  ashe , wadanda suka sani , suna daidaita  da wadanda ba su sani ba ?).       
Kuma ya yi umarni da komawa gare su yace :(To ku tambayi ma'abota ilimi in kun kasance baku sani ba).
Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya kwadaitar game da shi ya bayyana cewa alama ne na alheri (Wanda Allah ya nufe shi da  alheri zai fahimtar da shi addini).
  Yace : (Wanda ya kama hanya ta neman ilimi Allah zai saukake mishi hanya ta shiga Aljanna)
To ku bawa ilimi wani kaso na daga lokutanku,kuma ku kwadaitar da yaranku bisa kokari da jajarcewa wajen nemansa.domin shi ne hanya mafi dacewa ta tarbiya, kuma mafi tabbatuwar  yakini  wurin tsarkake zuciya.kuma ya fi kawo amintuwa daga fitintinu, kuma yake kawo tabbatuwa  da tsayuwa yayin  jarabawa, yafi kawo hakuri yayin musiba,kuma yana cikin kyawawa mafi daraja da aikin lada mafi girma na neman kusanci ga Allah, da samun daraja mafi daukaka.
Ya ku Musulmai!
Duk wanda Allah ya nufe shi da alheri zai sanar da shi addini, mafi alheri cikinku a lokacin jahiliyya sune mafi alherinku a lokacin musulunci in sun yi ilimi,kuma malamai sune magada Annabawa.
Shagaltuwa da ilimi na cikin Bakiyatussalihat da sadaka mai gudana bayan mutuwa,  da  samun lada mai dorewa bayan wafati,
An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : Idan mutum ya rasu ayyukansa zasu katse sai guda uku: Sadaka mai gudana, ko ilimi da ake amfana da shi, ko da na kwarai da yake mishi adu'a)
Sai dai fa ilimi na bukatar hakuri da lokaci da kokari da juriya, da bada kai,  gwargwadon wahalar  da aka sha gwargwadon yadda zaa  cinma manufa,da biyan bukata.
Neman ilimi na bukatar ikhlasi a niyya da azama ta gaskiya, da tsarkake zuciya,  da tsiraituwa daga duk  abin da zai kawo cikas ko kashe jiki,  to lalle duk wanda ya riki filo aboki ba shi ba riskan matsayi (Yaro bata dare ka yi suna).
(kuma Ba ya kasancewa ga muminai su fita zuwa yaki gaba daya. Saboda haka don mene ne wata jama'a daga kowane bangare daga gare su ba ta fita (zuwa neman ilimi ba) domin su nemi ilimi ga fahimtar addini kuma domin su yi gargadi ga mutanensu idan sun koma zuwa gare su, tsammaninsu, suna yin sauna? ).
Mai neman ilimi na bukatar laduba na shari'a a cikin nemansa  har ya zama abin koyi abin buga misali mai kyau, kuma ya zama ahali na karbar wannan sako, kuma cikin adilai na wannan Al'uma.
 Ya inganta daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, (wadanda zasu karbi wannan ilimi cikin mamaya sune adilan cikinsu, suna kore karkatarwar masu ketare iyaka da da'awar mabarnata da tawilin jahilai).
Bayan haka ya ku bayin Allah! dukkan ilmuka masu amfani an shar'anta nemansu, sawa'un tushensu Alkur'ani ne da sunna: kamar ilimin addini, na akida da tafsiri da hadisi da fikihu da wasunsu, ko tushensu ya samu asali ne daga sanin yau da kullum (Gogewa da gwaji) da dubi ga duniya da rayuwa kamar ilimin likitanci ko ilimin da ke nazari kan haske da sauti ko (kimiyya da fasaha), da waninsu.
, to duk wanda ya kyautata niyyarsa wajen nemansu ina fatan fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi : (Wanda ya kama hanya ta neman ilimi Allah zai saukake mishi hanya ta shiga Aljanna) ya game da shi.
Ina neman tsarin Allah daga sharrin shaidan abin jefewa
Shine wanda ya aika a cikin mabiya  al'adu wani Manzo daga gare  su yana karanta ayoyinsa a gare su kuma yana tsarkake su, kuma yana sanar da su littafin da hikimar sa ko da yake sun  kasance daga gabaninsa suna cikin bata bayyananna . Da wadansu mutane daga  gare su, basu ida riskuwa da su ba.alhali kuwa shine Mabuwayi Maihikima.
 
Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, godiyar da ta dace da daukakarsa, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai yake bai da abokin tarayya, cikin girmansa da kamalarsa, na shaida Annabi Muhammad bawansa ne kuma Manzonsa ne, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,da iyalan shi da sahabbansa da aminci tabbatacce mai yawa, har zuwa ranar sakayya.
Ya ku bayin Allah!
Lalle ilimi na da jakunkuna da ke adana shi, da masu tsaro da ke bada kariya a gare shi, da mazaje da ke daukanshi da shehunai da ke mishi hidima, ta hanyarsu ne yake tafiya ya yadu a duniya da kokarinsu.
Ya ku al'uma!
Lalle malami yana wakiltar Annabawa ne a ayyukansu na tarbiyantarwa da ilmantarwa, ya ke tashi da hidima don samar da al'uma masu tasowa nan gaba,kuma ya dasawa yara masu tasowa na wannan al'uma iri na kyakkyawan rayuwa da walwala na duniya da lahira,to lalle ya dace da a girmama shi a kimanta shi kuma ya dace da a mutunta shi, haka kuma a dauke kai game da kananan laifukansu a yafe masa kurakuransa.
Ya ku Malamai da masu bada tarbiya maza da mata.
Ku kasance abin koyi mai kyau ku siffantu da ilimi da ladubansa, to ku manya ne a idon dalibanku, daliban na sha'awan kwaikwayon ku da koyi da ku, to ku zama abin koyi nagari don Allah ku zame abin koyi nakwarai, idan kun bayyana musu kyan gaskiya to ku kasance cikin masu gaskiya, idan kun umarce su da hakuri to ku  zama cikin masu hakuri,
Fara da kanka ka hanu daga zalunci irin na rai   ***
idan ka hanu to kai ne mai hikima
To a nan ne zaa karbi abin da ka ke fadi a yi koyi * **
da ilimi daga gare ka, ilmantarwan ya yi amfani
Kar ka yi hani ga wani hali kuma ka aikata irin shi***
Babban laifi ne a gare ka in ka yi haka.
Ya ku Malamai!
Nauyin da ke kanku na da girma, amanar da ke wuyanku babba ce. 'ya'yan wannan al'uma amana ne a kan ku, kuma an bada ajiyar wannan al'uma a hannunku, abin da ake hanga na gabanta ya taallaka ne da nauyin da ke kanku. Ku ji tsoron Allah game da kiwon da aka baku, ku ji tsoron Allah game da kiwon da aka baku! (Dukkan ku masu kiwo ne kuma abin tambaya ne bisa kiwon da aka baku,).
To in kun kyautata to kun kyautatawa kanku ne, kuma haka ake zata muku,to kuwa kuna da falala mai girma a gurin Allah, in kun muzguna to kun muzgunawa kanku da al'umarku ne.
Ya ku dalibai zababbu 'ya'ya ga malamai masu biyayya!
Ku kasa kunnuwanku  ku saurara, wannan zance ne da ya kebance ku, daga mai tausaya muku kuma masoyinku:
Lalle girmama malami da kimanta shi ladabi ne na sharia kuma halaye ne na wajibi, kuma nasara ne na ilimi da na tarbiyya. A tafiyar Annabin Allah Musa da khidr Amincin Allah ya tabbata a gare su a kwai abin lura da wa'azi  da tunatarwa,
(yace shin ba zan bi ka ba don ka sanar da ni daga abin da aka sanar da kai na shiriya?). sai malamin ya maida mishi amsa da : (Lalle ne kai ba za ka iya yin hakuri tare da ni ba, kuma ya ya za ka yi hakuri da abin da baka kewaye sani da shi ba ga jarrabawa ).sai musa ya zanta mishi cewa ya san hakkin malami da wahala irin na neman ilimi,  (yace : zaka same ni in Allah ya so mai hakuri, kuma ba zan saba maka ba ga wani umarni).
Lalle falalar malami na da girma, kokarinsa da kyautarsa hakki ne da ba zaa saka masa ba sai da alheri, to na hore ku da ku kiyaye kar ku musu rashin ladabi, domin alama ce ta lalacewar tarbiya, da fandarewan dabiu, da hali mara fasali,  ba mai yarda da shi sai dan iska.
Kuna da abin koyi  mai kyau daga magabata, ga Rabi'u almajirin imamusshafi'I Allah ya jikansu da rahama, yana cewa : Ban iya bushewan ido ba na sha ruwa a gaban Imamusshafi'i yana kallo na sabo da kwarjininsa.
Ku girmama malamanku, kowa ku san matsayin shi, ku bawa kowani mai hakki hakkinsa, Allah ya datar da ku, ya azurta ku da ilimi mai amfani, da aiki na gari.
Ya Allah ka daukaka musulunci da musulmai.             


            

الجمعة، 12 يناير 2018

MUTUWA GA MUTUM

  HUDUBAR  JUMA'A  NA MASALLACIN ANNABI TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI  NA SHAIKH SALAH AL-BUDAIR  NA  25-4-1439 H
HUDUBAR FARKO
Yaku musulmai babu dauwama a  duniya  da za a yi fata  ko  wanzuwa  da za a bida
  mutane ba wani abu ba ne face mai tafiya da kuma dan mai tafiya ***zamani kuma ba wani abu ba ne sai shudewan yini da dare.
Mutuwa kuma ba wani abu ba ne sai abu ne  mai sauka kuma makusanci *** rayi kuma ba wani abu ba ne  fa ce  abin da ake nesa da haihuwar sa kuma mutuwa ke kusantowa ga zukata sai ta fita.

Kaito ya mutuwa  ba ta da dauke kafa idan muddar da  aka  diba ma rayi  ta  kai makurar sa*** sa'oi  za su mika ka ga wani  sashi na daga  lokaci   zuwa wani lokaci wanda babu wani  lokaci bayan shi .

   Abin mamaki  ga saurin ranaku cikin tafiyar su  za ta zo ta wuce mu kuma ta zo ta tafi da mu,  a ko wani rana   akwai buri wanda yana yin nesa,  manufansa daga lokaci da ya kusanto  .
      Ina wanda  suka  kasance  kafin mu ina  su ke *** Ina mutanen da  suka  kasance  kyawawa kuma masu  yin kawa .
Lalle  zamani ya biyo ta kansu  ya  karar da wani  adadi daga  cikin su ***Sa'annan muma yana zuwa kanmu .
Sau da yawa muna ganin mutum mamaci   bayan da ya kasance a raye***  ba da jimawa ba za a gane mana abin da muka ganewa wasu   .
Me ya same mu ne muke amin ta da mutuwa*** kai ka ce  ba za mu ganta  ta  zo  zuwa gare mu ba .
     Ya gafalalle ya wanda ya sha'afa  ko kun manta cewa mu 'yan adam ne  kaddara na kewaye da mu kuma mu dinnan muna cikin tafiya ne,  wanda za mu tafi zuwa kaburbura  , mutuwa  za ta hada da mu , tashin alkiyama zai tattaro da mu ,    to har zuwa yaushe ne za mu wa'azantu mu daina , to har sai zuwa yaushe ne kunnen ka zai kiyaye fadakarwan mai fadakarwa  ,  ga  zuciyar ka kuma baya tausasa sabo  da  mai zargi .
     Ase lokaci bai yi ba da zuciya za ta ji tsoro ***  To kuma ina kokarin ? a cikin gyangyadi muke ne ko kuma zuciyar ta sandare?  To ka farka   dan uwa na kuma  ka kiyaye  kar ka kwanta .
 Kwanciya za ka yi ya rudadde  bayan ga wuta ana kara kunna  ta *** zafin ta ba a kahse shi haka nan kuma gaushinta baya mutuwa.
Annabi ya kasance  amma bai dauwama ba ga al'umar sa *** Da Allah ya dauwamar da wani halitta kafin shi  , to , da shi ya dauwama .
Mutuwa  acikin mu tana da wasu masu wanda ba sa kuskurewa *** wan da kifiya ta tsere mishi a yau to fa gobe  ba  zata   tsere mishi ba  .
Allah madaukakin sarki ya ce : ( Kuma ba mu sanya dawwama   ga wani mutum ba a gabanin ka  . Shin to idan ka mutu to su ne madauwama ?  ,  ko wani rai mai dandanan mutuwa ne kuma muna jarraba ku da sharri da alheri domin fitina , kuma  zuwa gare mu ake mayar da ku  ) AYA 34-35 Al-Anbiya
     Ina wadanda muka yi mu'amala da su na tsawon lokaci muka saba da  su, ina wadanda mu ka karkata zuwa gare su da kauna da tausayawa ,?   Sau da yawa mun rintse idanuwan mu( mun yi kuka )   sabo da masoyanmu,  mutum nawa ne masu izza  mu ka binne  muka tafi kuma muka bar su   sau da yawa muna binne makusanci mu kwantar da shi  a cikin kabari ba za mu tsaya ba ?  shin ko mutuwa na tausayawa mara lafiya daga cikin mu sabo da raunin halin shi? Shin  ta bar wani  mai nema   (dan kasuwa)  sabo da 'ya'yan shi?  Shin ta saurarawa   ma'aboci iyalai sabo da iyalan shi ? .
    Ya bawan Allah  a ko wani rana akwai abun lura bayan abun lura *** Acikin mutuwa kuma akwai abu mai hani  da ka kasance  cikin wan da suke  hanuwa .
                                                                                                         Tohar zuwa yaushe? To har zuwa yaushe ? * wai kai yaushe ne za ka ji gargadi  kuma  ka ji tsoro.
                                                                                                Zuwa yaushe ne  za ka  dena cigaba da dogewa da ruduwa da gafala *** Sau da yawa  haka  ne  bacci  to yaushe ne ranar   farkawa.
                                                                                          Rayuwa ta saraya a wani lokaci  da za ka iya sayan cikin kasa da sama *** wani irin  bata abu mai karewa za ka saye shi  cikin  wauta   
                                                                                       Ka saida  fushi da yarda  *** sannan ka saida  aljanna  kuma da  wuta .
                                                     Yanzu kai masoyi ne ga rayin ka ko kuma makiyi ne gare shi *** to lalle kai kana jefa ta ga dukkan musibu .
                                                                     Hakika ka saida ta  cikin araha –ina mai ma bakin ciki***  wanda ta kasance ba abu ne da yake na tabbas ba a gare ta.
                                                                 A yau kana aikata abin da ka keso kuma da  abin da  ka ke sha'awa *** a gobe kuma  za ka mutu kuma a dauke alkaluma .
                                                             Mai laifi na zama fasiki ta hanyar aikata babban laifi *** haka nan kuma idan ya doge a kan kananan laifuka.
                                                                 Mutum ba zai fita daga imani ba*** sabo da ya aikata                      manyan laifuka na sabo   .
                          Kuma ya wajaba  a gare shi da ya tuba*** daga dukkan abin da zai  janyo mishi   zunubai .
  Allah madaukakin sarki ya ce : (  Kuma ku tuba zuwa ga Allah guda daya , ya ku muminai ko za ku samu babban rabo).
   (Lalle Allah na shimfida hanun shi da da dare don masu laifin wuni su tuba , kuma yana shimfida  hanun shi da wuni don masu laifin  dare su tuba har rana ta bulla daga yammacinta ).
 Ina neman gafarar Allah daga  zunubi na  da barna ta ***  lalle ni ko da na kasance ana boye min laifuka na to fa mai yawan laifi ne
                                                                 Ba wani sabo da  raina za ta janyo mi ni*** face na samu kai  na a tsakanin haske da duhu .
                                                             Hakika ina mamaki   bisa gafala ta  da kuma shammata ta***  a halin mutuwa zai kira ni gobe na amsa  
                                       Hakika na yi mamaki  na tsawon aminta daga mutuwa ta *** kuma gata zuwa gare  ni za ta sadado ta fisge ni.
                                                            Na sabawa Allah a wuni na da dare na *** cikin sabo na  saki jiki bone ya tabbata  a gare ni idan har aka haramta mi n Aljanna Adin .
                                                               Kuma bone  a gare ni muddin na shiga wuta kuma bone ya tabbata a gare ni.
 Allah madaukakin sarki ya ce : (  Ka ce ya bayi na wadan da suka yi barna a kan rayukan su !  kada ku yanke kauna daga rahamar Allah , lalle Allah na gafar ta zunubai  gaba daya  lalle shi mai gafara ne mai jin kai )
 HUDUBA NA BIYU
Ya ku musulmai Addini shi ne uwar kudin ku  kuma shi ne daukakan hali da makoma.
  duk wata  karaya addini na gyara ta*** amma karayan addini ba abin da zai gyara ta.
                           Dukkan wasu musibu idan sun bayyana suna da  sauki ko sun ko sun  girmama*** sabanin musiban da zai sami mutum a addinin shi.
Ga ruwan fitintinu na ambaliya  yana dukan juna, ga kasa cike da hanyoyi na macizai da kunamu da abubuwa masu cutarwa a cikin duwatsu na sanda.
 Duniya cike take da fitina da bala'i to ku shirya hakuri don bala'i,
An karbo daga Huzaifa Allah kara yarda a gare shi yace : Ya Manzon Allah lalle mun kasance muna cikin sharri sai Allah ya tafiyar da shi ya kawo mana alheri ta hanunka, to shin bayan wannan alherin ko akwai wani sharri? Sai ya ce : E,sai ya ce to menene shi? Yace wasu fitina kamar yankin duhun dare, sashi na bin sashe, zasu zo a rikice kamar fiskar shanu,baku fayyace wannan daga wancan.) Ahmad ne ya rawaito.
(Allah kara yarda a gare shi yace : fitina ba ta cutar da kai muddin ka san addininka  lallai ita fitina  idan gaskiya da bata suka rikirkice maka ka kasa sanin wadda zaka bi to   wannan ita ce fitina ) Ibn Abi Shaiba ne ya fitar da shi
    Allah ya kara yarda a gare shi ya ce '' Idan dayan ku ya so ya san  cewa fitina ta same shi ko bata same shi ba to ya yi dubi :  to in ya kasance abin da ya ke ganin shi a da haram ya koma yanan ganin shi halal , to, fitina ta same shi,  ko kuma abin da a da yake ganin shi halal ya koma yana ganin shi haram to, nan ma fitina ta same shi '' Hakim ne ya fito da shi
  Ma'ana ra'ayin mutum ya sanja  zuwa son rai da sha'awa .
   Malik Dan Anas yana cewa: "  duk lokacin da wani mutum ya zo mana mafi jayayya yana so mu maida abin da Jibrilu ya zo mana da shi  zuwa ga manzon Allah  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi"  .
       Yanzu zan zauna a bayan kasusuwa na  sun girgiza *** Ahalin mutuwa ta kasance ta fi kusa zuwa gare ni.
                                     Ina jayayya ga dukkan wani  mai cin karo mai yawan musu ***  na sanya addinin shi ya zamana abin da zai taba mini addini na .
                                   Na bar abin da na sani sabo da ra'ayin wani   na   a   hali  kuma  ilimi  na  yakini   ba daidai  yake da ra'ayin wani ba.
                                 Ni ban zame mai shiga cikin husuma ba *** wacce  za ta tunkude daga hagu zuwa dama.
                                      Kuma hakika an  sunnan ta mana wasu sunnoni   tsayayyu*** Wanda  zai sanya lahani ga dukkan wani  kofa  ko  kuma   wani  lokaci.
                 Gaskiya  ta kasance  bata boyuwa  *** tana bayyana  a  goshi kamar    yanda   safiya   ke   bayyana .
                                   Tafarkin jahamu bai kasance ya zamana  madadi a gare mu ba***  bisa  tafarkin  Dan Aminata  amintacce    .
       An karbo daga Abdullahi dan Dailami ya ce : (    Lallai farkon tafiyan addini shi ne barin sunna  ,   addini zai tafi sunna bayan sunna  ,  kamar yan da  igiya  ke tafiya gaba  bayan  gaba .
    Abubakar Siddik Allah ya yarda da shi ya ce : '' Ban kasance mai barin wani abu da Annabi ya kasance yana aikatawa ba  face sai na yi aiki da shi  , kuma lallai ni ina tsoron  na bar wani  abu daga umarnin sa ya zama na karkace ''.
       Ku  tabbata ya ku bayin Allah  akan  littafi  da sunna  da shari'a  da addini  da kuma dabi'u da halaye kyawawa  ku kiyaye masu batarwa,   masu tada fitina ,  ku kiyaye su kar su  fitine ku daga  wani sashi na daga abin da Allah ya saukar  a gare ka .
Ya  Allah muna rokon ka tabbatuwa  akan al'amari da kuma  azama bisa shiriya.



     

الجمعة، 29 ديسمبر 2017

KUDUS DA MATSAYINSA A GUN MUSULMI

Hudubar Masallacin Annabi  na shaikh Abdulbari subaiti 11-4- 1439 AH
Hudubar farko
(Tsarki ya tabbata ga wanda yayi tafiyar dare da bawansa da dare daga Masallaci mai alfarma zuwa masallacin Aksa wanda muka sanya albarka a gefensa domin mu nuna masa daga Ayoyinmu ) Al'isra 1
Allah na girmama kan shi, kuma yana girmama sha'aninsa sabo da ikonsa da kudurarsa ga abin da waninsa ba zai iya yi ba, kudurarsa ta bayyana a wannan tafiya ta ban mamaki, da dauwamammiyar mu'ujiza  da ta rikita kwakwale  ta kere tunanin masu hankula, sabo da fitanta daga abin da dan adam ya saba, wato tafiyan dare  da aka yi da Manzon Allah.
Daga masallacin kaba Mai Alfarma zuwa Masallacin Aksa  a wata tafiya manesaciya, da ya ga ayoyin Allah masu girma da kuma kasaitan mulkin Ubangiji, sa'annan kuma ya dawo a cikin wannan daren .
       Haka ne sha'anin wata aya ce mafi girma a cikin ayoyin  Annabtaka ,   kuma  da mu'ujiza mafi daukaka  cikinta akwai hikimomi da hukunce-hukunce, da darusa masu girman fasaha tafiya ce da Allah ya kebe masoyin shi da ita  kuma zababben shi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,  daga Masallaci mai alfarma zuwa Baitil Makdis  gurbin Annabtaka , kuma  daya daga cikin masallatayyan alkiblan musulmai, domin daukaka kuma da girmama  matsayin shi, da  sabunta azama ga Annabin mu Muhammad da tabbatar da shi , mu'ujiza ce rayayyiya  daga Ubangiji   , ta dauki dan Adam zuwa ga  duniyan sama   ta kuma dawo da shi zuwa ga doron kasa ,  duniya gaba daya a damkan sa take , ba  wani abin bautawa da gaskiya sai shi , ba  mu da  wani Ubangiji koma bayan shi .
        Girman Musulunci na bayyana a Isra'i da aka yi, kuma lallai shi dinnan Addini ne wanda Allah ya tattaro dukkan shari'o'i  da su ka gabata  a cikin sa, kuma shi ne cikamaki na dukkan shari'o'i,  tafiyar ta dada kulla dankon  'yan'uwantaka tsakanin Annabawa , kuma sakon su duka guda daya ne , a duk lokacin da Annabi ya sauka  a sama sai a fiskance su da fadin su  , (maraba  da dan'uwa na kwarai kuma Annabi ) Manzon Allah tsira da  amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Ni na  fi dacewa a cikin mutane  da Isa Dan Maryam  a duniya da lahira. Annabawa 'yan uwan juna ne Uban su daya uwa kowa da na shi, kuma Addininsu guda ne,)  
Dukkan Annabawa da sun riski Annabi Muhammad da ya wajaba  a gare su da su yi imani da shi, su kuma bi shi su taimaka mishi, kuma ya zama shi ne jagoran su abin bin su. Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce ga Umar Allah ya yarda da shi :(Hakika na zo muku da ita fara fat a tsabtace, da musa ya kasance a raye da ba abin da zai isan mishi sai dai ya bi ni)  Abin da ke karfafa wannan shi ne fadin Allah Madaukakin sarki :(Kuma a  lokacin  da Allah ya riki  alkawrin Annabawa : lalle ne  ban baku wani abu ba daga littafi da hikima , sa'annan  kuma wani Manzo ya je muku mai gaskatawa ga abin da yake tare da ku , lalle ne za ku gaskata shi ,  kuma lalle ne za ku taimake shi   ya ce :  ''shin kun tabbatar kuma kun riki alkawari na  a kan wannan a gare ku   suka ce mun tabbatar '' ya ce :'' to ku yi shaida kuma ni  a tare da ku ina daga masu shaida).  Ali Imran 81
Annabawa sun hadu a bayan  Annabi ya limance su sallah a masallacin Aksa sabo da daukakansa da darajarsa  kuma shine mafificin Annabawa kuma shugabansu kamar yadda ya zo a hadisin Isra'i wanda Annabi yake sifanta tafiyar  da cewa (sai ga Musa ya na tsaye yana sallah shi mutum ne mai karamin ruwa dunkulalle kamar irin mutanen kabilar Shanu'a, sai ga Isa dan Maryam shi ma yana tsaye yana sallah wanda ya fi kama da shi cikin mutane shine Urwa dan Mas'ud Assakafi, sai ga Ibrahim yana tsaye yana sallah sahibinku ne ya fi kama da shi a cikin mutane – wato yana nufin kansa- sai na tsaida sallah na limance su)
Wannan kyakkyawan halin na ingiza masu da'awar gaskiya da su yi koyi da Annabawa amincin Allah ya tabbata a gare su  su hadu akan biyayya da da'a da tsoron Allah su yi watsi da duk wasu sabuba na sabani da rarrabuwa.
Kudura na ban mamaki da Annabi  ya yi amfani da shi na tafiya daga masallacin ka'aba zuwa masallacin Aksa  ya yi kama da saurin yaduwar musulunci da wanzuwarsa a doron kasa,Addini ne da zai cika duniya ya keta dukkan iyakoki da kofofi, Musulunci ya yadu a zamanin farko wanda yana kusa da ace mu'ujiza ne, sai gashi a wannan zamanin namu ya sake yaduwa don ya gaskata mu'ujiza daga cikin mu'ujizozin Manzon Allah, wanda yace ga Adiyyu Dan Hatim : (Na rantse da wanda rai na ke hanunsa Allah zai cika wannan addini har mace ta yi tafiya daga garin Hira har ta je ta yi dawafi a ka'aba  ba tare da wani makusanci ba). Ya kuma ce :(Lalle Allah ya dunkule kasa ya tattaro min ita har na ga gabashinta da yammacinta kuma lalle mulkin al'uma ta zai kai duk inda aka tattaro min na daga gare ta). Ya ce (wannan addini zai isa ga duk inda dare da wuni ya kai,har ya zama ba wani gida a birni ko kauye sai musulunci ya shiga da daukakan mai daukaka ko da kaskancin makaskanci,daukaka ce da Allah zai daukaka musulunci da  musulmai da ita    da kuma kaskanci da zai kaskantar da shirka da masu shirka da ita ).
            Manzon Allah ya yi gaskiya  domin lallai musulunci a yau shi ne addini ne da ya fi saurin yaduwa ,  a tsawon kasa da fadin ta  , tare  da shaidar  makiya da kuma rubuce-rubucen su.
             Karfin yaduwan musulunci  ya samu ne sakamakon sauki irin na shari'ar sa da saukakawa ga  hukunce-hukuncen sa, da kuma tsarin sa mai adalci , da yalwar rahamar sa,  wanda  ta dulmuye har makiya  domin shi  baya aikata aiki na  halakarwa ko zalunci , ko kuma aikin kare –dangi   ko kuma   ramuwar gayya,  Allah madaukakin sarki ya ce : ( Ba mu turo ka ba , face rahama ga talikai )  kuma Allah madaukakin sarki ya ce : (  Lalle ne wannan Alkur'ani yana yana shiryarwa ga ( halayen ) wadanda suke mafi daidaita ). Suratul Isra'I 9
      Anyi mi'iraji da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi zuwa sammai  madaukaka  ya riski   wadannan  darajoji masu girma  sabo da irin  kyawawan halaye da bauta  da ke tattare da shi  , sabo da daukaka irin nata,  Ubangiji ya siffanta shi da ita  a wurin mafi daukaka da matsayi mafi girma , Allah madaukakin sarki ya ce  (Tsarki ya tabbata ga wanda ya yi tafiyan dare da bawan sa  . Isra'i Aya 1).
       Muna karantawa a tafiyan isra'i da mi'iraji  alaka mai karfi  da ke kulle tsakanin  masallacin Haram (Kaba) da wannan masallacin Annabi da  masallacin Aksa , cikin wannan akwai nuni ga al'uma kan kar ta yi sakaci game da sha'anin masallacin Aksa   sabo da matsayin shi da tsarkin shi da albarkan shi .
 Abu Zarri Allah ya kara yarda a gare shi ya ce :  ( na ce ya  Manzon Allah ! wani masallacin ne  na farkon da aka gina a doron kasa  sai ya ce: ''Masallacin Ka'aba  sai na ce sai wanne sai ya ce masallacin Aksa , sai na ce  nawa ne ratan da ke tsakanin su  sai ya ce : '' shekaru arba'in ''.)
        Manzon Allah  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Ba a nika gari sai ga masallatayya guda uku Masallacin Ka'aba da Masallacin Manzon Allah da  masallacin Aksa ) Buhari ne ya rawaito shi.
                 Masallacin Aksa da  tarihin shi da falalan shi yana tada wani kaimi na hadin kai tsakanin Musulmai ,  kuma yana karfafa dankon  'yan uwantaka domin bashi kariya  da tsarkake shi  daga kazantan  shirka da bata . Batun masallacin Aksa za ta wanzu   a  zukatan  mabiya  wannan Addinin  ba wani  abu da zai girgiza  kudurin mu kan haka  sabo da musun mai musu  ko kagen masu ketare iyaka.
           Isra'i da mi'iraji na koyar da mu cewa gaskiya a bayyane take , kuma za a bata kariya  duk yadda  farfagandan  masu karya ta kasaita   ko ta yawaita ,  to karya ginshikin ta na girgiza a kan kanshi kuma yana da rauni kuma yana da saurin halaka  ginin shi na lalacewa  Allah madaukakin sarki ya ce : (A'a muna jifa da gaskiya a kan karya sai ta  darkake ta , sai ga ta halakakka ) Sura Al-Anbiya  Aya na 18
    Annabi ya shiga garin Makka kewaye da dakin Ka'aba akwai gumaka dari uku da sittin (360) sai ya  rinka  sukan su da sanda a hanun shi yana cewa : ( Kuma ka ce  gaskiya ta zo karya ta lalace ,  lallai karya ta kasance lalatacciya) .  Suratul Isra'I Aya na 81
         Daga cikin mu'ujizozin Isra'i ; za mu tsinkayi wani darasi mai nauyi da fasaha  wanda hakan zai bayyana cikin kasancewan Allah na tare da bayinsa da taimaka musu da samun kulawansa daga duk wanda  ya yi riko da igiyarsa kuma da shiryarwarsa  , kasancewa tare da su bangaren kiyayewa da datarwa da taimako da karfafa   da kuma basu matsayi,  wannan  shine zai magance cutan masu tsarkin niyya  masu ribadi  masu bada kan su don kariya ga musulunci  da musulmai .
 Kuma  masu dako  da kulla makirci su sani  ikon Allah madaukaki  ya kere  duk wasu sabuba  don  ya bada taimako ga muminai ko da sun kasance 'yan kadan, sai Allah ya bada nasara ga muminai wadan da suka aminta da alkawarin shi Allah madaukakin sarki ya ce  : ( Da yawa kungiya kadan ta rinjayi  wata kungiya mai yawa da izinin Allah , kuma  Allah  yana tare da  masu hakuri) sura Al-bakara aya 249 Ya ce: ( To! Lalle ne , taimakon Allah yana kusa !) Al-bakara aya 214
       Umar Dan Khaddabi  yana cewa a wasiyyar sa da ya yi ga Sa'ad  Dan Abi wakkas  Allah ya yarda da su (  Lallai ku dinnan ba a baku nasara a kan makiyan ku sakamakon karfin tattali da shiri da  kuke da shi  sai dai ana baku nasara ne a kan su sabo da da'an ku ga Ubangijin ku da kuma sabon su a gare shi, idan kun yi dai-dai da su a sabo  sai su yi galaba a kan  ku  da karfin shiri da tattali ) .
       To idan kudus da masallacin Aksa   abin kulawa ne  da muhimmanci  ga zukatan musulmai to fa ya wajaba a gare su kankan da kai zuwa ga Allah  da ya kiyaye shi daga dukkan wata  kazantarwa,  kuma su yi adu'a ga mutanen Falastin  kan tabbatuwa da nasara  , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (  Ba wani musulmi da zai roki Allah madaukakin sarki da wani roko face sai Allah ya amsa mishi ita, ko ya tunkude mishi wata mummuna kwatankwacin ta , muddin bai roki wani abu na laifi ba ko yanke zumunci , sai  wani mutum ya ce a cikin mutanen : '' to, indai haka ne za mu yawaita adu'a''   , sai Annabi ya ce : abin da ke gun Allah shi ne mafi yawa .)
      HUDUBA TA BIYU:
Abubakar siddik  yana da wani maukifi (matsaya) wanda tarihi ya  adana,  wanda   ke cike da abin lura , mushirikai sun zo wa Abubakar a wayan garin  daren isra'I , don su bashi labari  cewa abokin shi na raya cewa anyi tafiyan dare da shi daga Makka zuwa baitil makdis  sannan ya dawo a wannan daren, a zaton su cewa zai karyata sahibin nashi (Annabi) sai ya fadi kalmarsa mashahuriya  wacce ta zama ka'ida da aka karbo  ( in har ya kasance ya fada to hakika ya yi gaskiya).
 Mushrikai su kansu sun san cewa a tarihin shi mutum ne mai gaskiya wanda baya karya  kuma  abin gaskatawa ne wanda ba a karyata shi   wannan shi ne zurfin gaskatawa daga zuciyan Abubakar  ya samu ne a dalilin imani , a lokacin  da imani yake  karkadawa yakini yake girgiza a wannan zamanin na mu  sai a samu wasu daga cikin mutanen mu wanda za su rika sanya shakku a addini       kuma suna  ja da abubuwan da suke tabbatattu a addini  , kuma suna fada da nassoshi na alkur'ani  suna karya ta sunna da hadisan Manzon Allah  su sanya hankulansu   su yi amfani da karamin  kwakwalwar su , su za su yi hukunci akan  nassoshi na kur'ani da hadisi,  amma muminai wadan da imani ya zauna a cikin zukatar su , kuma zuciyan su ta natsu da shi   to, misalin su shi ne fadin Imamu shafi'I Allah ya mishi rahama (  Mun yi imani da Allah da abin da ya zo daga Allah bisa  nufin  Allah  kuma munyi imani da Manzon Allah   da abin da ya zo daga Manzon Allah   ,  bisa muradin Manzon Allah)  
 
 
  
.


الجمعة، 15 ديسمبر 2017

MASALLACIN AKSA (KUDUS) A MUSULUNCI

Hudubar Masallacin Annabi  na shaikh Husain Al- Asshaikh  27-3- 1439 AH
Batu mai girma na cikin zuciyar kowani Musulmi : shine  batun Masallacin Aksa Kiblar farko na Musulmai kuma masallaci mai daraja na uku, kuma gurin da aka yi ISRA'I (Tafiyan dare ) da Shugaban Halittu.
shine batu mafi muhimmanci a yanzu wanda ba zai  gushe ba daga zuciyar  kowani musulmi daidaiku da al'uma, a duk yadda kalu bale ke fiskantar musulmai , da duk yadda musulmai suka samu kansu a ciki na fitintinu.
Kudus da abin da kasarta ta kumsa na masallacin Aksa batu ne na akida a gurin musulmai, kuma RIBADI ne mai  zurfin tarihi ba za a manta shi ba a a kowani yanayi ko a goge shi daga  kundin Musulunci, sabo da wani Alami ne daga cikin  alamomi na musulmai , kuma ginshiki ne daga ginshikanta da ba a sauya su, kuma guri ne mai tsarki daga cikin gurare masu alfarma a musulunci.
Ta yaya zai yiwu bayan ga littafin Ubangijinmu na tunatar da mu safiya da maraice da fadinsa Mai tsarki (Tsarki ya tabbata ga wanda yayi tafiyar dare da bawansa da dare daga Masallaci mai alfarma zuwa masallacin Aksa wanda muka sanya albarka a gefensa domin mu nuna masa daga Ayoyinmu lalle ne shi shi ne Mai ji Mai gani ) Al'isra 1
Masallacin Aksa daya ne daga cikin Masallatayya guda uku ne da ba ya halatta a nika gari zuwa ga wasu  sai zuwa gare su da sunan neman kusanci ga Allah da neman kari daga falalansa  kamar yadda hadisai suka zo daga Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi.
Kasar baitul Makdis nan ne kasar da za a hada halittu a tada su a ranar alkiyama , An karbo daga Maimuna baiwar Annabi ta ce : Ba mu labari game da baitul Makdis sai ya ce : (kasa ce na tattarowa da tadawa ).Ibnu Maja ya rawaito shi da isnadi Ingantacce.
Baitul Makdis na da matsayi mai girma a musulunci da falala na musamman, an karbo daga Abu Zarri Allah kara yarda a gare shi ya ce : (Muna tattaunawa a gaban Manzon Allah ko wanne ya fi falala Masallacin Annabi ko Masallacin Baitul Makdis, sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Salla guda a Masallaci na ya fi salloli hudu a cikin shi kuma madalla da  Masallaci, Yana dab da ya kasance mutum ya zama bai da abinda ya kai  igiyar dokinsa na daga kasa wanda zaa ga Baitul Makdis daga can  hakan ya fi mishi duniya da abin da ke cikinta) Hakim ne ya rawaito ya inganta shi Kuma Imam Azzahabi ya mara mishi baya wurin ingantawar.
Na daga cikin falalolin shi a musulunci shi ne gurin da aka yi tafiyar dare da Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi kuma daga nan ne aka tafi sama da shi,
An karbo daga Anas Dan Malik Allah ya kara mishi yarda cewa Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : An kawo min Alburak wata dabba ce fara mai tsawo ya fi jaki bai kai alfadari ba, yana sanya kofoton sa iya makuran ganinsa, ya ce Na hau shi har na zo baitul Makdis, sai ya ce sai na daure shi a tirken da Annabawa ke daure wa. Yace sai na shiga Masallaci na yi raka'a biyu a cikinsa, sai na fita sai Jibrilu ya zo min da kwano daya na giya daya kuma na nono sai na zami nono, sai Jibrilu ya ce ka zabi FIDIRA (Musulunci)  sai ya haura da mu zuwa sama.) Muslim ne ya ya rawaito.
Na daga cikin falalolin shi akwai hadisin Abdullahi Dan Amr Dan As  daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : (Yayin da Sulaiman dan Dawud ya kammala gina Baitul Makdis sai    ya roki Allah abu uku;  hukuncin da zai yi daidai da hukuncin sa, da mulkin da ba wanda ya dace ya samu irin shi a bayan sa ,  kada kuma wani ya zo wannan masallacin da ba abin da ya nufa sai salla a cikin shi face ya  fita daga zunuban shi kamar ranar da  mahaifiyar shi ta haife shi ) ,  sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :  - Amma biyun hakika an bashi su ina fatan  an bashi na uku) Nasa'i ya rawaito shi   da Ibn Maja Albani ya inganta shi .
           'YAN UWA A MUSULUNCI :
                    Kuma Baitul makdis da Masallacin Aksa na da falaloli masu girma  a Musulunci  wanda ya sanya malaman musulunci  tun a karnoni da suka shude ,  sukan ware su da talifi  daban-daban masu bin juna da rubutu daya bayan daya , game da falalan shi da girman hakkin shi ,    hakika  dunbin malamai na wannan al'umma    sun yi  rubutu takanas  akan shi:  Daga cikin su akwai Baha'uddin Ibn Asakir   a cikin littafin shi   ( Aljami'ulmustakasa fi  fada'ilil masjidi aksa )  . Daga cikin su akwai Aminuddin Ibn Hibatillah asshafi'I  a littafinsa (Kitabul Uns fi Fada'ilil Kudus),  a cikinsu  akwai Burhanuddin Alfazari  a littafin sa ( Ba'isul nufus ila ziyaratilkudus almaharus)    daga cikin su akwai Shihabuddin Ahmad Dan Muhammad  Almakadisi  a littafin shi  (  Musirulgaram ila ziyaratil kudus wa sham )  , daga cikin su akwai  Alhussainul Husaini a littafin shi ( Alraudulmugris fi fada'ilu baitilmakadis ) daga cikin su akwai  Ibnul jauzi  a cikin littafin sa ( Fada'ilul kudus )  daga cikin su akwai suyudi   a cikin littafin sa ( Ithafu Al'akhissa   bi fada'ili Almasjidil aksa) .
                    Da wannan ne ya sa musulmai gaba dayan su   ba za su yarda   su tabbatar da duk wani mataki da zai  taba batun kudus da  Masallacin Aksa ba  abu ne da yake mai tsarki a musulunci  baya halatta da kowani  irin hali  a taba shi  kai sai dai ma irin wannan tasarrufin ,  ba  abin da zai karawa musulmai  sai tsayuwa da jajarcewa da  dogewa   bisa ga neman hakkokin su tabbatattu  wanda ya yi daidai da   ginshikai  tabbatattu  don tantance gaskiya  da  tsawatarwa  ga zalunci , da kuma yiwa wanda a ka zalunta  adalci, kamar yanda  shari'o'i na sammai  da dokokin kasa da kasa suka tabbatatar .
               Kai duniya ma gaba daya a yau  ,  yana daukan duk wani mataki    irin wannan  abu ne da yake na keta dokokin da aka yi tarayya a kai na kasa da kasa, na cewa kudus   birnin tarayya    ne  na musulunci  ,  kuma gu ne mai tsarki daga  cikin tsarkakan gurare na musulmai .
     Lalle  batutuwa na al'uma ba a yin nasara ta hanyar huduba kawatacciya  ko kalmomi   masu   amsa amo ba ,   ba yi da wani amfani   ya- ma'abota musulunci  na nuna   bakin ciki da bacin rai  , ko kuma   daga  abubuwa na nuna   Allah wadarai da yawaita jerin gwano a titi don bayyana manufa , sau nawa  hakan ya faru da musulmai , da suka yi haka abin ya zo ya wuce ba a cimma manufa ba  tare da hakan  bai wuce ya zama wani abu na maida martani irin wanda ba zai tunkude zalunci ba ko ya kauda cuta ba , kuma ba zai hana tokobin mai ketare iyaka ba ko ketan mai keta ba,  to fa lalle mu sani ba makawa sai an ko ma ga Allah mai girma da daukaka  komawa na gaskiya ,  tare da kankan da kai da ikhlasi zuwa ga  Allah mai girma  da kasaita tabaraka wata ala .
         Al'uma tana samun nasara ne kawai idan ta taimaki al'uma ciki da waje ,  tana mai amsa kira  a waki'I, a duk lokacin da al'uma ta kasance mai riko da addinin Allah  tana mai girmama umarnin shi da shari'an shi  tana tunkuduwa  a  harkokin ta  daga addini na gaskiya  wan da  batun Masjidul Aksa ya tsayu a kai, to, a wannan lokacin ne za a samu waraka   da kuma nasara tabbatacce  , sa kuma samu mafita mai amfani , Allah madaukakin sarki ya ce : ( Idan kun taimaki Allah( wato addinin sa) zai taimake ku ( akan magautan ku ) Muhammad 7 .
        YA JAMA'AR MUSULMAI:
        Duk ranar da tsoratarwa na kur'ani da sunna ke galaba a kan zuciya ,  sannan hujjoji na waki'i suka gaskata haka a fagage na rayuwa  da lokutan ta , to musulmai ba za su taba fadawa cikin rauni ba , da walakanci  ba, kuma wani abu da zai same su na kaskanci da walakanci ,            Allah madaukakin sarki ya ce : (  Kuma kada ku yi rauni kuma kada ku yi bakin ciki alhali kuwa, ku ne mafiya daukaka idan kun kasance masu imani ) Ali Imrana 139    
            Hakika lokaci ya yi ga musulmai musamman   ga 'yan uwa da suke FALASDIN a halin suna tinkaran  kalubale mai hadari , wanda ta shafi amincin  al'iumman su gaba daya , da su hadu a kan da'a da tsoron Allah , kuma su yi sulhu bisa ga maslahohi na addini da lahira  kuma su  hadu don kauda  duk wani abin da zai kawo sabani  da rarrabuwa a tsakanin su,  su fita daga  dabar   gaba  zuwa ga farfajiya ta 'yan uwantaka , su fita daga wutan kiyayya , zuwa ga  haske na  zuciya  su kuma fita daga juyawa juna baya da  rarrabuwar kawuna , zuwa ga yafiya da hadin kai , su yi watsi da kungiyanci da bangaranci , su gudo zuwa ga ruhi na 'yan uwantaka na musulunci ,  da kauna na imani   A llah madaukakin sarki ya ce : (  Kuma ku yi da'a ga Allah da Manzon sa , kuma kada ku yi jayayya har ku raunana , kuma karfin ku ya tafi, kuma ku yi hakuri lalle ne Allah yana tare da masu hakuri ) Anfal 46
         A duk lokacin da musulmai suka tabbatar da   cikakken sako  na musulunci a waki'in su ba tare da sun tawaye ba kuma suka hakimantar da shi  hakimantarwa cikakke gamamme ,  kuma suka yi aiki da shi ciki da waje  , kuma suka rayu da musulunci don musulunci, to Allah ba zai tozartar da aikin su ba duk yadda wahala ta kai wahala  , ba za su taba ganin duhu ba  a kan hanyar su ta tafiya da kuma mafita  duk yanda musiba ta  yi girma  muddin  akan tafarki na musulunci suke tafiya  , kuma suna masu bin  hukunce –hukuncen shi  , kuma suna masu koyi  da  riko da   sunnan Annabi,   Allah madaukakin sarki ya ce : (  Lalle ne Allah yana   bada kariya ga wadanda suka yi imani ,) Hajj 38  .
             Amma fa muddin al'uma ta kasance   ta dauwama  wutan sha'awe-sha'awe na haramun na  kadawa  ,  ya yi awun gaba da ita  , abubuwa na shagaltarwa na bata na fisganta     taguwar son rai na fandarewa da shubuhohi na dibanta   to a wannan lokacin  za ta tinkari   ambaliyar fitintinu da jarabawowi  da nau'uka na bala'o'I masu yawa , Allah madaukakin sarki ya ce : (   Kuma abin da ya same ku na wata masifa  to, game da abin da hannayen ku suka sana'an ta ne ,  kuma ( Allah) yana yafewa ( wadan su laifuffuka ) masu yawa)  Shura 30 .
      Allah madaukakin sarki ya ce game da  yakin uhud : (  Shin kuma a lokacin da wata masifa hakika ta same ku, alhali kuwa kun samar da  biyun ta kunce : ( daga ina wannan yake  ka ce daga wurin rayukan ku ya ke )     lalle ne Allah akan dukkan komai mai ikon yi ne) Ali Imran 165.
       YA KU JAMA'AR MUSULMAI :
        Ba makawa  al'uma ta sakankance da wasu martabobi na yakini dukkan su  ba za su tsiratar da ita daga matsatsi da ta shiga ba ko kuma ta kawar da ita daga yanayi da ta shiga ba na bakin ciki face musulunci na gaskiya akan akida na tauhidi tacecce da bin sunna ingantacce ,  wanda yake shi ne tafarki na dai-dai   a littafi da  sunna bisa fahimtar magabata na al'uma  to wannan shi ne tushe na asali kuma shi ne ginshiki mai karfi na samun  daukaka da jagoranci , da kuma samun taimako da daukaka Allah madaukakin  sarki yana cewa : ( Wadan da sukayi imani kuma basu gauraya imanin su da zalunci ba wadan nan suna da  suna da aminci kuma su ne shiryayyu) . An'am 82
           Alkawari ne na tabbas  kuma labari ne na gaskiya ( Kuma ya kasance tabbatacce, taimakon Muminai wajibi ne a kan mu) ARRUM 47
        ( Rinjaye ga Allah ya ke kuma da manzon sa  kuma da muminai  kuma amma munafukai ba su sani ba ).  Munafikun 8  ( Hakika muminai sun rabauta ) muaminun 1

         YA KU JAMA'AR MUSULMAI:
    Lallai wajibi ne ga dukkan musulmai   bisa sabanin matsayin su    su tsaya bisa batu mai tushe  wato batun masallacin Aksa da kuma  Baitul makdis  da kasar FALASDIN  su tsaya tsayuwan daka a irin mahanga na musulunci   ba wanin sa ba  ta hanyar hadin kai mai tasiri , da kyakkyawan  motsi wanda zai kai ga samar  da da mai ido da cimma manufofi   Allah madaukakin sarki ya ce : (  Kuma ka ce ku yi aiki sa'annan Allah zai ga ayukan ku  da Manzon sa da muminai ) Tauba 105 .
            Ba makawa sai an yi amfani da basira mai karfi da cikakkiyar hikima   wanda da ita ne al'umar musulmi za su iya tinkarar kalubale   daban-daban kuma ko wani iri  wanda zai yi daidai da hadin kai  da kuma da'iran taimakekeniya da karfafan juna ,   da taimakon juna ba rikici  ko fada ko zage-zage ,  ko neman wani laifi  da wannan ne za a toshe zaluncin masu zalunci al'uma ta kai ga nasara  mai karfi  .
         Ba makawa sai anyi dubi bisa batu na al'uma da dubi wanda  yake akwai hangen nesa a ciki,  wanda zai tashi daga  motsi na zahiri  zuwa ga  bigire  mai tasiri  da kuma ayyuka  da aka auna su  wanda za su kai ga rinjayi  cikin jerin gwanon hada karfi da karfe  da kyakkyawan tsari don a kai ga matsaya na gaskiya wanda ya taso daga   tuta na addinin musulunci mai hikima , , da kuma abin da shari'ar shugaban Annabawa da Manzanni ta kebanta da shi, wanda ita ce za ta iya jan ragamar duniya gaba daya  zuwa ga wayewa da aminci da walwala da hadin kai da zaman lafiya .
        Dole ne al'uma ta tafi  akan kokari gurin hada karfi da karfe  don fiskantar kalubale  da salo da ya dace  da kuma  tattaunawa  mai kaiwa ga manufa nesa daga salo na cece ku ce da kuma   kalmomi na bangaranci  da ife-ife da ta'assubanci  ko agender  na wata kasa  , to wadan nan wasu abubuwa ne da ba za  su haifar  da wani abu ga al'uma ba sai sharri da bala'I  Allah madaukakin sarki ya ce : ( Sai ( al'umar) suka yayyanke al'amarin su  a tsakanin su guntu-guntu  kowace kungiya suna masu farin ciki da abin da yake a gare su ) Muaminun 53 .
    Ba makawa wurin amsa kiran fadin  Allah madaukakin sarki ( Lalle ne wannan ita ce al'ummar ku , ta zama al'umma guda kuma ni ne Ubangijin ku sai ku bauta mini )
                HUDUBA TA BIYU
     Kasar haramaini masu mulkin su kuma da talakawan su a ko yaushe suna tsaye tsayin daka   wurin bada kariya ga dukkan batutuwa na musulunci da kuma na larabci musamman batun FALASDINU , to matsayan wannan kasar da mahukuntan ta   game da batun FALASDINU  abu ne da yake tabbatacce ba za su girgiza  ko su sauka  daga kanta ba  batu ne dake cikin abu mafi muhimmanci  da suke iya kokarin su  ta fiskoki daban-daban , musamman  bangarorin da suka shafi bangarorin tattalin  arziki da na siyasa.
     A zamanin mai hidimawa masallatayya biyu masu alfarma sarki Salman  duniya ta shaida  ba da kulawa da cigaba da wannan tafiya  karkashin kulawan mai girma Allah ya kara kiyaye shi  sabo da la'akari da yayi da ita batu ne na musulunci   kafin ta zama batu ne na larabawa ,  wannan kasan tana ganin wani nauyi ne da ke kanta  kuma tana bautawa Ubangijinta da shi , kuma tana samun daukaka da ita da kuma hukuncin sakon ta na musulunci  da matsayinta a duniyance ,  sabo da haka  ba wani gurbi na neman kari ga duk wani mai kin gaskiya  bisa ga kokarin wannan kasa     haka kuma da mai  musanta hakan , da kuma  'yan sashi-fadi ,  da kuma mai kawo shakku   cikin   jinsin mu (na larabawa)  bisa ga kokarin da wannan kasa  take tashi da shi , to, ya wajaba a gare su da su ji tsoron Allah su sani cewa  duk wani dauki ba dadi  da ake yi don taba wannan kasa    mai alfarma to lalle fa suka ne ga fadar musulunci  da kuma suka ga wadanda suke rike da tutar bada kariya a gare shi , to, yin haka  kamar wata tawaga ne  da suna yaudarar kawunan su  kuma suna makirtar al'umar su .
      Allah madaukakin sarki ya ce : ( Suna yaudarayya da Allah da wadan da suka yi imani alhali ba su yaudarar kowa face kansu ,  kuma basu sakankancewa ) Bakara 9.
Kuma su sani wannan kasan tana tafiya ne  a kan tsari na musulunci  wanda ba ya bukatan  kari sabo da yabon mai yabo  ko kuma  jafa'i  sabo da farfagandan makiya masu fatan sharri  ga kasan,  Allah na sane kuma yana ganin nufin su.  

                        

الجمعة، 1 ديسمبر 2017

NI"IMAR RUWA GA AL"UMA

HUDUBAR  MASALLACIN ANNANBI  TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI NA SHAIK ABDULMUHSIN AL-KASIMI NA 13- 3-1439 AH
 HUDUBAR FARKO :
  Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah madaukakin sarki  muna gode mishi kuma muna neman taimakon sa , muna neman gafarar sa  , kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunan mu , da munanan ayyukan mu , duk wanda Allah ya shiryar da shi ba bu mai batar da shi , duk wan da ya batar kuma babu mai shiryar da shi , na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya , kuma na shaida Annabi Muhammadu bawan sa ne kuma Manzon sa ne tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan sa  da sahabban sa da aminci tabbatacce mai yawa .
 BAYAN HAKA :
Ku ji tsoron Allah -ya ku bayin Allah- hakkin tsoron sa   da tsoron Allah ne ake haskaka basira da zukata  kuma ake kankare kusakurai  da zunubai ,.
    YA KU MUSULMAI:
Allah mai tausayi ne ga bayinsa , yana tausaya musu ta inda ba su sani ba,  yana sanya musu sababi na maslahohin su ta inda ba su zata ba ,  lalle shi mai kyautatawa ne kuma mai rahama  ne   mai kyauta kuma mai karamci,  ya yalwata ni'imomin shi a gare mu na bayyane da na boye,  Allah madaukakin sarki ya ce : ( kuma idan kun kidaya ni'imar Allah ba ku iya lissafa ta )
Akwai  wata   ni'ima mutane basu isa su wadatu ga barin ta ba a ko wani hali, Allah ya sanya ta  dalilai ne na tabbatar da rububiyyar sa  Allah madaukakin sarki ya ce : (  Shin kuma ba su gani ba , cewa lalle mu muna kora ruwa zuwa ga kasa  kekasasshiya  sa'annan mu fitar game da shi wata shuka  , wadda dabbobin su , da su kansu ke ci  daga gare ta  ? ashe fa ba su gani ba ? )
                        Allah ya gagari bayin shi da su kawo kwatankwacin ta  (  Shin    kuma kun ga ruwa wannan da kuke sha  shin ku ne kuke saukar da shi daga girgije  ko kuwa  mu ne masu saukarwa ? Da mun so da mun mayar da shi ruwan zartsi to don me ba ku godewa ) , gaibi ne, ba wanda ya san lokacin shi na tabbas da gwrgodon shi da amfanin shi sai Allah  , Allah madaukakin sarki ya ce : ( Lalle Allah a wurin sa ne kawai sanin sa'a  yake , kuma yana saukar da girgije  kuma yana sanin abin da yake a cikin mahaifannai).
 yana daga cikin  hujjoji na tabbatar da uluhiyyar Allah   da cancantar shi da a bauta mishi shi kadan shi , akwai saukar da ruwa daga sama  Allah madaukakin sarki ya ce :(  kuma ya saukar da ruwa daga sama  sa'annan ya fitar da abinci  daga 'ya'yan itace game da shi  )  .
                    Kuma shi din yana daya daga cikin dalilai na fitarwa daga kabari da tadawa,  Allah madaukakin sarki ya ce:( Kuma akwai daga ayoyin sa  cewa lalle kai kana ganin kasa kekasasshiya , to, idan mun saukar da ruwa a kanta sai ta girgiza kuma ta kumbura, lalle wannan da ya raya ta hakika , mai rayar da matattu ne, lalle shi mai ikon yi ne akan ko wani abu ) da shi ne Allah ya ke rahama yake kuma azabtarwa ,  Allah madaukakin sarki ya ce:( kuma da sun tsayu sosai akan hanya da lalle mun shayar da su daga ruwa mai yawa) . 
         Ruwa daukaka ne kuma da girma da izza  ne, kuma al'arshin mai rahama yana kan ruwa, Allah madaukakin sarki ya ce : ( Al'arshin sa ya kasance a kan ruwa )  yana daga cikin ni'imomin Allah masu yawa  wanda Allah ya yi shi  har ga wadanda suka gabace mu  ni'ima da shi  , wanda ya gode daga cikin su Allah sai ya kara mishi, wanda kuma ya butulce  mishi sai Allah ya azabtar da shi , Allah madakakin sarki ya ce : ( Shin ba su gani ba  da yawa muka halakar da wani karni daga gabanin su , mun mallaka musu, a cikin kasa abin da  ba mu mallaka muku ba , kuma muka saki  sama akan su tana ta zuba ).
            Sabo da kasancewar sa ni'ima   mai girma , Allah ya turo gaba gare shi abin da  ke albishir da zuwan shi Allah madaukakin sarki ya ce : ( kuma shi ne ya aiko mana  iskokin bushara  gaba ga rahamar sa  )  yana daga cikin rahamar Allah ga bayin sa  ya jefa  farin ciki da annashuwa ga zukatan su ,  dalilin dubin su  zuwa ga abin da  suke kallo na daga ni'imomin shi  abin sabontarwa ,  yana daga cikin abin da  yake sanya walwala  ga zukata jin dadin da suke yi na saukar ruwan sama  bisa kasa  Allah madaukakin sarki ya ce : (  Kuma shi ne  ke saukar da girgije (ruwa) a bayan sun yanke kauna  kuma  yana watsa rahamar sa   alhali kuwa shi ne majibinci mai godiya) .
          Kuma kasa na farin ciki da gabatowan sa , sai  ta girgigiza  kuma ta kumburo  ta fitar da adon ta  Allah madaukakin sarki ya ce : ( Sa'annan idan muka saukar da ruwa  akan ta sai ta girgiza kuma ta kumbura , kuma ta tsirar  da tsiri daga ko  wani nau'I mai ban sha'awa)  da shi ne kasa ke rayuwa bayan mutuwar ta , Allah madaukakin sarki  ya ce : (  kuma muna saukar da ruwa daga sama  sai mu raya kasa da shi bayan mutuwar ta )   .
           Kuma halittu suna bishara ga  junan su da gabatoawan shi Allah madaukakin sarki ya ce : ( Sa'annan   idan Allah ya sami wadan da ya so daga bayin sa sai  ga su  suna bishara da shi )  kuma yana cikin sabuba na yardan Allah ga bawa in ya gode mishi game da ita ,               Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (  Lalle Allah na yarda game da bawa da ya ci abinci ya gode mi shi game da shi ko ya sha abin sha sai  ya gode mishi sabo da ta  )  MUSLIM NE YA RAWAITO .
        Ruwa  jinsin shi guda ne tare da babbancin lokuta da kuma wurare, Allah ya halicce shi ba launi  ya samar da shi ba tare da dandano ba  kuma ya saukar da shi ba tare da wari ba ,  abu ne mai dadi da yake shiga cikin ciki mai karfi  yana zuwa ya cike  kwarurruka  ya haura duwatsu , halitta ne mai girma  idan ya sauka a matsayin azaba babu mai yaye shi sai Allah , Allah madaukakin sarki ya ce : ( Zan tattara zuwa ga wani dutse ya tare ni daga ruwan  ,(NUHU ) ya ce : babu mai tsarewa a yau daga umarnin Allah face wanda ya yiwa rahama ,  sai taguwar ruwa ta shamakace a tsakanin su  sai  ya kasance daga wadanda aka nutsar).
          Amfaninsa ba shi kididdiguwa mai yawan tsarki ne ga gardi ga dadi mai taimakawa Allah madaukakin sarki ya ce :   (kuma  Muka saukar daga sama ruwa mai yawan  tsarki )  yana tsarkake jiki  da zukata, Allah Madaukakin Sarki ya ce : (  Alokacin da Allah ya ke rufe ku da gyanngyadi    domin aminci daga gare shi kuma yana saukar da ruwa daga sama a kan ku domin ya tsarkake ku da shi  kuma ya tafiyar da kazantar shaidan  daga barin ku) .
        Allah ya halicce shi da albarka  to sai ga 'yan kwayoyi kadan   kasa na rayuwa da su da wanda suke cikinta  Allah ya ce : (Kuma   Muka saukar da ruwa  daga sama mai albarka), da shi ne Allah ya ke tsirar da dukkan shuke-shuke  Allah madaukakin sarki ya ce : (   Sa'annan muka fitar game da shi daga dukkan 'ya'yan itace   )  Allah ya sanya shi mai kankara ne ga zunubai da kusakurai a cikin alola Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (  Idan bawa musulmi ya yi alola – ko mumini ya wanke fiskan sa  sai ya fita daga fiskarsa  dukkan kusakuran da ya kalla da idanuwan nasa tare da digon ruwan ko tare da digon karshe na ruwan, to idan ya wanke  hannayen sa sai ya fita daga hannayen nasa dukkan kusakuran da hannayen nasa suka aika ta  tare da  ruwan , ko tare da digon karshe na ruwan -  to idan ya wanke kafafuwan sa   sai  dukkan kusakuran da yayi tafiya da wannan kafan zuwa gare ta  ya fita tare da ruwan – ko tare da digon karshe na ruwan-  har ya fita tsarkakake daga  zunubai  ) MUSLIM NE YA RAWAITO
           Saukan sa zuwa doron kasa  bisa gwargwado  ya ke , ana kidanya adadin digon, Allah madaukakin sarki ya ce : (    Muka saukar da ruwa daga sama bisa gwargwado)  karin sa daga gwargwadon sa wani azaba, ne  aya mai ban mamaki  ana kiyayeshi  acikin kasa kuma yana da taskoki acikinta ba wanda yasansu sai Allah, Allah madaukakin sarki yace: ( shin baka gani bane Allah  ya saukar da ruwa daga sama  sa'an nan ya gudanar dashi yana mare mari acikin kasa ),wani sashin na fita daga dutse Allah madaukakin sarki yace( kuma lallai ne daga duwatsu ,hakika akwai abin da maremari suke bubbuga daga gareshi kuma lallai ne daga garesu hakika akwai abin da yake tsatsagewa har ruwa ya fita daga gareshi )mai muujiza idan ya sauka a doron kasa, kasa keka sassa sai ya canza launinta zuwa ga abin kallo mai ban kaye, Allah madaukakin sarki yace : (Ashe ba ka gani ba lalle ne  Allah ya saukar da ruwa daga sama sai kasa ta wayi gari koriya ? lalle Allah mai tausayawa ne mai kididdigewa )
Halittan Allah  da ya yi ga ruwan sama a matakansa alamari ne na ban mamaki Allah madaukakin sarki ya ce (Allah ne wanda ke aika iskoki sai su motsar da giragizai  sa'annan ya shin fida shi a cikin sama yadda ya ke so kuma ya sanyashi wani babbake sannan ka ga ruwa na fita daga tsakaninsa ,sa'annan idan Allah ya sami wadan da ya so daga bayinsa sai gashi suna bushara da shi .)
Na daga cikin cikan ni'mar Allah a gare mu bayan saukarsa kiyaye shi a kasa bayan saukarsa, Allah Madaukakin Sarki ya ce : (sa'annan muka saukar da ruwa daga sama sa'annan muka shayar da ku shi, kuma baku zama masu taskacewa a gare shi ba.)
Ni'ma ce makusanciyar riska mai saukin samuwa, idan bayi sun sabawa  Ubangijin su sai ya nesatar da su daga gare ta, Allah Madaukakin sarki ya ce : (ka ce ko kun gani idan ruwanku ya wayi gari fakakke to wane ne zai zo muku da ruwa wani mai bubbuga).
Kamar yadda wannan take ni'ima ce – to wannan iska mai taushi da  kananan digo wanda ake ni'imta bayi da shi to ta na iya sauyawa da umarnin Allah zuwa ga azaba, Allah ya halaka wasu mutane da wannan ruwa sabo da juyawa Allah baya da suka yi, shi ne farkon azabar da aka yi wa wata al'uma, Allah Madaukakin sarki ya ce :(Mutanen Nuhu sun karyata a gabaninsu ,sai suka karyata BawanMu ,kuma suka ce, Shi mahaukaci ne " kuma aka tsawace shi)(Saboda haka ya kira ubangijinsa (ya ce),lalle ni an rinjayeni sai ka yi taimako)
(sai muka bude kofofin sama da ruwa mai zuba ) (kuma muka bubbugar da kasa ta zama idanun ruwa sannan ruwa ya hadu akan wani umarni da aka riga aka kaddara shi. Kuma muka dauke Nuhu akan jirgi na alluna da kusoshi. Tana gudana a cikin kiyayewarmu domin sakamako ga wanda aka yi wa kafircin).Alkamar 9-14
Fir'auna ya yi girman kai ga musa ya mishi alfahari da ruwa sai ya ce : (Ashe mulkin Masar ba a gare ni ya ke ba , kuma wadannan kogunan  suna gudana daga karkashi na?) Zukhruf 51
Sai Allah ya halaka shi sakamakon girman kai da ya yi, ya sanya shi abin lura ga mutane,
Allah Madaukakin sarki ya ce : (Har a lokacin da nutsewa ta riske shi yace : Na yi imani cewa Hakika babu abin bautawa face wannan da banu Isra'ila suka yi imani da shi kuma kuma ni ina daga Musulmai). Yunus 90
 Ya kasance malalin Arimi (Dam) ga mutanen  Saba'i ya yin da suka kafurcewa ni'imar Allah sai Allah ya kekketa su da shi kekketawa, Allah Madaukakin sarki ya ce :(sai suka bijire saboda haka muka saki malalin arimi(dam) a kansu, kuma muka musanya musu gonakinsu biyu da wadansu gonaki biyu masu 'ya'yan itace kadan : Talakiya da goruba da wani abu na magarya kadan ). Saba'I 16.
Hakika Allah ya sanya shi nasara ga muminai a yakin badar, Allah Madaukakin sarki ya yace : (A lokacin da Allah ya ke rufe ku da gyangyadi  domin aminci daga gare shi , kuma yana saukar da ruwa daga sama a kanku, domin ya  tsarkake ku da shi, kuma ya tafiyar da kazantar shaidan daga barinku, kuma domin ya daure akan zukatanku, kuma ya tabbatar da kafafu da shi.) Anfal 11
Kuma shi yana daga cikin ni'imomin da idanuwa ke jin dadi da shi a cikin aljanna mai ni'ima.
Allah Madaukakin sarki ya ce : (A cikin ta akwai wadansu koguna na ruwa ba mai sakewa ba).
Kuma 'yan wuta suna neman agaji da shi  Allah Madaukakin sarki ya ce : (Kuma abokan wuta suka kirayi abokan Aljanna cewa , ku zubo a kanmu daga ruwa ko kuwa daga abin da Allah ya azurta ku, su ce : lalle ne Allah ya haramta su a kan kafurai) Araf 50
Bayan haka ya ku Musulmai!
To ruwa na daga cikin ayoyin Allah da ke wajabta imani, Allah Madaukakin sarki yace : (Kuma muka sanya dukkan komi mai rai daga ruwa shin ba za su yi imani ba? ) Anbiya' 30
Aya ce mai ban kaye ba wani da ke ja cewa daga Allah ne, ba kuma wanda  ke samar da shi koma bayansa. Allah Madaukakin sarki yace : ( Kuma lalle idan ka tambaye su wane ne ya saukar da ruwa daga sama har ya rayar da kasa,game da shi a bayan mutuwar ta lalle suna cewa, Allah ne).
Kuma wani ni'ima ce  mai girma daga Allah,tana tare da mu a kowani wuri da  lokaci, to ya wajaba a gare mu mu yi godiya game da ita, da tunani  cikin sha'aninta , da biyayya ga Mahaliccinta, kuma kada mu rudu da falalar da Allah ya mana da ita, kar mu yi barna a cikinta, kuma ya dace mu rike ta abin taimako don raya lahirar mu.
Ina neman tsarin Allah daga shaidan abin jefewa.
(sai nace ku nemi gafara daga Ubangijinku  lalle ne shi ya kasance mai  gafara ne, ya sako girgijen sama akan ku da ruwa mai bubbuga).
Allah ya sanya mini albarka ni da ku a cikin Alkur'ani Mai girma.
Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah bisa kyautatawarsa , da godiya bisa datarwarsa da baiwarsa, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah ina mai girmama sha'aninsa, na shaida Annabinmu Muhammad bawansa ne kuma Manzo sa ne, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabbansa, da aminci tabbatace mai yawa,
Ya ku musulmai !
Allah Mai azurta bayinsa ne mai biyayyansu da fajirinsu, (Ba wata dabba  a cikin kasa face ga Allah arzikinta ya ke)Hud 6
Kuma arzikin  Ubangiji yana sauka ne da biyayya a gare shi, da tuba zuwa a gare shi, Allah Madaukakin sarki ya ce :   (Kuma da lalle mutanen Alkaryu sun yi imani suka yi takawa da mun bude Albarkoki a kansu daga sama da kasa)
Kuma godiya na kiyaye ni'ima yana shelanta  karinta Allah Madaukakin sarki ya ce : (Kuma a lokacin da Ubangijinku ya sanar, lalle ne idan kun gode,hakika ina kara muku, kuma lalle ne idan kun kafirta, hakika azaba ta tabbas mai tsanani ce) Ibrahim  7
Sannan ku sani Allah ya umarce ku da salati da aminci ga Annabin sa ….)