الجمعة، 7 أغسطس 2020

YI WA KAI HISABI

 

 

اسم المترجم : أمين سعد عبد الله

اللغة : الهوسا

التاريخ : 17-12-1441هـ

Hudubar Juma'a a masallacin Annabi na Shaikh Abdul Muhsin  Al kasim 17-12-1441AH /  7-8-2020AD

 

Hudubar farko:

  Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Madaukakin sarki  muna gode mishi kuma muna neman taimakonsa, muna neman gafararSa, kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu, da munanan ayyukanmu, duk wanda Allah ya shiryar da shi babu mai batar da shi , duk wanda ya batar kuma babu mai shiryar da shi, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya, kuma na shaida Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa  da sahabbansa da aminci tabbatacce mai yawa.

Bayan haka: ku ji tsoron Allah-

Ya ku bayin Allah,- cancancin tsoronSa, takawa ita ce mafi alherin abin ribata kuma kyauta mafi yawa.

Ya ku musulmi!

Na daga cikin juyawan watanni da shekaru ga bayi na daga cikin ni'imomin Allah masu yawa ga bayi, Allah Mai tsarki ya ce ; (Kuma ya hore muku rana da wata suna madawwama biyu, kuma ya hore muku dare da wuni. Kuma ya baku dukkan abin da kuka roke shi, kuma idan kun kidaya ni'imar Allah ba za ku lissafe ta ba. Lalle ne mutum, hakika, mai yawan zalunci ne mai yawan kafurci)

Allah ya tsawatar ga duk wanda bai ribaci lokacinsa ba  da abin da zai amfanar da  shi a lahira Allah mai tsarki ya ce:- (Ase bamu baku tsawon rayuwa ba  wanda ya ci ace  mai wa'azantuwa ya wa'azantu? Kuma ga mai gargadi ya zo muku)

  kuma ni'imomi biyu idan mutum bai ribace su ba yayi asara  kuma zai yi nadama game da su.

 Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :-( Ni'imomi guda biyu mutane suna asara a cikin su, su ne ; lafiya da kuma lokaci ) Buhari ne ya rawaito

Allah ya yi  rantsuwa a ayoyi da dama  a cikin littafinSa  da wani yanki na lokaci na daga dare da yini da  alfijir da asubahi da la'sar  da walaha, hakika ga shi muna kusa da bankwana da shekara wacce ta tattaro wani abu na rayuwarmu,  muna bankwana da ayyukan mu a cikinta, wanda za a shimfida su a ranar taro  a gaba gare mu,  abin mamaki da irin saurin abin da ya shude  ya tafi,  kuma abin mamaki da girman abin da ya tattaro .

Dararraki da ranaku wasu taska ne na ayyuka  kuma matakai ne na rayuwa  na shekaru  ana tsofar da abin da ya ke sabo  a kusantar da abin da ya ke nesa  ranaku na shudewa ga shekaru suna tafiya  al'uma  suna bin bayan juna ,  bisa tafiya zuwa ga lahira  wannan na fiskantowa wancan kuma na juyawa,  wannan na samun lafiya wani kuma na samun cuta,  duka zuwa ga Allah za su koma.  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :- (Dukkan mutane suna wayan gari akwai mai saida kanshi, to, sai ya 'yantata  ko kuma ya  halaka ta ) Muslim ne ya rawaito

A cikin zamani  akwai wasu radadi da ke juyawa farin ciki, akwai kuma  farin ciki da ke juyawa bakin ciki  ranaku na wucewa ga ma'abotanta , kaman shekaru , shekaru kuma na wucewa ga ma'abotanta kamar ranaku mai hankali shi ne wanda ya riki wannan a matsayin abin lura, kuma abin wa'azantuwa  Allah Madaukakin sarki ya ce :-(Allah na juya dare da yini  lallai a hakan akwai abin lura ga masu basira ) Shekara  kan tafi  da abin da ke cikinta  abin da bayi suka aikata a cikinta na ayyuka,  za a bijiro  musu da ayyukansu , (Ana bawa mutum labari game da abin da ya kaddamar ko ya jinkirta a wannan ranar) Ka yi dubi zuwa ga takardun  ranakun ka da suka shude  wani abu ne ka adanawa kanka  a ciki don lahiran ka?  Ka kebanta da kanka ka  mata hisabi, hisabi  amintacce  wanda akwai  matsi a ciki,  Maimun dan Mihran - Allah ya mishi rahama- ya ce :-(Bawa ba zai zama mi takawa ba har sai ya kasance  yana mai tsanani ga rayinsa fiye da aboki ga abokin shi).

 Dare da yini na wucewa ne don su  nesatar daga duniya  su kusantar zuwa lahira, madalla da bawan da ya amfana da rayuwarsa  ya tsaya tare da ransa tsayawa na hisabi da kuma zargi yana gyara tafiyarsa  kuma yana riskan kusakuransa,  yakan bude shafi da daddare  na daga abin da ya aikata a wuninsa ,  idan ya kasance abubuwa ne masu kyau sai ya  doge a kan su,  idan kuma ya kasance ayyuka ne na zargi sai ya tuba daga gare su  sabo da shi matafiyi ne tafiyan da ba komawa 

 Abu Hatim Dan Hibban - Allah ya mishi rahama - ya ce:- ( Mafifitan masu hankali matsayi su ne wadan da suka dimanci  yiwa kansu muhasaba .

Tsinkaya bisa ga  aibobi na rayi   da kuma abubuwan da suke   tawaya gare ta   da laifukanta zai mata linzami daga zalunci, bawa ya san kan shi kuma ya san makomar shi zuwa ga kabari  yana haifar mishi da kankan da kai da kuma bautawa Allah,  ba zai yi alfahari da aikinsa ba duk yanda abu ya girmama,  ba zai kuma raina zunubai ba komin kankantan su.

 Abu Darda Allah ya kara yarda a gare shi yana cewa :- '' Mutum ba zai zama  cikakken fakihi ba  har sai ya kama mutane  da  laifi a hakkin Allah  , sa'annan kuma ya koma zuwa ga kanshi  sai ya kasance ya fi mata tsanani.

Idan ka zauna da mutane  ka kasance mai wa'azi ga zuciyarka ,  domin halittu suna murakaban zahirin ka ne , Allah  kuma yana murakaban badinin ka ,  duk wanda badinin sa ya yi kyau  ta hanyar murakaba da ikhlasi  to Allah sai ya zayyana zahirin shi  da kyau da rabauta.

Sanin hakkin Allah da  girman falalarSa da baiwarSa  da tuna yawan ni'imominSa  yana kira zuwa ga Allah ,  yana sa mutum kuma ya gane gajartawarsa wurin  godewa ni'imomin Allah  kuma  lallai  ya san cewa babu tsira sai da komawa zuwa gare shi,  ya dace a mishi da'a ba za a saba mishi ba  a gode mi shi ba za a butulce mishi ba.

Ibnul  Kayyim Allah ya mishi rahama ya ke cewa:- '' Farkon muhasaba shi ne mutum ya yi kiyasi tsakanin ni'imarSa mabuwayi da kuma  laifukansa  a wannan lokacin ne zai bayyana mishi lallai akwai banbanci  kuma ya san cewa lallai  ba don wani abu na afuwar Allah da rahamar sa ba  da halaka za a fada da kuma  musiba, nemar laifukan rayi yana  tsarkake ta  kuma ya gyara ta Allah Madaukakin sarki ya ce:-(Hakika wanda ya tsarkake ta ya rabauta, hakika kuma yayi asara wanda ya turbude ta )  

Malik dan Dinar ya ce :-''Allah ya yi rahama wa bawan da ya ke  cewa ransa  ase ke ba ma'abociya kaza-da – kaza ba?  Ase ba ke ce mai kaza-da-kaza ba?  Sannan sai ya sa mata linzami sannan ya sa mata birki  sannan ya lizimtar da ita da littafin Ubangijinta  sai ya kasance shi ne mai jan  ragamar ta .

Ba wani mai nisata wanda zai nisanci Allah  face sai da gafalarsa da mantuwarsa daga muhasabar sa ga Allah , Allah Madaukakin sarki ya ce (Lallai sun kasance ba su fatan hisabi)  wanda ya fada cikin munanan ayyuka  kuma ya dogara bisa  afuwar Allah da rahamarSa to hakika  ya yaudari kan sa lallai  mai karamci baya fuskantar ayyuka munana  (Ya kai mutum me ya rude ka game da Ubangijin ka Mai karamci )?  

Ibn Kasir Allah ya mishi rahama ya ce:-  (Me ya rude ka ya kai dan Adam  game da Ubangijin ka wanda ya ke mai karamci wato mai girma har ma  ka je zuwa ga saba mishi  ka fiskance shi da abin da bai dace ba ).

 Hisabi yana yin sauki ga mutanen da  suka yiwa kansu hisabi tun a duniya kuma ya kan yi tsauri ga mutanen da  suka riki wannan al'amari ba tare da muhasaba ba.

 Hasanul-Basari Allah ya mishi rahama ya ce :- '' (Baya dacewa ga mumini  face da ya rika yiwa kan shi zargi  yana mata mu'ataba  sai ya ce da ita me kike nufi da  kalma ta, me kike nufi da abinci na, amma fajiri zai shude ne  zai tafi ne  da kafansa baya zargin kansa, shi kuma mumini  yana mai tsayuwa a kansa yana mata hisabi).

Allah Madaukakin sarki ya ce :-(Lallai ne  wadanda suka yi takawa idan wani tashin hankali daga shaidan ya shafe su,  sai su tuna  (Allah)  sai ga su ,  sun zama  masu basira .

Taka-tsantsan  wurin afkawa cikin kuskure  da barin zunubai shi ne  ya fi sauki akan  neman tuba  kuma da zargin rayi bisa ga gajartawa cikin  da'a  domin ranaku a gare ka basu dauwama  kuma ba ka sani ba yaushe  ne  za ka kaura daga duniya  kuma ka yiwa kan ka magana  menene  kika gabatar a ranakun da su ka shude  kuma  wani shiri kike yi don ranaku masu fiskantowa?

Umar Dan Khaddabi Allah ya kara yarda a gare shi ya ce:- '' Ku yiwa kan ku hisabi  kafin a yi muku hisabi  ku aunata kafin a auna ku

  ka rika bibiyan ranka  a farkon  ko wani rana  wurin kiyaye sallolin nan guda biyar  a masallatayya cikin jam'i  tare da musulmai  kana neman guzuri na ilimi mai amfani tare da kai-komo wurin yada shi  da kuma ilmantar da shi  da kiyaye harshen ka daga abubuwan da suke muharramai da karya da rada  da batsa da alfasha  kuma ka kasance kana da tsantseni cikin abin da ka ke ci da abin da kake sha,  ka nisaci abin da baya halatta  ka yi kwadayin biyayya wa iyaye  ka sada zumunci,   ka yawaita ma'arufi da makusanta da na nesa  ka tsarkake zuciyan ka daga hasada  da gaba da kiyayya  ka kiyaye daga aukawa cikin mutuncin musulmai  ka yi kokari wurin tashi da wato  sha'ira na umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna  da bada hakkokin yara kuma da iyali  bisa ga fiskan da ya dace  mafi kamala  ka rintse idanuwan ka daga kallon abin da ya ke muharramai  sawa'un a hanyoyi ne ko wanin su.

 To dare da wuni  suna  nesantarwa ne daga duniya kuma suna kusantarwa ne zuwa ga lahira, madalla da bawan da ya amfana  da rayuwarsa  dukkan wayan gari  rana na faduwa  yana maka gargadi ne cewa fa wani  abu na shekarunka ya ragu  mai hankali shi ne wanda ya wa'azantu a jiyansa ya yi kokari a yau dinsa  ya shirya don gobensa  ka dauki mataki  na shiri  domin  tafiyan da take gaban ka, yi guzuri domin tafiyan ta kusanto ,  mafi alherin guzuri shi ne wanda a ka hada da tsoron Allah,  mafi darajan mutane a wurin Allah  shi ne wanda ya fi su tsoron shi .

 

Ina neman tsarin Allah daga sharrin shaidan abin jefewa

(Ya ku wadan da suka yi imani ku ji tsoron Allah kuma rayi ta yi dubi zuwa ga abin da  ta gabatar  don gobe . ku ji tsoron Allah lallai Allah Mai bada labarin abin  kuke aikatawa ne).

Allah ya sa mini albarka ni da ku a cikin Alkur'ani mai girma.

 


 

HUDUBA TA BIYU

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah bisa  kyautatawanSa,  godiya ta tabbata gare shi bisa  datarwanSa  da baiwanSa, na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya  ina mai girmama sha'aninSa na shaida Annabi Muhammad bawanSa ne kuma Manzon sa ne  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabban shi da aminci tabbatacce mai kari .

Ya ku musulmi:-

 Shekarun dan adam a nan duniya na rayuwarsa su ne  kasonsa, idan ya kyautata ribatarsu a nan duniya  cikin abin da zai amfane shi a gidan lahira to ya ci riba a kasuwancinsa, to idan kuma ya munanta ribatan su ya yawaita sabo da laifuka to ya yi hasara a kasuwancinsa, mai dace shi ne wanda ya yi hisabi wa kansa kafin Allah ya masa, ya ribaci lokacinsa ya san maganinsa daga cutarsa, bai yi sake ba har a yi mishi sakiya, alheri na cikin da'a sharri kuma na cikin sabo.

Rayuwa fage ne mai fadi na kyawawan ayyuka, jinkirta aiki da cewa sai nan gaba bai haifar da wani abu sai nadama, tuba na goge kuskure, mai samun walwala shine wanda ya adana ayyuka na kwarai a tsawon rayuwarsa. Shakiyyi shine wanda gabbansa suka shaide shi da munanan laifukansa.

To ku kiyaye ranakun rayuwanku kafin ku kadaita a kabarinku, ku ribaci ranakun rayuwarku kafin kwacewar lokaci, ku girmama masaukinku na sabon rayuwa da da'a.

Sannan ku sani Allah ya umarce ku da salati da aminci ga AnnabinSa.    

 

الجمعة، 31 يوليو 2020

FALALAN GOMAN FARKO NA ZULHAJJI 2

 

اسم المترجم : أمين سعد عبد الله

اللغة : الهوسا

التاريخ : 3-12-1441هـ

Hudubar Juma'a a masallacin Annabi na Shaikh Abdul Muhsin  Al kasim 3-12-1441AH / 24-7-2020AD

 

Hudubar farko:

  Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Madaukakin sarki  muna gode mishi kuma muna neman taimakonsa , muna neman gafarar sa, kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu , da munanan ayyukanmu , duk wanda Allah ya shiryar da shi babu mai batar da shi , duk wan da ya batar kuma babu mai shiryar da shi, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya, kuma na shaida Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa  da sahabbansa da aminci tabbatacce mai yawa.

 

Bayan haka: ku ji tsoron Allah-

Ya ku bayin Allah,- cancancin tsoronSa, ku yi murakabarSa a boye da bayyane.

Ya ku musulmi!

Allah na zaba a cikin halittun shi wanda ya so  kuma ( Ubangijinka na halittan abin da ya so kuma ya zaba) sai ya zabi manzanni  daga cikin mala'iku, da mutane, ya zabi ambatonSa daga cikin magana, kuma ya zabi dakunanSa daga doron kasa. Ya zabi ramadana da watanni masu alfarma daga cikin watanni, Jahiliyya sun kasance suna kari a kwanaki ta jinkirta don bin son rai, azuminsu bai zama a lokacinsa ba, hajjinsu kuma ba a kan lokacinsa ba, kuma Allah ya yi mana falala da turo Annabinmu Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kuma ga zamani ya zagayo kamar yadda ya ke, hajjinsa ya kasance a zulhajji, ya fada a cikin hudubarsa : Lalle zamani ya kewayo kamar yadda ya saba a sifarsa tun randa Allah ya halicci sammai da kasa)Buhari da Muslim.

         Sai adadi ya cika kidaya ya inganta al'amari ya koma bisa yadda ya gabata a littafin Allah a farko.

Fifiko tsakanin dararraki da ranaku na kira ne zuwa ga ribatan alherin da ke cikinsu, kuma Annabinmu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kwadaitar bisa ribatar ni'imomi da za su gushe ba makawa, sai ya ce : (Ka Ribaci Abubuwa Biyar Kafin Zuwan Biyar : Ka Ribaci Ƙuruciyarka Kafin Tsufanka, Ka Ribaci Lafiyarka Kafin Rashin Lafiyarka,Ka Ribaci Wadatarka Kafin Talaucinka, "Ka Ribaci Lokacinka Kafin Zuwan Shagula, Ka Ribaci Rayuwarka Kafin Mutuwarka) Nasa'i ne ya rawaito.  

Ga goman zulhijja ya shigo mana Allah ya yi rantsuwa da dararrakin su sai ya ce (ina rantsuwa da Alfajir)(da dararraki goma) , su ne ranakun Allah masu alhuruma , kuma cikamakin watanni sanannu wanda Allah ya ce game da su, (Hajji watanni ne sanannu).

Wuninsu ya fi daraja akan wunin goman karshe na Ramadan , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (mafificin ranakun duniya su ne ranaku goma) Ibnu Hibban ya rawaito,

falalan goman Zulhijja ya samu ne sakamakon tattaruwan manya manyan ibadoji a cikinta na daga salla – da azumi – da sadaka – da hajji – wanda hakan baya samuwa a waninta.

kuma dukkan ayyuka na kwarai a cikinta ya fi soyuwa zuwa ga Allah na daga irin wannan aikin idan ya faru a waninta.

Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Ba wasu ranaku wanda ayyukan alheri a cikin su ya fi soyuwa ga Allah irin wadannan ranaku)  wato yana nufin ranaku goma, sai suka ce ya Manzon Allah ko da jihadi a tafarkin Allah?  Sai ya ce: (ko da jihadi a tafarkin Allah sai dai mutumin da ya fita da rayinsa da dukiyarsa bai dawo ba da wani abu na daga wannan) Abu Dawuda ne ya rawaito asalinsa na Bukari.

Ibnu Rajab Allah ya kara yarda a gare shi ya ce '' kuma wannan hadisi yana nuni da cewa aiki na kwarai a wannan kwanaki goma ya fi soyuwa  ga Allah akan aiki a sauran kwanakin duniyaba tare da toge wani abu ba daga cikin su ''

Magabata Allah ya musu rahama sun kasance suna kokarin ayyuka na kwarai a cikin su '' Sa'id binu jubair Allah ya mishi rahama ya kasance idan goman farko na Zulhijja ya shigoya ya kan yi kokarin da ba za a'a iya ba ''

Na daga cikin falalan Allah da karamcin Sa Ya sanya  nau'uka na da'a daban daban a ciki na daga cikin abin da aka shar'anta akwai yawaita ambaton Allah , Allah subhanahu wa Ta'ala ya ke ce:(kuma su ambaci sunan Allah a ranaku sanannu) Ibnu Abbas Allah ya kara yarda a gare shi, shi da mahaifin shi ya ce:<< wadan nan kwanaki goman>> ambaton shi Allah Subhanahu wa Ta'ala a ciki na daga cikin ibadodi na kusanci Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce; (Ba wata rana da tafi girma da soyuwa wurin Allah aiki a cikin su a wurin Allah irin ranaku goma to ku yawaita a cikin su halala da kabarori Da kuma godiya wa Allah) Ahmad ne ya rawaito,

 Imam Annawawi Allah ya mishi rahama ya ce:<< mustahabbi ne yawaita  zikiri a wadannan goma kari akan su, mustahabbi ne na daga haka a ranar arfa fiye da sauran kwanaki goman, mafificin zikiri karatun littafin Allah shi ne shiriya kuma da haske bayyananne >>

Kabbarori wanda suke na saki wzaiwai ba kaidi a dukkan lokaci yana cikin manyan alamomi a watan zulhijja Ibnu Umar da Abu huraira Allah ya kara yarda a gare su sun kasance suna fita kasuwa a cikin ranakun nan guda goma suna kabarbari mutane suna kabbara da kabarbarin su , an shar'anta yin kabbara mai kaidi karshen salloli tun daga asuban ranar arfa ga alhazai da wasun su shehul islam Allah ya mishi rahama ya ce mafi ingancin zantuka a cikin kabarbari wanda jamhurin magabata suka yi da fukaha'u da sahabbai da limamai shi ne ayi kabbaran tun daga asuban asuban arfa har zuwa karshen ranakun attashrik karshen ko wani sallah.

Na daga cikin abin da ya ke mustahabbi a ranaku goma azumtan su, rana na tara shi ya fi dacewa a cikinta , Imam Annawawi- Allah ya mishi rahama- ya ce '' lallai mustahabbi ne mustahabbanci mai karfi '' .

Yin sadaka aiki ne na kwarai wanda ya ke yaye bakinciki ya ke tafiyar da bacin rai , mafi alheri  ta kasance a lokacin bukata da kuma lokaci mafi daukaka na zamani.

Tuba matsayinta a addini na da girma da daukaka domin ita ce sababi na samun rabauta da kuma samun sa'ada, Allah ya wajabta ta ga dukkan al'umma daga dukkan zunubbai. , sai ya ke ce ga wanda ya yi da'awan mata da da ga Allah (ase ba za su tuba zuwa ga Allah ba su nemi gafaran Shi ?) kuma ya ce ga muminai (ku tuba zuwa ga Allah gaba daya ya ku muminai ko za ku samu rabauta) , Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana rokon Allah a wuni so dari , kuma ya tuba zuwa gare Shi , Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ke cewa: (ya ku mutane ku tuba zuwa ga Allah domin ni ina tuba zuwa ga Allah sau dari a wuni) Bukari da muslim suka rawaito , mu muka fi dacewa da bukatuwa zuwa ga tuba , mafi alherin ranaku ga bawa shi ne ranan da ya tuba , Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce da Ka'ab binu Malik Allah ya kara yarda a gare shi (Albishirinka da mafi alherin rana albishirinka da mafi alherin ranan da ya zo a gareka tunda mahaifiyarka ta haife ka) Bukari da Muslim ne suka rawaito .

Abin mamaki da kyan tuba mutun zai tuba a mafi kyan ranaku zuwa ga Allah duk wanda ya yi gaskiya a tuban sa to darajarsa zata daukaka Allah zai canja mishi munanan shi ya maida su kyawawa .

A cikin ranaku goma na Zulhijja ana nufan dakin Allah da aikin haji daya daga cikin rukunnan musulunci kuma ginshikan shi masu girma Allah Subhanahu wa ta'ala ya ke cewa (Allah ya wajabta fiskantan daki  ga mutane duk wanda ya samu iko na zuwa) , wanda ya gaza yin hajji saboda wani uzuri to shima yana  tarayya da alhazai a cikin lada idan ya gaskata niya, ta iya yuyuwa ma mutumin da ya tafi da zuciyarsa sai ya riga wanda ya tafi da jikinsa .

A goman farko na Zulhijja akwai ranar arfa azumtansa yana kankare zunuban shekara guda da kuma shekara mai zuwa (Ba wata rana da Allah ya fi yawaita 'yanta bayi daga wuta kamar ranan arfa) Muslim ne ya rawaito.

A ciki ne akwai ranan suka mafi alherin ranaku na yanka kuma shi ne mafi bayyana kuma shi ne mafi yawan tara jama'a shi ne ake cewa yaumulhajjil akbar (ranan hajji mai girma) Allah Madaukakin Sarki ya ce: ( shelantawa daga Allah da ManzonSa zuwa ga mutane ranan hajji mafi girma) .

Shi ne mafi girman ranaku a wurin Allah Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:(lallai mafi girman ranaku a wurin Allah shi ne ranan suka sa'an nan kuma sai ranan sha daya) Abu dauda ne ya rawaito.

Kuma daya daga cikin I'idi ne na musulmai , rana ne na farin ciki da annashawa ta hanyan sauke wani rukuni daga cikin rukunnan musulunci, wasu mutane suna gafala tare da farin ciki daga ambaton Allah to ya kasance ambato a wannan ranaku yana da daraja , Allah subhanahu wa Ta'ala ya ce:(ku ambaci Allah a cikin ranaku kididdigaggu) – wato sune ranakun nan na Tashrik - , Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(Ranakun Tashrik ranaku ne na ci da sha da ambaton Allah) Muslim ne ya rawaito.

Ibnu Hajir Allah ya mishi rahama ya ce: '' Ya tabbata falalan wadan nan ranaku goma , saboda haka wadan nan ranaku na ayyamuttashrik falalan su ya tabbata ''

A cikin ranakun suka akwai ibada ta dukiya da kudi kuma ita ce mafi soyuwar ayyuka zuwa ga Allah, Allah ya hada su da sallah sai ya ce:(ka yi salla ga Ubangijinka kuma ka yi suka) , Allah ya kwadaitar bisa ga ikhlasi a wurin suka, kuma ya kasance Allah aka nufa a ciki Shi kadai ba alfahari ko riya ko kuma neman a ji ko kuma ya zama kwai tsurar al'ada ce, Allah subhanahu wa Ta'ala ya ce :(naman shi baya riskan Allah ko jinin su saide tsoron Allah ne ya ke riskan Shi) kuma << Annabi ya yi laiha da raguna biyu masu fari da baaki a kahgon su ya yanka su da hanun shi >> Bukari da Muslim ne suka rawaito. ''al'amlah '' (shi ne baki wanda saman shi akwai fari) "al'akran"( kuma shi ne mai kaho) , babu laifi mutun ya yi bashi don ya yi laiha kuma ya nemi mayuwa a wurin Allah kada ya rika zambo sakamakon tsadanta , domin ladan ta wurin Allah yana da girma duk wanda ya nufi ya yi laiha to ya haramta a gare shi a cikin ranaku goman nan da ya dauke wani abu na daga gashin shi ko farcen shi , Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ke cewa (Duk wanda ya kasance yanada abun yanka zai yanka to idan jinjirin watan zulhijjah ya kama to kada ya dauki wani abu na daga gashin shi ko kkuma kumban shi har sai ya yi laiha) Muslim ne ya rawaito.

Bayan haka ya ku musulmai:

Wanda ya samu sa'ida shi ne wanda ya ribaci lokutan nan na watannin nan da ranakun nan da sa'o'in nan ya kusanci Allah Majibincin shi da abin da ya ke na ayyukan da'a , ya wuci wani abu ya riske shi na wannan alheru ya samu sa'ada wanda zai aminta da su bayan haka daga wuta da abin da ke ciki na daga alheru kuma ya rabauta da aljanna wanda fadinta ya kai sammai da kasa .

Ina meman tsarin Allah daga shaidan abin jifa

(Ku yi gaggawa zuwa ga Uban gijin ku da aljannah wanda fadinta ya kai sama da kasa an tanadeta ga wanda suka yi imani da Allah da ManzanninSa wannan falala ne na Allah ya kan bada shi ga wanda ya so Allah Ma'aboci falala ne Mai girma).

Allah Ya sa mini albarka ni da ku a cikin alkur'ani mai girma. 

 

Huduba ta biyu :

   

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah bisa kyautatawanSa dodiya a gare Shi bisa datarwan shi da baiwan Sa na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai Ya ke ba Shi da abokin tarayya ina mai girmama Sha'aninSa , na shaida Annabin mu Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da sahabbansa da aminci tabbatacce mai kari.

Ya ku musulmai:

Addinin musulunci addini ne mai girma da an gina shi akan janyo maslahohi da kuma tunkude barna saboda wata hikima da Allah ya ke nufi da ita, ya shafawa mutane a doron kasa gabacin kasa da yammacinta da wata annoba wanda ba a taba irinta ba a tarihin doron kasa ko da sau daya kuma da boyuwarta da yaduwarta da gazawan samo maganinta wanda yana kama wanda ya kiyaye daga gareta a wani lokaci kuma ya kuskure da umarnin Allah wanda ake zaton zai kamu da ita.

 Hakika Allah ya kebance wannan gari (Alharamain Ashsharifain) da wasu darajoji kuma ya daukaka darajan jagororinta ta hanyan hidima da kuma kaunan su ga musulmai a dukkan doron kasa da kuma tsorace musu  abin da zai faru gare su na daga cutuwa, saboda haka ne jagororinta suka dauki matakai na hana yaduwar wannan cuta na annoba domin fatan gushewarta ba tare da an samu cakudayyan mutane ba sashin su ga sashi musamman a hajji tunda ana tafiya ne zuwa gare shi kuma ana zuwa a dawo yana karuwa a garuruwa, sai suka maida karin alhazai zuwa ga shekara mai fiskantowa domin fatan alheri da neman yayewan Allah da rahamarSa, Allah ya saka musu da alheri bisa ga musulunci da musumai.

Allah Subhanahu wa Ta'ala Ya siffantu da falala da karamci da rahama na daga wanda ya nufi hajji ya gazara yi to za a rubuta mishi ladan shi Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (lallai a cikin Madina akwai wasu mutane da baza ku yi wasu tafiya ba ko ku yanka wani kwari ba face sun kasance tare da ku) sai suka ce ya Manzon Allah : alhali suna Madina sai ya ce:(iye, uzuri ne ya tsare su) Bukari ne ya rawaito .

Sannan ku sani Allah Ya umarce ku da salati da  aminci ga AnnabinSa.

 


HUDUBAR BABBAR SALLAH

خطبة عيد الأضحى لفضيلة الشيخ أحمد طالب

اسم المترجم : أمين سعد عبد الله

اللغة : الهوسا

التاريخ : 10-12-1441هـ

Hudubar babbar sallah na masallacin Annabi tare da Shaikh Ahmad bin Hamid   Al dalib 10-12-1441AH / 31-7-2020AD

 

Hudubar farko:

Allahu Akbar Allahu Akbar Allahu Akbar

 

Allahu Akbar Allahu Akbar Allahu Akbar

 

Allahu Akbar Allahu Akbar Allahu Akbar

 

Allahu Akbar kabiran  , walhamdu lillahi kasiran , wa subhanallahi bukratan wa asila.

Allah Mai girma Abin girmamawa.

 Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Abin daukakawa  kuma tsarki ya tabbata ga Allah abin tsarkakewa  kuma ba abin bautawa da gaskiya sai Allah Abin kadaitawa  babu dabara ko karfi sai ga Allah Abin dogaro, abin fauwalawa na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya  muna masu  tabbatarwa da kuma kadaitawa, na shaida Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da aminci mai kari.

Tsarki ya tabbata ga Allah  kuma godiya ta tabbata ga Allah   ba abin bautawa da gaskiya sai Allah , kuma  Allah mai girma  ba  dabara  ko karfi sai ga Allah Madaukaki kasaitacce .

Mafi soyuwan magana zuwa ga Allah  kuma mafi soyuwan magana zuwa ga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  bisa duk abin da rana ta fito a kan shi wanda take mafi daukaka wanda aka 'yanta kuma mafi kyau akan dawakai masu linzami da sirdi  da kuma mafi tsadar raguna da aka sa musu alama na hadaya  karbabbiya

Allah Mai girma wanda  zai cika tsakanin sama da kasa ya kankare zunubai ko da ya kai tarukucen kumfan kogi ne  da fadowansu zuwa kasa kamar yanda 'ya'yan itace ke zuba .

Allah mai girma ……su ne dashen aljanna kuma masu tseratarwa  kuma garkuwa kuma Albakiyatussalihatu wanda ladan su ke wanzuwa sakayyan su ke dauwama .

Allah mai girma… suna shawagi a  kewayen al'arshi mai rahama suna da sauti kaman sautin kudan zuma   suna tunatarwa game da sahibinsu  ba zai gushe ba yana da abin da ake ambatonsa da shi gaba ga UbangijinSa, kuma Ubangijin ka bai kasance mai mantuwa ba.

Kuma ba wani mutum da ya fi daraja a wurin Allah akan mumini wanda  ya yi tsawon kwana a musulunci  yana yawaita ambaton Allah .

Allah mai girma…..

Sune sadaka na gangan jiki  kuma masu nauyaya mizani  kuma masoya zuwa ga Mai rahama kuma da su ne ake nade sunayen Allah kyawawa da siffofin shi Madaukaka  su ne masu tattaro abin da suka tarwatse  kuma su ne matattara na yin da'a.

Allah Mai girma….

(Ya ku wadanda suka bada gaskiya  ku ji tsoron Allah  ku fadi magana da take  dai-dai, zai gyara muku ayukan ku kuma ya gafarta muku zunubanku, duk wanda ya ke yiwa Allah biyayya da ManzonSa to hakika ya rabauta, rabauta mai girma ) Ahzab 71

(Ya ku wadanda suka yi imani ku ambaci Allah ambato mai yawa, ku yi masa tasbihi safiya da maraice , shi ne wanda ya ke salati a gare ku da mala'ikun sa domin ya fitar da ku  daga duhu zuwa haske  kuma ya kasance mai rahama  ne ga muminai, gaisuwan su ranar haduwan su da shi shi ne aminci , kuma ya tanada musu lada mai girma ) Ahzab 44.

Da shaidawa da salla da azumi da zakka da jahadi da  hajjin dakin Allah  ba wani abu ba ne sai wasu sifofi ne na girmama Allah  da kuma wasu dalilai ne na ambaton Allah ba wanda zai samu daukaka  da talbiya  ko ya koshi da  tarwiya  ko ya yi arfa da taskiya, ko ya tsaya wurin girmamawa  ko kuma ya kusanto da mika wuya  ko ya yi jifa da walaha ko ya yi dawafi da hantsi, ko ya yi suka da kabbara  ko ya yi jifa da garji, face wanda harshen sa ya kasance danye  ne daga amabaton Allah.

Allah mai girma.

 

 

HUDUBA TA BIYU

 

Allah Mai girma Allah Mai girma Allah Mai girma Allah Mai girma Allah Mai girma Allah Mai girma Allah Mai girma

(Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku lallai girgizan kasa wani abu ne mai girma,  ranar da za ku ganta duk wata mai shayarwa takans ingije abin da ta ke shayarwa, duk ma'abociya ciki zata sauke cikinta za ka ga mutane cikin maye alhali ba maye ba ne suke ba face azabar Allah ce mai tsanani). Haj 1-2.

 

  Allahu akbar kabiran, walhamdulillahi kasiran, wa subhanallahi bukratan wa asila,

Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya na shaida Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi.

Ku yi laiha ya ku bayin Allah –Allah ya karba muku laihanku ba wani abin da mai bauta zai kusanci Allah da shi a ranar laiha da ya kai zubar da jinin dabbobin gida ga Allah Ubangijin talikai  ya ci ya yi kyauta  ya yi sadaka ya bayyana manyan alamomin addinin Allah  sunnan baban ku Ibrahim  amincin Allah ya tabbata a gare shi da Annabinmu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi .

Ku sani cewa baya inganta a laiha a yi da  mara lafiya wacce rashin lafiyanta  ya bayyana ko makauniyar dabba wacce makantanta ya bayyana  ko gurguwan dabba  wacce bata iya tafiya tare da masu lafiya,  ko kuma mai gutsurarriyar kunne  wanda sama da rabin kunnen ta ya gutsure  ko kahonta , haka nan banda ramemmiya wanda babu bargo a kashin ta , haka nan kuma ba a so a yi da mara hakori  wanda hakwaranta na gaba suka cire daga asalin su   ko kuma wacce nonon ta ke motse kuma ya bushe tare da girma  haka nan kuma ba a so a yi da wacce ta kamu da cuta, cuta mai raba.

Ba ayi da rakumi  kasa da shekaru biyar , ko saniya sai  wacce ta kai shekaru biyu   ba ayi da akuya  sai wacce ta cika shekara ko rago sai wanda ya cika wata shida  rakumi na iya isarwa  mutane bakwai  saniya ma na isarwa mutum bakwai  abin da yake sunna shi ne a soke rakumi a tsaye an daure hanun shi na hagu , a yanka saniya kuma da dabbobi a baryan su na haku suna fiskantar alkibla  kuma za a ce ya yin  yanka ''Bismillahi'' , bisa wajabcin ''wallahu akbar'' bisa mustahabbanci .

Abinda yake sunna shi ne ya ci sulusi daga namanta ,  ya yi sadaka da sulusi yayi kyauta da sulusi.

 Kada ya saida fatan ta   ko wani abu na daga gare ta  kada kuma ya bawa mahauci ladansa daga cikinta  .

An sanya lokacin yanka tun daga kare sallan idi har zuwa karshen kwanaki biyu bayan sa .

Allah mai girma Allah mai girma ba abin bautawa da gaskiya sai Allah  kuma Allah mai girma Allah mai girma dukkan yabo da godiya na Allah ne.

 (Kuma rakuman,  mun sanya su a gare ku,  a ibadojin Allah kuna da wani alheri babba a cikin su . Sai ku ambaci sunan Allah a kansu suna tsaye akan kafafu uku  sa'annan idan  sasanninsu  suka fadi , to,  ku ci daga gare su , kuma ku ciyar da mai wadar zuci  da mai bara . kamar haka muka hore muku su,  tsammaninku, kuna godewa .

Namomin su ba za su sami Allah ba, haka jinainansu, amma takawa daga gare ku tana samun Sa. Kamar haka ya hore su  sabo da ku,  domin ku girmama Allah  sabo da shiriyar  da  ya yi mu ku . Kuma ka yi  bushara  ga masu kyautata yi.)

 

Ya ku bayin Allah ku riki mai daga adua mai bude kofofin sama …salati da aminci ga limamin Annabawa kuma shugaban masu takawa.

Adu'a.  

 

 

 

 

 


YALWAR AFUWAR ALLAH

اسم المترجم : أمين سعد عبد الله

اللغة : الهوسا

التاريخ : 10-12-1441هـ

Hudubar Juma'a a masallacin Annabi na Shaikh Abdulbari dan Awad Assubaiti 10-12-1441AH /31-7-2020AD

 

Yalwar afuwar Allah

 

Hudubar farko

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wadda ya sanya aljanna sakayyar hajji  mabruri,    ina kyautata yabo gare shi, tsarki ya tabbata a gare shi   kuma ina gode mishi  bisa dukkan falala da alheri  da ya saukake na  shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya  shi ne Mai yafiya kuma Mai gafara,  shi ne Mai yawan yafiya kuma Mai gafara  kuma na shaida shugaban mu kuma Annabinmu  Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne  ya bautawa UbangijinSa da yakini zuciyarsa  sai ta zama tana farin ciki   da kaunarsa  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabban shi, duk wanda ya kaunace su  shine abin taimakawa kuma mai samun lada.

Bayan haka;  

 Ina muku wasiya da ni kaina da tsoron Allah, Allah Madaukakin sarki ya ce :- (Ya ku wadan da suka yi imani ku ji tsoron Allah cancancin  tsoron shi kada ku mutu face kuna musulmai ).

Yafiyan  Allah kalma ce da take jefa natsuwa a cikin zuciya  da kwanciyan hankali a cikin zuciya  da kuma sika cikin abin da yake  wurin Allah.

(Hakika Allah ya kasance Mai yafiya ne kuma Mai yawan gafara yana  yafewa wanda yayi zunubi  kuma ya gafartawa wanda ya yi laifi kuma yana rangwantawa wanda yayi kuskure) ( shi ne wanda ya ke karban tuba daga bayinSa kuma yake yafewa daga kusakurai  kuma ya san abin  da kuke aikatawa ).

 

Na daga cikin kyawun afuwar Allah yana son  masu tuba  kuma yana farin ciki da komawa zuwa gare shi

Na daga cikin yalwan afuwar Allah da ribanya kyawawa da yake yi da kuma bada lada bisa ga nufan yin abu  ba tare da munana ba.

 Na daga  cikin kyakkyawan afuwan Allah shi ne yakan canza munanan  ayyuka ya maida su  kyawawa  bayan tuba  na gaskiya, idan bawa ya daina aikata aikin haramun  ya fiskanci sabuba na tuba  da da'a  ya kara imani tare da imaninsa  sai ya karfafi dalilai na imani  a cikin zuciyarsa, sai Allah ya karrama shi  da  kyakkyawan yafiyarSa.

Abin mamaki da yalwa da kuma kawa irin na afuwar Allah  Mai tsarki da Daukaka,

 Allah ya ce :- (sai wanda ya tuba ya yi imani kuma ya yi aiki , aiki na  kwarai to wadannan Allah zai canza musu laifukan su kyawawa, Allah ya kasance Mai gafara ne Mai jin kai) .

Na daga cikin yalwan afuwar Allah  cewa rahamarSa tana rigayar fushinSa  yafiyarSa kuma tana riga ukubarSa,  Buhari ya rawaito shi daga Hadisin Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce :- Na ji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa :- (Lallai  Allah yayin da ya yi halittan halitu  ya rubuta a wurin shi a saman al'arshin shi, lallai  rahama ta ta rigayi fushi na ).

Na daga cikin yalwar afuwar Allah  shi ne jinkirtawa bayinSa da yake yi  kafin ya kama su domin  Allah Mai tsarki da daukaka shi  yana fiskantar jahilcin bayi da hakuri  sa'annan kuma zunubinsu yana fiskantar sa da gafara,  sannan bayyana sabo kuma yana fiskantar shi da suturtawa, kafurcewa ni'ima  kuma Allah yana fiskantar ta  da ni'imtarwa.

    Na daga cikin yalwar afuwar Allah da ya sanya masu kankare zunubai nau'uka daban –daban, na daga cikin masu kankare zunubai akwai yalwata alwala, da ambaton Allah karshen farillu, da yawan taku zuwa masallatayya, da azumin ramadana da azumin ranar Arafa da azumin ranar Ashura., da adu'ar kaffatul majlis da umara da Hajji da sauke sallolin farilla. Da sadaka da hakuri da halartan majlisai na zikiri, da salati ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Na daga cikin koyarwar Annabi kwadayin neman afuwa da yafiya yana rokon Allah a lokacin da ya wayi gari da lokacin yammaci (Ya Allah ina rokonka afuwa da waraka a addini na da duniya ta da iyalai na da dukiya ta).  

Allah ka sa min albarka ni da ku cikin Alkur'ani mai girma.

 

HUDUBA TA BIYU

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga wanda  da ni'imarSa ce kyawawa ke cika  ina kyautata yabo a gare shi kuma ina gode mishi bisa kyautarSa  masu yawa,  na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya  Abin bautar halittu na shaida  shugabanmu Muhammad bawanSa ne kuma Manzon sa ne , shi ne abin koyin mu a duk wani yanayi da aka shiga na tsanani  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  da sahabbansa ma'abota falala abin girmamawa.

  Bayan  haka, ina muku wasiyya da kaina da tsoron Allah  duk  wanda ya dimanci da'a ga Allah  to zai rabauta da afuwar Allah.

 

Tare da wannan falala mai girma da kuma yafiya mai yawa,  mutum zai kiyaye daga ruduwa da afuwar Allah  da girman karamcinSa  Allah Madaukakin sarki ya ce :-(Ya kai mutum  mai ya  ruda ka  game da Ubangijin ka Mai karamci ).

 Ya dace a wadannan kwanaki a bayyana manyan alamomi na musulunci na daga ciki akwai  kabbarori  wanda suke masu kaidi  karshen salloli na farilla,  wanda ke farawa tun daga safiyan ranar arfa  har zuwa faduwan ranar karshe na ayyamut tashrik .

 Allah Mai girma ba abin bautawa da gaskiya sai Allah  kuma Allah Mai girma  ba bu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma  Allah Mai girma dukkan yabo da godiya na shi ne.

  ku saurara kuma ku yi salati  ya ku bayin Allah bisa ga Manzon nan na shiriya  hakika Allah ya karrama ku a littafinSa.