الأحد، 22 مارس 2020

HAKURI BISA BALA'I


Hudubar Masallacin Annabi na shaikh Abdullahi Bin Abdurrahman Albuaijan  18-7-1441AH /12-3-2020AC
Hudubar Farko:
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Mai amsa adu'a Mai yaye bakin ciki da bala'i ina gode mishi bisa ni'imomi daban daban, muna neman tsarin Allah daga sharrin abin da ya halitta na daga  bala'i da annoba yana sanya shi ga wanda ya so kuma ya tunkude shi daga wanda ya so.
Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke bai da abokin tarayya, kasaita da yabo nashi ne da buwaya da girmame girmame da dawwama da wanzuwa duka nashi ne,  na shaida Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne cikamakin Annabawa ma'abocin isra'i da mi'iraji da tabki da kuma lema, tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi da iyalansa da sahabbansa da wanda ya bisu da kyautatawa a halin sauki da kuma halin cuta.
 Bayan haka:
lallai mafi  kyan  zance shi ne littafin Allah mafi  alherin shiriya  shi ne  shiriyan  Manzon  Allah tsira da amincin Allah su tabbatauma a gare shi mafi sharrin al'amura sune fararrunta, dukkan bidi'a bata ce kuma dukkan bata na wuta.
ya ku bayin Allah : ina muku wasiyya da ni kaina da tsoron Allah, domin ita ce  mafaka, kuma  da bin sunnar  Annabi ne  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ake samun kubuta (Ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah rai ya dubi abin da ya kaddamar sabo da gobe, ku ji tsoron Allah, lallai Allah Masani ne ga abin da ku ke aikatawa).

Ya tawagar musulmai
Duniya gida ce ta musibu da kuma bala'u da kuma jarabawowi da kuma fitintinu  gida ce ta jin zafi da kuma haduwa da ba- zata, gida ce ta radadi da kuma azaba da kuma lafiya da kuma cuta da rashin lafiya da kuma waraka da sauki da kuma bala'i gida ce ta farin ciki da bakin ciki, gida ce ta jin rashin dadi da kuma bacin rai da tsanani da wahalar duniya, kurkuku ce ga mumini kuma aljanna ce ga kafiri, akwai yawan musibu da kuma jarabawowi wanda  Allah ke jarraba mai da'a da fajiri da su, na mumini da kafiri, ba a jira bayan lafiya sai rashin lafiya bayan samarta sai tsufa, bayan wadatuwa sai talauci da rashi, hanyan rayuwa da ba ta canjawa kuma bata sauyawa daga su ne a duk yanda ilimi ya ci gaba aka samu habaka a'aha ko da dan adam ya kaura ne zuwa sarari na sama da kuma wata ko da ya kutsa cikin nitson karkashin kasa da koguna ya zauna a can dole ne zai hadu da tawaya da kuma gazawa kuma ilimi da hankali yana i'itirafi da gazawa irin na duniya.
(ya ku jama'r  aljanu da mutane in kuka samu damar ku fita daga sassan  sammai da kassai to ku fita, baza  ku fita ba sai da karfi ).
Lallai ita ce kudura  ta Allah wacce take tana da girma mashi'arSa da iradarSa  al'marinSa da hikimarSa dukkan wani abu a hanunsa ya ke al'mari nashi ne kafin da bayan, abin da ya so ya ke kasancewa, abin da bai so ba bai kasancewa, ba wani abu da ku ke so face abin da Allah ya so ba'a tambayan shi game da abin da ya ke aikatawa, sai dai al'marin shi idan ya so wani abu zai ce da shi ne kasance sai ya kasance tsarki ya tabbata ga Allah wanda mulkin komai ke hanun shi kuma zuwa gare shi za ku koma .

Ya ku bayin Allah :
Ya dace ga mumini a lokacin tsanani da yalwa da kunci da yalwa da wadata ya tuba zuwa ga Allah ya fawwala al'amarinshi zuwa gare shi ya nemi mafaka a wurin Allah  ya dogara gare shi duk wanda ya dogara ga Allah to Allah ya isam mashi kuma ya sani cewa duk wani abu da ya same shi bai kasance da ya kuskure shi ba duk kuma abin da ya kuskure shi bai kasance da ya sameshi ba abin mamaki da al'amarin mumini dukkan al'amuransa alheri ne a gare shi idan abu mai dadi ya same shi sai ya gode sai ya kasance alheri a gare shi idan kuma cuta ko wani abu mara kyau ya same shi sai ya yi hakuri hakan sai ya zama alheri gare shi (Ba wani abu da zai samu na musiba a doron kasa ko kuma a kan kawunan ku face yana rubuce a littafi kafun a halicce ta lallai hakan  ya ke gudana a wurin Allah, domin kada ku yi bakin ciki bisa ga abin da ya tsere muku ko kuma ku yi farin ciki bisa ga abin da ya zo muku Allah ba ya son mai takama mai  alfahari )
 To ya wajaba a gareku ku yarda ku nemi lada a wurin Allah ku nemi lada daga wurin Allah da sakayya ku mika wuya ga abin da Allah ya kaddarta ya hukunta ku sakankance ladan Allah bisa ga musiba da kuma cuta. Allah ya ce (ka yi albishir ga masu hakuri wadanda idan musiba ta same su sai su ce daga Allah muke kuma gare shi za mu koma wadan nan suna da kyakkyawan yabo daga wurin Ubangijinsu da kuma rahama wadannan su ne shiryayyu).

Huduba ta biyu

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya shar'anta halal da haram, Mahaliccin rayuka da jikkuna ya tunkude musibu da kuma rashin lafiya Mai yin ni'ma ga bayinSa da lafiya daga abubuwa masu bijirowa na dare da wuni daga  cikin bala'i ya sanya mishi rahama da daukaka da  kankaran zunubai daga cikin cuta ya sanya lada da kuma  adana da tsarkaka bisa ga lafiya da waraka ku kasance masu godiya bisa ga bala'i da azaba ku kasance masu hakuri, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabinmu Muhammad amintacce da kuma bisa alayensa da sahabbansa da tabi'ai.

 
Ya ku bayin Allah :

Lallai annoba shi ne abin taimako  ga bakin ciki da kuma tashin hankali sa'an nan da ci baya da kuma tashin tasina gashi ya rikita sashi da yawa na duniya a cikin yan tsirarun kwanaki to ku yi kokari wurin tumbuke shi da kuma iyakance shi, An karbo daga Sa'd dan abi wakkas cewa ya tambayi  Usama dan zaid ya ce menene ka ji daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa game da annoba, Usama sai ya ce na ji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa (Annoba wata tsoratarwa ce ko kuma azaba ce da Allah ke turo ta ga banu isra'ila ko kuma ga wadanda suke kafin ku, to idan kun ji wani abu makamancinta a kasa to kada ku je kasan idan kuma ta faru a wata kasa kuna cikinta to kada ku fita domin guje mata) Muslim ne ya rawaito

Ya tawagan musulmai
Ku ji tsoron yada jita- jita, kage da kuma kambama abu da kuma tsoratarwa da isgilanci ku gode wa Allah bisa ga lafiya kada ku kai kanku ga bala'i ku ji tsoron sabuban yaduwar cuta da kuma wuraren annoba ku roki Allah lafiya da waraka da sauki  ku katangu da zikirori da adu'oyi duk wanda ya yi fata a wurin Allah ba zai yi hasara ba, ku gujewa kaddaran Allah zuwa wata kadarar Allah ku kankan da kai zuwa ga Allah kada kuma ku yanke tsammani daga rahamar Allah.

** ya ma'boci bakin  ciki lallai  bakin ciki yana  yayewa ****
** albishirinka  da  alheri domin mai yaye bakin ciki shi ne Allah ****
**shi yanke tsammani wani sa'i ya kan katse ga ma'bocin shi****
**kar ka yanke tsammani domin Allah shi ne mai isarwa ****

** Allah yana kawo sauki bayan bakin ciki****
**kar ka gaza ka gajiya lallai mai yayewa shi ne Allah****

**idan an jarrabeka to ka zama kana da aminci da Allah ka yarda  da shi****
**lallai wanda ya ke yaye bala'i shi ne Allah****

**idan Allah ya hukunta kawai ka mika wuya bisa ga kudurarSa ****

**mutum baida wani hila ko dabara cikin abin da Allah ya hukunta ****

**na rantse da Allah ba ka da wani koma bayan Allah ****

**Allah ya isan maka a ko wani abu kana da Allah ****

** ya ma'aboci bakin ciki lallai bakin ciki abin yayewa ne ****

** albishirinka da alheri lallai mai yaye bakin ciki shi ne Allah ****

Ya Allah Mai yaye bakin ciki ya mai amsa adu'a ka yaye mana bala'i ka dauke mana cuta ka gaggauto mana da waraka ka hore mana magani ba abin bautawa da gaskiya sai kai, tsarki ya tabbata a gare ka, mu mun kasance cikin wanda suka yi zalunci
Ya Allah ka tunkude mana tsada da annoba da riba da zina da girgizan kasa da bala'u da mummunan fitina abin da ya bayyana daga gare ta da abin da ya boyu daga gare mu musamman haka ma da sauran garuruwan musulmai baki daya.
Ya Allah ya Mai bada mulki makwarkwadan mu na hanunka hukuncin mu a hanunka ya ke abin da ka hukunta game da mu shi ne a'dalci muna neman tsari gareka daga mummunan kaddara da kuma fadawa kololuwa na tsiya da dariya na makiya da kuma saukan bala'i da yaduwar annoba , ya Allah ma'aboci  kasaita da girmame girmame ya Mai saukar da kyauta kai ne ka isar mana madalla kuma da abin dogaro ka gyara mana sha'ninmu gaba daya kar ka kyale mu zuwa ga kawunan mu ko da kebtawan ido ne muna rokonka amincin da bayansa babu jirkita  , da yarda wanda bayansa ba fushi da kuma yaye bakin ciki wanda bayansa ba bakin ciki , ya Alla gareka muka dogara kuma zuwa gareka muka mika wuya kuma zuwa gareka ne za mu koma muna neman tsarinka daga sharrace- sharracen kawunanmu da kuma sharrin ko wace dabba da kai ke rike da makwarkwadanta .                  
  

ALLAH MAI TAUSAYI NE GA BAYINSA


Hudubar Masallacin Annabi Na shaikh Ahmad Dalib 25/7/1441AH/ 20/3/2020AC
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah muna gode masa kuma muna neman taimakonsa da gafararsa, muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu, da munanan ayyukanmu, duk wanda Allah ya shiryar da shi babu mai batar da shi, kuma duk wanda ya batar babu mai shiryar da shi, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah,shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, na kuma shaida Annabi Muhammad bawanSa ne kuma manzonSa ne.tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa da aminci tabbatacce.
(Ya ku wadanda suka bada gaskiya ku ji tsoron Allah cancancin tsoronSa kada ku mutu face kuna musulmai)
(ya ku mutane ku ji tsoron Allah wanda ya halitta ku daga rai guda kuma ya halitta matarsa daga gare shi ya yada daga gare su mazaje masu yawa da mata, ku ji tsoron Allah da ku ke roko da (sunan) shi. Da zumunci, lalle Allah ya kasance mai tsaro ne a kan ku.)
(ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah ku fadi zance na daidai. zai gyara muku ayyukan ku kuma ya gafarta muku zunubanku, duk wanda ya ke yi wa Allah biyayya da ManzonSa to ya rabauta rabauta mai girma.)

Lalle zance mafi gaskiya shine littafin Allah,  kuma  mafi kyaun shiryarwa  shi ne shiryarwan Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, mafi sharrin al'amura shi ne  fararrun su , kuma dukkan fararrun abubuwa bidi'a  ne  , kuma dukkan bidi'a bata ce  , kuma dukkan bata na wuta 
Bayan haka:
Ya ku mutane
Ku sani lalle Ubangijinku Allah ne wanda ba abin bautawa da gaskiya sai shi,ya yalwaci dukkan komai a rahama da ilimi, ya halicci dukkan komai ya kaddara shi kaddarawa, ya iyakance dukkan komai a adadi, ya gudanar da shi gudanarwa,
Ya yi ludufi da abin da ya so cikin abin da ya ke so zuwa ga wanda ya so. Ya kasance da boyayyiyar kaddararSa da iliminSa mai zurfi goni ne Mai tausayi  ga abin da ya boyu na daga halittunSa , da kuma zartarwa ga hukuncin sa .
 Ya yi ludufi da basirarSa bisa ga abin da ya ke na gani na hakika sai ya riske shi, yayi ludufi   da jinSa ga boyeyyen sautuka  sai ya tantance su , ya yi ludufi da ilimin sa   ga abubuwan da suke kananu  masu halartowa a zuciya  sai ya  banbance su ,
    (Wanda ya fari halittan sammai da kasa,  ta yaya zai kasance yana da Da a halin  bai da mata , kuma  ya halicci  dukkan komai  a hali kuwa shi masani ne ga dukkan komai. Wancanninku shi ne Ubangijin ku ba abin bautawa da gaskiya sai shi  mahaliccin dukkan komai , to ku bauta mishi lallai shi  wakili ne ga dukkan komai,  gani ba ya riskan shi  a hali  kuwa shi  mai tausayi ne goni ).

(Kuma ku boye fadin ku ko ku bayyana shi , lalle shi masani ne  ga abin da ke cikin kiraza . Ku saurara ashe , bai sani ba ; wanda ya yi halitta alhali kuwa shi Mai tausayi ne  goni).
Ya yi ludufi ga abubuwan da suka boyu na wahayin sa  tun daga mulakutin sammai da ayoyinSa da ake karantawa wanda aka sauke su a rarrabe ga matayen Annabi ma'abota dakuna tun daga Baitul Izza har zuwa gidan Annabtaka
(Ku tuna abin da ake karantawa a gidajenku na daga ayoyin Allah da hikima kuma lalle Allah Mai ludufi ne mai bada labari).
Ya zartar da ludufin al'amarin shi, ruwa daga sararin sama zuwa doron kasa inda ba tsirrai ko shuka, ya shayar   da shi zuwa ga tsirrai   da jijiyoyin itace masu koshi da ruwa ya isar da ruwa mai dadin sha ga lambuna.

(Ashe ba ka ga Allah ya saukar da ruwa daga sama  sai kasa  ta zama koriya  lallai Allah mai ludufi ne kuma goni).
Ya zartar da ludufin shi cikin halittun shi  da irin ludufi na halittan sa  zuwa ga  mai raya bitane ya fitar da su, da tsanani irin na jiki  sai ya halaka ta,  da kuma  gungu mai yawa sai ya rarraba su, kuma da dunbin  dukiyaya halaka ya wargaza shi,  Ya yi shawagi  ga wuyan jabberawa  sai ya kaskantar da su,  da lafiya na yanayin su sai ya illantar da ita, da tabbatattun kafafuwan su sai ya zamar da su, ya daga benaye abin daukakawa sun  tsawaita da runduna  abin karfafawa, da masu yawan ibada da masu bauta  da masu keta iyaka da masharrata.
Ya haura zuwa ga  biranen rayuka masu cunkoso da jikuna da suke hade babu sauti na motsin kafa ko  shafa, kamar ba a rayu ba a jiya.
Ya yi gaba da masoya ya muamalance su da halin  makiya, sai suka zama sun yanke masa zumunci sun yi nesa da shi, sai shamaki ya katange tsakanin masoya juna.suna yiwa rogo kallon kitse tamkar yadda mai jin kishi ya ke kallon kawalwainiya.
Ba don komai ba sai don wani abu da ya faru daga gare mu, da wani abu da ya dauke daga gare mu, kada ku zaci cewa makiyi ya yi galaba ne, sai dai Mai kiyayewan ne (Allah) ya juya baya. Ko zasu kankan da kai, ko zasu komo, ko zasu wa'azantu.
Tsatsan zukata ta yawaita, to sai Masanin gaibi  ya tausasa, duk abin da ya yi tsauri zai yi rauni, kuma duk abin da ya yi taushi zai yi tsauri, domin Allah ya dauraye wadanda suka yi imani ya koke kafirai. Kuma ya san wadanda suka yi nifaka.kuma ya dauki fansa daga wadanda suka yi laifi ya warkar da zukatar muminai,kuma ya riki masu shahada a cikin su, lalle Ubangiji na Mai ludufi ne ga wanda ya so. lalle shi Masani ne Mai hikima.    

Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya isa, tsira da aminci ga AnnabinSa zababbe, da iyalansa da sahabbai ma'abota biyayya da wafa'i, da wanda ya bi da kyautatawa ya bi sawunsu.
Bayan haka ku ji tsoron Allah cancancin tsoronSa, duk wanda ya ji tsoron Allah zai sanya masa mafita kuma ya azurta shi ta inda bai zata ba. (Duk wanda ya dogara ga Allah to shi ya isan masa, Lalle Allah Mai iyar da umarninSa ne,) Lalle Allah ya sanya ma'auni ga dukkan komai.(Wanda ya ji tsoron Allah zai sanya masa sauki cikin al'amarinsa) (Wanda ya ji tsoron Allah zai kankare masa laifukansa kuma ya girmama ladansa.)
     Ya ku musulmai!
Allah Mai tausayi ne ga bayinSa yana tausaya wa mai karamin karfi dalilin mai rauni cikin halittu, ko da masu karfi sun ki, yana zartar da ludufinSa mai zurfi ga kaskantacce a cikin bayinSa ko da masu izza sun ki, yana azurta wanda ya so Shi Mai karfi ne Mabuwayi tsarki ya tabbata a gare shi,.. yana karanta ni'imomi masu yawa ga bayinSa kuma ya habaka kadan na daga da'a ga bawanSa,
Iya gwargwadon zurfin ludufi iya gwargwadon riskarsa, shine wanda in ka kira shi zai amsa ma, in ka nufe shi zai baka mafaka, kuma in ka kaunace shi zai kusanto ka, kuma idan ka masa da'a sai ya saka maka, idan ka saba masa sai yana iya baka waraka , idan ka juya masa baya sai ya kira ka, idan ka kusanto shi sai ya shirye ka.
Yana sakanya a gare ka in ka kyautata yana yafiya a gare ka in ka gajarta duk wanda ya rusuna a gare shi zai daukaka shi wanda ya nuna bukatuwa zuwa gare shi zai wadata shi ba ya bukata daga masoya wasu hanyoyi ko kuma sabuba umarninSa kusantarwa ne haninSa kuma ladabtarwa ne kyautanSa zabi ne haninSa adana ne matattaran ludufanSa tausasawa ne da kusantarwa shi makusanci ne mai amsawa duk wanda ya shaida Allah  ga  zuciyansa to zai dauke masa duk wasu abubuwa masu yawa mafi ludufi da kuma mafi girman shi mafi darajan shi da daukakan shi shi ne ya yi  ludufi cikin bayinSa ta hanyan taimakawa a cikin kaddara kuma da yarda da kuma tawali'u da  tuba da kankan da kai da komawa da rusunawa da imani.
Bayan  haka ya ku bayin Allah
Ku sanya gidajenku alkibila ku tsaida sallah ku yi da'a  ga wanda Allah ya jagorantar da al'amuranku a gare su cikin da'a wa Allah ku yi sallah ku yi salati da aminci bisa ga alkibila mafi tsarki da kuma mashaya na farin ciki da kuma  Annabi mafi daukaka da kuma waliyyi mafi kusa shugabanmu Muhammadu Annabi Ummiyi hakika Allah ya zabe shi, lallai Allah da mala'ikunSa suna salati ga Annabi .


السبت، 1 فبراير 2020

FALALAN MUSULUNCI DA WAJABCIN SHIGANSA


Hudubar Masllacin Annabi na Sheikh Ahmad Bin Dalib 6-6-1441Ah 31-01-2020AC
Hudubar farko
 Ya ku musulmai!
Ku sani ba wani abu da ya ke mafi kamala da cika kamar abin da Allah  tsarki ya tabbata a gare shi  ya cika mana ya kammala mana shi ya kuma jingina shi mabuwayi da daukaka ga kansa kuma ya yarda da shi ga masu karamci, Allah Mabuwayi da Daukaka ya ce :  (A yau na cika muku addininku kuma na cika muku ni'imata a gare ku ni na yardar muku musulunci addini gare ku)
Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bayyana shi cikakken bayani, ya jinginta shi ga kansa mai daraja,  ya kafa tushensa da asasinsa, ya fifita abin da ya ke na dole da abin da ke biye da shi, da abin da ke tawaye shi, da abin da ke warware shi, kuma lalle shi gaskiya ne bayyananniya, kuma hanya mikakkiya da tafarki madaidaici, kuma shiryarwa ne mabayyaniya,kuma shi ya fi cancanta da bi a yi hakuri a kansa har zuwa gamuwa da Mafi iya mahukunta zartar da hukunci, Allah Tabaraka wa Ta'ala ya ce :  (Ya ku wadannan mutane in kun kasance cikin shakku daga addini na to ni ba zan bautawa wadanda ku ke bautawa ba, ba Allah ba,sai dai ni ina bautawa Allah wanda ya ke karbar rayukanku, kuma an umarce ni da na kasance cikin muminai.ka tsayar da kanka ga addinin totar kada ka kasance cikin mushrikai. Kada ka bautawa wani ba Allah ba, abin da ba zai amfane ka ba, ba zai cutar da kai ba, to muddin ka yi haka to lallai kana cikin azzalumai.Idan Allah ya sa ma cuta to ba mai yaye ma sai Shi, in ya nufe ka da alheri ba mai ije falalarSa rahamarSa na samun wanda ya ga dama daga bayinSa, Shi Mai gafara ne Mai jinkai. Ka ce ya ku mutane hakika gaskiya ta zo muku daga Ubangijinku, to duk wanda ya shiryu don kansa, kuma duk wanda ya bata to hakika ya bata ne ga kansa kawai.Ni ban kasance wakili ba a kanku. Ka bi abin da aka yi wahayi a gare ka kuma ka yi hakuri har Allah ya yi hukunci shi ne, mafi alherin  mahukunta.

        Allah ya riki alkawarin annabawa da mabiyansu bisa imani da shugabanmu  Muhammad  cikamakin Annabawa da manzanni da imani da abin da ya zo da shi daga Ubangijin talikai, Allah Matsarkaki ya ce :  ( Kuma alokacin da Allah ya riki alkawarin annabawa :"Lalle ne ban baku wani abu ba daga littafi da hikima, sa'an nan wani manzo ya je muku, mai gaskatawa ga abin da yake tare da ku, lalle ne za ku gaskata shi, kuma lalle ne za ku taimake shi," ya ce : shin kun tabbatar, kuma kun riki alkawari Na a kan wannan a gare ku?" suka ce : " mun tabbatar" ya ce : "To ku yi shaida, kuma Ni a tare da ku ina daga masu shaida. To wadanda suka juya baya a bayan wannan, to, wadannan su ne fasikai.Shin wanin Addinin Allah suke nema, alhali kuwa a gare shi ne wadanda ke cikin sama da kasa suka sallamawa, a kan so da ki, kuma zuwa gare shi ake mayar da su.)
To duk wanda ya cika yana da sakayya mafi cika, kuma a bashi rabo biyu daga rahamar Allah Daukakakke Mafi daukaka, Allah Madaukakin sarki ya ce : ( Ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah, ku yi imani da ManzonSa zai baku rabo biyu daga rahamarSa, kuma ya sanya muku wani haske wanda ku ke yin tafiya da shi, kuma ya gafarta muku, kuma Allah Mai gafara ne Mai rahama.Domin kada ma'abota littafi su san cewa lalle basu da ikon yin  komai ga falalar Allah, kuma ita falalar ga hannun Allah kawai take, yana bayar da ita ga wanda ya so, kuma Allah Mai falala ne Mai girma.)
        Musulmai su suka fi dacewa da wannan ribanyawar da haske da gafara, sabo da su ne suka yi imani da dukkan Annabawan Allah da manzanninSa, kamar yadda Ubangiji Mabuwayi da daukaka ya bada labari game da su, a fadinSa : ( Manzo Allah ya yi imani da abin da aka saukar zuwa gare shi daga Ubangijinsa da muminai, kowannensu ya yi imani da Allah da mala'ikunSa da littatafanSa da manzanninSa, ba mu rarrabewa a tsakanin daya daga manzanninSa, kuma suka ce :Mun ji mun yi da'a, (muna neman) gafararka ya Ubangijinmu, kuma zuwa a gare ka makoma take).
Wannan al'uma ita ta fi karancin al'umu ajali kuma ta fi su lada, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Misalinku da misalin ahlul kitabi kamar mutum ne ya dauki 'yan kodago ijara yace : wa zai mini aiki daga safiya zuwa rabin wuni na bashi kiradi guda? Sai yace : wa zai min aikin daga rabin wuni zuwa lokacin la'asar akan kiradi? sai  nasara suka yi, sannan sai yace :Wa zai min aiki daga la'asar zuwa faduwar rana a kan kiradi biyu? To sai ku kuka amsa  sai yahudawa da nasara suka yi fushi suka ce : yaya mu da muka fi aiki kuma ladanmu ya fi karanta ? sai Allah ya ce : shin ko na tawaye muku hakkinku? Sai suka ce : a'a, sai yace : to wannan falala ce na kan bawa wanda na so,)
Wannan al'uma ita ce ta zo karshe a zamani a duniya, amma kuma ita  tafi daukaka a duniya da lahira, kamar yadda Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Allah ya batar da wadanda suke kafin mu daga rabauta da juma'a, sai ranar asabat ta zama ga yahudawa, ranar lahadi kuma ta nasara,  sai mu Allah ya shiryar da mu ga ranar juma'a, ya kuma sanya juma'a sannan asabat sai lahadi, to haka nan zasu zama su suke baya gare mu ranar alkiyama, mu ne na karshe a duniya amma na farko a ranar alkiyama).
Sai Allah ya hada mana a wannan Addini na tafarkin masoyin shi Ibrahim da sunnar zababbanSa Muhammad tsakanin kamalar fiskantar Allah da sauki gurin bautawa Allah, shine Addini mafi soyuwa a gurin Allah,  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Mafi soyuwan Addini a gurin Allah shine Addinin hanifiyya mai sauki,)
     To dadi ya tabbata ga mutumin da Allah ya hada masa tsakanin tafarki na musulunci da daidaituwa akan sunnan mafificin halittu, mafificin tsira da aminci su tabbata a gare shi, Ubayyu bin Ka'ab ya ce : "ku riki tafarki da sunna, sabo da ba wani bawa da zai zama kan tafarki da sunna da zai  ambaci Allah to sai idanuwansa su cika da hawaye sabo da tsoron Allah, sannan wuta ta taba shi,to haka nan ba wani bawa da zai zama kan tafarki da sunna da zai  ambaci Allah Mai rahama to sai tsikan jikinsa ya tashi sabo da tsoron Allah face ya kasance tamkar itaciya ce da ganyenta sun bushe, to haka zunubansa zai rika karkadewa kamar yadda ganyen wannan itaciyar kekarkadewa ya  zube. Kuma lalle tsakaitawa a kan sunna ya fi alheri bisa ijtihadi bisa sabanin tafarki da sunna,"  
To duk wanda ya kasance kamar haka kuma Allah ya tseratar da shi daga alfahari da girman kai da jiji da kai da riya to zai cinma buri ko da kuwa aikinsa kadan ne,
Abu Darda'u ya ce : (Ina ma da barcin masu hankali da wayo da shan ruwansu za su yi kamunga ga kwana ba barci  da azumi na wawaye, misalin kwayar zarra na ibada na mai da'a ya fi daraja a kan ibadan masu ruduwa da aikinsu).
   Allah ya sa min albarka ni da ku a cikin Alkur'ani mai girma Allah ya amfane ni da ku da abin da ke ciki na daga ayoyi da ambato mai hikima.
Ina fadin magana ta wannan kuma ina nema wa kai na da ku gafarar Allah, to ku ma ku nemi gafararSa lalle shi mai gafara ne mai jinkai.

Huduba ta biyu

     Allah Mabuwayi da Daukaka ya ce :  (Allah ya shaida ba abin bautawa da face shi, mala'iku da ma'abota ilimi sun shaida yana tsaye da adalci, ba abin bautawa face shi, Mabuwayi Mai hikima. Lalle ne addini a wurin Allah shine musulunci, kuma wadanda aka bai wa littafi basu saba ba face a bayan ilimi ya zo musu, bisa zalunci a tsakaninsu, kuma wanda ya kafirta da ayoyin Allah to lalle ne Allah Mai gaugawar sakamako ne. To idan sun yi musu da kai sai ka ce : Na sallama fiska ta ga Allah kuma wanda ya bi ni (haka) kuma ka ce ga wadanda aka baiwa littafi da ummiyai, "shin kun sallama"? to idan sun sallama, hakika sun shiryu, kuma idan sun juya to kawai abin da ke kan ka shine isarwa, kuma Allah mai gani ne ga bayinSa. Lalle ne wadanda suke kafirta da ayoyin Allah, kuma suna kashe annabawa  ba da wani hakki ba, kuma suna kashe wadanda ke umarni da yin adalci daga mutane to, ka yi musu bushara da azaba mai radadi.wadannan ne wadanda ayyukansu suka baci a cikin duniya da lahira, kuma basu da wasu mataimaka.  

الجمعة، 24 يناير 2020

SAKAMAKO MAI DACEWA


Hudubar Masllacin Annabi na SheikhAbdulmuhsin Bin Muhammad Alkasim  15-5-1441AH 10-1-2020 A
Hudubar farko
Sakamako mai dacewa
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, muna gode masa kuma muna neman taimakonsa
Muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu  da munanan ayyukanmu, duk wanda Allah ya shiryar babu mai batar da shi, wanda ya batar kuma babu mai shiryar da shi, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya,kuma na shaida Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa. Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabbansa da aminci tabbatacce mai yawa.

Bayan haka, ku ji tsoron Allah -ya ku bayin Allah- cancancin tsoronSa, ku yi murakabarSa a halin sirri da ganawa,
Ya ku musulmai!
Allah ya kagi halittar halitu sai ya kyautata abin da ya sana'anta, tsarki ya tabbata a gare shi ya kuma kyautata addininSa da abin da ya shar'anta, Mai hikima ne kuma Masani, Adili ne Mai jinkai, cikin halittarsa da umarninSa akwai sunnoni da basu sabawa ko sauyawa game da halittunSa, daga ciki akwai sakawa bayi  daidai da ayyukan da suka yi, in na alheri to da alheri in na sharri to da sharri, (Sakamako mai dacewa) da kaddara da sharia duk sun yi taron dangi bisa hakan, Allah Madaukakin sarki yace : (To wanda ya aikata wani aiki  gwargwado nauyin zarra na alheri to zai gan shi. To wanda ya aikata  wani aiki  gwargwado nauyin zarra na sharri to zai gan shi).
Allah ya gandaya ladaddaki masu yawa ga ayyukan alheri wanda yake irin su kuma daidai da su, sakayyar kan kasance daga jinsin da'ar , shehun musulunci Ibnu Taimiyya  Allah ya masa rahama ya ce: (sakayya a ko yaushe daga na kasancewa daga jinsin aikin da  mutum ya yi ne).kuma babu wata sakayya ga wanda ya kyautata sai kyautatawa Allah Madaukakin sarki yace : (shin kyautatawa na da wani sakamako face kyautatawa).
Wanda ya kiyaye dokokin Allah da hakkokinSa to Allah ma zai kiyaye shi a duniya da lahira, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: (ka kiyaye Allah sai Allah ya kiyaye ka) Tirmizi ne ya rawaito
Idan bawa ya nemi shiriya da gaskiya sai Allah ya shiryar da shi Allah Madaukakin sarki yace : (Wadanda suka bi shiriya sai Allah ya kara musu shiriya).
Cika alkawarin Allah na daga cikin imani da shi da kuma da abin da ManzonSa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya zo da shi, sakayyarsa shine Allah na saka wa ma'abocinsa da aljanna. Allah Madaukakin sarki yace : (kuma ku cika alkawari na zan cika muku naku alkawarin)
Wanda ya gaskata Allah sai Allah ya karrama shi da abin da ya ke so da kuma kari Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: (muddin ka yi wa Allah gaskiya to zai gaskata ka.) Nasa'i ne ya rawaito. Ibnu kayyim  Allah ya masa rahama ya ce: (Bawa bai da wani abu da ya fi amfani kamar gaskiyarsa ga Ubangijinsa, duk wanda ya mu'amalanci Allah da gaskiya cikin dukkan al'amuransa sai Allah ya mishi abin da ya fi abin da ya ke yi wa waninsa na kyautatawa).
Iya gwargwadon kusantar bawa ga Ubangijinsa ta hanyar da'a da ibada iya kusancin Allah gare shi, Allah Madaukakin sarki ya ce a  hadisul kudusi : : (muddin bawa na ya kusance ni da taki to zan kusance shi da zira'i, idan ya kusance ni da zira'i zan kusance shi da ba'i) Buhari ne ya rawaito.
Bawa na da abinda ya zata daga ubangijin sa in alkairi ne to zai samu alheri in kuma ya munana zato to zai samu kwatankwacin haka manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (ina inda bawa na ya zace ni) bukari ne ya rawaito
Kuma tauhidi shi ne tushen alheri da sa'ada duk wanda ya hadu da Allah da shi to zai rabauta da aljanna Aa farkon lamari ko karshen sa Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : Allah madaukakiun sarki ya ce (ya dan adam da za ka zo mini da cikin kasa na kusakwarai sannan ka hadu da ni ba ka hadani da wani to da zan zo maka da cikin kasa na gafara  )tirmizi ne ya rawaito
Duk wanda ya kyautata a wan nan duniya da imani da tauhidi to a lahira yana da aljanna da ganin ubangiji mai daukaka Allah Madaukakin sarki ya ce : (ga wadanda  su ka kyautata suna da kyakkyawa da klari ) sallah na da kofa a cikin aljanna da za a rika kiran masu yinta daga gare shi saboda sheki na gabban alwala  da tsarki za a gane wannan alumma ranar alkiyama da shi Mnzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce(lallai aluamma ta za a kira su ranar alkiyama suna masu hasken goshi da kafafuwa sakamakon gurbin alola ) bukari da muslim ne suka rawaito
(kayan ado da bawa  ya ke sawa yana isa ga mumini har inda alolan sa ya isa ) muslim ne ya rawaito
Mai kiran sallah ya na daga muryanshi da shelantawa na sallah sai sakayyarsa  ya zama daga jinsin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi (mai kiran sallan shi ne mafi tsawon wuya a mutane ranar alkiyama )  muslim ne ya rawaito (ba wanda zai ji iya sautin mai kiran sallah aljani ne ko mutun  ko itaciya ko dutse face ya yi mishi  shaida ranar alkiyama  ) bukari ne ya rawaito Allah ya yi izini a daukaka masallatayya a ambaci ku sunan shi a cikin su  duk wanda ya gina wa Allah masallaci alhlin yana nemar  yardan Allah to Allah zai gina mishi kwatan kwacin shi  a alja) bukari da muslim na su ka rawaito
Kuma sadaka dalili ne na imani kuma rance ne abin ribanyawa a wurin Allah  duk wanda ya ciyar da wani abu to Allah zai maye  mishi  da abinda ya fii shi na alheri
Manzon Allah tsira da amincin Allaah su tabbata a gare shi ya ce :(Allah madakakin sarki ya ce : ya kai dan adam ka ciyar zan ciyar da kai ) bukari da muslim ne suka rawaito
(ba wata rana da bayi za su wayi gari a cikin shi face malayiku biyu sun sauka dayansu sai ya ce ya allah duk mai ciyarwa ka maye mishi daya kuma ya ce : ya allah duk mutumin da ke kame hanu to ka bashi lalatacce  ) Bukari da muslim ne su ka rawaito
  (ku ci ku sha ababan farin ciki sakamakon abin da ku ka gabatar a ranakun da su ka shude )
Mujahid Allah ya mishi rahama yace : (Ta sauka ne akan masu azumi). Za a kirayesu ne ta kofan rayyan kuma warin baskin mai azumi ya fi kamshin turaren almiski a wurin Allah
 Duk wanda ya mutu yana halin ihrami to za a tashi yana mai talbiya,
Ambaton Allah na raya zukata kuma yana sa karfin jiki, ma'abotansa basu da sakayya da ya fi Allah ya ambace su, Allah Madaukakin sarki ya ce : (ku ambace ni zan ambace ku)    Duk wanda ya ambaci Allah a wani hali to Allah zai ambace shi a hali mafi kyau Allah Madaukakin sarki ya ce a hadisin kudsi (Ni ina tare da shi idan ya ambace ni, idan ya ambace ni a zuciyarsa sai na ambace shi a zuciya ta, idan kuma ya ambace ni cikin jama'a ne to sai na ambace shi a jama'ar da suka fi alheri a kan su.) Buhari da Muslim ne suka rawaito.
Majalisai na zikiri dausayi ne na aljanna, bawa na da abin da ya ke so a cikinta gun Ubangijinsa, wasu mutane uku suka fiskanto Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, dayansu sai ya ga wani wuri a majlisin sai ya zauna a wurin amma dayan sai ya zauna a bayansu, amma na ukun sai ya juya baya ya tafi sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace :Ase ba zan baku labari game da mutanen nan uku ba? Shi na farkon su ya nemi mafaka a gurin Allah sai Allah ya ba shi, shi dayan kuma sai ya ya ji kunya sai Allah ma ya ji kunyarsa, amma dayan sai ya juya baya sai Allah ma ya juya masa baya. Buhari da Muslim ne suka rawaito.
Addini daukaka ne ga ma'abotansa, to duk wanda ya taimaki addinin Allah to shi wanda zaa taimaka wa ne  Allah Madaukakin sarki ya ce :(Lalle Allah zai taimakawa wanda ya taimaki addininSa)
Wanda ya nusar ga alheri to yana da lada kwatankwacin ladan wanda ya yi aikin, kuma wanda ya sunnanta wata sunna kyakkyawa to yana da ladanta da ladan wanda ya yi aiki da ita har zuwa ranar alkiyama.
Kuma jarabawa sunnar Allah ce a halittunSa, kuma girma sakayya na ga girman jarabawar, duk wanda ya rungumi kaddara ya yarda to yana da yardar Allah, wanda ya yi fushi kuma zai hadu da fushin Allah.
Hakuri wajibi ne a umarni da hani da kuanyar shiga Aljannama kaddara, duk wanda ya jure ya yi hakuri to Allah zai bashi juriya da hakuri, duk wanda ya nemi sanin Allah a halin sauki to  Allah zai kawo mishi dauki yayin tsanani.
Gyaruwan al'uma na ga ilimi, :(wanda ya bi wata hanya yana mai neman ilimi to Allah zi saukake mishi da shi hanyar zuwa aljanna.)Muslim ne ya rawaito shi.
Dukkan dan Adam mai kuskure ne kuma mafi alherin masu kuskure sune masu tuba).

   
Wanda Allah ya datar da shi zuwa ga tuba sai ya fiskanci Allah yana mai tuba to Allah zai karbi tubansa kuma ya bashi lada  Allah Madaukakin sarki ya ce : (wanda ya tuba bayan zalunci da ya yi ya kuma gyara to Allah zai karbi tubarsa.
 Mumini idan mutuwa ta zo mishi sai a mishi albishir da yardar Allah da karamarSa, to sai ya zama ba wani abu da ya fi soyuwa a gare shi sama da abin da ke gaba gare shi sai ya kaunaci gamuwa da Allah sai Allah ma ya so haduwa da shi,  duk wanda ya muamalanci halittu da alheri sai Allah ya muamalance shi da kwatankwacinsa a duniya da lahira. Kuma mafi karamcin halittu shine Annabinmu Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, duk wanda ya mishi salati guda to Allah zai mishi guda goma, Ansarawa (sahaban Annabi na madina) ba mai son su sai mumuni, wanda ya so su Allah zai so shi.
Kuma Allah na tausayawa masu tausayi ne cikin bayinSa, duk wanda ba ya tausayawa mutane to Allah ma ba zai tausaya mishi ba, Manzo Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (wanda bai tausayi to ba zaa tausaya mishi ba) Buhari da Muslim ne suka rawaito.
Wata mace mazinaciya ta tausaya wa kare sai Allah ya mata rahama ya gafarta mata.
Wadanda suka fi dacewa da kyautatawa sune 'yan uwa makusanta, wanda ya sada zumuncinsa sai Allah ma ya sada masa.
Akwai aminci cikin sallama wa mutane, Manzo Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (ku yada sallama za ku samu aminci) Ibnu Hibban ne ya rawaito.
Wadanda ya kankan da kai sabo da Allah to zai daukaka shi, Allah bai karawa bawa wani abu sabo da yafiya face buwaya, Allah Madaukakin sarki ya ce : (su yi rangwami su yi afuwa shin ba ku son Allah ya muku gafara ne).

Ibnu kasir Allah ya mishi rahama yace : (To lalle sakayya na daga jinsin irin wannan aiki to kamar yadda zaka yafe wa wanda ya ma laifi kai ma za a yafe maka haka nan kamar yadda ka yi rangwami kai ma za a ma rangwami ).
Duk wanda ya kaunaci wani bawa don Allah to Allah zai kaunace shi, haka duk wanda ya yi wa dan'uwansa adu'a a bayan idonsa to sai mala'ikan da aka wakilta da shi ya ce :amin kai ma Allah ya baka kwatankwacinsa.
Kuma buda wa wani a majlisai  sakayyarsa na daga jinsinsa,     Allah Madaukakin sarki ya ce : (ya ku wadanda suka yi imani da Allah idan an ce da ku ku buda a majlisai to ku buda Allah zai buda muku).
Duk wanda ya yafe wa musulmi to Allah ma zai yafe masa kurakuransa ranar alkiyama.
Allah na kasance wa tare da mutum kamar yadda mutum ke tsayawa dan'uwansa musulmi,
Manzon Allah tsira da amincin Allaah su tabbata a gare shi ya ce :(Duk wanda ya tsaya wurin biya wa dan uwansa bukata to Allah ma zai kasance cikin biya masa bukata, duk wanda ya yaye wa musulmi wani bakinciki to Allah ma zai yaye masa bakinciki daga bakincikin ranar alkiyama, duk wanda ya rufa asirin wani musulmi to Allah ma zai rufa asirinsa ranar alkiyama)Buhari da muslim ne suka rawaito.
(duk wanda ya yassara wa mara galihu to shi ma Allah zai yassara mishi duniya da lahira. Allah na taimakon bawa muddin bawa na taimakon dan'uwansa) Muslim ne ya rawaito.
Duk wanda ya yafe wa halittu  shi ma Allah zai yafe masa, duk wanda ya 'yanta bawa, Allah zai 'yanta shi daga wuta gaba a madadin gaba. Duk wanda ya ci bashin dukiyar mutane yana nufin ya biya to Allah zai biya mishi, duk wanda ya wadatu da Allah da kuma abin da ya bashi to, to Allah zai wadata shi kuma ya isan mishi, Manzon Allah tsira da amincin Allaah su tabbata a gare shi ya ce :(Duk wanda ya nemi wadatar Allah to Allah zai wadata shi) Buhari da Muslim ne suka rawaito.
Idan mutum ya kame kai daga haram da rokon mutane to Allah zai sanya shi ya zama mai kame wa, Manzon Allah tsira da amincin Allaah su tabbata a gare shi ya ce :(Lalle ne duk wanda ya nemi ya zama mai kamun kai to Allah zai maida shi mai kamewa.) Buhari da Muslim ne suka rawaito.
Ba wani bawa da zai tausayawa wani bawa face shi ma Allah ya tausaya masa, Manzon Allah tsira da amincin Allaah su tabbata a gare shi ya ce :(Ya Allah duk wanda ya jibinci wani abu na jagoranci a cikin al'umata ya kuma tausaya musu to ya Allah ka tausaya masa.) Muslim ne ya rawaito.
 Alheri na zuwa da alheri ne, ta daya hanun kuma shi ma sharri na zuwa da sharri ne, to sakayyar mummuna ita ce mummuna kwatankwaciyarta. (Kuma ba a saka muku face da abin da ku ka kasance kuna aikatawa.)
Wanda zuciyarsa ta makance daga ganin gaskiya sai Allah ya makantar da ganinsa a Matattara, (Kuma wanda ya kasance a nan makaho to a lahira yana makaho kuma mafi bace wa bisa tafarki).
Duk wanda ya kaucewa gaskiya bayan ya santa to Allah zai karkatar da zuciyarsa daga shiriya ya jefa mishi shakku da tabewa.  (Kuma a yayin da suka karkace sai Allah ya karkatar da zukatansu).
Bijirewa alheri da addini karshensa tube rigar imani ne,  
Allah Madaukakin sarki ya ce : (kuma hakika idan aka saukar da wata sura sai sashinsu ya yi dubi zuwa ga sashi(su ce), shin wani mutum yana ganinku? Sa'anan kuma sai su juya. Allah ya juyar da zukatansu, domin hakika su mutane ne da ba su fahimta.)
Duk wanda ya bar da'a  ya shakala yinta da gangan to Allah zai tabar da shi ya mantar da shi kansa ya bar shi cikin azaba, Allah Madaukakin sarki ya ce : (sun mance  Allah sai ya manta da su)
Lalacewar badini akibar ta kara lalacewar, Allah Madaukakin sarki ya ce : (A cikin zukatansu akwai wata cuta sai Allah ya kara musu wata cuta.)
Duk wanda ya yi shamaki wa basirarsa daga addini to Allah zai masa shamaki daga ganinsa ranar sakayya, Allah Madaukakin sarki ya ce : (A a ha lalle ne su a wannan ranar abin shamakacewa ne daga Ubangijinsu).
Shirka shine mafi girman zunubi  to duk wanda ya ta'allaka zuciyarsa da wani abu ba Allah ba sai a kyale shi da shi, duk wanda ya nufi riya ko sum'a  neman a ji da aikinsa  sai a saka mishi da irin aikin shi, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce : (Duk wanda ya yi sum'a(neman aji) to sai Allah ya sa a ji shi wanda ya  yi riya sai Allah ya mai da shi mai riya) Buhari da Muslim ne suka rawaito.
Mai bauta wa wanin Allah tababbe ne a duniya da lahira,
 Allah Madaukakin sarki ya ce : (kuma suka riki gumaka baicin Allah domin su kasance mataimaka a gare su. A aha za su kafirta da ibadar su kuma su kasance makiyansu.)
Wanda ya yi wani aiki ya hada Allah da wani a cikinsa sai Allah ya bar shi da shirkansa, wanda ya kasance yana bautawa wani abu baicin Allah to zai bi shi cikin wutar jahannama, duk wanda ya rantse da wani addini bisa karya koma bayan musulunci to ya koma kamar yadda ya ambata, duk wanda ya suranta sura zaa azabtar da shi da ita ranar alkiyama, kuma a kallafa masa da ya busa masa rai, kuma ba zai iya busawa ba, duk wanda ya nemi yardan mutane wajen fusata Allah, to Allah zai yi fushi da shi kuma ya sanya mutane ma su yi fushi da shi, duk wanda ya tsani haduwa da Allah da Allah to Allah ma ya tsani haduwa da shi, duk wanda ya nufi ya yi kaidi da yaudara da makirci da hila ga addini to Allah zai mishi daurin talala kuma in ya tashi ya mishi kamun ba zata, Allah Madaukakin sarki ya ce : (su ka yi makirci kuma Allah ya shirya musu sakamakon makircinsu Allah shi ne ya fi makirai sakamakon makirci ) kuma ya ce : (suna  yaudaran Allah shi kuma ya na maida musu   yaudaran su )
Wanda ya jinkirta salla Allah zai jinkirta shi  Manzon Allsah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (wasu mutane ba za su gushe ba suna yin jinkiri har sai Allah ya jinkirta su ) muslim ne ya rawaito  duk wanda ya ki yin sujjada a duniya sai a hana shi yinta ranar alkiyama  Allah Madaukakin sarki ya ce (ranar da ake  yayewa ga makengema kuma a kira su zuwa ga sujjada ba za su samu daama ba )(gannansu ta na wulakance saboda wulakanci tana lullube su ana kiransu a duniya zuwa sujjada alhalin sauna masu lafiya ) girman kai shi ne dagun kai a kan gaskiya ga halittu sai a tada ma'botan shi kamar kwayan zarra mutane na taka su duk wanda ya yi karya guda daya da ta yadu to lallai Allah ranar alkiyama zai juya muka mukinsa zuwa keyasa mazinata wani harshen wuta zai rika zuwa musu tun diga kasansu Allah ya na debe albarkan riba  maciyinshi kuma za a rika wurwurishi da duwatsu a cikin bakin shi  ranar alkiyama duk wanda ya boye ilimi Allah zai sanya mishi linzami irin linzami na wuta ranar alkiyama duk wanda ya ci gululi zai zo da abinda ya ci na gululi ranar alkiyama duk wanda ya hana saurar ruwa Allah zai ce da shi ranar alkiyama a yau zan hana ka falalata kamar yanda ka hana abinda ba hanunka ne ya aikatashi ba duk wanda ya sha giya a duniya san nan bai tuba ba to an haramta mishi ita ranar alkiyama wanda ya sanya alhariri daga cikin maza a duniya to ba zai sanya ta ba a lahira wanda kuma ya yi da'awa irin da'wa na karya domin ya kara dukiya ba abinda zai kara mishi a wurin Allah sai talauci butulcewa ni'ma yana shelanta gushewanta Allah ba ya canja wani abu na ni'ma tare da mutane da jin dadi na rayuwa har sai sun canja daga kawunan su da zalunci da sabo izgilanci da addini da ma'botan addini sakayyansa na daga jinsinsa wanda ya yi izgilanci ga bayin Allah Allah ma zai mar izgili alaman munafiki shi ne kin mutanen madina na daga nasarawa wanda kuma ya ki su Allah zai ki shi duk wanda ya kashe rayi tare da wani abu to za a rika azabtar da shi da wannan abun har ranar alkiyama , mai sata na miji ya shinpida hanunshi ne akan barna saboda haka ta cancanci a yanketa ,duk wanda ya yi kazafi wa kuyangansa ko kuma bawansa alhali kuma shi ya barranta daga wannan to za amishi bulala ranar alkiyama za a kafawa   mahayinci tuta wanda za a sanshi da shi a ranar alkiyama duk wanda ya la'anci wani abu wanda wannan abun bai cancanci hakan ba to la'nan zata dawo kanshi Allah ya tsine wa wanda ya tsine wa iyayenshi zalunci duhhai ne ranar alkiyama duk wanda ya yi zalunci gorgodon kaidi na taki Allah zai nadeshi daga kassai guda bakwai
Yanke zumunci na makusanta yafi muni akan waninsa Allah yana cewa ga mahaifa (ba ki yarda na sadar da wanda ya sadaki ba na yanke wanda ya yankeki ba ) bukari da muslim ne suka rawaito Allah ya yi alkawarin narkon azaba ga wadanda suke azabtar da mutane ba tare da hakki ba Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (lallai Allah yana azabtar da wadanda suke azabtar da mutane a duniya ) muslim ne ya rawaito riskar da cutarwa da wahalarwa ga halittu karshensa baya haifar da da mai ido Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (duk wanda ya cutar to Allah ma ya cutar da shi duk wanda ya wahalar to shi ma Allah ya wahalar da shi) tirmizi ne ya rawaito , duk wanda aka bawa wani abu na jagoranci na musulmai sai ya kuntata musu ko kuma ya shamaki tsakaninshi da su gameda bukatunsu to Allah ma sai ya yi shamaki tsakaninshi da shi duk wanda ya bibiyi al'auran mutane to Allah ma zai bibiyi al'aurarsa har sai ya kunyatashi a gidansa mai cin nama yana kekketa mutuncin mutane da harshensa zai zo ranar alkiyama yanada farata daga karafunan nuhas bagwanja yana pippige fiskansa da su wanda ya ji zancen wasu mutane wanda suke suna kin hakan za a kwararamishi a kunnenshi harsashi na narkakken dalma ranar alkiyama garin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi amintacce ne duk wanda ya bada tsoro ga mutanenta Allah ma zai tsorata shi wanda ya kasance yanada mata biyu ya karkata zuwa ga dayansu zai zo ranar alkiyama tsaginshi a karkace idan bawa ya bude kofan roko to Allah zai bude mishi kofan talauci rowa da kamkame hanu yana goge albarka kuma yana wajabta tsananin hisabi Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (kada ka kididdige Allah ma sai ya kididdige maka) bukari da muslim ne suka rawaito
Bayan haka ya ku musulmai :
Allah mai dubi ne ga bayinsa kuma yana dakonsu a madakata kuma zai sakanya wa kowa abunda ya aikata sakayya na daga jinsin aikin wanda ya yi daidai da shi a alheri ne ko na sharri kamar yanda ka ke hisabi kaima za amaka hisabi duk wanda ya nufi ya san makomansa a wurin Ubangijinsa to ya duba abinda ya ke da shi a wurin Allah domin Allah yana saukar da bawa ne inda bawa ya saukar da kansa
Ina neman tsarin Allah daga shaidan abin jifa
Duk wanda ya yi aiki na kwarai to don kansa wanda kuma ya munana to don kansa Ubangijinka bai zama mai zalunci ba ga bayi Allah sa mini albarka ni da ku a cikin alkur'ani mai girma

                     Huduba ta biyu
dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah bisa kyautatawansa dukkan godiya bisa ga datarwansa da kuma baiwansa , na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya ina mai girmama sha'ninsa na shaida cewa annabin mu Muhammad bawansa ne kuma manzonsa ne tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalanshi da aminci tabbatacce mai kari

ya ku musulmai
duniya gida ne na aiki lahira kuma gida ne na sakayya Allah ya kan gaggauto wa bawansa da wani sakayya a nan duniya shi ni'man da ke hade da godiya ga ma'bota da'a albishir ne  , su kuma musibu tare da hakuri daukaka ne ko kankaran zunubai , amma mai sabo wanda ya juya baya to idan an jarrabeshi to wannan ukuba ce da gaggawa abinda ya ke gurin Allah shi ya fi tsanani idan kuma an jinkirta ukubarsa to jinkirin da Allah ya misahi kamar  daurin talala ne
sannan ku sani Allah yana umurtan ku da salati da aminci ga annabin sa.              

LOKACIN HUNTURU GA MUSULMI


Hudubar Masllacin Annabi na Sheikh Salah Bin Muhammad Albudair  22-5-1441AH 17-1-2020 AC
Hudubar farko
Ya ku musulmai
Hunturu ya sauka gare ku bayan shudewar bazara mai tururi, busa irin na jaura ya kada muku bayan hurawan garji, tsananin sanyi ya zo muku bayan gushewar yanayin zafi.
(Allah yana juyar da dare da yini, lalle ne a cikin wannan akwai abin lura ga masu basira.)
To ku yi lura da ido na basira cikin shanin girman Allah da ikonSa da halittarSa, ku yi tunani game da hunturu da gajimare da ruwan sama, ku yi lura ga yayyafi da mamakon ruwa, ku dubi yadda yankin  gajimare ke saukowa ga girgije mai girma, ku yi dubi zuwa ga duwatsu masu sanyi da garuruwa masu kankara, da birane da sanyi ya mamaye su da fari fari, ku yi tasbihi ga Allah Mahalicci Masani Mai girma,Wanda ya kirkiri duniya ya samar da ita, kuma ku ba komi ba ne face wani yanki dan kadan daga halittanSa na ban mamaki mai ban tsoro, to ku girmama Allah cancancin girmamawanSa ku ji tsoron tsananinSa da azabanSa ku kame daga saba masa da rena shanin hakkinSa .
Ya ku musulmai
Hakika hunturu ya zo da karfinsa da tsananinsa da kuma tsaurinsa, to ku kiyaye daga sanyi domin yana kankarar da gine-gine kuma yana rusa jiki yana tsofatar da tsoffi , Rabi'u Bin Dabi'u ya ce : (Idan hunturu ya zo to ku dundumani domin tsoho hunturu na lalata sha'nin sa)
 wani kuma ya ce : (Hunturu ya zo ga shi ba ni da rigan sanyi, *** tsananin  sanyi kuma abokin jayayya ne  ba a maida shi  sai dai ana mishi garkuwa).
An rawaito cewa Umar Allah ya kara mishi yarda ya ce : (lallai hunturu ya zo kuma shi makiyi ne to ku kimtsa masa kimtsawa na daga fata da huffofi da safanni, ku riki fatu ya zama rigan waje da 'yar ciki, domin lallai sanyi makiyi ne mai saurin shiga jiki mai wuyan fita).
Ya ku iyaye da kuma majibinta al'amura  : ku tausaya wa 'yan yaran ku da jariranku  ku tufatar da su ku musu rahama, to ita rahama ba a a cire ta  sai daga zuciyan shakiyyi, kuma sau dayawa akan samu baba da ya kaurace wa 'yayansa ya daina ciyar da su, sabo da sabaninsa da matarsa ko wacce ya sake ta, baya tufatar da su alokacin bazara ko hunturu ko idi baya basu ciyarwa ko ya kyautata musu sai wasu bare sun musu sadaka da makusanta, to wani irin kekashewar zuciya ce wannan wani irin tsauri ne wannan wani irin hankali ne wannan wani irin tunani ne  ya sa wannan baba azzalumi ja'iri ne wanda ya wofantar da yaransa ya kyale su ya yada su ya barsu su ka daidaice!?  wani maula ( Bawa) ya ce ga Abdullahi dan Amr Allah ya kara yarda a gare shi : (lallai ni ina so na zauna wata guda a wannan gari na baitul-makdis sai ya ce da shi : shin ka barwa iyalanka abin da zai ciyar da su na wannan wata ?  sai ya ce: a'a , sai ya ce : to koma zuwa ga iyalanka ka bar musu abincin su,Lallai ni na ji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa : (ya isa laifi ga mutun ya wofantar da wanda ya ke ciyarwa ) Ahmad ne ya rawaito da Abu Dauda , a wurin muslim kuma : (ya isa laifi ga mutun da ya buya daga wanda ya ke mallakan ciyarwansa)
Ya ku musulmai !
Ba abin da ya fi tsanani kamar gagaran daukan nauyin hunturu da kuma ta'azzara a gare ka na tufatarwa a halin kuma kana da laruran haka kana bukatan shi, mutun nawa ne cikin talakawa suka gagara rigan sanyi da za su sa ko mayafi ko abun lullubuwa ko kuma abun karyawa ko kuma magani ya gagare su ko na yaransu ba za su iya samun kudinsa ba, an ce da wasu mai ka tanadar wa sanyi sai ya ce : (tsawon karkarwa da kadawan jiki da kekasawa).
 To ku tuna masu rauni da talakawa da miskinai da wadanda mazajensu suka rasu suka barsu na daga mata da marayu da kuma mabukata, ku tuna 'yan gudun hijira da wadanda suke yasassu da kuma wadanda aka kora daga garuruwansu wanda sanyin hunturu ya bugesu kankara ya lullubesu, iska mai tsanani ya kakkashe su, talaka yana kuka mai rauni yana neman taimako wanda yake halin kaka ni kayi yana ta kururuwa hanunsa ya kuntata (baida abinda zai ci) kokawansa ya yi girma tsananin sanyi na hunturu ya sauka gidan sa dattijo ya kwana yana sandare, Mumunai su ne makukusantan mutane da rahama da shafaka da tausayawa da kyautatawa su suka fi tausayawa ga talakawa kuma da yatimai da miskinai su suka fi bada kulawa ga wadanda mazajensu suka mutu suka barsu da ku wadanda aka sake su da kuma masu rauni sune suka fi tausayawa wadanda suke masu tsananin bukata kuma suka fi amfanar da wadanda suke cikin kunci da bakin ciki ba wani abu da suke da shi da zai ishe su ba mafaka da za su fake to ku bibiyesu ku bincikesu ku taimaka musu ku lullubesu da mayafai da fatu ku agaza musu da hanyoyi na jin dumi .
Tausayawa da kyautatawa daga musulmi ga dan uwan shi musulmi shi ne abu mafi girma na dumamawa ga wanda ba yi da abin dumi .
An karbo daga Abu sa'id Alkudri Allah ya kara yarda a gare shi ya ce yayin da muna cikin halin yanayi na tafiya tare da Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi sai wani mutumi ya zo akan abar hawansa sai ya rinka juya ganinsa yana kallo dama da hagu sai Manzon  Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ke cewa: (To duk wanda ya kasance yana da wani sauran abin hawa to ya taimaka da shi ga wanda bai da abin hawa, wanda ya ke da wani saura na  guzuri to ya taimaka ga wanda bai da guzuri) sai ya ambata nau'uka daban daban na dukiya abin da ya  ambata har muka ga cewa wani bai da wani hakki a cikinmu akan wani abin da ya karu kan bukatu a dukiyansa, muslim ne ya rawaitoshi
Ya ku musulmai !
Karamci a lokacin hunturu da tsanani da ciyarwa da kyautatawa idan har an samu karanci na guzuri da abinci da yawan fari abu ne mai daraja kuma  abun girmamawa ba masu siffantuwa da shi sai mutane masu yawan kyauta da tausayawa Allah Mabuwayi ya ce  :(ko  kuwa ciyarwa, a cikin yini ma'abucin yunwa, ga maraya ma'abucin zumunta, ko kuwa wani matalauci ma'abucin turbaya).
      Ibrahim Annakha'i yake cewa : a irin ranakun da abinci yana da wahala a wannan ranan .
Muhammad dan Abdus bamalike ya yi sadaka a wani daren hunturu da kiman amfanin gonansa gaba daya alhali kuma kimansu ya kai dinari dari na zinari ya ce ban yi bacci ba a daren saboda bakinciki game da talakawan al'umman Muhammad,
 Darfat binul Abd yake cewa : mu a lokacin hunturu muna kira ne ( kowa da kowa) tawaga tawaga *** ba a gani mai gayyatan abinci  a cikinmu yana kiran daidaiku  .
Kansa' ta ce Allah ya kara yarda a gare ta a lokacin da take wakan juyayi ga dan uwanta sakhr : lallai sakhr din nan shi ne mai kula da mu kuma shi ne shugaban mu lallai sakra din nan a lokacin da aka yi hunturu mai yawan soke dabba ne.
Aus binu hajar yake cewa : masu suka ne a wurin yaki sa'annan kuma masu ciyarwa ne ga baki*** idan sararin samaniya ya yi fatsi fatsi saboda tsananin sanyi
Shi kuma kars : shi ne tsananin sanyi mai ratsa jiki
Wani yake cewa : dan uwan hunturu bakonsa ya san cewa abin da ke tukunyarsa  *** zai yawaita kuma zai yi dadi
Wani kuma yake cewa : dan uwan hunturu tukunyansa ba ya gushewa  *** yana zuba a cikinsa sannan kuma yana fita.
Ku yi kyauta, ku yi sadaka, ku ciyar da mayunwaci da wanda ke cikin talauci  mayunwaci, ku shayar da wanda ya fada cikin tsananin kishi da mai jin kishi kuma ku tufata da mukamukinsa ke karkadawa jijiyoyin wuyansa ke girgizuwa saboda tsanani sanyi ku bibiyi makobtanku da  wanda suke muku hidima da ma'aikata da makusanta da talakawa da masu rauni da masu kiwo a sahara ba mumini ba ne mutuminda zai koshi makobcinsa na cikin yunwa ku toshe yunwan miskini da bukatansa da talaucinsa  , an karbo daga a'yisha Allah ya kara yarda a gare ta ta ce  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (lallai Allah yana renon dabinon dayanku da lomansa kamar yanda dayanku yake rainon irinsa har ya zame kaman dutsen uhudu) Ahmad ne ya rawaito
Ina fadin abinda kuke ji ina neman gafaran Allah kuma ku nemi gafaranshi domin shi lallai mai yawan  karban tuba ne kuma mai gafara .
Huduba ta biyu
Ya ku musulmai
A lokacin hunturu ne mutane ke neman jin dumi daga sanyi da wuta suna jin dadin shi kuma suna kewaye shi kuma su kunnashi a gidajensu da gonakinsu da kuma shemominsu kamar shi ne iyayan itacensu , abincinsu kuma abinda ke hadasu
Wuta ita ce 'ya'yan itace da ake ki lokacin hunturu duk wanda ya ke son cin 'ya'yan itace na hunturu to ya ji dumi Allah mabuwayi da daukaka yake cewa (wannan wuta din mun sanyata a matsayin tunatarwa ne da kuma jin dadi ga mutane da suke matafiya) duk wanda ya ruruta wutansa ya kunnata ya yi dafu da ita ya dafa masa ya ji dumi ya rike shi kaman abin hira ya amfana da ita to kar ya bar gaushi  ko wuta a makamashin ko abin sanya gaushin face ya kashe ta a dare ne ko wuni tsoron gobara ko shakewa (da hayakinta) domin wuta fa makiyi ne da ba a sa mar linzami tartsatsinsa kan fire baa kuma amintuwa da harshensa,
  
Daga ibnu Umar Allah ya kara yarda a gare su daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya ce : kar ku bar wuta a gidajenku yayin barci) Buhari da Muslim ne suka rawaito.
Daga Abu Musa Al'Ash'ari Allah ya kara yarda a gare shi  yace an yi gobara a wani gida ya kone da mutanen gidan a garin Madina cikin dare a yayin da a ka labartawa Manzon Allah tsira da amincin Allah su game da shaninsu sai yace : ( Lalle ita wuta makiyiya ce a gare kum to idan kun zo barci to ku kashe ta ) Buhari da Muslim ne suka rawaito.
Haka ma na'urorin jin dumi na wutan lantarki  in an tsoraci zafin wutan nata ko tururin nata to an shar'anta da a kashe ta bayan kammala bukata da ita, a yi nesa da wayoyinta  daga shinfidi da tufafi da fefofi da yara don gujewa hatsura da aukuwan mummunar abin da ba a zata ba.
Ku yi salati da aminci ga Ahmad mai shiryarwa mai ceton bayi kaffataninsu.