السبت، 13 يونيو 2020

Allah Abin godiya

                                                                                                     

ترجمة الخطبة

اسم المترجم :أمين سعد عبد الله

اللغة : الهوسا

التاريخ : 6-10-1441هـ

 

Hudubar Juma'a a Masallacin Annabi Na shaikh Ahmad Dalib 6/10/1441AH/29/5/ 2020AC

Hudubar farko

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah muna gode masa kuma muna neman taimakonsa da gafararsa, muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu, da munanan ayyukanmu, duk wanda Allah ya shiryar da shi babu mai batar da shi, kuma duk wanda ya batar babu mai shiryar da shi, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, na kuma shaida Annabi Muhammad bawanSa ne kuma manzonSa ne. tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa da aminci tabbatacce.

(Ya ku wadanda suka bada gaskiya ku ji tsoron Allah cancancin tsoronSa kada ku mutu face kuna musulmai)

(ya ku mutane ku ji tsoron Allah wanda ya halitta ku daga rai guda kuma ya halitta matarsa daga gare shi ya yada daga gare su mazaje masu yawa da mata, ku ji tsoron Allah da ku ke roko da (sunan) shi. Da zumunci, lalle Allah ya kasance mai tsaro ne a kan ku.)

(ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah ku fadi zance na daidai. zai gyara muku ayyukan ku kuma ya gafarta muku zunubanku, duk wanda ya ke yi wa Allah biyayya da ManzonSa to ya rabauta rabauta mai girma.)

 

Bayan haka, lalle mafi alherin zance shine maganar Allah, kuma mafi alherin shiriya ita ce shiriyar Annabinmu Muhammad, kuma sharrin al'amura sune fararrunta, kuma dukkan bidi'a bata ce, kuma dukkan bata na wuta.

Lalle ni ina muku godiya ga Allah Ubangijin talikai. Mai rahama Mai jinkai.Mai mulki ranar sakayya.

(Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya halicci sammai da kasa, kuma ya sanya duhu da haske, sannan wadanda suka kafirta suna karkacewa Ubangijinsu).

(Wanda ya saukar da littafi ga bawanSa bai sanya karkata ba gare shi.madaidaici domin ya yi gargadi da azaba mai tsanani daga gare shi. Kuma ya yi albishir ga muminai wadanda suke aikata ayyuka na kwarai da (cewa) suna da wata lada mai kyau. Suna masu dawwama a cikinta har abada).

(Wanda bai riki da ba. Kuma bai da abokin tarayya, kuma bai da wani majibinci da zai taimake shi daga walakanci).

 (wanda yake abin da ya ke cikin sammai da kasa nasa ne.godiya tasa ce a lahira, kuma shi Mai hikima ne Mai labartawa. Ya san abin da yake shiga cikin kasa da abin da ya ke fitowa daga gare ta, Shine Mai rahama Mai gafara).

(Wanda ya fari halittan sammai da kasa,Mai sanya mala'iku manzanni masu fukafukai bibbiyu da uku-uku da hurhudu, yana kara abin da yaso cikin halittar, lalle Allah Mai iko ne ga dukkan komai).

(Wanda ya sanya muku kasa tabbatacciya, da sama ginanniya kuma ya suranta ku, sa'annan ya kyautata surorinku, kuma ya azurta ku daga abubuwa masu dadi. Wancan shine Allah Ubangijinku, albarkar Allah Ubangijin talikai ta bayyana.(Shine rayayye ba abin bautawa face shi, ku kira shi kuna masu tsarkake addini a gare shi, Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu).

   To yabo da godiya sun tabbata ga Allah,wanda ya ke ciyarwa ba a ciyar da shi, ya mana baiwa sai ya ciyar da mu ya shayar da mu, dukkan wani abu mai kyau na jarabawa Allah ya mana.

Godiya ga Allah ba irin na mai bankwana, ko wanda ake sakawa ba ko mai butulcewa ba ko kuma wanda ya wadatu daga gare shi ba Ubangijinmu.

Godiya tasa ce bisa halittanmu da azurta mu da shiryar da mu da yayi, godiya gare shi bisa ilmantar da mu da ya yi, ya kuma tseratar da mu ya yaye mana bakinciki, ya bamu mafaka, godiya gare shi bisa imani, godiya gare shi bisa musulunci, godiya gare shi bisa Alkur'ani. godiya gare shi bisa iyalai da dukiya da waraka, ya wulakanta makiyinmu ya yalwata mana arziki ya bayyana amincinmu ya hada rarrabarmu,ya kyautata samun lafiyarmu, kuma ya bamu dukkan abin da muka roke shi to dukkan yabo da godiya na shi ne mai yawa mai tsarki mai albarka a cikinsa kamar yadda Ubangijinmu ya ke so kuma ya yarda.

(Sabo da haka godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin sammai kuma Ubangijin kasa, Ubangijin halittu. Kuma gare shi ne girma ya ke a cikin sammai da kasa, kuma Shi ne Mabuwayi Mai hikima). Dukkan yabo da godiya ta sa ce kamar yadda muke fadi, dukkan yabo da godiya ta sa ce sama da yadda muke fadi, dukkan yabo da godiya ta sa ce har sai ya  yarda, dukkan yabo da godiya ta sa ce har bayan  yarda, kuma godiya tasa ce a farko kuma godiya tasa ce a karshe, kuma godiya tasa ce a bayyane kuma godiya tasa ce a boye, kuma dukkan godiya tasa ce a kowane hali, Mai girma Madaukaki.

Ya samar da mu kuma ya tattale mu ya taimake mu,to godiya tasa ce, ya datar da mu ya fahimtar da mu ya mana ilhama, to godiya ta tabbata a gare shi,ya shaidar da mu kuma ya shiryar da mu ya sanya mana walwala, to godiya ta tabbata a gare shi.

Ya tsaida mai shaidar rahama cikinmu sai ya kubutar da mai lafiya ya warkar da mara lafiya, ya zabi wanda ya kai ga ajalinsa cikinmu zuwa kusancinSa. Ya katange zukata daga firgici da gazawa da kwadayi.

ya bibiye mu da yalwan falalolinSa, bai muamalance mu da tsagoron adalcinsa ba, ya isar da mu zuwa watan ramadan ya jiyar da mu alkur'ani daga kwarin daki mai alfarma da kusa da raudan abin girmamawa.ya tsaida wanda ya so a cikin su daga bayinSa a matsaya na salihai masu azumi da tsayuwa da tilawa da ambato da tadabburi da tafakkuri da tuntuntuni da godiya, kebantar da su ya tabbata fatan ka sa su cikin kebabbunka.

Allah ya yawaita mana juma'o'i a cikinsa ya bibiyar da alherori a cikinsa ya kwarara mana albarkokin sama, sannan Allah ya cika mana da kammaluwan ranakunsa da dararakinsa, da halartan girmama Ubangijinmu. Da daukaka daren ja'izozi da wayan garinsa da taimakonsa ga shan ruwa da da buda baki da cin abinci, to godiya ta tabbata a gare shi.

 Godiya ta tabbata a ga Allah da ya nunawa musulmai alheri mai yawa a kansu sau da yawa aka kammala karatun Alkur'ani a gidaje, raka'o'i da dama an sallata a dakuna, littafi mai amfani nawa aka karanta,darusa nawa aka yada su kuma suka amfanar kuma wa'azuzzuka nawa ne aka yada su ta gidajen radiyo suka fadakar.

Godiya ta tabbata ga Allah da ya bayyana boyayyen imani daga gurin da aka manta shi, kur'anai da dama an kaurace musu sai gasu an fito da suka ga haske,zukata nawa ne suka kakashe sai ga su sun lausasa, idanuwa nawa ne da suka bushe sai gasu suna zubar da hawaye, rayuka nawa ne suka saba sai gasu sun hada kai, mutum nawa ne suka juya wa juna baya sai gasu sun fiskanto juna, ruhi nawa ne suka yanke zumunci sai gasu sun sadar,

Godiya ta tabbata  ga Allah da ya sanya musulmai a cikin miskinai kamar Ansar a cikin Muhajirun, wadanda suka bayar da masauki suka yi taimako, suka karfafe su suka karbe su kuma suka yi shafa'a suka bada shafa'a. suka tattaro suka rarraba, suka ciyar suka fifita, arziki nawa suka raba,da basuka da aka biya, mata nawa ne da suka rasa  mazajensu suka rufa musu asiri, marayu nawa aka dau nauyi, bukatu nawa aka biya, kwanukan abinci nawa aka shimfida, tafuka nawa aka hana roko, gidaje nawa ne aka cika su da alheri,basu kasance da su kauracewa sunnonin Manzon Allah ba ko su bar koyarwarsa  ba, gari mai kyau tsirransa na fita da izinin Ubangijinsa.

Godiya ta tabbata ga Allah da ya nuna mana tausayi irin na jagora da nasiha irin na mataimaki, da shiryarwa irin na alami,da agazawa na likita,da kulawa irin na mai tsaro, da tausayi irin mai nasiha, da daukaka kiran sallah, da walakantuwa irin na fajirci da fasikanci da sabo.

Godiya ta tabbata ga Allah da ya shafe mu da rinjaye irin nasa.sabo da horarwa, ya zartar da ludufi na kudurarSa a cikinmu domin ladabtarwa, da ya so da ya kama mu da fushinSa ya azabtar da mu azabtarwa. (kuma da Allah yana kama mutane saboda abin da suka aikata, da bai bar wata dabba ba a kanta(kasa) amma yana jinkirta musu zuwa ga ajalin da aka ambata, sa'anan idan ajalin su ya zo to lalle Allah ya kasance Mai gani ga bayinSa).

             (To shin  kuna fatan idan kun juya (daga umarnin)  za ku yi barna a cikin kasa kuma ku yanke zumuntan ku )

Shin ya wuci idan kun samu dama da ku yi barna a  bayan kasa ,   ku watsar da littafin Ubangijin ku  a bayan bayan ku ! shin kuna fatan idan kun samu aminci da ku yi barna a doron kasa kuma ku aminta da makirci na Ubangijin ku  shin kuna fatan idan kun bayyana da ku yi barna a doron kasa  kuma ku bi soye-soyen rayukan ku, shin kuna fatan  idan kun sauka kasuwannin ku da kuma makwancinku,  da ku bayyana abin da aka ki ku bi sha'awe-sha'wen ku! Shin kuna fatan idan  mai kiran sallan ku idan ya kira salla da ku yi barna a doron kasa! Ba za ku amsa zuwa ga abinda zai rayar da ku ba .

YA KU BAYIN ALLAH :

Idan kun tsoraci talauci to ku nemi wadata cikin talakawan ku, idan kun tsoraci galaba to, ku nemi taimako cikin  masu raunin ku , domin da su ne ake azurta ku kuma ake baku nasara , da zaluntan su kuma da fin karfin su da'ira take juyawa akan ku  sa'annan ayi galaba akan ku   a rinjaye ku .

Zaku sulale daga shari'a ne a sadade  idan musiba ta sauka sai  ku ce daga ina ne wannan! (Ka ce shi daga wurin kawunan ku ya  ke lalle Allah mai iko ne ga dukkan komai )

Ku sani lallai izza na cikin da'a , kaskanci kuma na cikin sabo

(Wanda ya kasance yana son daukaka to daukaka a wurin Allah ne yake  gaba daya zuwa gare shi magana mai dadi ke hawa , kuma aiki na  kwarai yana dauka ta ,  kuma wadan da ke yin makircin munanan ayuka  suna da wata azaba mai tsanani  kuma makircin wadannan yana yin tasgaro ).

(Izza na Allah ne da Manzon shi da muminai sai dai munafukai ba su sani ba )  

Ba makawa  a samu mai shaida a halittu bisa kalmar gaskiya ,  cikin  ma'abota rarrabuwa da ,munafunci , sai su ambaci irin jinsin fadin masoyan su na daga kafurai da mushirikai , (Hakika cututtuka da sauki  sun shafi iyayen mu) har su yardar da rayukan su shakiyyai  kame da ayukan su masu halakarwa , sai wasu mutane su riske su -muna neman tsarin Allah daga halin su  sun yi alkawari da Allah a lokacin cuta to idan ya yaye azaba sai su saba alkawarin ,  (Sai ya biyar mu su da munafunci a cikin zukatan su  har zuwa ga ranar da su ke haduwa da shi  sabo da sabawa Allah ga abin da suka yi masa alkawari, kuma sabo da abin da suka kasance suna yi na karya shin  ba su sani ba cewa lalle ne Allah yana sanin asirin su da ganawan su Kuma lalle Allah ne  Masanin abubuwan fake?  ) (Ka da ranka ta tafi zuwa gare su kana mai hasara ) ( Kada ka yi bakin ciki a gare su kuma  kar ka kasance cikin kunci bisa abin da suke yi na makirci , lalle Allah  yana tare da wadan da suka yi takawa  , kuma yana tare da masu kyautatawa).

Amma ma'abota imani  sun gaskata  abin da suka alkawartawa  Allah a gare shi  a cikin su akwai wanda ya biya bukatan sa  akwai kuma wanda ya ke jira basu sanja ba .(Kuma da  wadan su, sunyi furuci  da laifin su sun hada aiki na kwarai da wani mummuna, akwai tsammanin Allah ya karbi tubansu, lalle Allah Mai gafara ne Mai jinkai ).

Suna cewa:-  (Ya Ubangijinmu mun zalunci kawunanmu to muddin ba ka gafarta mana ba ka jikanmu ba zamu kasance cikin hasararru)

Suna cewa :-(Ya Ubangijinmu ka gafarta mana zunubanmu da barnanmu a cikin al'amarinmu, kuma ka tabbatar da digadigan mu , kuma ka taimake mu akan mutanennan kafurai).

Suna cewa:- (Ya Ubangijinmu kar ka rike mu idan mun yi mantuwa ko kuskure, Ya Ubangijin mu  kuma kada  ka aza nauyi a kan mu kamar yanda ka aza nauyi akan wadanda suka gabace  mu .  Ya Ubangijin mu kada ka sanya mu daukan abin da babu iko gare mu  da shi, kuma ka yafe mana , kuma ka gafarta mana  kuma ka yi jinkai  a gare mu kai  ne Majibincinmu sabo da haka ka taimake mu akan mutanennan kafurai).

Misalin tawaga biyu kamar makaho da kurma   da mai gani da mai ji shin za su yi daidai ase ba za ku wa'azantu  ba (Godiya ta tabbata ga Allah sai dai mafiya yawan su ba su sani ba ..

 

 

   HUDUBA TA BIYU

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah kamar yanda ya dace da girman  fuskanSa  da kasaitan ikon sa  kuma  godiya na sa ne kamar yanda ya dace  da  yalwan afuwar sa  da kayun kayutatawanSa kuma kyakkyawan yabo na shi ne kamar yanda ya dace da girman rahamar sa da yalwan gafararSa.

Yana da godiya na har abada , godiyan da  adadi bai iyakance shi ,  kuma har abda ba zai katse shi ba , kamar yanda ya dace da a gode mi shi.

 Dukkan godiya na shi ne bisa ga ni'imomi  wanda ba sa kidanyuwa da da falalolin da  ba sa iyakantuwa , da kuma hukuncin da ba a maidawa , godiya na  shi ne bisa ga  rahamarsa wacce ta yalwaci dukkan komai na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah majibincin salihai, na shaida kuma shugabanmu Muhammadu bawan sa ne kumsa Manzon sa ne  shugaban masu takawa

(Ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah ku kasance tare da masu gaskiya ) ku tuna ni'imomin Allah  kuma ku tuna ranakun Allah  ku kiyaye ni'imomin ; ta hanyan da'a  wa Allah , kuma ku nemi karin su ta hanyan godewa Allah , ku dauki izina a cikin halittun Allah da kuma abin da aka nuna muku na daga ayoyin Allah , ba abin da ya fi zama wa'azi a gare ku kamar maganan Allah .

Allah yana cewa:- Ka ce: « Godiya ta tabbata ga A1lah, kuma aminci ya tabbata bisa ga bãyinSa, waɗanda Ya zãɓa. » Shin Allah ne Mafi alhẽri koabin da suke yin shirki da Shi?
60. Kõ wãne ne Ya halitta sammai da ƙasa kuma Ya saukar muku, daga, sama, wani ruwa, Muka tsirar, game da shi, gõnaki mãsu sha'awa, ba ya kasancẽwa gare ku, ku tsirar da itãcensu? Shin, akwai abin bautãwa tãre da Allah? Ã'a, sũ mutãne ne suna daidaitãwa ( Allah da wani ) .
61. Kõ kuwa wãne ne Ya sanya ƙasa tabbatacciya, kuma Ya sanya kõguna a tsakãninta kuma Ya sanya mata manyan duwãtsu tabatattu, kuma Ya sanya wani shãmaki a tsakãnin tẽkuna biyu? Shin akwai wani abin bautãwa tãre da Allah. Ã'a, mafi yawansu ba su sanĩ ba.
62. Kõ wãne ne yake karɓã , kuma ya sanya ku mamãyan ƙasa? Shin akwai wani abin bautawa tãre da Allah? Kaɗan ƙwarai kuke yin tunãni.
63. Kõ wãne ne yake shiryarwa a cikin duffan ƙasa da tẽku,kuma wãne ne Yake aikõwar iskõki dõmin bãyar da bushãra a gaba ga rahamarSa? Ashe akwai wani abin bautãwa tãre da Allah? tsarki yã tabbata ga Allah daga barin abin da suke shirki da Shi.

64. Kõ wãne ne yake fã ra halitta sa'an nan kuma ya mayar da ita,kuma Wãne ne Ya azurta ku daga sama da ƙasa? Ashe, akwai wani abin bautãwa tãre da Allah? Ka ce: « Ku kãwo dalĩlinku idan kun kasance mãsu gaskiya. »
65. Ka ce: « Bãbu wanda ya san gaibi a cikin sammai da ƙasa fãce Allah. Kuma bã su sansancẽwar a yaushe ne zã a tãyar da su. »
66. Ã'a, saninsu ya kai a cikin Lãhira Ã'a, sunã cikin shakka daga gare ta. Ã'a, sũ da gare ta makãfin zũci ne.
67. Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: « Shin idan mun kasance turɓaya, mu da ubanninmu, shin, haƙĩƙa, waɗanda ake fitarwa ne? »
68. « Lalle ne, haƙĩƙa, an yi mana wa'adi ga wannan, mũ da ubanninmu, daga gabãnin haka. Wannan bã kõme ba ne fãce tãtsũniyõyin farko. »
69. Ka ce: « Ku yi tafiya a cikin ƙasa, sa'an nan ku dũba, yãya ãƙibar mãsu laifi take? »
70. Kuma kada ka yi baƙin ciki a kansu, kuma kada ka kasance a cikin ƙuncin rai daga abin da suke ƙullãwa na mãkirci.
71. Kuma sunã cẽwa, « A yaushe wannan wa'adi ( zai auku ) , idan kun kasance mãsu gaskiya? »
72. Ka ce: « Akwai fatan sãshen abin da kuke, nẽman gaggãwarsa, ya kasance yã kuturta ( 1 ) a gare ku. »
73. Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa Mai falala ne a kan mutãne kuma amma mafi yawansu, bã su gõdẽwa.
74. Kuma lalle Ubangijinka, haƙĩƙa Yanã sanin abin da ƙirãzansu suke, ɓõyẽwa, da abin da suke hayyanãwa.
75. Kuma bãbu wata ( mas'ala ) mai bõyuwa, a cikin sama da ƙasa fãce tanã a cikin littafi bayyananne.
76. Lalle ne wannan Alƙur'ãni ( 2 ) yanã gaya wa Banĩ Isrãĩla mafi yawan abin da sũ suke sãɓa wa jũnansu a ciki.

77. Kuma lalle shi haƙĩƙa shiriya ce da rahama ga mũminai.
78. « Lalle Ubangijinka Yanã yin hukunci a tsakãninsu da hukuncinsa, kuma Shi ne Mabuwãyi, Masani. »
79. Sabõda haka, ka dõgara ga Allah, lalle ne, kai ne a kan gaskiya bayyananniya.
80. Lalle ne kai, bã ka jiyar da matattu, kuma bã ka sa kurãme su ji kiranka, idan sun jũya sunã mãsu bãyar da bãya.
81. Kuma kai ba ka zama mai shiryar da ɗimammu daga ɓata ba. Bã ka jiyarwa fãce wanda yake yin ĩmãni da ãyõyinMu. To, sũ ne mãsu sallamãwa ( al'amari zuwa ga Allah ) .
82. Kuma idan magana ta auku a kansu, Munã fitar musu da wata dabba ( 1 ) daga ƙasa, tanã yi musu magana, cẽwa « Lalle mutãne sun kasance game da ayoyinMu, ba su yin ĩmãnin yaƙĩni. »
83. Kuma a rãnar da Muke tãrãwa daga kõwace al'umma, wata ƙungiya daga waɗanda suke ƙaryata ãyõyinMu, sai ga su anã kangesu. ( ga kõra )
84. Har idan sun zo, ( Allah ) zai ce, « Ashe kun ƙaryata ãyõyinNa, kuma ba ku kẽwaye su da sani ba? To, mẽne ne kuka kasance kunã aikatãwa? »
85. Kuma magana ta auku a kansu, sabõda zãluncin da suka yi. To, sũ bã su da ta cẽwa.
86. Shin, ba su gani ba, cẽwa, lalle Mũ, Mun sanya dare dõmin su natsu a cikinsa, kuma da yini mai sanya gani? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi! Dõmin mutãne waɗanda suka yi ĩmãni.
87. Kuma da rãnar ( 2 ) da ake hũsa a cikin ƙaho, sai wandayake a cikin sammai da waɗanda suke a cikin ƙasa su firgita, fãce wanda Allah Ya so, kuma dukansu, su je Masa sunã ƙasƙantattu.
88. Kuma kanã ganin duwãtsu, kanã zaton su sandararru, alhãli kuwa sũ sunã shũɗẽwa shũɗewar girgije, bisa sanã'ar Allah wanda Ya kyautata kõwane abu. Lalle Shi, Mai lãbartãwa ne game da abin da kuke aikatãwa.

89. Wanda ya zo da kyakkyawan aiki guda, to, yanã da mafi alhẽri daga gare shi. Kuma sũ daga wata firgita, ( 1 ) a yinin nan, amintattu ne.
90. Kuma wanda ya zo da mugun aiki, to, an kife fuskõkinsu a cikin wuta. Ko zã a sãka muku fãce da abin da kuka kasance kũnã aikatãwa?
91. ( Ka ce ) : « An umurce ni, in bauta wa Ubangijin wannan Gari, ( 2 ) Wanda Ya mayar da shi Hurumi, kuma Yanã da dukan kõme. Kuma an umurce ni da in kasance daga mãsu sallamãwa. »
92. « Kuma inã karanta Alƙur'ãni. » To, wanda ya shiryu, yã shiryu ne dõmin kansa kawai. Kuma wanda ya ɓãce, to, ka ce: « Ni daga mãsu gargaɗi kawai nake. »
93. Kuma ka ce: « Gõdiya ta tabbata ga Allah. Zai nũna muku ãyõyinSa, har ku sansu. » Kuma Ubangijinka bai zama Mai shagala daga barin abin da kuke aikatãwa ba.


Sunan Allah "Al-Hakim" Mai Hikima

اسم المترجم : أمين سعد عبد الله

اللغة  : الهوسا

التاريخ : 13/10/1441هـ

 

 

Hudubar Masllacin Annabi na SheikhAbdulmuhsin Bin Muhammad Alkasim 13-10-1441AH / 5-6-2020 AH

Hudubar farko

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, muna gode maSa kuma muna neman taimakonSa

Muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu  da munanan ayyukanmu, duk wanda Allah ya shiryar babu mai batar da shi, wanda ya batar kuma babu mai shiryar da shi, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya,kuma na shaida Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa. Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabbansa da aminci tabbatacce mai yawa.

Bayan haka, ku ji tsoron Allah -ya ku bayin Allah-cancancin tsoronSa ku yi riko da igiya mai karfi na musulunci

Ya ku musulmai

Fidira ta shaida duniya na da Ubangiji Mai kamala a zatinSa da sifofinSa, yana siffantuwa da dukkan sifa ta kamala mafi kamalarta da mafi girmanta da gayarta, dukkan yabo da godiya da kyautata ambato na shi ne, na daga cikin girmama Allah tabbatar masa da siffofinSa ta kamala da daukaka.

Sunan Allah "Al-Hakim" yazo cikin littafin Allah sama da gurare casa'in (90).

Allah Mai hikima ne yana sanya abubuwa bigirin su yana saukar da su a wurarensu da ya dace da su a cikin halitta da umarninSa yana da cikakken hikima wacce ke hade da daukaka Mabuwaya da ilimi da gwanancewa da kuma yalwa da kuma tuba da godiya, hikimarSa ta kai kololuwa da ta gagari hankula iyakancewa a hakikaninta harsuna sun kasa furta hakikaninta bayani game da ita , da hikimarSa ne ( Abin da ke cikin sammai da kasa suka yi tasbihi zuwa ga Allah).

Tsarki ya tabbata a gare Shi Mai hikima ne abin bauta a sama da kasa (Lallai shi ne abin bautawa a sama kuma Shi ne abin bautawa a kasa yana da hikima kuma Masani ne) ya godewa kansa da kansa saboda shi Mai hikima ne (Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ke cikin sammai da abin da ke cikin kasa duka nashi ne kuma yana da yabo a lahira kuma Shi Mai hikima ne Gwani) Allah ya yabi kanshi tsarki ya tabbata gare Shi lallai cewa yana da girmame - girmame kuma ya cikamake ayar da cewa Shi Mai hikima ne  (Yana da girmame - girmame a cikin sammai da kasa kuma shi Mabuwayi ne Mai hikima) kuma yana da rundunoni a sama da kasa yana gudanar da su kaman yanda ya so shi Mai hikima (Allah na da rundunan sammai da kasa kuma Allah ya kasance Masani ne kuma Mai hikima) ya kirayi Musa Alaihissalam ya sanar da shi da zatinSa cewa shi Mai hikima ne  (Ya musa lalle ne Ni Mabuwayi ne kuma Mai hikima).

Ya kyautata yabo ga littafinSa cewa lallai ya zo ne daga wurinUbangiji Mai hikima yana sanya ko wani abu a bigiren Shi kuma ya saukar da shi a wurin shi matsayin shi sai ya kasance littafi ne gamamme da ya kunshi cikakkiyar hikima Allah subhanahu wa ta'ala ya ce :(Littafi ne da an kyautata ayoyinsa kuma aka yi bayanin shi daki daki daga wurin Mai hikima Mai labartawa) da hikimanSa subhanahu ya bude arziki ga mutane kuma ya ke rike ta (Ba wani abin da Allah ya ke budewa mutane na arziki na rahama ko kuma ya rike face da abin da Allah ke bude wa mutane na rahama ba mai rike haka nan kuma abin da ya ke rikewa ba mai turo ta bayan Shi  lallai Shi Mabuwayi ne mai hikima) , Mala'iku suna matsayi na yarda da gazawa da kuma kasawa a ilimi sun tabbatar da ilimin Allah suka mika wuya ga al'amarinSa (sai suka ce tsarki ya tabbata a gare Ka ba mu da ilimi sai abin da ka ilmantar da mu lallai kai din nan Masani ne kuma Mai hikima) masu daukan al'arshi da wanda ke kewayenta suna adu'a wa musulmai da gafara da shiga gidajen aljannah kuma da cikamake addu'ansu cewa lallai shi din nan da sunan shi  tsarkakakke kuma Mai hikima  (Ya Ubangijinmu ka shigar da su gidajen Aljanna na adn wanda ka yi alkawarin shi gare su kuma ka gyara daga cikin iyayen su da matayen su da kuma zuri'an su lallai kai din nan Mabuwayi ne Mai hikima) .

Allah ya ce ga dukkan Manzannai cewa wahayin da ya ke saukarwa daga gun Shi ne Mai hikima (Haka nan ne ya ke wahayi zuwa gareka da wadanda su ke kafun kai Allah Mabuwayi Mai hikima) Annabawa amincin Allah su tabbata a gare su sun kasance suna rokon Allah ne wurin tabbatar da fatan su da kuma burace - buracen su da sunan Shi tsarki ya tabbata a gare Shi Mai hikima , Ibrahim Alaihissalatu wassalam ya roki Ubangijinsa da sunan Shi Mai hikima da ya turo zuwa gare mu Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi (Ya Ubangiji ka turo a cikinsu manzo wanda ya ke karanta a gare su ayoyinKa kuma yana sanar da su littafi kuma da hikima yana tsarkake su, lallai kai din nan Mabuwayi ne Mai hikima) Ibrahim amincin Allah su tabbata a gare shi ya zo garin shi ya yi hijira zuwa ga Allah sai ya ce lallai Allah Mai hikima ne (sai ya ce lallai ni zan kaura zuwa Ubangijina kuma lallai shi din nan shi ne Mabuwayi Mai hikima), zamani ya tsawaita ga Ibrahim amincin Allah su tabbata a gare shi bai haihu ba ba a haifa mishi ba, sai mala'iku suka yi wa matarsa  albishir da wani da wanda  a halin ita tana tsohuwa kuma bakarariya, sai ta yi mamakin haka sai mala'iku suka ce da ita lallai Allah Masani ne Mai hikima (sai suka ce haka nan ne Ubangijinki ya ce domin lalle Shi Mai hikima ne kuma Masani) Yakubu alaihissalatu wassalam tare da hakurin shi da sauraron yaye bakin ciki sakamakon rasa yusuf da ya yi da dan uwan shi ya tabbatar da ilimin Allah a cikin zaben zamani da ya dace saboda abin da ya ke fata a gare shi na yaye bakin ciki ya sakankance da hikimar Allah wurin shirya sabuba na yaye bakin ciki sai ya fiskanci Allah da sunan shi Mai hikima tare da fatan shi da addu'a (To hakuri  abu ne  mai kyau ya wuci Allah ya  kawo mini su gaba daya lallai  shi din nan Masani ne Mai hikima) bayan yayewan bakin ciki daga Yusuf alaihissalatu wassalam da tsawon musibu da wahalhalu wanda ya hadu da su ya tuna ni'imomin Allah da falalanSa sai ya tabbatar da su tare da tabbatar da ni'iman Allah a hakan sai ya ke cewa (Hakika ya kyautata mini tunda ya fitar da ni daga kurkuku ya zo mini da ku daga kauye bayan shaidan ya shiga tsakani na da 'yan uwana lallah Ubangijina Mai ludufi ne ga abin da ya so kuma lallai Shi Masani ne Mai hikima).

Kuma sunan Shi Subhanahu Mai hikima ya kumshi hikimomi a halittanSa da umarninSa wurin iradarSa ta adiini da kuma ta duniya , Ibnul kayyim Allah ya mishi rahama ya ke cewa tare da izza kamalar kudurarSa da hikima kuma kamalar iliminSa wadan nan siffofi biyu Allah kan hukunta abin da ya so  kuma ya umarnin abin da ya so ya yi hanin abin da ya so kuma ya kyautata yabo kuma ya bi kadu wadan nan siffofi ne da su ke masdarin su shi ne halitta da umarni.

Da hikimansa ne Allah subhanahu wa ta'ala ya halicci halittu gaba daya da tsari mafi kyau ya jera su mafi kamalan jerawa ya kyautata gudanar da su ya kyautata kaddara su ya bawa ko wani mahaluki halittarsa da ta dace da shi ta dace da shi (Ya bawa kowa halittar da ta dace da shi san nan ya shiryar) Allah ya kalubalanci halittu cewa su kawo ko da halitta daya ne wanda akwai tawaya cikin halittarSa, Allah ya kalubalanci da su samar da cikin halittanSa guda daya wanda akwai rashi daidaitu (ka sake dubawa da gani shin za ka ga akwai wani abu na tsagewa?) Da a ce hankulan halittu gaba daya za su hadu domin su bada shawara ga misalin halittan Mai rahama ko kuma abin da ke kusantan shi ko kuma abin da ke kusa da shi ko kuma abin da Allah ya sanya cikin halittan Sa abubuwa na rayayyu na daga kyau da kuma tsari da kyautatawa ba za su iya ba saboda haka Allah ya umarci halittu da su wadatu da ta'ammuli da lura cikin abin da Allah ya halitta Mai hikima cikin halittunSa tare da tsinkayan bisa wasu abin da ke ciki na daga kyau da kyautatawa (ka yi dubi me ke cikin sammai da kasa) da hikimarSa ne Subhanahu ya samar da bayinSa da zatinSa tsarkakakka da kuma mika wuya da umarninSa da haninSa, ya saukar da littafinSa kuma yana so da ya karbi tuban mu kuma ba gyaruwa game da al'amuran duniya sai da addini haka nan kuma wasu magabata suke cewa (Ba don a cikin umarninSa da shari'ansa ba sai wannan hikima mai girma wanda ita ce tushe na alheru da kuma kamalan zatinSa da hakan ya kasance abu ne cikakke kuma mai waraka).

Shi ne wanda tsarki ya tabbata a gare Shi Mai hikima cikin  umarninSa a cikin duniya  wanda ya ke jarabta bayinSa da shi domin ya gyara su  ya daga darajar su ba wani abu da bawa zai kasance yana da shi na zabi kaman nufin rashin lafiya da tawayan arziki kawai abin da zai yi to ya yi imani ne kuma ya yarda  kuma ya riki abubuwa na sababi wanda aka  shar'anta da kuma abubuwan da suke na halal sai ya tunkude kaddaran Allah da abin da ke gudana wa bawa ba tare da zabin shi ba wanda ba yi da karfi wurin tunkude shi sai ya yarda kuma ya mika wuya ya shaida izzan Allah ne a cikin hukuncinSa da kuma a'adalcinSa da kuma abin da ya hukunta.

HikimanSa na gudana a gare Shi kuma lallai duk abin da ya same shi bai kasance da ya kuskure shi ba abin da kuma ya kuskure shi bai kasance da ya same shi ba lallai hakan ke wajabta masa a'adalcin Allah da hikimanSa lallai Allah Mabuwayi hakika ya bayyana wasu hikimomi ga bayinSa sai ya bada labari cewa saukar da littafi da ya ke yi don tabbatar da mumunai ne ya shiryar da su kuma da yin albishir a gare su (ka ce ruhi mai tsarki ya sauka da shi daga Ubangijinka (Mala'ika Jibril) da gaskiya domin ya tabbatar da wadanda suka yi imani kuma da shiriya ne da albishir ga musulmai) ya tura manzanni domin kada wani ya zama yana da hujjar cewa shi ya jahilci addini (Manzanni ne masu albishir kuma da gargadi domin kada ya zamana mutane suna da hujja a kan Allah bayan zuwan manzanni ) Hakika kuma Allah ya jarabci mutane yana kuma yi musu ibtila'i kuma zai sake yi musu ibtila'i  domin ya duba ya ga gaskiyan ta'allukin su da Shi Allah(Wai mutane suna zaton za su ce sun yi imani ne a kyale su a halin kuma ba a'a jarraba su) Allah ya shamake ilimin gaibi ga bayinSa sai ya kebantar da shi ga kansa saboda hikima , (Masanin gaibi abin da ya faku da kuma shahada Shi Mai hikima ne kuma Gwani).

Bayan haka ya ku musulmai:

Lallai Allah Shi kadan shi halitta da umarni na Shi ne yana aikata abin da ya so a cikin duniyarSa, a cikin shari'arSa yana hukunta abin da ya ke so abin da ya nufa , ba a fiskantar da tambaya gare shi, ba a suka cikin hikimanSa da wata magana (Ba a'a tambaya don me ya ke aikatawa amma su (halittu) ana tambayan su )

Musulmi yana bautawa Allah ne da abin da sunan Alhakimu ya kumsa na ma'ana, idan bawa ya sakankance da hikimar Allah sai ya ji dadi da halittan Allah wanda ya ke Albadi'u da aikin Shi wanda akwai kyautatawa a ciki da kwarewa da kuma girmama shari'an Allah ya ji tsoron shi Allah Madaukaki, ya ji kunya daga  saba mishi ko ya ji kunya daga kurakuran shi, ya mika wuya ga umarnin shi da hanin shi ya tsananta farin ciki da cewa Allah ya shiryar da shi zuwa ga wannan addini saboda hikimanSa da ya nufa da ita game da shi kuma lallai shari'a daga mai hikima ne ta zo domin ya sanya dan adam cikin walwala ko da bala'i ya sauka a gare shi sai ya yarda da abin da Allah ya hukunta ya kaddara masa ya mika wsuya cewa hakan Allah ya hukunta a gare shi cikin gyara da kuma alheri (Ya wuci ku tsani wani abu kuma sai ya zamana alheri a gare ku) kuma ya sakankance cewa bayan hakan akwai hikima  da bai santa ba  kuma lallai yana  kai komo cikin ni'iman Allah ne a halin yalwa kuma da halin cuta , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ke cewa: (Mamaki da ala'amarin mumini, lallai dukkan ala'amarin shi alheri ne a gare shi hakan baya kasancewa ga wani sai ga mumini idan alheri ya same shi sai ya yi godiya sai hakan ya zama alheri a gare shi idan kuma cuta ta same shi sai ya yi hakuri hakan sai ya zama alheri a gare shi) Muslim ne ya rawaito.

Ina neman tsarin Allah diga sharrin shaidan abin jefewa.

(Yana gudanar da ala'amura ba wani mai ceto face bayan izinin Shi wancannin ku Shi ne Allah Ubangijin ku, ku bauta miShi, ba za ku yi tunani ba ?) Allah ya sa mini albarka ni da ku a cikin Alkur'ani mai girma.

 

Huduba ta biyu:

  Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah bisa kyautatawanSa, godiya a gare Shi bisa datarwanSa da kuma baiwanSa, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya ina mai girmama sha'aninSa na shaida Annabin mu Muhammad bawanSa ne kuma Manzon Sa ne tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa da sahabbansa da aminci tabbatacce mai kari.

Ya ku musulmai:

Allah ya gina al'amuran bayinSa da ya sanar da su wasu ma'anoni  na dalilin halittansu  da umarninSa ba tare da zurfafawa cikin su ba da kuma bayanin su daya bayan daya ba, wan nan abu ne da ke faruwa a cikin ala'amura a tushensu da kuma rassansu abin da ba ya boyuwa ga bayi wasu ma'nonin na hikimanSa cikin abin da ya kirkira haka nan kuma da umarninSa da shari'anSa da kuma abin da ke kasancewa a duniya na kaddara ya ishesu cikin saninSa ta fiska na gaba daya abin da ya kumsa na hikima  da ya kai kololuwa su fahimci hakikanin bayaninSa daki daki ba ko hikimansa daki daki ba daya bayan daya hakan kuma yana daga cikin ilimin gaibi ne wanda Allah ya barwa kanSa shi .

 sannan ku sani lallai Allah ya umarce ku da salati da aminci ga AnnabinSa sai ya ce: a cikin littafinSa mafi hikima da ya saukar (Ya ku wadanda suka yi imani lallai Allah da mala'ikunSa suna salati ga Annabi ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi da aminci tabbatacce mai yawa).     

   

الأربعاء، 27 مايو 2020

HUDUBAR KARAMAR SALLAR IDI NA MASALLACIN ANNABI 1441AH

Hudubar idi na masallacin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi 1-10-1441Ah /24/5/2020Ad

    Na Shaikh Abdullahi dan Abdurrahman Al-Buaijan

Huduba ta farko

Allah Mai girma Allah Mai girma, Ba abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Allah Mai girma kuma Allah Mai girma kuma dukkan yabo  da godiya na Allah ne, Allah ne Mafi girma Mai girma, dukkan yabo  da godiya masu yawa sun tabbata ga Allah, Tsarki ya tabbata ga Allah safiya da maraice godiya sun tabbata ga Allah bisa datarwanShi da kyautatawanShi , godiya bisa ga yalwan kyautanSa da baiwarSa dukkan godiya da yabo sun tabbata ga Allah wanda ya shiryar da mu zuwa ga musulunci ya kuma datar da mu zuwa ga azumi kuma da tsayuwan dare dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya kwararamana daga cikin taskokin kyautanSa , abinda ba ya iyakantuwa shi ne wanda ya fi dacewa a bauta wa kuma shi ne yafi dacewa da a ambata kuma shi ne wanda ya fi cancanta da a godewa kuma Allah mai girma ya shar'anta mana shari'o'I da hukunce hukunce kuma ya sa sauki a ciki dukkan yabo da godiya sun tabbata ga wanda ya fara kuma ya ke maidawa , Ma'aboci al'arshi Madaukaki , mai yafiya kuma mai yawan gafara mawadaci abun godiya mai aykata duk abinda ya so , wanda ya shiryar da shi ne zai samu walwala kuma shi ne wanda ke kan daidai wanda kuma ya baar to shi ne tsinanne daga rahama abun korewa wanda ya shiryar da shi zuwa ga hanyan tsira to shi ne shiryayye .

Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allahshi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya ga dukkan komai mai sheda ne shi yayi ni'ma a gare mu da shedawa na tauhidi da kuma shaidawa cewa Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne zababbe cikin bayinSa Ma'boci manhaji shiryayye da kuma abin bi wanda ya ke na daidai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalanSa da sahabbanSa salati na din din din har zuwa ranan alkawari

 Bayan haka :

Muna muku barka da ranan idi, Allah ya sa muku albarka a cikin dukkan wani abu sabo ya sa ku walwala da bushara ya sa muku kari, Allah mafi girma Allah mafi girma ba abin bautawa da gaskiya sai Allah Allah shi ne mafi girma dukkan yabo da godiya naShi ne.

Ya ku musulmai , ban kwana irin na ramadana kafin 'yan kwanaki ne mu ke fiskantan watan ramadana gashi a yau kuma muna mishi ban kwana yana kokarin shudewa ya zama cikin zamani abin tarihi haka nan ne kuma lokacin ya ke tafiya rayuwa shekaru na mutum su kare wata mai daraja ya tafi dararrakinsa da abun rayawa da wuninsa abun dulmuya a cikin bauta gajiyansa ya tafi wahalansa ya kare ladansa kuma ya tabbata in Allah ya so wata ne mai albarka da falala da kuma alheri da kuma da'a wanda ranakunsa sun kare an kuma nade ayyukansa masu rabauta sun ci riba sun masu kokari  kuma sun  samu ganima, ina ma da mu san wadanda aka karma musu mu taya su murna, mu kuma san wadanda aka maida musu jajanta musu!

Ya farin cikin wadanda suka rabauta! Hakika Allah ya musu ilhama na tuba, ya datar da su ga da'a, muna rokon Allah ya karba musu kuma ya basu daidaituwa a kan tafarki.

Ya kaiton wanda ya yi hasara, hakika sun rasa alheri, an musu shamaki daga Ubangijinsu, damammaki na rayuwa sun kwace musu, da lokuta na alheri basu ribace shi ba sai hasara da nadama, sai dai kofofin tuba basu gushe ba suna bude ba a rufe su bayan ramadana,kuma Ubangijinmu Mai daukaka da buwaya yana karbar tuba daga bayinSa a dukkan lokaci da wuri,

(Kace ya ku bayi na wadanda suka barnata ma kawunansu!kada ku yanke tsammani daga rahamar Allah, lalle Allah na gafarta zunubai gaba daya kuma shi Mai gafara ne Mai jinkai).

      Ya ku musulmai!

Lallai na daga cikin alamu na karbar ayyuka akwai sauyawa daga wani hali zuwa hali mafi kyau, to ku roki Allah tabbatuwa akan daa har zuwa mutuwa, ku nemi tsarin Allah daga juyawar zuciya, da kuma lalacewa bayan gyaruwa, abin mamaki da dabbancin kaskancin sabo bayan daukaka na da'a, ya tabbata daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,(Lalle dayanku zai yi aiki irin na 'yan aljanna har sai ya kasance tsakaninsa da ita zira'i sai littafinsa ya rigaya sai ya yi aiki irin na 'yan wuta sai ya shigeta, kuma lalle dayanku zai yi aiki irin na 'yan wuta har sai ya kasance tsakaninta da shi saura zira'i sai ya yi aiki irin na 'yan aljanna si ya shige ta.)

 

Allah Mai girma Allah Mai girma, Ba abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Allah Mai girma kuma Allah Mai girma kuma dukkan yabo  da godiya na Allah ne.

Ya jama'ar musulmai… [ fiskantar karamar idi da farinciki da taya murna]

Muna muku murna da idin karamar sallah, hakika Allah ya rubuta muku lada kuma ya yafe muku laifukan ku, ya gafarta muku zunubai ya daga darajojinku kuma ya kankare muku kurakurai, ku godewa Allah ku roke shi karbar ayyuka da tabbatuwa. Muna taya ku murna da kuka fifita yardar Allah bisa ga jin dadi na duniya da sha'awe sha'awe, kuka kyautata kuma kuka cika kuka yi abin da ya dace na ibada, kuka samu mafi girman sakayya in sha Allahu, barkanku da samun yin azumi kuma barkanku da samun tsayuwa, barkanku da yawaita ayyuka na da'a, barkanku da farin ciki na idi da kawa na idi da walwala, ku ji dadi da duk wani abu da ya ke sabo.

 

Allah Mai girma Allah Mai girma, Ba abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Allah Mai girma kuma Allah Mai girma kuma dukkan yabo  da godiya na Allah ne.

Ya ku bayin Allah! Yafiya da rangwami.

Lalle Allah ya cikamake azumi da idi karama mai albarka kuma ya sanya ta cikin manyan alamomi na addini, na daga cikin sunnar mafificin Annabawa da Manzanni a bayyana farinciki a tsakanin musulmai da bayyana jin dadi da walwala da annashawa da kawa, to ku yada abubuwa na kauna  kyawawa, da kalamai masu dadi, ku jefa duk kayan kamshi da dadadawa.

 ku yada walwala  a doron kasa da  ku  yi dariya da sifa ta murmushi mai ban kaye, ku yi gaishe gaishe na idi domin yana kara kauna ta kuma karfafi soyayya da 'yan uwantaka,

ku shigar da farinciki a zukata, ku binne kyashi da bakinciki, ku shigar da farinciki ga iyalai da makusanta da makwabta, ku yi wasici ga juna da gaskiya da rahama, ku tausayawa wanda ke doron kasa sai wanda ke sama ya tausaya muku.

Yau rana ne na afuwa da kauda kai da rangwami, wanda ke son afuwa da gafara daga Allah to ya yafe ya ya kuma yi afuwa ga mutane, domin sakayya na kasancrwa ne da irin nau'in aikin da mutum yayi, Allah Madaukakin sarki ya ce (su yi rangwame su yi afuwa, shin ba ku son Allah ya gafarta muku)

(kuma lalle ne wanda ya yi hakuri ya gafarta to shi wancan aiki haki yana daga manyan al'amura).

      Ku yi afuwa ga wanda ya yi zalunci ku dauke kai daga wanda ya muzguna.

(kuma ku yi gaggawa zuwa ga neman gafara daga Ubangijinku da wata Aljanna fadinta sammai da kasa ne)

Yau rana ne na biyayya da kyautatawa,to ku kyautata kamar yadda Allah ya kyautata zuwa gare ku Allah yana son masu kyautatawa , a yau rana ne na sada zumunci , da kauna , ku sada zumuncin wanda ya yanke muku ku bawa wanda ya hana ku , ku yafe wa wanda ya zalunce ku ba wai mai sadarwa shi ne wanda mai rama abinda aka mishi ba na alheri , a yau rana ne na sanin yakamata to ku yi wasici wa junan ku da masu rauninku ku yi musu wasici da alheri ku tausayawa kananan ku , kuma ku girmama manyan ku , ku kyautata zuwa ga talakawan ku , ku shigar da farin ciki a cikin zukatansu da annashawa ku yaye musu bakin ciki da bacin rai kuma ku magance musu ciwonda suka ji ku ji tsoron Allah ku kyautata ku sulhunta tsakanin ku kada shaidan ya fitineku ku yi sulhu tsakanin 'yan uwanku .

An karbo daga Abu huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:(ana bude kofofin Aljanna ranan litini da alhamis sai a gafartawa dukkan wani bawa wanda ba ya hada Allah da wani sai mutumin da kawai ya kasance tsakaninshi da dan uwan shi akwai gaba sai a ce da shi a sararawa wadannan har lokacin da suka yi sulhu ku jira wadannan mutane biyu sai sun yi sulhu ku jira wadannan mutane biyu har sai sun gyara tsakanin su) Muslim ne ya rawaito .

To ku gyara kawunanku ya ku bayin Allah bisa ga tsarkake zukatan ku da kuma aminci zukata ku jaddada alaka na kauna da soyayya tsakaninku da tausayi imanin dayan ku ba zai cika ba har sai ya so ma dan uwan shi abinda ya so ma kanshi kuma ku yi kyauta za ku so juna .

Allah mai girma , Allah mai girma , Allah mai girma ba abin bautawa da gaskiya sai Allah , Allah mai girma Allah mai girma dukkan godiya nashi ne .

Bayin Allah :

Lallai ku din nan 'yan uwa ne daga uba da uwa (A'adam da Hawwa'u) sai dai shaidan yana iya rarraba tsakaninku ya jirkita zaman lafiyan tsakanin ku da 'yan uwantakan ku hakika ya fidda mahaifan ku biyu daga Aljanna ta hanyan rudi, ya byyana tsakaninku kuma adawa da kiyayya to ku yi riko da igiyan Allah ku yi sulhu tsakanin 'yan uwanku ku jo tsoron Allah kada ku rarraba kada ku cece ku ce sai ku dare karfinku ya tafi.

An karbo daga Abu huraira ya ce Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (kada ku yanke zumunci kada ku juya wa juna baya kada ku yi gaba kada ku yi hasada kada ku yi tajassusi (leken asiri) kuma kada ku yi bincike,kada ku yi munajasha ku kasance bayin Allah 'yan uwan juna, ku kasance 'yan uwa kamar yadda Allah ya umarce ku)Muslim ne ya rawaito.

   Allah Mai girma Allah Mai girma, Ba abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Allah Mai girma kuma Allah Mai girma kuma dukkan yabo  da godiya na Allah ne.

Ya jama'ar musulmai… [Tasirin akida a tarbiya]

Lalle Allah ya zaba muku musulunci, to kada ku mutu face kuna musulmi, to ku kiyaye tushen shi da rukunan shi, ''An gina musulunci akan abubuwa guda biyar , shaidawa ba abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Annabi Muhammadu Manzon Allah ne, da tsaida sallah, da bada zakkah, da azumin ramadana da yin Hajjin dakin Allah''.

Ku kiyaye imani domin shine tushe kuma a kan shi a ke gini, shine tsagoron addini da dalakin shi, shine (Imani da Allah da mala'ikunSa da littatafanSa da MazanninSa da ranar lahira da imani da kaddara na alheri da sharri).

Ku yi kokari wurin murakabar Allah a kowani zamani da kowani wuri, don shine hakikanin ihsani wato (ka bautawa Allah kamar kana ganinSa to in ba ka ganinSa shi yana ganinka)

Ya ku bayin Allah Tauhidi shine tushen addini kuma abin rikon shi mai karfi, kuma shine asali da ake gini a kan shi, da kuma hukunce hukunce, bisa shi ne ake karbar ibada kuma ya inganta ko akasin haka,  da ayyukan da'a  da shi ne ake samun tsira na duniya da lahira kuma shine hakkin Allah a kan bayi, An karbo daga Mu'azu dan Jabal ya ce na kasance goye akan jaki da ake kira Ufairu a bayan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yace : sai yace ya Mu'azu ko ka san hakkin Allah akan bayi da hakkin bayi a kan Allah? Sai na ce  : a'a Allah da ManzonSa suka fi sani, sai yace : (Hakkin Allah akan bayi shine su bauta masa kada su hada shi da wani, hakkin bayi kuma a kan Allah shine kada ya azabtar da wanda ba ya hada shi da wani.yace sai nace ya manzon Allah ba zan yi wa mutane albishir ba? Sai yace a'a kada ka musu albishir su saki jiki) Buhari ne ya rawaito.

Lalle tauhidi shine mabubbuga na hadin kai da fahimtan juna da 'yan uwantaka. Da shi ne ake samun haduwar kalma kuma al'uma ke zama tsintsiya madaurinki daya. Da shi ne ake zartar da alakoki ko a kulla wani abu. Da shi ne al'uma ke iya tsayawa a kan kafanta a samu zaman lafiya.

Ku godewa Allah bisa ga shiryarwa kuma ku roke shi tabbatuwa a kanta.

  Allah Mai girma Allah Mai girma, Ba abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Allah Mai girma kuma Allah Mai girma kuma dukkan yabo  da godiya na Allah ne.

      Ya ku musulmai! [Tasirin ibada da muamaloli]

Ku maida hakkoki zuwa ga ma'abotanta, ku sauke abin da ke kan ku nauyi, ku bada amana ga ma'abotanta, ku bawa dan kodago hakkinsa kafin zufansa ya bushe,

An karbo daga Abu Huraira Allah kara yarda a gare shi ya ce : (Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( wanda ya kasance yana da wani abu na zalunci da ya ci wa dan'uwansa na mutunci ne ko waninsa to ya warware daga gare shi  tun a yau kafin ya kasance dinari ko dirhami  in ya kasance yana da aiki na kwarai sai a dauka daga gare shi gwargwadon abin da ya zalunta, in kuma bai da kyawawa sai a dauka daga laifukan sahibin nasa sai a dora masa.) Buhari ne ya rawaito.

Ya ku bayin Allah! Ku cika alkawura da kuma yarjejeniya a hakkoki da muamala da suran abubuwa na cinikayya cikin hukunce hukunce da aka dora muku na hakkoki (Duk wanda ya cika abin da ya yi wa Allah alkawari to zai bashi lada mai girma).

 Domin hakan na cikin abin da ke karfafa zumunci da alaka, kuma ya kara kauna da soyayya, ya kuma kara aminci da tausayawa juna,

An karbo daga nu'uman dan Bashir Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : na ji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : (Lalle halal a bayyane ya ke kuma haram a bayyane ya ke a tsakanin su akwai wasu al'amura masu rikitarwa, da yawa daga cikin mutane basu san su ba, duk wanda ya tsoraci shubhohi to ya kubutar da addininsa da mutuncinsa, to duk wanda ya fada cikin shubhohi to ya auka cikin haram, kaman mai kiwo ne yana kiwo ne a bakin iyaka yana kusa da ya fada a ciki, ku saurara ! lalle kowane sarki na da iyakansa,ku saurara iyakan Allah shine abin da ya haramta, ku saurara lalle a cikin jiki akwai wata tsoka idan ta gyaru to dukkan jiki ya gyaru, idan ta baci to dukkan jiki ya baci, ku saurara ita ce zuciya).

Ku bi umarnin Allah, ku kame daga abin da ya haramta,ku nesaci shubhohi ku gyara niyoyi, ku sabonta zumunci da kauna da soyayya da alakoki.

Allah Mai girma Allah Mai girma, Ba abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Allah Mai girma kuma Allah Mai girma kuma dukkan yabo  da godiya na Allah ne.

 

Huduba ta biyu

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah da ya yalwata ni'imomi, ya kiyaye mu daga azaba, ya tula mana mamako na karamci.

Allah Mai girma Allah Mai girma, Ba abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Allah Mai girma kuma Allah Mai girma kuma dukkan yabo  da godiya na Allah ne.

Ya ku bayin Allah ! ku ji tsoron Allah a sirrace da bayyane, ku lazimci Alkur'ani da sunnoni, ku nesaci alfahasha wanda ya bayyana da abin da ya boyu, ku nesaci shubuhohi, Da shubuhohi da sabuba na fitintinu ko Allah zai dauke muku bala'i da jarrabawa.

Allah Mai girma Allah Mai girma, Allah Mai girma,  Ba abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Allah Mai girma kuma Allah Mai girma kuma dukkan yabo  da godiya na Allah ne.

 

 Ya jama'ar musulmai! [ Ayyukan idi karama]

Allah ya shar'antawa bayinSa da su cike azumin ramadan da zakkan fidda kai, da sallar idi da kabarbari da ambato, girmamawa da godiya ga Allah bisa ni'imar cikan azumi da tsayuwa, hakika sharia ta wajabta zakkan fidda kai ga musulmai wanda tsarkaka ne ga mai azumi daga wass, da batsa kuma abinci ne ga miskinai, lokacinta shine kafin fita zuwa sallar idi, duk wanda ya jinkirtata to ya wajaba a gare shi ya gaggauta fitar da ita, duk wanda ya fitar kafin sallah to zakka ce a gare shi ,karbabba, wanda kuma ya fitar bayan idi to ita sadaka ce daga cikin sadakoki, An karbo daga dan Umar Allah ya kara yarda a gare shi shi da mahaifin shi ya ce :(Manzon Allah ya wajabta zakkan fidda kai sa'i guda na dabino ko kuma sa'i guda na sha'iri bisa ga bawa da da na miji da mace da kuma yaro da babba na daga musulmai). Buhari ne ya rawaito.

Na daga cikin manyan alamomi na addini ga musulmai a ranar idi kabbarori, kuma sunna ne ga maza da mata, tun daga faduwan ranan karshe na ramadana Allah Madaukakin sarki ya ce ; (Kuma don ku kammala adadi kuma ku girmama Allah bisa shiryar da ku da yayi ko za ku gode)

Allah Mai girma Allah Mai girma, Ba abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Allah Mai girma kuma Allah Mai girma kuma dukkan yabo  da godiya na Allah ne.

Allah Mai girma Allah Mai girma,  Allahu mai girma, Ba abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Allah Mai girma kuma Allah Mai girma kuma dukkan yabo  da godiya na Allah ne.

 Ya ku musulmai!

Hakika uzuri ya killace ku a wannan yanayida aka samu kai a ciki da naku sa rashin halartar idi, to ku yi kwadayin yin ta a gidajenku, kuma lokacinta na farawa ne tum daga dagowar rana  har zuwa zawali, zai yi kabbarori bakwai araka'ar farko, a raka'a ta biyu kabbarori biyar, sai ya karanta suratul q wal kurani majid  ko sabihisma rabbika a raka'ar farko, a raka'a iktarabatissaatu wan shakkal kamar ko hal'ataka hadisul gashiya,ko da abin da ya sauwaka na daga kur'ani.

Allah Mai girma Allah Mai girma,  Allahu mai girma, Ba abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Allah Mai girma kuma Allah Mai girma kuma dukkan yabo  da godiya na Allah ne.

Ya taron mata!

 Lalle Allah Mai hikima ne a cikin gudanarwarsa, Masani ne cikinhalittunsa da mulkinsa, adalci ne al'amarinSa da hukuncinSa. Ya tura sako da bayani ya saukar littafi don mutane su tsaida gaskiya da mizani ta ti umarni da adalci  yin adalci  ya yi hani ga zalunci da tawaye hakki sai ya ce : (lalle na umartanku da ku maida amana zuwa ga ma'abotanta, idan kuka yi hukunci tsakanin mutane to ku yi hukunci da adalci.)  

Hakika Allah ya yi adalci tskanin maza ga mata a shariarSa da hukunce hukuncenSa ya kuma kebance kowannensu da abinda ya dace da halittarsa da kudurarSa da karfinsa ya daidaita tsakaninsu a komabayan haka na daga magana da karramawa da alkawarin lada da azaba da kuma dora nauyi na sharia.

Hakika musulunci ya bada kariya ga mace ya shar'anta hakkokinta ya daukaka matsayinta ya yi umarni da a bata kulawa a kuma ciyar da ita a mutunta tam a gyara a katange ta, hakika Annabi ya yi wasiya ga mace a Hajji bankwana, na daga cikin abin da ya ambata (Ku saurara ku yi wasiyya ta alheri game da mata, lalle su mataimaka ne a gre ku,, ku saurara lalle kuna da hakki a kan matayenku, su ma suna da hakki a kan ku,

Hakkinsu mata a kan ku  ku kyautata zuwa gare su cikin tufatar da su , Tirmiz ne ya rawaito.

Ya ku taron mataAllah!

Gudumawar da mace za ta bada ranar idi kamar gudumawar da na miji zai bada ne, zata yi tarayya wurin yada farinciki da karfafan dankon zumunci da afuwa da rangwami da gyara, da tsarkake zukata da karfafan alakoki da hamaka kauna da sada zumunci da yin ziyzrce ziyarce, da taimakawa talakawa da miskinai da marasa galihu da yin ma'arufi. (ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku  wanda ya halicce ku daga rai guda ya halitta masa matarsa daga gare shi ya kuma yada daga gare su maza masu yawa da mata, ku ji tsoron Allah da ku ke magiya da shi ku ji tsoron mahaifa, lalle Allah ya kasance a gare ku mai tsaro).

 

 


الجمعة، 22 مايو 2020

BANKWANA DA WATAN RAMADANA

Hudubar masallacin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi na 29/9/1441

 

Hudubar farko:

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah tsira da amincin Allah su tabbata ga manzonSa

Bayan haka :

watan ramadana ya kare , wanda Allah ya bamu labari cewa wasu 'yan kwanaki ne kididdigaggu sai gashi ya wuce kaman kyabtawan ido, ya wuce kaman hasken walkiya, hakika zukata sun kasance sun yi shaukin zuwan shi, ga shi a yau kuma yana shelanta tafiya kuma yana juyawa yana mai ban kwana, ba abin mamaki ba ne a samu zuciya ta samu nau'uka daban daban na abin da ta ke ji na daga cikin labaran zuciya, muna jin falalan Allah a gare mu da ya shiryar da mu zuwa ga musulunci kuma ya sanar da mu alkur'ani, kuma ya riskar da mu ramadana ya taimake mu zuwa ga azumi da kuma tsayuwa, shi ne mai ni'imtarwa mai yawan kyauta, Allah Madaukakin sarki ya ke cewa:(suna goranta maka don sun musulunta ka ce kar ku min gori bisa musuluncin ku sai dai Allah Shi ne zai goranta muku saboda ya shiryar da ku zuwa ga imani) wan nan shi ne halin masu tafiya zuwa ga Allah suna shelantawa da dukkan ladabi mai girma da daukaka da rusunawa da jingina ni'ma zuwa ga ma'bocinta (sai ya ce wannan falala ne na Ubangijina) wan nan shi ne abin da ya dace duk wasu ayyukan kwarai a rufe da su, a fiskanci ayyukan girmamawa da su (Dukkan godiya a gare shi ta ke a duniya da kuma lahira hukunci  ma naShi ne kuma gare shi za ku koma) lallai Shi Madaukaki mai falala na hakika da dukkan wani abu mai kyau ga halittunSa ,

An karbo daga Anas Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Ba wani ni'ma da Allah zai yiwa bawa sai bawan ya ce godiya ta tabbata ga Allah face sai abin da aka bashi zai fi abin da ya rika) wan nan shi ne yanayin halin 'yan aljanna a lokacin da suka kai kololuwa gurin buri da samun yardan Allah sannan suka shiga aljanna harsunan su na daga murya da godiyan Allah Madaukaki suna cikamake adu'arsu da shi da ayyuka na kwarai , Allah Madaukakin sarki ya ke cewa (sai suka ce dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah da ya tafiyar mana da bakin ciki lallai Ubangijin mu mai yawan gafara ne kuma mai yawan godiya)(wanda ya bamu masauki a gidan dawwama daga cikin falalanSa , ba wani gajiya ko wahala da zai shafe mu)

Gaggautawa zuwa ga godiyan Allah da kyautata yabo bisa ga ni'mominsa a yayin kammala wannan watan falala shi ne manhaji na musulunci da kuma taujihin alkura'ani , Allah Madaukakin sarki ya ce: (Domin ku cike adadin kuma ku girmama Allah bisa ga abin da ya shiryar da ku ko za ku gode) ya zo a hadisi wanda Bukari da Muslim suka rawaito shi daga Abu huraira Allah ya kara yarda a gare shi daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(Mai azumi nada farin ciki guda biyu , farin ciki guda yayin shan ruwansa farin ciki guda kuma yayin haduwa da Ubangijinsa )

 Tabbatar da ma'ana ta yabo da godiya ta watan ramadana alama ce ta kyautata zaton bawa ga Allah da kuma fatansa cewa Allah ya karba mishi abin da ya yi na da'a kuma ya kankare mishi tawaya da aka samu a aiki da kuma gafala na daga halaka da kuma jahilci , yayin sauke nauyi , hakika ya zo a hadisul kudusi (Ni ina inda bawa na ya zaceNi) idan bawa ya kyautata zato ga Ubangijin shi to ya lizimta a gare shi da ya yawaita addu'a don Allah ya karba mishi da'an shi yana mai ladabi tare da Allah da neman tabbatar da zaton shi da gaskiyan fatan shi.

Hakikanin godiya a karshen watan ramadan shi ne gyaruwan aikin bawa da lazimtan shi ga da'a ga Ubangijin shi da gaggautawa zuwa ga wurin samun yardar Allah , Allah Mabuwayi da daukaka ya ke cewa(ku yi aikin godiya ya ku mutanen Dauda , kadan ne daga cikin bayi Na su ke masu godiya) Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kan yi tsayuwan dare har kafafuwarsa su kumbura sai a ce da shi kai da Allah ya gafarta maka abin da ya gabata na daga zunubanka da abin da ya jinkirta? Sai ya ce : (Ashe ba zan zama bawa mai yawan godiya ba ?).

Musulmi wanda Allah ya haskaka zuciyarsa a cikin watan ramadana ya kara fadada da imani ya sha daga mabubbuganSa, ya koshi daga tabkinSa, ya yi tsayuwan daren Sa , ya azumci wuninSa , to ba zai gushe ba yana tsere zuwa ga ayyuka na da'a har bayan watan ramadana, ba zai yi sakaci ba wurin neman ayyuka na ganima wanda ya ci daga dadinta a cikin azumin shi da kuma sallarsa da biyayyarsa, duk wanda ya dandani dadin ganawa da Allah ya kuma dandani dadin imani a ramadana natsuwa da kwanciyar hankali ya kwararo a cikin zuciyarsa to ba zai  yi sakaci ba wurin barin wannan sa'ada din ya tsere mishi, zai zame ne zuciyarsa  na ta'allake da Ubangijin shi kuma zai zame yana ta debe kewa da Ubangijin shi, kuma tare da Allah kuma zuwa ga Allah, idan lokacin ramadana ya kare lallai lokuta na alheri na bibiyan juna falaloli na Mai rahama ba a'a iya iyakance su lokuta na da fifiko wurin kima da kuma lada a duk lokacin da aka samu nunfasawa na wani lokaci da  dama ta samu to mai hankali zai yi gaggawa ne ya tashi zuwa gare ta, mai komawa zuwa ga Ubangijin shi zai ribace ta, Allah Madaukakin sarki ya ce: (ka yi sujada ka kusanto)

A dukkan safiya da gari zai waye fage ne na yin hailala da kuma godiya da kabarbari da kuma istigfari.

 A dukka yammaci in ya sake duhun shi  to lokaci ne na ganima wanda zai  farauce shi, wanda ya san kimanta shi ne masu yawan ibada a cikin dare wanda sassan su ke nesatan makwanci suna rokon Ubangijinsu suna bisa halin tsoro da  kuma tsammani.

 Wadanda suka san hakikanin rayuwa da kuma kimanta suna da iko lokutan su su zama duka lokuta ne na ayyukan alheri, za su kuma rika  kai komo cikin nau'uka na mubadara ta hanyan ayyuka na kwarai da, yada ilimi da taimaka wa mabukaci da girmama bako da kuma shafa kan maraya da kuma gyara da gina masallaci da kuma yalwata nasiha da karfafan tsangayoyi  na alkur'ani  da tarayya wurin gidauniya  na alheri da kuma aiki bisa habaka kasa da kuma daga al'uma, Allah Madaukakin sarki ya ce: (Duk wanda ya ke son lahira kuma ya yi aiki don ita irin aikinta a halin yana mumini to wadan nan ayyukan su za su zama abin godiya).

Musulmi ya kan hadu da wani nau'i na bala'i ko annoba a zuciyansa ko iyalansa idan ya godewa Allah kuma ya nemi ladan musiban a wurin Allah ya yi imani da abin da Allah ya hukunta ya kaddara to Allah sai ya girmama mishi ladan shi, ya maida mishi da mafi alheri kuma ya rubuta masa rahama da gafara da shiriya Allah Madaukakin sarki ya ce:( lallai za mu  jarabe ku da wani abu na tsoro da yunwa da tawaya na daga dukiya da rayuka da 'ya'yan itace, ka yi albishir ga masu hakuri wadanda idan musiba ta same su sai su ce : ga Allah muke kuma gare shi za mu koma, wadan nan suna da wani kyakkyawan ambato daga Ubangijinsu da kuma rahama kuma lallai wadan nan su ne shiryayyu)

Haka na zuwa ne a wani yanayi na annoba wanda ya sanya abu mai motsi ya zama ya natsu ya mosta kuma abin da ya ke zaune gu daya, ya yi yawo a doron kasa ya sanya zukata cikin tsoro da  idanuwa kuru kuru na daga abin da jiki ke kwanta dama, da abubuwa da ke faruwa na kamuwa da cututtuka daya bayan daya da ake gani a wan nan yanayi na kunci mai tsanani akan fiskanci ludufin Allah boyayye  rahamomin Allah su kewaye mu sai Allah ya kiyaye bayi daga wan nan annoba mai ragargazawa ya katange kasa daga rashin lafiya mai halakarwa ya dauke bakin ciki daga al'uma tasirin shi a doron kasa ya zamana dan kadan ne san nan ya tunkude shi da falalanSa ga Ubangiji wani abu ne da ba mai wahala ba.

wannan shi ne yaye bakin ciki mai girma, zai sanya idin mu ya zama zai zo gare mu nan kusa cikin mafi kyan idi kuma wanda ya fi farin ciki da kuma jin dadi domin tufafin da za mu sa sabo a cikin idi shi ne na tsoron Allah da kuma lafiya, abin hawa mai laushi da za mu hau shi ne na aminci da zaman lafiya shakatawa da walwala shi ne mu shaki tacecciyar iska wacce ta kubuta daga wan nan annoba da kuma farin ciki na haduwan iyalai da 'yan uwa da makusanta da kuma makwabta, shi ne a samu labarin suna cikin koshin lafiya suna cikin ni'ma, shin bayan wannan ganima akwai wani abu kuma na nema ? ku tafi a doron kasa ku yi dubi zuwa ga halin da wadan su su ke ciki, domin ku san kaye na hali da daukaka da ni'ima a kuma kima na ludufi, abin mamaki da girman Allah da rahamarSa Mahalicci, lallai  halarto da ni'ima da gode wa Allah da harshe da zuciya yana sanya karin samun rahama da ludufi .

Huduba ta biyu:

Musulmi yana cika watan ramadana ne yana mai godiya da farin ciki saboda riskan cikan shi yana lullube da rahamar Allah yayin shan ruwan shi ni'man Allah da falalanSa yana mai gaggawa zuwa ga jefa farin ciki a al'umansa, sai ya fitar da zakkan fidda kansa domin tsarkakewa ga mai azumi daga kazanta da wasa kuma ya farantawa talakawa rayi ya wajaba ga musulmi haka kuma ga duk wanda musulmi ke daukan nauyin shi, mikdarin shi shi ne sa'i daga cikin abincin gari.

An karbo daga dan Umar Allah ya kara yarda a gare shi shi da mahaifin shi ya ce :(Manzon Allah ya wajabta zakkan fidda kai sa'i guda na dabino ko kuma sa'i guda na sha'iri bisa ga bawa da da na miji da mace da kuma yaro da babba na daga musulmai kuma ya umarni da a fitar da shi kafin fitan mutane zuwa sallah). Ya halatta gabatar da shi da rana daya ko rana biyu saboda abin da aka rawaito daga ibnu Umar cewa sun kasance suna badawa kafun fita eidi da rana daya ko rana biyu.

Tare da dakatar da sallah da aka yi a masallatai da kuma wuraren sallah na idi saboda wannan annoban an shar'antawa musulmai sallan idi a gidajensu a jama'a ko kuma a daidaiku, kuma za a fara kabarbari ne tun daga faduwan ranar daren idi sannan idan aka sallace ta a gida to sai a yanke kabarbarin tare da shiga salla. Ana sallatanta sifanta ne rak'a biyu ba tare da huduba ba za a yi kabbaran harama a farko sannan a yi kabarbari guda shida bayanta, a rak'a ta biyu kuma za a yi kabbara na tashi sannan kuma a yi kabarbari guda biyar bayanta , lokacin sallar idi na fara shigowa ne tun daga bayan hudowar rana da kuma bullowanta da mikidarin mashi biyu ko kuma da mikidarin abin da bai gaza minti ashirin ba kuma zai ci gaba lokacin nata har zuwa lokacin sallan walaha kafin shigan lokacin sallan azahar da kusan sulusin sa'a, hakika hani ya zo daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi na hani ga sallah a lokacin da rana ke hudowa. 

Allah ya karba mana ayyukanmu na kwarai da ayyukan ku na kwarai.