الأربعاء، 20 مايو 2020

FALALAR SALLAR DARE DA KARATUN ALKUR'ANI

 

اللغة : الهوسا

التاريخ 8/9/1441هـ

Hudubar masallacin Annabi  na shaikh Abdullah Bin Abdurrahman Albuaijan

8/9/1441 AH 1/5/2020 AD

 

Hudubar farko

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya sanya da'a gare shi ya zama dalili ne na samun yardarSa, ya sanya yardarSa kuma a matsayin dalili ne na rabauta da AljannarSa ya kuma datar da mumunai zuwa ga bauta masa, sai suka kauracewa ababan jindadi da sha'awe sha'awensu suka fifita samun yardarSa.

Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya abin godiya abin girmamawa, shaidawar da zan hadu da Allah  da ita a halin ina ni kadai na tilo. Na shaida Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne Allah ya isa Mai shaida. Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa da sahabbansa da aminci abin kari mai yawa.

Bayan haka, lalle mafi alherin zance shine maganar Allah, kuma mafi alherin shiriya ita ce shiriyar Annabinmu Muhammad dan Abdullah, kuma sharrin al'amura sune fararrunta, kuma dukkan bidi'a bata ce, kuma dukkan bata na wuta,

ya ku bayin Allah ina muku wasiya da ni kai na da tsoron Allah Mabuwayi da daukaka, to ita ce wasiyar Allah ga mutanen farko da na karshe, (Hakika mun yi wasiyya ga wadanda muka baiwa littafi kafin ku da ku kan ku da ku ji tsoron Allah).

    Ya ku bayin Allah! Biyayya ga Allah ita ce mafi alherin ganima da abin ribata, kuma yardarSa ita ce mafi alherin riba da abin nema, Aljanna an kewaye ta da abubuwan ki, wuta kuma an rufe ta da abubuwan sha'awa, abin sani za ku samu ladan ku cike a ranar alkiyama, to duk wanda a ka nesatar daga wuta aka shigar Aljanna to hakika ya rabauta.

Ya ku masu azumi!

Allah ya karbi biyayyarku, ya gyara halayenku, ya datar da ku cikin abin da ya rage a wannan wata, ya kuma rubuta muku tabbatuwa  bisa da'a a gare shi a tsawon ranakun zamani.

Ya ku jama'ar musulmi!

Ramadan wata ne na ibada da tuba, watan neman kusanci ne da komawa ga Allah, wata ne  na tuba da dawowa ga Allah da ikhlasi da khushu'i da sujudi da ruku'i, wata ne na azumi da tsayuwa, wata ne na biyayya  da kyautatawa da karatun Alkur'ani.

Ya ku masu azumi!

Karbabbiyar ibada na da tasiri a imani, tasirinta na ga zuciya da rai , gyara niyya da tsarkake rayuka da takawa da ikhlasi da khushu'i  ga Allah Mafi daukaka.

Tasirinta da ke gabbai da jiki; kamewa daga ayyukan sabo da abin da aka haramta da jurewa gun aikata ayyukan alheri da da'a.

To ku sa Allah a idanuwanku cikin ayyukanku, to shi Allah bai dubi ga surorinku ko jikunanku sai dai yana dubi ne ga zukatanku ne da ayyukanku , so da yawa wani mai azumin baida wani abu a azuminshi sai kishin ruwa da yunwa da gajiya sau da yawa wani mai tsayuwan dare bai da wani abu na daga tsayuwan shi sai hana ido barci da wahala.

Ya jama'ar musulmai :

Lallai Allah ya saukar da Alkur'ani a watan azumi  sai yace: (watan ramadana ne wanda aka saukar da Alku'ani yana shiriya ga mutane da hujjoji bayyanannu daga shiriya da rarrabewa) kuma Allah ya ce : (lallai mu muka saukar da shi a daren lailatulkadri ) (wa ya sanar da kai menene lailatulkadri)(lailatul kadri mafi alheri ne  daga wasu watanni dubu) (Mala'iku da Ruhi suna sauka a cikinsa da izinin Ubangijinsu saboda kowane umurni) (sallama ne shi daren har fitar alfajiri) kur'ani ya sauka a daren lailatul kadari na  ramadana zuwa baitul izza a sama ta duniya san nan ya sauka zuwa doron kasa a rarrabe cikin shekaru ashirin da uku  gorgodon abubuwan da ke faruwa da kuma sabuban sauka, to karatun kur'ni a watan da aka saukar da shi , na daga cikin mafificin ayyukan kusanci  saboda haka ne Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana fiskantan karatun kur'ani a cikin watan ramadan Jibrilu ya kasance yana zuwa mishi a ko wani dare a cikin watan ya yi bitan kur'ani da shi .

An karbo daga Ibnu Abbas Allah ya kara yarda a gare su ya ke  cewa:( Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance mafi kyauta cikin mutane kuma kyautansa ya  fi kasancewa ne a watan azumi a yayinda ya ke haduwa da Jibril , jibrilu ya kasance yana haduwa da shi a ko wani dare na ramadan sai ya yi bitan Alkur'ani da shi to Annabi na da yawan kyautan alheri a yayin da ya hadu da shi sama da iska da ake turowa) .

To ya ku bayin Allah ku riki karatun Alkur'ani  ku karanta shi da tajwidin shi kuma ku nemi fahimtar ma'anoninsa ku yi tadabburinsa  , to an karbo daga abdullahi dan Mas'ud Allah ya yarda da shia ya ce : Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbat a a gare shi ya ce:(Duk wanda ya karanta harafi  yana da kyakkyawa , kuma kyakkyawa na da kwatan kwacinta guda goma, ba zan ce alif lal mim harafi ne sai dai alif harafi ne lam harafi ne mim harafi ne) Tirmizi ne ya rawaito shi kuma ya inganta shi , kuma aga gare shi Allah ya kara yarda a gare shi ya ce Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(lallai wan nan alkur'ani wani abin ci ne to ku koya daga wan nan abincin iya iyawan ku lallai wan nan alkur'ani igiyan Allah ne kuma haske ne mai bbayyanawa  komin kuma waraka ne mai amfani kuma kariya ne ga wanda ya yi riko da shi da kuma tsira ga wanda ya bishi ba zai zame ba har ya zama abin zargi, ba zai kuma karkace ba har ya zama abin mikarwa ,kuma abubuwan mamakinsa ba za su kare ba kuma yawan maimaita shi ba zai tsufar da shi ba to ku yi tilawarsa , don lallai Allah zai ba ku lada bisa ga tilawarsa kyakyawa goma ga ko wani harafi amma ni ba zan ce alif lam mim sai de da: alif, da lam, da mim …. )  Dabrani ne ya rawaito .

An karbo daga Abdullahi dan Umar Allah ya kara yarda a gare su ya ce : Mazon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (Ana cewa ga ma'abocin Alkur'ani a ranar alkiyama , ka karanta ka haura kuma ka yi tilawa kamar  yanda ka kasance kana tilawa a duniya domin matsayinka tana a'ayan karshe da ka karantata) Tirmizi ne ya rawaito .

To ku karanta Alkur'ani bayin Allah kar ku kaurace masa , na hore ku da kar  ku da yankewa  alkur'ani, na hore ku kada manta  Alkur'ani don hakan hasara ne da nadama, da juyawan hankali ne da abin zargi.

Muna neman tsarin Allah  da mu kasance  cikin wadan da  Manzon Allah  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  zai kai karan    su wurin Allah ,   sabo da kauracewa kur'ani da suka yi :-  (kuma Manzo ya ce : Ya Ubangijina! Lalle mutanena sun riki wannan Alkur'ani abin kauracewa).

Ya ku bayin Allah ! Mafi girman ambaton Allah Mabuwayi da Daukaka shine Alkur'ani,  barin karanta shi kaura ce masa ne  da kuma juya masa baya Allah madaukakin sari ya ce :- (Duk wanda ya  kauda kai daga ambato na  (Alkur'ani) , to lallai ne rayuwa mai kunci ta tabbata a gare shi  ,kuma  muna tayar da shi a ranar kiyama yana makaho.   Ya ce  Ubangiji '' don me aka tayar da ni makaho , alhali kuwa na kasance mai gani ?  . Y a ce '' kamar wancan ne ayoyin mu suka je maka  sai ka mance su ,  kuma kamar haka a yau ake mance ka.

An karbo daga Abu Musa Al-ash'ari Allah ya kara yarda a gare shi ya ce:- Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :-    (misalin muminin da ya ke karanta kur'ani  kamar misalin tanjarin ne kamshin shi na da dadi dandanon shi ma na da dadi ,   kuma misalin muminin da baya karanta kur'ani  kamar misalin dabino ne, bai da kamshi kuma dandanon sa na da dadi , kuma misalin munafiki da yake karanta kur'ani kamar turaren wuta ne  kamshin shi na da dadi kuma dandanon shi na da dadi) Buhari da Muslum ne suka rawaito .Hakika Magabata sun kasance suna kwadayin karanta kur'ani  da lura da ma'anonin shi  suna da wuridin da suke yi ko wani rana  ba sa yankewa daga gare ta musamman a wannan watan. 

Watan  ramadana da aka saukar da alkur'ani a cikin ta , to ku kwadaici yawaita tilawar sa kada  na'urori na zamani da shirye-shirye masu shagaltarwa su yi gogayya da shi  

  YA KU BAYIN ALLAH:

A halin kuna wannan yanayi to ku nemi magani da waraka   da karatun alkur'ani  domin shi waraka ne da rahama ga muminai .

 Ku dukufa a kan shi a gidajen ku, a lokacin da ku ke kadaicen ku ko a bayyanen ku , ku karanta shi kuma  ku saurare shi a sauran lokutan ku .

Kuma wanda hakan ya mi shi nauyi ,  ko karanta kur'anin ya gagara a gare shi  to, ya saurari tilawar sa , domin shi ma mai sauraron abokin tarayyan mai karantawa ne a lada da sakayya .

Allah yana cewa : (Idan an karanta Alkur'ani to ku  saurare shi  ku yi shuru ko za ku samu rahama)

 

 

HUDUBA TA BIYU

Dukkan yabo da godiya sun tabbata  ga Allah Masanin gaibi Mai yafe zunubai da sauran kusakurai da laifuka , kuma Mai yaye bakin ciki yana  shimfida hanunSa da dare don mai laifin yini ya tuba ,  kuma yana shimfida hanunSa da rana don mai laifin dare ya tuba .

 

 

YA KU BAYIN ALLAH:

Ku yiwa kanku hisabi kafin a mu ku  hisabi , kuma ku auna ayyukanku  kafin a aunaku  kuma kafin ayi kira gare ku : lallai su dinnan ayyukanku ne muke  kididdige  mu ku , sa'annan mu cika muku ita  duk wanda ya samu alheri to, ya godewa Allah , kuma wanda ya samu koma bayan haka to, kada ya zargi kowa sai kansa.   

(Duk wanda ya aikata  wani aiki kyakkyawa kwatankwacin kwayar  zarra zai gani, haka  kuma duk wanda ya aikata mummuna kwatankwacin kwayar zarra zai gani) 

 

 

YA KU BAYIN ALLAH:

Tsayuwar dare kusanta ne ga Allah  ba mai kiyaye ta sai muminai , haka kuma sunna ce da ba mai juriya  a kanta sai masu tsoron Allah ,   (Wadan da suke kwana don Ubangijinsu  suna  masu sujada da tsayuwa )  

Wadan da Allah ya ce  game da su :- (sasannin su  na nisanta daga wuraren  kwanciya ,  suna  kiran  Ubangijin su bisa ga tsoro da tsammani,  kuma suna  ciyarwa daga abin da muka azurta su . )

Sabo da haka  wani rai  bai san  abin da  aka boye  musu ba , na sanyin idanu , domin  sakamako  ga abin da suka kasance  suna aikatawa .

Wadan da Allah ya daukaka su (Lalle masu takawa suna a cikin lambunan ita ce  da maremari. Suna masu karbar abin da Ubangijinsu ya ba su ,  sun kasance  masu kyautatawa  a gabanin  haka (a duniya).  Sun kasance a lokaci kadan na dare suke yin barci . Kuma a lokutan asuba suna ta  yin istigfari)

Bayin Allah lokacin yin Tahajjud cikin dare  shi ya fi sabo da lokuta irin na kusanci Allah Madaukakin sarki ya  ce :- (Lalle ne tashin dare  shi ne  mafi  tsananin natsuwa ,  kuma mafi daidaituwa  ga magana )

Kuma lokaci ne da a cikin shi  Allah yake saukowa zuwa  saman duniya yana kira; shin akwai mai

roko na amsa mishi, shin akwai mai neman gafara na gafarta masa ? shin akwai mai tuba na karbi tubansa ? , kuma lokaci ne wanda ake bude kofofin sama ana amsa adu'a.

 karatun kur'ani shi ne mafi girman kusanci da munini zai  nemi kusanci da shi a wan nan lokaci, maganan Allah da kuma salla, mafi lokacin da kuma bawa ya fi kusa da UbangijinSa shi ne a lokacin da yake sujada (shin, wanda  ya ke mai tawali'u sa'o'in dare , yana mai sujada kuma yana mai tsayi ga sallah yana tsoron  lahira kuma yana fatan rahamar ubangijinSa  ).

Mafificin tsayuwa shi ne tsayuwan dare (sallar nafila) na ramadana, shi ne ya fi karfi a cikin sunnoni kuma na daga cikin mafificin nafilfilu, to an karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (Duk wanda ya yi tsayuwan ramadana yana mai imani kuma da neman lada za a gafarta mishi abin da ya gabata na daga zunuban shi kuma wanda ya yi tsayuwan lailatul kadri yana mai imani da neman lada za a gafarta mishi abin da ya gabata na daga zunubansa) ya zo a ckin sahihu muslim daga Urwatu dan Zubair cewa Ummul mu'minina A'isha Allah ya kara yarda a gare ta ta bashi labarin cewa:( Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya fita cikin dare sai ya yi salla a masallaci , sai wasu mutane su ka bi sallansa suka yi koyi da shi sai  da aka wayi gari sai mutane suka bada labarin hakan sai mutane suka hallara   sama da wadancan sai manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya fito a dare na biyu sai mutane suka yi koyi da sallanSa sai mutane suka wayi gari suna ambaton hakan sai mutane suka cika masallaci a wannan dare na ukun sai Annabi  ya fito ya yi sallah sai mutane suka yi koyi da sallan shi yayin da aka zo dare na hudu masallacin ya kasa daukan jama'a Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sai bai fito ba har zuwa lokacin da aka fita zuwa sallan asubahi yayin da aka kare sallan asuba sai ya juyo ya fiskanci mutane san nan ya yi Tashahhudi (Ashhadu alla ilaha illaallah wa ashhadu anna muhammadarrasulullah) sai ya ce : bayan haka lallai bai boyu mini ba sha'aninku na daren jiya sai de na tsoraci kar a farlanta muku sallan dare ne ku gagara yinta).

Mutane sun kasance bayan haka suna sallatanta  jama'a kashi –kashi, kuma  a daidaiku har zuwa lokacin da Umar dan kaddabi Allah ya kara yarda a gare shi ya hada su a mai karatu guda daya ,

An karbo daga Abdurrahman dan Abdu Alkari cewa ya ce : na fita tare da Umar dan kaddabi a cikin watan ramadana zuwa masallaci sai ga mutane su na warwatse a rarrabe wan nan na salla shi kadansa wasu jama'a  na  koyi da sallan sa , sai Umar ya ke cewa wallahi ; ni ina ganin da kun hada wadan nan mutanen bisa ga makaranci guda daya da zai fi dacewa sai ya hada su ga Ubayya dan ka'ab .

Bayan haka ya ku bayin Allah duk wanda niyarsa ta kasance ta gaskiya gurin azama ga yin salla a daya daga cikin masallatayya biyu masu alfarma,  ko wasunsu na daga masallatayya , amma ; hakan ya gagara yiwuwa a gare shi ko wani abu ya yi shamaki tsakanin shi da hakan sai ya yi salla a gidan sa to lallai ladansa na nan cikakke a rubuce insha Allahu ; domin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ke cewa:( lallai abin sani kawai ga ko wani mutum yana da abin da ya nufa ) kuma ya ke cewa :(Duk mutumin da ya himmatu da aikata wata kyakkyawa bai samu aikatata ba to za a rubuta mishi kyakkyawa guda) Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ke cewa : (Idan bawa ya yi tafiya ko ya yi rashin lafiya to za a rubuta mishi kwatankwacin abin da ya kasance yana aikatawa a halin yana mazaunin gida mai lafiya) .

Hakika Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ke cewa yayin da ya kusanto Madina yana dawowa daga yakin tabuka( lallai a garin Madina akwai wasu mutane da ba ku tafi wata tafiya ba ko kuma kuka keta wani kwari ba face kun yi tarayya da su a lada sai suka ce: ya Manzon Allah ahalin suna Madina ? sai ya ce : E, suna Madina uzuri ne ya hana su )

 to ku yi albishir     

 

  

  

   

ABUBUWAN MAMAKI GUDA 4

 

 
الوصف: cbc250ed-6a0e-4037-8d54-a9eb3d0a0577                                                                                                                           

ترجمة الخطبة

اسم المترجم :أمين سعد عبد الله

اللغة : الهوسا

التاريخ : 15-9-1441هـ

 

Hudubar Masallacin Annabi Na shaikh Ahmad Dalib 15/9/1441AH/7/5/ 2020AC

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah muna gode masa kuma muna neman taimakonsa da gafararsa, muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu, da munanan ayyukanmu, duk wanda Allah ya shiryar da shi babu mai batar da shi, kuma duk wanda ya batar babu mai shiryar da shi, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, na kuma shaida Annabi Muhammad bawanSa ne kuma manzonSa ne. tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa da aminci tabbatacce.

(Ya ku wadanda suka bada gaskiya ku ji tsoron Allah cancancin tsoronSa kada ku mutu face kuna musulmai)

(ya ku mutane ku ji tsoron Allah wanda ya halitta ku daga rai guda kuma ya halitta matarsa daga gare shi ya yada daga gare su mazaje masu yawa da mata, ku ji tsoron Allah da ku ke roko da (sunan) shi. Da zumunci, lalle Allah ya kasance mai tsaro ne a kan ku.)

(ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah ku fadi zance na daidai. zai gyara muku ayyukan ku kuma ya gafarta muku zunubanku, duk wanda ya ke yi wa Allah biyayya da ManzonSa to ya rabauta rabauta mai girma.)

 

Bayan haka, lalle mafi alherin zance shine maganar Allah, kuma mafi alherin shiriya ita ce shiriyar Annabinmu Muhammad, kuma sharrin al'amura sune fararrunta, kuma dukkan bidi'a bata ce, kuma dukkan bata na wuta.

Ku sani ya ku bayin Allah lallai ba makawa bin hanyar zuwa lahira dole sai da ilimi wanda ke yaye wa zuciya makanci, da kuma aiki wanda zai dauke wa mutun shamaki na basira da iklasi wanda zai kubutar da mutun daga hasara na faduwa da kuma tsoro wanda zai sa mutun ya kiyaye bala'o'i na rudi.

 Dukkan halittu matattu ne sai malamai, malamai kuma dukkansu masu bacci ne sai masu aiki, masu aiki kuma dukkansu rudaddu ne sai wanda suke masu  iklasi, su kuma masu iklasi suna cikin wani hadari mai girma (shin , kuma wanda ya kasance matacce, sa'an nan Muka rayar da shi Muka sanya wani haske dominsa, yana tafiya da shi , yana zama kamar wanda misalinsa yana cikin duffai , shi shi kuma ba mai fita ba daga gare su ? kamar wancan ne aka kawata wa kafirai abin da suka kasance suna aikatawa).

Abin mamaki dukkan mamaki ga mutumin da ya ke aiki amma bai damu da sanin abin da ke gaba gare shi ba na daga al'amari ko labari, ko kuma ya nemi sanin abin da zai zo bayan mutuwa gaba gare shi ta hanyar nazari da dubi ga dalilai da kuma wa'azuzzuka da ayoyi da kuma gargadi ba. (shin ba su yi dubi ba a cikin mulkin sammai da kasa, da kuma abin da Allah ya halitta daga kome kuma akwai tsammani kasancewar ajalin su, hakika ya kusanta? to da wani labari a bayansa su ke yin imani) ( wanda Allah ya batar, to babu mai shiryarwa a gare shi kuma yana barin su a cikin batarsu suna dimuwa) abin mamaki ya kaiton makanci irin na zuciyarsa (shin to, ba su yi tafiya ba a cikin kasa domin zukata wadanda za su yi hankali da su da kunnuwa da za su yi saurare da su, su kasance a gare su ? domin lallai ne idanu ba su makanta, amma zukata wadanda ke a cikin kiraza su ke makanta).

Abin mamaki dukkan mamaki ga malamin da ba ya wa'azantuwa da abin da ya sani na yakini sai abin da ya ke gaba gare shi na daga musibu masu girma da kuma abubuwa na cikas da ke gaba masu fadi ya tsorata daga kasala ya gargadu zuwa ga jahadi da kuma aiki (ka ce, shi (Alkur'ani) babban labari ne mai girma. ku, masu bijirewa ne daga gare shi) ya kaiton hijabin idanuwansa (Bone ya tabbata ga masu nakkasawa) (wadanda su ke idan su ka auna daga mutane suna cika mudu)(kuma idan sun auna musu , da zakka , ko da sikeli , suna ragewa)(shin wadancan ba su tabbata cewa lallai su , ana tayar da su ba?) (domin yini mai girma) (yinin da mutane ke tashi zuwa ga Ubangijin halitta).

Abin mamaki dukkan mamaki, ga mai aiki wanda ya sarayar da iklasi ya sarayar da mabudin samun kubuta ta hanyar lalata zuciyarsa  (ka ce, ''Ni mutum ne kawai kamarku, ana yin wahayi zuwa gare ni cewa : lallai ne abin bautawarku Abin bautawa guda daya ne, saboda haka wanda ya kasance ya na fatan haduwa da Ubangijinsa, to sai ya yi aiki na kwarai, kuma kada ya hada kowa ga bautawa Ubangijinsa.) kaito da hasaran faduwan mutum ya rasa riba! (kuma aka halaka dukkan 'yayan itacensa, sai ya wayi gari yana juyar da tafunansa biyu , saboda abin da ya kashe a cikinta , alhali ita tana kwance a rassanta, kuma yana cewa , kaitona dadai ban tara wani da Ubangijina ba!) (kuma wata jama'a ba ta kasance a gare shi ba, wadanda ke taimakon sa baicin Allah, kuma bai kasance mai taimakon kansa ba) abin mamaki dukkan mamaki ga mai iklasi wanda ba ya duba zuwa ga mua'amalar Allah Madaukaki tare da masoyanSa da ManzanninSa wadanda su ne masu nusar da halittu daga wurin Allah sai ya halarto da tsoronsu, ga masoyi na farko yana cewa (kuma a lokacin da Ibrahim ya ce ,''ya Ubangijina! Ka sanya wannan gari amintacce, kuma ka nisata ni ni da 'ya'yana daga bautawa gumakai) ya na shaida tsoron su masoyi cikakke yana ce da shi (kuma an yi wahayi zuwa gare ka da kuma zuwa ga wadanda su ke gabaninka , ''lallai idan ka yi shirka hakika, aikinka zai baci ,kuma lallai za ka kasance daga masu hasara.)

To ya kai mai rudin kansa (To, a yau ba za a karbi fansa daga gare ku ba . kuma ba za a karba daga wadanda su ke kafirai ba makomarku wuta ce , ita ce mai dacewa da ku kuma makomarku din nan ta munana ) (shin, lokaci bai yi ba ga wadanda su ka yi imani zukatansu su yi tawaliu ga ambaton Allah da abin da ya sauka daga gaskiya ? kada su kasance kamar wadanda aka baiwa littafi a gabanin haka sai zamani ya  yi tsawo a kansu , saboda haka zukatansu su ka kekashe, kuma masu yawa daga cikinsu fasikai ne) .

Allah ya sa mini albarka ni da ku a cikin Alkura'ani mai girma .

Huduba ta biyu

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya isa, tsira da aminci su tabbata ga Annabi zababbe da alayenSa da sahabbanSa ma'abota da'a da kuma cika alkawari, da kuma wanda ya bi su da kyautatawa kuma ya bi sawu, lallai Allah ya kira ku da sunan imani kuma da tsoronsa ya kira ku Ya gargade ku game da faduwa irin na mantuwa da kuma radadi irin na hasara ya kuma sanar da ku tserewan yanayi da halaye a ranan komawa, girman tasirin Alkura'ani da an saukar da shi ne a kan duwatsu , ya kuma sanar da ku da kamalan sunayenSa Madaukaki da kyawawa.

(ya ku wadanda su ka yi imani ! ku bi Allah da takawa , kuma rai ya dubi abin da ya gabatar domin gobe, kuma ku bi Allah da takawa lallai Allah , Mai kididdigewa ne ga abin da kuke aikatawa) (kuma kada ku kasance kamar wadanda suka manta Allah shi kuma Ya mantar da su rayukansu, wadannan su ne fasikai) ('yan wuta da 'yan Aljanna ba su daidaita . 'Yan Aljanna su ne masu babban rabo) (Da Mun saukar da wannan Alkura'ani a kan dutse, da lallai ka ga dutsen yana mai tawali'u, mai tsatsagewa saboda tsoron Allahh , kuma wadancan misalai Muna bayyana su ne ga mutane, da fatan za su yi tunani) (wanda ya saukar da Alkur'ani shi ne Allah, wanda babu wani abin bautawa face shi, masanin fake da bayyane, Shi ne Mai rahama Mai jin kai) (Shi ne Allah, wanda babu abin bautawa face Shi Mai mulki Mai tsarki, aminci Mai amintarwa , Mai tsarewa , Mabuwayi , Mai tilastawa, Mai kamun kai, tsarki ya tabbata a gare shi daga abin da suke yi na shirka da shi) (Shi ne Allah, Mai halitta Mai ginawa, Mai surantawa, yana da sunaye masu kyau, abin da ke a cikin sammai da kasa suna tsarkake Shi , kuma Shi ne Mabuwayi , Mai hikima).

Tsarki ya tabbata gare Shi Madaukaki bai halicce ku don wasa ko kuma don kazanta ba sai dai kawai domin ku nemi gafaran Shi kuma domin a muku  rahama (shin, to kun yi zaton cewa Mun halitta ku ne da wasa, kuma lallai ku zuwa gare mu ba za ku koma ba?) (Allah Mamallaki, Gaskiya, Ya daukaka babu abin bautawa face Shi, Shi ne Ubangijin Al'arshi , mai daraja) (kuma wanda ya kira tare da Allah wadansu abubuwan bautawa na daban , ba yana da wani dalili game da shi (kiran) ba , to hisabinsa yana wurin Ubangijinsa kawai lallai ne kafirai ba su cin nasara) (kuma ka ce, ''Ya Ubangijina ! Ka yi gafara Ka yi rahama kuma Kai ne Mafi alherin masu rahama).                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                   

                                                                                                               


LOKUTA MASU DARAJA A KAN YAWAITA AYYUKAN ALHERI A CIKINSU

Hudubar masallacin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi na 22/9/1441 na shaihk Ali dan Abdurrahman Alhuzaifi.

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai.

 

Huduban farko :

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah ubangijin kasa da sammai a hanun shi ne alheru su ke , shi ne kuma wanda ya ke gafarta zunubai yana tunkude mummuna da abinda aka ki ina kyautata yabo ga ubangijina kuma ina gode mishi bisa ni'mominSa masu yawa wanda ba mai iya  kididdige su sai shi wanda muka sani daga cikinsu da wanda ba mu sani ba shi ne ma'aboci falala da kuma kyawawa ,na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya mai amsa addu'o'i , na shaida cewa Annabin mu kuma shugaban mu muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne mai kira zuwa ga  Aljanna masu yawa wanda aka karfafe shi da mu'jizozi, ya Allah ka yi dadin tsira da aminci bisa albarka ga bawanKa kuma ManzonKa Muhammad da iyalanSa da sahabbanSa wadanda suka tsere zuwa ga ayyuka na kwarai.

Bayan haka:

Ku ji tsoron Allah ta hanyan kusantazuwa gare shi da ayyukan yardanSa da kuma nesatan fushinSa da azabansa ta hanyan barin abubuwan da ya haramta.

Ya ku musulmai :

Hakika Allah ya kwarara muku a wan nan wata albarkoki daga cikin albarkatu  da alherori Allah ya yi baiwa a cikin shi da nau'uka na biyayya masu yawa Allah kuma ya kiyaye ku daga abubuwan da suke muharramai da kuma abinda aka ki da abinda Allah ya boye muku na daga lada bayan mutuwa shi ne abunda zai faranta wa mumini rai kuma duk wani mai musabaka a cikin alheri zai yi musabaka zuwa gare shi , Allah madaukakin sarki ya ce (ka ce da falalan Allah da rahamarSa saboda haka su yi farin ciki shi ne ya fi akan abin da su ke tattarawa) sai suka bi kyawawa da kyawawa to ku bi ayyuka na kyawawa da kyawawa ku kasance a kjarshen watan ku kun dada tsananta kokari kun fa girmama neman daidai ku yi kuma nesa daga zunubai da sabo wanda suke bata ayyuka na kwarai ko suke rage ladansu, Allah madaukakin sarki ya ce: (ya ku wadanda suka yi imani ku yi da'a wa Allah ku yi da'a wa ManzonSa kada ku bata ayyukanku) a'aya ubangijin mu mai rahama mai jin kai ya shar'anta mana wasu kofofi na falaloli da ayyuka na kwarai domin mu yawaita alheri dama da muka samu na rayuwa baka san wani aiki ne Allah zai karba ba ya tsiratar da kai daga azaba da shi , Allah Madaukakin sarki ya ce : (ya ku wadanda suka yi imani ku yi ruku'u ku yi sujjada ku bauta wa ubangijinku ku aikata alheri ko za ku samu rabauta)

An karbo daga Abi zarrin Allah ya kara yarda a gare shi ya ce Mazon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(kar ka rena aikin alheri komin kankantan shi ko da ma a ce ka hadu da dan uwanka ne da sakekken fiska) Muslim ne ya rawaito , duk wanda ya nemi rabauta da tsira da kuma rayuwa na dindin din cikin ni'ma dawwamammiya to ya yi aiki na kwarai a cikin wadan nan ranaku masu falala da dararraki masu albarka domin lallai abinda ya shude ba zai dawoba na daga lokaci masu daraja su ne lokaci na ayyuka kuma da tabbatar da alherori na daga burace burace , an karbo daga Abu huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce :Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:( ku gaggauta da ayyuka abubuwa guda bakwai ,shin akwai abinda ku ke jira facetalauci abin mantawa ? ko wadata abin ………? Ko kuma rashin lafiya ? ko kuma tsufa ? ko kuma mutuwa shiryayyiya ? ko kuma dajjal to sharrin abinda ya ke boye da ake jira ? ko kuma tashin alkiyama domin tashin alkiyama shi ya fi zafi shi ya fi bala'I kuma shi ya fi daci )Tirmizi ne ya rawaito kuma ya ce: hadisi ne hasan ku din nan ya jama'ar musulmai kuna goman karshe na ayyukan albarkatoci da kuma  ayyuka ku sani abin la'akari shi ne karshen su kuma lailatul kadri na kaura a cikin wan nan goman ne duk wanda aka datar da shi ya yi tsayuwan darenta to za a gafarta mishi abinda ya gabata na daga zunuban shi , An karbo daga Abu huraira Allah ya kara yarda a gare shi daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (duk wanda ya yi tsayuwan daren lailatul kadri yana mai imani kuma da neman lada za a gafarta mishi abinda ya gabata na daga zunubban shi) Bukari da Muslim ne suka rawaito , alherin ta da albarkatun ta ko wani musulmi na iya riska bauta a cikinta shi ne abinda ya fi na daga ibadan watanni dubu wanda ba a cikin daren lailatulkadri ba Allah ya kebance wan nan al'umma da ita wan nan kuma falalan Allah ne da ya ke bawa wanda ya so Allah ma'abocin falala ne mai girma,ya ku musulmai : ku ku yawaita na daga adu'a da adauke bakin ciki daga al'umma hakika Allah ya muku alkawarin amsa addu'a a wannan wata mai girma kuma ku yi tawakkali zuwa ga Allah da ayyukan ku na kwarai domin lallai hakan na daga cikin sabuba na amsa adu'a ku tsanannta wurin adu'a a wurin rokon Allah ubangiji mai jin kai wurin dauke wan nan annoba  daga kasashe musamman ga kasashen musulmai , kuma ya dauke daga bayin Allah domin Allah ubangijin dukkan komai ne amma dan adam sunada rauni suna da gajiyawa ba su mallaki wani abu ba wa kansu na amfani ko na cutarwa Allah Madaukakin sarki ya ce (Allah ya halicci mutum cikin rauni) haka kuma Allah subhanahu wa ta'ala ya ce:(ku kirayi  Ubangijinku kuna masu kankan da kai da kuma a boye, lalle ne shi ba ya son masu wuce iyaka. Kuma kada ku yi barna a cikin kasa a bayan gyaranta, kuma ku kiraye shi saboda tsoro da kuma tsammani lalle ne rahamar Allah Makusanciya ce ga masu kyautatawa).

Allah ya sa min albarka ni da ku a cikin Alkur'ani mai girma.

 

Huduba ta biyu         

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Mai rahama Mai jinkai Mabuwayi Mai hikima, ina kyautata yabo ga Ubangiji na kuma ina gode masa bisa abin da ya kwarara a gare mu na daga ni'imomi, da kuma tunkude musibu a gare mu da azaba na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya Ma'aboci daukaka da girma, kuma na shaida Annabinmu kuma shugabanmu Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, ma'aboci dabiu na karamci, to ya Allah ka yi dadin tsira da aminci da albarka ga bawanka kuma ManzonKa Muhammad daiyalansa da sahabbansa wadanda suka taimakawa wannan addini mikakke.

Bayan haka ku ji tsoron Allah cancancin tsoronSa, ku yi riko da igiya mai karfi na musulunci.

Ya ku musulmai hakika Ubangijinku ya kirayeku da fadinSa (Ya ku wadanda suka yi imani ku tuba zuwa ga Allah tuba ta gaskiya, mai yiwuwa Ubangijinku ya kankare muku miyagun ayyukanku, kuma ya shigar da ku gidajen Aljanna koramu na gudana a karkashin su, a ranar da Allah bai kunyatar da Annabi da wadanda suka yi imani tare da shi, haskensu yana tafiya gaba gare su da jihohin damansu). Kuma Allah Madaukaki ya ce : ( ku tuba zuwa ga Allah gabadayanku ya ku wadanda suka yi imani ko zaku samu rabauta)

 Hakika Allah ya muku baiwa na tuba a wannan tsanani, lalle kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (lalle Allah ya fi farinciki da tubar bawanSa sama da mutumin da abar hawansa ta bace a cikin jeji ya neme ta har ya gaji sai ya kama barci a karkashin wata bishiya yana farkawa sai ga dabbar tsaye a kan shi, sai ya riki linzaminta ya ce : Ya Allah kai ne bawa na nine Ubangijinka ya yi kuskure sabo da tsaban farinciki.) muslim ne ya rawaito daga hadisin Anas Allah ya kara yarda a gare shi.

Kada ku warware tubanku da abin da ke kishiyantar ta, ku yawaita tilawan Alkur'ani a watan Alkur'ani, domin shi ne kalacen ruhi, zuciya na amfana da shi sama da komai a wannan wata, domin shine anbato mai hikima kuma mai shiryarwa ga tafarki mikakke, shi ne mai hukunci na gaskiya cikin abin da mutane suka saba a cikinsa.

Ya ku bayin Allah! Lalle Allah da mala'ikunSa suna salati ga Annabi ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi da aminci tabbatacce mai yawa.