الجمعة، 24 يناير 2020

FALALAN GARIN MADINA


Hudubar Masllacin Annabi na SheikhAbdullah Bin Abdurrahman Abuaijan   29-5-1441AH 24-1-2020 A
Hudubar farko
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, muna gode masa kuma muna neman taimakonsa muna neman gafararsa
Muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu  da munanan ayyukanmu, duk wanda Allah ya shiryar babu mai batar da shi, wanda ya batar kuma babu mai shiryar da shi, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya, yana halitta abin da ya so kuma ya zabi abin da ya so, wanda ya kagi sammai da kasa, komai a kaddare ya ke a gare shi, na shaida Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne amintacce, cikamakin Annabawa da manzanni, ya isar da sako, ya sauke amana  ya kuma yi nasiha ga al'uma, ya yi jahadi don Allah cancancin jahadi har mutuwa ta zo mishi, Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabbansa baki daya.
Bayan haka,
Mafi alherin zance shine maganar Allah, mafi alherin shiriya shi ne koyarwar Annabi Muhammad, mafi sharrin al'amura shine fararrunsu, kuma dukkan bid'ah bata ce, kuma dukkan bata na wuta.
Ya ku bayin Allah ku ji tsoron Allah cikin umarninsa ku hanu daga abin da ya yi hani a kai ya kuma tsawatar. Ku sani duk wani babba da karami abu ne rubutacce a littafi  (ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah kuma rayi ya yi dubi ga abin da ya gabatar don gobe, ku ji tsoron Allah lalle Allah Masani ne ga abin da ku ke aikatawa)
Ya ku jama'ar musulmai!
Allah kan zabawa fifiko mahalli da wuri kamar yadda ya ke zaba mishi lokaci da zamani, da ahali, da mataimaka, hakika Allah ya fifita awasu sassa a doron kasa sai suka zama sune mafi daukakan garuruwa kamar yadda ya sanya makka masaukar wahayi, kuma alkibla ga musulmai, kuma ya sanya ta uwar alkaryu kuma gari mai aminci da masallaci mai alfarma, gurin da zukatan mumunai ke karkata zuwa gare shi.
Garin Madina ya samu daukaka ne sabo da hijiran Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, a nan ne musulunci ya yadu, ana ce da shi Daiba
Zama ya yi dadi a cikinshi tsakanin duwatsun shi biyu harami ne kuma shi ne masulala na I'mani da mafakarsa da masaukinsa kuma da makoncinsa da mabinnansa
Ya ku bayin Allah :
Hakika Allah ya daukaka garin madina ya fifitashi kuma ya umarci annabinsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da ya yi hijira zuwa gare shi ya haramta abinda ke tsakanin duwatsun shi biyu ya tsine wa duk wanda ya yi barna a cikin shi kuma kokuma  ya bada mafaka ga mabarnaci a cikin shi to ku bawa garin hakkin shi kuma ku ji alhurman da ya ke tattare da shi  an karbo daga Anas Allah ya kara yarda a gare shi daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Madina  harami ne daga kaza zuwa kaza ba a'a yanke itaciyansa ba a'a farsar da barna a cikinsa to duk wanda ya farar da barna a cikinsa to tsinuwan Allah ta tabbata a gare shi da mala'iku da mutane baki daya) Buhari ne ya rawaito
An karbo daga A'mir dan Sa'ad daga baban shi ya ce :Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (lallai ni na haramta tsakanin duwatsun garin madina guda biyu da atsinke kayansa ko a kashe abin farautansa ) Muslim ne ya rawaito
Kuma an karbo daga Aliyu Allah ya kara yarda a gare shi lallai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (garin Madina haram ne daga  A'ir zuwa kaza duk wanda ya farar da barna a cikinsa to tsinuwan Allah ta tabbata a gare shi da Mala'iku da mutane baki daya ba za a karba mishi nafila ko farilla ba ) Buhari ne ya rawaito
Ya jama'ar musulmai
Madina masulala ne na i'mani Allah ya ambace shi da gida da kuma i'mani, a cikinsa ne alkura'ani ya yi ta sauka mai dumbin yawa, a ciki ne aka shar'anta hukunce hukunce, rukunnai suka kafu, zaman lafiya ta tabbatu,   
   Daga nan ne tutocin musulunci suka taso a ka bude garuruwa, Allah ya daukaka addininSa ya taimaki bawanSa ya rusa makiyanSa,
Daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Lalle imani na sulalewa zuwa Madina kamar yadda maciji ke sulalewa zuwa raminsa.) Muslim ne ya rawaito.
Madina sulke ne mai bada kariya, kuma garkuwa ne mai tsawo, ya kore kazantarsa yana tsarkake mai dadinsa, mala'iku na tsaronsa daga kofofinsa, firgicin Masih-Addujjal ba zai shige shi ba, ko annoba, daga Anas dan Malik, Allah ya kara yarda a gare shi daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Ba wani gari face dujjal zai taka shi face Makkah da Madina, ba wani kofa daga cikin kofofinta face Mala'iku na jere cikin sahu suna kare su, sannan Madina zai kada da mutanen cikinsa girgizawa uku, sai Allah ya fitar da duk wani kafiri da munafuki,) Buhari ne ya rawaito.
Daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (A kofofin Madina akwai Mala'iku annoba ko dujjal ba zai shiga garin ba) Muslim ne ya rawaito.
Ya ku bayin Allah ! ma'abocin Kazanta ko kaidi bai da mazauni a garin Madina, amincin Allah ya tabbata a gare shi,
Daga Aisha diyar Sa'ad ta ce na ji Sa'ad Allah kara yarda a gare shi ya na cewa, na ji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya na cewa :Ba wanda zai yi wa mutanen madina kaidi face ya narke kamar yadda gishiri ke narkewa a ruwa,) Buhari ne ya rawaito.
An karbo daga Jabir Allah kara yarda a gare su ya ce Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : Madina tamkar zuga zugi ne ya kore kazantarsa ya tace mai tsarkinsa.) Muslim ne ya rawaito.  
Lalle Ibarahim ya haramta Makkah ya mar adu'a da albarka, kuma lalle Annabi ya haramta Madina ya yi mar adu'a da ribin abin da Annabi Ibrahim ya roka wa mutanen  Makka An karbo daga Abdullahi bin zaid Bin Asim cewa Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :( Lalle Ibrahim ya sanya alfarma ga Makka ya yi adu'a ga mutanenta, lalle ni kuma na sanya alfarma ga Madina kamar yadda Ibrahim ya sanya wa Makka, ni kuma na roki Allah game da sa'in madina da mudunsa da ribin abin da Ibrahim ya roka wa mutanen makka) Muslim ne ya rawaito.  
   Daga Anas -Allah ya kara yarda a gare shi- daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Ya Allah ka sanya albarka ga Madina ribin abin da ka sanya a makka).  Buhari ne ya rawaito.

Ya ku bayin Allah!
Lallai Madina ya kasance mafi soyuwan gari ga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance yana nuna masa kauna da wafa'i kuma yana bayyana hakan karara An karbo daga A'isha Allah ya kara yarda a gare ta tace : Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (ya Allah ka sanya mana kaunar Madina kamar yadda ka sa mana kaunar Makka ko ma sama da haka. Ya Allah ka sa albarka ga sa'inmu da mudunmu ka inganta mana shi, ka kaurar da Annoban zazzabinsa zuwa juhfa)  Buhari ne ya rawaito.
   Daga Anas -Allah ya kara yarda a gare shi- idan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya dawo daga tafiya ya hangi gine –ginen Madina sai ya saki dabbarsa in yana kan dabbarsa ne sai ya kada ta sabo da kaunar Madina.) . Buhari ne ya rawaito.
Ya kasance idan ya fiskanto Madina sai ya kara sauri idan dutsen Uhud ya bayyana gare shi sai yace : wannan dutse ne da ya ke sonmu mu ma muna son shi,
An karbo daga Abu Humaid yace mun fita tare da Manzon Allah a yakin tabuka ya koro hadisin sannan ya ce : sai muka fiskanto har muka zo wadil kura sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace :( Lalle ni zan kara sauri wanda ya ke so cikin ku to ya yi sauri tare da ni wanda ya so kuma ya zauna, sai muka fita har muka kusanto Madina sai yace : Wannan Daba ne wannan dutsen Uhudu ne shi dutse ne da yana son mu muna son shi). Muslim ne ya rawaito.
Hakika zukatan masu ziyara ta ta'allaku da Madina kuma ya bar wasu abubuwa na tarihi a zukatansu na  tsananin kauna sai zukatansu ta tausasa zuwa ga garin suna masu tsanani shauki , ya Allah ka sanya mu daga cikin masu son sa (garin ke nan)
Ya jama'ar musulmai :
Madina shi ya fi muku alheri kar ku ki shi   Allah ya zabe shi ga Annabin ku to ku zabi abinda ya zaba ku ladabtu da kusanci ku san hakkin makobci an karbo daga abi  Zuhair Allah ya kara yarda da a gare shi ya ce  na ji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa (za a bude garin yaman wasu mutane za su zo suna kora dabbobinsu suna daukan iyalansu da ma wadanda suka biye musu, Madina yafi alheri agare su da sun sani za abude Sham sai wasu mutane su zo suna kora dabbobinsu sai su dibi iyalansu da ma wadanda suka musu da'a alhali Madina yafi alheri a gare su da sun kasance suna sani kuma za a bude  garin Iraki sai wasu mutane su zo suna kora dabbobinsu sai su dibi iyalansu da ma wadanda suka musu da'a alhali Madina yafi alheri a gare su da sun kasance suna sani) Bukari ne ya rawaito
An karbo daga ibnu Umar Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (Duk wanda zai mutu a Madina to ya mutu a cikinsa lallai ni  zan yi  ceto ga wanda ya mutu a cikin shi ) Tirmizi ne ya rawaitoshi kuma ya inganta shi
An karbo daga A'mir dan Sa'd daga babansa Allah ya kara yarda a gare su ya ce : Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Madina ya fi alheri a gare su da sun kasance suna sani duk wanda ya bar garin halin ya tsani garin to Allah zai sanja shi da wani wanda ya fi alheri ba wani da zai tabbata a ciki ya yi hakuri da  wahala da tsanani irin nashi face na kasance mai ceto a gare shi ko mai shaida a gare shi ranar alkiyama) Muslim ne ya rawaito ,Allah ya samini albarka ni da ku a cikin alkur'ani mai girma

Huduba ta biyu  
Ya ku bayin Allah
  lallai Madina na da daukaka da falala to ku nemeshi da alhurma da kima da wasu laduba da ya ya wajaba a yi ladabi a iyakoki na harami dama masallacin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi haka nan kuma da wurinda Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ke lallai adabi tare da shi yana raye kamar yimishi ladabi ne a bayan ya rasu hakika Allah ya umarci a yi ladabi gaba gare shi a kuma yi kasa da murya , Allah madaukakin sarki ya ce : (ya ku wadanda suka yi imani kada ku sha gaban Allah da Manzonsa ku ji tsoron Allah lallai Allah mai ji ne  masani )(ya ku wadanda su ka yi I'mani kar ku daga sautukanku sama da sautin Annabi kada kuma ku bayyana zance a gare shi kamar yanda sashinku ke daga murya ga sashi don kada ayyukanku su rushe a halin baku sani ba)( lallai wadanda su ke kankan da sauti gaba daManzon Allah wadan nan su ne wadanda Allah ya jarabi zukatansu da takawa suna da wata gafara da lada mai girma )(lallai wadanda su ke kiranka a bayan dakuna mafiya yawansu basu da hankali ) (da a ce sun yi hakuri har ka fito zuwa gare su da ya kasance mafi alheri a gare su Allah mai gafara ne mai jin kai )
ku ladabtu ya ku bayin Allah a gaba gare shi da kyakyawan laduba an karbo daga Sa'ib da yazid ya ce : na kasance ina tsaye a masallaci sai wani ya jefeni da tsakuwa sai na duba sai naga Umar dan kaddabi ne sai ya ce je ka taho  min da wadancan mutane guda biyu sai na taho mishi da shi sai ya ce : ku waye ? ko kuma daga ina ku ke sai suka ce : daga garin Dayif sai ya ce : da kun kasance mutanen garin Madina ne da na jiyar da ku a jikinku (da na azabtar da ku) kuna daga muryan ku a masallacin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ? ) Buhari ne ya rawaito .
Allah ka daukaka musulunci da musulmai .      

الأحد، 5 يناير 2020

BARNA A KASA DA BAWA DUKIYA KARIYA A MUSULUNCI


Hudubar Masallacin Annabi na shaikh Husain bin Abdul'aziz Al- Ashaikh 8-5-1441Ah /3-1-2020Ac

Na daga cikin ginshiki na yanke a wannan addini namu akwai haramcin cin kazantacciyar dukiya, na daga cikin mafi munin dukiya na haram ribatar da wasu ke yi a ma'aikata ko watanta na yin awun gaba da dukiyar al'uma (sata) ko yi ma dukiyar ta'annuti, ta kowace fiska a ka yi ta ko ta wace hanya aka bijiro da ita. Allah Madaukakin sarki ya ce (ya ku wadanda suka yi imani kada ku ci dukiyarku  a tsakanin ku bisa bata sai dai ta hanyar kasuwanci bisa yarjejeniya daga gare ku.)  
To dukiyar kasa asalinta tana da alhurma sabo da mallakan al'uma ne baki daya, ana sarrafa ta ne wajen amfanin kowa da kowa, da maslahohin da ake tarayya a kanta.
To duk wanda ya riki wani aiki, kowani irin aiki ne to shi abin tambaya ne gaba ga Allah na dukkan nauyin da aka dora masa, to ba ya halatta ya yi gaban kansa a ciki face abin da ya zo daidai da koyarwar shariar Allah a kankanin abu ne ko babba, sawa'un cikin abu mai kima ne ko mara kima, da kuma abin da tsari ya shirya don cinma maslahohi na gabadaya da amfani iri iri na kowa da kowa.
Lalle sakaci cikin shanin kowane dukiya yana komawa ne ga bangaren wanda ya yi sakacin ko da wani ma'aikaci ne kuwa wannan laifi ne a mahanga na sharia tsarkakakkiya, haka ma yin rufa-rufa ga wani sabo da dangantaka ko abokantaka ko don neman wani anfanin kai, to duka sun shigo cikin satan dukiyar al'uma, kuma yana cikin barna a doron kasa da ha'intar shugaban kasa jagoran musulmai da kuma ha'intar al'uma, sakamakon abin da wannan ha'inci ya kumsa na hadura da ke barazana ga zaman lafiyar al'uma da tattalin arzikinta da habakanta da ci gabanta da yalwanta. Allah Madaukakin sarki ya ce (Duk wanda ya ci gululi zai zo da abin da ya ci na gululi  ranar alkiyama sa'annan a cika wa kowane rai  sakamakon abin da ya aikata kuma ba za a zalunce su ba).
Ana cewa  gallar rajulu fa huwa  yagullu wato mutum ya yi gululi idan ya yi ha'inci, Al'aghlal : shine cin amanar wani nauyi da aka dorawa mutum wanda ya hada dukkan nau'ukanta, kuma ana fassara ta da satan dukiyar al'uma ta dukkan fiskokin sata, sabo da haka ne a ke cewa ga mahauci ya yi gululi idan ya saci wani abu na nama bayan ya dauki fata.
   
   Allah Madaukakin sarki ya ce (kada ku yi barna a ban kasa bayan an gyara ta.)
Al'uma ba zata ta ba gyaruwa ta yi kyau ba sai kowa ya tashi da nauyin da ke kan shi na amana bisa yanayi mafi kyau, a yi taimakekeniya gurin kiyaye dukiyar al'uma, ta kowace hanya da ta sawwaka, Allah Madaukakin sarki ya ce game da AnnabinSa yusuf   (ka sanya ni a kan taskokin kasa, lalle ne ni, mai tsarewa ne, kuma masani.)
 Haka kuma a kissar musa game da yaran mata biyu na shuaibu ( ya Baba ka bashi aikin kodago, lalle ne mafi alherin wanda ka bawa aikin kodago shi ne mai karfi amintacce.)
  Lalle ribatar dama na aiki ko waninsa don a yi awun gaba da dukiyar al'uma ba bisa halacci ba na daga cikin manyan laifuka na zunubai da kuma munanan al'amura, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Lalle wasu mutane na kutsawa cikin dukiyar Allah ba tare da hakki ba,to wuta ta tabbata a gare su ranar alkiyama) Buhari ne ya rawaito.
Ibnu Hajar Allah ya masa rahama yace : ( wato suna barna a dukiyar musulmai).
Lalle kalmar malaman fikihun musulunci ta nassatan cewa dukiyar al'uma kamar dukiyar maraya ne wurin wajabcin kiyaye ta, da haramcin dauka daga gare ta, da matsanancin kwadayin tafiyar da ita a gurarenta da suka dace ba tare da yin sakaci ba ko tawace fiska.
Ya 'Yan uwa a Musulunci
Na daga cikin abubuwa na bayyane da ke faruwa daga wasu ma'aikata na gabatar da wasu a matsayi da fifita su a kan wasu ba tare da cancanci ba, tare da fakewa da wata doka da ta fito daga shugaban kasa, don tabbatar da maslahar kowa da kowa na daga 'yan kasa, sai wannan ma'aikacin ya riki wannan kamar wata garabasa yana zaton tamkar dukiyarsa ne na aljihunsa, sai ya gabatar da wanda bai cancanta ba bisa wanda ya cancanta. Na daga cikin irin wannan akwai sakaci da wasu ke yi wajen bada kwangila ba bisa ka'ida ba, ko don maslahar kai, da wuce gona da iri wajen sanya farashin aikin, wanda in da na kan shi ne bai zai yarda da haka ba. Yana daga cikin sakaci na rashin kulawa  da dukiyar al'uma kamar lambuna da asibitoci da wuraren shakatawa  da hanyoyi da makamantarsu.
Yana daga ciki amfani da abin da yake mallakar hukuma ne wurin bukatun kai ba tare da izini da ke bisa tsari ba daga shugaban kasa.
Na daga cikin sakaci da wasu ke yi akwai tafiyar da magani  na kasa da makamantarsa da raba shi ba ga bigerin shi da ya dace ba,na daga ciki akwai kasuwantar da daukan aiki da cin riba a cikinsa, ko srayar da lokacin aiki ko jinkirta abin da aka dorawa mutum na aiki ta fiskar da ba haka ya dace ba, wadannan da makamantarsu na cikin nau'uka na barna, kuma ha'intar jagoran al'umar musulmi ne da ita kanta al'umar sabo da abin da ke ciki na barna  mai girma da sharri mai fadi wanda zai haifar da cutarwarsa mai tsanani, kuma zai kawo cikas ga ci gaban kasa da habakarta da ma mutanenta    Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Lalle sau da yawa wani na kutsawa cikin dukiyar Allah da manzonSa cikin abin da ransa ya so ranar alkiyama bai da wani abu sai wuta.) Tirmizi ne ya rawaito kuma yace Hadisi ne Hasan sahih, kuma Ibnu Hibban ma ya rawaito shi a littafinsa Sahih da sanadi ingantacce.

Ya ku bayin Allah
Lalle abin da yak e wajibi ga duk wanda ya biye wa ransa abin da ya raya masa har ya yi gaba da fadi da dukiyar al'uma ta ko wace irin hanya ce daga cikin hanyoyi da ya koma ga Ubangijinsa ya tuba ga Mahaliccinsa ya rabu da wannan kudin haramun ta hanyar maida shi ga taskar kasa, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : : (Yana kan mutuum abin da ya sata har sai ya mayar da shi).Ahmad da Abu Dauda da Tirmizi ne suka rawaito kuma Tirmizi ya ce Hadisi ne ingantacce.

Malaman fikihu sun yi tarayya kan cewa duk wanda ya lalata wani abu na dukiyar al'uma to dole ne ya biya haka kuma in ya dauki wani abu daga ciki ba tare da hakki ba to ya dawo da shi ga taskar kasa wato Baitul mali na musulmai.
Hakika Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kafa mana wata ka'ida  ga duk wanda ya rike wata amana na musulmai da kada ya ribaci wani abu na aikin hukuma da makamancinsa ya yi amfani da shi cikin maslahar kansa, wannan shi ake cewa ilimin tsarin gudanarwa  Tushe da bada kariya ga dukiyar al'uma, sai yace ga wanda ya je tattaro dukiyar zakka bayan yace wannan naku ne wannan kuma an bani kyauta ne :   (To me ya sa dayanku ba zai zauna a gidan iyayensa ba ya ga ko za a kawo masa kyauta ko aa, na rantse da wanda rai na ke hanunSa dayanku ba zai dauki wani abu ba face ya zo da shi ranar alkiyama yana dauke da shi a wuyarsa.) Buhari da Muslim ne suka rawaito.
Ku ji tsoron Allah yak u bayin Allah ku yi taimakekeniya dukkanku wurin kiyaye dukiyar al'uma ta dukkan hanyoyi da za ku iya yin hakan ku kiyaye kada ku yi sakaci da hakan Allah Madaukakin sarki yace : (ku yi taimakon juna bias da'a da takawa kada ku yi taimakekeniya a kan laifi da gaba)
Duk wanda ya biye wa ransa wurin sabo ko wani irin sabo ne da ya sani in ya faku daga idon mutane to fa  Allah na tsinkayar sirrinsa da bayyanensa ku tuna fadin Allah Madaukakin sarki : (ku sani lalle Allah yana sanin abin da ke cikin zukatanku to lalle ku kiyaye shi) da fadinSa  : (ya san maha'intar idanuwa da abin da zukata ke boyewa.)
Na daga cikin nusarwar Manzon Allah : (Duk namar da ta tsiro daga haram to wuta ce ta fi dace wa da ita). Kada ka gabatar da duniya mai karewa a kan lahira mai wanzuwa, kada ka shigar da wani abu ga kanka da iyalanka sai halal mai tsarki da dukiya tsarkakakkiya.
Ya zo cikin kissar yaron da mashi da ba a san daga ina ba ya kashe shi a yakin khaibar mutane na cewa barkan shi da samun Aljanna sai  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : (A'a  ahir, na rantse da wanda rai na ke hanunSa lalle bargon da ya dauka a ranan khaibar kafin a raba ganima na babbaka da wuta a kan shi). Buhari da Muslim ne suka rawaito.
An rawaito daga Abubakar :"Duk wanda ya nemi arziki ta hanyar haram to zai rasa albarkan, ba za ka ga wani gurbi na kwarai ba a dukiyarsa idan ya ciyar da dukiyarsa gurin abincinsa to zai hadu da ukubarsa  a lahira, idan ya ciyar da iyalansa da shi to hakika  ya ha'ince su bai kyauta musu  ba, kuma ba abin mamaki ba ne in dansa ya zama mara biyayya a gare shi. Halayen wadanda yake daukan nauyi ya lalace, suka zama kwatankwacinsa kuma ya hadu da alhakin abin da ya aikata a rayuwarsa ta duniya kuma azabar lahira ta fi tsanani."

Huduba ta biyu
Ya tabbata daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi : (Kafafuwan bawa ba za su gusa ba a ranar alkiyama har sai an tambaye shi game da rayuwarsa yadda ya tafiyar daita, da iliminsa cikin abin da ya tafiyar da shi da dukiyarsa ta wacce hanya ya same ta kuma ta yaya ya kasha ta, da jikinsa ta yaya ya tsofatar da shi).
Ku tsarkakar da hanyar ku ta neman abinci ku nesanci kazantattun hanyoyi za ku tsarkaka ku rabauta, za ku yi nasara kuma ku ji dadi.
Ibnu Taimiyya Allah ya masa rahama yace: "Abinci na hadewa ne ya cakudu da jiki  ya tsiro da shi sai ya zama kamar sinadari ne nasa, idan abincin ya zaman a kazanta ne sai jikin ma ya kazance sai wuta ta wajaba a gare shi, sabo da haka ne Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi y ace : (Duk namar da ta tsiro daga haram to wuta ce ta fi dace wa da ita). Aljanna tsarkakakkiya ce bam ai shiganta sai mai tsarki."
Abin da ake nufi da ci ya kunshi da wani abu da ya ke amfana da shi a kan saya a ji dadi a wannan rayuwa.  

الاثنين، 30 ديسمبر 2019

SABUNTA IMANI


Hudubar Juma'a  a Masallacin Annabi na shaikh AbdulBari Subaiti 1-5-1441AH
HUDUBAR FARKO
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, wanda ya halicci sammai da kasa, ya sanya duhu da haske  ina kyautata yabo a gare shi ina gode  mishi da  yammaci da safiya  da lokacin sammako, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah  shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, wanda yace : ( kuma rayayyu ba zasu yi daidai da matattu ba Allah na jiyar da wanda ya so, amma kai ba za ka jiyar da wanda yake cikin kabari ba)
 Na shaida shugabanmu Muhammad bawansa ne kuma manzonSa ne, ya yi gargadi a kan gafala da gajiyawa, tsira da amincin Allah su tabbata gare shi,da iyalan shi da sahabbansa wadanda suka samu babban falala da lada Bayan haka.
Ina muku nasiha da ni kai na da jin tsoron Allah Allah Madaukakin sarki ya ce:-(yA ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah cancancin tsoronSa kada ku mutu face kuna musulmai).
 Bibiyar imani da ba shi kulawa na daga cikin sifar musulmi kuma abin nanatawar masu hankali, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace :(Imani na tsufa ya kode a cikin dayanku kamar yadda tufafi ke tsofewa ya kode, to ku roki Allah Madaukakin sarki : da ya sabunta muku imani a cikin zukatanku).
Kamar yanda tufafi ke tsofewa,  ai wato kamar yanda  sabon  tufafi yake tsofewa  sabo da dadewa ana amfani da shi, Manzon Allah tsira da amincin  Allah su tabbata a gare shi ya ce :- (An ambaci zuciya ne  kawai da zuciya  sabo da  jujjuyawa da yake yi ,  misalin zuciya kamar misalin gashi ne  da aka rataye ta a wani itaciya iska na kada ta  cikinta  da wajenta)
  Mumini na sabunta imaninsa , sabo da imani ba ya tabbatuwa a hali guda,  sai dai yana gajiyawa sabo da dadewa  ya raunana sakamakon gajiyawa a bangaren ibada , ko daina ibada ko kuma gafala daga Allah, da dulmuyar rayi a cikin sha'awe-sha'awensa  to mutum wani halitta ne da ke da iyaka a ikonsa, yana da rauni a fidirarsa  yana tsakanin gajiyawa da gajartawa  Allah Madaukakin sarki ya ce:-(An halicci dan adam a halin yana mai rauni).
Duk wani abu da zai sami musulmi na yanke ibada daga wani lokaci zuwa wani lokaci ko kuma zamewar kafarsa , to hakika baya kubuta daga hukunci na Ubangiji  daga ciki akwai komawa zuwa  ga Ubangiji da fadakar zuciya  Allah Mai tsarki da daukaka yana son masu yawan tuba yana farin ciki da tubarsu, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:-
  (Na rantse da wanda raina ke hanun shi  da badon kuna aikata zunubai ba  da Allah ya tafiyar da ku ya zo da wasu mutane masu yin zunubai , kuma suna neman gafara sai ya gafarta musu.)
  Imani na karuwa yana raguwa , yana karuwa da biyayya kuma yana raguwa da sabawa Allah , idan zuciyar dayanku ta farka daga gafalarta,  ya rika ayyuka na da'a ya riki sabuba na imani to imaninsa  zai karu ya yi karfi ko yakininsa ya yi karfi  idan ya yi dubi zuwa ga ni'imomin Allah  a  gare shi  sai kaunar sa ga Allah ta karu   sai ya yi  lafazi na ambaton Allah ya gaggauta cikin tuba da  ayyuka na alheri  domin ya riski abin da ya gajarta da abin da  ya tsere mishi a dalilin  gafala  sabo da haka ne lalle abin kwadayi ne   kwarai wurin bibiyan imani  da kuma aiki bisa  daga darajar shi  na daga cikin sifa na salihai  , Abu Darda Allah ya kara yarda a gare shi yana cewa: "Na daga cikin fikihun bawa  ya rinka bibiyan imaninsa da abin da ya tawaya daga gare shi , na daga cikin fikihun bawa  yasan cewa    yana karuwa ne shi ko yana raguwa". 
Umar Allah ya kara yarda a gare shi ya kasance yana cewa sahabban shi , ''  ku zo mu kara imani '' sai su ambaci Allah Mabuwayi .
Ibn Mas'ud Allah ya kara yarda a gare shi yana cewa a cikin adu'arsa (Ya Allah ka kara mana imani da yakini da  fahimta).
 Mu'az  bin Jabal -Allah ya  kara yarda  a  gare shi - yana cewa wani mutum (zauna tare da  mu , mu kara imani na wani lokaci).
Duk yanda imanin mumini  ya kai kololuwa a daraja to ba zai aminta wa kansa ba, tafarkinsa shi ne komawa zuwa ga Allah yana neman tabbatuwa a kan tafarki, Allah Madaukakin sarki yace a harshen bayinSa muminai: (ya Ubangijinmu kar ka karkatar da zukatanmu bayan ka shiryar da mu).
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana yawaita fadinsa.: ya mai juya zukata da basira tabbatar da zuciya ta bisa addininka).
Idan mumini ya san shaidan  na dakonsa ne, to ya yi kokari don yayi  yaki da fizgarsa, ya tunkude waswasinsa, ya toshe kofofin yaudarasa, kada ya mika wuya, kada ya samu karayar zuci, yana mai neman agaji daga Ubangijinsa, Allah Madaukakin sarki ya ce: ((To idan ka zo karanta kur'ani to ka nemi tsarin Allah daga shaidan abin jefe wa. Lalle shi bai da iko a kan wadanda suka yi imani, kuma suna  dogaro ne ga Ubangijinsa)
Mafi alherin guzuri ga wanda ya ke neman guzuri, kuma mafi alherin abokin tafiya a hanyar tabbatuwa bisa tafarki shine riko da littafin Allah da aiki da shi, wanda ya yi riko da shi Allah zai kare shi, wanda ya bi shi kuma Allah zai kubutar da shi.
Musulmi fadakakke yana yin kokari don ya ga ya fita daga yanayi na gafala, da sharri na rauni da gajiyawa, sabo da zai ji farinciki ne idan ya yi biyayya ga Allah, yana mai neman yardar Ubangijinsa, wani mutum ya tambayi Manzon Allah menene imani? Sai Manzon Allah ya ce :( idan kyawawan ayyukanka suka burge ka munanan ayyukanka suka bata maka rai to kai mumini ne).
  Ta yaya zai gafala daga Allah ya gajiya daga ibada wanda zuciyarsa akwai haske na Alkur'ani! Yana dandana halawar imani kuma ya san cewa yana da Ubangiji mai tausayi wanda ke yafe kusakuran masu tuba kuma yana gafarta zunubai, Allah Madaukakin sarki ya ce : (kuma wanda ya aikata mummuna ko ya zalunci kan shi sannan ya nemi gafarar Allah to zai samu Allah Mai gafara ne Mai jinkai)
Ambaton Allah da tunani cikin ayoyinSa yana farkar da zuciya kuma yana kara imani kuma yana tsarkake zuciya; Allah Madaukakin sarki ya ce : (Abin sani kawai, muminai sune wadanda suke idan an ambaci Allah zukatansu su firgita, kuma idan an karanta musu ayoyinsa sai su kara musu imani, kuma ga Ubangijinsu suke dogara.)
Ya dace ga musulmi ya dawo da ransa in ya gafala, da gabbansa idan sun yi rauni ko gajiya a ibada, domin tsoron fushin Allah da ukubarSa, na daga cikin Adu'ar Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, (Ya Allah ina neman tsarinka daga gushewar ni'imarka da juyawar afiyarka da azaba bagtatan da dukkan abin da zai fusata ka,)
Zuciya kan karkata zuwa ga duniya a wasu lokuta tana ta neman abin duniya ido rufe wasu lokuta, sabo da haka ne Allah ya umarce mu da yawaita ambato, don a samu daidaito,  a gare mu tsakanin neman abin duniya da sauke nauyin wajibi na addini, : (ya ku wadanda suka yi imani ku ambaci Allah ambato mai yawa ku yi tasbihi safiya da maraice).
 Kamar yadda zurfafawa cikin abubuwan da aka halatta da barna da wuce gona da iri cikin al'adu yana haifar da gajiya Allah Madaukakin sarki ya ce : (ya 'yan adam ku riki adonku a gun dukkan masallaci ku ci ku sha kada ku yi barna, lalle shi bai son mabarnata.)
Ba ya boyu wa ga masu hankali cewa abota da masu raunin himma da marasa  manufa kan haifar da gajiya wa da gafala.
Idan musulmi bai ankara ba daga gafala da ya ke ciki ya gaza tunkude gaza wa da yake da shi da rauni to sai sifa ta tsauri da kekashewar zuciya ta yi galaba a kan shi da rauni da nauyi wajen sauke nauyin ibada,  da'a ta yi mishi wahala zuciya ta yi tsatsa ya dushe hasken imani
Allah Madaukakin sarki ya ce : (Bone ya tabbata ga wanda zukatarsu suka kekashe daga ambaton Allah wadancan suna cikin wata bata bayyananna).
 Idan musulmi bai magance zuciyarsa ba to zai dangana da halin nan da Allah  Mai tsarki ya bada labari game da ita, a fadinsa (sa'annan kuma zukatanku suka kekashe daga bayan wancan, sabo da haka suka zama kamar duwatsu, ko mafi tsanani  ga kekashewa, kuma lalle ne daga duwatsu hakika akwai abin da maremari suke bubbuga daga gare shi, kuma lalle ne daga gare su hakika akwai abin da ya ke tsatsagewa har ruwa ya fita daga gare su, hakika, akwai abin da ya ke fadowa domin tsoron Allah, kuma Allah bai zama gafili ba daga abin da ku ke aikatawa.)
Allah ya sa mana albaka ni da ku cikin Alkur'ani Mai girma kuma ya amfanar da ni da ku da abin da ke ciki na ayoyi da ambato mai hikima. Iya abin da ya sawwaka kenan cikin abin da zan fada tare da neman gafarar Allah, kuma ku nemi gafararSa domin shi Mai gafara ne Mai jinkai.
  
    HUDUBA TA BIYU
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya amsa kiran wanda ya roke shi, musulmi na gode masa a sirrinsa da ganawarsa, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya ba wani Ubangiji koma bayanSa, na shaida Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne kuma  zababbenSa ne, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa da sahabbansa wadanda suka rabauta da kaunarSa kuma da yardarSa.  
Bayan haka :To ina muku wasiyya da ni kai na da jin tsoron Allah.
 Duk wani abu da ya samu musulmi na gafala kuma alama na gazawa ta afka mishi kafa ta zame, to lalle kofar tuba a bude take, hanyoyin alheri birjik su ke, Allah na son masu yawan tuba da komawa gare shi, kuma yana cewa a hadisul kudsi : (ya ku bayi na lalle ku masu yin kuskure ne cikin dare da wuni, ni kuma mai gafarta zunubai ne baki daya, ku nemi gafara ta zan gafarta muku).  
Ku yi salati ga Annabin shiriya. Hakika Allah ya umarce ku da hakan a littafinSa sai ya ce :(Lalle Allah da mala'ikunSa suna salati ga Annabi, ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi da aminci tabbatacce.)  

الجمعة، 20 ديسمبر 2019

FIDIRA


Hudubar Masallacin Annabi na Shaikh Aliyu bin Abdurrahman Alhuzaifi 23-4-1441 Ah 20-12-2019Ac
Da sunan Allah Mai rahama Mai jinkai.

Hudubar farko
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Mabuwayi Masani, wanda ya halicci mutum cikin mafi kyan tsari, wanda ya tausayawa mukallafai da saukar musu wannan littafi mai daraja, wanda ya yi baiwa ga halittu da ni'imomin da basu gidayuwa na daga falalarsa mai girma, ina kyautata yabo ga Ubangiji na kuma ina gode mishi bisa ni'imominsa da baiwarsa da alherunsa da muka sani da wadanda bamu sani ba, ba abin bauta wa da gaskiya sai shi, Ma'abocin kyautatawan da bai katsewa   da  kyautayinsa dadadde, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya, Mai rahama Mai jinkai, na kuma shaida Annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawansa ne kuma ManzonSa ne, mai shiryarwa zuwa ga tafarki mikakke, ya Allah ka yi dadin tsira da aminci da albarka ga bawanka kuma Manzonka Muhammad da iyalansa da sahabbansa wadanda suka rabauta da daukaka na duniya, a lahira kuma suka rabauta da ni'ima na har abada.
Bayan haka, ku ji tsoron Allah wanda ya halicce ku ya baku duk abin da kuke kauna ya tunkude muku abin da kuka tsana, ya ku mutane! Ina tunatar da ku da ni kai na da ni'ima da ta fi kowacce, dukkaninta Allah ya ni'imta mutum da su, muddin ya kiyaye ta ya bata matsayinta cancancin matsayinta, ya kiyaye ta ya mutu a kanta to hakika ya samu sa'ida a rayuwarsa da bayan mutuwarsa sa'idar da bai zai taba tsiyacewa ba da ita har abada ya kuma rabauta da  alhairu, kuma ya tsira daga sharri da abubuwa masu halakarwa, Allah zai gyara dukkan lamuransa baki daya a rayuwarsa, kuma ya jikansa bayan mutuwarsa, kuma wannan shine babban rabo, idan mutum ya sauya wannan ni'ima mai girma ta hanyar kafurcewa ko munafunci ko da wani aiki da ke kishiyantar wannan ni'imar ya sarayar da ita da rashin kiyaye ta to hakika ya yi hasara mabayyaniyar hasara, ko da an hada mishi abubuwan jin dadin duniya da kyalakyalanta, to ba wani abu bane ita sai inuwa mai gushewa, kuma jindadi ne mai kaucewa, kuma ni'ima ce mai karewa jindadinta na tafiya ta bar hasara. Allah Madaukakin sarki yace (Rayuwar duniya ba wata aba ba ce face jindadi mai rudi) Allah Madaukakin sarki yace (ya ku mutane lalle alkawarin Allah gaskiya ne kada rayuwar duniya ta rude ku, kada wani mai rudi ya rude ku daga Allah.)
     Ya ku bayin Allah! Ko kun san wannan ni'ima mafi girma wanda Allah ya yi ga mutum ya kuma mutunta shi da ita? Lalle ita ce ni'ima ta fidira, to menene hakikanin fidira, ana nufi da fidira halin da Allah ya halicci mutum a kai, mai iya karbar kadaita Allah shi kadai ba Ubangiji koma bayanSa, kuma ba abin bauta bayan shi, mai kaunar Alheri mai kin sharri mai karkata zuwa ga biyayya, mai gano munin abubuwan da aka haramta, mai sanin gaskiya a dunkule, kuma masanin bata a dunkule, da ace wannan fidirar da Allah ya halicci mutum a kai ta kubuta daga shaidanun mutane da aljanu da abubuwa masu tasiri da ke iya sanja ta to da ta zabi tauhidi da musulunci, sai dai wannan fidira bata iya wadata da kanta wurin sanin gaskiya daki- daki daya -bayan daya kuma ta yi aiki da shi haka ma sanin sharri da bata daya bayan daya da nesatansu, to don haka ne Allah Mai tsarki ya turo manzanni, kuma na karshen su shine Annabinmu Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi don su kiyaye fidira  kuma su koyar da ita sharia su taimake ta da haske na wahayi a matsayin manhaji na rayuwa, na daga cikin dalili da ke nuni cewa fidira ita ce halin da Allah ya halicci mutum a kai da lafiyayyar dabi'a mai iya amsar addini mai son musulunci akwai fadin Allah Madaukakin sarki ( ka tsayar da mafiskantar ka ga addini kana mai totar izuwa gare shi kirar Allah ce wacce ya kera mutune a kanta, babu musanyawa ga addinin Allah)  Ibnu kasir Allah ya masa rahama yace a cikin tafsirisa : ( ma'anarsa Allah Madaukaki ya daidaita halittunsa gaba dayansu a kan fidira bisa dabia mikakkiya da ba a haifan kowa face a kan haka, ba fifiko tsakanin mutane cikin haka)  ta tike.
An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : Dukkan abin haihuwa ana haifansa ne akan musulunci to iyayensa ne ke yahudantar da shi ko kiristantar da shi ko majusantar da shi, kamar yadda dabba lafiyayya kan haifi lafiyaya babu wani abu da ku ke gani na gutsurarren hanci ko kunne.) Buhari da Muslim ne suka rawaito.
 An karbo daga Iyad dan  Himar Allah ya kara yarda a gare shi, yace watarana Annabi ya yi huduba sai ya fada a cikin hudubar tasa : lalle Ubangiji na ya umarce ni da na sanar da ku abin da baku sani ba. dukkan dukiyan da na bawa bayi na na halal , lalle na halicci bayi na akan addini hanifiya gabadayansu sai shaidanu suka zo musu suka batar da su daga addinin su. suka haramta musu abin da aka halatta musu suka umarce su da su yi shirka da abin da ban saukar da shi ba na hujja)  Muslim ne ya rawaito
Imamul Bagawi Allah  ya mishi rahama ya ce a cikin tafsirinsa: "Ance ma'nansa dukkan wani abin haifa ana haifansa ne a farkon halittansa bisa fidra wato dabi'u masu lafiya da halaye da suke a shirye don karban addini da zai tafi ne bisa lazimtar ta sabo da wannan addinin kyanshi na nan cikin hankali sai dai kawai zai kauce ne daga wannan zuwa wanin shi sabo da wata musiba da ta faru na daban kamar koyi ko kwaikwayo, da mutun zai kubuta daga wannan musibun to ba zai kudurta wani abu ba sai addini) . maganar ta kare.
 wato fidra ana nufi da ita mahalli na imani wanda shi ne dabia'n da mutun ya tafi a kan shi wanda aka halicce shi akanta  a halinsa na dan adam kuma zuciyarsa a shirye ta ke don karban ilimi mai amfani da aiki na kwarai,  ma'ana na biyu a tafsirin fidra shi ne hasken wahayi da ilimin sharia.
Ibnu abbas Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : "Babu canji ga halittan Allah ai ga addinin Allah"
Imamul Buhari ya ce : "fadinsa la tabdila li kalkillah ma'ana babu canji ga halittan Allah lidinillahi wato dabiyun mutanen farko shi ne addinin mutanen farko addini da fidra kuma shi ne al islam .
maganan ya tike.
 To sai ya bayyana cewa fidra ita ce mahalli ko bigire na imani da addini shi ne abin da aka haifi mutun akai na daga halitta mikakkiya ko dabi'a mikakkiya wanda ana nufin da fidra shi ne halin da ya ke cikinta  na asali shi ne na shari'a da imani.
Zan koro misalai na wadannan ma'anoni biyu, kamar misalin fidira da aka haifi mutum a kai, kamar misalin fitila ne na wutan lantarki wanda aka sana'anta aka yi shi ya rika karbar  wutar lantarki, shi wutan lantarki kamar ilimi ne da wahayi da ke cikin zuciya idan aka hada kwan lantarki da wayan lantarki mai wuta sai ya yi haske ya haskaka ya bada launi, idan ba a hada su ba to ba dayansu da zai amfanar shi kadan shi wurin haskakawa, to haka nan ma fidira ba za ta amfanar da ma'abocinta ba sai da ilimi mai amfani da aiki na kwarai.
    Fidira ita ce abin da Allah ya karrama mutum da ita ya fifita shi da wannan fidira wacce da ita ne ya ke sanin ma'arufi ya ki abu na munkari  ya siffanta abu mai kyau da kyau ya munanta abu  mara kyau, idan fidira ta juya ta rushe to kuwa mutum ya zama mamaci ko da yana tafiya a  doron kasa, Allah Madaukakin sarki ya ce :( shin kuma wanda ya kasance matacce, sa'annan muka rayar da shi, kuma muka sanya wani haske dominsa yana tafiya da shi, yana zama kamar wanda misalinsa yana cikin duffai, shi kuma ba mai fita ba daga gare su.)
Fidirar mutum ba ta samun kiyayewa ta karu da haske da sheki ta cika a karfi da rayuwa face da ilimi mai amfani da aiki na kwarai, da imani da aiki na da'a, domin da'a ke ciyar da ita ta sanya ta ta yi karfi, kuma nesatan abubuwan da aka haramta na kare ta daga abubuwa  masu darkakewa, duk wani umarni na wajibi ko mustahabbi na kiyaye Fidira ya raya ta    Allah Madaukakin sarki ya ce :( ya ku wadanda suka yi imani ku amsa wa Allah kuma ku amsa wa  Manzo idan ya kiraye ku zuwa ga abin da yake rayar da ku).
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :( Abubuwa goma suna cikin fidira : rage gashin baki da barin gemu da yin aswaki da shaka ruwa da yanke kumba da wanke matattara da ke tsakanin yatsu,da cire gashin hamata, da tsarki da ruwa, wato istinja'i) Muslim ne ya rawaito.
 Idan wadannan ta'adodin na cikin  Fidira to wasunsu na daga farillu sun fi dace wa su shigo ciki,
An karbo daga Bara'u dan Azib Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce da ni :idan kazo kwanciya to ka yi alwala, alwala irin na salla, ka kishingida a baryarka na dama, ka ce : ya Allah na mika rayi na a gare ka na fiskantar da fiska ta a gare ka, na fawwala al'amari na zuwa gare ka, na komar da baya ta zuwa gare ka, halin kwadayi da tsoro  gare ka, ba mafaka da matsirata daga gare ka sai izuwa gare ka, na yi imani da littafinka da ka saukar, da Annabinka da ka turo, to idan ka mutu to zaka mutu ne a kan fidira ka sanya su karshen abin da za ka fadi.)Buhari da Muslim ne suka rawaito.
 Idan fidira ta kasance ita ce sa'adar mutum ta hanyar gyaruwarta to lalacewarta kuwa ita ce daidaicewar mutum da walakantarsa da hasararsa to ya wajaba mutum ya nesaci abin da zai sanja ta ya lalata ta, kuma mafi hadarin aiki da zai sanja ta ya lalata ta shine shirka, wato hada Allah da wani a bauta, ko sifanta Allah da abin da ya tsarkaka daga shi, na daga da ko aboki, kamar fadin mushrikan larabawa kafin turo Manzo na cewa : Mala'iku 'ya'ya mata ne na Allah, da wanda ya yi irin wannan zance,
 An karbo daga Abdullahi dan Abbas Allah ya kara yarda a gare su daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : Allah Madaukakin sarki ya ce :Dan Adam ya karyata Ni , kuma bai dace ya yi hakan ba, Dan Adam ya zage Ni kuma bai dace ya yi hakan ba, Amma karya ta Ni da yayi ita ce zaton sa da ya yi na cewa ba zan iya maida shi kamar yadda ya ke ba, amma zagi Na da ya yi shi ne cewa da ya yi ina da da, tsarki ya tabbata a gare Ni da na riki da,) Buhari ne ya rawaito. A hadisin Abu Huraira :Amma zaginsa gare Ni cewarsa : Allah ya riki da  Alhali kuwa Nine Allah tilo Assamad bai haifa ba kuma ba a haife shi ba, bai da wanda yake kininSa,
Wannan yayi nuni da fadinsu ya fi muni a kan masu bautan gumaka. shirka Allah ba ya gafarta shi sai da tuba Allah  Madaukakin sarki ya ce :( lalle wanda ya ke hada Allah da wani to hakika Allah ya haramta Aljanna a gare shi kuma babu wasu mataimaka ga azzalumai )
Na daga cikin abin da ya ke sauya fidra kuma ya bata ta akwai zunubai da aikata sabo Allah bai halaka alumman da su ka gabace mu ba face sabo da lalacewan fidransu da kuma ketare iyakansu daga umarnin Allah mabuwayi da daukaka Allah bai tsiratar da muminai ba da su ke tare da su face da gyaruwan fidrarsu Allah madaukakin sarki ya ce (sai muka tsiratar da wadanda suka yi imani sun kasance kuma suna jin tsoron Allah) ga wannan aya akwai abin lura cikin halaka mutanen ludu gaba dayansu ba wanda ya tsira daga cikin su ko da mutun daya saboda lalacewan fidran su da kuma juyawanta suna aikata alfahasha mai mummuna ba wanda ya tsira sai ludu amincin Allah su tabbata a gare shi da 'ya'yansa mata biyu
Sabo yana lalata fidra ta fiskan abin lura shi ne ko wani Annabi da Allah ya halaka alummarsa wasu sashi sun yi imani da shi sai Allah ya tsiratar da su daga shi amma mutanen ludu hakika sabo ya lalata musu fidrar su sai aka yi musu mafi tsananin ukuba a doron kasa
Na daga cikin abin da ya ke lalata fidra akwai yin zina domin yana da tasiri wurin kazanta zuciya, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (mai zina ba zai yi zina ba a yayin da ya ke zina a halin yana mumini, Barawo ba zai yi sata ba a yayin da ya ke sata a halin yana mumini  mai shan giya ba zai sha giya ba ayayin da ya ke shan giya a halin yana mumini ) Buhari da Muslim ne suka rawaito daga Abi Huraira
  Ibnu mas'ud Alla ya kara yarda a gare shi ya ce: "An hada zina tare da shirka" yana nufin fadin Allah Madaukakin sarki (mazinaci ba zai aura ba face mazinaciya ko mushrika )
To fa giya ita ce ummul kaba'isi wato uwar kazanta Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (ku nisaci ummul kaba'isi) Ibnu Hibban ne ya rawaito da baihaki daga hadisin usman Allah ya kara yarda a gare shi manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (giya matattara ce ta laifi) saboda tana rusa fidra ta lalata gudanarwa da hankali, kayan maye da miyagun kwayoyi su suka fi tsananin lalata fidra da hankali kuma su suka fi hatsari ga alumma, to giya illan ta kan iya zame wa kebabbiya ga mai shanta, kuma yana katangewa daga jin alkura'ani wanda shi ne sababin dukkan alheri, kuma yana kai ma'abocin shi zuwa ga ukuba.
 Na daga cikin abin da ya ke lalata fidra akwai zaluncin bayi ga junan su, rushewar duniya na ga zaluntar bayi sashin su ga sashe,   Allah madaukakin satrki ya ce (kuma wadancan alkaryu mun halaka su a lokacin da suka yi zalunci kuma muka sanya lokacin alkawarin ga halaka su)
Ya kai mutum rabautar ka da gyaruwarka da farincikinka da daidaituwan al'amuranka gaba dayansu da gadanka ga Aljanna mai ni'ima da tsirar ka daga azaban jahima na ga kiyaye daidaitacciyar fidira ta hanyar riko da wannan sharia ta musulunci mikakkiya, Allah Madaukakin satrki ya ce (kuma lalle wannan ne tafarki na yana madaidaici sai ku bi shi kuma kada ku bi wasu hanyoyi su rarraba ku daga barin hanya ta, wannan ne Allah ya muku wasiyya da shi ko za ku ji tsoron Allah)
 Allah ya sanya mini albarka ni da ku a Alkur'ani mai girma ya kuma amfane ni da ku da abin da ke cikinsa na ayoyi da ambato mai hikima.

Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai Mai karfi, Majibincin masu tsoron Allah, ina kyautata yabo ga Ubangiji na kuma ina gode masa bisa ga ni'imominSa da ba mai iya kididdige su sai shi, muna gode masa irin godiyar masu shukura, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya,  Allan mutanen farko da na karshe, kuma na shaida Annabinmu kuma shugabammu Muhammdu bawansa ne kuma ManzonSa ne mai gaskiya amintacce Allah ka yi dadin tsira da aminci da albarka bisa ga bawanka kuma Manzon ka muhammad da iyalansa da sahabbansa da wanda suka bi su da kyautatawa zuwa ranan sakayya, bayan haka ku ji soron Allah madaukaki cancancin soron shi ku kiyaye saba wa shari'arsa ba wanda zai rabauta cikin wanda su ka saba mishi. 
Ya ku bayin Allah ku kyautatawa kanku ta hanyar daidaituwa kan tafarki, hakika Allah ya kyautata muku da shiriya da nau'ka na karama ya kai mutun : ka tsarkake ranka daga kazantaccen abubuwa ka tsarkaketa ta hanyan amsa kira da karban abinda Ubangijinka ke kiran ka zuwa gare shi Allah Madukakin sarki ya ce (ku amsa wa Ubangijinku tun gabanin wani yini ya zo ba bu makawa gare shi daga Allah ba ku da wata mafaka a ranan nan kuma ba ku iya yin wani musu )
Idan ka amsa ya kai mutun ga umarni to za ka tashi da shi idan ka amsa kira ga hani kuma to za ka nesace shi, to hakika matsayinka zai daukaka a wurin Ubangijinka kuma ka karrama  kanka ka gode wa ni'man fidra wacce ta ke ita ce mafi girman ni'ma. Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Lalle Allah na daga darajan wasu mutane da wannan Alkur'ani, kuma ya kan yi kasa da wasu dalilin shi)
da kuma abin da al ummu su ka canja wanda ta wofanta daga fidrar Allah ba su amsa kiran Manzanninsu ba sai su ka walakanta a wurin Allah kuma za su auka cikin tozarci da kuma hasara ) Allah madaukakin sarki ya ce:( saboda haka ko wannen su mun kama shi da laifinsa daga cikin su akwai wanda muka aika iskar tsakuwa akan sa kuma daga cikin su akwai wanda tsawa ta kama kuma daga cikin su akwai wanda muka birkice kasa da shi , kuma daga cikinsu akwai wanda muka nutsar, baya yiwuwa ga Allah ya zalunce su , amma sun kasan ce kan su su ke zalunta )

Ya ku bayin Allah! lallai Allah da mala'ikunsa suna salati ga Annabi, ya ku wadanda su ka yi imani ku yi salati gare shi da aminci tabbatacce .      

الأحد، 15 ديسمبر 2019

SURAR DA KE BAYANIN DALILAN TSIRA DAGA HASARA


Hudubar Masallacin Annabi na shaikh Ahmad Bin Dalib 16-4-1441Ah/13-12-2019
Hudubar farko
Allah yana fadi a cikin littafinSa mai girma, kuma shi ne mafi gaskiyar masu magana. (Ina rantsuwa da zamani. Lalle mutum na cikin hasara. Face wadanda suka yi imani kuma suka yi aiki na kwarai kuma suka yi wasiyya ga juna da gaskiya kuma suka yi wasiyya da hakuri.)
Allah ya yi rantsuwa da Asr wato zamani ko kuma wani yanki na shi, wato lokacin yammaci, shi aka yi rantsuwa da shi kan cewa lalle jinsi na mutum na cikin hasara, to kowa duk wanda ya kasance haka to makomarsa gidan halaka tir da matabbata, sai Allah ya toge daga cikin hasararrun wadanda suka siffatu da sifofin nan guda hudu da ayoyi bayyanannu suka nuna:
Sifa ta farko ita ce  a fadinSa: "Face wadanda suka yi imani" Imani kuma asalin shi da kamalarsa bai samuwa sai da ilimi.
Sifa ta biyu ita ce  a fadinSa:" kuma suka yi aiki na kwarai" shi aiki na kwarai shi ne wanda aka yi shi don Allah kuma bisa koyarwar Manzon Allah.
 Sifa ta uku ita ce  a fadinSa Madaukakin ambato :" : "kuma suka yi wasiyya ga juna da gaskiya" Hakikaninta kira zuwa ga Allah.
Sifa ta hudu ita ce  a fadinSa Tabaraka wata'ala : " kuma suka yi wasiyya da hakuri." Wato suka Siffatu da wannan sifa mai kubutarwa daga hasara.
Duk wanda ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, kuma ya yarda musulunci shine addini, kuma ya yarda Muhammad  a matsayin Annabi kuma Manzo, ya san abin da Allah ya ke kauna, ya fahimci manufa na wahayin Allah, ya yi aiki na kwarai don Allah, ya tsarkake shi daga shirka, da bidia abin munantarwa, ya maida kansa kamili ta hanyar ilimi mai amfani da aiki na kwarai, sannan ya yi kokari wurin maida waninsa ma kamili ta hanyar kiransa zuwa ga gaskiyan da ya samu, ya yi wasiyya kuma ya nemi a mar nasiha da abin da zaa tambayi kowa a kabarinsa na sanin Allah da sanin Manzonsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da sanin addinin musulunci, sani da ke tare da dalilanta na  daga littafin Allah  da sunnan Manzonsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da kuma abin da aka karbo daga sahabbai da limamai na addini  masu shiryarwa. Kuma ya yi hakuri bisa imani da aiki na kwarai, da kuma kira zuwa ga Allah Mabuwayi da daukaka yana yin shi a aikace da neman sani da ilmantarwa, da kuma hakuri bisa abin da ke faruwa na cutarwa ga duk wanda ya  riki tafarkin Annabawa, to hakika wallahi ya tsira da hasara na rantse da Ubangijin zamani.
Sabo da cika na wannan sura mai girma tare da gajarcinta wajen bayanin abin da zaa umarci mutane don su tsira su rabauta Abu Abdullahi Imam Al shafi'i Allah ya jikan shi ya ke cewa: "Wannan sura da Allah bai saukar da wata hujja ba ga bayinSa sai ita to ta ishe su."
Ai da ta ishe su wajen tsaida musu hujja sabo da wajabcin riko da umarnin Allah na sharia, ta hanyar gaskata wahayi na Allah, da bin umarninSa da nesatan haninSa,da kudurta abin da Allah Mai tsarki  ya halatta.
Allah sa min Albarka ni da ku.

Huduba ta biyu
Allah Madaukakin sarki yana cewa  (ka sani cewa ba abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma ka nemi gafarar zunubinka da na muminai maza da muminai mata Allah ya sa majuyarku da mazauninku).
 Sufyan Bin Uyaina  Allah ya masa rahama ya ce : "sai ya fara da ilimi kafi fadi da aiki,"  dukkan shiriya na cikin sanin ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, Addinin gaskiya gabadayansa ya kunshi neman gafara ne gurin Allah da tuba zuwa gare shi furuci da aiki,
Allah Mabuwayi da Dauka yana cewa  (Suna so su bice hasken Allah da bakunansu alhali kuwa Allah Mai kammala haskenSa ne ko da kafurai sun ki.shi ne wanda ya turo ManzonSa da shiriya da Addinin gaskiya don ya daukaka shi akan dukkan addinai ko da mushrikai sun ki)

الأربعاء، 11 ديسمبر 2019

HUNTURU LOKACIN KAKA NE NA MUMINI


Hudubar Masallacin Annabi na shaikh Abdullah Bin    Abdurrahman Albuaijan 9-4-1441AH/6-12-2019AC
Hudubar farko
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah masanin gaibi Mai suturce aibi mai yaye bakinciki Mai yafe zunubai Mai tsinkayan dukkan sirri da ke zukata, muna gode masa kuma muna neman taimakonSa muna neman gafararSa muna kuma tuba zuwa gare shi.
Muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu, muna riko da shi (Allah) a dukkan al'amuranmu da yanayinmu.
Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai yake ba shi da abokin tarayya.
Kuma na shaida Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, ya isar da sako kuma ya sauke amana.ya yi nasiha ga al'uma ya yi jahadi don Allah cancancin jahadi har mutuwa ta zo masa. Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalanSa da sahabbanSa baki daya.
Bayan haka,
Mafi alherin zance shine maganar Allah, mafi alherin shiriya shi ne koyarwar Annabi Muhammad, mafi sharrin al'amura shine fararrunsu, kuma dukkan bid'ah bata ce, kuma dukkan bata na wuta.
Ya ku bayin Allah ku ji tsoron Allah cikin umarninsa ku hanu daga abin da ya yi hani a kai ya kuma tsawatar. (ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah cancancin tsoronSa kada ku mutu face kuna musulmi)
 Ya ku bayin Allah!
Lallai ga karewan kwanaki akwai abin lura, ga abin da ya shude kuma a kwai tunatarwa da izina (Allah na juya dare da wuni, lalle ga hakan  akwai abin lura ga ma'abota basira).  
Ranaku da watanni da lokutan shekara, da shekaru na shudewa suna bin junan su, burace – burace da ajali na karewa, wasu al'uman na riskan wasu,  (Duk wanda ke kanta zai kare sai fiskar Ubangijinka ma'aboci daukaka da karamci zai wanzu).
 Ya ku jama'ar Musulmai!
 Hakika lokacin hunturu ya fiskanto ku, sanyinsa mai gargadi ne, Allah ya yiwa jahannama izini da ta numfasa a cikinsa, An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi yace :Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( wuta ta koka zuwa ga Ubangijinta sai ta ce :" sashi na ya ci sashi, sai Allah ya sanya mata numfasawa biyu :numfasawa daya a lokacin hunturu,dayan kuma a lokacin bazara, shi numfasawarta na lokacin hunturu to shine jaura, na lokacin bazara kuma shine wannan iska mai tururi)Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
An rawaito daga Umar dan khaddabi cewa idan hunturu ya zo sai ya bibiyi talakawansa sai ya rubuta zuwa gare su : "Lalle hunturu ya zo kuma shi makiyi ne to ku masa shiri na daga fatu da hoffofi da safanni, ku riki fatu a matsayin riga 'yar ciki da ta waje, domin sanyi makiyi ne mai saurin shiga (jiki) mai dadewa bai fita ba".
  To ku bibiyi bayin Allah -masu rauni- ku taimaka musu bisa sanyin hunturu, ku bibiye su don basu abinci da tufafi da mayafi, ku nemi ladan su gurin Allah a ranar gamuwa, (Duk abin da ku ke ciyarwa na alheri to don kan ku ne, ba wani abu da za ku ciyar face don neman yardar  Allah, ba wani abu da zaku ciyar na alheri face an cika muku shi, a halin ku ba zaa zalunce ku ba.)


Ya ku bayin Allah!
Ku yi lura da wadannan zamuna da lokutan shekara da abin da ke cikinsu na maslahohi da hikimomi, da ace zamanin gaba daya lokaci guda ne cikin lokutan shekara da wasu maslahohin an rasa su wato na sauran fasalin, kamar da dukkan shekara bazara ce to da an rasa amfani da maslahohin hunturu, haka ma in da kaka ne gaba dayansa ko   damina  dukaninsa.
Abin mamaki ta yaya zaa sabawa Ubangiji***
                     Ko ta yaya wani mai korewa zai kore shi*
Cikin komai akwai alama tasa***
                    Da ke nuni cewa shi kadai ne*

Ya ku jama'ar Musulmai!
Hunturu ya fiskanto, to maraba da ganimar masu bautan Allah, da kuma kaka ta muminai, dare na tsawaita cikin shi sai su samu rabon su na barci, sannan hakarkarinsu na yin nesa daga makwanci, don su yi tsayuwan dare, wuninsa mai sanyi na gajarta don ya saukake musu wahalar azumi.
Allah Madaukakin sarki ya ce : (lallai masu tsoron Allah suna cikin lambuna da maremari. Suna masu dibar abin da Ubangijinsu ya ba su, lallai su sun kasance masu kyautatawa a gabanin haka(a duniya). Sun kasance a lokaci kadan na dare suke yin barci. Kuma a lokutan asuba suna ta yin istigfari.)
Lokacin Hunturu -Ya ku bayin Allah! - Lokaci ne na kaka ga muminai, suna kiwo cikin gonakan da'a ga Allah. Suna shakatawa a fagage na ibadoji zukatansu na walwawa cikin dausayin kusantar Ubangiji, an samu saukin wahala da gajiya, azumin bai gajiyar da su, ko dare ya kuntata gare su ga barcinsu ko tsayuwansu na  dare.
An rawaito daga Amir dan Mas'ud Allah ya kara yarda a gare shi ya ce :Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :"Azumi cikin hunturu wata ganima ce na ruwan sanyi)Ahmad da Tirmizi ne suka rawaito.
Abdullahi dan salam ya ce :A yayin da Annabi ya zo garin Madina mutane sun yi cacarindo zuwa gare shi, Sai na shigo cikin mutane don na gan shi, a yayin da na samu ganin fiskar shi sai na tabbatar wannan fiskar ba na makaryaci ba ne,farkon maganar da ya fara da ita ya ce  : (ya ku mutane ku yada sallama ku ciyar da abinci, ku sada zumunci, ku yi salla a halin mutane suna barci za ku shiga Aljannar Ubangijinku da aminci).Ahmad da Tirmizi ne suka rawaito,kuma ya inganta shi.
Yayin da mutuwa ta zo wa Mu'az Bin Jabal sai ya ce ga kuyangarsa : "kaiton ki shin gari ya waye? Sai tace : a'a, sai ya kyale ta zuwa bayan wani dan lokaci sai ya ce: ki duba, da ta duba sai tace ; "e"  sai ya ce : Ina neman tsarin Allah daga safiyar da za ta kai zuwa ga wuta, sannan sai yace : Maraba da mutuwa, maraba da bakon da yazo ana halin talauci, duk wanda ya yi nadama ba zai rabauta ba, Allah ka san ba wai ina bukatar zama a duniya ba ne sabo da tona sabbin rami na koramai ba, ko dashen itatuwa ba, sai dai ina son zama ne don na dage da kokari a daren hunturu mai tsawo, da kuma fiskantar kishin garji a lokacin tsananin zafi, da kuma gogayya da malamai a sahun halkan ambaton Allah."

Ya ku bayin Allah!
A lokacin hunturu ne dare ke tsawaita wuni ke gajarta, Hakika Allah ya sanya dare sutura, ya sanya barci kuma hutu, wuni kuma don neman abin rayuwa.
(Allah ne wanda ya sanya muku dare domin ku natsu a cikinsa, da rana mai ganarwa, lalle Allah hakika Ma'abocin falala ne a kan mutane, kuma amma mafi yawan mutane ba su godewa.)
 Hakika dimantan kwana ba barci wata cuta ce mai tafiyar da nashadi, mai kashe jiki,  mai hana neman arziki da aiki, kuma yana banzatar da lokuta, kuma yana shagaltarwa daga da'a, kuma ya sabawa sunna.
Allah Madaukakin sarki ya ce :(kuma na daga cikin ayoyinSa barcinku a cikin dare da wuni, da neman ku ga falalarSa, lalle a cikin wannan akwai ayoyi ga mutane masu saurarawa.)
 Annabi ya kasance yana kin barci kafinta da zance bayanta –wato sallar lisha-
Ina neman tsarin Allah daga sharrin shaidan abin jefewa. (kuma shi ne wanda ya sanya muku dare ya zama tufa, da barci ya zama hutawa, da yini ya zama lokacin tashi).
Allah ya sa min albarka ni da ku a cikin Alkur'ani.

Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah bisa datarwarSa da kyautatawarSa, tsira da amincin Allah su tabbata ga Muhammad Mai kira zuwa ga yardarSa, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalanSa da sahabbansa, da 'yan uwansa.
Ya jama'ar Musulmai!
Lalle ba abin da musulunci ya bari a halin rayuwa , ya yi la'akari da sanjawar zamani da lokuta sai ya shar'anta hukunce –hukunce na azima da sauki a yayin larura.
Na daga cikin abin da Allah ya ke daga darajoji da shi, ya kuma kankare kusakurai da laifuka akwai gaggautawa zuwa ga tsarki, wanda sharadi ne na ibadoji, kuma rabi ne na imani, kuma sharadi ne na salla wanda yake rukuni ne na musulunci. To dagewa  da jurewa da hakuri ga abin da aka ki, da bauta ta hanyan amfani da ruwa a lokacin sanyi a hunturu, na cikin masu kankare zunubai, An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce :Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :"Ase ba zan nusar da ku ga abin da Allah ke goge zunubai da shi ba, kuma ya daga darajoji da shi? Su ka ce : E ya Manzon Allah,sai yace : Yalwata alwala a halin ba a so, da yawan taku zuwa ga masallatayya, da jiran salla bayan idar da salla: Wancannin ku shi ne Ribadi )Muslim ne ya rawaito.

Ya ku bayin Allah
Na daga cikin sauki irin na shari'a da hikima na musulunci da rangwami da saukakawa mutane a yayin wahala mai bijirowa, da cutuwa da ake tsammani  (kuma bai sanya muku wani abu na kunci ba a addini)
  Duk wani abu mai wahala na janyo  saukakawa, (kuma Allah bai dora wa rai sai abin da ya ba shi, Allah zai sanya sauki bayan tsanani.
   Musulunci ya shar'anta sauki  yayin kunci da whala  da larura, na daga ciki akwai mara lafiya,
Kai har ma mai laifiyan idan ya  tsoracewa kansa, amfani da ruwa to an shar'anta masa taimama da kasa, kamar yadda a ka shar'anta wa wanda ya ji ciwo da ya yi shafa kan abin da ya rufe ciwon ko ma a kan maganin.

  An karbo daga Jabir Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : Mun fita a wata tafiya  sai dutse ya samu wani mutum ya mishi rotse a kai, sai ya yi mafarki sai ya tambayi mutanensa sai yace : ko ina da sauki ko zan iya na yi taimama? Sai suka ce ba ka da wani sauki tunda za ka iya amfani da ruwa, sai ya yi wanka sai ya mutu. Yayin da suka zo gun Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare sai aka bashi labarin hakan sai ya ce:  sun kashe shi Allah ya kashe su, me ya sa ba za su tambaya ba idan basu sani ba, ba komai ba ne maganin jahilci sai tambaya. Ai daya yi taimama kawai da ya isan masa ya matse ko ya daure ciwon nasa da tsumma, sai ya shafa kan ciwo ya kuma wanke sauran jikin nasa )
An karbo daga Amru dan As  Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : Na yi mafarki a dare mai dari a yakin zatus salasil, sai na tausayawa kai na na yi taimama don in nayi wanka zan halaka.sai na yi (jagorancin ) salla ga mutane na sallar asuba, sai su ka ambaci hakan ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sai yace : ya Amru ka yi limanci wa mutanenka a halin kana janaba? Sai na gaya mishi abin da ya hana ni wanka nace ni na ji fadin Allah da ya ke cewa : (kuma kada ku jefa kan ku ga halaka lalle Allah ya kasance mai tausayi ne a gare ku),sai Manzon Allah ya yi dariya bai ce komai ba. Abu Dauda ya rawaito Albani kuma ya inganta shi.