الخميس، 27 أبريل 2017

MIKA WUYA GA ALLAH

HUDUBAR JUMA'A TA MASALLACIN ANNABI  2 GA SHA'ABAN 1438 AH NA SHAIKH HUSAINI AL- ASSHAIK.
HUDUBAR FARKO
A LOKACIN DA DUNIYA KE KUSA TA ZAMA TA HADE GU GUDA SAKAMAKON BUNKASA NA ILIMI DA CI GABA DA DAN ADAM KE SAMU,SAI GA FANDAREWA NA MANHAJA NA YAWAITA DA FITINTINU MASU HADARI,WADANDA KE SHAFAR ADDINI  NA GASKIYA DA KYAWAWAN DABIU, HAKA NE DAN ADAM YAKE DA ZARAN YA SAMU WATA DAMA DON FADIN ALBARKACIN BAKINSA DA TUNANINSA DA MANHAJARSA.
KU SAURARA! LALLE MUSULMAI A YAU SUNA CIKIN BUKATAR LAFIYAYYEN MA'AUNI DA ZASU BANBANCE TSAKANIN ABU MAI INGANCI DA MARA KYAU, TO AI SUNA DA WASU TABBATATUN ABUBUWA DAGA UBANGIJI DA WA SU KA'IDOJI DAGA ALLAH WADANDA ZAI TSALLAKA DASU ZUWA BAKIN GABA NA TSIRA DAGA DUKKAN WATA FIKIRA MAI ILLA DA KUMA FANDARARREN TSARI,WANDA ZAI HASKAKA MUSU HANYA TA MUSULUNCI DA MIKAKKAR MANHAJI (YA KU MUTANE HAKIKA WATA HUJJA TA ZO MUKU DAGA UBANGIJINKU, MUN SAUKAR MUKU DA HASKE BAYYANANNE, TO AMMA WADANDA SUKA YI IMANI DA ALLAH KUMA SUKA KANKAME SHI,TO ZAI SHIGAR DA SU CIKIN WATA RAHAMA DAGA GARE SHI DA FALALA YA SHIRYAR DA SU ZUWA GARE SHI TAFARKI MIKAKKE.)
RAYUWA TA TSIYATA BAZA TA KAU BA, HAKA BA ZAA FITA DAGA WAHALHALU BA A DUNIYA DA LAHIRA  HAR SAI MUTANE SUN MIKA WUYA GA MANHAJIN LITTAFIN UBANGIJINSU,SU KUMA MIKA WUYA GA KOYARWAR ANNABINSU DA AKA TURO MUSU.
 LALLE BABBAN GINSHIKI NA GYARUWA DA RABAUTAR AL'UMAR MUSULMAI, DAIDAIKUN SU DA GABADAYANSU, SHI NE MIKA WUYA NA GABADAYA GA SHARIAR ALLAH MABUWAYI DA DAUKAKA.A KYALE DUK WANI ABU DA KAI KOMO A MIKA WUYA GA HUKUNCIN ALLAH MAI GIRMA DA DAUKAKA DA NA MANZONSA TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI.
LALLE WAJIBIN MUSULMAI SHINE GIRMAMA UMARNIN ALLAH MAI GIRMA DA DAUKAKA, DA MURAKABARSA A BOYE DA BAYYANE, CIKIN TSANANI DA SAUKI, CIKIN ABIN DA RAI KE SO DA WANDA BAI SO. CIKIN YANAYI NA CUTA DA AKASINTA, DA LOKACIN YALWA DA LOKACIN KUNCI, ALLAH MADAUKAKIN SARKI YA CE, (BAI DACEWA GA MUMINI KO MUMINA IN ALLAH YA YI HUKUNCI DA MANZONSA NA WANI UMARNI DA SU KASANCE SUNA DA ZABI CIKIN UMARNINSU, DUK MAI SABA WA ALLAH DA MANZONSA TO YA BATA BATA BAYYANANNE).
WANNAN AYAR MAI GIRMA TANA KAFA MANA WATA KA'IDA NA ASALI WANDA YA WAJABA TA KASANCE TSARI NE GA RAYUWAR MUSULMAI, KUMA YA ZAUNA CIKIN ZUKATARSU, KUMA SU ZARTAR DA SHI A WAKI'INSU, LALLE SHI DIN NAN TUSHE NE MAI GIRMA WANDA KE WAJABTAWA MAI KIWO DA WANDA AKE KIWATA, GA DAIDAIKU DA KUMA AL'UMA DA SU AMSA KIRAN UMARNIN ALLAH MAI GIRMA DA DAUKAKA, DA NA MANZON ALLAH TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI, A DUKKAN YANAYI  DA SAURAN BANGARORI,DA FAGAGE NA RAYUWA DA KAI KOMO NA YAU DA KULLUM.
WANNAN AYAR TANA TABBATAR DA WATA KA'IDA MAI GIRMA, DA KE NUNA NA DAGA CIKIN ABIN DA KE HUKUNTA IMANI, DA SIFFARSA DA RUKUNANSA AKWAI GAGGAWA ZUWA GA NEMAN YARDAR ALLAH MABUWAYI DA DAUKAKA,DA NEMAN SHIRIYA DAGA KOYARWAR MANZON ALLAH TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI,DA RUSUNAWA DA SALLAMAWA DA MIKA WUYA GA HUKUNCIN ALLAH DA HUKUNCIN MANZON ALLAH TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI A DUKKAN WANI SHA'ANI NA DUNIYA DA ADDINI, HAR YA ZAMA BAWA BAI DA WANI ZABI KO GANIN DAMA WURIN ZARTAR DA UMARNIN ALLAH MAI GIRMA DA DAUKAKA DA UMARNIN MANZONSA DUK YANDA RAI DA SHA'AWE SHA'AWE SUKA KARKATA ZUWA GA WANINSA, NA DAGA CIKIN ABIN DA IMANI KE LIZIMTAWA AL'UMA MUSULMAI SU RAYU KARKASHIN INUWA NA SHARI'A MAI TSARKI, KUMA YA ZAME ABIN DA RANSA KE SO DA ABIN DA ZAI FISKANTA SHI NE BIYE WA ABIN DA YA ZO A LITTAFIN ALLAH MAI TSARKI DA SUNNAR MANZONSA  A HARKOKINSA NA YAU DA KULLUM DA DUK WANI KAI KOMO NASHI.
WANNAN SHI NE TAFARKIN MUTANEN KWARAI MASU RABAUTA, KUMA TAFARKIN MASU TAKAWA DA CIN NASARA.
IMAMU AHMAD YA RAWAITO CEWA ANNABI TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI YA NEMAWA JULAIBIB WATA MACE DAGA CIKIN ANSAR A GUN MAHAIFINTA, YA ZO A KISSAR MAHAIFIYARTA TACE; ANNABI YA RASA WANDA ZAI NEMAWA SAI JULAIBIB TO NA RANTSE DA ALLAH BA ZA MU AURA MISHI BA, SAI YARINYAR TA CE :SO KU KE KU KI BIN UMARNIN ANNABI BAYAN  SHI YA YARDA DA SHI GARE KU TO KU AURA MISHI, SAI ANNABI YA MATA ADU'A YANA CEWA :YA ALLAH KA KWARARA ALHERI GARE TA KWARARAWA, KADA KA SANYA MUSU WAHALA A RAYUWA, TO SAI TA ZAMA BA WATA MACE CIKIN ANSAR DA TA KAI TA CIYARWA.
YA KU MUSULMAI!
LALLE NA DAGA CIKIN ALAMOMI NA IMANI INGANTACCE: TSAYAWA KAN DOKOKI NA ALLAH DA LAZIMTAR BIN SUNNAR MANZON ALLAH TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI DA GIRMAMA TARIHINSA DA TAFIYA AKAN KOYARWARSA, YA ZO DAGA DA'WUS KAN CEWA YA TAMBAYI ABDULLAHI DAN ABBAS GAME DA RAKA'OI BIYU BAYAN LA'ASAR SAI YA HANE SHI, SAI IBNU ABBAS YA KARANTA WANNAN AYAR (BAI DACE BA GA MUMINI KO MUMINA BA). AN KARBO DAGA SALIM DAN ABDULLAH KAN ABDULLAHI DAN UMAR YA CE: NA JI MANZON ALLAH TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI YANA CEWA : (KAR KU HANA MATAYENKU ZUWA MASALLACI IDAN SUN NEMI IZININKU, SAI BILAL DAN ABDULLAHI YA CE ; ( WALLAHI ZA MU HANA SU. SAI ABDULLAHI YA FISKANTO YA MISHI MUMMUNAR ZAGI BAN TABA JI YA YI WA WANI IRIN SHI BA. YA CE INA BAKA LABARIN ANNABI YA CE KANA CEWA ZAMU HANA SU). MUSLIM NE YA RAWAITO.
A RAYUWAR SAHABBAI DA TABI'AI AKWAI IRIN WANNAN  DA YAWA WURIN GIRMAMA UMARNIN ALLAH DA UMARNIN MANZON ALLAH TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI DA KUMA DIMANTAR BIN UMARNINSU DA KIYAYE SABA MUSU.
YA 'YANUWA MUSULMAI!
LALLE MAGABATA NA WANNAN AL'UMA SUN FI KOWA TSANANIN TSAYUWA DON TUNKUDE DUNIYA DA KYALA KYALANTA DA RABAUTANTA DA NASARARTA, DA AMINCINTA DA ZAMAN LAFIYARTA.
AMMA LOKACIN DA SUKA TSAYA INDA ALLAH YA YI UMARNI, SUKA ZABA WA KANSU ABIN DA SHARIAR ALLAH TA ZABA MUSU SAI SUKA RABAUTA DA ALHERIN DUNIYA DA WALWALARTA DA YARDAN ALLAH A LAHIRA.
AN KARBO DAGA A'ISHA ALLAH KARA YARDA A GARE TA TA CE:( ALLAH YA JIKAN MATAYEN MUHAJIRAN FARKO YAYIN DA ALLAH YA SAUKAR DA :( KUMA SU YI LULLUBI DA MAYAFANSU AKAN ALJIHOHINSU) SAI SUKA TSAGA SAMAN MAYAFANSU SUKA YI HIJABI DA SU.) BUHARI NE YA RAWAITO SHI MUALLAKI DA ABU DAUDA DA SANADINSA INGANTACCE.  
IBNU HAJAR YACE : KWARJALLAYENSU, JAM'I NE NA KWARJALLE WATO ZANI DA SUKE DAURAWA, FADINSA : SUKA SA HIJABI WATO SUKA RUFE FISKANSU.
ABIN DA YAKE WAJIBI GA DUKKAN MUSULMI YA TSAYA GA SHARIAR ALLAH, KUMA YA HAKIMANTAR DA DOKOKIN ALLAH MADAUKAKI DA BUWAYA CIKIN ABINDA RAI KE SO KO YAKE SHA'AWA KO YAKE KWADAYINSA, IDAN RANSA YA KIRAYE SHI ZUWA GA NEMAN WANI ABU NA NEMAN DUNIYA KO WATA SHA'AWA TA JIKI TO YA YI DUBI ZUWA GA HUKUNCIN HAKAN KO YA TAFI DAIDAI DA MANHAJI NA SHARIA MAI INGANCI, KUMA YA YI GARGADI GA RANSA MAI YAWAN UMARNI DA MUMMUNA, YA NESACI RUDUWA DA WANNAN DUNIYA MAI KAREWA MAI GUSHEWA, (ABIN DA KE GUN ALLAH YA FI ALHERI KUMA YA FI WANZUWA, ASE BA ZAKU HANKALTA BA).
YAYIN DA AKA HARAMTA GIYA HARAMTAWA NA KARSHE KWATA KWATA DA FADIN SA MADAUKAKI (TO SHIN KU MASU HANUWA NE?)  A KA KARANTA WA UMAR SAI YA CE: MUN HANU MUN HANU, SAHABBAI SUKA RINKA SHEKAR DA GIYA A KWARARO SUKA FASA TUKWANENTA SUKA HANU DAGA GARE TA.
TO YA KU JAMA'AR MUSULMAI!
KU YI RIKO DA ADDININKU, KU GABATAR DA SHI AKA KO WANI ABU MAI TSADA DA KIMA SAI KU SAMU RIBA DA WALWALA KU RABAUTA (DUK WANDA KE YI WA ALLAH  DA MANZONSA BIYAYYA TO HAKIKA YA RABAUTA RABAUTA MAI GIRMA).
HUDUBA TA BIYU
YA JAMA'AR MUSULMAI!
DUK MUTUMIN DA BAI BI SHARIAR ALLAH BA KUMA YA BI SON RANSA TO HAKIKA YA ZAME DAGA HANYA YA FANDARE DAGA TAFARKIN DAIDAI MIKAKKE YA  KUMA FADA CIKIN BATA NA NESA, KUMA YA BAUDE BAUDEWA MAI ZURFI.
ALLAH MADAUKAKIN SARKI YA CE BAYAN YA AMBACI SHANIN MUMINAI  (BAI DACEWA GA MUMINI KO MUMINA IN ALLAH YA YI HUKUNCI DA MANZONSA NA WANI UMARNI DA SU KASANCE SUNA DA ZABI CIKIN UMARNINSU, DUK MAI SABA WA ALLAH DA MANZONSA TO YA BATA BATA BAYYANANNE).
GA MANZONSA TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI YA NA MAGANA DA AL'UMARSA YANA KIRAN SU ZUWA GA TAFARKIN WALWALA DA JIRGIN  TSIRA, YANA MAI CEWA : (KOWANNENKU ZAI SHIGA ALJANNA SAI WANDA YA KI, SAI SUKA CE WA YE ZAI KI YA MANZON ALLAH? SAI YA CE : WANDA YA MIN BIYAYYA ZAI SHIGA ALJANNA, WANDA YA SABA MIN TO HAKIKA SHI YA KI.)
KU KIYAYE BIN SON RAI DA BIN SHAIDAN, KU NESANCI MUNANAN ABUBUWA DA DA SABON ALLAH, ZAKU SHIGA ALJANNAR MAI RAHAMA ZAKU RABAUTA DA YARDAR MAI KYAUTA.
   
  
  



الجمعة، 14 أبريل 2017

LURA DA DAUKAN IZINA

HUDUBAR JUMA'A NA  MASALLACIN ANNABI NA SHEIKH ALIYU ABDURRAHMAN ALHUZAIFI  17 RAJAB 1438 AH
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Masanin gaibi, mai juya zukata, Mai yawan gafarar zunubai, ina yabon Ubangijina da godiya a gare shi bisa ni'imominsa da ba mai iya kididdige su sai shi, Na shaida ba abin bauta wa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya, mulki da kyakyawan yabo na shi ne, kuma shi ne mai iko ga dukkan komai,
Na shaida Annabinmu kuma shugabanmu Muhammad bawansa ne, kuma Manzonsa ne, Mai albishir kuma Mai gargadi, ya Allah ka yi dadin tsira da aminci da albarka bisa ga bawanka kuma Manzonka  Muhammad da iyalansa da sahabbansa  wadanda Allah ya jibince su, to madallah da majibinci kuma madalla da mai taimako,
Bayan haka ku ji tsoron Allah Mai tsarki, a sirracenku da a bayyanenku, don ya jibinci al'amuranku ya kuma gyara halayenku, domin takawa hanya ce ta mutanen kwarai da masu rabauta, rashin takawa shi ne  bayyanannen hasara, ya ku bayin Allah ku kasance daga cikin ma'abota lura da imani, ku bi tafarkin masu hankula da kyautatawa, ma'abuta lura su ne masu lafiyayyen hankali mikakke, kuma  masu lafiyayyen fidira, kuma suke amfana da wahayi,  suna fahimtar ma'anonin abin da Allah ya saukar bisa manufar Allah da Manzonsa, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, suna aiki da maganar Allah don  fatan ladarsa da tsoron ukubarsa, Allah Madaukakin Sarki ya ce : (kuma wadanda suka nisanci shaidanu ga bauta musu, kuma suka maida al'amari ga Allah, suna da bushara ,to, ka bayar da bushara ga bayi na . wadanda ke sauraron magana sa'annan su bi mafi kyaunta . wadancan sune Allah ya shiryar da su  , kuma wadancan su ne masu hankali)
Lura  na daga ayukan masu hankali   mai haskakawa      kuma yana daga cikin ayyukan masu basira masu gogewa  lura yana shiryarwa zuwa ga rabauta da tsira daga ayuka masu halakarwa, kuma yana datar da ma'abocin shi zuwa ga ayuka na kworai , kuma ya shiryar da shi zuwa ga hanyar mutanen kirki masu  neman  kawo gyara  kuma karshen shi yana zamewa zuwa ga alheri , wanda ya rasa lura  tunatarwa bazai mishi amfani ba  zai fada cikin halaka kuma zai bi sha'awe-sha'awen rayuka, kuma ya bi ta hanyar mabarnata sai ya zame cikin masu nadama ,  lura shi ne kaura daga wani hali da ya shude  ma'abocin ukuba da azaba  zuwa ga kyakkyawan yanayi ta hanyar nisantar sabuban ukuba da azaba  ko kuma kaura daga tarihin mutanen kworai  da abinda Allah ya karrama su da shi , zuwa da aiki da ayukan su da bin sawun su , ko kuma tunani cikin abin halittu da sanin tsirrin da suka kunsa da sifofin su da hikimar samar da su don bautawa mahaliccin su  da kebance shi da tauhidi da biyayya  albarka da daukaka ya tabbata agare shi  .
Hakika Allah mabuwayi da daukaka ya halicci halittu  kuma ya sanyawa duniya hanyoyin da suke tafiya a kai sai ya sanya da'a sababi ne na dukkan alheri a duniya  da lahira  ya sanya sabo sababi ne na dukkan sharri a duniya da lahira  shin akwai wanda ya taba zama shakiyyi sabo da biyayya ga Allah?  Ko kuma akwai wanda ya rabauta  sabo da sabawa Allah? Hakika Allah mai tsarki ya bamu kissa a littafinsa haka ma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bamu kissoshi  da wasu halaye  na Annabawa da Manzanni da muminai wanda a cikin shi akwai abin lura  da kuma abu na koyi ga wanda ke bayan su , da abinda akwai tsira daga ukubobi a cikin shi  da kuma rabauta da alheri  ,  da abinda akwai kyakkyawan karshe tare da shi da daga darajoji  Allah madaukakin sarki ya ce: (Lallai ne hakika abin kula ya kasance ne acikin kissoshin su  , ga masu hankali. Bai kasance kirkirarren labari ba, kuma amma shi gaskatawa ne ga abin da yake a gaba gare shi, da rarrabewar dukkan abubuwa , da shiriya da rahama ga mutane wadanda suka yi imani)  Allah madaukakin sarki ya ce  :( Sa'annan kuma muna kubutar da manzanninmu da wadanda suka yi imani  , kamar wannanne, tabbatacce ne a gare mu mu kubutar da masu imani )  Allah mai tsarki ya ce game da masu karyatawa :( Kuma suka kulla makirci, kuma muka kulla sakamakon makirci alhali su ba su sani ba . ka duba yadda akibar makircin su ta kasance  lallai mu mun darkake su da mutanen su gaba daya  . wadancan gidajen su ne wofintattu sabo da zalunci da suka yi   lallai ne a wancan akwai aya ga mutane da  suke sani).Muka  tsirar  da wadanda suka yi imani ,  kuma sun kasance suna  takawa).
Yayin da Allah ya ambaci dewa daga cikin kissoshin Annabawa tsira da amincin Allah su tabbata a gare su  a cikin suratul Shu'ara'I  ya ciken kissan  da fadin sa madaukakin sarki , bayan tsiran Manzannin sa da muminai tare da su :(  Hakika  lallai  akwai aya a cikin wancannanka, yawancin su ba su kasance muminai ba . Hakika Ubangijinka lallai shi ne mabuwayi mai jinkai )
Ibn kasir Allah ya mishi rahama ya ce: Hakika  lallai  akwai aya a cikin wancannanka.
Ai a wannan kissan da abunda ke cikinta na ban al'ajabi da taimako da karfafa ga  bayin Allah muminai akwai nuni da hujja na yanke  da hikima na kololuwa ( lallai Ubangijinka shi ne mabuwayi  )  wato wanda ya buwayi dukkan komai  kuma yayi galaba a kansa kuma ya fi karfinsa mai jinkai da halittunsa baya gaggawa ga wanda ya saba mishi sai dai ma yana sarara mishi kuma ya jinkirta mishi , sa'annan ya damke shi damka irin na mabuwayi mai iko,  Sa'id Dan Jubair  Allah ya kara mishi rahama ya ce  mai jinkai ga duk wanda ya tuba zuwa gare shi , maganan ta tike  a fadin Allah madaukakin sarki a kissan mutanen Ludu  amincin Allah ya tabbata a gare shi  lallai a cikin hakan a kwai ayoyi ga masu lura  katada yake cewa  ga masu lura Bagawi ya ambaci haka a cikin tafsirin sa mafi amfana da  abubuwan da suke faruwa na tarihi , da hikimomi na yanayi ,sai masu lura masu tunani wadanda suke koyi da  mutane na kwarai   masu neman gyara , kuma sukan bar ma'abota barna da fasadi amma shi wanda baya lura baya wa'azantuwa !  baya wa kanshi hisabi baya aiki don lahiransa addinin shi baya hanashi aikata komai , ko hankalin shi baya hana shi aikata munanan aiyuka  da laifuka wannan kamar fa dabba ne  Allah madaukakin sarki ya ce: (  ko kana zaton cewa ,  mafi yawansu suna ji , ko kuwa suna hankali ?  su ba su zama ba  face dabbobin gida  suke . A'a, su ne mafi bacewa ga hanya.)
A cikin Hadisi daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gashi : (Lallai ne idan mumini yayi rashin lafiya sai cutar ta buge shi har ya mutu ,to zai zama  kaffara ne ga  zunubansa da suka shude, idan Allah ya sauwaka mishi to zai zama kankara ne ga zunubansa da suka shude, kuma wazi ne ga lokaci mai fiskantowa. Idan kuma munafuki ya yi rashin lafiya, sannan ya samu sauki to zai zama kaman rakumi ne da masu shi suka daure shi sannan suka sake shi, to bai san don me aka daure shi ba kuma don me aka sake shi ba.)  Nasa'I ne bya rawaito



 Allah bai ambaci tarihin Annabawa ba da Manzanni  da cikamakin su  Annabinmu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  face don  ayi izina da tarihin su  a yi kuma koyi da shiryarwar su da halayen su  mku bi tafarkin su  hakika Allah ya umarci Annabinsa Muhammada tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  da yayi koyi da su  sai mai tsarki ya ce :(  Wadancanne Allah ya shiryar sabo da haka  ka yi koyi da shiryarwar su . )  Allah madaukakin sarki ya ce :( Sabo da haka ka yi hakuri kamar yadda masu karfin niyya daga Manzannai suka yi hakuri).
 Allah madaukakin sarki ya ce game da  muminin yasin  :( Ya mutane na ku bi Manzannin nan ,  ku bi wadanda  ba su tambayarku wata ijara  , kuma su shiryayyu ne ).  Cikamakin su Annabin mu Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi wanda  Allah ya goge sauran shari'u da shi  kuma ya aiko shi da   shari'a mafi kamala   da addini , Allah ya dauki nauyi ga duk wanda ya yi riko da shi zai shiryar da shi ya bashi  kyakkyawar rayuwa  a duniya da lahira ya shigar tare da shi mafificin halitta gidan aminci  Allah madaukakin sarki ya ce : (Kuma wadannan da suka yi da'a ga Allah da Manzon sa , to wadannan suna tare da wadanda Allah ya yi ni'ima a kansu , daga Annabawa da masu yawan gaskatawa , da masu shahada da saliha  kuma wadannan nan sun kyautatu da zama abokan tafiya )  
To wani girmamawa ne ya fi wannan , to wani daukakane ya ke kusa da wannan  matsayi?, kamar yanda Allah  ya kissanta mana  kissoshin Annabawa amincin Allah ya tabbata a gare su da wadanda suka yi imani da su don muyi  koyi da su  kuma mu bi tafarkin tsira tare da su  muyi lura da tarihinsu mu kuma san halayen su  ,Allah ya kuma bamu kissan labaran masu karyata su kuma masu  musu da  gaskiya kuma masu girman kai daga binsu  wanda  suka fifita rayuwan duniya akan na lahira  masu bin sha'awe – sha'awen su da jin dadi , don fa mu yi izina da ukubar su, kuma mu wa'azantu da abinda ya faru da su  na walakacin duniya da azabar lahira kuma mu gargadu daga tsinuwan da aka tabbatar a gare su .
Allah madaukakin sarki ya ce :(Da Adawa da Samudawa ,  alhali kuwa lallai alamun azaba sun bayyana a gare su , daga gidajen su  kuma sahidan ya kawata musu ayukan su . sabo da haka ya kange su daga hanyar Allah  kuma sun kasance masu basira  .
Kuma Karuna da Fir'auna da Hamana . kuma lallai Musa ya zo musu da hujjoji, sai suka yi girman kai acikin kasa kuma ba su kasance masu tserewa ba , sabo da haka ko wannan su mun kama shi da  laifinsa: wato daga cikin su akwai wanda muka aika iskar tsakuwa a kansa ,  kuma daga cikin su akwai wanda tsawa ta kama , kuma daga cikin su akwai wanda muka birkice kasa da shi , kuma daga cikin su akwai wanda muka nutsar, ba ya yiwuwa ga Allah ya zalunce su , amma sun kasance kansu suke zalunta .
Allah madaukakin sarki ya ce :( ko wannan su ya karyata Manzanni  sai narko ya tabbata a gare su )  Allah madaukakin sarki ya ce a kissan Banu ndir :( To ku lura fa ya masu basirori,)  tarihin manzanni tsra da amincin Allah su tabbata a gare su tare da masu karyatawa na daga masu sabawa Allah da  Manzanni  mutane sun san su zamani bayan zamani , na karshe ya karba a gun na farko , wannan na daga cikin manyan hujjojin Allah akan bayinsa wurin karfafan gaskiya da sanin tauhidi  da taimakawa masu kadaita Allah  a cikin bata da shirka da gargadi daga gare  shi  amma lura da dabi'un halittu  da gano hikimanta da siffofinta  da tunani akan kirkiran da Allah ya mata da  tunani cikin  aikin  Ubangiji gayarsa da kuma fa'idansa shi ne kadaita Allah madaukakin sarki mabuwayi da daukaka da kuma bauta masa da mishi da'a , to wanda ya kebanta da halitta shi ne abin bautawa bisa cancanci . Allah madaukakin sarki ya ce : (  Kuma lallai ne da abin lura a cikin dabbobin ni'ima; muna shayar da ku daga   abinda yake a cikin cikunansu  daga tsakanin tukar tumbi da jini, nono tsantsan mai saukin hadiya ga masu sha ) Aallah madaukakin sarki ya ce :( Allah yana juyar da dare da yini , lallai ne a cikin wannan akwai abin kula da ma'abota gannai)
  "ka ce ku yi dubi me ke cikin sammai da kasa, kuma ayoyi da gargadi ba za su yi amfani ba ga mutanen da basu ba da gaskiya da Allah ba "
To shi tuntuntuni cikin halittu ibada ne ga musulmi, amma daukan izina cikin wadannan halittu yana kara wa musulmi imani, kuma yana kara mishi zurfi cikin yakini, Allah Madaukakin sarki ya ke cewa :( Lalle ne a cikin sammai da kasa akwai ayoyi ga masu imani)
Tunani da lura na tabbatar da mai shakku, yana kuma raya zukata, yana haskaka gannai, yana mikar da halaye, shi kuma kauda kai daga tunani da lura yana kekasar da zukata, yana haifar da gafala,yana ja zuwa ga nadama, yana kuma jefa mutum cikin sabo    An karbo daga Abu Huraira Allah kara yarda a gare shi ya ce : ( Lalle Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce a isra'I : yayin da na sauko zuwa sama ta duniya sai na dubi kasa ta, to sai ga wata iska da kara da hayaki, sai na ce : me ye wannan ya kai Jibrilu? Sai yace : wadannan shaidanu ne ake kona su a gaban dan Adan basu tunani ga mulkin sammai da kasa ba don haka ba da sun ga abin mamaki) Ahmad ne ya rawaito
Aallah madaukakin sarki ya ce :( Lalle ne wadanda suka yi takawa idan wani tashin hankali daga shaidan ya shafe su, sai su tuna (Allah) sai ga su sun zama masu basira. Kuma 'yan uwansu (shaidanu ) suna taimakon su a cikin bata  sa'anan kuma ba su takaitawa).
Allah sanya albarka a gare ni da gare ku cikin Alkur'ani.
 Huduba ta biyu :
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya haskaka zukatan masoyansa da Alkur'ani, ya haskaka gannansu da imani, ya kawata ayyukansu da kyautatawa,
Ina kyautata yabo ga Ubangiji na kuma ina gode mishi, bisa ga ni'imominsa da ba mai iyakance su koma bayansa,
Na shaida ba abin bauta wa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya, mulki da yabo duka na shi ne, Mai rahama mai jinkai.
Na shaida cewa Annabinmu kuma shugabanmu bawansa ne kuma manzonsa ne, wanda aka kebantar da shi da dunkulallun kalmomi masu kamalar ma'ana da cikan bayani, Ya Allah ka yi salati da aminci da albarka bisa ga bawanka kuma manzonka  Muhammad da iyalansa da sahabbansa, da wadanda suka bi su da kyautatawa
Bayan haka. Ku ji tsoron Allah Madaukaki zai gafarta muku,zai tattaro muku dukkan alheri a rayuwanku da bayan mutuwarku,
Ya ku bayin Allah ! Ku yi wa kan ku hisabi kafin a yi muku hisabi, kowannen ku ya duba game da karshen al'amari, da karewar ajali, to wanda ya yawaita lura to kurakuransa za su karanta, wanda duk ya kiyaye sabawa Allah da zunubai to zai rayu cikin aminci, kuma a datar da shi zuwa ga kyakkyawan karshe, mai samun sa'ada shi ne wanda ya waazantu da waninsa, mai hasara kuwa shi ne wanda waninsa ya waazantu da shi.
Hakika Allah ya  yi zambo ga masu bin son rai wadanda basu yi lura ba suka wa'azantu da abin da Allah ya basu na labarai, Allah Madaukakin sarki ya ce :( Kuma suka karyata kuma suka bi son zuciyarsu, alhali kuwa kowane al'amari (wanda suke son su tare daga Annabi ) an tabbatar da shi.  Kuma lalle abin da yake  akwai tsawatarwa a cikinsa na labarai ya zo musu.)
Ku saurara Allah Madaukakin sarki na da wasu hanyoyin da ya saba bada lada da alhaki akan su to duk wanda ya ci karo da sunnar Allah to za ta tambadar da shi ta tarwatsa shi ya fado ya kaskanta, Allah Madaukaki ya ce : (A kan hanyar Allah (ta gyaran jama'a) a cikin wadanda suka shude gabaninka , kuma ba za ka sami musanya wa ba ga hanyar Allah.)
Ya zo a hadisi (ku yawaita ambaton mai katse jin dadi mutuwa)

Ya ku bayin Allah : Lalle Allah da Mala'iku na salati ga Annabi ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi kuma ku yi sallama domin amintarwa a gare shi.
  
  

 vv

الخميس، 30 مارس 2017

Istigfari (Neman gafar)

Hudubar Masallacin Annabi  na shaikh Aliyu  Abdurrahman Alhuzaifi 3/7/1438 Ah
Da sunan Allah mai rahma mai jin kai
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Mai rahma Mai jin kai masani mai hikima ma'boci mai falala may girma ina keawtata yabo da ubangijina kuma ina gode mishi ina tuba zuwa gare shi ina neman gafararsa,  na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya ma'aboci al'arshi mai girma. na shaida Annabinmu  kuma shugabanmu Muhammad bawansa ne kuma manzonsane ma'abocin  halaye masu girma, ya Allah ka yi dadin tsira da aminci ga bawanka kuma manzonka  Muhammad da iyalansa da sahabbansa masu da'awa(kira zuwa ga Allah)Masu shiryarwa zuwa ga tafarki mikakke, bayan haka,
Ku ji tsoron Allah da aiki don neman yardarsa da kauracewa abin da ya haramta don ku rabauta da yardarsa da ni'imar aljannarsa kuma ku tsira daga fushinsa da ukubarsa,
Ya ku musulmai! Lalle ubangijinmu Allah mai girma da daukaka ya yawaita kofofin alheri, da hanyoyin ayyuka na da'a da falala da rahama da kyauta da karamci daga Ubangiji Mabuwayi da daukaka, don musulmi ya shiga daga kowane kofa na alheri, kuma ya bi kowane tafarki na da'a, don Allah ya gyara masa duniyarsa kuma ya daga darajarsa a lahirarsa, don Majibinci Mai daukaka  ya karrama shi da daddadar rayuwa, da walwala a rayuwarsa kuma ya samu ni'ima zaunanniya, da yardar Ubangiji bayan mutuwarsa. Allah Madaukakin sarki ya ce :(sai ku yi tsere zuwa ga ayyukan alheri, inda kuka kasance duka Allah zai zo da ku gaba daya, Lalle ne Allah akan kome mai ikon yi ne.)
Allah Madaukakin sarki yace game da Annabawa wadan da su abin koyi ne  ga mutane tsira da amincin Allah su tabbata a gare su gaba daya : (Sun kasance suna gudun tsere zuwa ga ayyukan alheri. Kuma suna kiran mu akan kwadayi da fargaba. Sun kasance masu saunar (aikata sabo) gare mu.
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce da Mu'az : ( Ase ba zan nusar da kai ga kofofin alheri ba, Azumi garkuwa ne, sadaka na tunkude kusakurai, kamar yadda ruwa ke kashe wuta,da  sallar mutum cikin dare, sai ya karanta : ( Sasanninsu na nisanta daga wuraren kwanciya, suna kiran Ubangijinsu bisa ga tsoro da tsammani kuma suna ciyarwa daga abin da muka azurta su.Sabo da haka wani rai bai san abin da aka boye musu ba na sanyin idanu, domin sakamako ga abin da suka kasance suna aikatawa).sannan yace ase ba zan baka labari ba ga tushen al'amura da ginshikinsa, da kololuwar tozonsa? Sai na ce : E, a bani labari ya Manzon Allah.sai ya ce : Tushen al'amari shine musulunci, ginshikinsa shine salla kololuwar tozonsa shi ne Jahadi a tafarkin Allah ) Tirmizi ne ya rawaito ya kuma inganta shi.
Na daga cikin kofofi na alheri da hanyoyi na ayyukan kwarai da da'a da sabuba na kankare munanan zunubbai  akwai neman gafara (Istigfari), Istigfari sunna ne na Annabawa da Manzanni  tsira da amincin Allah su tabbata a gare su, Allah Madaukakin sarki yace  game da mahaifa biyu na mutum  amincin Allah da rahamarsa  da albarkarsa ya tabbata a gare su, :
(suka ce ya Ubangijinmu ! Mun zalunci kanmu. Kuma idan ba ka gafarta mana ba, kuma ka yi mana rahama, hakika muna kasancewa daga masu hasara)
Nuhu amincin Allah ya tabbata a gare shi ya ce : (ya ubangiji na ka yi mini gafara (ni) da mahaifa na biyu, da wanda ya shiga gida na yana muminai maza da mata).
Allah mabuwayi da daukaka yace game da Ibrahim amincin Allah ya tabbata a gare shi, : (ya Ubangijinmu ! ka yi gafara gare ni, kuma ga mahaifana, kuma da muminai, a ranar da hisabi ya ke tsayawa).
Allah madaukaki yace game da Musa amincin Allah ya tabbata a gare shi :(Yace : Ya Ubangiji na ka gafarta mini ni da dan'u wa na , kuma ka shigar da mu a cikin rahamarka alhali kuwa kai ne mafi rahamar masu rahama.!)
Allah madaukai yace : Kuma Dawuda ya tabbata cewa mun fitine shi sabo da haka ya nemi Ubangijinsa gafara kuma ya fadi yana mai sujada, kuma yana maida al'amari ga Allah.)
Allah Madaukakin sarki yace yana mai umarni ga Annabinsa  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, (saboda haka ka sani cewa babu abin bautawa face Allah kuma ka nemi gafara ga zunubinka, kuma sabo da muminai maza da muminai  mata).  
Na daga cikin koyarwar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yawan istigfari, tare da cewa Allah ya gafarta masa abin da yan gabata na daga zunuban shi da abin da ya jinkirta, an karbo daga Abdullahi dan umar رضي الله عنهما (ya ce: mun kasance muna kirga wa annabi صلى الله عليه وسلم  a majlisi daya fadinsa ya ubangiji ka gafarta mini ka karbi tubana domin kai mai yawan karban tuba ne har so dari ) Abu Dawuda ne ya rawaito da Tirmizi kuma yace hadisi ne hasan kuma ingantacce,
  kuma an karbo daga A'isha رضي الله عنها  ta ce (Annabi ya kasance yana yawaita cewa  subhanallahi wa bi hamdihi  astagfirullaha wa atubu ilaihi"  kafin mutuwarsa ) Buhari  da Muslim ne suka rawaito,  kuma an karbo dagaAbu Huraira رضي الله عنه  yace : (Ban ga wanda yafi manzon Allah  صلى الله عليه وسلم yawaita fadin  cewa Astagfirullaha wa atubu ilaih ba )  Nasa'i ne yarawaito
 (mai tsira da amincin Allah sutabbata a gareshi ya kasance yana cewa bayan sallama daga salla: Astagfirullah sau  uku) Muslim ne ya rawaito daga hadisin Sauban Allah ya kara yarda a gare shi.   
Sa'annan daga bisani sai ya fadi zikirorin da aka shar'anta fadinsu a bayan sallolin farilla.

Kuma lallai NEMAN GAFARA Dabi'ar salihai ne, kuma aiki ne na mutane masu biyayya, da takawa, kuma alama ce ta muminan mutane,    Allah (تعالى) yana cewa:
"Ya Ubangijinmu! Ka gafarta mana zunubanmu, kuma ka kankare mana munanan aiyukanmu, kuma ka dauki rayukanmu tare da masu yin biyayya" [Ali-imrana: 193].
Kuma Allah (تعالى) yana cewa:
"Wadanda suke cewa: Ya Ubangijinmu! Lallai mu mun yi Imani; sai ka gafarta mana zunubanmu, kuma ka katange mu daga azabar wuta   *   Masu hakuri, da masu gaskiya, da masu kankan da kai, da masu ciyarwa, da masu yin istigfari a lokutan asuba" [Ali-imrana: 16-17].
Alhasan yace: Sun yi ta sallah har zuwa lokacin sahur, sannan suka fiskanci ibadar neman gafara.
Kuma Allah (تعالى) yana cewa:
"Sune kuma Wadanda, idan suka aikata wata alfasha, ko suka zalunci kayukansu su kan tuna Allah; sai su nemi gafarar zunubansu, Kuma wanene zai gafarta zunubai idan ba Allah ba, kuma basa dogewa akan abinda suke aikatawa, alhalin suna sane" [Ali-imrana: 135].
Ibnu-rajab yace: ((Shi kuma neman gafara daga zunubai shine: Neman lullube su.    kuma lallai bawa yana da matukar bukata zuwa ga hakan; saboda ko-yaushe ya kan yi kuskure cikin dare da rana. Kuma lallai ambaton TUBA DA NEMAN GAFARA ya maimaitu a cikin alkur'ani, da kuma yin umurni da su, da kwadaitarwa zuwa gare su)). … Maganarsa ta kare.

            Kuma lallai NEMAN GAFARA DAGA Ubangiji mabuwayi da daukaka Allah ta'alah yayi alkawari da cewa zai amsa, kuma zai yi gafara.

            Kuma lallai an shar'anta cewa Bawa ya rika neman gafara a kan zunubi aiyananne, sananne; saboda fadin Annabi (صلى الله عليه وسلم):
"Lallai bawana ya aikata wani zunubi, Sannan yace: Ya Ubangijina, lallai ni na aikata wani zunubi; sai ka gafarta mini shi, Sai Allah yace: Bawana lallai ya san cewa  yana da Ubangijin da yake  gafarta zunubai, ya kuma tafiyar da shi, to lallai na gafarta wa Bawana", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi daga hadisin  Abu-hurairah (رضي الله عنه).

            Kamar yadda shari'a ta zo da cewa: Bawa ya rika neman gafara, a sake ba kaidi; sai yace: Ya Ubangijina! ka gafarta min, kuma kayi mini rahama. Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma ka ce: Ya Ubangijina! Ka yi gafara kuma ka yi rahama, domin kai ne mafi alherin masu rahama" [Mu'uminuna: 118].
Kuma lallai Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya kasance yana sanar da mutumin da ya musulunta da cewa ya rika yin addu'a da wadannan kalmomin :
"Ya Allah ka yi gafara a gare ni, ka yi mini rahama, ka shiryar da ni, ka bani lafiya, ka azurta ni", Muslim ya ruwaito shi daga hadisin Darik dan Ashyam (Allah ya kara yarda a gare shi).

            Kamar yadda aka shar'anta: Bawa ya rika nema daga Ubangijinsa cewa ya gafarta masa zunubansa gabadayansu; wadanda ya san su da wadanda bai sansu ba; wannan kuma saboda zunubai dayawa babu wanda ya sansu sai Allah, kuma lallai bawa za a kama shi akansu;    Ya zo daga Abu-Musa al'ash'ariy (رضي الله عنه) daga Annabi(صلى الله عليه وسلم) lallai shi ya kasance yana yin addu'a da wannan addu'ar:
"Ya Allah! Ka gafarta min kurakuraina da jahilcina, da ketare iyakana cikin lamari, da abinda kai ne ka fini saninsa. Ya Allah! Ka gafarta mini gaskena da wasana, da kuskurena da gangancina, kuma dukkan haka, akwai shi a wurina. Ya Allah! Ka gafarta mini abinda na gabatar da wanda na jinkirta, da abinda na boye da abinda na bayyanar, da abinda kai ne ka fi ni saninsa, kai ne Mai gabatarwa, kuma kai ne Mai jinkirtarwa, kuma lallai kai akan kowani abu mai iko ne", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Da kuma saboda fadin Annabi (صلى الله عليه وسلم):
"Shirka a cikin wannan al'ummar tafi buya fiye da tafiyar tururuwa, Sai Abubakar (رضي الله عنه) yace: To ta yaya za a kubuta daga gare ta, ya Manzon Allah? Sai yace: Ka rika cewa: Ya Allah ina neman ka tsare ni kan yin shirka a gare ka alhalin ina sane, Ina kuma neman gafararka daga zunubin da ban sani ba", Ibnu-Hibbana ya ruwaito shi, daga hadisin Abubakar, Da kuma Ahmad, daga hadisin Abu Musa.
An ruwaito daga Abu-hurairah (رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) lallai shi ya kasance yana yin addu'a:
"Ya Allah! Ka gafarta min zunubaina dukkansu; kananansu da manyansu, na kuskurensu dana gangancinsu, na sirrinsu dana bayyanansu, na farkonsu da na karshensu", Muslim ya ruwaito shi, da Abu-dawud.
            Idan bawa ya rokiUbangijinSa gafarar zunubansa; wadanda ya sani daga cikinsu da wadanda bai sani ba, to lallai an datar da shi; dace mai girma.

            Kuma bawa ya roki Ubangijinsa gafarar zunubai cikin ikhlasi da naci da roko mai tattare da kankan-da kai yana kunsan TUBA DAGA ZUNUBAN, Shi kuma ROKON A DATAR DA MUTUM ZUWA GA TUBAN yana kunsan NEMAN GAFARAR; saboda haka, kowanne daga cikin ISTIGFAAR da TUBA idan aka ambace shi ba tare da dayanba to yana kunsan ma'anan dayan.  Idan kuma ambatonsu ya hadu a cikin nassoshin Kur'ani ko hadisi to Ma'anan: ISTIGFAARI sai ya zama: Neman shafe zunubi da gusar da alamarsa ko gurbin da ya bari, tare da bada kariya kan sharrin da ya gabata na zunubin, da kuma suturce shi. Ita kuma TUBA sai ma'ananta ya zama: Komawa zuwa ga Allah; ta hanyar barin aikata zunubai, da kuma kare bawa daga abinda ya ke tsoro; na munanan aiyukansa a rayuwar da yake fiskanta, tare da yin azama ko niyyar ba zai sake aikata zunubin ba.
Kuma lallai AyarAllah ta ambaci ISTIGFAARI da TUBA a hade, a inda Allah yake cewa:
"Kuma ku nemi gafarar Ubangijinku, sa'annan ku tuba zuwa gare shi, zai jiyar da ku dadi jiyarwa mai kyau, zuwa ga wani lokaci ambatacce, kuma ya baiwa dukkan ma'abocin girma girmansa, Idan kuma kuka juya to lallai ni ina tsoron azabar yini mai girma akanku" [Hud: 3].
Da wassu ayoyin wadanda ba wannan ba.
Kuma lallai Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Ya ku mutane! Ku tuba zuwa ga Ubangijinku, kuma ku nemi gafararSa; saboda Ni na kan tuba zuwa gare shi, ina kuma neman gafararSa; a kowani yini sau dari", Annasa'iy ne ya ruwaito shi, daga hadisin Al'agarri Almuzaniy (رضي الله عنه).

            Kuma lallai bawa yana da matsananciyar bukatar YIN ISTIGFAARI, a ko-da-yaushe,      musamman kuma a wannan zamanin saboda yawaitan ZUNUBAI da FITINTINU,    wannan kuma domin Allah ya datar da shi a rayuwarsa, da kuma bayan mutuwarsa, ya kuma gyara masa sha'aninsa.    Saboda yin istigfaari ya kan bude kofofin alherori,   ya kuma tunkude sharrori da ukubobi.
            Kuma lallai itama al'ummar musulmai tana da matsananciyar bukata zuwa ga dawwama kan neman gafara; domin Allah ya yaye mata ukubobi da suka sauka a gare ta, ya kuma tunkude mata ukobobin da za su sake sauka a gare ta.
            Kuma babu wanda zai yi sakaci KAN NEMAN GAFARA sai wanda ya jahilci amfanoninsa da albarkokinsa,     saboda falolinsa sun zo dayawa a cikin ALKUR'ANI da SUNNAH; Allah (تعالى) yana cewa dangane da annabi Salihu (عليه السلام):
"Ya ku mutanena! Don me kuke gaggawan aikata mummuna gabanin kyakkyawa, Da dai kun nemi gafarar Allah; da tsammanin za a yi rahama a gare ku" [Naml: 46].   Saboda da yin istigfaari ne ake yin rahama ga al'ummah.
Kuma Allah (تعالى) yana fada dangane da annabi Nuhu (عليه السلام):
"Sai nace: KU NEMI GAFARAR UBANGIJINKU lallai shi ya kasance mai yawan gafara   *    Zai saki ruwan sama akanku; mamako   *     kuma ya karfafe ku da wata dukiya, da 'ya'ya, kuma ya sanya muku gonakai, kuma ya sanya muku koguna" [Nuh:10-12].
Kuma Allah (تعالى) yake fadi dangane da annabi Hudu (عليه السلام):
"Kuma, ya mutanena! Ku nemi gafarar Ubangijinku, sa'annan ku tuba zuwa gare shi; sai ya saki ruwan sama akanku, ya kuma kara muku wani karfi akan karfinku, Kuma kada ku juya baya kuna masu laifi" [Hudu: 52].
Allah (تعالى) yace:
"Allah bai kasance zai azabta su ba alhalin kana cikinsu, kuma Allah bai kasance mai azabta su ba; matukar suna neman gafara" [Anfaal: 33].
Abu-Musa yake cewa (رضي الله عنه):
((Lallai wannan al'ummah a cikinku akwai abubuwan samun aminci guda biyu;   Amma dangane da wannan annabin –صلى الله عليه وسلم- to shi kam ya shude, Yayin da shi kuma NEMAN GAFARA zai ci gaba da wanzuwa a cikinku har zuwa tashin kiyama)).
            Don haka; Wannan al'ummar; Idan ta yawaita istigfaari = zai dauke mata musibun da suka sauka ko suka auku, sannan ya tunkude mata wadanda za su sauka a gaba;     saboda bala'i baya sauka sai idan an yi ZUNUBI,  kuma ba a yaye shi sai da yin TUBA da ISTIGFAARI,     An ruwaito daga Abdullahi dan Abbas (رضي الله عنهما) yace: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Duk wanda ya lazimci yin istigfaari Allah zai sanya masa mafita daga kowani kunci, da kuma yayewa daga kowani bakin ciki, ya kuma azurta shi ta yadda baya tsammani", Abu-dawud ya ruwaito shi.

            Kuma lallai KALMOMI DA AKA KIYAYE SU MASU ALBARKA na ISTIGFAARI sun zo daga Annabi (صلى الله عليه وسلم),     kuma lallai cikin fadin wadannan kalmomin akwai lada mai yawa;
            Yana daga cikinsu:
            Fadinsa (صلى الله عليه وسلم):
"Duk wanda ya fadI: ASTAGFIRUL LAHAL ALZIY LA ILAHA ILLA HUWAL HAYYAL KAYYUMA, WA ATUBU ILAIHI, Duk wanda ya fadi haka to an gafarta zunubansa, koda kuwa ya gudu a wurin yaki". Abu-dawud da Tirmiziy suka ruwaito shi, da Hakim, kuma yace: hadisi ne ingantacce, akan sharadin Bukhariy da Muslim.
An ruwaito daga Abu-Sa'id alkhudriy, daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), lallai yace:
"Duk wanda ya fada a lokacin da ya tafo zuwa ga shumfudinsa: ASTAGFIRUL LAHA ALLAZIY LA ILAHA ILLA HUWAL HAYYUL KAYYUMU, WA ATUBU ILAIHI, sau uku, to Allah zai gafarta zunubansa, koda sun kai kumfan teku", Tirmiziy ne ya ruwaito shi.
An ruwaito daga Ubadah dan As-samit (رضي الله عنه) yace: Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Duk wanda ya tashi daga barcinsa, a cikin dare' Sa'annan yace: LA ILAHA ILLAL LAHU, WAHDAHU LA SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDU, WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN KADIR, SUBHANAL LAHI, WALHAMDU LILLAHI, WA ILAHA ILLAL LAHU, WALLAHU AKBAR, ALLAHUMMAG FIR LIY, Sai yayi addu'a to an amsa masa, idan kuma ya tashi yayi sallah to an karbi sallarsa", Bukhariy ne ya ruwaito shi.
Ya zo cikin wani hadisin cewa:
"Duk wanda a gabanin ketowar alfijir din juma'a yace: ASTAGFIRUL LAHAL ALZIY LA ILAHA ILLA HUWAL HAYYAL KAYYUMA, WA ATUBU ILAIHI, sau uku, an gafarta zunubansa koda sun kasance misalin kumfar teku ne".
Kuma an ruwaito daga Shaddad dau Aus (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Jagoran laffuzan neman gafara shine bawa yace: ALLAHUMMA ANTA RABBIY LA ILAHA ILLA ANTA; KHALAKTANIY, WA ANA ABDUKA, WA ANA ALA AHDIKA WA WA'ADIKA MASTADA'ATU, A'UZU BIKA MIN SHARRI MA SANA'ATU, ABU'U LAKA BI NI'IMATIKA ALAYYA, WA ABU'U BI ZANBIY; FAGFIR LIY; FA INNAHU LA YAGFIRUZ ZUNUBA ILLA ANTA, Duk wanda ya fadi kalmomin nan cikin yini yana mai samun yakini akansu sai ya mutu a wannan yinin nasa, gabanin yayi yammaci ya shiga aljannah. Wanda kuma ya fade su cikin dare, alhalin yana da yakini akansu sai ya mutu gabanin yayi yammaci to yana cikin 'yan aljannah", Bukhariy ya ruwaito shi.
An ruwaito daga Anas (رضي الله عنه) yace: Na ji Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: Allah (تعالى) yana cewa:
"Ya kai dan Adam! Da zunubanka za su cika sashen sama gabadaya, sannan sai ka nemi gafarata sai in gafarta maka, ba zan damu ba!", Tirmiziy ya ruwaito shi, kuma yace: hadisi ne mai kyau.

            Kamar yadda kuma ake shar'anta neman GAFARAR ALLAH  a lokacin yin wata ibada ko bayan kammala ta; wannan kuma domin ta magance abinda ya kasance a cikin ibadar na tawaya ko nakasa, tare da nisantar da mutum daga ji-da kai, ko riya;    Allah (تعالى) yana cewa:
"Sa'annan ku tafo ta wurin da mutane suke gangarowa, kuma ku nemi gafarar Allah, lallai Allah Mai gafara ne Mai rahama" [Bakarah: 199].
Kuma Allah (سبحانه) yana cewa:
"Kuma ku tsayar da sallah, kuma ku bada zakka, ku bada rance wa Allah rance mai kyau,    kuma duk abinda kuka gabatar ga kayukanku na alkhairi za ku same shi a wurin Allah, zai kasance mafifici kuma zai fi girma ga sakamako, Kuma ku roki Allah gafara; lallai Allah Mai gafara ne Mai rahama" [Muzammil: 20].
Sai Allah yayi umurnin a nemi gafararSa a lokacin da ake yin wadannan aiyukan da'an, da kuma bayan kammala su.

            Haka kuma an shar'anta musulmi ya rika neman gafara ga 'yan'uwansa muminai; maza da mata, da musulmai maza da msulmai mata, rayayyu daga cikinsu da wadanda suka mutu,    wannan kuma a matsayin kyautatawarsa ne a gare su, da bayyanar da soyayya, da lafiyar zuciya, tare da amfanar da musulmai, da kuma (tsoma baki) don neman cetonsu a wurin Allah;    Allah (تعالى) yana cewa:
"Da kuma wadanda suka zo a bayansu, suna cewa: Ya Ubangijinmu ka yi mana gafara, tare da 'yan'uwanmu da suka rigaye mu da Imani, kuma kada ka sanya wani kulli a cikin zukatanmu dangane da wadanda suka yi imani, Ya Ubangijinmu lallai kai Mai tausayi ne, Mai rahama" [Hahsri: 10].
An ruwaito daga Ubadah dan Assamit (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) lallai shi yace:
"Duk wanda ya nemi gafara ga muminai maza da muminai mata to lallai Allah zai rubuta masa lada a madadin kowani mumini namiji da mumina mace", Alhaisamiy yace: Isnadin wannan hadisin yana da kyau (jayyid).
Wannan kuma kamar nema musu gafara kenan a lokacin yin sallar janaza a gare su, da kuma nema musu gafara a makabartai idan musulmi ya ziyarce su.
Hakan kuma koyi ne da Mala'ikun da suke dauke da al'arshi, da kuma sauran Mala'iku makusanta,   Allah yana cewa:
"Wadanda suke rike da al'arshi, da wadanda suke kewayensa suna yin tasbihi da gode wa Ubangijinsu, kuma suna yin imani da shi, suna kuma neman gafarar Allah ga wadanda suka yi imani (suna cewa) Ya Ubangijinmu! Lallai ka yalwaci kowani abu da rahama da kuma ilimi; sai ka yi gafara ga wadanda suka tuba, suka kuma bi hanyarka, kuma ka kare su daga azabar wutar jahim" [Gafir: 7].  
Yin haka kuma yana daga cikin manyan hakkokin muminai!

            Ya ku bayin Allah… !
            Ku amsawa umurnin Ubangijinku,    Allah yana cewa a cikin hadisin kudusiy:
"Ya ku bayina ! lallai ku, kuna yin laifi dare da rana, Ni kuma ina gafarta zunubai gabadaya; sai ku nemi gafarata; zan gafarta muku", Muslim ya ruwaito shi daga hadisin Abi-zarrin.

Sai ku fiskanci Ubangijinku da neman gafararSa, za ku ga karamcinSa da kyautarSa da falalarSa, da albarkokinSa, kuma za ku sami shafe aiyukanku munana, da daukaka darajoji,      Hadisi y azo daga Abu-hurairah (رضي الله عنه) yace: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Na rantse da wanda raina yake hannunsa! Da ace bakwa yin zunubi to da Allah ta'alah ya tafiyar da ku, kuma da ya zo da wassu mutanen wadanda suke yin zunubi; sai suna neman gafarar Allah ta'alah sai ya gafarta musu", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma saboda kasancewarsa Allah madaukaki Mai yalwar gafara ne, mai baiwa da kyauta da karamci, yana son a rika neman gafararSa, ana rokonSa    Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma duk wanda ya aikata mummunan aiki, ko ya zalunci kansa, sa'annan sai ya nemi gafarar Allah, to lallai zai sami Allah Mai yawan gafara Mai rahama" [Nisa'i: 110].


            Allah yayi mini albarka Ni da KU, cikin alkur'ani mai girma, ya kuma amfanar da mu da abinda ke cikinsa na ayoyi da tunatarwa mai hikima,      kuma ya amfanar da mu da shiriyar shugaban manzanni, da kuma maganganunsa mikakku,    Ina fadar maganata wannan, kuma ina neman gafarar Allah Mai girma Mai daraja wa Ni da Ku, da kuma sauran musulmai da muminai,     Ku nemi gafararSa; lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.        

Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya sun tabbata Allah Mai gafara abin godiya, Ga Ubangiji na na da sunaye kyawawa da sifofi madaukaka, ina godewa Ubangiji na bisa ga ni'imominsa masu girma, kuma na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya, kuma na shaida shugabanmu kuma Annabinmu Muhammad bawansa ne kuma Manzonsa ne, zababbe, ya Allah ka yi salati da aminci ga bawanka kuma Manzonka Muhammad da iyalansa da Iyalansa da sahabbansa masu tsoron Allah, bayan haka,
Ku ji tsoron Allah Madaukaki, ta hanyar  neman yardarsa da aiki da biyayyarsa da nesatan abin da ya haramta, hakika Ubangijimu ya baku iko na aiki na kwarai ya kuma sanya wannan duniya gida ne na aiki, lahira kuma gidan sakayya, Hakika masu aiki da ikhlasi a wannan gida da kyautatawa sun rabauta, masu barna wadanda suka bijire sun yi hasara, kai kace ka ajali ya zo muku, ga buri ya juya baya, kuna da abin lura daga wadanda suka shude, kuma game da labarunsu da tarihinsu kuna da izina a ciki, na cikin  kabari dayansu na fatan ya dawo duniya don ya yi salla raka'a biyu,kuma ya nemi gafara da yawa, sai dai faufau da a amsa masa, Allah madaukakin sarki ya ce : ( Har idan mutuwa ta je wa dayansu sai yace : ya Ubangiji na ku mayar da ni (duniya)* Tsammani na in aikata aiki na kwarai cikin abin da na bari, kayya lalle ne ita kalma ce shi ne mafadinta alhali kuwa a baya gare su akwai wani shamaki har ranar da zaa tayar da su.)
Kar ka rena kadan na daga alheri ko kadan na sharri, ya zo a hadisi : (Na hore ku rena kananan zunubai, don suna taruwa ga mutum har su halka shi,
Ya zo a hadisi ( kar ku rena wani abu na aikin alheri,
Ya ku bayin Allah : Lalle Allah da Mala'iku na salti ga Annabi ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi kuma ku yi sallama domin amintarwa a gare shi.