الخميس، 16 مارس 2017

Ba dabara ko iko sai ga Allah( Lahaula wala kuwwata illa billah

HUDUBAR JUMA'A NA MASALLACIN ANNABI 18/6/1438 AH,  NA SHEIK HUSAINI BIN ABDUL'AZIZ  AL- ASSHAIKH
A irin wannan zamani da ke cike da fitintinu ga musibu sun yawaita,  makiya na mulkan al'umar musulmai wanda hakan ke haifar da radadi da bakinciki mai yawa kuma daban- daban, to lalle bukatuwa na tsananta zuwa ga tunatar da musulmai game da mafita na dahir daga dukkan kowane bakinciki, da sabuba na hakika da zaa kubuta daga dukkan bacin rai da wahalhalu.
Ya ku Musulmai!
 Wannan rayuwa mai kare wa cike take da musibu da gajiyarwa  (Wahala) Allah ya ce: (Hakika  Mun halitta mutum cikin wahala)
Lalle tushe mai girma na fita daga wadannan musibu a wannan rayuwa ta duniya da kuma kubuta daga damuwowinta yana kasance wa ne cikin tabbatar da tsoron Allah a boye da kuma bayyane, da komawa  gare shi da dawowa zuwa ga kusancinsa dare da wuni , da bada lokaci na gabadaya don girmarsa cikin sauki da tsanani,  Allah madaukakin sarki ya ce ( Duk wanda  ya ji tsoron Allah zai sanya masa mafita.Kuma ya azurta shi daga inda ba ya zato, kuma wanda ya dogara ga Allah to Allah ne Mai ishinsa.) Allah Mai girma da daukaka ya ce :(To wanda ya ji tsoron Allah zai sanya masa wani sauki daga al'amarinsa).
Na daga cikin naui na rusunawa da kankan da kai da mika wuya ga Allah mai girma da daukaka akwai abin da Annabi ya shiryar da wasu sahabbai kuma ya musu wasiya da shi ciki da waje fadi da aiki da hali da dabia hakika ya shiryar da Abu Musa Allah ya yarda da shi da fadinsa a gare shi:  ( kace la haula wala kuwwata illa billahi domin ita taska ce daga cikin taskokin aljannah)Bukhari da Muslim ne suka  rawaito
Abu zarri Allah ya kara yarda a gare shi yace:(masoyina tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya min wasiya kan na yawaita fadin la haula wala kuwwata illah billahi
           Lallai ita din nan wasiya ce madaukakiya     mai girma da babbar  ambato, kalmomin ta dan kadanne amma ma'anoninta na da girma, zikiri wanda harshe ke furta shi zuciya ya sakankance da shi  lallai shaanin shine babu mai taimako game da tabbatar da maslahohin duniya da lahira face Allah mabuwayi da daukaka to duk wanda Allah ya taimaka shine abin taimako wanda kuma ya tabar shine tababbe.
Zikiri ne wanda bawa zai sakankance da shi cewa bashi da dabara shi ko wanin shi na ya fita daga wani halin zuwa wani halin haka nan bai da karfi bisa ga wani sha'ani daga cikin sha'anunnukansa ko tabbatar da manufa daga cikin manufofinsa face da tsoron ALLah mai karfi madaukaki mai girma.
Zikiri ne da bawa zai bayyana hakikanin talaucinsa da kankan dakai da kai ga ubangijinsa kuma yana cikin larura da bukatuwa zuwa ga mahaliccinsa mabuwayi mai rinjayi.
Zikiri ne da yake fita daga harshen bawa zuciyan shi na kadaita tilo mai girman shaani daga gunshi ake nemo nasara da galaba da yayewa da mafita ALLah mai tsarki da daukaka yace :(Allah zai sanya sauki abayan tsanani )zikiri dashi ake samun rabauta da nasara da mafita da kubuta Allah madaukakin sarki yace : (yaku wadanda sukayi imani idan kun hadu da wata kungiyar yaki to ku tabbata kuma ku ambaci ALLah da yawa ko kuna cin nasara )
Lallai zikiri ne da ya dace da ko wani musulmi da ya furta shi da harshen magana da aiki, tun da sirri ne na tauhidi, wanda ke hukunta rusuna wa mahalicci,da tare wa gare shi da kubuta daga dabara ko karfi sai daga gare shi, Mabuwayi da daukaka.
Ibnul kayyim Allah ya yi mishi rahama yace ;( Wannan kalmar tana da tasiri na ban mamaki wurin tafiyar da abubuwa masu tsanani, da dauke wahala da shiga ga masu mulki da ake tsoro, da dauke manyan wahalhalu).
Ya ku bayin Allah:
 ku saurara ga wannan kissa mai girma wanda hujja ce mai haske bisa ga karfin tauhidi wanda ke warware bakin ciki duk yanda ya girmama, kuma ke tafiyar da wahalhalu duk yanda  ta tsananta .
Wata kissa ce da da yawa daga cikin malaman tafsiri sun ambata ta, ta zo ta fiskoki daban –dabam, mafi karancin darajanta a ce hassan , ita ce Auf dan Malik al-ashja'I yana da da wanda ake cewa Salim mushirikai sun kama shi cikin fursunonin yaki sai ya zo wurin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai ya ce da shi ya Manzon Allah : lallai abokan gaba sun kama da na ( cikin kaman mun yaki) ya kuma koka mishi talauci , sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: ( Ba abin da ya wuni a wurin iyalan Muhammadu sai mudu  to ka ji tsoron Allah ka yi hakuri ka yawaita fadin lahaula wala kuwwata illa billahi0)  
 A wata ruwaya kuma  ya zo cewa ya umarce shi ne  kuma ya umarci uwan dan da haka, sai mutumin ya akaita hakan , yayin da yake cikin gidan shi, sai ga dan shi ya zo mishi a halin makiya din sun gafala daga gare shi sai yasamo rakuma ya zo da su zuwa ga baban shi, da ma baban matalauci ne  baban sai ya zo gun Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sai ya ba shi labarin Auf da labarin rakuma , sai Manzon Allah ya ce da shi: (  ka aikata abin da ka so da su ka yi abinda ka saba yi da rakumar ka  da su ).
 Fadin Allah:( ( Duk wanda  ya ji tsoron Allah zai sanya masa mafita.Kuma ya azurta shi daga inda ba ya zato, kuma wanda ya dogara ga Allah to Allah ne Mai ishinsa.) Allah Mai girma da daukaka ya ce :(To wanda ya ji tsoron Allah zai sanya masa wani sauki daga al'amarinsa). Daga nanne sahabbai suka tafi akan wannan wasiyyar din cikin fadi kuma da aikatawa.
 Ibnu Abiddunya ya rawaito cewa Abu Ubaida da aka katange shi sai  Umar ya rubuta zuwa gare shi: duk abin da ya sauka zuwa ga  mutum na tsanani Allah zai yaye bayan haka,  kuma hakika tsanani daya ba zai ci galaba akan sauki biyu ba , kuma yana ce mishi : ( ku yi hakuri kuma ku yi dauriya  kuma ku yi zaman  dako, kuma ku yi takawa ko za ku ci nasara).
 Lallai ta'alluki da Allah  da dogaro gare shi da ambaton sa a harshe ,  na daga cikin abin da yake tafiyar da bakin ciki duk yanda ya tsananta makomanta zai zama yayewa ne da mafita .
Fudail ya ce : wallahi da mutum zai yanke tsammani daga halittu ka ji ba ka bukatar komai daga gare su , to da majibincin ya baka du abin da kaake so.
Na daga cikin sabuba wanda yake yaye bakin ciki ya tafiyar da bacin rai shi ne dan Adam a duk lokacin da  yayewa ya yi jinkiri har ma ya yanke tsammani daga gare shi bayan ya yawaita rokon sa da kankan da kai zuwa gare shi kuma bai ga wani alama na amsa aduwar ba a gare shi, to ya wajaba ya koma ya zargi kan shi ya sake sabon tuba ya yi tuba na gaskiya ya dukufa zuwa ga Allah yana mai tsarkake niya yana mai rusunawa majibinci  kuma ya yi ikirari da cewa yana cikin wadanda  suka cancanci jarabawa ya sauka a gare su  kuma ba ya cikin wadanda suke ahlin amsar adu'a sai dai yana fatar rahamar Ubangijin sa   kuma yana neman afuwar sa,  to anan ne fa amsar adu'arsa za ta zo da yayewar bakin cikin shi sabo da Allah madaukaki yana tare da duk wadanda zukatan su suka  rusuna zuwa gare shi don shi kamar yadda Malaman  magabata suka tabbatar.
Ya ku Musulmai!
Ku kiyaye irin wannan zikiri mai girma a kowani lokaci da yanayi,don alherin sa nau'uka ne daban daban , falalolinsa na da yawa, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Ba wani mutum a doron kasa da zai ce : La'ilaha illalah Wallahu Akbar wa subhanallah wala haula wala kuwwata illa billa, face an kankare masa kusakuran shi, ko da sun fi yawan tarukucen saman teku ne.) Ahmad ya rawaito, Tirmizi ya ce Hasan ne Hakim kuma ya inganta shi kuma zahabi ya mar muwafaka.
An karbo daga Ubada dan samit Allah ya yarda da da shi ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(Wanda ya tashi cikin dare sai yace : La'ilaha illallahu Wahdahu la sharika lahu lahul mulku wa lahul hamdu wa huwa ala kulli shai'in kadir, Alhamdu lillahi wa subhanallahi wa lailaha illallahu wallahu Akbar wala haula wala kuwwata illa billah, sai yace ya Allah ka gafarta mini, ko ya yi adua zaa amsa masa,  kuma in ya yi alwala ya yi sallah za a karbi sallar sa) Buhari ne ya rawaito.
Lalle adua ne na alheri ga bawa kuma kariya ne da katange wa ne ga maslahohinsa, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (wanda ya ce- idan ya fita daga gidan shi - Bismillah na dogara gare shi ba dabara ko karfi sai gare shi, za a ce da shi :An isanmaka an baka kariya kuma shaidan zai yi nesa da shi).Abu Dauda da Tirmizi ne suka rawaito.
Sabo da wannan zikiri ne da ke hukunta mika wuya ga Allah da maida al'amari a gare shi, da yarda da rusuna wa gare shi,tsarki ya tabbata a gare shi, kuma ba mai maida al'amarinsa, kuma bawa bai mallaki komai ba na al'amarinsa,ragamar al'amura na hanun Allah madaukaki, al'amuran bayi na jawuwa ne bisa hukuncinsa da kaddararsa, ba mai maida al'amarinsa ko bin kadun hukuncinsa.
To kai musulmi ka kasance  mai natsuwar zuciya mai kwanciyan hankali mai sakankance wa da yaye wan bakinciki da samun mafita, duk abin da ke duniya na karkashin iko ne na Allah.
Duk abin da ke wannan duniya ko yaya karfinsa ya kai, ko tsananin ya kai to hakika tana karkashin karfin Allah ne da umarninsa, da hukuncinsa da kaddararsa, to duk wani mai karfi mai rauni ne a gun Allah mai girma da daukaka,ya kai bawan Allah ka shagaltar da kanka da sauran ayyukan da'a da nau'uka na alheri, ka lazimci ambatonsa da nau'uka na zikiri daban daban a yanayi na sauki da cuta ko tsanani da yelwa. Na daga cikin abin da ya inganta daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi cewa:(Duk wanda yake son Allah ya amsa mishi adu'a yayin tsanani da bakin ciki to ya yawaita adu'a lokacin yalwa ).
 Aikata aiki na alheri mai yawa   da falala mai girma, duniya ba za ta yi dadi ba sai da ambaton Allah , lahira kuma ba za ta yi dadi ba sai da afuwar sa, aljanna kuma ba za ta yi dadi ba sai da ganinsa,  ka kasance mai yawan ambaton lahaula wala kuwwata illa billahi don tana taimakawa wajen dauke abubuwa masu nauyi kuma tana  tunkude abubuwa na ban tsoro da tsanani, da ita ake samun daukaka a dukkan  yanayi  Allah ne wanda ake neman taimako a gare shi , kuma a gare shi ake dogaro, babu dabara ko karfi sai ga Allah mai girma .

  HUDUBA NA BIYU :
 Ya ku Musulmai
 mumini mai kadaita  Allah  mai kiyaye dokokin Allah , mai lazimtar biyayyar sa da kuma biyayyar Manzonsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi Allah na tare da shi  da kiyayewar sa na musamman Allah madaukakin sarki ya ce :(  Allah yana tare da wadanda suka yi takawa  da kuma wadanda suke su masu kyautatawa ne  ).
Wanda Allah ya kasance tare da shi to lallai yana tare da bangaren da ba a yin galaba akansu,  kuma da mai kiyayewanda   ba ya yin bacci da mai shiryarwan da ba ya bacewa , kamar yanda katada ya ce: (  lallai ita mai taimakawa ne tana hukunta samun nasara da karfafa da kiyayewa da taimako da  fita daga zaure na bakin ciki da wahalhalu masu tsanani.
 Duk wanda ya kiyaye Allah ya kuma kiyaye hakkokin sa  zai same shi gaba gare shi  a duk halin da yake ciki  wanda ya nemi sanin Allah a lokacin yalwa to Allah zai kawo mi shi dauki a yayin tsanani,  sai ya tsiratar da shi a yayin tsanani ya kubutar da shi daga musibu,  wanda ya yi mu'amala da Allah  da takawa da biyayya   , cikin yardan sa to Allah zai masa mu'amala da tausasa wa  da taimaka wa  a yayin fadawarsa cikin  tsanani,   ya zo a Hadisil kudusi : (Bawa na ba zai gushe ba  yana kusanta na da nafilfilu har na so shi  idan na so shi sai  na kasance  jin sa da ya ke ji da shi,  da kuma ganin sa da yake gani da shi da hanunsa da yake damka da shi ,  da kafarsa da yake tafiya da itakuma  idan ya roke ni zan ba shi , kuma idan ya nemi tsari na zan bashi)  Buhari ne ya rawaito.
Sannan ku sani mafi tsarkin abin da rayuwarmu za ta mike  da shi shagaltuwa da salati da aminci ga Annabi mai girma,  ya Allah  ka yi dadin tsira da aminci da albarka ga bawanka  kuma manzon ka Annabinmu Muhammad ,  ya Allah ka yarda da Al-kulafa'ur rashidun
Abubakar daUmar da Usman da Aliyu ya Allah ka  gyara halayenmu da halayen musulmai, ya Allah ka yaye bakin ciki  ka gusar da bacin rai , ya Allah ka tsiratar da bayin ka musulmai daga dukkan wata jarabawa da fitina , ya Allah ka yi maganin makiya musulmai domin su ba za su gagare ka ba   ya mai girma , ya Allah   ka kiyaye 'yan uwan mu musulmai a ko ina ya Allah ka kasan ce mai taimakon su da ba su nasara  ya  mabuwayi ya mai karfi,  ya Allah ka datar da kadimul haramaini  ash-sharifaini  cikin abin da ka ke so kuma ka yarda da shi ya Allah ka taimaki addini da shi ka daukaka kalmar musulmai da shi,  ya Allah ka gafartawa musulmai maza da musulmai mata rayayyu daga cikin su da matattu ya Allah ka bamu kyakkyawa anan duniya da kyakkyawa a lahira  kuma ka kare mu daga azabar wuta .  
         




السبت، 4 مارس 2017

HAKKOKIN MA'AURATA NA SHEIKH BUDAIR

HUDUBAR JUMA'A A MASALLACIN ANNABI  13/05/1438AH, NA SHAIKH SALAH BIN MUHAMMAD AL-BUDAIR.
HUDUBAR FARKO:
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, wanda falalolinsa sun game a wurin yalwa, ni'imominsa kuma sun kasu iri iri a rabe ko a tare, Na shaida ba abin bauta wa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya, wanda ya ce :Duk wanda ya kusanc ni da kwatankwacin taki to zan kusance shi da zira'I, na shaida Annabinmu  kuma shugabanmu Muhammad  bawansa ne kuma Manzonsa ne, falalarsa  na da yawa tamkar girgije,kimarsa ya fi karan hanci,kyawawan halayensa ya fi cikakken wata  haske, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da iyalansa da sahabbansa da suke tsinkaya daga haskensa, da kuma bin sawunsa, salati na har abada mudin sama na haskakuwa da wata kasa na kawatuwa da ruwa.
Bayan haka , Ya ku Musulmai:
Ku ji tsoron Allah  don shine abu mafi daraja da zaka samu, biyayya gare shi ke kai wa kololuwa. (Ya ku wadanda suka bada gaskiya ku ji tsoron Allah hakkin tsoronsa kar ku mutu face kuna musulmai) Al-Imran 102
Ya ku musulmai :
Hakkoki tsakanin ma'aurata biyu ya ta'allaka ne da Kulla aure, wanda kuma ke lazimta kyakkyawar muamala  da juna, kada  daya ya jinkirta bawa daya  hakkin shi, ko ya ki  bada abin da ke kan shi. Kyautata muamalarsa ga abokin zamansa da tausaya masa da juriya bisa ga cutarwarsa sabo da fadin Allah (su matayen suna da hakki akan maza irin wanda mazan suke da shi akansu, da abin sani.)
Ita kyakkyawar mu'amala da kyakkyawan zama ta fi kawo sanyin ido, da kwanciyan hankali da daddadan rayuwa, Allah madaukakin sarki ya ce :- ( ku yi mu'amala da su da kyakkyawa)  ma'ana ku yi cakudedeniya da abota da su, da bishara da kuma sakin fiska , da bada hakkoki da aka farlanta, kamar na daga sadaki da ciyarwa da raba kwana, da barin cutar da ita da kakkausar magana , da bijire mata,  da karkata zuwa ga watanta,  da rashin hada mata fiska, da turmuke mata ba tare da wani laifi ba , sa'annan Allah na ladabtar da bayinsa da fadin sa (  sa'annan kuma idan kun ki su , to, akwai tsammanin ku ki wani abu, alhali kuwa  Allah ya sanya wani alheri a cikinsa mai yawa)  a cikin ayan akwai kwadaitarwa bisa rike su da kyautata zamantakewa da su, ko da mazajen sun tsani wani abu daga cikin halayen su, domin rai ya ki abu ba ya nuni da kore alheri ga wannan abu, ta iya yuwuwa  abinda rai ya ki ya zama shi ya fi amfani a addini, kuma ya fi zamewa abin godiya a karshe , sau da yawa abin ki kan komawa abin yabo, kuma abin yabo kan koma wa abin zargi, Hakika  miji kan tsani mata  sabo da wata sifa daga cikin sifofinta, amma kuma a rike ta din akwai wani alheri da yawa da bai sani ba,   kuma ba zai gane hakan ba, Abdullahi dan Abbas  Allah ya yarda da shi da mahaifin shi ya ce: "Ta iya yiwuwa Allah  zai azurta shi da Da daga gare ta , sai Allah ya sanya alheri mai yawa acikinsa."
Ya ku musulmai:
Lallai mutum yana da wahala ya samu wanda ya ke kauna  wanda bai da wani abu da ya ki tare da shi  ,  to yayi hakuri da abin  da ya ki sabo da abin da ya ke so,  yana da wahala ka samu mutane biyu  suna mu'amala ko wannensu ya yarda da dukkan dabi'un junansu, ba wasu mutane biyu da za su yi mu'amala  da junan su fa ce daya na kawaici ga dan uwansa, An karbo daga Abu huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:-  ( Kada mumini ya tsani mumina, idan ya ki wani hali na ta to zai so wani hali nata ) Muslim ne ya rawaito .
Wato kada  mutum ya ki matar sa ki na gaba daya wanda zai sanya shi ya rabu da ita ya sake ta ya warware kullin aure, to idan ya tsani wani hali nata mara kyau to kuwa zai samu wani hali nata abin yarda.
To  ya ku mazaje :
  ku riki matayenku kar ku yi gaggawan kosawa ko fada, kar ku yi gaggawan rabuwa   kada ku yi gaggawa zuwa ga shika , kar ku kambama abu wurin nuna tsana da kiyayya  sau da yawa rauni na hankali  yakan yi galaba a kan mutum,  fushi ya rinjaye shi  sai ya yi aiki na wauta da shirme  ya yi gaggawa  ya yi shika sannan daga baya kuma ya dawo yana nadama a halin kuma wato komai  ya tsere mishi  ya wuyata  ta koma  gare shi.
Ya ke mata mumina:
 kar ki zama cikin masu ci don tarawa, kuma ki zama kina yawaita zargi, mai yawan hayaniya da saurin fushi, wacce bata bin umarnin mijinta , kuma in ya yi rantsuwa bata biye mishi  , ki kyautatawa mijinki , ki kasance kusa da kaunarsa, mai taimaka masa yayin bukatarsa  mai amsa kiransa,  mai sauka zuwa ga bukatarsa  mai ambaton  falalarsa da   kyautatawarsa, kar ki zama mai munana mishi mu'amala  , kar ki yi musu da shi yayin fushin sa da fusatan shi,  kar ki tsawwala mishi  yayin da ya cije ko ya harzuka .
 Mu'awiya Allah ya kara mishi yarda ya ce da Akil dan Abu talib : " A cikin mata wacce tafi soyuwa a gareka ? sai ya ce :- mai biyewa  abin da mu ke so, sai yace " To waccece kuma ka fi ki acikinsu ?sai ya ce :" wacce tafi nesa da abin da kake so ", sai Mu'awiya ya ce :- wannan suka  na duniya kenan, sai ya ce:-Da  ma'auni na  adalci .
 An karbo daga abu Uzaina Assadafi    Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:- (Mafi alherin matanku sune,  masu tsananin kauna masu  yawan haihuwa , mai aikta  (abin da ka ke so)  mai share ma hawaye, muddin suka ji tsoron Allah , mafi sharrin matayen ku kuma sune masu bayyana tsiraici , masu alfahari sune munafukai, ba wanda zai shiga aljanna a cikin su, face kamar farin hankaka.)  Baihaki ne ya fito da shi, Farin hankaka  wato mai farin fiffike da kafafuwa: yana nufin karancin masu shiga aljanna a cikinsu, don samun wannan sifa na da wahala a cikin hankaki.
 An karbo daga Husain dan  Mihsan daga wata gogon  shi cewa ta shiga wurin Manzon Allah sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata  agare shi ,  sai ya biya mata bukatar tata , sai manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce mata ( ko ke  kina  da miji ? sai  ta  ce e,  sai ya ce   yaya kike a gun shi? sai ta ce bana gajartawa ( a hakkinsa) sai abinda ya gagareni,  sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:- to,  ki duba matsayinki a gunshi domin shi ne aljannan ki kuma wutanki)  . Nasa'I ne ya rawaito shi
Idan rayuwa ta kasance ana rayata cike  da  kyawawan halaye ba kiyayya ba gaba, to ya haramta akan mace ta nemi shika , ko kuma ta nemi kul'i, a daya daga cikin zantuka mafi inganci a maganganun malamai,
An karbo daga saubana Allah ya kara mishi yarda ya ce:- Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi  ya ce  ( Dukkan matan da ta tambayi mijinta saki ba tare da wani laifi ba to, kamshin aljanna ya haramta a gare ta ) Abu Dauda da Tirmizi ne suka  rawaito.
An karbo daga Ukubata dan Amir Allah ya kara yarda a gare shi ya ce :-( Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:-  lallai mataye wadanda suke neman fansa,  da masu neman  warware auren su sune munafukai ) Dabarani ne ya rawaito shi    Ibnu kudama ya ce :- wannan yana nuni cewa haramun ne  yin khul'I ba tare da bukata ba sabo da akwai cutarwa ga ita da kuma mijin nata ,  da kuma  gusar da maslahohin aure ba tare da bukata ba,  sabo da haka ya haramta.
Mustahabbi ne  a sulhunta  tsakanin ma'aurata  biyu wadanda suke rikici da junansu
An karbo daga Abdullahi dan Abbas Allah ya kara yarda a gare su shi da mahaifinsa  cewa mijin  barira ya kasance bawa ana ce da shi  Mugisu, kai  ka ce ina kallo zuwa gare shi yana  shawagi a bayanta yana kuka  hawaye na zuba  a gemun sa,  sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya ce ga Abbas :-  (  Ya Abbas baka mamaki irin kaunar da mugisu yake yi wa barira da kuma irin kin da barira take yiwa shi Mugisu?  sai ya ce da ita da kin koma mishi, sai ta ce ya Manzon Allah umarni ne ka ke min?  sai ya ce: a'a  sai dai kawai ina nema mishi alfarma ne, sai ta ce bani da bukata  zuwa gare shi  ).Buhari ne ya fito da shi.       
Ibnu Hajar –Allah ya rahimce shi - yace : " wannan Yana nuni cewa idan mace ta ki miji bai kasance wa ga waliyinta da ya tilasta mata kan zama da shi. Idan ta so shi kuma bai kasance wa ga waliyinta da ya raba su,
 Allah ya amfanar da mu da Alkur'ani da sunna da abin da ke cikin su na daga ayoyi da shiriya bayyanannu da wazi da hikima.
Ina neman gafaran Allah ku nemi gafararsar sa, Ubangiji na Makusanci ne Mai amsawa.
 HUDUBA TA BIYU
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Mai shiryar da wanda ya nemi shiriyarsa, Mai bada kariya ga wanda ya nemi kariyarsa, Mai isarwa ga wanda ya kirdadi yardarsa, na shaida ba abin bauta wa da gaskiya sai Allah ba wanda ya cancanci a bauta wa da gaskiya koma bayan shi, Kuma na shaida Annabinmu   kuma shugabanmu  Muhammad bawansa ne kuma manzonsa ne, Allah ya yi dadin tsira a gare shi da iyalansa da sahabbansa da wanda ya bi sunnarsa  ya nemi shiriya da shiryarwarsa.
Bayan haka Ya ku Musulmai !
Allah ya sanya shika da warware igiyar da aka kulla tsakanin ma'aurata biyu a hanun miji, sai dai  ya haramta ya munana amfani da hakkin nasa cikin sakin da rikon sa wata hanya don ribatar ita matar da firgita ta, ya sanya shi kamar wata bulala ce a fiskar ta don ya bautar da ita da tsorata ta, da walakanta ta, Allah madaukakin sarki ya ce : ( To ku rike su da kyautata wa ko ku sake su da kyautata wa.) An karbo daga ASSUDI  kan fadinsa  (ko a sake su da kyautata wa) " Da ya bata cikakken hakkinta kada ya cutar da ita, ko ya zage ta, "
Wanda ya katange matarsa bai sake ba bai kuma barta ta yi aure ba idan iddarta ya kare, ya cutar da ita da duka, da kuntata mata, ko ya hana ta hakkokinta na daga ciyarwa da kason kwana, da makamancinsu don ta fanshi kanta daga gare shi, sai ta yi, to khulin ya baci kuma zaa maida mata abin da ta bada don fansan.  
 Allah madaukaki ya ce: ( Kuma kada ku hana su aure domin ku tafi da sashen  abin  da kuka basu ).
Idan ta zo da alfahasha sai ya hana ta aure don ta fanshi kanta daga gare shi sai ta yi hakan to khul'in ya inganta. Sabo da fadin Allah Madaukaki: (kuma kada ku hana su aure domin ku tafi da sashin abin da ku ka ba su, face idan suka zo da wata alfahasha bayyananniya.)
Ba ya dace wa rike wacce ba ta kamun kai, sabo da tawaya ne ga mijin a addinin shi da dabiunsa da bata sunansa da zubar da mutuncinsa, bai da amincin kada ta bata mishi shimfidinsa da jingina mishi wani da da ba nashi ba, kuma mace mai sakaci da hakkokin Allah na wajibi kamar sallah da makamancinta, wacce ba ta jin nasiha  Mustahabbi ne a sake ta.
Ya ku Musulmai :
Daga cikin mazaje akwai wanda  ya sanya furta shika da yawaita shi abin ambato a bakinsa kuma abin sabon shi da al'adan shi,da abu mafi soyuwa a gare shi a abu mai kima da mara kima da babba da karami da mai girma da abin da bai taka kara ya karya ba.
Na daga cikin al'adu mara kyau akwai  rantsuwar shika
kamar yace : In kiyi magana da wane to mata ta ta saku,ko saku ya tabbata a gare ni idan na ci abincin wane. Ko shika ya tabbata  a gare ni muddin kika yi  tafiya da wane, ko shika ta tabbata a gare ni muddin mata ta ta shiga gidan wane, ko yace wa bako: Shika ta tabbata a gare ni muddin baka ci abinci a gu na ba, wannan dare , ko kuma in gobe baka ci abincin dare a guna ba, amma ba shikan yake nufi ba, ko rabuwa ba, sai dai ya yi hakan ne kamar rantsuwa, don yana nufin kwadaitarwa ko hanawa,ko tilastawa.
Wadannan lafuza ne haramtattu da ayyuka ne na laifi, da walakanta rayuwan zamantakewa da rena hakkokin mace da yara da wasa da shika  da hukunce – hukuncenta.
Ya wajaba ga miji ya kiyaye harshensa daga yawaita furucin shika, da tsoratarwa da ita da jirwaye da kamar ruwa game da  aukar da ita.
Ibnul Arabi yace a cikin Ahkamul Kur'an : (Na daga cikin rikan ayoyin Allah da izgilanci abin da aka rawaito daga Abdullahi dan Abbas kan cewa an tambaye shi game da mutumin da yace da matarsa : Ke sakakkiya ce sau dari, sai yace : Ukun ya isan maka a gare ta, sauran casa'in da bakwai ka riki ayoyin Allah da su bisa izgili ).

Ku ji tsoron Allah ya ku Musulmai kada ku riki ayoyin Allah abin izgili kar ku ketare iyakokin Allah madaukaki,(Duk wanda ke ketare dokokin Allah to ya zalunci kansa) ,( kuma duk wanda ke katare dokokin Allah to wannan yana cikin azzalumai.)
Ku yi salati da sallama ga Ahmad Alhadi mai ceton talikai gaba daya to duk wanda yayi salati guda agare shi Allah zai mishi salati goma.
Ya Allah ka yi salati da aminci ga bawanka kuma manzon ka Muhammad da kuma dukkan Iyalai da sahabbai ka yarda da mu tare da su da baiwanka da karamcinka ya Mai karamci Ya Mai yawan kyauta.
Ya Allah ka daukaka musulunci da musulmai,ka kaskantar da shirka da mushrikai,ka ruguza makiya addini, ka sanya wannan gari cikin aminci da natsuwa, da wadata da yalwa da sauran kasashen musulmai.
Ya Allah ka datar da jagoranmu shugabanmu cikin abin da ka ke so kuma ka yarda da shi, ka riki makwarkwadan shi zuwa ga biyayya da takawa, ka datar da dukkan jagororin musulmai cikin yin hukunci  da shariarka, da bin sunnar Annabinka Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Ya Allah ka sanya arzikinmu cikin yelwa, kar ka sa wani ya mana dariyan keta, kar ka bawa wani azzalumi karfi akanmu.
Ya Allah ka warkar da marasa lafiyanmu, ka bada waraka ga wanda aka jarabta a cikinmu, ka jikan matattunmu, ka kwance kamammunmu, ka taimake mu a kan wanda ya yi gaba da mu, ya Ubangijin talikai.
Ya Allah ka dayyaba mu don haduwa da kai, ya Allah ka dayyaba mu don haduwa da kai, ka azurta mu da yarda da hukuncinka,ka sa mu wadatu da kyautarka, ka sa mu wadatu da halal naka akan haram naka.mu wadatu da falalarka akan waninka.
Ya mai girman afuwa, ya mai girman afuwa, ya mai yalwan gafara ya mai yalwan gafara, ya makusancin  rahama, ka gafarta mana baki daya, ka gafarta mana baki daya, ka sa mu walwala da takawarka, ka sanya mu ji tsoronka kamar muna ganinka.
Ya Allah ka bamu ruwa, ya Allah ka bamu ruwa, ya Allah ka bamu ruwa, ya Allah ka saukar mana da  ruwa kar ka sanya mu cikin masu yanke kauna.ya Allah ka sanya aduar mu karbabbiya ce, kiran mu daukakakkiya ce.
Karshen aduarmu  shi ne dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai.  


FALALAR MADINA DA LADUBAN MASALLACIN ANNABI NA SHEIKH SUDAIS

Hudubar Juma'a na Masallacin Annabi  4/6/1438 AH Tare da sheikh Abdurrahman Bin Abdul'Aziz Assudais
  Da sunan Allah mai rahama mai jin kai
 FALALAR   MADINA DA LADUBBAN MASALLACIN ANNABI  
Huduban farko
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah , muna gode maka , Ubangijina  muna neman taimakonka, muna neman gafararka muna tuba zuwa gare ka, kuma muna sake  kyautata dukkan yabo a gare ka  . To dukkan yabo ga Allah   ba yankewa ga zamanin shi*  iya adadin  abinda ya bada na ni'ima a halin godiya ya gajerta .
Ina yabo gare shi  bisa ga ni'imominsa masu yawa kuma ina gode mishi bisa falalolinsa masu yawa tsarki ya tabbbata a gare shi shi ne ma'abocin baiwa da kadartawa,  wanda ya kebanta da halittawa da zabi wanda ya fada a cikin littafinsa mafi hikima ,  kuma Ubangijinka yana halitta abin da yake so kuma yake zabi  Alqasas 68.
 Kuma na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya mabuwayi mai yawan gafara tsarki ya tabbata a gare shi shi ne Allah guda daya mai yawan rinjayi, na shaida Annabin mu Muhammad bawan Allah ne kuma Manzonsa ne  zababbe mafi alherin wanda yayi taku a kasar Daba ( Madina) gidajen ansarawa gurin hijiran sahabbai zababbu, Allah ya yi salati da aminci da albarka a gare shi da iyalansa tsarkaka, da sahabbansa masu biyayya da tabi'ai da wanda suka bisu da kyautatawa,  muddin dare da wuni na bibiyan juna.
BAYAN HAKA:
 Ya ku Musulmai: Daga mimbarin masallacin mafi alherin halittu , ina muku wasiyya da ni kai na da wasiyya mafi alheri, ku ji tsoron Allah mabuwayi da daukaka domin shi ne matattaran dukkan alheri kuma mabubbugan dukkan albarkatu, kuma shi ne aminci daga dukkan musibu, kuma kariya ne daga dukkan wasu bala'I (ya ku wadanda kuka yi imani ku ji tsoron Allah hakikanin tsoronsa  kada ku mutu face kuna musulmai)
Tsoron Allah shi ne tushen al'amari to ka sanya *** tsoron sa tattali don gyara al'amarinka
Kuma ka gaggauta himmatuwa zuwa ga mishi da'a ***domin fa baka sani ba yaushe ne za a tafiyar da rayuwarka
Bayin Allah , lallai mai lura a yanayi na wannan duniya   zai samu mafi girman dalili na kadaituwan Allah, da kuma mafi girman shaida bisa ga rububiyyarsa da cikan hikimarsa da iliminsa da kudurarsa kasantuan shi mabuwayi da daukaka  yana zaban abinda ya so na daga mutane da wurare  yakan kuma kebance abinda yaso na daga abubuwa da zamani sabo da wasu manufofi masu girma  da wasu manyan hadafi  wanda maslahohi na bayi ke dore akansu   bashi da abokin tarayya tsarki ya tabbata a gare shi yana zaba kamar irin zabinsa , kuma yana gudanarwa kamar irin gudanarwarsa    ( kuma Ubangijinka yana halitta abin da yake so kuma yake zabi  Alqasas 68).
Lallai na daga cikin mafi bayyana na wannan zabin, zabin sa da yayi tsarki ya tabbata a gare shi na daibataddaiba Madina garin Annabi don ta kasance garin hijira na Manzonsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi , ita take biye wa Makkah mafi alherin bigire  kuma mafi daukakan guri   da doron kasa  mai biye mata wurin alfarma da girmamawa,  da daukakawa da mutuntawa gari mafi kima ,  da sanyin idon garuruwa da adon kasashe  da hasken birane  lallai ita ce gari na masoyi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  matsira na itaciya mai yabanya daular farko na musulunci,   a cikin  ta ne ka'idodin addini ya cika  a kasanta ne mai tsarki a ka dabbaka hukunce-hukunce na musulunci da sha'anoninsa  , muna karantawa a tarihinta  tarihin al'umma, wacce aka haifa tare da bullowan alfijir rananta ta haska  tare da wanzuwansa tarihinsa ya haska , sai ga shi nan tattare da shi akwai tarihi na daula wanda ke cike da dukkan ma'anoni da siffofi masu kyau na imani  da akida , da raya kasa, da ilimi, da ci gaba, lallai ita ne Almadinatul munauwara bata gushe ba da alheru da albarkatu da suke kewaye da ita Daiba masoyiya , kuma daba mai hankali . 
Allah ya sanya ta mafarin sakon Musulunci   madauwami  kuma wurin saukan wahayinsa  kuma mashinfidi na da'awar Annabinsa , kuma  wani kango ne na daga kangoyen shiriya , kuma dutse ne madaukaki , kifiyoyin makiya  na faduwa a gabansa , ita ce manara na musulunci kuma makwancin imani, kuma wurin renon akida , kuma matattaran  ci gaba , kuma daga inda jagoranci ya tashi  da jan ragama  na duniyan musulunci  bisa  haske  na manhajin tsakatsakiya da daidaito nesa daga  fandarewa da ketare iyaka, da kuma ta'addanci da bangaranci da tsoratarwa ,  da kuma tabbatar da bin littafin Allah da sunna kamar yanda Allah madaukakin sarki ya ce : (  ku yi riko da igiyan Allah gaba daya kar ku rarraba ).
  Daga nan ne ci gaba na musulunci ya taso  ya busa alheri , da aminci da rahama  da adalci da rangwami da salama ,  (  Ba mu turo ka ba sai rahama ga talikai)  bisa ga tushen tauhidi da tsarkake addini a gare shi da tabbatar da akida ingantacciya  da lafiyayyen kuduri , da manhaja mikakkiya  da kuma  samun daukaka na alamomi na addini ,  aka daga tuta na sunna da lazimtar manhaja na magabata na korai wanda  wannan kasa mai albarka ta tafi a kai .
  A Daiba akwai zane na Annabi da kuma  Ma'ahad ***
 mai haskakawa hakika zanen kan goge asake shimfida shi  amma ayoyin ba sa goguwa daga gida mai alhurma***
 a gare ta akwai mimbari   na shiriya wanda ya kasance yakan haura  da ayoyi bayyanannu da sauran manya-manyan wurar***da guri na shi da yake salla da sujjada
Akwai dakna wanda yakasance  a tsakiyar su yake sauka *** wani haske daga Allah da ake haskakawa da shi kuma a kunna
Wasu manyan alamomi bisa tsawon zamani ba a shafe alamomin su ba  *** lalacewa ya zo musu amma an asake sabunta alamomin na su
Ya ku jama'ar musulmi :
 Lallai itane Madina da ake cewa Daibatuddaiba garin hijira  kasar sunna  wanda ya ziyarce ta  don neman kusanci da lada  da kuma kauna na wadannan guraren  Allah zai saka mishi ya kuma bashi lada, ase ba ita ce masulalan imani ba  garin hijiran shugaban dan  adnan  amincin Allah da salati su tabbata a a gare shi mafi cika da kamala Buhari da Muslim sun fitar a hadisin (Abu Huraira Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce lallai imani na sulalewa zuwa ga Madina kamar yanda macijiya ke sulalewa zuwa raminta  )
Wannan gaba gare kiu Daiba ne da gidajenta *** hakika ansa albarka wa gidajen a cikin talikai 
Wannan Madina hakika  an dora mata kambu samanta   wanda aka sanya mata shiriya
Ita ce masulala na imani a zamanin da yake koka tsagewan gini na ababan mutunci
Ya ku 'yan uwa na na imani: na daga cikin falalanta Allah ya dada  kiwata ku , lallai Allah wanda sunan shi ya daukaka yabon  shi ya girmama  hakika  ya kara imani akanta inada ya ce: ( da wadanda suka zaunar da gidajen su (ga musuiunci)  kuma (suka zabi) imani , a gabanin zuwansu  suna son wanda yayi hijira suwa gare su  kuma basa tunanin wata bukata a cikin kirazansu daga abinda aka baiwa muhajirina , kuma suna fifita wadansu akan kawunansu kuma  koda suna da wata lalura. Wanda ya sabawa rowar ransa  , to wadannan sune masu babban rabo ) Alhashr aya na 9
Imamu Malik Allah ya mishi rahama yana cewa: a cikin  siyakin ambaton sa na falalan madina  akan watanta na daga sassan duniya( lallai Madina ambata  masauki na imani da hijira  , amma watanta na daga alkaryu an bude su ne da takuba) .
Kuma na daga cikin falalarsa lallai Allah ya  umarci Annabin shi da hijira zuwa gare shi an karbo daga Abi Musa   ya rawaito daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :  (Ya gaci cikin bacci y a ce lallai ni zanyi hijira daga garin makka  zuwa wata kasa  wanda ke da itatuwan dabino , sai tunani na ya tafi kan  Yamama ko Hajar ase ita ce garin Madina Yasriba ) Buhari da Muslim ne suka rawaito.
 'Yan uawa Musulmai:
 Ya masoya shugaban halittu- Allah ya kara haske fiskokin ku ,  ku saurara na daga cikin mafi daukakan falaloli na madina :- an gina masallaci na Annabi a cikinta , wanda an assasashi ne akan tsoron Allah,  Allah madaukakin sarki ya ce : (Kada ka tsaya a cikinsa har abada. Lalle ne Masallaci wanda aka yi harsashinsa akan takawa tun farkon yini , shi ne mafi cancantar ka tsaya a cikinsa. A cikinsa akwai wadansu maza suna son su tsarkaka. Kuma Allah yana son masu neman tsarkakuwa) Tauba :108
Muslim ya fitar a sahihinsa na daga hadisin Abu sa'id Alkhudri yace : ( Na shiga wa manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a halin yana dakin wasu shashi na daga matayensa : sai na ce ya manzon Allah wani masallaci ne cikin masallatayya biyu  aka yi harsashinsa  a kan takawa? ya ce : sai ya dauki cikin tafi na tsakuwoyi  ya buga su ga kasa, sannan yace : wannan masallacin naku ne," ga masallacin Madina .
Na daga cikin falala na wannan masallacin mai albarka shi ne daya daga cikin masllatayya uku da ba ya halatta a nika gari sai zuwa gare su. An karbo da Abu Sa'id Alkudri Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : na ji manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : Kada ku nika gari sai zuwa ga masallatayya guda uku: Masallacin Makka da wannan Masallacin nawa da Masallacin Aksa) Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
Na daga cikin falalarsa kuma ana ribanya ladan sallah a cikinsa na farilla ne ko na nafila, cikin zance mafi inganci na malamai, An karbo daga Abu Huraira Allah kara yarda agare shi ya ce  :Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : Sallah a Masallaci na ya fi sallah dubu a wani masallaci sai dai Masallacin Makkah) Bukhari da muslim ne suka rawaito
Kuma masallaci na ya kasance kai bai ma gushe ba abin buri ****
Zukatan da suka bata hanya  na rarrafawa zuwa gare shi.
Akwai miliyoyi da ke kwana bisa kauna ta su wayi gari ****
Cikin tunani na da haukan kauna ta idan sun yi tafiya.
  A cikin sa akwai bigire wanda Dausayi ne daga cikin dausayi ne Aljanna, An karbo daga Abu Huraira Allah kara yarda a gare shi, yace : Tsakanin gida na da minbari na dausayi ne daga cikin dausayin Aljanna. Kuma minbari na na kan tabki na,) Bukhari da muslim ne ya rawaito.  Kuma a riwayar Ahmad : Minbari na wannan na  kan tabki daga cikin tabkunan Aljanna, a riwayar Nasa'i, kuma lalle kafafun Minbari na matabbata ne a Aljanna.
 Ya jama'ar musulmi  hakika Allah ya sanya wannan gari mai daukaka  harami amintacce ba a zubar da jini a cikinta ba a daukan makami  don yaki, Muslim ya fitar a cikin Sahih nasa daga hadisin sahlu dan Hanif Allah ya kara yarda a gare shi yace : Manzon Allah ya sunkuyo da hanun shi zuwa ga Madina sai ya ce :(Ita  Harami ne amintacce)  
Madina na da Alhurma tun daga tsakanin duwatsunta biyu da konannun duwatsunta biyu da Manyan duwatsunta da hanyoyi tsakanin duwatsun. Daga Aliyu Allah kara yarda a gare shi yace : ( Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:  Madina harami ne tun daga dutsen Air zuwa saur) Bukhari da Muslim ne suka rawaito
Ba a koran abin farautar ta, baa kama tsuntsunta ko abin farautar, ba a yanke kayarta, ba a tsinke itaciyarta, ba a cire ciyayinta, ba a cire danyen itacenta ba a cire wata bishiya deaga ita sai dai idan mutum zai yi ciyayi wa rakumin ba a tsintan tsintuwa a cikinta sai ga mai shelantawa  ba wan da zai yi makida ga mutanen garin  Madina ko ya nufe su da mummunan abu ko  sharri face  ya narke kamar yadda gishiri ke narke wa a ruwa Manzon shiriya tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yake cewa: ( duk wanda ya tsorata da mutanen Madina bisa zalunci   mabuwa yi da daukaka Allah zai tsorata shi kuma tsinuwan Allah ya tabbata a gare shi da Mala'iku da mutane baki daya , Allah ba zai karbi daga gare shi ba ranar alkiyama , aiki na farilla ko na nafila ).  Imamu Ahmad ne ya rawaito shi
 YA KU MUSULMAI:
Wanda ya bayyana a Madina wata bidi'a  ya fari wata barna ko ya bada  mafaka  ga mabarnaci to ya kai kan shi ga halaka mai tsanani, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa : (  Madina harami ne   tsakanin  dutsen air zuwa dutsen saur duk wanda  ya farar da  abu a cikinta  na fitina ko ya bada mafaka wa mabarnaci to  to tsinuwan Allah ya tabbata a gare shi da Mala
Ikunsa da Mutane baki daya ba za a karba daga gare shi ba  aikin farilla ko na nafila)  Buhari da Muslim ne suka rawaito .
 YA KU BAYIN ALLAH:
Na daga cikin falalan Madina  ita ce masoyiyar masoyi  masoyiyar abin kauna  tsira  da amincicin Allah su tabbata a gare shi  wanda ya kasace yana cewa : ( Ya Allah ka sanya son garin Madina zuwa gare mu kamar yanda kamar yanda muke son garin Makka ko ma sama da haka  ) Buhari da Muslim ne suka rawaito .
 Ita ce gidan shi wurin hijiran shi a nan ne ya kafa mihrabinsa kuma ya  daga mimbarinsa  a ciki ne kuma makoncinsa yake kuma a nan ne za atada shi .
 Wurin hijiranMusdafa mai shiryarwa kuma makwancinsa*** wanda yake abin komawa ga jarumai idan tsanani ya tsananta
Abin komawa ga zakuna idan yaki yayi tsamari***
Gari ne na masoyi gari ne abin kauna ga mazauna daiba wurin masauki  zamewa a cikinta tare da imani daukaka ne kuma da yalwa zamewa dan garin tare da tsoron Allah daukaka ne kuma da kaiwa kololuwa
Ya jin dadin wanda suka zauna a cikinta***ya walwalan mazauna cikinta *** Ya rabautan wanda ya jibinci zama acikinta har mutuwa ta zo mishi a kasanta
 An karbo daga Abdullahi dan Umar Allah ya kara mishi yarda shi da mahaifinshi  ya ce Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( duk mutumin da zai iya ya mutu a garin Madina to ya aikata haka  domin ni zan yi ceto ga duk wanda ya mutu acikinta) Imamu Ahmad ya fito da shi.
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance idan ya dawo daga tafiya yakan dubi kangonnin Madina  da kuma manya-manyan itatuwanta   da kuma darajojinta  sai ya kafe abun hawarsa sai ya kada dabbarsa sai ya ingizata  ya sata ta kara sauri don kaunan wannan gari na  Madina idan ya fiskantota sa ya ce : ( wannan garin Daba ne sai ya ce wannan kuma Uhudu ne dutse ne da yana son mu , muna son shi  ).
Na daga cikin falalansa cewa tsoro na Dajjal ba zai shigo mata ba ko firgici ba zai zo gare ta ba  kafansa shi Dujjal ba zai taka zuwa gare ta ba Mala'iku suna kofofinta  suna bakin garin da kofofinta da hanyoyinta da mashiganta suna gadinta suna bada kariya a gare ta an karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya ce  :( A bakin kofofin Madina akwai Mala'iku wanda annoba ba zai shige ta ba ko kuma dajjal ) Buhari da Muslim ne suka rawaito.
Ya ku Musulmai:
 Zama a cikinta akwai albarka wanda zai sa a dauki watanta ba komai ba a wurin yalwa na rayuwa da rafahiyya ,  an karbo daga Abu Huraira  Allah ya kara yarda a gare shi ya ce  Manzon Allah tsira da Amincin  Allah su tabbata a gare shi  ya ce :(   Wani lokaci zai zowa mutane mutum zai kira dan baffansa da makusancin shi , taho zuwa ga yalwa , taho zuwa ga yalwa , kuma Madina ne tafi alheri a gare su da sun kasance sun sani . ) Muslim ne ya rawaito shi
  Ya ku mazauna cikin Daiba    ya ishe ku *** daga tafiya zuwa neman daukaka kusantan Ahmadu
To duk mai neman wanin ta  zuwa wani gari ko da ta daukaka*** game da wani a bin duniya to bazai  samu shiryuwa ba.
 'yan uwa na imani:
  Madina na da albarka a sa'in sa da mudun ta da kilonta  da dabinon ta  da kadan nata da mai yawanta  Annabi ya masa addu'a ya ce: (  Ya Allah ka sanya a madina  ribi biyu na abinda kasanya a Makka na albarka) Buhari da Muslim ne suka rawaito
YA JAMA'AR MUSULMI :
Wannan ita ce Daba  garin shugaban halittu : Falalolinta basa kirguwa, albarkatunta basa kididdiguwa  , ya zauna a tsawon tarihi a shudewan karnoni  gini ne na kololuwa ta zamana wuri ne katangange na imani da 'yan uwantaka   da kuma makoma ne na akida kuma masdari ne na da'awa  .
 Allah mai girma!  a Daiba akwai kamsasan  abubuwa na tunawa , na dindindin  akwai kuma kamsasan abubuwa na gwarzanta na daukaka.
YA KU MUSULMAI:
Lallai bada kulawa ga Madina madaukakiya  ya doru a kanmu , da kuma bada kulawa ga girman alfarmarta ga dukkan alheri da ta kunsan  kuma hanyar yada darajar ta abu ne mai kawo ceto,  falalanta gami da   tattaro wurarenta na daukaka  ta dace da wuraren da aka raya su da wahayi da saukarwa  Jibrilu da Mika'ilu sun yi kai koma a cikinta    mala'iku sun haura da Mala'ika Jibrilu  dan a girmama farfajiyarta a shaki kamshin iskarta  a ribaci lokutan cikinta a kuma yawaita ayuka na kwarai a cikinta .
Ya gidan mafi alherin Manzanni da wanda ke tare da shi*** an shiryar da mutane  kuma an kebe shi da ayoyi
Ina da tsananin kauna a gare ki  da matukar  so ***  da kuma  shauki mai kunna  garwashi.
   Ya jama'a makusanta abin misali ,  ya dace ga duk wanda ya nufi kusantar Madina ya zamana yana da saukin hali  da tausasawa mai kiyaye alhurmar wurin nata  tare da la'akari da mazaunanta , ya yi tarayya da su a majalisain su ba a kalacen su ba  ya yi cunkoso tare da su a lokutan su ba a abincin su ba , ya kuma ribaci halayensu ba arzikinsu ba  ya tsinkaya daga biyayyansu ba daga alkamarsu ba , kuma ya kwadaici kaunarsu ba kwayarsu ba .
Ya tawagan maziyarta zababbu :- ga ku kuna gabatowa zuwa garin Musdafa Al-mukhta'; na bada fasan mahaifina da mahaifiya ta a gare shi tsira da   amincin Allah su tabbata a gafre shi – ku tuna wajabcin bin sunnarsa  da taku kan tafarkin sa, da sha a koshi daga tarihin sa Allah madaukakin sarki ya ce : (  in kun kasance kuna son Allah to ku bini Allah zai so ku kuma ya gafarta muku zunuban ku) Ali Imran 31
  Abinda da'ansa da kaunar sa ke hukuntawa  shi ne neman sanin laduban ziyarar masallacin sa da laduban yin sallama a gare shi da abokan shi biyu- yardan Allah ya tabbata a gare su – da kuma laduban zama a garin sa  Madina na Annabi abin haskakawa  , bata gushe ba tana  albarkatu     na kewaye da ita a katanganta  da kuma  kadaita Annabi wurin  bin shi, a halayen sa irin na Muhammad  , da kuma dabi'unsa na zababbe da kuma rashin shan gabansa ko da ga sauti a wurinsa.
 Ya ku wadanda suka yi imani kada  ku daukaka sautunttukanku bisa sautin Annabi , sama  kuma kada ku  bayyana sauti gare  shi  a magana kamar bayyanawar sashinku ga sashi , domin kada ayyukan ku su baci alhali kuwa ku baku sani ba ).
AL'UMAR MUSULMI:  Lallai wajibi ne a gare mu gaba daya da mukula da laduba game da wannan gari na Madina mai tsarki sai dai-Allah abin neman taimako!- Shin na daga ladabi bawa ya aikata acikinta abinda zai sabawa akida ingantacce   da sunna mikakkiya , ko kuma ya kirkiri wata bidi'a ko wani abu na sabawa?! 
 Ku ji tsoron Allah Ubangijinku-ya ku musulmai- ku kyautata ladabi tare da garin shugaban halittu  ku lazamci dukkan laduba na Musulunci a masallacin mafi alherin halittu, lallai wajibi ne a gare mu gaba daya da mu yabi Allah mu gode mi shi bisa abinda ya bamu  na ni'ima a wannan bigire mai albarka , kuma mu kula da ladabi a cikinta da zaman lafiya da bin tsari a gidaddajenta   da kuma  tsakanin maziyartanta  kuma maziyartanta  su kimtsa don  ziyara , kada su shagaltu da barin ibada ta hanyar amfani da wayan tafi da gidanka ko daukan hotuna ko makamantan su su nisanci cunkokso da cutar da 'yan uwansu, kuma mace idan ta halarci wannan masallacin mai daraja ya da ce ta siffantu da hijabi da kame kai kuma rashin cakudaidainiya da maza .
muna rokon Allah da ya azurta mu da ladabtuwa da   laduba na musulunci kuma ya azurtamu da binsunnan shugaban halittu da baiwansa da karamcin sa  kuma ya azurta Musulmai da ladabi na kusanci da kyautata zama  a kusa da shugaban halittu mafi girman salati da  mafi tsarkin aminci a gare shi   kuma bisa  ga iyalansa da sahabbansa masu karamci .
 Ina neman tsarin Allah daga sharrin shaidan abin jefewa
 (Lallai abin koyi mai kyau ya kasance gare ku daga manzon Allah ga wanda ya kasance yana fatan rahamar Allah da ranar lahira  kuma ya ambaci Allah da yawa )
Allah ya sa mini albarka ni da ku  a wahayi biyu kuma ya amfane ni da ku da shiryarwan  shugaban haliyttu   (aljanu da mutane)  ina fadi na wannan kuma ina neman gafaran Allah da ni da ku da kuma dukkan Musulmai , ku nemi gafaransa domin shi mnai yawan gafara ne mai jin kai.
HUDUBA TA BIYU:
Dukkan yabo sun tabbata ga Allah mai wadatarwa da ni'ima da baiwa na shaida ba bu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya  ya korara mana daga ni'imomin shi masu yawa   cikin aminci da imani, kuma ya yalwata a gare mu na daga karamcin ludufinsa,  na baiwa da kyautata  na shaida cewa Annabinmu Muhammadu bawan Allah ne kuma Manzon sa ne Allah ya yi dadin tsirada aminci da albarka a gare shi da ilansa da sahabbansa  , da tabi'ai dawanda  suka bisu da kyautatawa zuwa ranar sakayya
 BAYAN HAKA:
Ku ji tsoron Allah- bayin Allah- ku gode mishi bisa abinda yayi na baiwa a gare ku game da wadannan wurare masu  tsarki da bigire madaukaka.
 'Yan uwa na musulunci ku saurara : na daga cikin falalan Allah madaukakin sarki   wannan gari na Musdafa ya rabauta da karin kulawa   daga jagorori na wannan gari mai albarka  tunda a ka kafa har zuwa yau . Mafi hasken hujjoji dake furta  haka da dalilai masu nuna  hakan    :  wannan fadadawa na gini na tarihi mai bankaye  mai jan hankali wanda ake kidanya shi cikin abin alfahari ga duk wani Musulmi kuma haske ne mai haskakawa a fiskan tarihi ta yanda zai bada daman  tattaro adadin mafi girma na masu nufo wannan masallaci na Annabi  da kuma masu ziyarar sa daga sassan duniya  don hidima ga  masallacin Musdafa amincin Allah ya tabbata a gare shi  da neman hutu ga maziyartan shi  da masu nufo shi da basu dama don yin ibadansu da biyayyan su cikin tsari na hidima na musamman ,  acikin wani yanayi wanda  ke kunshe da sauki da natsuwa ,  hakika a maganan gaskiya ta dace a nada mata kambu na  hedkwata  na har abada  na wurin shakatawa da kuma wayewa na musulunci  .
 Ya 'yar uwar makka a sama ki yi haske***  ki yi alfahari cikin dimuwa kina ma adontawa dai haskakawa   Allah ya sakawa jagororin wannan gari mai albarka- garin tauhidi da sunnu- mafi alherin sakayya ya sakawa kadimul haramaini da alheri bisa ga wannan kokari madaidaici wurin hidimawa  harami biyu masu daraja  da masu fiskantosu, da kuma abinda ya gabatar kuma yake gabatarwa ga musulunci da musulmai Allah ya sanya shi a mizanin ayyukan shi na kwarai.
Wannan kenan ku yi salati da aminci-Allah ya muku rahama- bisa ga mai shiryarwa mai albishir kuma fitila mai haskakawa  kamar yanda mai tausayi gwani ya umarce ku da   sai ya ce : ( Lallai Allah da Mala'ikunsa suna salati ga Annabi ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi da aminci tabbatacce )
Ya ku masu fatan ceto mafi alheri *** daga Ahmadu ku yi salati a gare shi da aminci
Ma'aboci daukaka yayi salati a gare shi da aminci muddin mai talbiya na talbiya ko   mai ihrami na tahalluli .
 ya Allah ka yi dadin tsira da aminci ga wannan rahama da ka bamu shi, da kuma ni' ima da ka bamu kyautansa  : Annabinmu Muhammad dan Abdullahi , ya Allah ka yarda da kalifofinsa masu shiryarwa Abubakar da Umar da Usman da Ali da sauran sahabbai da tabi'ai da wanda ya bi su da kyautatawa har zuwa ranar sakayya     kuma ka game rahamarka da mu tare da su  ya mafi tausayin masu tausayi.
 Ya Allah ka daukaka musulunci da Musulmai, ya Allah ka daukaka musulunci da musulmai ,  ka bada aminci ga masu umura da ziyara ka sanya wannan gari cikin aminci da kwanciyar  hankali cikin kyauta da yalwa  da sauran garuruwan musulmai  ya Allah  ka bamu aminci  a garuruwan mu kuma ka gyara kuma ka datar kuma ka kiyaye jagororinmu da shuwagabanninmu, ka karfafi shugaban mu  da gaskiya kuma jagoran al'amuran mu , ya Allah ka datar da shi da mataimakan shi biyu da 'yanuwansa zuwa ga abinda akwai daukaka na musulunci da gyaruwa  na musulmai .
Allah ka datar da dukkan jagororin musulmai don su yi hukunci da shari'anka da bin littafinka da sunnan Annabin ka  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi Ya Allah ka sanya su rahama bisa ga bayin ka muminai.
 Ya Allah ka gyara halayen musulmai a ko ina ,  Ya Allah ka gyara halayen musulmai a ko ina , Allah ka kare jinannakin su, Allah ka kare jinannakin su ya Ubangijin talikai ya Allah ka bamu kyakkyawa anan duniya da kuma kyakkyawa a lahira ka kre mu daga azabar wuta .
( Ya Ubangiji ka karba daga gare mu domin kai mai ji ne masani  kuma ka karbi tubanmu  don kai mai  karban tuba ne kuma mai jiin kai . karshen adu ar mu shi ne dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah ubangijin talikai  tsira da amincin Allah su tabbata ga  shugabanmu Muhammadu da iyalansa da sahabbansa baki daya.       





   
     

    
بسم الله الرحمن الرحيم
Godiya ta tabbata ga Allah; Ubangijin qasa da sama, Mai amsa addu'a, Wanda yake faran bayi da ni'imomi, Kuma yake yaye mummuna da bala'i, Ina yabon Ubangijina kuma ina godiya a gare shi, Ina tuba zuwa gare shi, ina neman gafararSa, Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai yake bashi da abokan tarayya,  Ma'abucin buwaya da girma.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawansa ne manzonsa ne wanda aka turo shi da shrai'a cikakkiya, mai haske.
Ya Allah ka yi daxin salati da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka Muhammadu,    da iyalansa da sahabbansa masu rigaye zuwa ga aiyukan biyayya ababen godiya.
Bayan haka:
Ku kiyaye dokokin Allah da taqawa, iyakar kiyayewa, saboda duk wanda yayi riqo da taqawa to sai Allah ya haxa masa alkhairi a duniyarsa da lahirarsa. Wanda kuma ya nisanci taqawa to sai ya tave a qarshen lamuransa, ko da kuwa duniyarsa ta fiskance shi.

Ya ku Musulmai!!
Lallai Allah ya qaddara sabbuban alkhairori, da samun rabo a duniya da lahira, Kuma ya qaddara sabbuban sharrukan duniya da lahira, saboda haka; Duk wanda ya yi riqo da sabbuban alkhairi da rabauta to sai Allah ya lamunce masa samun gyaruwan rayuwarsa ta duniya, A lahira kuma zai kasance yana da kyakkyawan makoma, yana mai dawwama cikin aljannonin ni'imah, tare da rabauta da samun yardar Ubangiji Mai rahama. Allah (تعالى) yana cewa:
"Ba komai ba ne sakamakon kyautatawa face kyautatawa" [Suratur Rahman: 60].
            Wanda kuma yayi aiki da sabbuban sharri, to sai ya girbe sakamakon aikinsa, a rayuwarsa ta duniya, da kuma bayan mutuwa. Allah yana cewa:
 "Wanda ya aikata mummunan aiki za a saka masa da shi, Kuma ba zai sami wani masoyi ba, baicin Allah, kuma ba zai sami mataimaki ba" [Suratun Nisa'i: 123].

            Ku saurara!
            [Yin addu'a] Lallai yana daga cikin sabbuban gyaruwa da kawo gyara, da rabauta, da yawaitar samuwan alkhairori, da tunkuxe fitintinun da suke sauka, da uqubobi, da xauke musibun da ake cikinsu, da baqin ciki: YIN ADDU'Ada ikhlasi, da zuciya da take halarce, tare da yin naci, Saboda Ubangiji Mabuwayi da xaukaka yana son a riqa yin addu'a, kuma yayi umurni da shi. Shi kuma addu'a yana yin amfani akan abinda ya sauka, da wanda bai sauka ba (na musibobi), Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma Ubangijinku ya ce: Ku roqe ni zan amsa muku, Lallai waxannan da suke kangarewa daga bauta mini, za su shiga jahannama qasqantattu" [Ghafir: 60].
            Kuma addu'a shine Bauta, kamar yadda ya zo a cikin hadisin Annu'uman xan Bashir (رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), Ya ce:
"Addu'a shine bauta (ibada)", Abu-dawud ya ruwaito shi da Attirmiziy, kuma yace: Hadisi ne mai kyau ingantacce.
Kuma an ruwaito daga Abu-hurairah (رضي الله عنه), yace: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Babu wani abu wanda yafi matsayi a wurin Allah fiye da addu'a", Attirmiziy ya ruwaito shi, da Ibnu-Hibbana a cikin sahihinsa, da Alhakim, kuma yace: Isnadinsa ingantacce ne.
            Kuma Addu'a abun kwaxaitarwa ne akansa a kowani lokaci, kuma ibada ne wanda Allah ya ke bada sakayya akansa da mafi girman sakamako, Kuma addu'a yana tabbatar da ababen nema gabaxayansu; kevantattu, da waxanda suka game, na addini, da na duniya, a cikin wannan rayuwar da bayan mutuwa.
Kuma saboda amfanin da addu'a yake da su masu girma Allah ta'alah ya shar'anta yinsa a cikin ibadodin da aka farlanta, a matsayin wajibi ko mustahabbi, saboda rahamar Ubangijinmu da karramawa da yin baiwa, domin bayi muyi aiki da wannan sababin; da Allah ya sanar da mu Shi. Kuma lallai da Allah bai sanar da mu yin addu'a ba, to da kwakwalenmu basu shiryu izuwa gare shi ba, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma aka ilmantar da ku, abinda Ku da ubanninku baku sani ba" [Suratul An'am: 91].
Don haka; Yabo da godiya na Allah ne, yabo mai yawa, mai daxi, mai albarka, kamar yadda Ubangijinmu yake so, kuma kamar yadda Ubangiji ya yarda.

            Kuma buqatar yin addu'a a ko-da-yaushe ta kan yi tsanani, Musamman a wannan zamanin, Wanda fitintinu suka bayyana, kuma suka yawaita, tare da saukar bala'oi da annoba masu halakarwa, da kuma saukar ababen baqanta rai, ga Musulmai, da bayyanar qungiyoyin bidi'a; waxannan da suke rarrabe kan Musulmai, kuma suke halatta zubar da katangaggen jini da kwasar dukiya ta haramaun, suke kuma kyamar ilimi da ma'abutansa, kuma suke yin fatawa da jahilci, da kuma vata. A lokacin da maqiyan Musulunci suke taruwa don murqushe shi, suke kuma shisshirya makirce-makirce akan masu Imani, su kuma Musulman suke tavar da junansu, suke rarrabewa, suke savani, a tsakaninsu. A kuma lokacin da dangogin cutuwa suka riski kowanne daga cikin xaixaikun Musulman da aka fitar da su, daga gidajensu, da zalunci, kuma cutuka suka shafe su, buqatunsu suka zama da wahala, Lallai a irin waxannan halaye masu tsanani; waxanda Musulmai suke quna da wutansu a garurrukan da fitintinu suka kunnuBuqatuwar yin addu'a tana yawaita.

            Kuma lallai haqiqa Allah yayi yabo akan waxanda suke roqonSa, suke kuma qanqan-da kai izuwa gare shi Mabuwayi da xaukaka; IDAN har manyan lamura  ko tsanani suka sauka akansu, Allah (تعالى) yana cewa dangane da iyayenMu guda biyu (Adamu da Hauwa'u عليهما السلام):
 "Su biyun, suka ce: Ya Ubangijinmu! lallai ne Mu mun zalunci kayukanmu, idan har baka gafarta mana kayi rahama a gare mu ba, zamu kasance daga cikin masu hasara" [Suratul A'araf: 23]. Kuma Allah (تعالى) yace:
"Kuma tabbas zamu jarrabe ku da wani abu na tsoro da yunwa da tawaya cikin dukiya da rayuka da 'ya'yan itatuwa, Kuma ka yi bishara ga masu haquri * Waxannan da idan musiba ta same su, sai su ce: Lallai Mu daga Allah muke, kuma lallai Mu zuwa gare shi masu komawa ne * Waxannan akansu akwai albarku daga Ubangijinsu, da wata rahama, Kuma waxannan sune shiryayyu" [Suratul Baqarah: 155].kuma Allah mabuwayi da xaukaka ya faxa dangane da annabi Yunus s(عليه السلام):
"Kuma annabi Yunus sa'ad da ya tafi yana mai fushi, sai yayi zaton cewa ba za mu quntata masa ba, sai yayi kira a cikin duffai, cewa: babu abin bautawa face kai, tsarki ya tabbata a gare ka, lallai Ni kasance daga azzalumai" [Suratul Anbiya'i: 87].
Hadisi ya zo daga Sa'ad xan Abiy-Waqqas (رضي الله عنه) yace, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Addu'ar annabi Yunus wanda kifi ya haxiye, a lokacin da ya roqi Allah alhalin yana cikin kifi, babu wani Mutum Musulmai da zai yi roqo da shi, face Allah ya amsa masa addu'ah", Ahmad ya ruwaito shi, da Attirmiziy, da Alhakim, kuma yace: Isnadinsa ingantacce ne.
            Kuma a yayin da Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya kirayi qabilar Saqifu zuwa ga Musulunci, sai suka qi karvar da'awarsa, sannan suka jefe shi da duwatsu, sai ya roqi Ubangijinsa yana mai cewa:
"Ya Allah ina koka raunin qarfina zuwa gare ka, da qarancin dabarata, da qasqancin da nake da shi a wurin Mutane, Ya mafi rahamar masu rahama; izuwa ga Wa; zaka jivintar da Ni; zuwa ga maqiyin da yake xaure min fiska, ko kuma izuwa ga wani maqiyin da ka mallaka masa lamarina, Idan baka yi fushi da ni, ba; to bani da damuwa, Saidai kuma  lafiyarka ita tafi yalwa a gare ni. Ina neman tsari da hasken fiskarka wanda ya haskaka duffai, kuma lamarin duniya da lahira suka gyaru da shi, kada fushinka ya sauka akaina, Komawa naka ne, har sai ka yarda, Babu dabara babu qarfi face daga wurinka".

            Da yin addu'oi ne, ake fiskantar tsanani da ababen vacin rai, na abubuwan da Mutum ba zai iya tunkuxe maka su ba; saboda Yazo daga Sauban (رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Babu abinda ke tunkuxe qaddara sai addu'a, kuma babu abinda yake qara tsawon rai sai xa'a ga iyaye da sada zumunci, Kuma lallai mutum ana haramta masa arziqi saboda wani zunubin da ya aikata", Ibnu-Hibbana ya rawaito shi a cikin sahihinsa, da Alhakim, kuma yace: Isnadinsa ingantacce ne.
An ruwaito daga Abdullahi xan Umar (رضي الله عنهما), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), yace:
"Lallai addu'a yana amfani daga abinda ya sauka, da kuma wanda bai sauka ba, Ya ku bayin Allah; Sai ku lazimci yin addu'a", Attirmiziy ya ruwaito shi, da Alhakim.
An ruwaito daga Abu-Hurairata (رضي الله عنه) yace: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: Lallai Allah (تعالى) yana cewa:
"Ni, Ina yadda bawana ke zatona, kuma Ni ina tare da shi idan ya roqe ne", Bukhariy ya ruwaito shi, da Muslim.
Kuma lallai wannan lada da falala ya kai yadda ya kai (A ce, Allah yana tare da bawansa; idan ya roqe shi!).

            Kamar yadda Allah yayi zargi ga waxanda  suke barin roqon Allah ko addu'a a lokacin da uqubobi suka sauka, ko bayyanar fitintinu; Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma haqiqa mun kama su, da azaba, saidai basu qanqan da kai ga Ubangijinsu ba, kuma ba sa yin tawali'u" [Suratul Muminuna: 76]. Kuma Allah mabuwayi da xaukaka yace:
"Kuma lallai mun aika zuwa ga al'ummai daga gabaninka, sai muka kama su da tsanani da cuta, tsammaninsu za su qanqan da kai * To, don me lokacin da tsananinmu ya je musu basu yi tawali'u ba, Sai zukatansu suka qaiqashe, kuma Shexan ya qawata musu abinda suka kasance suke aikatawa" [Suratul An'am: 42-43]. Kuma Allah (تعالى) yace:
"Kuma ba mu aika wani annabi a cikin wata alqarya (sai suka qaryata shi) ba, face mun kama mutanenta da azaba, da cuta, tsammaninsu za su qasqantar da kai" [Suratul A'araf: 94].
            Kuma lallai qin yin addu'a, a lokacin tsanani dogewa ne, akan zunubai, da kuma raina lamarin kamu ko damqar Ubangiji mai tsanani, Allah (سبحانه) yana cewa:
"Lallai damqar Ubangijinka mai tsanani ce" [Suratul Buruj: 12].
            Kuma lallai shi addu'a sababi ne mai girma na sauqar alkhairori da albarkoki, da tunkuxe sharri, ko xauke shi, daga mai yin addu'ar.
            Kuma yin addu'a shine sababin da ya fi qarfi domin fita daga sharrin da ya auku, da mummunan yanayin da ake ciki, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma da Ayyuba a lokacin da ya kirayi Ubangijinsa lallai ne Ni, cuta ta shafe ni, kuma kai ne mafi rahamar masu tausayi * Sai muka amsa masa, sa'annan muka kwaranye abinda ke a tare da shi na cuta, Kuma muka kawo masa iyalansa da kwatankwacinsu tare da su, saboda rahama daga gare mu, da tunatarwa ga masu ibada" [Suratul Anbiya'i: 83-84]. Kuma Allah (تعالى) yace:
"Ko, Wane ne ya ke amsawa mai buqata, idan ya roqe shi, kuma ya kwaranye mummuna" [Suratun Naqml: 62]. Ai, Babu wani da yake aikata hakan, sai Allah (تعالى).
Kuma Allah (سبحانه) yace:
"Ka ce Wane ne yake tsirar da ku daga duffan tudu da ruwa, kuna roqonsa bisa ga qanqan da kai, kuma a voye; Lallai ne idan ka tsiratar da mu daga wannan (masifa), zamu kasance masu godiya * Ka ce: Allah ne, yake tseratar da ku daga gare ta, da kuma dukan baqin ciki, Sa'annan sai ku kuma ku ci-gaba da yin shirka" [Suratul An'am: 62-63].
            Shi Musulmi wajibi ne akansa ya riqa addu'a da kwaxayin Allah (تعالى) ya gyara masa sha'anoninsa, gabaxaya, yana mai xaga buqatunsa zuwa ga UbangijinSa gabaxayansu, ya riqa roqonSa kowani abu. Kuma mafi girman abin nema shine aljannah, da kuvuta daga aukawa wuta, Allah (تعالى) yana faxa a cikin hadisin Qudusiy:
"Ya ku bayina! dukkaniku vatattu ne, sai wanda na shiryar da shi; ku nemi shiryarwata; in shiryar da ku. Ya ku bayina! dukkaninku mayunwata ne sai wanda na ciyar da shi; sai ku nemi ciyarwata; in ciyar da ku. Ya ku bayina! kowanenku tsirara ya ke; babu tufafi sai wanda na tufatar da shi; sai ku nemi tufatarwata, in tufatar da ku. Ya ku bayina ! lallai kuna yin laifi dare da rana, ni kuma ina gafarta zunubai gabaxaya; sai ku nemi gafarata; in yi muku gafara", Muslim ya ruwaito shi daga hadisin Abu-zarri (رضي الله عنه). Ma'anar hadisin kuma shine: Ku roqe ni shiriya, da ciyarwa, da tufatarwa da gafara.
Kuma y azo a cikin hadisi cewa:
"Xayanku ya riqa roqon UbangijinSa koda akan igiyar takalminsa ne (da ya tsinke), da gishirin abincinsa".

          Kuma dayawa, addu'a ta kan canza abinda yake gudana a tarihi daga sharri zuwa ga alheri, ko kuma daga abu mai kyau zuwa wanda yafi shi kyau, Allah (تعالى) yana cewa dangane da Babanmu annabi Ibrahim (عليه الصلاة والسلام):
"Ya Ubangijinmu! Ka aiko a cikinsu, wani manzo, daga gare su, yana karanta musu ayoyinka, kuma yana karantar da su wannan littafin da hikima, kuma yana tsarkake su, lallai ne kai, kai ne Mabuwayi Mai hikima" [Suratul Baqara: 129]. Kuma an ruwaito daga Abu-Umamah (رضي الله عنه), yace: Na ce: Ya ma'aikin Allah! Menene farkon lamarinka? Sai yace: Ni addu'ar babana ne annabi Ibrahim, kuma busharar annabi Isah, Sai mamata ta gani a mafarki cewa wani haske ya fita daga gare ta, wanda har ya haskaka benayen qasar Sham", Ahmad ya ruwaito shi. 
Kuma saboda wannan addu'ar ta annabi Ibrahima; Musulmai suka kasance cikin alheri madawwami, kai, dukkan dumiya itama wannan addu'ar ta shafe su.
            Haka, addu'ar da annabi Nuhu (عليه الصلاة والسلام) itama ta kasance alheri ga muminai masu tauhidi, sharri ga mushirkai.
            Haka addu'ar da annabi Isah (صلى الله عليه وسلم) zai yi; shi da sahabbansa waxanda za a killace su a jikin dutsen AXXUR, a qarshen zamani itama zata kasance nasara ce ga muminai, sa'annan halaka ga YAJUJU da MAJUJU, waxanda suke kamar farar da za ta game dukkan qasa (duniya), Mafi sharrin halitta, masu tsananin varna da qetare iyaka da qirman kai,  saboda Ya zo cikin hadisin Annawas xan Sam'an (رضي الله عنه) bayan annabi Isa ya kashe MASIHU AD-DAJJAL:
"Sai Allah (تعالى) yayi wahayi ga annabi Isah (صلى الله عليه وسلم) cewa: Lallai ni na fitar da wassu bayi, waxanda wani bashi da ikon yaqarsu, Sai ka killace bayina a wajen dutsen Ax-xur. Sai Allah ya tayar da Ya'ajuju da ma'ajuju alhalin suna gaggawa daga kowani tudun qasa; Sai na farkonsu su shige ta jikin wani qaramin teku na xabariya, sai su shanye dukkan ruwan da ke cikinsa, Sai na qarshensu su zo shigewa sai su ce: Lallai wannan, da akwai ruwa a cikinsa, To, sai a killace annabin Allah Isah (صلى الله عليه وسلم)shi da sahabbansa; har sai ya kasance kan Saniya yafi alheri ga xayansu, fiye da dinari xari ga xayanku a yau, to daga nan, sai annabin Allah; Isah ya bayyanar da kwaxayinsa shida sahabbansa (رضي الله عنهم) wa Ubangijinsu maxaukaki; ta hanyar roqonsa, Sai Allah (تعالى) ya saukar da tsutsotsi a wuyan Ya'ajuju da Ma'ajuju, sai su wayi gari sun mutu, kamar mutuwar rai guda xaya. Sa'annan sai annabin Allah; Isah da sahabbansa su sauka kan qasa, saidai kuma ba za su sami daidai da taqi xaya ba, a doron qasa face gawar Ja'ajuju da ma'ajuju da warinsu ya cike shi; Sai annabin Allah; Isah ya bayyanar da kwaxayinsa shida sahabbansa (رضي الله عنهم) wa Ubangijinsu maxaukaki; ta hanyar roqonsa, Sai Allah (تعالى) ya turo da wassu tsuntsaye, waxanda suke kama da wuyan raqumi, sai su tattare su; su kai su, su jefa, a wurin da Allah (تعالى) ya nufa", Muslim ya ruwaito shi.

            Kuma addu'ar da annabi (صلى الله عليه وسلم) shugaban halitta,  yayi; shi da sahabbansa, a yaqin badar, itama ta kasance wata nasara ce ga Musulunci, har abada, kuma tavewa ce, ga kafirci har abada; Allah (تعالى) yana cewa:
"A lokacin da kuke neman agajin Ubangijiku sai ya amsa muku; da cewa: lallai ne Ni zan taimaka muku da dubu daga cikin Mala'iku, a jere" [Suratul Anfal: 9]. Sai Annabi (صلى الله عليه وسلم) yayi ta yin addu'a, kuma ya nace, wajen yin addu'ar, har sai da mayafinsa ya faxi, A nan ne, Abubakar (رضي الله عنه) ya rungume shi, sa'annan ya ce:  Yadda kake yin magiya wa Ubangijinka, ya isa, ya ma'aikin Allah! Kuma lallai Allah zai cika maka abinda ya yi maka alkawari.

            Kuma lallai yin addu'ar taimakon gaskiya, da ruguje varna, yana daga nasiha ga Allah da littafinSa, da ManzonSa, da jagororin Musulmai, da kuma sauran Mutanensu.
            Kuma babu wanda zai guje wa yin addu'a, yana mai qaurace masa face wanda ya tozarta rabonsa a duniya da lahira, sa'annan ya tozarta abinda ya wajaba akansa na haqqin Musulunci da Musulmai. Ya zo a cikin hadisi cewa:
"Duk wanda bai himmatu da lamarin Musulmai ba to baya cikinsu".
            Kuma da a ce, za mu yi ta bibiyar fa'idodin addu'a da albarkokinsa, da alherorinsa, da natijojinsa, daxaxa, kuma ababen mamaki, to da, ambaton hakan yayi tsayi. Saidai abinda muka riga muka yi ishara, a baya, ya isar.
           
            Kuma lallai addu'a yana da SHARRUXA, DA LADDUBA;
Kuma yana daga cikin sharruxan addu'aCin abinci na halal, da sanya tufar halal, Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace wasahabinsa Sa'ad xan Abiy-Waqqas (رضي الله عنه):
"Ka kyautata abincinka; sai a amsa maka addu'arka".
Kuma yana daga cikin sharruxansa: Riqo da Sunnah, da kuma amsawa Allah (تعالى) ; ta hanyar aikata abubuwan da ya yi umurni, da nisantar abubuwan da yayi hani, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma idan bayina suka tambaye ka dangane da ni, ka ce: Lallai ni, a kusa nake, ina amsa addu'ar mai addu'a idan ya roqe ni, Sai su nemi amsawata, kuma su yi Imani da ni, tsammaninsu za su shiryu" [Suratul Baqara:186]. Kuma Allah (تعالى) yace:
"Kuma yana amsawa wadannan da suka yi imani,  suka kuma aikata aiyukan kwarai, kuma yana qara musu sakamako daga falalarsa" [Suratush Shurah: 26]. Mutumin da aka zalunce shi, shi kuma ana amsa masa, idan yayi addu'a; koda kuwa kafiri ne, ko xan bidi'a.
            Kuma yana daga cikin sharruxansa: Yin ikhlasi da halarto da zuciya, da yin naci, wa Allah, da yin gaskiya cikin neman mafaka, daga Ubangiji (تعالى), Allah ta'alah yana cewa:
"Sai ku roqi Allah kuna masu tsarkake addini a gare shi, ko da kuwa kafirai sun qi" [Suratul gafir: 15].
Ya zo cikin hadisi cewa, "Allah baya karvar addu'a daga zuciya rafkananniya mai wargi".
            Kuma yana daga cikin sharruxansa: Kada ya yi, addu'a da savo, ko yanke zumunta, kuma kada ya qetare iyaka, cikin addu'a.
            Kuma yana daga cikin sabbuban amsa addu'a: Yin yabo wa Allah (تعالىda sunayensa mafiya kyau, da sifofinsa maxaukaka, tare da yin salati wa annabi (صلى الله عليه وسلم); Ya zo cikin wani hadisi cewa; Lallai annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ji wani Mutum yana cewa:
"Ya Allah, lallai ne Ni ina roqonka , da shaidawata cewa babu abin bautawa da gaskiya sai kai, Makaxaici, Wanda ake nufi da biyan buqata, wanda bai haifu ba, kuma ba a haife shi ba, kuma bashi da wani wanda yake daidai da shi, Sai yace: Lallai ne, ka roqi Allah da sunanSa da yafi girma; wanda idan aka roqe shi da shi ya kan bayar, idan kuma aka yi addu'a da shi, ya kan amsa", Abu-dawud ya ruwaito shi, da Attirmiziy, kuma yace: Hadisi ne mai kyau (hasan).
Da kuma Ibnu-Majah da Ibnu-Hibbana, da Alhakim, daga hadisin Buraidah (رضي الله عنه).
An kuma ruwaito daga Fadalah (رضي الله عنه), yace: Wata-rana Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana zaune, sai wani Mutum ya shigo yayi sallah, Sa'annan ya ce:
"Ya Allah, ka gafarta mini, ka yi mini rahama, Sai Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace: Ka yi gaggawa ya kai mai sallah, Idan ka zo sallah; sai ka zauna, to ka yi godiya wa Allah da abinda ya cancance shi, San'annan sai ka yi min salati, Sa'annan sai ka roqi Allah", Ahmad ya ruwaito shi, da Abu-dawud, da Attirmiziy, kuma yace: Hadisi ne hasan.
A cikin wani hadisin kuma:
"Lallai addu'a yana rataye tsakanin sama da qasa har sai ya yi salati wa Annabi (صلى الله عليه وسلم)".
            Kuma yana daga cikin ladduban addu'a da sharruxan karvarsa: Kada ya yi gaggawar amsawa, A'a yayi haquri, Ya zo a cikin hadisi cewa:
"Za a amsa wa xayanku matuqar bai yi gaggawa ba; yace: Na roqa, na roqa, amma ba a amsa mini ba", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi, daga hadisin Abu-hurairah (رضي الله عنه).
            Kuma lallai, dawwama kan addu'a (da yawaita yinsa), a tare da shi akwai amsawa, Ya zo cikin hadisi cewa:
"Babu wani Musulmi a bayan qasa, wanda zai roqi Allah da wata addu'ar face, Allah ya bashi ita, ko kuma ya tunkuxe masa wani mummunan kwatankwacinta, matuqar bai roqi sabo, ko yanke zumunta ba. Sai wani Mutum yace: To, lallai za mu yawaita! Sai yace: Allah zai fi ku yawaitawa", Attirmiziy ya ruwaito shi, kuma yace: Hadisi ne, hasan sahih, kuma Alhakim ya ruwaito shi daga riwayar Abiy-Sa'id, sa'annan ya yi qari a cikinsa: Ko kuma, a ijiye masa kwatankwacin addu'arsa.

            Kuma ya dace, Musulmi ya yi kirdadon lokutan amsa addu'a, An ce wa Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم):
Wace addu'a ce, aka fi amsawa? Sai yace: "Ta qarshe dare, da bayan sallolin farilla", Attirmiziy ya ruwaito shi, yace: Hadisi ne, hasan, daga hadisin Abiy-Umamah. Kuma ya zo cikin wani hadisin cewa:
"Ubangijinmu yana sauka zuwa ga saman duniya, a cikin xaya bisu ukun dare na qarshe; Sai ya ce: Wa zai yi roqo sai na amsa masa, Wa zai tambaye ni sai na bashi, Wa zai nemi gafarata sai na gafarta masa", Bukhariy ya ruwaito shi, da Muslim daga hadisin Abu-hurairah.
            Da kuma tsakanin kiran sallah da yin iqamah, Nan ma ba a mayar da addu'a: Ya zo cikin hadisi cewa:
"Lokacin da bawa yafi kasancewa kusa da UbangijinSa shine a lokacin sujjada; Sai ku yawaita addu'a", Muslim ya ruwaito shi daga hadisin Abu-hurairah.
            Da kuma lokacin ganin ka'abah, da lokacin saukan ruwa, da hali na buqatuwa, da bayan khatamar alqur'ani gabadaya, da bayan yin sadaka.

            Ka yi mamakin girman rabauta, da nasara, da samun ladan Mutumin da ya killace zuciyarsa, ga Allah (تعالى); yana roqonSa, yana fatanSa, yana kuma dogara akanSa, yana neman taimakonSa.
            Da kuma tavewa, da girman shirka ko kafircin wanda yake roqon kabari, ko yake neman agaji daga Annabawa (عليهم الصلاة والسلام), da waliyyai, ko yake roqonsu koma bayan Allah (تعالى), ko yake xaga buqatunsa zuwa ga wani mala'ika makusanci, ko wani annabi mursali; saboda Annabawan Allah (عليهم الصلاة والسلام) sun zo ne, don kiran Mutane, cewa su keve Allah (تعالى) da yin roqo a gare shi, sa'annan su kaxaita shi da bauta shi kaxai. Su kuma waliyyai an umurce mu da mu riqa yin aiki irin nasu, sa'annan mu so, su, kuma aka hane mu, kan roqonsu, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma lallai masallatai na Allah ne, kada ku roqi wani tare da Allah"[suratul Jinn: 18]. Kuma Allah (تعالى) ya ce:
"Kuma ka ce: Kawai ni, ina roqon Ubangijina ne, kuma ba zan tara kowa da shi ba" [Jinn: 20].       
Kuma wanda baya halarce, da matattu babu wani daga cikinsu da yake amsa addu'a; saboda addu'a babu mai amsa shi idan ba Allah Mabuwayi da daukaka ba, Allah (سبحانه) yana cewa:
"Kiran gaskiya nasa ne, Wadanda kuma suke roqon waninshi basa amsa musu da komai, face kamar mai shumfuda tafukansa zuwa ga ruwa domin ya kai ga bakinsa, kuma shi ba mai kaiwa gare shi ba ne, Kuma kiran kafirai (ga wanin Allah) bai zama ba, face a cikin bata" [Suratur Ra'ad: 14]. Kuma Allah (تعالى) yace:
"Babu wanda ya fi bata fiye da wanda ke roqon wanin Allah, wanda ba zai amsa masa ba, har ranar qiyama, alhalin (wadanda ake roqan) sun gafala da kiran masu kiran * Kuma idan aka tattara mutane, za su kasance abokan gaba a gare su, kuma za su kasance masu kafircewa ga bautan da suka yi a gare su" [Ahqaf: 5-6].
Kuma Allah (تعالى) yace, alhalin yana bada labarin aiyukanSa:
"Yana shigar da dare a cikin yini, kuma yana shigar da yini cikin dare, kuma ya hore wata da rana; kowannensu yana gudana zuwa ga ajali ambatacce. Wannan shine Allah Ubangijinku, mulki nasa ne, kuma waxanda kuke roqa waninSa basa mallakar ko da fatar kwallon dabino * Idan kuka roqe su, to ba za su ji kiranku ba, koda sun ji to ba za su amsa muku ba, kuma a ranar qiyama za su kafirce wa shirkarku, kuma babu mai baka labari, kamar wanda ya sani", [Fadir: 13-14].
            Kuma lallai Allah bai yi izinin a roqi waninSa ba, duk irin kusancin da yake da shi, Allah (تعالى) yana cewa:
"Almasihu ya ce: Ya ku 'ya'yan Isra'ila, Ku bauta wa Allah; Ubangijina, kuma Ubangijinku; lallai ne duk wanda ya yi shirka da Allah to, lallai Allah ya haramta masa aljanna, kuma makomarsa itace wuta, kuma babu wassu mataimaka ga azzalumai" [Ma'idah: 72]. Kuma me tsarki da daukaka (Allah) ya ce ''kuma baya umurninku da ku riki mala'iku da annabawa iyayengiji . shin ze umarceku da kafirci ne bayan kun riga kun zama masu sallamawa (musulmi)
Ya zo cikin hadisi cewa: "Wanda ya mutu alhalin yana roqon wani koma bayan Allah ya shiga wuta", Bukhariy ya ruwaito shi daga hadisin Abdullahi dan Mas'ud (رضي الله عنه).

            Ya kai Musulmi!!
            Wannan shine littafin Allah, da hadisan ManzonSa (صلى الله عليه وسلم) suna bayyana maka cewa, lallai ADDU'A shine BAUTA, kuma lallai Allah mabuwayi da xaukaka shine kawai ya kevanta da addu'a, ba a yinsa sai ga Allah maxaukaki, kuma duk wanda ya haxa wani da Allah a cikin addu'a to wannan mushirki ne mai babbar shirka.
Kuma kada wani ya yi koyi da wani cikin vata da shirka; saboda shirka da kafirci basu auku a cikin 'ya'yan Adam ba face, da sababin taqalidanci, da bin mutane vatattu, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma shin wancan, shine mafi zama alheri ga liyafa, ko kuma itaciyar zaqummi * Lallai Mu mun sanya ta fitina ga azzalumai * Lallai ita wata bishiya ce, wadda take fita daga asalin wutar jahima * Fudarta, kai kace kayukan shexanu ne * Lallai su haqiqa masu ci ne daga gare ta, sa'annan masu cika cikinsu ne daga gare ta * Sa'annan suna da wani gauraye a kanta, daga ruwan zafi * Sa'annan lallai makomarsu izuwa ga wutar jahimu take * Lallai su, sun iske Ubanninsu suna datattu *  Sai suka kasance akan gurabansu suke ta yin gaggawa" [As-safat: 62-70].
Kuma Allah (ta'alah) yana cewa:
"Kuma ku roqi Ubangijinku da qanqan da kai, da kuma a boye, Lallai ne shi, baya son masu qetare iyaka kuma kada kuyi barna a cikin kasa bayan gyaranta kuma ku kirayeshi saboda tsoro da tsammani : lallai ne rahamar Allah makusanciya ce daga masu kyautatawa" [A'araf: 55].

            ALLAH YAYI MINI ALBARKA, NI DA KU A CIKIN ALQUR'ANI MAI GIRMA.

HUXUBA TA BIYU
            Yabo da godiya sun tabbata ga Allah Mai rahama, Mai jin qai, Mabuwayi Mai hikima, Ma'abucin sunaye da suka fi kyau, da sifofi maxaukaka.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya, Maxaukakin da Yafi xaukaka.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawansa ne manzonsa ne Zavavve.
Ya Allah ka yi daxin salati da sallama da albarka, ga bawanka kuma manzonka Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa Masu taqawa.
Bayan haka:

Ku kiyaye dokokin Allah, sai ya gyara muku aikyukanku, sa'annan ya sanya ku daga cikin masu rabauta a yanzu, da kuma bayan komawa izuwa ga makoma.

Ya ku Bayin Allah!
            Ku kasance, masu bayyanar da kwaxayi zuwa ga Allah, masu dawwamar da yin roqo a gare shi (da yawaitawa); saboda Duk wanda ya roqi Allah baya tavewa, wanda kuma ya yi fatan samun Allah ba a hana shi.
Umar Allah kara yarda a gare shi yace : Lalle ni ba na dorawa kai na damuwar amsa adua sai dai na kan damu da yin aduar, in har an min dacen yin adua to Allah ya lamunce amsa aduar.
Kuma kowani Mutum yana da buqatun da suke sabuntuwa, da ababen nema a kowani lokaci masu yawa; Don haka; Sai kowa ya roqi UbangijinSa, duk abinda ya san alheri ne. kuma ya yi wa Musulmai da aka zalunta a addini adu'a, ya kuma nemi tsarin Allah daga  duk abinda ya san sharri ne.
Kuma mafi girman abin roqo shine neman samun yardar Allah, da kuma aljannah.
Shi kuma mafi girman abinda ake neman tsari daga gare shi, shine wuta da sabubanta.
Kuma Mutum Musulmi ya yi naciyar roqon abinda ya dame shi, daga wajen Ubangijinsa; saboda Allah Mawadaci ne, Mai karimci, Abun godiya, Mai yawan baiwa, Mai girma, Mai iko, Allah maxaukaki yana cewa:
"Ya ku bayina! Da, na-farkonku da na-qarshenku, da mutanenku da aljanunku zasu tsaya a bigire xaya, sai kowanne ya roqe ni, sai in bada kowanne xaya abinda ya roqa; to ba zai rage komai daga cikin abinda ke wurina ba sai kamar gwargwadon abinda allura ta rage; idan aka tsoma ta a cikin ruwan teku", Muslim ya ruwaito shi/ ya zo a hadisi :Wanda bai roki Allah ba zai yi fushi da shi,

            Kuma mustahabbi ne, Musulmi ya riqi addu'oi masu gamewa, waxanda suka zo daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), kamar faxinsa maxaukakin sarki:
"Ya Ubangijinmu ka bamu mai kyau a Duniya, a lahira ma mai kyau, ka kare mu daga azabar wuta" [Baqara: 201].
Da kuma misalin
"Ya Allah, lallai ne Ni ina roqonka aljanna da abinda ya kusantar zuwa gare ta na zance ko aiki, Kuma ina neman tsarinka daga wuta da kuma abinda ya kusantar zuwa gare ta na zance, ko aiki".

            Ya ku bayin Allah!
             "Lallai Allah da Mala'ikunSa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi imani ku yi salati a gare shi domin amintarwa" [Ahzab: 56].

Addu'a ….
……………….
……………….

……………….