الجمعة، 18 أكتوبر 2019

BADA KARIYA GA AKIDAR MUSULUNCI DAGA SIHIRI DA BOKANCI


Hudubar Masallacin Annabi  na shaikh Abdullah Bin Abdurrahman Albuaijan 19 safar 1441Ah.
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya shiryar da mu ga imani. Ya bayyana mana manyan ginshikai na gaskiya da hujja, ya turo manzanni ya saukar da littafi a gare su tare da mizani.
Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya, shaidawa ta gaskiya da imani, Na shaida Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, an turo shi zuwa ga mutane da aljanu.sai Allah ya tseratar da mu daga dulmuya cikin bata.ya kuma kubutar da mu daga gangarawa cikin kafurci da hasara.tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabbanSa da wanda ya bi su da kyautatawa.
Bayan haka :
Lalle mafi alherin zance shine maganar Allah, mafi alherin shiriya ita ce shiriyar Muhammad dan Abdullah, kuma mafi sharrin al'amura shine fararrunta, kuma dukkan fararrun al'amura bid'a ce kuma dukkan bid'ah bata ce, kuma dukkan bata na wuta.
Ya ku bayin Allah! Ina muku wasiyya da ni kai na da tsoron Allah,Mabuwayi da daukaka,domin shine wasiyyar Allah ga mutanen farko da na karshe (Hakika mun yi wasiyya ga wadanda aka bawa littafi gabaninku da ku kanku da ku ji tsoron Allah).
Ya jamaar musulmi!
Allah ya bawa mutum hanyoyi masu yawa na samun ilimi.ya bashi hankali da fahimta, ya mishi umarni da neman ilimi sai ya ce : (ka yi karatu da sunan Ubangijinka mafi karamci. Wanda ya koyar da alkalami. Ya sanar da mutum abin da bai sani ba).
Allah ya zabi mutum don ya khalifantar da shi a doron kasa kuma ya bashi ilimi don aiki da samun daukaka, ya bashi hankali don a fiskantar da magana gare shi a kuma dora mishi nauyi na sharia sai yace : (A yayin da  Ubangijinka yace ga Malaiku lalle Ni zan sanya mamayi a doron kasa, sai suka ce :zaka sanya a cikinta wanda zai yi barna kuma ya zubar da jini alhali mu muna tasbihi da godiya a gare ka kuma muna tsarkake ka,sai yace lalle ni na san abin da baku sani ba).
  Sai Allah Madaukakin sarki  ya bayyana cewa samun daukaka da daraja na ga ilimi sai yace :( Allah na daukaka darajan wadanda suka yi imani daga cikin ku da wadanda aka bawa ilimi darajoji).

Ya ku bayin Allah!
Lalle mutum ana haifansa jahili ne bai san komai ba, Allah Madaukakin sarki  yace : ( Allah ya fitar da ku daga cikunan uwayenku baku san komai ba).
Hakika Allah ya dauke shamaki na kadan daga cikin ilmomi sai ya bada dama ga bayi da zasu iya riskan su, amma mafi yawan ilimi ya boyu daga riskar mutum. Allah ya ce :  ( Kuma ba a baku wani abu na ilimi ba face dan kadan)  Allah ya kebanta da ilimin gaibi ya boye shi, ya sanya ba wanda ya san hakikanin tawilin shi sai shi kadai. ( A gare shi mabudan gaibi suke, ba wanda ya san su sai shi).
An karbo daga Abdullahi dan Umar Allah ya kara yarda a gare su ya ce daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : (Mabudan gaibi guda biyar ne. ba wanda ya san su sai Allah, Ba wanda ya san abin da mahaifa zata rage sai Allah, ba wanda ya san gobe sai Allah,ba wanda ya san yaushe ruwa zai zo sai Allah,ba wanda ya san rai a wace kasa zai mutu sai Allah, ba wanda ya san yaushe Alkiyama zata tashi sai Allah, sai ya karanta fadin Allah ( A gare shi mabudan gaibi suke, ba wanda ya san su sai shi ya san abin da ke cikin tudu da kogi, ba wani ganye da zai fado face ya san da shi, ko kwaya cikin duhun kasa ko danye ko busasshe face yana cikin littafi bayyananne).Bukhari ne ya rawaito.
Na daga cikin hikima da sunnar Allah ya sanya shamaki tsakanin gaibi da halittunSa har ma da mafi soyuwan mutum cikin bayinSa, Ba wani mala'ika na kusa ko Annabi Manzo, ( Kace ba wanda ya san gaibi cikin sammai da kasa face Allah) kuma ya umarci Manzon Allah da ya maida al'amura zuwa ga Allah, kuma ya bada labari game da kansa cewa bai san gaibi ba, kuma ko tsinkayar wani abu na hakan, face abin da Allah ya sanar da shi, sai yace :  ( Kace ban mallakawa kai na wani abu na amfani ba ko cuta face abin da Allah ya so, da ace na san gaibi da na nemi yawaitawa daga alheri kuma wani abu mummuna bai shafe ni ba.).
 Ya jamaar musulmi!
Zukata na neman sanin gaibi, kuma dukkan boyayyen abu ana kwadayin shi, a cikin su akwai wanda shaidanu kan kaskantar da su da mataimakansu makaryata, da bokanci da duba da masu duba da taurari da sihiri suna kage da karerayi suna fadin abin da ba su sani ba game da Allah,  ( Kace Ubangiji na ya haramta alfahasha ne kawai wanda ya bayyana ko ya boyu daga cikin su da laifi da zalunci ba tare da gaskiya ba kokuma ayi shirka a hada Allah da wani cikin abin da bai saukar ba da shi na hujja ko ku fadi abin da baku sani ba game da Allah .)  kuma hakika shaidanu sun kasance  suna haurawa zuwa sama sai su saci ji don su labartawa mataimakansu na daga bokaye su kuma sai su gayawa mutane labarin to ku saurara lallai shaidanu an hana su satan  ji kuma an yi shamaki tsakaninsu da shi tun lokacin da aka turo Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  hakika alkura'ni ya bada labarin hakan game da su sai ya ce :( lallai mun nemi satar ji daga  sama sai muka sami an cika ta  da matsara masu karfi da taurari masu konewa. Hakika mun kasance gabanta don sauraru, duk wanda yake neman saurara to wanda ya yi sauraru a yanzu ya saci ji to  zai sami tauraru mai dako gare shi da aka dakatar da shi don a jefe shi da shi  (lalle mu bamu sani ba sharri ake nufa da wanda ke doron kasa ko kuma Ubangijinsu ya na nufinsu da shiriya ne) Allah Madaukakin sarki ya ce :  shaidanu ba su sauka da wannan alkura'n  ba  kuma ba zai kamata gare su su saukar da shi ba, kuma baza su samu ikon saukar da shi ba hakika su ababan nesantarwa ne game da  barin jin zancen mala'iku )
Hakika Allah ya hana su zuwa sauraro zuwa ga duniyan sama ya sanya taurari abin jifa ga su ta kowani jiha da suka  fiskanci sama Allah Madaukakin sarki ya ce (Hakika mun kawata saman duniya da adon taurari , Mun kiyaye ta daga kowani shaidani mai taurin kai , ba za su yi sauraro zuwa ga mala'ikun sama ba ana jefesu daga kowace nahiya, ababan korewa suna da azaba madawwamiya a lahira , sai wanda ya fauta guda daya daga mala'iku kuma tauraru mai tsananin haske ya bi shi)  
 ya ku bayin Allah imani da alkura'ni mai girma ba ya haduwa a zuciya da gaskata wadan nan bokaye (dujjalai) sabo da haka ne Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (Duk wanda ya zo ga boka ko dan duba ya gaskata shi cikin abin da ya ke fadi to hakika ya kafurta da abin da aka saukar wa Muhammadu,)
Ku yi katanga da akidar ku kuma ku yi riko da alkura'ninku kuma ku sani lallai Allah shi ne masanin gaibi ba ya bayyana saninSa ga wani .
                                                                             Huduba ta biyu

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai  kyakkyawan karshe  na ga masu tsoron Allah babu gaba sai ga azzalumai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabinmu Muhammad da iyalansa da sahabbansa baki daya ya ku bayin Allah
Hakika an yi jarabawa ga mutane ta hanyar shigowan bokaye da matsafa da masu duba da 'yan tsubbu sai suka yi galaba akan masu rauninsu suna musu dako da wasa da hankulansu dukkan isgilanci har sai sun komo zuwa gare su a lokacin sauki da lokacin cuta suka gaskata su a sha'nin ilimin gaibi da labarin sama, hakika kuma ya tabbata daga Annabi Muhammad an karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce :Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (duk wanda ya zo ga mai duba ko boka sa'nnan kuma ya gaskata shi cikin abin da ya fadi to hakika ya kafurce da abin da aka saukar ga Muhammadu)
An kuma karbo daga Imrana dan Husaini ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (baya tare da mu duk mutumin da yake camfi ko ake mishi camfi kokuma ya ke bokanci ko ake mishi bokanci ko ya ke sihiri ko ake mishi sihiri).
Lallai shaidanu kayan hajansu shi ne karya da kirkira kage Allah Madaukakin sarki ya ce (shin bazan baku labari ba bisa ga wanda shaidanu ke sauka a gare shi , suna sauka ne a bisa dukkan mai yawan karya ko mai kage mai zunubi , su shaidanu suna jefa saurara daga mala'iku ga bokaye yawancin su makaryata ne).
An karbo daga A'isha Allah ya kara yarda a gare ta ta ce: wasu mutane sun tambayi Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi game da masu bokanci sai ya ce :lallai su din nan ba kome bane sai suka ce ya Manzon Allah lallai fa suna bamu labarin a wasu lokutan abin da zai kasance kuma sai ya kasance gaskiya, sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : lallai mala'iku suna sauka zuwa sama a wurin gajimare sai su ambaci abubuwanda za a hukunta a sama sai shaidanu su sauraresu sai su dauki wannan sakon su kai shi zuwa ga  bokaye sai su kara musu karairayi akan abin da suka ji guda dari daga garesu) . A wata riwayan (wancan kalma ce guda daya na gaskiya wanda aljani zai fizgota sai sautin ya fada kunnen masoyansa kamar yanda kukan kaza yake tabbatuwa a kunne sai ya . cakuda shi da karerayi sama da karya dari) Bukari da muslim ne suka rawaito
Ya ku jama'n musulmi
Lallai shaidanun mutane da aljanu abokan juna ne kuma makiya ne a gare ku Allah ya ce( sashinsu na wahayi zuwa ga sashi suna masu kawata zance na rudi ) kuma hakika Allah ya musu alkawarin narkon azaba gaba daya sai ya ce (A ranar da za a tada su gaba daya ya tawagar aljanu gashi kun yawaita akan mutane sai masoyansu na daga mutane suka ce : ya Ubangijinmu sashinmu sun ji dadi da sashi kuma gashi mun kai lokacin da ka sanya mana sai ya ce ai wuta ne makoman ku kuna masu dawwama a cikinta sai inda Allah ya so lallai Ubangijinka mai hikima ne kuma masani)
Bayan haka: ya jama'r musulmai lallai Allah shi ne wanda ya kebanta shi kadan shi da sanin gaibi duk wanda ya ikirarin tarayya da Allah a cikin wani abu na wannan to hakika ya sanya wa Allah abokin tarayya kuma ya yi karya ga Allah da Manzo lallai ku saurara duk wanda ya bar da'a wa Allah zuwa da'a ga waninSa ya biye mishi cikin ala'marin addininsa to hakika ya yi shirka ga Allah Madaukakin sarki, Allah Madaukakin sarki ya ce (lallai shaidanu suna yin wahayi zuwa ga masoyansu domin su yi jayayya da ku, muddin kuka musu da'a to lallai ku din nan kuna cikin masu shirka) ku yi riko da addininku da akidar ku domin ku kuna kan hanya mai haske darenta kaman wuninta ne ba mai zamewa sai wanda ya ke halakakke.


 

الجمعة، 27 سبتمبر 2019

NEMAN MAFAKA WURIN UBANGIJI DA TUNKUDE BALA'I


Hudubar Masallacin Annabi 28-1-1441AH na shaikh Husain Al-Assheikh.
HUDUBAR FARKO
Duniya ba ta tabbatuwa a hali guda, sai an samu wasu lokuta wani yanayi na kunci da bakinciki kan gitta wa mutum, har ma da bacin rai a wasu lokuta,sabo da wasu sabuba ta fiskoki mabanbanta.
To ku saurara ! lalle komawa zuwa ga Allah bisa gaskiya ita ce hanya guda kadai da zata kubutar ta kuma bada kariya daga dukkan bakinciki da bacin rai.tare da kankan da kai  ga Majibinci Allah Tabaraka wa Ta'ala.
Allah Madaukakin sarki ya ce :"kuma lalle ne, Hakika, muna sanin cewa lalle kai,kirjinka yana yin kunci game da abin da suke fada(na izgili). Sabo da haka ka yi tasbihi game da gode wa Ubangijinka, kuma ka kasance cikin masu sujada. Kuma ka bautawa Ubangijinka har mutuwa ta zo maka."
Biyayya ga Allah abu ne na farinciki kamar yadda Takawa kuma abu ne mai sanya annashawa da walwala,to ka lazimci da'a ga Ubangijinka zai yaye ma dukkan bakinciki da ka shiga ya cire maka duk wani kunci. Allah Madaukakin sarki ya ce :"Duk wanda ya ji tsoron Allah to zai sanya mishi mafita kuma ya azurta shi daga ta inda bai tsammani" Allah Mai tsarki da daukaka ya ce :"Lalle masu biyayya na cikin ni'ima"
Kuma wannan ni'imar ta hada da jin dadin zuciya da farincikinta a nan duniya.
Idan ka shiga kunci  ka fada cikin duhun bacin rai to ka lazimci littafin Allah ta hanyar karanta shi da lura da ma'anoninSa tare da amsa kiranSa da aiki da shi, domin haske ne da waraka daga dukkan wahalhalu. Allah Madaukakin sarki ya ce : "ya ku mutane hakika waazi ya zo muku daga Ubanginku da waraka daga abin da yake cikin kiraza da shiriya da rahama ga muminai"
 Allah Madaukakin sarki ya ce : "ka ce shi (Alkur'ani) shiriya ne da waraka ga wadanda suka yi imani"
To duk wanda ya lizimtawa kansa maganar UbangijinSa, hasken sa ya haskaka masa zuciya to zai yaye mar duk wani bakinciki da bacin rai.
Ya Dan'uwa na musulmi:
Idan bakinciki da bacin rai ya dame ka to ka marairaice gaba ga Ubangijinka, ka nuna bukatuwarka zuwa gare shi,ka kankan da kai zuwa ga Mahaliccinka ka rusuna da adu'a, Allah  Madaukakin sarki ya ce : "kuma da Ayyuba a sa'ad da ya yi kiran UbangijinSa, (yace,) lalle ni, cuta ta shafe ni, alhali kuwa kai ne mafi rahamar masu rahama.Sai muka amsa masa, sa'anan muka yaye mishi abin da ke gare shi na cuta, kuma muka kawo masa mutanensa da kwatankwacinsu tare da su, sabo da rahama daga wurinMu da tunatarwa ga masu ibada."
     ka kankan da kai zuwa ga Mai iko ga kowani abu kankan da kai na gaskiya ka roke shi da harshe da gabbai cikin khushu'i ciki da waje, tare da cikakken marairaicewa irin na bawa ga Mahaliccinsa, da bawa ga Majibincinsa, tare da sakankancewa ba tsira da mafaka sai a gare shi Allah  Madaukakin sarki ya ce : "kuma mai kifi a sa'ad da ya tafi yana mai fushi, sai yayi zaton cewa ba za mu kuntata masa ba, sai ya yi kira a cikin duffai cewa ,: Babu abin bautawa face kai. Tsarki ya tabbata a gare ka.Lalle ne ni, na kasance daga azzalumai.sai muka amsa masa, kuma muka tsiratar da shi daga bakin ciki, kamar haka ne muke tsiratar da masu imani."
 Ya tabbata a sunna kwadaitarwa bisa ga wannan Adu'a, kuma ba wani musulmi da zai roki Allah da shi face Allah ya amsa masa, kuma yana cikin adu'o'in yaye bakin ciki da kwaranye bala'i sabo da abin da ya kumsa na ma'ana mai girma na kadaita Allah da girmama shi ta tsarkake shi da bayyana gajartawa da gazawa,na dan-Adam  da zaluntar kai wajen cika alkawari na hakkokin Mahalicci tsarki ya tabbata a gare shi, ba wata ni'ima ga zuciya ko jin dadi ga rai face da cikar tauhidi da tsaida hakki na imani.
Sabo da haka ne ya zo a cikin Bukhari da Muslim Daga Abdullahi dan Abbas  Manzon Allah (tsira da amincin Alllah su tabbata a garshi) ya kasance yana yin wannan addu'ar a lokacinda yaji kansa a yanayin damuwa:
La ilaaha ill-Allaah al-‘Azeem ul-Haleem, Laa
ilaaha ill-Allaah Rabb il-‘arshil-‘azeem, Laa ilaaha
ill-Allaah Rabbis- samawaati wa Rabb il-ard wa
Rabbil-‘arsh il-kareem
Ma'ana :(Ba abin bautawa da gaskiya sai Allah Mai girma Mahakurci, Ba abin bautawa da gaskiya sai Allah Ubangijin Al'arshi Mai girma, Ba abin bautawa da gaskiya sai Allah Ubangijin sammai da kassai Ubangijin Al'arshi mai girma".

Na daga cikin Aduo'in yaye bakinciki da bacin rai wanda ya kumshi rusuna wa Allah  Mabuwayi da daukaka da tawassuli da sunayenSa kyawawa da sifofinSa Madaukaka  akwai : "Ba abin bautawa da gaskiya sai Allah Mahakurci Mai girma.Tsarki ya tabbata ga Allah,Albarka ta tabbata ga Ubangijin Al'arshi Mai girma. Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai."
Ya tabbata daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace :"Ba wata musiba da zata samu wani mutum sai ya ce :

"Ya Ubangiji ni Bawanka ne dan bawanka dan baiwarka, makwankwadar kaina tana hannunka, kuma duk abinda ka Hukunta akaina, kuma Adalci ne Hukuncinka a gareni, ina rokonka da dukkan suna da yake naka wanda ka kira kanka da shi, ko ka saukar da shi a cikin littafinka, ko ka sanar da wani daga cikin bayinka, ko ka fifita saninsa akankin kanka, kasanya Alkur'ani Kakar zuciya ta, da hasken zuciya ta, da kuma yayewar bakin ciki na, da tafiyar damuwa." Face Allah ya tafiyar masa da damuwarsa da bacin ransa ya sauya masa su da farinciki kamar yadda ya zo a nassin Hadisin sabo da haka Annabi yayi umarni da a koye shi (An ce ya Manzon Allah ba za mu koye shi ba sai ya ce : "Ya dace duk wanda ya ji ya koya"
  Na daga cikin adu'o'i  na neman tunkude bakinciki da bacin rai :
 "Ya Ubangiji lallai ni ina neman tsari da kai daga Bacin rai da kuma damuwa, da gajiyawa da Kasala, da rowa da tsoro, da dabaibayewar bashi da galabar Mutane''
Daga ciki akwai (Allah Ubangiji na ba zan hada ka da wani ba   .) daga ciki akwai ya hayyu ya kayyum ; ya rayayye tsayayye  ina neman agaji da rahamar ka.
Ya kai musulmi:

Na daga cikin sabuba mafi girma na farin ciki da jin dadi da walwala  da annashuwa ;  shi ne ka tsaya gaba ga Ubangijin ka  da sallan farilla ko nafila  a lokutan da ba na hani ba kana mai kushu'i  tare da marairaicewa da nuna bukatuwa  ga Ubangiji mabuwayi  kasaitacce  Allah Madaukakin sarki ya ce:- (Ku nemi taimako da hakuri da salla )

Buhari ya rawaito daga Ummu salama Allah ya kara yarda a gare ta  ta ce wata rana  Annabi  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya farka cikin dare   sai ya ce '' tsarki ya tabbata ga Allah , me aka saukar na fitintinu a wannan dare me aka bude na taskoki ? ku tada ma'abota dakuna  sau da yawa  wata za ta zama tana cikin tufafi a duniya amma a cikin tsiraici a lahira .)
 A wata ruwayan kuma (har su samu su yi salla)
Ibn Hajar ya ce;  a wannan hadisi  akwai mustahabbancin gaggautawa zuwa ga salla yayin da aka tsoraci wani sharri , a wurin Muslim kuma fadin sa   tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi (Idan dayan ku ya ga abin da ya tsana (a cikin bacci) to ya tashi ya yi sallah)  A kan haka aikin magabata ya kasance kamar yadda Ibnu Abbas da waninSa suka rawaito.

Huduba ta biyu

Ya ku Bayin Allah!

Kyautatawa da nau'ukanSa na da tasiri na ban mamaki wurin tunkude naui daban –daban na bala'i musamman sadaka. Allah madaukakin sarki ya ce:- (Allah na saka wa masu sadaka). Allah madaukakin sarki ya ce:- (Ku kyautata Allah na son masu kyautatawa).
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(Aikata ayyukan alheri na kare fadawa bala'i, sadakar boye na dushe fushin Ubangiji, sada zumunta na karan tsawon kwana.) Dabarani ya fito da shi a littafinsa Alkabir, Imamul Baihaki da Munziri suka ce isnadinsa hasan ne yana da hanyoyi masu yawa da zasu karfafe shi.
Ya 'yan Uwa a Musulunci:
Samun farinciki da walwala na cikin daa ga Allah da da'a ga ManzonSa  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da aiki na kwarai da gaggawa zuwa ga ayyukan alheri, da lizimtar wajibabbu, da sauran ayyukan da'a,
  Allah madaukakin sarki ya ce:- (wanda ya yi aiki na kwarai namiji ne ko mace a halin yana mumini to zamu raya shi daddadan rayuwa kuma mu saka masa da lada fiye da abin da suka kasance suna aikatawa.)


الأربعاء، 25 سبتمبر 2019

Girman Allah da girmamawanSa ga bawanSa


Hudubar Masallacin Annabi 14-1-1441AH na shaikh Aliyu Bin Abdurrahman Alhuzaifi.
HUDUBAR FARKO
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Mabuwayi mai yawan gafara, yana juya dare akan wuni kuma yana juya yini a kan dare, lalle akwai abin lura a hakan ga masu basira,ina kyautata yabo ga Ubangiji na kuma ina gode mishi bisa ni'imominSa da ba mai iya kididdige su sai shi, daga wadanda muka sani da wadanda ba mu san su ba,sunayen Ubangijinmu sun tsarkaka, siffofinsa sun kasaita, ba abin bautawa da gaskiya sai Allah Tilo Mai rinjaye,na shaida Annabinmu shugabanmu Muhammad bawanSa ne kuma manzonSa ne mai Albishir da rahamar Allah da AljannarSa, mai gargadi da ukubar duniya da azabar wuta, ya Allah ka yi dadin tsira da aminci da albarka ga bawanka kuma Manzonka Muhammad da iyalansa da sahabbansa ma'abota biyayya. Bayan haka ku ji tsoron Allah Madaukaki ta hanyar neman yardarSa da tsoracewa fushinSa da ukubarSa,Allah Tsarki ya tabbata a gare shi yace " Kuma Ubangijinka yake halitta abin da ya so ya kuma zaba, zabi bai kasance na su ba, tsarki ya tabbata ga Allah Madaukaki daga  abin da suke yi na shirka"
Lalle Ubangiji Mabuwayi da daukaka ya halicci halittu da kudurarsa da iliminSa da hikimarSa da rahamarSa ya samar da wannan duniya da ake gani, ya sanya mata wani ajali da zata kare zuwa gare shi ba zata wuce shi ba,ya halicci wannan duniya da muke ciki tare da sababi, ya halicci abin da ke zamewa da sababi kuma shine ke halitta sababi da abin da ke kawo sababin: To duk abin da Allah ya so zai kasance duk abin da bai so ba kuma ba zai kasance ba.Allah Madaukakin sarki ya ce: Allah ne Mahaliccin dukkan komai kuma shine wakili akan kome. Shi ke da mabudan sammai da kasa kuma wadanda suka kafirta da ayoyin Allah, wadannan su ne masu hasara.     Kuma ya ce: "To shine da halittar kuma da umarnin Albarkar Allah Ubangijin halittu ta bayyana! ".
Mutum halitta ne daga cikin halittun Allah na ban mamaki, Allah ya hada mishi sifofi na ban al'ajabi, wdanda ke rarrabe ga wasu halittu da ba shi ba. Allah ya ce : "Lalle ne Mun halitta mutum a cikin mafi kyawon tsayuwa".Allah Madaukakin sarki ya ce: kuma a cikin rayukan ku (akwai ayoyi) kuma ba za ku duba ba?"
Ya kuma ce : "kuma akwai daga ayoyinSa ya halitta ku daga turbaya sai ga ku kun zama mutum kuna watsuwa" kuma Allah ya yi baiwa ga bani adam bisa karrama su sai yace "kuma Lalle ne Mun girmama 'yan Adam kuma muka dauke su a cikin kasa da teku kuma muka azurta su daga abubuwa masu dadi, kuma muka fifita su a kan mafiya yawa daga cikin wadanda muka halitta, fifitawa."
Kuma girmamawa da Allah ya yi wa bani Adam girmama wa ne na gaba daya ga mai biyayya da mai fajirci a nan duniya da ni'imomi, amma kebantacciyar girmama wa a lahira da yardarSa da Aljanna ta ni'ima ga muminai ne kawai, kafuri bai da rabo a lahira, kuma Ubangijinka ba ya zaluntar kowa, amma a lahira Ubangiji bai girmamawa sai ga wanda ya mishi biyayya cikin Mutane da Aljanu.
Ibnu Asakir ya rawaito daga Hadisin Anas dan Malik Allah ya kara yarda a gare shi"Daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace :(Lalle mala'iku sun ce : ya Ubangijinmu ka halicce mu ka halicci bani Adam sai ka sanya su suna cin abinci kuma suna shan abin sha,suna sanya tufafi kuma suna auren mata, kuma suna hawan dabbobi,suna barci suna hutawa, amma mu baka sanya mana wani abu na daga wannan ba, to ka sanya musu a duniya mu kuma ka sanya mana a lahira sai Allah Mabuwayi da daukaka ya ce: Ba zan sanya wanda na halita da hanu na na kuma busa mishi rayi na ba tamkar wadda na ce da shi kasance ! sai ya kasance"
akwai wani hadisin da zai karfafe shi daga hadisin Abdullahi dan Amr wanda Dabrani ya rawaito.
Na daga cikin ni'imomi masu girma da aka yi wa bani Adam akwai hore masa abubuwa masu amfani da maslahohi da ni'imomi, Allah Madaukakin sarki ya ce: "Ase baku ga yadda Allah ya hore muku abin da ke cikin sammai da kasa ba ya kuma yalwata muku ni'imominSa na zahiri da badini " Allah Madaukakin sarki ya ce: ya hore muku abin da ke cikin sammai da kasa baki daya, daga gare shi, lalle cikin haka akwai ayoyi ga mutanen da suke masu tunani."
  Hikima na yalwata ni'imomi ga bani Adam ita ce :don su mika wuya ta hanyar da'a ga Allah Madaukaki su kuma gode masa, kada kuma su hada shi da wani a cikin bauta, Allah Madaukakin sarki ya ce:"kamar wancan ne Allah ya ke cika ni'imarSa a gare ku ko zaku mika wuya.
Ibnu kasir Allah ya mishi rahama ya ce a tafsirinsa:"Ai haka zai sanya muku abin da zaku taimaki kanku cikin al'amuranku da abin da za ku bukace shi don ya zme muku abin da za agaza muku wurin bin Allah da bauta masa"
Allah bai yi nuni ga ambaton dan Adam ba tun da ya halicci Adam da hanunSa da abin da ya ke tsakanin marhala zuwa wata marhala na mutum  face don ya bayyana mishi nauyin da ke kan shi a wannan rayuwa ta duniya kuma ya sanar da shi aikin da ke kan shi, da hikimar da ya sa aka halitta shi, kuma an kallafa mishi umarni da hani kuma yana mai dauke da wannan sharia da kuma daukakaka na bautawa Ubangijinsa Allah Madaukakin sarki ya ce:   " yanzu mutum na zaton zaa bar shi haka kawai ne " Imamusshafi'I Allah ya mishi rahama yace : wato ba za a umarce shi ba ko a hana shi,
Allah Madaukakin sarki ya ce: " To kuna zaton cewa mun halicce ku don wasa ne kuma ba za ku dawo zuwa gare mu ba?
Na daga cikin abin da Allah ya tsara wannan duniya  da abin da ya halitta na sabuba da ke tasiri a samuwar wadannan abubuwa, lalle Allah ya bayyana mana daga cikin sunnoninSa a rayuwa cewa ayyukan dan Adam na inganta rayuwa ta yi dadi idan ayyukan sun yi kyau a nan duniya, haka kuma rayuwa kan baci idan ayyuka suka lalace, kuma ayyukan dan Adam na shiga har cikin dabbobi da tsirrai ya yi tasiri wurin gyaruwansu ko bacin su, bisa rahamar Allah da adalcinsa, don ya lazimtawa mutum da'a kuma ya kauracrwa abubuwan da aka haramta.   Allah Madaukakin sarki ya ce game da albarkar rayuwa da alherinta na ga kyautatuwan ayyukan mutum :- (Da mutanen  alkarya za su yi imani su yi takawa da mun bude mu su  albarkatu daga sama da kasa  sai dai sun karyata sai muka rike su da abin da suka kasance suna aikatawa )

Kuma Allah Madaukakin sarki ya ce :-  (Da ma'abota littafi za su yi imani  su yi takawa da mun kankare musu laifukan su  kuma da mun shigar da su aljanna na ni'ima .  Kuma da a ce sun tsaida attaura da linjila  da abin da aka saukar musu daga Ubangijin su  da sun ci daga saman su da kuma karkashin kafan su )
Kuma Alkur'ani shi ne abin da Allah ya saukar ga musulmai da ahlul kitabi  ba wanda  ya sanja shi sabo da kiyaye shi , kuma Allah Madaukakin sarki ya ce :- (Wadanda suka yi imani basu chakuda imanin su da zalunci ba wadannan suna da aminci kuma su ne shiryayyu)
Wato basu churkuda imanin su da shirka ba , kamar  inda annabin shi ya  fassara shi kuma Allah Madaukakin sarki ya ce :- (Ya ku wadan da suka yi imani in za ku taimaki Allah Allah zai gtaimake ku). Wato in za ku taimaki addinin Allah to zai taimake ku.
 Kuma Allah mabuwayi da daukaka ya ce :- ( Wadan da in mun basu matsayi a doron kasa sai su tsaida salla kuma su bada zakka su yi umarni da kyakkyawa su yi hani da mummuna  , kuma lallai akibar al'amura na wurin Allah ).
Ibn Kasir Allah  ya mishi rahama  ya ce a tafsiri  : ''Umar Dan Abdul-aziz ya yi huduba sai ya karaanta wannan aya sai ya ce : 'ku saurara wannan aya bata tsaya akan jagora kadai ba sai dai ta kunci shugaba da talakawa  a sai  ba zan baku labari ba  da abin da yake hakkin ku ne akan shugaba da kuma abin da ya ke hakkin shi ne akan ku:- na daga  ciki , shi ne ya rike ku da hakkokin Allah da ke kan ku  kuma ya karbi hakkokin wasun ku da ke kan wasu  kuma ya shirye ku zuwa ga abinda yake dacewa iya'iyawan shi  , to, ku kuma ya wajaba a gare Ku ,  ku mishi da'a'' . Afadin Allah (kuma lallai akibar al'amura na wurin Allah ).
Akwai aminci ga wanda ya tashi da wadannan al'amura guda hudu :  Na daga wani da kuma kaidi na makiya  kamar yanda Allah Madaukakin sarki ya ce:- (muddin kuka yi hakuri kuka yi takawa to kaidin su ba zai cutar da ku ba da wani abu  lallai Allah ya iyakance abin da suke aikatawa).
Kuma kamar yanda gyaruwan aikin mutum  yakan game da alheri  to haka namma yake shafi shi mai aikin shi kan shi ,  kamar yanda Allah Madaukakin sarki ya ce :- (Duk wanda ya yi aiki na kwarai  na miji ko mace a halin yana mumini to za mu raya shi rayuwa daddada  kuma za mu sakanya mu su  da ladan su da mafi kyaun abin da suka kasance suna aikatawa).
Ta daya bangaren kuma  da ke kishiyantan wannan  shi kan shi barna na aikin mutum yana cutar da shi kan shi mutum din   kuma ya shigar da shi  barnan a cikin rayuwa ,  Allah Madaukakin sarki ya ce :- (Da a ce gaskiya zai bi soye-soyen rayukan su da sammai da ksa sun   lalace da abin da ke cikin su )  

 Kuma Allah Madaukakin sarki ya ce:- (Barna ta bayyana a doron kasa da taiku  sakamakon abinda hannayen mutane ya aikata  don ya dandana musu wani sashi na abinda suka aikata  ko za su dawo ). Kuma Allah Madaukakin sarki ya ce :- (Duk wani abin da ya same ku na musiba to sakamakon abin da hannayen ku suka aikata ne  kuma yana yafiya ga mafi yawa)

To ka yi lura ya kai mutum halin wadannan da suka munana aiki  abin da ya sauka a gare su  Allah Madaukakin sarki ya ce :- (Sau dayawa muka halaka daga alkaryu wanda sun kasance azzalumai   bayan su muka tada wasu mutane daban)
An karbo daga Abdullahi Dan Umar  Allah ya kara yarda a gare su ya ce :-(  Abubuwa biyar na tare da wasu abub uwa biyar : Alfahasha ba zata bayyana ba a cikin mutane har kuma su bayyana ta karara  face annoba ta bayyana a cikin su da cututtuka irin wanda ba a samu ba daga wadanda suka gabace su.kuma muddin jagororinsu ba su yi hukunci da littafin Allah ba face Allah ya sanya yakinsu a tsakaninsu, kuma ba wasu mutane da zasu hana zakkan dukiyar su face an damke su da fari a kuma hana su ruwan sama ba don dabbobi da ba a saukar musu da ruwa ba, kuma zasu tawaye kilo ba face an rike su fari da zalunci shugaba, baza su warware alkawarin Allah da Manzo ba face Allah ya dora musu makiya akan su, su rika kwace wani sashi na abin da ke hanun su) Ibnu Maja ya rawaito

  Allah Madaukakin sarki ya ce :- (Kuma dan adam bai da wani abu sai abin da ya aikata . Kuma aikin sa da sannu za a gani ). Allah ya sa min albarka ni da ku a cikin alkur'ani mai girma

 HUDUBA TA BIYU
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah mabuwayi mai yawan gafara mai hakuri mai yawan godiya , ina kyautata yabo ga Ubangiji na kuma ina gode mishi  ina tuba zuwa gare shi kuma ina neman gafarar sa ,  to lallai godiya ta tabbata ga Ubangijina a duniya da lahira  bisa falalar sa  da baiwar sa cikin abin da muka sani da wadda ba mu sani  na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya masani da abinda ke cikin zukata  ,  na shaida Annabin mu kuma shugaban mu Muhammad    bawan sa ne kuma Manzon sa ne  wanda aka turo shi  da shiriya da haske Allah ka yi dadin tsira  da aminci da Albarka  bisa ga bawan ka kuma Manzon ka Muhammad  da iyalan sa da sahabban sa  wanda suka yi fintinkau zuwa ga dukkan aiki na da'a .

Bayan haka  ku ji tsoron Allah Madaukaki don ku riki tafarki  zuwa ga Allah wanda zai shigar da ku cikin aljannar sa  ku rabauta da yardan sa   ya kai dan adam yi dubi zuwa ga ni'imomin  Allah a gare ka  da ya ni'imtar kai wanda ba wanda ke da kudura na iyakance su sai Allah kuma ka tashi da godiya gare shi game da su  da zai kwace mafi karancin ni'ima to ba wanda ya isa ya dawo ma da ita sai shi  .
A cikin ni'imar Allah ba wani abu kankani   a halin kuma ga ka ya kai mutum ta hanyar daidaiton ka da gyaruwan ka  da yadawan ka ga alheri  da kuma kamewan ka daga sharri   za ka kasance ka taimaka wurin kiyaye muhallin ka na zama(matattara)  da kuma tseratar da kanka daga sharrace-sharrace , da ukubobi , ka sani lallai kai abin tambaya ne game da ayukan ka a rayuwar ka  da kuma bayan mutuwar ka   to ka yi dubi me za ka gayawa Ubangijin ka Allah Madaukakin sarki ya ce:- (Ya kai  mutum lallai ne kai mai aikin wahal da kai ne zuwa ga Ubangijin ka , wahala mai tsanani to, kai mai haduwa da shi ne.  To amma wanda aka baiwa littafin sa da damarsa .  To za a yi masa hisabi mai sauki . Kuma ya juya zuwa ga iyalan sa (a cikin aljanna) yana mai raha. Kuma amma wanda aka baiwa littafin sa daga wajen bayan sa .  To za shi dinga kiran halaka kuma ya shiga (wutar) sa'ira .

    
Ya zo a hadisi:- (Kafan bawa baza su gushe ba har sai an tambaye shi game da abubuwa guda hudu;  game da rayuwan sa   cikin abin da ya karar da su da samrtan sa   a cikin me ya tafiyar da , da dukiyar sa  daga ina ya same su kuma a me ya ciyar da su,    da kuma aikin sa  mai ya aiwatar da shi ).
Ka sani ya kai mutum lallai gidan ka da ke wanzuwa na dindindi ita ce take gaban ka bayan mutuwa, to dadi ya tabbata a gare ka in ka rayata da ayuka na kwarai  , kuma azaba ya tabbata a gare ka in ka yarda da wannan duniya taka ka manta lahirar ka ,  duniyar ka za ta juya ma baya ne in ka kaunace ta ko  ka ki ta , lahira kuma za ta fiskanto ka  bisa ga abin da ka kaddamar  kuma ita  ta har abada ce .

Ya ku bayin Allah ! lalle Allah da mala'ikunSa suna salati ga Annabi ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi da aminci tabbatacce.

 














   

الثلاثاء، 3 سبتمبر 2019

wasiyya ga dalibai


Hudubar Masallacin Annabi na sheikh Salah Dan Muhammad AlBudair.29 zulhajji 1440AH

Hudubar Farko

Ya ku musulmai
Kokari zuwa ga halaye na mutunci da kyawawan dabi'u dabi'a ce na masu juriya kuma al'ada ce na masu kokari, ilimi shi ne daukaka mai daga darajan mai nemansa kuma aga kiman ma'abocinsa a ido , duk wanda ya so ilimi to falalolin shi kuwa zai kewaye shi abubuwan adonsa su sauka a farfajiyansa. Almuzani ya ce : "na ji shafi'I Allah ya yarda da shi yana cewa duk wanda ya nemi ilimin alkura'ani to kimarsa za ta kara girma duk kuma wanda ya yi nazarin ilimin fikihu matsayinsa zai yi kyau, duk wanda ya rubuta hadisi zai zama yanada karfin hujja duk wanda ya yi nazari a ilimin lugga dabi'arsa za ta tausasa, duk wanda yayi nazari a ilimin hisabi ra'ayin shi zai yawaita duk wanda bai kare kansa ba to iliminsa ba zai mishi amfani ba" .
Al'umma na samun karfi ne ta hanyan ilimi ###  hukunci a cikin zamani ana danganta shi ne zuwa ga alkalami ###sau da yawa tokuba na zubar da jini #### alkaluma kuma na zubo da hikimomi ###da mutane za su yi a'adalci ### da falala a tsakaninsu zata kasance ne  ### ta hanyar digon tawada ba ta hanyar zubar da jini ba ### ka dukufa wurin neman ilimi #### za ka kai kololuwa a matsayi ### a falala  wanda yana kumshe da daukaka da karamci.
ilimi a lokacin fitina ya na baka kariya, a lokacinci  kadaici yana dauke ma kewa yana sanya daukaka a cikin iyalai 
ya ku musulmai:
ga sabuwar shekarar karatu ta kunno kai nan ba da jimawa ba za a bude makarantu da jami'o'i za a karbi dalibai da kauna da maraba to saboda haka ga wasu wasiyyoyi ga dalibai maza da dalibai mata game da wannan munasabar:
Ya kai dalibi to ka koma makaranta tare da kwadayin karatu da farinciki da annashuwa da himma da kokari ka cire mutuwan jiki da jin tawaya da sakaci da kasala .
samun daukaka na ga kokari ### rasawa kuma na ga kasala  ### to ka kafu za ka samu cimma burinka nan kusa  ### lallai matashi wanda ya siffantu da himma irin na mutanen farko ### kuma bai saba rage zance ko aiki ba duk wanda ya sarayarda himma to ba zai cimma bukatunsa ba ### duk wanda ya yi jifa da kifiyoyi na ji ji da kai to ba zai samu ba .
Hakika mai himma ma'aboci hankali za iya cimma gaci ta hanyar da'a ga himmarsa da kuma sabawa son rai.
ya ku dalibai : ku yi sammako ku gaggauto zuwa ga ajin karatu, na horeku da ku nesaci  jinkiri da ja da baya  domin a cikin sammako akwai albarka da samun arziki da najahi da kuma dace,  Tirmizi ya rawaito daga sakr dan gamidi Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (ya Allah ka sa albarka ga alummata a cikin sammakonta , sai ya ce ya kuma kasance  idan ya tura mayaka ko kuma runduna yana turasu ne a farkon wuni sakru ya kasance mutun ne dan kasuwa ya kasance kuma idan ya tura kasuwanci yana tura su ne da jijjifi sai ya zama hanshakin mai kudi dukiyarsa ta yawaita)   
Samun albarkan rana baya tabbatuwa sai da riskan sallan asubahi domin lallai sallan asubahi tamkar wata iska ce mai kamshi da wani yanayi mai dadi ku sammaka kuma ku yi katanga da adu'oyi  na neman kariya da azkar da suka zo daga annabi wadanda suke jefa debe kewa a cikin rayi da farin ciki a cikin zuciya su kara karfi da nashadi a jiki da kariya da kiyayewa ,duk wanda ya bawa ransa rabonta na more rayuwa da mutuwan jikin da sabo da jinkiri da bacci daga barin aikin shi da makarantan shi da hissarsa na karatu to hakika zai rasa  manufarsa danashinar sa zata yi girma, duk wanda ya yawaita kwanciya to zai rasa biyan bukata wanda ya lizimci kasala to zai yi asaran fatarsa shi mutun sakali mai kasala yana rayuwa ne matsiyaci zai zama yayi nesa amma duk wanda ya yi hakuri  to zai rabauta, da hakuri ne ake bude kofofin da suke rufe kuma ayi dace.
Baccin safiya wato yin bacci baya sallar asuba ya halatta sai dai idan zai kai ga sarayar da wajibi, kuma baccin kailula wato baccin azahar mustshabbi ne saboda hadisin Anas Allah ya kara yarda  a gare shi ya ce manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata  a gare shi ya ce (ku yi baccin kailula saboda shaidanu basa yin baccin kailula ) abu nua'im ne ya fitar dashi 
 saboda kailula yana maida nashadi ga kwakwalwa da kuma jiki yana taimaka wa wurin bita da sauke nauyin da ya wajaba akan mutun da kuzari da kuma karfi da nashadi.
ku kiyaye kashe dare da hira domin yana haifar da wahala da kuma sa nauyin jiki kuma bala'i ne da ke bata yanayi, mutun ya kasa sakewa ya kashe mishi kuzari ya jefa mishi gajiya na zuciya da jiki kada  ka fi karfin idanunka ka hana shi barci idan barci ya zo, ka yi barci a farkon dare ka hutar da idanuwanka biyu, kada ka cutar da iyayenka,  a ko wani safiya sau da yawa mun ga wanda ya sarayar da aikin shi ko ya bar karatun shi ko kuma yayi sakaci da iyayen shi da iyalan shi sakamakon bata dare kan abin da ya ke na haram abun zargi tare da wasu abokan banza masu batarwa masu lalatarwa. ya kai dalibi ka yi kwadayin samun ladabi da tsabta da tsarkin zuciya da girmama malami da  lazimtan tsari da kiyaye abin da aka dora ma na karatu, da kiyaye wurin karatu da kuma abin da aka dora ma na karatu na makaranta, ka ji tsoron Allah domin Allah ba abin da ke boyuwa  a gare shi na zuciya ba wani kwayan zarra ko kwayan hancin dibino da zai shiga wa Allah duhu, ka sanya ilim shi ne babban tattalinka ladabi ya zama shi ne tufafinka ka kasance mafi cikan mutane ladabi, mafi tsananinsu wurin kankan da kai, kuma ka zama ka fi su tsarkaka da kuma addini ka zama ka fi su karancin shirme da kuma yawan fushi, ka abokanci mutanen kwarai ka yi nesa daga mutanen sharri, kar ka kusance su kar ka aminta da su kar ka yi cakudedeniya da su ko ka zauna da su, kada ka zauna zuwa ga mutanen banza domin halayen wawaye yana raba  mafi sharrin mutane shi ne wanda bai damu mutane su gan shi ba yana mummunan abu, duk wanda ya so yayi ababan mutunci to zai nesaci abubuwa na haramun kar ka saki ganinka kada ka kafa ganinka zuwa ga waninka domin idanuwa tarkon shaidan ne duk wanda ya saki ganin shi zai hadu da ajalin shi, na horeka kar ka kai kanka wuraren abin tuhuma da  abin da zai haifar da shakku na horeka da kar ka yi abin daza ka zo kana bada uzuri ka dauki izina daga waninka duk mutumin da luran shi ya yi yawa to kusakuren shi za su karanta, lallai rabautacce mai samun sa'ada yana da abin wa'azi ga wanin shi kuma yana mai daukan gogewa a matsayin abin da zai yi mishi hukunci  abin da zai rika lura da shi, na gargade ka da dukkan wani wasa wanda zai haifar da kiyayya ko ya zubar da kwarjini,  ba daukaka shi ne a kyakkyawan tufafi ba sai dai daukaka na nan ga ilimi ne da ladabi da addini, harshe waziri ne na mutun idan baka iya fadan magana wanda ya ke na daidai ba to ka yi shuru daga abin da yake ba daidai ba shi kanshi shi ne daidai, kada ka kasance cikin wanda ya ke aibata wa sannan ya na yawaita zagi yana yawaita suka ga abokai kada ka bankado laifukan mutane muddin sun boye sai Allah ya tona asirinka na daga laifuka, ka ambaci kyawawan abin da ka gani a cikinsu a duk lokacin da aka ambace su  kar ka aibata wani cikinsu a abin da kai ma kana da shi kar ka yi abokantaka da mai kasala, Abubakar alkawarizmi ya na cewa :" kar ka abokanci mai kasala a duk halayensa## sau da yawa mutun na kwarai kan lalace sakamakon bacin wani## raban wawa zuwa ga mai wayo abu ne da yake cikin sauri## baka ganin gaushi da ake dora shi a cikin toka shi ke nan sai gaushin ya mutu ?
A tarbiyantar da al'uma su taso kan kyawawan laduba wajibi ne da ya rataya ne a kan iyaye da majibinta al'amura,  wani daga cikin masu hikima ya ce : "ku yi gaggawa ta hanyan ladabtar da yaranku kafin shungulla su rarraba tsakaninku"
Ya ku dalibai : ku yi gaugawa zuwa ga ilimi wanda  dage mishi  ya dace agare ku, ku kiyayi hayaniya da kuma gajiya da kosawa da kasawa da yankewa .
Ka nema kada ka yi hayaniya wurin neman, laifin dalibi shi ne ya yi hayaniya ku nemi ilimi duk wanda ya nemi ilimi zai mikar da shi tun yana karami kuma zai gabatar da shi idan ya girma.
 Urwa dan zubair ya ce :" 'ya'ya na 'ya'ya na ku nemi ilimi in kun kasance kanana ba a bukatanku, to ya wuci ku zame manya  ba za a wadatu da ku ba."
ku yi kwadayi bisa makarantu domin  makarantu su ne wurin dashe, duk wanda darasi ya kwace mishi to dashe ya baci mishi, ku dimanci kallo a cikin littafi kada ku gaji daga leke leke a littafi da bincike da karatu da kuma daukan rubutu da bita da kuma mudarasa a tsakani da hadda.
Ibnul jauzi Allah ya mishi rahama ya ce : da zan ce lallai ni din nan na tsinkayi littafi littafi da ya kai mujalladi dubu ashirin kai dama sai na ce ma ya kasance ya fi haka a lokacin da na ke nema,
Ya ku dalibai  kokari kokari a tsakanin alkaluma da kuma litttatafai da tawada da abun rubutu har ku riski burinku, wasunsu suka ce na yi kura shekara arba'in ban yi kailula ba ban kwanta ba face littafi na dore akan kirji na an tambayi Imamu Ahmad bin Hanbal Allah ya mishi rahama zuwa yaushe ne mutun zai nemi ilimi sai ya ce "tare da kurtun tawada har zuwa akai shi makabarta" ya kai dalibi kasa natsuwa da bi a hankali da kaifin hankali na horeka da kar kayi gaggawa a wurin tafiya da hauka da nuna danyen kai da yaranta, wanda ke koro sharri ya jefa mutun cikin nadama hakika wanda ya bi a tsanaki zai iya riskan hajarsa wanda ya yi gaggawa kuma zai iya fadawa cikin kuskure, duk wanda ya yi amfani da wayar salula a yayin da yake tuki to hakika ya kai kansa ga hatsarin mutuwa ya kai kansa zuwa ga bakin halaka da abin da ya ke makruhi saboda waya yana dauke hankali da ji ya sa mutun ya rasa kulawa da halartowa da hankali duk mutuninda idonsa ya kafu akan waya ya saki kunnuwarsa ya sunkuyar da kansa da kafadunsa ya shagalta da tattaunawa da ture ture da yada tagrida da ababan kallo  a halin yana tafiya to hakika ya zo da wani babban laifi da wani abin da aka ki, to ka sanya tunanika ka tattaro da hankalinka zuwa ga inda ka nufa da abin da ka fiskanta da tukinka idan wani abu ya zo ma na tunani ko na sada wani zumunci ta wayarka to ka fita daga kan hanya ka tsaida abin hawanka to ka kare bukatarka da wayarka ka kame kanka daga cutar da musulmai da kuma shi kanshi sharrinka kafin wani abin ki ya faru har ya sanyaka ka yi bakinciki da nadama da hasara da kaji radadi ka ce wayane ya mantar da ni ya makantar da ni ya shagaltar da ni a wannan lokacin kuma nadama ba zata yi amfani ba bayan kafarka ta riga ta zame.
Kuyi salati da aminci bisa ga Ahmadu mai shiryarwa mai   
mai ceto ga halittu gaba daya .                       

 

Huduba ta biyu

Ya ku dalibai : girmama malami fa wajibi ne mutunta shi da kimanta shi da kankan da kai  a gare shi farilla ne na tilas, sanin falalan ilimi da gode wa mai kyau aiki ne daga cikin abubuwa na kyawawan dabi'u masu daraja dalibi na siffantuwa da ladabi a ajinsa hakama tare da abokan karatunsa domin wannan shi ne girmama ilimi da kuma ma'abotansa Umar dan kaddabi Allah ya kara  yarda agareshui ya ce : (ku nemi ilimi kuma ku ilmantar da mutane shi ku nemi ilimin mutuntawa da kuma nitsuwa ku yi tawaliu ga wanda kuka koya daga gareshi da kuma wanda kuke koyarda shi kar ku kasance masu jiji da kai na daga malammai shi malami yana cikin manyanmu ne abun girmamawa cikin manya kuma girmama manya yana cikin abnda aka samo daga hadisi)
  An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda  a gare shi daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata  a gare shi ya ce (Duk mutuminda bai tausaya wa karaminmu ba kuma bai san kiman ko hakkin babbanmu ba to baya tare da mu)
Tashi don malami ka girmamashi ###
                                      malami ya kusa ya zama manzo .
yanzu ka san wanda yafi daukaka ###
fiye da wanda yake gina kuma ya tada rayuka da hankula ?!.
tsarki ya tabbata a gare ka mafi aherin masu ilmantarwa ### ka ilmantar da alkalami karnonin da suka shude na farko
.ka fidda wannan hankalin daga duhunsa ### ka shiryar da shi zuwa ga hanya na haske bayyananne .
katuro Annabi Musa da attaura yana mai shiryarwa ### dan batulu kuma ya ilmantar da injila .
sai ka bubbugo da mabubbuga na bayani ## sai ya shayar da hadisi kuma ya bada alkura'ani (tanzila).