الجمعة، 3 مايو 2019

Ayyukan Biyayya a Watan Ramadan


Hudubar Masallacin Annabi 28-8-1440AH Sheikh Abdulmuhsin Alkasim
Hudubar Farko
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah muna gode masa kuma muna neman taimakonsa da gafararsa, muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu, da munanan ayyukanmu, duk wanda Allah ya shiryar da shi babu mai batar da shi, kuma duk wanda ya batar babu mai shiryar da shi, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah,shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, na kuma shaida Annabinmu Muhammad bawansa ne kuma manzonsa ne, tsira da amincin Allah su tabbata gare shi da iyalansa da sahabbansa da aminci tabbatacciya mai yawa.
Bayan haka,
 ku ji tsoron Allah yadda ya dace a ji tsoron shi, ku yi riko da igiya mai karfi na musulunci.
Ya ku Musulmai!
Ranaku da dararraki na ta tafiya da sauri,ga shekara na kokarin nade tabarmarsa da gaggawa,.bayi na tafiya zuwa ga Allah ! kuma su riski ayyukansa.
Na daga falalar Allah da karamcinsa ya zaba mana wasu lokuta na da'a, ya zabi wasu ranaku da dararraki da wasu sa'o'i, domin kwadayin rahamar Allah ya yawaita a samu karin kaimi da masu zage damtse,da gasar masu gasa cikin ayyukan alheri, a duk lokacin da jinjirin watar ramadana ya kada sai ya buso mana da wasu albarka masu yawa, sai musulmai su fiskance shi da annashawa, zukatarsu su cika da farinciki sabo da shi,ta iya yiwuwa sa'a guda da zaa riska ta daga darajan mutum ta sa Allah ya yarda da shi ya kuma samu walwala,
Ga wata mafi daraja ta dumfaro mu,lokaci ne mai girma da Allah ya kebance ta da daukakawa da girmamawa, sai ya turo manzonsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya sauke littafinsa a cikinta,ya wajabta azumtarta, sa'ointa na da albarka, lokutan cikinta ana raya su da ayyukan alheri, alheri na bibiyan juna a ciki,albarka na gamewa a ciki,lokaci ne na kyautatawa da bada sadakoki, lokaci ne na gafara da kankare laifuka, wuninta azumi darenta kuma tsayuwan dare ana nafila, ana raya ta da sallah da karatun Alkur'ani,Ana bude kofofin Aljanna,ana kulle kofofin wuta,ana daure shaidanu a cikinta, a cikinta akwai dare guda da ya fi watanni dubu, wanda ya rasa alherinta lalle ya yi hasara.
Ramadana fage ne mai fadi na gasa cikin ayyukan da'a,  kuma wani kyauta ne na tsarkake rayuka daga kazanta da laifuka,wata ne mai girma ana ribanya ayyukan Alheri, ana kankare kusakurai da laifuka, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(Salloli guda biyar da juma'a zuwa juma'a da Ramadan zuwa ramadan kankara ne ga abin da ke tsakanin su muddin aka nesaci manyan zunubai)Muslim ne ya rawaito
A cikin ta musulmai ke sauke rukuni daga cikin rukunan musulunci, kuma wani abu ne na aiki bayyananne da ke nuna girman wannan addini da hadin kan musulmai, a cikinta ne fadin Allah Madaukakin sarki ke bayyana na cewa : (Lalle wannan Al'umarku ce Al'uma guda Ni kuma Ubangijinku ne to ku bauta mini).
Ribatan lokutan alheri budi ne daga Allah ga wanda ya so na daga bayinSa, a cikin Ramadan tushen ibadoji  kuma mafi girma ke haduwa ga musulmai, sallah sadarwa ne tsakanin bawa da Ubangijinsa, bata rabuwa da musulmi a dukkan rayuwarsa,sallan mutum cikin jam'I farilla ne ta fi sallarsa a gidansa da kasuwansa da lada ashirin da bakwai.
Ya dace ga musulmi da ya nemi taimako da azuminsa bisa sallarsa, kuma ya zama yana kaso mafi girma na sallah To ( wanda ya yi tsayuwan Ramadan bisa imani da neman lada zaa gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa)Bukhari da muslim ne ya rawaito. Duk ( wanda ya yi tsayuwan dare  tare da liman har aka tashi  za a rubuta mishi cikakken tsayuwan dare ) Tirmizi ne ya rawaito.
Zakka da sadaka tsarkaka ne da habaka ga dukiya kuma  wadata ne ga zuci da tsarkaka, tasirinta a bayyane yake ga rayi da dukiya da   da, tana tunkude bala'I, tana janyo yalwa, wanda ya yi wa bayin Allah kyauta Allah zai yi masa, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(Allah Mabuwayi da daukaka ya ce: Ya kai dan Adam ka ciyar zan ciyar da kai)Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Dukkan mutum na karkashin inuwar sadakarsa ranar alkiyan, to ku yi sadaka ko da da dan kadan ne, ka jiyar wa kanka dadi, ka sadar da zumunci da shi ga wanda bai da shi, Duk wanda ya shayar da mai azumi to yana da kwatankwacinsa na lada, kuma na daga cikin kyautarsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi akwai ciyarwa da kuma kyauta, yana bada kyautar mutumin da bai tsoron talauci, in ya ciyar zai bada da yawa, in ya bada kyauta zai yawaita , ba ya maida mai tambaya. Baa tambayarsa wani abu ba face sai ya bada,
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance mafi kyauta a cikin azumi to shi yafi iska mai busawa.
Azumi shi ne   alami mafi girma cikin alamomin addini  a cikin wannan wata mai falala  musulmai na guzurin tsoron Allah a cikin shi,  Allah madaukakin sarki ya ce :-(Ya ku wadanda suka yi imani  an wajabta muku yin azumi kamar yanda aka wajabtawa wadanda suka gabace ku ko za ku samu tsoron Allah)
Ladan shi ba yi da kididdiga ko iyaka, Allah Madaukakin sarki ya ce a hadisin Alkudsi:  ( Dukkan aikin dan adam na shi ne sai azumi, lalle shi nawa ne kuma ni nake sakanya wa game da shi)  Buhari da Muslim ne  suka rawaito.
Kuma ( wanda ya yi azumin ramadana yana mai neman lada an gafarta mishi zunuban sa)
Azumi kan yi shamaki tsakanin ma'abocin shi da sharrace-sharrace  da laifuka  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:- ( azumi garkuwa ce   ).
Umra na daga cikin ayukan da ake riba ta a wannan wata  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :- (yin umra a watan Ramadan na dai-dai da Hajji )Buhari da muslim ne suka rawaito
Kuma kur'ani maganan Allah ne madaukaki kuma hujjan sa ne kan halittun shi , kuma shi wani mabubbuga ne na hikima  , kuma aya ne na sako  babu hanya zuwa ga Allah sai ta hanyar shi   babu tsira gare mu ba tare da shi ba  haske ne  na basira  da kuma gani  wanda ya kusance shi zai samu daukaka , wanda ya yi riko da shi kuma zai samu buwaya  karanta shi lada ne da kuma shiriya , bitar sa kuma ilimi ne da tabbatuwa akan tafarki  aiki da shi kuma wani katanga ne da kuma aminci , koyar da shi kuma da kira zuwa gare shi kambi ne  akan kawunan masu da'a ,  a cikin ramadana ne kur'ani ya sauka  sabo da haka ake karfafa yawan karanta shi a cikin sa da lura da ma'anonin shi  da  koya da koyar da shi  da kuma aiki da shi da riko da koyarwar sa , Allah mabuwayi da daukaka ya ce:- (watan  ramadan wanda aka saukar da kur'rani acikinta  shiriya ne ga mutane,  kuma da bayyanannu na daga shiriya da kuma rarrabewa).
Jibrilu alaihissalatu wassalam  ya kasance yana bitar alkur'a ni da Annabin mu tsira da amincin Allah su tabbata a gare  shi  sau daya a ko wani  shekara , a shekaran da ya rasu kuma ya yi bita da shi  sau biyu  amincin Allah ya tabbata a gare shi .
Adu'a ibada ce kuma kusanci ne   wani garabasa ne ba tare da wahala ba ,  kuma riba ne da ba  tsiya tare da shi  kuma shi yana janyo yalwa , kuma makiyi ne ga dukkan wani bala'i   mutum ba zai taba halaka ba muddin yana tare da adu'a  da shi ne bawa  zai kai ga burin shi ya kuma  riski bukatar shi , sau dayawa yakan kusanto da abin da ke nesa kuma sau dayawa yakan saukake abin da ke da tsanani , sau dayawa yakan yaye bakin cikin abin da akwai bakin ciki a ciki,  kuma mafi karbuwan adu'a  shi ne wanda ya kasance a cikin  yankin karshe na dare  idan bawa ya marairaice gaba ga  Ubangijin shi to, Allah zai amsa rokon shi ,  idan rayi ta ji  yunwa sai zukata su yi taushi , mai azumi ba'a maida adu'ar sa  Ibn Rajab Allah ya kara mishi rahama ya ce :-(Mai azumi yana cikin bauta ne a daren sa da wunin sa  ana kuma amsa mi shi adu'a a azumin shi ya yin shan ruwan shi  , to, a haka shi   mai azumi ne kuma mai hakuri  a daren shi kuma yana mai ci kuma mai godiya ) .
Wanda aka yiwa dace shi ne wanda ya yawaita kwankwasa  kofar sama  ya sanyawa kanshi cikin wadannan kwanaki da dararraki   hyana mai adana .
  Ambaton Allah ibada ce mai girma kuma mai sauki  wanda ya ambaci Allah Allah zai ambace shi , bawa idan harshen shi bai shagaltu da zikiri ba to maganganu marasa amfani za su shagaltar da shi   da kuma sabonnin su .
  Addini mu'amala ne mafi dacewan halittu da kyautatawan ka shi ne wanda  Allah ya hada hakkinsa da na su ,  to iyaye biyu aljannan ka ne  kuma wutan ka  su suka fi dacewa a cikin mutane wurin kyautata mu'amala da su   , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :- ( Hancin shi ya dumbuli kasa , kuma hancin shi ya dumbuli kasa kuma hancinsa ya dumbuli kasa! Sai aka ce :wanene ya Manzon Allah? Sai yace : duk wanda ya riski iyayensa a halin girma dayansu ko dukansu biyu kuma bai shiga Aljanna ba)Muslim ne ya rawaito. kuma (Zumunci na danfare da Al'arshi yana cewa: duk wanda ya sada mini Allah zai sada mishi, wanda ya yanke min Allah zai yanke mishi, wanda zai burge shi a yalwata mi shi arzikin shi a kuma jinkirta mishi  a bayan shi to ya sada zumuncin shi .) Buhari da Muslim ne suka rawaito
 Yan daga cikin cikan da'a a  kiyaye ta daga dukkan abin da zai tawaye ta ko ya warware ta  mai azumi yana da tsananin bukatan  kiyaye ibadar sa da kiyaye azumin shi daga abubuwan da za su kyata shi  ko bata shi  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya ce:- (Idan ranar da dayan ku ke azumi ne kada ya yi batsa  kada kuma ya yi hayaniya  , idan wani ya zage shi ko ya nemi   fada da shi   to ya ce lallai ni mutum ne mai azumi) Buhari da Muslim ne suka rawaito .
Ya kasance daga cikin koyarwan magabata Allah ya musu rahama  idan sun yi azumi sai su zauna a masallatai sai su ce :- za mu kiyaye azumin mu ba za mu ci naman wani ba Imamu Ahmad Allah ya mi shi rahama ya ce :- ( Ya dace ga mai azumi ya kula da azumin shi  daga harshen shi kar ya yi musu ).
BAYAN HAKA YA KU  MUSULMAI:
Biyayya baya  cika  kuma baya tsayuwa a kan kafan sa  ya zauna da gindin sa face da kauna  wanda za ta yi riko da ma'abocinta zuwa ga ikhlasi ,  da kuma gaskiyan da zai yi nuni da kyakkyawan  bi, kuma  aiki baya kasancewa kusanci sai idan har abin da ya sa a ka yi shi imani ne ba al'ada ba ko son rai  ba kuma neman suna ba ko  don  riya ba ,  har sai ya kasance babban manufan yin shi shi ne neman lada a wurin Allah  da kuma neman yardan sa ,  idan imani da neman lada ya hadu a aiki  , sai karbuwan aikin da kuma gafara ya tabbata.
Ina neman tsarin Allah daga shaidan abin jefewa
(Ku yi gaggawa zuwa ga neman gafara daga Ubangijin ku  da aljanna wanda fadin ta   sammai da kasa an tanade shi ga masu takawa).
HUDUBA TA BIYU
Dukkan yabo sun tabbata ga Allah bisa kyautatawan sa  godiya kuma ta tabbata a gare shi bisa datarwan sa  da baiwan sa , na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya  ina mai girmama sha'anin sa , na shaida Annabin mu Muhammad bawan sa ne kuma Manzon sa ne tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  da iyalan sa da sahabban sa da aminci tabbatacce mai kari .
YA KU MUSULMAI
Duniya za ta kare da farin cikinta da  bakin cikin ta  shekaru kuma su kare da tsawon su da kuma gajartan su , kowa ya hadu da Ubangijin shi  to anan ne fa dukiya ba zai yi amfani ba ko da  sai wanda ya zo wa Allah da zuciya  lafiyayye , to ku fiskanci watan ku da tuba na gaskiya , ku kulla azama  bisa ribatan shi da raya lokutan shi da da'a  rayuwan duniya fa ba wani abu ba ne sai wani 'yan numfasawa ne kididdigaggu da kuma ajali iyakantacce  to ku ribaci lokuta mafi daukaka , kuma hasararre shi ne wanda ya riski watan azumi ba a gafarta mishi ba .
 Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :-( Hancin shi ya dumbuli kasa, hancin shi ya dumbuli kasa , mutum da ya riski ramadan har ya fita ba a gafarta mishi ba)  Tirmizi ne ya rawaito
(Duk wanda bai bar fadin  zur ba da  aiki da shi ba , to Allah baya bukatan   ya bar abin cin sa da abin  shan sa ) buhari da muslim ne suka rawaito
Mafi girman Abin da ke gyara  zuciya ambaton Allah, da lazimtar kur'ani mai girma, da tsayuwan dare , da zama da salihai.
Sannan ku sani hakika Allah ya umarce ku da salati da aminci ga Annabin shi.


الجمعة، 19 أبريل 2019

watan sha'aban shiri ne don ramadan


Tarjamar Hudubar Masllacin Annabi Na shaikh Abdullah bin Abdurrahman Albuaijan 14-8-1440AH/19/4/2019AD

Hudubar farko
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya halicci sammai da kasa, ya sanya duhu da haske, mai sauya ranaku da watanni, mai karar da shekaru da zamuna.
Ina gode masa ga dukkan al'amura,muddin iskar gabas da ta yamma na kadawa.
Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, bisa gaskiya da yakini. Ina adana ta ga Allah  ranar da rai bai mallaki wani abu ba ga wani rai, kuma al'amari a wannan rana na Allah ne.
Kuma na shaida Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne, ya isar da sako ya sauke.amana, ya yi jahadi a tafarkin Allah har yakini ya zo mishi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabban shi baki daya.
Bayan haka !Lalle Alkur'ani shine zance da magana mafi kyau,Addini a gurin Allah shine musulunci,Mafi alherin shiriya shine koyarwar Annabinmu Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,(Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku ku tsoraci wata rana da mahaifi ba zai fanshi danSa ba, ko shi da ya fanshi mahaifinSa da wani abu, lalle alkawarin Allah gaskiya ne kada rayuwar duniya ta rude ku, kada wani mai rudi game da Allah ya rude ku.)
     Ya Ku jama'ar musulmi!
Lalle Allah ya sanya lokuta tamkar wata ma'adana ce ga aiki, (To duk wanda ya yi wani aiki da ya kai kwayar zarra na alheri zai gan shi. To duk wanda ya yi wani aiki da ya kai kwayar zarra na sharri zai gan shi)
Wanda ya yi hasara shi ne wanda ya hasarar da lokuta mafi alheri, mahrumi shine wanda aka hana shi ribatar lokutan da'a, hakika Allah ya sanya zamani ya zama hanya ne ga muminai zuwa ga biyayya ga Ubangijinsu, hasara ce ga wasu mutane da zai zama gafala ne ga kawunan su, to ku raya kawunanku,ta hanyar yin biyayya ga Allah, domin zukata na rayuwa ne da ambaton Allah (Abin da ku ka gabatar na alheri don kawunanku zaku same shi a gurin Allah).
Ya ku bayin Allah!
Lalle zamani na da fifiko kan sashi bisa ranaku ko watanni ko sa'oi, mafi alherin abin da mutum zai raya shekarunsa da shi ya raya lokacinsa sune ayyuka masu falala da abin da zai kusanto da kai ga ubangiji, da aikata ayyukan alheri da da'a, Allah Madaukakin sarki ya ce : (kuma shine wanda ya sanya dare da yini akan mayewa ga wanda ya ke son ya yi tunani ko kuwa ya yi nufin ya gode,)
Ku saurara! Lalle kuna cikin wata mai girma wanda da yawa daga cikin mutane na gafala daga shi tir da gafala kason wadanda aka hana alheri,kayan hajan lalatatu,
Ku saurara! Lalle kuna cikin wata mai girma da ake daga ayyuka a cikinsa zuwa ga Ubangijin talikai, to ku cike karshensa da tuba, da ayyuka na kwarai,ko Allah zai bamu kyakkyawan karshe,
Ku saurara! Lalle kuna cikin wata mai girma da manzon Allah ke kokarin yin azumi a cikin shi.
An karbo daga Usama dan Zaid yace da Manzon Allah tsira amincin Allah su tabbata a gare shi, ban ga kana yawaita azumi a wani wata ba kamar yadda naga ka ke yawaita wa a wannan watan na sha'abana ba, sai yace :( Ai wannan wata ne da mutane ke gafala daga shi yana tsakanin rajab da ramadan kuma wata ne da ake daga ayyuka zuwa ga Ubangijin talikai to sai na so a daga ayyuka na ina mai azumi.
An karbo daga Aisha Allah kara yarda agare ta tace : Manzon Allah ya kasance yana azumi har muce ba zai sha ba, wani sa'i kuma yana sha har muce ba zai yi azumi ba,ban taba ganin manzon Allah ya cika wani wata  yana azumi ba sai ramadan ba watan da naga yana yawaita azumi acikin shi kamar  sha'aban,)Muslim ne ya rawaito
An karbo daga gare ta ta ce: ya kasance mafi soyuwan watanni a gurin manzon Allah da ya azumce shi shine sha'aban) Abu Dawuda ne ya rawaito shi a sunan nashi kuma Albani ya inganta shi.
Ya Ku jama'ar musulmi!
Lalle a daren  tsakiyan sha'aban Allah na da gafara da take game muminai amma ana haramtawa masu gaba da kiyayya da kullin juna da kafurai, An karbo daga Abu Musa Al'ash'ari Allah ya kara yarda a gare shi, yace :Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yace: (Lalle Allah na tsinkaya a tsakiyar daren sha'aban sai ya gafartawa dukkan halittun shi banda mushriki ko mai gaba da wani,)Ibnu Majah ne ya rawaito da waninsa,Ibnu Hibban da Albani sun inganta shi    
 Ku yafe ku yi rangwame  ku dauke kai ku tausayawa juna, ku yi afuwa, ku sada zumunci, kar ku yi hasada, kar ku yi munajasha, kar ku yi kiyayya kar ku juyawa juna baya, ku zama bayin Allah  'yan uwan juna.
 An karbo daga Abu huraira Allah ya kara yarda a gare shi, yace :Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yace: (Lalle ana bude kofofin Aljanna ranar litini da ranar Alhamis, sai a gafartawa dukkan bawan da bai hada Allah da wani face mutumin da akwai kiyayya da dan'uwan shi, sai ace : ku dakanci wadannan biyun har sai sun yi sulhu! ku dakanci wadannan biyun har sai sun yi sulhu! ku dakanci wadannan biyun har sai sun yi sulhu!) Muslim ne ya rawaito.
Ya ku bayin Allah!
Sha'aban sha gaban daya daga cikin rukunnen musulunci ne, shine Azumin watan ramadan da aka saukar da Alkur'ani a cikinsa.
To shi fage ne na sabo da koyo, da kimtsawa da shiryawa, da shigowan watan imani don fiskantar watan ramadan,
Sha'aban da ramadan kamar sunnoni ne na ratibi  ga sallolin farillah. Shi kamar wani gwaji ne don sabo da watan ramadan don rage wahalansa da nauyin sa da dandana zakin azumi da dadinsa sai mutum ya shiga azumin ramadana da kuzarinsa da karsashinsa.
 Ya Ku jama'ar musulmi!
Duk wanda akwai biyan azumin watan ramadana da ya gabata a kansa to ya gaggauta azumtarsa kafin shigowan watan ramadan, don jinkiri game da haka zai iya zama sababi daga cikin sabuba na sakaci,
An karbo daga Aisha Allah kara yarda a gare ta tace : Azumi na kasancewa a kai na ba na samun daman biyansa har sai sha'aban sabo da matsayin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,)
To ku gaggauta ayyukan alheri –Allah ya muku rahama- kafin ajali ya zo, (ku gaggauta  zuwa ga gafara daga Ubangijinku, da Aljanna wanda fadinta ya kai sammai da kasa an tanade shi ga masu takawa.)

 Huduba ta biyu.
Dukkan yabo ya tabbata ga Allah bisa kyautatawarsa godiya ta tabbata a gare shi bisa datarwarsa  da baiwarsa, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya, ina mai girmama shaninsa,na shaida Annabi Muhammad bawansa ne kuma Manzon sa ne, mai kira zuwa ga neman yardarsa, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabbansa da aminci tabbatacce mai yawa.
Ya ku musulmai!
Lalle Allah madaukakin sarki, ya farlanta azumin watan ramadan a wannan wata, wato ina nufin  sha'aban  a shekara ta uku bayan hijira: Manzon Allah ya yi azumi
Ramadan sau tara, sannan ya koma ga Ubangijinsa.
 Allah madaukakin sarki yace; (Ya ku wadanda suka yi imani An wajabta muku azumi kamar yadda aka wajabta shi ga wadanda suka gabace ku ko zaku ji tsoron Alla)
. Ranaku ne kididdigaggu to duk wanda ya ke maralafiya a cikinku ko yana matafiyi to gwargwadon abin da ya sha na daga kwanaki a wadansu kwanaki yana kansa. Fidiya yana kan wadanda ke da ikon yin azumi tare da wahala ita ce abincin miskinai, duk wanda ya yi tadauwa'i na alheri to ya fi alheri a gare shi, ku yi azumi shi ya fi amfani a gare ku, in kun kasance kun san hakan yafi ( watan ramadan shine wanda aka sauke Alkur'ani a cikinsa mai shiryar da mutane daga bata, ayoyi na shiriya mabayyana da rarrabewa tsakanin karya da gaskiya. Duka wanda ya ga wata daga cikin ku to ya azumce shi, wanda ya kasance mara lafiya ko a kan tafiya to gwargwadon abin da ya sha na kansa na wasu kwanaki, Allah na nufin sauki gare ku bai nufin tsanani gare ku, sabo da ku cika adadin kuma ku girmama Allah bisa shiryarwar da ya muku kuma don ku gode masa bisa wannan ni'ima,)
An karbo daga Abdullahi dan umar Allah ya kara yarda a gare shi, yace :Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yace: (Lalle An gina musulunci akan  abubuwa biyar :Bisa a bautawa Allah a kafurcewa waninsa, ya tsaida salla ya bada zakka da hajji dakin Allah da azumin ramadan )Muslim ne ya rawaito.
An karbo daga Abu huraira Allah ya kara yarda a gare shi, yace :Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yace: (wanda ya yi azumin ramadana yana mai imani da neman lada zaa gafarta masa abin da ya gabata na daga zunubansa kuma wanda ya yi tsayuwan dare na ramadan bisa imani da neman lada to zaa gafarta mishi dukkan abin da ya gabata na daga zunubansa) Bukhari ne ya rawaito
 Ya ku bayin Allah!
Ba abin da ya rage a wannan wata sai ranaku kididdigaggu, to ya dace ga musulmai da su shirya wa wannan wata,da su kimtsa masa, kuma su yi gaggawa  su yi tsere da rigegeniya bisa biyayya ga Allah . to sam barka ga wanda ya riski ramadan,barka da duk wanda aka datar da shi zuwa ga alheri da ayyukan kwarai, ya mai neman alheri ka fiskanto ya mai neman sharri ka gajarta,
To ku nuna wa Allah alheri daga kawunanku, don matsiyaci shine wanda aka haramta mishi biyayya  ga ubangijinsa, kuma lokutan alheri suka tsere mishi bai fadaku ba. Ya yiwa kansa barna har mutuwa ta shammace shi bai tuba daga zunubansa ba.  


   


الخميس، 4 أبريل 2019

Ni'imar Aminci da zaman lafiya



Hudubar Juma'a na Masallacin Annabi na shaikh Abdullah Dan Abdurrahman Al-Buaijan 15-7-1440 AH.

HUDUBAR FARKO :
  Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Madaukakin sarki,  muna gode mishi kuma muna neman taimakonsa ,  kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu , da munanan ayyukanmu , duk wanda Allah ya shiryar da shi babu mai batar da shi , duk wan da ya batar kuma babu mai shiryar da shi , na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bai da abokin tarayya,
Wanzuwa da kyakkyawan yabo nasa ne, Kaddartawa da hukuntawa na hanunsa, shi ke gudanar da al'amura daga kasa zuwa sama, yana aikata abin da ya so, ba za ku samu damar ku so abu ba sai idan Allah ya nufa.
 kuma na shaida Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne, ya isar da sako ya bada amana, yayi nasiha ga al'uma, ya yi jihadi a tafarkin Allah cancancin jihadi har yakini ya zo masa (Mutuwa) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa  da sahabbansa baki daya.
Bayan haka :
Lalle mafi alherin zance shine maganar Allah,  kuma mafi alherin shiryarwa shine shiryarwar Annabi Muhammad, kuma mafi sharrin al'amura sune fararrunta, kuma dukkan bidiah bata ne kuma dukkan bata na wuta,
Ya ku bayin Allah ina muku wasiyya da ni kai na da ku ji tsoron Allah, shine wasiyar Allah ga mutanen farko da na karshe, Allah Madaukakin sarki ya ce :(, haƙĩƙa, Mun yi wasiyya ga waɗanda aka bai wa Littãfi a gabãninku, da kũ, cewa ku bi Allah da taƙawa,) 
Allah Madaukakin sarki ya ce :
  ( Ya ku mutãne! Ku bi Ubangijinku da taƙawa Wanda Ya halitta ku daga rai guda, kuma Ya halitta, daga gare shi, matarsa, kuma Ya watsa daga gare su maza mãsu yawa da mãtã. Kuma ku bi Allah da taƙawa Wanda kuke rõƙon jũna da (sũnan), shi, da kuma zumunta . Lalle ne Allah Ya kasance, a kanku, Mai tsaro ne). 
Ya ku jama'ar musulmi!
Hakika Allah ya yalwata mana ni'imomi da ba zasu kididdigu ba,kuma ya bude mana kofofin  kyautarsa gare mu, kyautar da ba za ta kirgu ba, ya girmama mu da aminci da yalwa,da kwanciyar hankali da wadata, ya yi nesa da mu daga fitintinu da bala'i da musibu na tsautsayi da hasara, da falalar Allah tare da rikon mu da akidarmu da kokarin jagororinmu da malamanmu, Allah madaukakin sarki ya ce : ( Ku tuna a lõkacin da kuke kaɗan, waɗanda ake raunanarwã a cikin ƙasa kunã tsõron mutãne su cafe ku, sai Ya tattara ku (a wurin natsuwa, Maɗina), kuma Ya ƙarfafã ku da taimakonSa kuma Ya azurtã ku daga abũbuwa mãsu dãɗi; Tsammãninku, kunã gõdewa).
Zaman lafiya na daya daga cikin abubuwan da ke mikar da rayuwan mutum, da shi ake samun kwanciyar hankali da natsuwa,
Zaman lafiya na daga cikin hadafin da kowace al'uma ke nema.kuma ta yi amfani da duk wata hanya ko karfi da take da sh,
Zaman lafiya ni'ima ce da ba wanda ya san kimanta da girman muhimmancinta face wanda ya konu da wutan rashinta,
  Zaman lafiya ni'ima ce da rayuwa bai dadi in babu ita,haka ba natsuwa da tabbatuwa guri guda in an rasa ta, Manzo Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(Duk wanda ya wayi gari cikin aminci a gidansa da lafiya a jikinsa, yana da abincin wuninsa to tamkar an tattara masa duniya ne)
Lalle amincin rai da mutunci da dukiya na daga cikin  mafi girman ni'imomi,duk dan adam na bukatarsa, a dukkan zamani da wuri,don ya samu hutu da natsuwa,
Amma idan wutan fitina ta kunnu al'amura suka rikirkice, ya tsoracewa rai da mutunci da dukiya, kuma mutane suka farga daga tashin hankali na bala'i idanuwa suka karkace, zukata suka isa makogoro sabo da tsoro to a nan ne mutum zai yi nadama a lokacin da nadama ba zata yi amfani ba, sai ya yi da na sani game da sakaci da yayi game da aminci da ni'imomi.
Ku yi dubi da idanuwa  ga wasu al'umu da garuruwa, da sun kasance cikin alheri da nitsuwa, yayin da wutar fitina ta kunnu a cikinsu kasa ta yi musu kunci yanayi ya sauya ba daya daga cikinsu da ya samu kwanciyar hankali, to lalle cikin wannan akwai abin lura da waazi ga duk wani wanda akwai kwayar zarra na imani a zuciyarsa.
Hakika alkur'ani ya yi bayani daki daki kuma ya buga misalai mafi ban   kaye:(kuma Allah ya buga misalin wata alkarya ta kasance tana cikin aminci da natsuwa, arzikinta na zuwa mata da yalwa daga ko ina sai ta butulcewa ni'imomin Allah sai ya dandana musu azbar yunwa da tsoro sabo da abin da suka kasance suna aikatawa)
Ku dubi yanda Allah ya ni'imta wasu mutane ya kwarara musu ruwan ni'ima daga taskarsa amma suka juya baya sai bala'i ya sauka a gare su
(Lalle hakika akwai aya ga Saba'awa a cikin mazauninsu: gonakin lambu biyu, dama da hagu, "Ku ci daga arzikin Ubangijinku, kuma ku yi godiya gare shi. Gari mai dadin zama, da Ubangiji Mai gafara" sai suka bijire, sabo da haka muka saki malalin Arimi (Dam) a kan su, kuma muka musanya musu gonakinsu biyu da wadansu gonaki biyu masu 'ya'yan ita ce kadan: talakiya da goruba da wani abu na magarya kadan, wancan, da shi muka yi musu sakamako sabo da kafurcinsu.kuma lallai ba mu yi wa kowa irin wannan sakamako face kafurai. . Kuma Muka sanya, a tsakaninsu da tsakãnin  garũruwan da Muka Sanya albarka a cikinsu, waɗansu garũruwa mãsuganin jũna kuma Muka ƙaddara tafiya a cikinsu, "Ku yi tafiya a cikinsu, darũruwa da rãnaiku, kunã amintattu."  Sai suka ce: "Ya Ubangijinmu! Ka nĩsantar da tsakãnin tafiyõyinmu," kuma suka zãlunci kansu, sabõda haka Muka sanya su lãbãran hĩra kuma Muka kekkħce su kõwace, irin kekkħcewa. Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga dukan mai yawan haƙuri, mai yawan gõdiya). 

  .  Ya Ku Jama'ar musulmai!
Rudani da hayaniya ba su sa a cinma manufa sai dai fitintinu da bala'i, ba abin da zasu haifar face  tashin- tashina da rikici da hasara, mun gani kuru kuru abin da ya faru da wasu al'umu a da yawa daga cikin wasu garuruwa a sakamakon hakan.rayuka da dama da basu ci ba basu sha ba aka sarayar da su,!Dukiya adananna da yawa an lalata ta,aka keta mutuncin masu mutunci, jama'a da dama sun gudu, dangi da iyalai an tarwatsa su,wasu yara an maida su marayu,an rusa gidaje.
Lalle tada fitina  makauniyar kira ce da abokan gaba suka shirya ta, wawaye da maha'inta kuma suke tallata ta, mashirmata kuma suke biye mata.
Abin da yake wajibinmu shi ne mu yake ta, mu zama tsintsiya madaurinki daya a gaban duk wanda ke son yayi batanci gare mu ko raba kanmu,ko ya ke barazana ga zaman lafiyarmu,ko ya yi tawaye ga jagororinmu da shuwagabanninmu.
To ku yi riko da addininku, ku dunkule ku hade don fiskantan abokan gabanku, ku tsayu a kan tafarkinku.
Ku sani lalle Allah ya wajabta muku biyayya ga jagororinku, Allah Madaukakin sarki yace : (ya ku wadanda suka yi imani ku yi da'a ga Allah kuma ku yi da'a ga Manzon Allah, da ma'abota jagoranci daga cikinku),
To biyayya ga jagororinmu na daga cikin addininmu wanda shine kariya ga al'amarinmu, akwai kuma gyara ga duniyarmu da muke rayuwa a cikinta.
An karbo daga Irbad dan sariya Allah ya kara yarda a gare shi ya ce, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya mana sallar asuba sai ya juyo ya mana wani wazi mai ratsa jiki wanda zukata sun tsorata, idanuwa sun zubar da hawaye, sai muka ce ya Manzon Allah tamkar wannan wazi ne na ban kwana, to a mana wasiya, sai yace :(Ina muku wasiya da ku ji tsoron Allah ku ji ku bi ko da kuwa an dora muku jagorancin bawa ne dan habasha,to duk wanda ya rayu cikinku zai ga sabani mai yawa,to ku yi riko da sunna ta da sunnar kalifofi na shiryayyu wadanda aka shiryar da su,ku riko ta da hakoran cin tuwonku,na hore ku da ku nesaci fararrun abubuwa a addini don dukkan bidia bata ce)Hakim ne ya rawaito shi a Mustadrak.
Ku roki Allah tabbatuwa a kan addininku,ku kiyayi fitintinu, ku zama kuna tare da jagororinku,kuna komawa zuwa ga malamanku, ku hada kai don fiskantar makiyanku da duk wanda ke son ku samu matsala a zaman lafiyarku da hadin kanku,
Ina neman tsarin Allah daga sharrin shaidan abin jefewa. (Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi ɗã'a ga Allah, kuma ku yi ɗã'a ga ManzonSa, da ma'abũta al'amari daga cikinku.(3) Idan kun yi jãyayya a cikin wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da ManzonSa idan kun kasance kunã ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Wannan ne mafi alheri, kuma mafi kyau ga fassara).
Allah sa mini Albarka da ni da ku cikin Alkur'ani mai gairma, ya amfane ni da ku da abin da ke ciki na ayoyi da ambato mai hikima,
Ina fadin abin da kuke ji, ina neman gafarar Allah ni da ku da sauran musulmai daga dukkan zunubai, to ku nemi gafararSa don shi mai gafara ne Mai jinkai.

Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah da ya sako ni'imomi, ya tunkude azaba, ya sanya mu al'uma mafi alheri, ya cusa imani a cikin zukatanmu, ya sanya aminci da zaman lafiya a kasarmu, to godiya ta tabbata ga Allah a farko da karshe, hukunci nashi ne kuma gare shi zaku koma.
Ya ku bayin Allah!
Allah ya halicci mutane a mataki mataki, ya sanya fifiko a tsakaninsu cikin kudura da baiwa, ya sanya malamai magada Annabawa, ya daga matsayin su da darajojin su, wannan falala ne na Allah ya na bawa wanda ya so, ya shiryar da mutane ga komawa gare su da koyi da su,To su ne masu rikon ilimi da bada kariya ga  addini, da kiyaye mutunci, ya tabbata daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : (Adilai ne na kowane mamaya  Zasu dauki wannanan ilimi, zasu kore jirkitawan masu ketare iyaka, da cogen mabarnata, da tawilin jahilai) .
To idan fitina ta taso, bidi'o'i suka cakuda da sunna, wawayen mutane suka tsoma baki cikin al'amarin al'uma, gaskiya ta jirkita da bata, malami da jahili suka jirkice, abubuwa suka rincabe,to ku riki akidarku da gaske, ku aminta da malamanku da jagororinku, ku ji tsoron Allah akan kawunan ku da al'umarku, kar ku bi ko wani mai ihu, ku banbance tsakanin jerin gwanon kalmomi na gaba da na baya.
(Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun haɗu da wata ƙungiyar yãƙi, to, ku tabbata, kuma ku ambaci(2) Allah da yawa, tsammãninku kunã cin nasara.   . Kuma ku yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, kuma kada ku yi jãyayya har ku raunana kuma karfinku ya tafi, kuma ku yi haƙuri. Lalle ne Allah Yanã tãre da mãsu haƙuri.)

 Ya ku matasa...
Ku ne ruhin Al'uma kuma mahanganta , da ku ne zata rayu ta yi kyau, al'uma ta taso a birni da kauye,daku  ake karya logon batattu da mabarnata,
To ku kiyaye dukkan kiyayewa daga fitintinu, da kuma kai komo a cikinta da mara mata baya, to addinin ku na da wajibi da ya hau kanku to ku bada shi, magabatanku na da hakki a kanku to ku cika, kuma kasarku na da wajibi da ya doru a kanku to ku kiyaye shi, ku ji tsoron Allah ku sani zaku hadu da shi.
(Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku karɓa wa Allah, kuma ku karɓa wa Manzo, idan Ya kirãye ku zuwa ga abin da Yake rãyar da ku; Kuma ku sani cewa Allah Yanã shãmakacewa a tsakãnin mutum da zũciyarsa, kuma lalle ne Shĩ, a zuwa gare Shi ake tãra ku.
   Kuma ku ji tsõron fitina wadda bã ta sãmun waɗanda suka yi zãlunci daga gare ku keɓe, kuma ku sani, lalle ne Allah Mai tsananin uƙũba ne).
Bayan haka yaku jama'ar musulmai
 Musulmai gangan jiki ne guda kuma gini ne guda, ketare iyaka ga dayan su to ketare iyaka ne ga dukkaninsu, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yace :Misalin mumini cikin kaunarsu da son junansu da tausayawa juna tamkar jiki ne idan wani gaba na ciwo sai sauran gabbai su amsa da rashin barci da zazzabi). Muslim ne ya rawaito
   Lallai musibarku da musibar mu na ga abin da ya faru  na yaudara da taaddancin da a ka nufi 'yan uwanmu musulmai da zubar da jinin masallata da tsoratar da wadanda ke cikin aminci, da keta alfarmar dakin Allah,
Kuma ba su tuhumce su ba, fãce kawai domin sun yi ĩmãni da Allah, lalle musiba ce mai girma,babban abin firgitarwa ne, muna neman ladanta a gurin Allah, kuma abin da ke gun Allah ya fi alheri kuma ya fi wanzuwa.
To daga Allah muke kuma gare shi za mu koma, Allah kyautata ta'aziyyar 'yan uwan mu, ya girmama musibarsu, Allah ka yi gaggawan bawa marasa lafiyan cikinsu lafiya, Allah gafartawa matattu ya daga darajojinsu cikin madaukaka,
Ya Allah ka daukaka musulunci da musulmai  


الجمعة، 1 مارس 2019

BIYAN BASHI A MUSULUNCI


Hudubar Masallacin Annabi na shaikh Husain Al- Asshaikh 24-6-1440
Hudubar farko
Kiyaye hakkokin jama'a na daga cikin abubuwa na tushe kuma na kat da shariar musulunci ta karfafa, sawaun ta bangaren bata kariya ko kiyaye ta, na daga cikin abin da wasu mutane ke sakaci da shi akwai baiwa  masu hakki hakkokinsu musamman bashi, wanda ke kan mutum na rance,na farashin wani abu da ya saya ko rance da ya ranta, ko ladan wani dan kodago ya yi mishi aikin kodago,da makamantarsu.
To abin da ya ke wajibi ga musulmi ya yi kokarin sauke nauyin da ke kansa, ya biya abin da ke kansa na hakkin 'yan uwansa Allah Madaukakin sarki ya ce :(kada ku ci dukiyarku a tsakaninku ta hanyar barna).
Lalle abin da ya ke farilla akan kowane musulmi na dole ya bada gabadayan hakkokin halittu, cikakke ba tare da ya tawaye ba, na daga cikin bayyanannen laifi da zunubi mai girma akwai sulalewa daga biyan basuka ko gujewa masu hakkin, da kin biyan bashin da jinkirta shi sai gaba mai zuwa tare da halin biya, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(zalunci ne mawadaci ya jinkirta biyan bashi).Muslim ne ya rawaito.
Almadalu shine jinkirta biyan hakki da ya dace a biya tare da halin biya da iko, amma ya ki biya akan lokacin to ya aikata haramun ya kuma fada cikin  zalunci  ga ma'abota hakki na daga cikin halittu, karshen zalunci hasara ne kuma abin kunya ne duniya da lahira.
Ya 'yan Uwa Musulmi!
Bashi al'amarinsa babba ne, shaninsa mai girma ne a musulunci, sabo da haka ne Abu Huraira Allah kara yarda a gare shi yace zaa zo ga Annabi da mammaci wanda akwai bashi a kansa  sai ya ce :(Shin ya bar abin da zaa biya bashinsa da shi? In an bada bayanin cewa  ya bar abin biya sai ya mishi sallah,in ba haka ba sai yace : ku yi sallah ga sahibinku,) Hadisin Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
    To ya kai wanda bai damuwa da biyan bashi, bai kulawada hakkin mai hakki, ka ji tsoron Allah Ubangijinka !
Muslim ya rawaito a sahih na shi daga Abdullahi dan Amr Allah kara yarda a gare shi ya ce : (Ana gafartawa dukkan shahidi sai wanda akwai bashi a kansa)
Haka kuma a gun nasa cewa wani mutum ya zo ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi sai ya ce:ya Manzon Allah, shin yanzu in an kashe ni a tafarkin Allah zaa gafarta min dukkan zunubai na? ya ce :E a halin kana mai hakuri kana neman lada kana mai fiskanta ba mai juya baya ba, ban da bashi, dazu Jibrilu ya fada min haka.)
To ya kai Musulmi ka sauke hakkin wani da ke kanka, ka kiyaye jinkirta biyan bashin dukiyan mutane a halin kana da kuduran biyanta, to ka gaggauta kafin wucewan lokaci,sanda zai zama ba wani abu na hakkokin halittu sai daukan fansa da kyawawa ko munana, Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata agare shi sai ya ce:( Duk wanda ya ke da wani hakki akansa na zaluncin dan uwansa game da mutuncinsa ko wani abu to ya warware daga gare shi a yau kafin ya zama dinari ko dirhami, in ya lasance yana da ayyukan kwarai sai a dauka daga gare shi gwargwadon abin da ya zalunce shi, to idan bai da kyawawa sai a dauka daga laifukan sahibin nasa sai a dora mishi).
Nasa'i ya rawaito daga Muhammad dan Muhsin Allah kara yarda a gare shi ya ce"(Mun kasance zaune a gurin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai ya daga kansa zuwa sama, sai ya sanya tafin hanunsa akan goshinsa, sannan ya ce : (Tsarki ya tabbata ga Allah! Me aka saukar na tsanani? Sai sahabbai suka yi shuru suka firgita da gari ya waye sai na tambaye shi ya Manzon Allah  wani tsanani ne wanda ya sauka? Sai ya ce :  Na rantse da wanda  rai na ya ke hanun shi , da ace wani mutum   za a kashe shi a tafarkin Allah  sannan a raya shi sannan a kashe shi sannan a raya shi , sannan  a kashe shi alhali akwai bashi akan shi to da ba zai shiga Aljanna ba har sai anbiya mishi wannan bashin .)
YA DAN UWANA MUSULMI:
Ka kasance cikin himma na gaskiya wurin sauke nauyin halittu  kuma ka halarto da kyakkyawar niyya  a lokacin biya da cika alkawari  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce :- (Duk wanda ya karbi dukiyan mutane  da nufin zai biya to Allah zai biya mishi ) buhari ne ya rawaito
Kai kuma mai bin bashi ka kasance mai rangwame mai saukin hali mai kyauta , duk wanda ya kasance yana cikin matsanancin hali ka yi mishi rangwame  zuwa sanda zai samu , sabo da fadin Allah madaukakin sarki :-( Idan  ya kasance  matalauci ne  to a jinkirta mishi zuwa  lokacin da Allah zai hore  mishi )
Daga cikin ayuka masu falala  akwai  ;  yin hakuri ga wanda bai samu ba da yafewa wanda ya rasa ,  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce:(Wani attajiri ya kasance yana bawa mutane bashi  idan ya ga  wanda ya gagara biya sai ya ce wa yaran shi ku yafe mishi ko muma Allah zai yafe mana  to kuma sai Allah ya yafe mishi ).
A ruwayar musulim Allah madaukakin sarki ya ce :-(Mu muka fi dacewa da hakan bisa gare shi   to a yafe mishi ). Ya zo a hadisi kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce:(Duk wanda ya saukake wa wanda ke mawuyacin hali  to Allah zai saukake mishi a duniya da lahira  ) Buhari da muslim ne suka rawaito.
  YA KAI   DAN UWA MUSULMI:
To ka ribaci    ladannan mai girma da falala mai auki ta hanyar tausayawa wanda ya rasa , kana mai  jinkirtawa  zuwa ga wani ajali   ko kuma ta hanyar yin rangwami da kubuta daga hakki  wannan shi ne lada mafi girma da sakayya mafi yalwa .
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:-( duk wanda  ke son Allah ya tsiratar da shi daga bakin ciki na ranar alkiyama  to ya yayewa matalauci     ) Muslim ne ya rawaito
HUDUBA TA BIYU
Yana daga cikin abin da musulunci ya wajabta akwai cika ladan mai kodago , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:-(ku bawa mai aikin kodago ladan sa kafin zufan sa ya bushe)  wasu malamai masu tantancewa sun ce hadisi ne  mai kyau .
To ya haramta a tawaye hakkin sa ko a rika cewa sai nan gaba , kan haka ne ma  Allah  madaukakin sarki  ya ce:-(mutum uku ni ne zanyi musu da su ranar alkiyama  sai ya ambata daga cikin su:- da mutumin da ya dauki hayan dan kodago,  ya nemi ya cikata mishi  ya nemi hakki daga gunshi bai bashi ladan shi ba)  Buhari ne ya rawaito


       

الجمعة، 8 فبراير 2019

RYUWAR DUNIYA A MAHANGAN MUSULUNCI


HUDUBAR MASALLACIN ANNABI NA SHAIKH ABDULLAH BIN ABDURRAHMAN         ALBUAIJAN 3/6/1440AH
Lalle Dukkan Yabo da godiya sun tabbata ga Allah muna gode mishi kuma muna neman taimakonsa kuma muna neman gafararsa , muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunan mu da munanan ayyukanmu, duk wanda Allah ya shiryar da shi babu mai batar da shi, kuma wanda Allah ya batar da shi babu mai shiryar da shi, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, shi ke da wanzuwa da kyakkyawan yabo, kaddartawa da hukuntawa na hanunsa, yana gudanar da al'amura daga sama zuwa kasa, yana aikata abin da ya so, ba za ku so ba sai abin da Allah ya halitta ya yarda.
 kuma na shaida Annabi Muhammad bawansa ne kuma manzonsa ne, ya isar da sako, ya sauke amana ya yi nasiha ga al'uma, ya yi jahadi a tafarkin Allah cancancin jahadi har mutuwa ta zo mishi, tsira da amincin Allah su tabbata agare shi da iyalansa da sahabbansa baki daya, bayan haka:
To lalle mafi alherin zance shine maganar Allah, kuma mafi kyan shiryarwa ita ce shiryarwar manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata agare shi, kuma mafi sharrin al'amura sune fararrun ta, kuma dukkan bidi'a bata ce kuma dukkan bata na wuta,
Ya ku bayin Allah ku ji tsoron Allah cikin abin da ya yi umarni, ku hanu daga abin da ya hana ya tsawatar,kuna dukkan karami da babba abin rubutawa ne,
(ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah cancancin tsoronsa kada ku mutu face kuna musulmai)

Ya ku jama'ar musulmai!
Allah ya kaddara abubuwan kaddarawa ya sanya musu lokaci, ya kuma kasa musu arziki, ya rubuta ga kowanne rabonsa na rabauta ko tsiyace wa, da rabon shi na ni'ima da yalwa da kuma tsanani da cuta, to duk wanda ya yarda zi samu yarda wanda ya fusata yana da fushi, dukkan komai da hukuncin Allah ne da kaddararsa.
 Ya ku bayin Allah ! hakika Allah ya rubuta arzikin bani-adam tun sunacikin mahaifa, idan mutum ya cika wata hudu acikin mahaifiyarsa, sai Allah ya turo masa mala'ika da aka wakiltawa kula da mahaifa sai ya busa masa rai da izinin Allah ya rubuta masa ajalinsa da aikinsa da arziki kuma shakiyyi ne ko sa'idi,
An karbo daga Abdullahi dan Mas’ud (R.A) yace manzon Allah (S.A.W) ya bamu labari, shi ne mai gaskiya abin gaskatawa yace: lallai kowanne dayanku ana tara halittarsa a cikin mahaifiyarsa, tsawon kwana arba’in yana maniyyi, sannan , ya canja ya zama gudan jinni kwatankwacin
wannan, sannan ya juya ya zama tsoka kwatankwacin haka sannan, ya juya ya zama tsoka kwatankwacin haka, sai a aiko
mala’ika ya busa masa rai, a umarce shi da rubuta kalmomi guda hudu: A rubuta arzikinsa da ajalinsa da a ayyukansa da kuma dan wuta ne ko aljanna na rantse da wanda babu wani abin bautawa da gaskiya face shi lallai dayanku zai yi aiki irin na ‘yan Aljanna har ya zamanto baa bin da ke tsakaninsa da
Aljanna sai zira’i daya sai rubutun can ya rigaye shi, yayi aiki irin na ‘yan wuta, sai ya shige ta, lallai dayannku zai yi aiki irin na ‘yan wuta har abin da ke tsakaninsa da ita bai wuce zira’i daya ba, sai littafi ya rigaye shi sai yayi aiki irin aikin yan aljanna sai a shige ta) Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Arziki abu ne da an riga an kasa shi, dukkan komai an yi shi ne da hukunci na Ubangiji da ajali sananne,to ku dai ku nemi halal,ku nemi taimakon Allah,wajen neman arziki, ku kuma kyautata zato ga Allah,domin mummunar zato abin zargi ne da bai da amfani, Allah na ga inda bawansa ya  kyautata zato a gare shi, to ya kai bawan Allah ka rika kyakkawan fata,ka yarda da kason da Allah ya diba maka, na hore ka da ka nesaci kwadayi da tsoro da handama, na hore ka da sakaci,   domin hakan wauta ne da almubazzaranci, idan musiba ta same ka kada kace da da ba don kaza ba, sai dai kace Haka Allah ya kaddara, kuma abin da ya so shi ya ke aikatawa.
Ya ku bayin Allah!
Allah shine mai bayarwa shi ne Mai azurtawa, hannayensa biyu a shinfide suke yana ciyarwa yadda ya so, taskokin sa ba su karewa, damarsa a cike take ciyarwa bata rage ta, mai yawan kyauta ne dare da wuni.
"An karbo daga Abu-zarri (رضي الله عنه). Yace, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace cikin abin da ya rawaito daga Ubangijinsa Mai tsarki da daukaka ya ce : Ya ku bayi na ! lalle na haramta zalunci wa kai na kuma na sanya shi haramun a tsakaninku, to kada ku yi zalunci,
Ya ku bayina! dukkaniku batattu ne, sai wanda na shiryar da shi; ku nemi shiryarwata; in shiryar da ku. Ya ku bayina! dukkaninku mayunwata ne sai wanda na ciyar da shi; sai ku nemi ciyarwata; in ciyar da ku. Ya ku bayina! kowanenku tsirara ya ke; babu tufafi sai wanda na tufatar da shi; sai ku nemi tufatarwata, in tufatar da ku. Ya ku bayina ! lallai kuna yin laifi dare da rana, ni kuma ina gafarta zunubai gabadaya; sai ku nemi gafarata; in yi muku gafara  ya ku bayi na ba ku kai abin da zaku cutar da ni ba balle ku iya cutar da ni, haka kuma ba ku kai abin da za ku iya amfanar da ni ba balle ku amfanar da ni, ya ku bayi na da a ce na farkonku da na karshenku da mutanenku da aljaninku zasu kasance da zuciyan mutum guda mafi tsoron Allah a cikinku, to hakan ba zai kara komai a mulki na ba, ya ku bayi na da ace na farkonku da na karshenku da mutanenku da aljaninku zasu kasance da zuciyan mutum guda mafi fajirci a cikinku da hakan ba zai rage komai ba a mulki na, , ya ku bayi na da a ce na farkonku da na karshenku da mutanenku da aljaninku zasu tsaya a kan wata kasa guda suka roke ni na kuma bawa kowa bukatansa da hakan ba zai rage wani abu na daga gare ni ba face kamar abin da allura zai rage in an sa cikin kogi, ya ku bayi na lallai ayyukan ku ne nake kididdige  muku na cika muku, to wanda ya samu alheri ya godewa Allah, wanda ya samu sabanin haka to kar ya zargi kowa sai kansa) " Muslim ya ruwaito shi.
Ya ku bayin Allah !
Lalle Allah ya dauki nauyin azurtawa,sai yace : (Ba wata dabba  a cikin kasa face ga Allah arzikinta ya ke kuma ya san matabbatarta da ma'azarta , duka suna cikin littafi bayyananne)  
Yana azurta jariri a cikin mahaifiyarsa da kifi a cikin ruwa, da macizai a cikin rami, Allah bai taba halittar wasu halittu ba ya sarayar  da su, da bawa zai gujewa arzikinsa da arzikin ya riske shi, (Allah na yalwata arziki ga wanda ya so daga cikin bayinsa kuma yakan kuntata wanda ya so).
Ya ku musulmai!
Allah kan jarrabi mutum da arziki don ya kyautata ya bo ya gode, ya kan kuntata  don jarabawa ba don ya manta ba   ko gazawa, to a nan sai ya lizimci hakuri.
Duk wanda talauci ta sauka gare shi sai ya kai kuka ga wanin Allah to ba zai toshe mishi talaucin sa ba, duk wanda ya nemi kame kai to Allah zai bashi kamewa, wanda ya nemi ya wadatu Allah zai wadata shi, wanda ya nemi ya zama mahakurci Allah zai maishe shi mahakurci,
To hakuri bisa talauci da tsanani da tsadar rayuwa da jarabawa abu ne na wajibi a sharia  kuma al'amari ne na larura na dole, Allah ya zargi ga hakan sai ya ce : (To shi mutum idan Ubangijinsa ya jarrabe shi ya karrama shi ya masa ni'ima sai yace Ubangiji na ya karramani, to amma idan ya jarrabce shi ya ya kuntta mishi arzikinsa sai ya ce Ubangiji na ya wulakanta ni)
Ya ku bayin Allah!
Tsoron Allah shine abu mai riba  mafi alheri ga bawa, shine mafita daga duk wani kunci da sharri, (Duk wanda ya ji tsoron Allah zai sanya mishi mafita kuma ya azurta shi daga ta inda bai zato).
Tsoron Allah shi ne taskar sammai da kasa,abin da ke gurin Allah ba a riskarsa da saba masa, (Kuma da lalle mutanen Alkaryu sun yi imani suka yi takawa da mun bude Albarkoki a kansu daga sama da kasa to amma sai suka karyata sai muka kama su da abin da suka kasance suna aikatawa)
      Allah ya sanya min albarka ni da ku a cikin Alkur'ani mai girma,kuma ya amfane ni da ku da abin da ke cikinsa na ayoyi da ambato mai hikima, ina fadin abin da kuke ji ina neman gafarar Allah mai girma, ga ni da ku daga dukkan zunubai, kuma ku nemi gafarar sa lalle shi Mai gafara ne Mai jinkai.
Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah,wanda ya halicci mutuwa da rayuwa don ya jarrabe ku  wanene ya fi kyan aiki, ya kuma sanya Albakiyatussalihatu ya zama mafi alheri a gurin Ubangijinka a lada da ku kyakkyawan fata, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabinmu Muhammad wanda ya fi tsarkin zance da aiki cikin halittu, da iyalansa da sahabbansa masu mutunci da falala da tabiai da wadanda suka bi su da kyautatawa har zuwa ranar sakayya.
Ya ku bayin Allah !
Aiki mabudi ne na kyakkyawan fata, mafi tsarkin abin nema shine sana'ar hanu, hannu mai mikawa ya fi hannu mai karba, kame kai ya fi alheri bisa roko, wanda ya wadatu daga waninsa ya daukaka kuma ya kare mutuncin kansa, Manzon Allah tsiran da amincincin Allah su tabbata a gare shi yace: Na rantse da wanda rai na ke hanunsa dayanku ya dauki igiyarsa ya je ya yi kirare ya dora a bayansa ya fi alheri a gare shi da ya zo ga mutum ya roke shi, sawa'un ya ba shi ko ya hana shi,) Bukhari ne ya rawaito.
Hakika Annabi Musa amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance yana kiwon dabobi ana biyansa, Annabin Allah Zakariyya ya kasance kafinta ne, Annabin Allah Dauda amincin Allah ya tabbata a gare shi ya kasance yana ci daga aikin hanunsa, Annabinmu Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana kiwon dabbobi na mutanen makka bisa wasu sulalla, ba wani abinci da mutum zai ci da ya fi alheri bisa aikin hanunsa, Aiki daukaka ne zaman banza kuma barna ne, (Shi, (Allah), Yã sanya muku ƙasa hõrarriya, sai ku tafi cikin sãsanninta, kuma ku ci daga arzikinSa, kuma zuwa gare shi ne tãshin yake)
 (Ku tafi a doron kasa ku nema daga falalar Allah)
  Ku dogara gare shi, to  duk wanda ya dogara a gare shi ya isan masa,     (Kuma kada ku yi bakinciki game da abin da ya tsere muku, kuma kada ku yi farinciki bisa abin da ya ba ku)
Ya ku musulmai!
Duniya mai karewa ne kuma mai gushewa ce, lalle gidan lahira ita ce gidan rayuwa, ba rayuwa kamar rayuwar lahira, Duniya jin dadi ne na rudi,mai saurin wucewa, mai saurin sanjawa, ba ta tabbatuwa a hali guda, ta fi tsananin juyawa a kan ranaku da dararraki, idan ta sauka a guri sai ta bata shi, in ta bayyana sai ta bada tsoro,sau da yawa takan sa mutum dariya kuma ta sa shi kuka, ta faranta kuma ta jiyar da ciwo, ta fiskanto ta kuma juya baya, ita ba wata aba ba ce sai farinciki da bakinciki, jin dadi ne na holewa da kuma juyayi, kuma walwala ne da annashwa,da bakinciki da bacin rai,kuma wargi ne da wasa, da kawa da alfahari da  tinkaho da yawa    (Ku sani cewa rãyuwar dũniya wãsã ɗai ce da shagala da ƙawa da alafahri a tsakãninku da gãsar wadãta ta dũkiya da ɗiya, kamar misãlin shũka wadda yabanyarta ta bãyar da sha'awa ga manõma, sa'an nan ta ƙħƙashe, har ka ganta tã zama rawaya sa'an nan ta kõma rauno. Kuma, alãmra akwai azãba mai tsanani da gãfara daga Allah da yarda. Kuma rãyuwar dũniya ba ta zama ba fãce ɗan jin dãɗin rũɗi kawai).
   Mutum bai da wani abu cikinta sai abin da ya gabatar ko ya ci ya karar, ko ya sanya tufafi har ya tsufar ya rididdige, ko ya yi sadaka ya shude, to ka kasance a duniya kamar wani bako ko mai ketare hanya, jin dadin rayuwar duniya dan kadan ne, lahira ta fi alheri ga wanda ya ji tsoron Allah, kuma ita ta fi alheri da wanzuwa, ka guji duniya Allah zai so ka, ka guji abin hanun mutane, sai mutane su so ka.
Bayan haka ya jama'ar musulmai!
To lalle duniya za ta kaura tana mai juya baya,lalle kuma lahira za ta fiskanto, kowacce na da 'ya'ya, to ku kasance daga 'ya'yan lahira, kar ku kasance daga yaran duniya, to lalle yau aiki ne ba hisabi, gobe kuma hisabi ne ba aiki.
To ka gaggauto zuwa ga Aljannar Adni,domin ita ce masaukanka na farko cikinta akwai shemomi,
ya kai mai saida wannan da raha kana mai gaggawa,
    kai ka ce baka sani bane aaha zaka sani.
To in baka sani ba ne to wannan musiba ce.
In ka kasance kana sane to musibar ta fi girma.