الثلاثاء، 14 يوليو 2020

GODIYA BISA NI'IMOMI

اسم المترجم : أمين سعد عبد الله

اللغة : الهوسا

التاريخ : 12-11-1441هـ

Hudubar Juma'a a masallacin Annabi na Shaikh Aliyu Bin Abdurrahman Al-Huzaifi 12-11-1441AH / 2-7-2020AD

 

Hudubar farko

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Majibinci abin godiya, Ma'aboci al'arshi mai girma, wanda ake fata don yaye dukkan bakinciki mai tsanani, ina kyautata yabo ga Ubangiji kuma ina gode masa bisa ni'imominSa ba mai iyakance su face shi cikin wadanda  muka sani da wadanda ba mu sani ba, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, Mai aikata abin da ya so, na shaida Annabinmu kuma shugabanmu Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne. abin koyi a dukkan al'amura na shiriya, Allah ka yi dadin tsira da aminci da albarka ga bawanka Muhammad da iyalansa da sahabbansa wadanda suka taimaki musulunci da aiki da shi da kuma kira zuwa gare shi da jahadi don daukaka kalmarSa har zuwa lokacin da tauhidi ya wargaza duhun shirka,

Bayan haka ku ji tsoron Allah Ubangijinku, ta hanyar tashi da wajibabbu, da kauracewa muharramai za ku rabauta da daddadar  rayuwa da kyakkyawan karshe. Allah Madaukakin Sarki yace : (wancan gida na lahira muna sanya ta ne ga wadanda ba su son dagun kai a doron kasa ko barna, akiba na ga masu takawa).

Ya ku musulmai!

Hakika Allah ya halicci wannan duniya ne don ya cika al'amarinSa a ciki kuma  mashiarSa ta zartu a cikinsu ya yi  hukunci a cikin Su da hukuncinSa da ba mai bin sawu, kuma ya gudanar da su da gudanarwarSa wanda ke cike da hikima da iliminSa da hikimarSa, da rahamarSa da kudurarSa, halittu na sanjawa ne daga wani yanayi zuwa wani yanayi ne tsakanin falalarSa da rahamarSa da adalcinSa da hikimarSa.

Duk abin da ya samu halitta na yalwa da alheri to fa tsaban falalarSa ne da rahamarSa, Allah Madaukakin sarki ya ce :   (Duk abin da ya same ka na kyakkyawa to daga Allah ne) kuma Mai tsarki yace : (Duk abin da Allah zai budewa mutane na rahama to ba mai rike ta kuma abin da ya rike to ba mai turowa  bayanSa kuma shi Mabuwayi ne Mai hikima) Allah Madaukakin sarki ya ce :   (Ashe baku gani cewa Allah ya hore muku abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin kasa kuma ya yalwata muku ni'imominSa bayyanannu da na boyayyu).  Allah Madaukakin sarki ya ce :   (kuma duk abin da ke gare ku na ni'ima to daga Allah ne). kuma Allah Mai tsarki ya ce :  (kuma idan kun kidaya ni'imar Allah ba ku iya lissafa ta, lalle ne Allah Mai yawan gafara ne Mai jinkai).

To ni'imomi mafarinsu daga Ubangiji ne,Mabuwayi da daukaka kuma karshen su ma daga gare Shi ne ba wani da ya cancanci ni'ima daga gare Shi , na daga cikin rahaman Allah ga bayin Shi da ya umarci bayi da su yi godiya bisa ni'imomi domin su wanzu su karu, ya gargadi daga rashin godiya game da su domin kada su gushe ko su kauce, sai Allah Mabuwayi ya ce (ka ambata yayin da Ubangijinku ya ce muddin ku ka gode to lallai zan kara muku idan kuma ku ka butulce , to lallai azabaTa na da tsanani)

Godiya wa ni'imomi ana yi ne ta hanyan tashi da farillu da kuma rashin aikata alfahasha da munkarai , ya kuma tafiyar da ni'imomi cikin abin da zai yardar da Allah Madaukaki da kuma girmama Mai ni'ima Mabuwayi da daukaka , Allah Mai tsarki ya ce :(ku godewa ni'imar Allah in kun kasance Shi kadai ku ke bautawa) kuma Allah Madaukakin sarki ya ce :(ku yi aikin godiya ya iyalan Dauda , kuma kadan ne daga cikin bayi Na masu godiya) wasu ma'abota ilimi suka ce ''Ba wani lokaci da zai zo a dare ko wuni face a iyalan Dauda akwai mai ruku'i  ko sujada ko kuma wani mai aikin da'a"

 To ka tuna ya kai musulmi ni'imomin Allah a gareka ka yi tunani yanda Ubangijinka ya fari wadannan ni'imomi a gareka alhali kai kuma ba ka cancance su ba a gare Shi , ka yi godiya game da su ga Ubangiji Mai tsarki , kamar yanda Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi godiya ga Ubangijin Shi  da su a fadinsa (Ya Mai yalwan gafara : ya Mai shimfida hannaye biyu da rahama , Ya Ma'aboci dukkan ganawa ya Makura na dukkan kokawa ya mai karamcin rangwame ya Mai girman kyauta ya Mai fara ni'imomi tun kafin cancancanta ya Ubangijin mu ya Shugabanmu Majibincinmu ya makuran bukatanmu ina rokon Ka ya Allah kar ka soya halitta ta da wuta) Hakim ne ya rawaito a cikin Al- mustadrak daga hadisin Amru dan shu'aibu daga babansa daga kakansa kuma ya ce hadisi ne ingantacce .

Tuna ni'imomi da girmama su yana haifar da kaunar Allah da jin kunyarSa,  ta yaya zai kasance daga mai hankali ya fiskanci Mai kyautatawa da muzgunawa, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (ku kaunaci Allah saboda kalace da ya ke baku, na daga ni'imarSa , kuma ku kaunace ni saboda kaunan Allah, ku so iyalan gidana saboda kaunata) Tirmizi ne ya rawaito kuma ya inganta shi da Hakim kuma ya ce sahihi ne daga hadisin Ibnu Abbas  Allah ya kara yarda a gare su , wannan na daga cikin gudanarwan Allah da kyautanSa da alherori da albarkatu da kyawawa ga bayi ba wani da ya isa ya cika ni'imomin Allah da da'a domin falala dukkan shi na Allah ne  Madaukaki sai dai Allah yana yafiya kuma yana rahama yana bada falala kuma yana yarda da kadan na daga ayyuka na kwarai da iklasi da kuma bin sunnah annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (aikin dayanku ba zai shigar da shi aljanna ba sai aka ce : ko kai ma ya Manzon Allah ? sai ya ce ko nima sai dai Allah ya lullubeni da rahamarSa) Ahmad ne ya rawaito daga hadisin Abu Huraira Allah kara yarda a gare su , Ibnu Rajab Allah ya mishi rahama ya ce game da bayi na kwarai : sun kasance suna tuhuman ayyukansu da kula da ayyukansu da tuban su kuma suna tsoron kada a ki karba musu sai hakan ya kasance yana sanya musu tsananin tsoro , da yawan kokari cikin ayyuka na kwarai , Hasan dan basari Allah ya mishi rahama ya ce '' na riski wasu mutane da dayansu ya ciyar da abin da ya kai cikin doron kasa to da bai amunta ba saboda girman zunubi a cikin zuciyansa''  ta tike.

Kamar yanda alheri da ni'imomi da yalwa da hukuncin Allah ne da kaddararSa da falalanSa da rahamarSa haka nan musibu da sharrori  da ukubobi  duka da hukuncin  Allah ne da kaddararSa da a'adalcinSa da hikimarSa , Allah Madaukakin sarki ya ce :(Allah ne Mahaliccin dukkan komai kuma Shi wakili ne ga dukkan komai) An karbo daga Abdullahi dan Amr Allah ya kara yarda a gare shi shi da mahaifin shi daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (lallai Allah ya rubuta kaddarori na halittu kafin ma ya halicci sammmai da kasa da shekara dubu hamsin , al'arshinSa kuma yana kan ruwa) Muslim ne ya rawaito da Tirmizi .

Allah Mabuwayi da daukaka ya halicci sabuba kuma ya halicci abin da ya ke bayan sabuba , Ubangiji yana halitta da sababi kuma yana halitta ba tare da sababi ba , abin da ya so shi ke kasancewa , abin da bai so ba baya kasancewa , yana yin jarabawa da alheri kuma yana yin jarabawa da sharri , Allah Madaukakin sarki ya ce:(Hakika muna jarabtan ku da sharri kuma da alkairi a matsayin fitina kuma gare mu ne za ku koma) , sai ya bada lada ga masu yin da'a masu godiya kuma ya yi ukuba ga masu sabo masu juhudi (musanta ni'ima) dukkan duniya na gudana ne bisa sunnar Allah yanda Allah ya so kuma ya bayyana a cikin littafinSa to Allah mai girma Mai iko Mai tausayi Mabuwayi ,Mai hikima Shi ne wanda ya kyautata duniya kuma ya ke tunkude shi Allah Madaukakin sarki ya ce :(Yana gudanar da al'amari kuma yana saukar da ayoyi daki daki ko za ku samu sakankancewa game da haduwa da Ubangijinku) AllahMai tsarki ya ce :(Yana gudanar da al'amura ba wani mai ceto face bayan izininSa , wancannin ku Shi ne Ubangijinku ku bauta miShi shin ba za ku yi tunani ba?) Allah Mabuwayi ya ce:(Wanda ke cikin sammai da kasa suna tambayan Shi a ko wani rana kuma yana cikin sha'ani)

An karbo daga Abu Darda'i Allah ya kara yarda a gare Shi ya ce : Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(Dukkan ko wani rana yana cikin sha'ani na daga cikin sha'anoniSa ya gafarta zunubai ya yaye bakin ciki ya amsa mai roko , ya dauke wa wasu mutane kuma ya sanyawa wasu mutane) Bazzar ne ya rawaito .

  Da duniya na tafiya ne a cikin zamaninta kaman yanda mutane suke so da jarabawa bai faru ga Annabawa ba amincin Allah su tabbata a gare su da kuma bai kasance suna da kyakkyawan akiba ba su da mabiyansu da kuma wanda suka saba musu ba su kasance suna da nau'o'i  na ukubobi ba sai dai hukunci na Allah ne Shi kadan Shi , Allah Madaukakin sarki ya ce :(ka ce lallai al'amari duka naShi ne) Allah Madaukakin sarki ya ce: (wadanda suke bautawa wani koma bayan Allah ba wani abin da suka mallaka ko da tantanin kwallon dibino ba).

Musibu na kankare laifuka ga musulmi kuma suna daga darajojin shi,

An karbo daga Abu Huraira daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Bala'i ba zai gushe ba ga mumini da mumina a cikin rayinsa da dansa kuma a dukiyarsa har ya hadu da Allah bayi da wani kuskure) Tirmizi ne ya rawaito kuma ya ce hadisi ne hasanun sahihun da Hakim kuma suka inganta shi.

An karbo daga Muhammad dan Kalid Assulami daga babansa daga kakansa ya ce: na ji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa : (lallai bawa idan wani matsayi ya tsere a gare shi daga Allah to bai riske ta ba da aikin shi sai Allah ya jarrabe shi a jikinshi ko kuma a dukiyansa ko kuma a dansa sannan Allah ya hakurtar da shi a kan haka har ya riski wannan matsayi din da ya tsere mishi daga Allah Madaukaki) Abu dauda ne ya rawaito shi da Ahmad da Abu ya'ala.

Bala'i na zuwa ne gwargwadon karfin addinin mutun da kuma raunin shi, An karbo daga Mus'ab dan sa'ad daga babansa ya ce : na ce : ya Manzon Allah : a cikin mutane wanene ya fi bala'i sai ya ce: (Annabawa sannan sai wadanda suka fi riko sai wadanda suka fi riko, ana jarabtan mutun ne gwargwadon addininsa idan har ya kasance addininsa nada karfi to sai bala'insa ya yi karfi idan ya kasance a cikin addininsa yana da rauni sai Allah ya jarrabe shi gwargwadon addininsa bawa ba zai gushe ba yana haduwa da bala'ai har ya bar shi yana tafiya a doron kasa bai da wani laifi tare da shi) Tirmizi ne ya rawaito kuma ya ce hadisi ne hasan sahihi kuma Ibnu Maja ma ya rawaito shi.

 Musibu kuma da bala'o'i da annobobi suna sauka ne gamagari ; domin a bada lada ga al'umar musulmi saboda hakurin da suka yi da neman lada a wurin Allah kuma abin lura ne ga mutane don su yi tunani cikin kofofi na zunubai da suka aikata domin kada su maimaita irin zunuban saboda su aikata abin da ya fi girma kuma saboda kada a yi musu ukuba da abin da ya fi girma domin su wa'azantu da abin da suka kasance a ciki na daga ni'imomi kafin saukar bala'i domin waraka ko lafiya ta tabbata a cikinsu da aminci da yalwa ta hanyar da'a, Allah Madaukakin sarki ya ce: a cikin sunnoninSa (ya wuci Ubangijinku ya muku rahama idan kun koma kuma muma mu koma)

Allah Mabuwayi da daukaka ba ya dawwamar da annoba sai dai yana dauke ta idan ya so, ku jira yayewa daga Allah , ku fiskanci bala'i da addu'a da kuma komawa zuwa ga Allah domin lallai Ubangiji tsarki ya tabbata a gare Shi Mawadaci ne daga azabtar da mutane sai dai Shi Allah Madaukaki yana so musu ne don su yi aiki na kwarai kuma su kauracewa munanan laifuka, Allah Madaukakin sarki ya ce :(Idan bayiNa suka tambaye ka game da Ni ka ce: lallai Ni iNa kusa kuma Ina amsa kiran mai kira idan ya kiraye Ni , to su amsa kira Na kuma su yi imani da Ni ko za su samu shiriya) Allah Madaukakin sarki ya ce: ( lallai rahamar Allah kusa ta ke ga masu kyautata wa).

Allah ya sa mini albarka ni da ku a cikin alkur'ani mai girma .

 

Huduba ta biyu :

 

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai na shaida ba abin bautawa  da gaskiya sai Allah Shi kadai ya ke ba Shi da abokin tarayya Mai karfi kuma AlMatinu na shaida Annabinmu kuma shugabanmu Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne amintacce , Allah ka yi dadin tsira da aminci da albarka bisa ga bawanKa  da kuma ManzonKa Muhammad da iyalanSa da sahabbanSa baki daya.

Bayan haka : ku ji tsoron Allah cancancin takawa ku yi riko da igiya mai karfi na musulunci, ya ku bayin Allah ku sani lallai wadatuwan  bawa  da kuma sa'adarsa yana cikin bukatuwansa  zuwa ga Ubangijinsa ne da yakininsa da hakan , Allah Madaukakin sarki ya ce: (Ya ku mutane ku talakawa ne zuwa ga Allah kuma lallai Allah kuma Shi Mawadaci ne abin godiya).

Lallai dukkan tabewa ga bawa da hasararsa da halakarsa gurin zatonsa cewa ya wadatu daga Ubangijinsa kuma ya rudu da kansa da abin da Allah ya bashi Allah Mai tsarki da daukaka ya ce: (lallai wanda ya yi rowa kuma ya wadatu ya karyata kyakkyawa da sannu za mu kama shi da tsanani ba zai amfane shi ba dukiyansa idan ya halaka) , an karbo daga Abdullahi dan Abbas Allah ya kara yarda a gare su shi da mahaifinshi ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (Ni'imomi guda biyu mutane da yawa suna hasara a cikinsu : lafiya da kuma zama haka) Bukari ne ya rawaito .

Ya ku bayin Allah lallai Allah da mala'ikunSa suna salati ga Annabi ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi da aminci tabbatacce mai yawa .

     

      

 

 


DARUSA DAGA SULHUN HUDAIBIYYA A WANNAN YANAYI NA KORONA

اسم المترجم : أمين سعد عبد الله

اللغة : الهوسا

التاريخ : 19-11-1441هـ

Hudubar Juma'a a masallacin Annabi na Shaikh Abdulbari dan Awad Assubaiti 19-11-1441AH / 9-7-2020AD

 

Hudubar farko

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzon Allah, bayan haka.

Tarihin Annabi kan haskaka mana hanyar tafiya a rayuwa. Na daga cikin shafuka na sira masu kamshi akwai tarihin sulhun Hudaibiyya da darusansa da  mawakif na sa da abin da ya faru a ciki Allah ya ambace shi da budi Allah Madaukakin sarki ya ce:- (Lalle Mu Mun yi ma budi wanda yake budi bayyananne).

Sahabbai sunyi bushara  da mafarkin da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya gani cewa za su shiga Makka kuma su yi dawafi  a dakin Allah Madaukakin sarki ya ce :- (Lalle ne Hakika Allah ya gaskata wa ManzonSa mafarkinsa da gaskiya: Lalle  za ku shiga masallacin Harami in Allah ya so,  kuna  amintattu kuna masu aske kawukan ku da  masu saisaye , ba ku jin tsoro).

  Mutum dubu da dari hudu  daga cikin masu umra suka tafi  tare da Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  suna da kuzari game da abin da suke ji  na karfin guiwa,  zukatan su na cike da  shu'uri  suna masu nufan dakin kaba  bayan yankewan shekaru da  wannan wurin din mai albarka  wanda zukata ke karkata zuwa gare ta  wanda ta kasance kuma bata gushe ba  kuma baza ta gushe ba  wato shudewan zamani da kuma lokaci , alkibla ne da zukata kuma  wurin karkata ne da zuciya  rayuka kan samu natsuwa a farfajiyan ta  kuma   ta dauki ibra a kasanta kuma  ta zubar da hawaye   Ibrahima alaihissalam  ya mata adu'a (Allah Ubangiji lallai na zaunar daga cikin  zuri'a ta  a  kwari wanda ba yi da shuki  a wurin dakin ka mai alfarma , Ya Ubangijin mu domin su tsaida sallah ka sanya  zukata na mutane na karkata zuwa gare su )

Shauki zuwa ga masallaci mai alfarma  da kwadayin wurare na alheri da ibada  dalili ne na rayuwan zukata  kuma dalili ne na hasken zuciya da kuma lafiyan ta  Allah Madaukakin sarki ya ke cewa (Lallai kawai masu raya masallatan Allah su ne wadan da suka yi imani da Allah da ranar lahira  kuma suka tsaida salla  suka bada zakksa  ba su ji tsoron kowa  ba sai Allah  to, ya wuci wadannan su kasance cikin shiryayyu) Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi harama  daga zulhulaifa  ya fara talbiya  asaniyya  kusa daga makka  asaniyya kusa da makka taguwar sa ta durkusa wato alkasuwa wato ta kwanta taki ta tafi  daga wurinta   sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :-( Ba kin tafiya ta yi ba  kuma wannan ba dabi'arta ba ne sai dai akwai abin da ya  rike ta ne  wanda ya rike giwa ,)Buhari ne ya rawaito

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya tunkude daga  taguwarsa alkasuwa  yayin da aka tsarge ta ta yi tirjiya  da fadin sa cewa a'a wannan ba dabi'ar ta ba ne  wannan baya cikin halinta  domin ya bada hanzari ga dabba wanda yake ba magana take yi ba  sabo da sanin halin ta na asali  da kuma wato siranta mai kyau  domin ya koyar da al'umar sa darasi wurin mu'amala da  hukunci mai kyau bisa ga maukifi da aka samu  akai da kuma  cikin dauke  laifi da samar da uzuri da mutumin da yake da  wasu abubuwa da suke abun shaida na alheri  da falala a baya  Manzon Allah  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya tura Usman  Allah ya yarda  da shi da sako na musulunci  wato ita ce zaman lafiya ba kiyayya ba  ya basu labari cewa mu ba mu zo don yakan wani ba  Usmanu sai ya zo garin makka ya gayawa Kuraishawa  game da sakon Manzon Allah  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi cewa sun zo ne suna masu ziyaran dakin kaba  suna masu girmamawa da alfarmarsa da kuma dawafi da shi  sai suka ki , aka samu kai komo tsakanin Manzon Allah da kuraishawa  Annabi ya yi amfani da tausayawa  a cikin al'amura  da kuma dauke kai cikin abin da ba zai cutar da addini ba  wanda kuma ba zai bata sha'ani  na hakkin Allah ba Manzon Allah  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ke cewa (Na rantse da wanda raina yake hanun sa  ba za su tambaye ni wata khudda ba wanda suke girmamata  na alhurmomin Allah face na basu ita) Buhari ne ya rawaito .

Manzon Allah  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya rinjayar da  bangare na maslahan kare jinayen musulmai   da kuma  kubutar rayuka kuma yayi dubi zuwa ga karshen al'amari  a assasawa al'uma fikhu na manufa  da kuma gaya  ya kasance a makka a hudaibiyya  mutane dayawa daga cikin muminai  da kuma masu rauni daga maza da mata  da 'yan yara , da'ace  sahabbai sun shiga makka aka samu yaki a tsakani da ba wanda zai aminta da  ya kubuta  daga a taba shi  kamar yanda Allah mai tsarki da daukaka yake cewa :-(Kuma ba domin wadan su  maza muminai da wadan su mata muminai ba  ba ku sansu ba,  ku taka su  har wani aibi ya same ku daga gare su ba  ba da sani ba  (da Allah ya yi muku izinin yaki )

Amfanin sulhun ya bayyana  karara  da kuma fa'idoji na zahiri wanda  ya kasance karshen shi bude  garin makka da kuma musuluntar mutanenta  da shigan mutane addinin  Allah  tawaga-tawaga.

 Na daga cikin dubi zuwa ga makoma na al'amura kasancewan haji a wannan shekara  wani nau'i ne daban, an kebe shi da wani adadi iyakantacce da wasu ka'idoji  da aka shar'anta  a karkashin wannan yanayi na korona ,  da cutarwanta ya game komai  annobanta ya taba ko wani abu ,  wannan matakin mai hikima wanda    jagorori suka dauka  na mamlakar arabiyya saudiyya  ita ta dace wato tana cikin abubuwa da suke mafi muhimmanci  yana tafiya tare da manufofi na shari'a  kuma yana fadawa ne akan maslahan musulmai  wurin kiyaye rayuka da kuma tunkude duk wani abu da   zai ka ga hadari  wanda yake tabbatacce , ko kuma wanda aka fi  rinjayin zato akan shi  da kuma yin taka tsantsan  wurin yaduwar wannan annoba din  da kuma cututtuka  masu yaduwa.

 Tattaunawa da aka yi  ya haifar da  ittifaki da tarihi ya ambace shi  da sulhun hudaibiya  wanda sahabbai suka koma zuwa garin madina  ba tare da sun yi dawafi a dakin ka'aba ba  sai dai Allah ya girmama su ya  yalwata musu lada  ta inda ya yarda da su sai  yake cewa  hakika Allah ya yarda da muminai  ya yin da suke mubaya'a  a gare ka  karkashin bishiya shi ya san abin da ke cikin zukatan su  sannan ya saukar da natsuwa a gare su kuma  ya basu ladan budi a kusa,  da wannan ne zai bayyana wa musulmi  cewa idan yayi iya kokarin shi  ya yi iya abin da zai iya  wani abu ya yi shamaki tsakanin shi da ibada  don sauke wannan ibadan  to kada ya yi fushi kuma kada ya yi bakin ciki domin za a maida mishi abin da ya rasa  ladan shi kuma yana rubuce falalan Allah kuma yana da yalwa  an karbo daga Abdullahi Dan Abbas  Allah ya kara yarda a gare shi ya ce :- Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:-(Cikin abin da ya ke rawaitowa daga Ubangijin shi  mai tsarki da daukaka  lallai Allah ya rubuta kyawawa da munana  sannan ya bayyana haka  duk wanda ya nufi aikata kyakkyawa bai aikata ba to za a rubuta  mishi ladan shi cikakke   idan kuma ya nufi aikatawa sai ya aikata  to za a rubuta mi shi ladan shi guda goma  har zuwa  dari bakwai  zuwa ga ribi mai yawa  idan kuma ya himmatu da mummuna bai aikata ba to Allah zai rubuta mishi kyakkyawa guda cikakke,  I dan kuma ya himmatu da ita sannan ya aikata ta to  za a rubuta mi shi  mummuna guda daya) Buhari ne ya rawaito da muslim.

Madalla da irin wannan falala mai girma  wanda mai jinkai mai rahama ya ke kwaranyo da shi  zuwa ga bayin shi muminai  yayin da aka gama sulhu tsakanin Manzon Allah  da kuraishawa  Manzon Allah ya tashi sai ya ke cewa  ku tashi ku soke  abin yankan ku  kuma ku aske kawunan ku , ya fadi haka  har sau uku ba daya daga cikin su da ya tashi  sai wani alamomi na bakin ciki ya bayyana a gare shi  a zaton wasu daga cikin su wannan sulhun ci baya ne  sai ummu salma ta yi nuni  zuwa ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tace ya Annabin Allah kana so a yi hakan? To ka fita kada ka ka fadi ko kalma ga daya daga cikinsu, har sai ka soke rakuminka, ka kira mai askinka ya maka aski, sai ya fita bai yi wa kowa magana ba daga cikinsu ya aikata haka ya soke dabbarSa kuma  ya kira mai askinSa ya masa aski yayinda suka ga haka kowa sai ya tashi ya soke dabbarsa sai wannan yayiwa wannan aski wannan ma ya yiwa wannan aski har sashinsu ya kusa ya ti fada da sashi saboda bakinciki ) Bukari ne ya rawaito

Shawara mai zurfi daga ummu salama Allah ya kara yarda a gareta ga Annabi manzo wanda ya canga akwalar abinda ya faru na waki'I a wannan mawuyacin yanayi wannan maukifi da waninsa da yawa yana tabbatar da matsayi da daukaka irin na mace a musulunci da karrama musulunci gareta da kuma karfafanta ga sakon musuluncin lallai mace mai hankali mai tunani mai ra'ayi da ayyukanta na da dauri wurin sana'anta wato rayuuwa da gina shi da kuma habaka shi .

Ummu salama  Allah ya kara yarda a gareta ta raya da shawaranta daya daga cikin mafi rukunnai na tarbiyya abun koyi a aikace wanda ita ce mafi yawan amfani a dasa ginshiki kuma dabi'u da kuma gyara halaye .

Yana bayyana a sulhul hudaibiya kaunar sahabbai ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi wanda ba a kwatanta shi da kuma daukaka wanda ba irinsa , abin da ke nuni ga haka Urwa daya daga cikin jakadun kuraishawa zuwa ga Annabi  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi fadinsa ga mutanensa kaman yanda ya zo a cikin Buhari sai Urwa ya koma ga mutanensa sai ya ce ya mutane na: '' wallahi ; hakika naje wurin sarakuna naje ga kaisar da kisra da Najashi wallahi ni ban taba ganin wani sarki ba ko da su daya wanda mutanensa ke girmama shi kamar yanda mutanen Muhammadu da sahabban Muhammadu suke girmama shi ba wallahi in da zai fitar da majina to face sai ta fadi a tafin hanun daya daga cikinsu ya shafe a fiskansa da kuma fatansa , idan ya umarce su gaggawa suke yi don su aikata umarninsa idan ya yi alola suna dab da su yi fada da juna wurin ruwan alolansa, idan ya yi magana sai su sassauta muryansu gaba gare Shi ba sa iya daga ido su yi dubi zuwa gare shi saboda girmama shi lallai shi yabijiro muku da wata hanya ta shiriya to ku karbeta''. 

 

Huduba ta biyu :

             

Yayinda Suhailu dan amru ya zo don tattaunawa da Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ga jakadan kuraishawa manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sai ya ke cewa: (hakika al'amarinku ya saukaka) Bukari ne ya rawaito ,

Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi tafa'a'ul wannan abin nanatawan  musulmi a cikin al'amura masu jujjuyawa zai yi fatan alheri kuma ya kyautata zato ga Ubangijinsa a irin wannan yanayi na annoba muna kyautata zato ga ubangijinmu muna sakankancewa cewa lallai  yaye bakin ciki na tahowa bala'i kuma na gushewa kuma komi zai koma daidai iska a bigire mai tsarki ya kwanta ya tsarkaka ya yi dadi zukata su je su yi dawafi da jikunkuna a ka'aba sannan kafafuwa su taka su yi sa'ayi tsakanin safa da marwa ba da jimawa ba mu'munai za su yi farin ciki Allah Madaukakin sarki ya ce : (Hakika Allah ya gasgata ManzonSa da mafarki da suka yi na gaskiya cewa za ku shiga masallacin alharam in Allah ya so kuna cikin amunci kuma kuna masu aske kawunan ku kuna masu gajarta gashinku ba kwa tsoro).      

     


الخميس، 2 يوليو 2020

FALALAR SALATI GA ANNABI

اسم المترجم : أمين سعد عبد الله

اللغة : الهوسا

التاؤيخ : 26-10-1441هـ                                                                                                                            

 

Hudubar farko

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga wanda ya cike manzancin sama da shari'armu,ya sanya Annabinmu ya zama cikamakin Annabawa da Manzanni ya sanya al'umarmu ta zama tsaka – tsakiya kuma mafi alherin al'uma da  a ka fitarwa mutane, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya, yana halittan abin da ya so  ya kuma zaba, na shaida Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne  Al Musdafa Zababbe, daga cikin zababbun zababbu .

Ya shugabanci halittu ba ja ,  to shi ne bayyananne halittu na baya.

Annabin gaskiya wanda ya zo da gaskiya  mafificin halittu  kuma mafi kyaun su a dabi'u da halitta , kuma mafi fasahan su a wurin furuci.

Hakika ya isar da sako ya sauke nauyin amana kuma ya yi nasiha wa al'uma  ya yi jahada a tafarkin Allah cancancin jahadi har mutuwa ta zo mishi  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  da iyalan shoi da sahabban shi da wanda suka bisu  da kyautatawa har zuwa ranar sakayya .

 Bayan haka.

Bayan haka, lalle mafi alherin zance shine maganar Allah, kuma mafi alherin shiriya ita ce shiriyar Annabinmu Muhammad, kuma sharrin al'amura sune fararrunta, kuma dukkan bidi'a bata ce, kuma dukkan bata na wuta.

(Ya ku wadanda suka bada gaskiya ku ji tsoron Allah cancancin tsoronSa kada ku mutu face kuna musulmai)

Ya jama'ar musulmi!

Allah ya kan zabi Manzanni a cikin mala'iku da mutane,   hakika ya zabi Muhammad tsira da amincin Alla su tabbata a gare shi,  daga mafi tsada da kima na ma'adanai  kuma ya  girmama shi ya fifita shi akan sauran mutane ya sanya shiryarwar sa  shi ne ma'auni na fifiko kuma da kiyasi  bai bata ba , kuma bai ketare  haddi ba ,  kuma baya yin magana daga son zuciyar sa , (maganarsa)  bata zamo ba , face wahayi ne da ake aikowa, (mala'ika) mai tsananin karfi  ya sanar da shi ,  Ma'abucin karfi da kwarji sa'annan ya daidaita .

 Allah ya tsiratar da dan -adam ta dalilinsa  daga duhun shirka, da kudurkumin jahilci  da zurfin duhu, daga kuma tabarbarewan halaye da  dabi'u , da juyawar fidira  da kekkecewa  da radadi da zunubai da karkasuwa , sai ya kasance mai kwadayin shiryar da mu da tseratar da mu  da kuma samun walwalar mu Allah Madaukakin sarki ya ce :- (Lalle ne hakika Manzo daga cikin ku ya je muku .  abin da kuka wahala da shi mai nauyi ne a kansa. Mai kwadayi ne sabo da ku. Ga muminai mai tausayi ne,  mai jin kai .)

An karbo daga Abdullahi dan Amr dan As Allah ya kara yarda a gare shi cewa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya karanta fadin Allah a cikin sha'anin Ibrahim (Ya Ubangiji lalle su dinnaan sun batar da dewa daga cikin mutane  duk wanda ya bi ni to lallai shi, yana tare da ni )

Isa alaihissalam  ya ce :- (In za ka azabtar da su to bayin ka ne in kuma za ka gafarta musu to kai mabuwayi ne mai hikima ) sai Manzon Allah ya daga hannayen sa sai ya ce:- (Ya Allah al'uma ta  al'umata) sai ya yi kuka  sai Allah mabuwayi da daukaka ya ce ya Jibrilu tafi zuwa ga Muhammad ka ce  lallai mu za mu yardar da kai game da sha'anin al'umar ka  ba za mu musguna  maka ba)

An karbo daga Jabir  Allah ya kara yarda a gare su, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :-(Misali na da misalin ku kamar misalin  mutum ne ya kunna wuta  sai  kwari da fari suka rinka kokarin fadawa a cikin ta , shi kuma ya na kokarin tare su daga gare ta  to ni ina kokarin katange ku ne daga wuta  alhali ku kuma kuna kokarin ficewa daga hanuna ) Muslim ne ya rawaito

Na daga cikin bada kulawarsa ga al'umarsa akwai adana musu adu'arsa da yayi  a ranar  da mutum zai gujewa dan'uwansa da mahaifiyarsa da mahaifinsa, da matarsa da yaransa, kowane mutum a wannan rana da shanin da ya ishe shi.    An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi cewa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  yace : ( ko wani Annabi na da adu'a karbabbiya, to ni na adana nawa don nemawa Al'umata ceto , za a bada ta in sha Allahu ga duk wanda ya mutu cikin al'uma ta bai hada Allah da wani). Tirmizi ne ya rawaito.

 


 

Ya ku bayin Allah!

Hakika Allah ya umarce mu da mu sakawa duk mutumin da ya kyautata mana, sai yace : (shin akwai wani abu ga sakayyar kyautatawa face  kyautatawa).

(To duk wanda ya yi muku wani alheri to ku kyautata masa).

Ku saurara! lalle na daga cikin hakkin Annabinmu Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da ya ke kan mu shine mu saka masa bisa kyautatawarsa gare mu, da falalarsa da ke kan mu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, to yin salati a gare shi na daga cikin mafi girman hanyar tsira. Da kuma sadarwa mafi kima, da kusanci mafi girma da da'a mafi tsarkaka. Kuma yana cikin mafi girman abin da mutum zai raya lokuta da shi. A ribanya kyawawa da shi, a daga darajoji da shi, a kankare laifuka da shi, a yaye bakinciki da bacin rai da damuwa, tare da ribin gomomin salati daga Allah.

AlHaitami yace hadisi ne mai daraja ta biyu wanda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : ( Ba wani bawa da zai tuna ni sai ya min salati face  Allah ya rubuta masa kyawawa goma ya kankare masa laifuka goma, ya kuma daga daraojinsa guda goma.

An karbo daga Ubayyu dan ka'ab Allah ya kara yarda a gare shi ya ce: na ce ya Manzon Allah  ni ina yawaita salati a gare ka kamar nawa ne zan sanya na daga salati na ? sai ya ce:- '' iya abinda ka so'' sa ya ce: '' kamar rubu'i daya bisa hudu yayin da ka so  idan ka kara akan haka to, ya fi alheri a gare ka  , sai na ce kamar rabi fa sai ya ce : '' iya yanda  ka so idan ka kara akan haka ma  ya fi alheri a gare ka  sai na ce to zan yi biyu bisa uku  sai ya ce ka yi iya yanda ka so idan ma  ka kara akan hakan alheri ne a gare ka  sai naq ce to,zan sanya salati na gaba daya a gare ka ,  sai ya ce  : - '' to in dai haka ne za a dauke damuwan ka  a yafe ma zunuban ka  Tirmizi ne ya rawaito kuma ya ce hadisi ne mai daraja na biyu).

Ya ku jamaa'ar musulmi:

 Lallai Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi shi ne mafi karamcin  mutane , Allah ya hada imani da shi da imani da  kansa da biyayya gare shi da kuma biyayya ga kansa  da kaunar sa da kaunar Allah  da ambaton  Allah da ambaton sa , shaidawa na tauhidi  shi ne  daya daga cikin alamomi masu girma na musulunci ,  adireshin  imani  kuma shi ne ramzin  zaman lafi  kuma jumla na kiran salla ana maimaita shi a  wurin kiran salla a ko wani rana bisa kunnuwa  na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah na shaida Annabi Muhammad Manzon sa ne  imani ba ya kulluwa da daya daga cikin  shahada guda biyu sai an hada  ta da daya  sabo da haka ya wajaba a gare mu da shari'a na Allah da kuma hakkin sa  da ke kan mu  da kwadayin sa bisa  siran mu  da mu cika zukatan mu  da kaunar sa  da kimanta shi da girmama shi  da bin sunnar sa da tafarkin sa  .

Ku saurara lallai ne  yana daga cikin babbar  alama ta kaunarsa    da kuma wajibi na hakkinsa da sunnarsa da yake mafi karfi  da da'a ga Ubangijinsa   yawaita salati a gare shi (lallai Allah da mala'iku suna salati ga Annabi,  Ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi da aminci tabbatacce ) .

To ya bayin Allah : Ku yawaita salati ga Manzon Allah  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ku motsa harsunan ku da shi  ku danyaya labban ku da shi .

Ya bayin Allah:  lallai Allah  hakika ya ribanya  ladan salati ga Annabi  ya girmama ma'abotansa da masu yin sa. An karbo daga Abu  Dalha Al-ansari Allah ya kara yarda a gare shi ya ce ( Manzon Allah ya wayi gari wata rana  zuciyan sa tsarkake cikin dadin rai ana gani a fiskan sa da walwala sai suka ce ya manzon Allah yau ka wayi gari cikin annashawa a cikin dadin rai  ana ganin haka a fiskarka sai ya ce :- haka ne  wani mai zuwa ya zo min daga wurin Ubangiji na mabuwayi da daukaka sai ya ce duk wanda ya ma salati guda a cikin al'umarka  , to Allah  zai rubuta mishi kyawa guda goma da ita kuma zai goge mishi  guda goma na laifuka da ita  zai daga darajojin shi guda goma kwatankwacin su.)

  An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara mishi yarda  ya ce Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a garew shi ya ce:- (Mafi dacewan mutane gare ni  ranar alkiyama shi ne wanda yafi  yawaita min salati )  

Ku raya zukata ya ku bayin Allah da ambaton sa  ku yi salati a gare shi don bin umarnin Allah  da koyi da sunnarsa da wafa'I da hakkin sa  da kusanci zuwa ga  Allah da girmamawa  da kauna da girmamawa ga Manzon Allah tsira da amincin  Allah su tabbata a gare shi  da kari wurin kyawawan ayuka da kuma kankare laifuka .

Ina neman tsarin Allah daga sharrin shaidan abin jefewa (lallai Allah da mala'iku suna salati ga Annabi,  Ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi da aminci tabbatacce mai yawa.

HUDUBA  TA BIYU

 Dukkan yabo da godiya sun tabbata  ga Allah Ubangijin talikai wanda ya turo cikin ummiyyai  Manzo a cikin su wanda yana karanta musu ayoyin sa  kuma yana tsarkake su yana sanar da su littafi  da hikima ko da da can sun kasance kafin  haka cikin bata bayyananne .

Ya ku taron Musulmi:

Lallai yana daga cikin mafi tsadan adu'o'i da  zikiri kayan ado mafi haske  shi ne yawaita salati da aminci ga Annabi zababbe  a safiya da maraice  da hantsi da yammaci  ana yinta ne ga masu kauna  alama ce wata sima ce  wata shi'ar ne kamar a ranar Juma'a domin shi ne mafificin ranaku  , an karbo  daga Aus dan Aus Allah ya kara yarda a gare shi  ya ce Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :- (lallai na daga cikin mafificin ranakun ku shi ne ranar juma'a  a ciki ne aka halicci Adamu  kuma a ciki ne aka dauki ransa  a ciki ne kuma za a yi busa  a ciki ne kuma za a yi tsawa  to, ku yawaita salati a gare ni , domin salatin ku ana bijiro min da ita  Abu Dauda ne ya rawaito Albani ya  kyautata shi)

Duk wanda yake son Allah ya yabe shi kuma ya  girmama shi  kuma ya daukaka shi ya kambama shi  Mala'iku masu daraja   su ambace shi  a daga ambaton shi da darajojin shi da kuma matsayin shi to ya yawaita salati ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a ko wani yanayi  da ko wani lokaci da sauran ranakunsu , musamman idan ya zo wurin ambaton shi a magana ne . An karbo daga Aliyu dan Usaini daga Baban sa  cewa Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce  :-  (lallai mai rowa shi ne wanda aka ambace ni a gaba gare shi bai yi salati a gare ni ba Tirmizi ne ya rawaito )

Ya ku bayin Allah:

Lallai salati ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  kusanci ne ba tare da kaidi  da lokaci ko kuma wuri ba, sai dai  tana wajabtane a  wasu lokuta daga ciki akwai  lokacin da aka ambaci sunan shi  a harshe  ko kuma lokacin da ka ji ya yin kiran salla. An karbo daga Abdullahi dan Amru dan As  cewa ya ji Manzon Allah tsira  da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa  (idan kun ji mai kiran salla na kiran salla to ku fadi abin da ya ke fada ,  sannan ku min salati ,    duk wanda ya min salati Allah zai mishi salati da ita guda goma  sannan ku nema min wasila  domin wani matsayi ne a aljanna domin  bata dace ba ga kowa sai wani bawa daga cikin bayin Allah  ina fata kuma in kasance ni ne shi  wanda ya roka min wasila  to cetota ta tabbata a gare shi   Muslim ne ya rawaito)

 

An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara mi shi yarda  ya ce Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :- ( Hancin shi ya dumbuli kasa duk mutumin da aka ambace ni  bai yi salati a gare ni  ba Tirmizi ne ya rawaito.

Ya ku bayin Allah:

Yin salati ga Annabi yana zama dole a wurare da dama daga ciki akawai  tahiyan karshe ,da  yayin shiga masallaci,  da kuma yayin fita daga gare shi  da yin adu'a da kuma  yayin musiba  na bakin ciki da yayin haduwa  da mutane  da taruwan mutane da kuma  tsakanin kabbarori na idi , da bayan kiran ladani, da wasu wurare daban da ba wannan ba  da lokutan da aka samu ya zo daga sunna .

Ya ku bayin Allah!

Salati ga Annabi na yiwuwa da ko wace siga aka yi, da kuma kowace jumla aka hada shi, sigogi daban- daban sun zo kuma dukkansu suna isarwa ga abin bukata, kuma sun gamsar wurin salati ga Annabi abin kauna,

    An karbo daga Abu Mas'ud Al0Ansari Allah ya kara mi shi yarda  ya ce Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya zo mana muna majlisar sa'ad bin Ubada, sai Bashir bin Sa'ad ya ce :Allah ya mana umarni da mu maka salati ya Manzon Allah, to yaya za mu maka salati? Sai ManzonAllah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi shuru har muka yi fatan ina ma da baa tambaye shi ba, sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace :  ku ce ya Allah ka yi dadin tsira ga  Muhammad da iyalan Muhammad, kamar yadda ka yi dadin tsira ga iyalan Ibrahim ka yi albarka ga Muhammad da iyalan Muhammad kamar yadda kayi albarka ga iyalan Ibrahim a cikin talikai,  kai abin godewa ne kuma abin girmamawa, shi kuma sallama shi ne kamar yadda kuka sani )   

 

  An karbo daga Abu Humaid Assa'idi  cewa sun ce ya Manzon Allah, yaya zamu  yi salati a gare ka sai ya ce ku ce:- '' Ya Allah ka yi dadin  tsira ga Muhammad da matayen sa da zuri'ar sa ,  kamar yanda kayi dadin tsira ga iyalan Ibrahim ka sa albarka ga Muhammad da matayen shi da zuri'ar shi , kamar yanda ka sa albarka ga iyalan Ibrahim lallai kai abin godiya ne abin girmamawa .)

 Ya ku masoya ga manzon Allah :

Lallai salati ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi na da faidoji da basa kididdiguwa suna da kuma tasiri da amfani da ba a iya iyakance su, a ciki akwai maslahohi na duniya da lahira wanda ba a  iya kwalkwale su  a duk lokacin da masoyi ya yawaita ambaton abin kaunarsa da halarto da shi a zuciyarsa da bijiro da kyawawan sa  da ma;anonin sa masu janyo kaunarsa , sai son ya ribanya , sai shaukinsa kuma ya karu  hakan sai ya kasance abu ne mai karfafa guiwa  zuwa ga binsa  , ba abin da ya fi kawo sanyin ido ga masoyi kamar ganin abin kaunarsa, ba abinda ya fi kawo mishi kwaciyar zuciya  kamar ambaton shi da halarto  da kyawawan sa .

Kuma duk lokacin da mutum ya juya baya daga ambaton sa sai kaunar sa ya ragu daga zuciyarsa.

Sa'annan ku sani  cewa salati ga Annabi tsira da amincin  Allah su tabbata a gare shi  kusanci ne da  da'a  da ake bijiro da shi gare shi  ku yi fatan su kasance sun dace da manhajinsa wurin bi ,  ku yi nesa daga wuce gona da iri da bin son rai da kirkiran bidi'o'i,  duk wanda ya yi wani aiki wanda babu umarnin mu  a ciki to an maida mishi.        

   

 

 

 


 


 

 


 

 

 


 

 


 

 


 

 


 

 


 


الأربعاء، 1 يوليو 2020

NI'IMA TA LAFIYA

اسم المترجم : أمين سعد عبد الله

اللغة : الهوسا

التاؤيخ : 5-11-1441هـ

Hudubar Juma'a a masallacin Annabi na Shaikh Husaini Al-Assheikh

Mafi girman ni'imomin duniya ita ce ni'imar lafiyan jiki, ba wata  ni'mar da ta ke daidai da ita na daga cikin ni'imomin duniya  duk yanda ta yi dadi , Allah ya azurta mu gaba daya da lafiya da waraka saboda haka ne ba wanda ya san dadin lafiya sai wanda ya dandani dacin cututtuka da rashin lafiya Allah ya kare mu da ni da ku daga su Manzon Alla tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Ni'imomi guda biyu mutane na hasara a cikinsu, shi ne lafiya da kuma zaman banza)Buhari ne ya rawaito

'yan uwa a musulunci :

Mai samun farin ciki, wanda aka datar da shi , shi ne wanda ya san ni'ma yayin samuwanta ya kuma tashi da hakkin ta , ya kuma ji kimanta a jikin shi , mafi wajabcin godiya ga ni'ma na lafiya shi ne ka hakabata ya kai musulmi wurin da'a ga Allah na sauke wajibabbu da kiyayewa bisa ga umarce umarce, da yin nesa daga bakaken abubuwa da mununan laifuka , da gaggautawa zuwa ga ayyukan nafilfilu da kuma ayyuka na kwarai Allah Madaukakin sarki ya ce:(ku yi gaggawa zuwa ga gafara daga Ubangijinku da aljanna wanda fadinta ya kai sammai da kasa an tattaleta ga masu tsoron Allah),

Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ke cewa (ku gaggauta da ayyuka kafin abu guda bakwai, shin akwai abin da ku ke jira ne face talauci abin mantawa? Ko wadata abin da ke sa dagawa?, ko kuma rashin lafiya da ke yin barna?, ko tsufa da ke kararwa? ko kuma mamaci abun shiryawa?,ko kuma dajjal? to sharrin abin da ya ke boye da ake jira ko kuma tashin alkiyama? kuma tashn alkiyama shi ya fi tsanani shi ya fi daci)Tirmizi ne ya rawaito kuma ya ce hadisi ne hasan .

'yan uwa na musulunci :

Musulmi a  ko wani halin da ya ke ciki yana cikin alheri ne mai girma da lada mai yawa a duk lokacin da ya yi ikilasin niyarsa ga Allah ya yi gaskiya a wurin biyayyan sa , duk wanda aka jarabce shi da rashin lafiya ya yi hakuri ya nemi lada to hakan zai zamo mishi daukaka ne a darajojin shi kuma da kankara ne ga laifukan shi , Allah Madaukakin sarki ya ce : (hakika za mu jarabe ku da wani abu na tsoro da yunwa da tawaya na daga dukiya da rayuka da 'yayan itace ka yi albishir ga masu hakuri) (wadanda idan musiba ta same su sai su ce lallai daga Allah mu ke kuma gare Shi za mu koma) (wadannan suna da kyakkyawan ambato daga wurin ubangijin su kuma da rahama kuma wadannan su ne shiryayyu) , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:(ba wata musiba da zata samu musulmi na rashin lafiya ne ko wani abu koma bayan haka face Allah ya kankare mishi laifukan shi kamar yanda ganyen itace ta ke karkadewa diga itaciya) Muslim ne ya rawaito.

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya shiga wa Ummussa'ibsa ya  ce :(mai ke gare ki ne ya ummussa'ib kina karkarwa ? sai ta ke cewa zazzabi ne , kar Allah ya mata albarka sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : kar ki zagi zazzabi domin tana tafiyar da kusakuran bani a'adama kamar yanda zugazugi ke tafiyar da kazantan karfe) Muslim ne ya rawaito.

Na daga cikin mafi girman ni'imar Allah cewa Allah yana gudanar da lada ga bawa mai  rashin lafiya irin ladan aikin da yake yi a halin yana mai lafiya, kamar yadda ya zo a sahihul Buhari Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shiya ce :     (Idan bawa ya yi rashin lafiya ko tafiya to Allah Madaukaki zai  ci gaba da rubuta masa ladan aikin da ya saba yi a halin yana da lafiya mazaunin gida).

                                                                                                                          Ka sani ya kai wanda a ka jarabta da rashin lafiya  Allah na kusa da bawanSa to ka nemi mafaka a gare shi, ka roke shi waraka da lafiya kana tsayuwa a kan sabuba na jinya wadanda su kansu suna cikin hakikanin  dogaro ga Allah Mabuwayi da daukaka, da Allah ne kadai bakin cikinka ke yayewa kuma cutarka ta tafi ( kuma idan na yi rashin lafiya to shi ke warkar da ni).      

Ka kasance bisa yakinin rahamar Allah da falalarSa, kuma shi ne Mai warkarwa kuma Isasshe,  ( kuma lalle tare da tsanani akwai sauki. To kuma lalle tare da tsanani akwai sauki)


 

Huduba ta biyu

Duk yadda dan adam ya kai da karfi da bunkasa da tunbatsa a fagen ilimi to fa sifa ta rauni na damfare da shi, Allah Madaukakin Sarki ya ce ( kuma ba a baku wani abu na ilimi ba face kadan). Kuma Mai tsarki yace : (Kuma an halicci mutum da rauni).

To cikakken  Karfi na hakika sifa ne ga Allah  Alkawiyyu Al Matin Mamallakin dukkan komai bisa hakika, Mai gudanar da al'amura kuma Mai tunkude su, kowani abu na faruwa ne da hukuncinSa da kaddararSa. Kuma karkashin gudanarwarSa da ganin damarSa (Mashi'arSa)  ( Ya ku mutane ku talakawa ne zuwa ga Allah, kuma Allah shi Mawadaci ne Abin godiya).  

To mu yi kokari wurin bauta masa, mu kafu wurin masa biyayya kuma mu kankan da kai a gare shi mu nemi mafaka daga bangarenSa. Allah Madaukakin Sarki yace :( ku tuba zuwa ga Allah Ya ku wadanda suka yi imani ko zaku rabauta)