الأربعاء، 22 أغسطس 2018

HUDUBAR BABBAN SALLA 1439


Hudubar Idi na Masllacin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sheikh Salah bin Muhammad Al-Budair 10-12-1439
HUDUBAR FARKO
 ( ALLAHU AKBAR  ALLAHU AKBAR      ALLAHU AKBAR   ALLAHU AKBAR  ALLAHU AKBAR  ALLAHU AKBAR ) Allah mai girma Allah mai girma  Allah mai girma  Allah mai girma Allah mai girma Allah mai girma. Ba abin bautawa da gaskiya sai Allah  ( WALLAHU AKBAR  ALLAHU AKBAR WA LILLAHIL HAMDU) kuma Allah mai girma Allah mai girma  dukkan yabo da godiya na shi ne , (ALLAHU AKBAR KABIRAN  WALHAMDULILLAHI KASIRAN WA SUBHANALLAHI BUKRATAN WA ASILA ) Allah mai girma kuma babba dukkan yabo da  godiya masu tarin yawa na shi ne , kuma tsarki ya tabbata ga  Allah safiya da maraice .
       Allah mai girma  safiya da maraice ***  Zuciya mai kauna  kuma mai yarda  na wayan gari da shi
Allah mai girma hasken duhu idan ya yi duhu  *** wata ya bayyana gare mu mai haske mai kaye 
Allah mai girma da safiya idan ***  haske idan ya sulale zuwa ga zukat masu kyau
          Allah shi ne  mafi  girman wanda za a kira kuma shi ne mafi darajan wanda za a yi fata a gare shi  kuma shi ne mafi daukakan wanda ke bada kyauta   Allah mai girma  cikin kauna  da kankan da kai  da girmamawa  da daukaka .
     Allah mai girma Allah mai girma  ba abin bautawa da gaskiya sai Allah   kuma Allah mai girma Allah mai girma dukkan yabo da godiya na shi ne.
     Dukkan yabo da godiya na shi  ne ,  dukkan yabo da godiya na shi ne bana bukatan canza wani da shi ,  godiya wanda zai kai da yardan sa mafi cika  , ina gode mishi  godewa na kololuwa   kuma mafi cika da kamala kuma mafi girma mafi gamewa. 
   Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya ya yalwata mana ni'imomin sa masu yawa  da kuma ladufan sa masu girma ,  na shaida cewa Annabin  mu kuma shugaban mu  Muhammad   bawan sa ne kuma Manzon sa ne  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  da kuma dukkan Annabawa  da dukkan iyalan su da mabiyan su  masu daraja tsira da amincin Allah  abin ribanyawa masu tsarki na dindindin ba tare da yankewa ba  .
        BAYAN HAKA:-
TO YA KU MUSULMAI:-
Ku ji tsoron Ubangijin ku hakika mai tsoron Allah ya rabauta  mabarnaci kuma shakiyyi ya yi hasara .
(Ya ku wadan da suka yi imanin ku ji tsoron Allah cancancin tsoron sa kar ku mutu face kuna  musulmai ).
 YA KU MUSULMAI  :-
Ina tayya ku murna a gare  ku bisa ga wannan rana  mai girma , ina taya ku murna ga wannan rana na idi mai  sa'ida  .
 Ina taya ku murna da wannan ranar Hajji mafi girma.
 ina taya  ku murna da wannan rana na  yanka mai kayatarwa.
Ina taya ku murna da wannan rana na gangami mai girma
Iska ya kada sai ya bada kyauta na shauki mai yawa ga zuciya *** Ya koro zuwa  gare ni  na daga farin cikin abin da ya koro
An karbo  daga Abdullahi dan Kurad Allah ya kara yarda a gare shi daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (LallaiMafi girman ranaku a wurin Allah madaukin sarki  shi ne ranar yanka   sannan kuma sai ranar shanya ). ABU DAUDA NE YA RAWAITO SHI .
 Tsayuwa a daren shi  jifa  da suka  da dawafi  a safiyan shi   to abun mamaki da irin girman wannan rana  abin mamaki kuma da irin taruwan da ake yi a cikin shi .
Allah mai girma Allah mai girma  ba abin bautawa da gaskiya sai Allah , kuma Allah mai girma Allah mai girma  dukkan yabo da godiya na shi ne .
  YA KU MUSULMAI :-
Tun lokacin da aka kafa wannan addinin  aka dasa ginshikanta  musulunci ya daukaka  da darajan shi :- Shugaban hanifai  baba ga Annabawa wanda ya gina ka'aba abin girmamawa Ibrahim Alkhalil tsira da  amincin Allah su tabbata a gare shi  sai ga muminai tawaga –tawaga suna shauki  zuwa ga daki abin girmamawa  , kuma gari mai alfarma  bukatu ba sa yankewa daga gare shi aba a kare bauta a cikin shi  da tunani da dubi .
      Tsarki ya tabbata ga Allah abin bauta   wanda ya shar'anta a gare mu wadannan ibadodi masu girma  kuma ya shiryar da mu zuwa gare su wadannan alamomi na addini  da dalilai ya kawata mu da wadannan manyan alamomi   da tutoci   .
Tsarki ya tabbata gare shi sa'annan kuma tsarki ya tabbata gare shi wanda zai koma zuwa gare shi *** Kafin mu dutsen judiyyi sun yi tasbihi da sandararrun abubuwa 
Allah mai girma Allah mai girma ba abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Allah mai girma Allah mai girma  dukkan yabo da godiya sun tabbata gare shi
  YA KU MUSULMAI :-
Na daga ni'imomi bayyanannu  da  falaloli   na zahiri kuma wannan shi ne mafi girman abin alfahari na zamani  kuma mafi daraja ,  daga cikin alamomin shi  shi ne Allah ya kebance wannan kasa mai albarka  da hidimawa wadan nan garuruwa biyu masu alfarma madaukaka da wuraren ibadodi masu tsarki  da kulawa da ayukan haji da kuma alhazai  sai ya bata daukakanta   , ya damka mata jagorancin ta  ya mika mata jan ragamar su kai madalla da wannan girmamawa na wannan ni'ima da wannan kyauta  abin mamaki da girman wannan kyauta abin mamaki da girman wannan kyauta sannan abin mamaki da girman wannan kyauta  .
    Sarakunan wannan kasa ta sunna da gommnonin ta da  mazajenta  sun yi alwashin ba da kawunan su don hidimawa  aikin hajji da alhazai.
Sai suka jagoranci al'amura na hajji * Allah da musulunci da Addini na godiya gare su.
Cikin mu akwai masu daukaka  addinin Allah da ba shi kariya *  cikin mu akwai masu zare tokobi don taimaka addinin Allah.
Amma shi makiyi idan ya ga ni'ima sai ya yi kus, idan ya ga kuskure sai ya yi murna, idan ya ga wata falala sai ya yi shuru
Yana boye gaba alhali bata boyuwa    *makiyi yana fadin abin da ya gani na abin da ya mishi dadi
Masoyi  yana da wani ido  na bayyane ***game da abin kiyayya  shi kauna na da wasu alamomi     
Yin kiyayya ga wannan kasa mai albarka da kokarin taba amincinta da zaman lafiyanta   shi ne kiyayya ga alkiblan musulmai  da  wuraren su masu tsarki  da hurmomin su da hajjin su da ibadodin su  da kuma gaba ga musulmai   kwatankwacin fadin mai fadi  :-
Kai dinnan ba mai mulki ne kawai don tunkude wanin shi ba sai dai tauhidi ne don  rushe shirka    Allah mai girma Allah mai girma ba abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Allah mai girma Allah mai girma  dukkan yabo da godiya sun tabbata gare shi.
YA KU MUSULMAI:-
 Yana  daga cikin   tushe na ma'abota imani ma'abota hadisi da sunna masu kiyaye  addini da taskace shi da kuma kundin ilimi  da kuma masu daukan shi  girmamawa ne ga littafin Allah da sunna,  littafi shi ne shirin su sunna kuma ita ce hujjar su Manzon Allah shi ne abin koyin su   suna koyar da tauhidi da akida    suna kuma karfafan shari'a kuma suna rusa bidi'a  abin muni  suna kin kungiyanci  abin kaskanci  ba  su da wani abin bi  wanda suke ta'assubanci   sai manzon Allah  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ,    suna neman sanin halayen shi   kuma suna girmama fadin shi  suna kuduri da shi  suna dogaro da shi suna gaskata shi suna karban shi  suna mika wuya gare shi ba sa jayayya da shi  .

 Allah mai girma Allah mai girma ba abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Allah mai girma Allah mai girma  dukkan yabo da godiya sun tabbata gare shi
YA KU MUSULMAI :-
Lallai kuna rayuwa a cikin farfajiya na aminci mai yalwa da arzikin bajinta na jin dadi mai yawa , mutane a kewayen ku ana musu kwace ana kashe su a kama su a matsayin kamanmun yaki  da kuma bayi   da kuyangu suna dandanan bala'I da annoba  kuma suna  jin jiki     a wurin tsada da kore su a gidajen su da karar da su   ku kiyaye amincin ku da kasar ku da zaman lafiyan ku .
     Gari nawa  ne  aka samu sabanin kalma kuma aka  warware  wilayan da aka kulla  sai ga shi kwarjinin hukunci ya zube  babu jagora  babu hadin kan jama'a   to ga mutanen cikin ta sai yakan junansu suke yi suna rarraba kawunan su suka rasa aminci da zaman lafiya sai ga shi  da suka rasa shi ya zama  rashin  na su ya musu muni, dawo da shi ya gagara  . Amru Dan As ya ce  a cikin wasiyyan da ya yiwa dan shi sai ga shi ya ce  : ( Ya dana shugaba  adili ya fi alheri akan ruwan sama mai yawan zuba  ).
 Jagora mai yawan zalunci ya fi alheri   akan fitinan da za ta dauwama  Abdullahi Dan mubarak Allah ya mishi rahama ya ce :-
Lallai jama'a igiyan Allah ne to ku yi riko da ita  ita ce*** igiya mai karfi ga wanda  ya yi hisabi  .
 Allah yana tunkudewa da shugaba abubuwa masu wahala  *** game da  addinin mu bisa rahama gare shi da yarda 
Ba don jagorori ba da ba mu samu aminci a hanyoyin mu ba *** kuma zai kasance masu raunin mu abin kwata ne ga masu karfin mu
 Idan hayaniya ta yawaita kara ta daukaka  aka tada zanga-zanga to to farkon wanda zai tsaya a bayan  ta    ya ruruta wutanta su ne makiya musulunci  , wanda siyasar su ta tsaya ne akan  yin ko oho da hakkin musulmai   da kuma halatta dukiyoyin su   da kuma lalata garuruwan su   da rusa tattalin arzikin su ,  da fada da addinin su,  kuma   musulunci idan  sun yake shi   sai ya yi karfi idan suka barshi  sai ya yadu  , wanda  baya  cutuwa don wani ya saba mishi   ko  ya yi ridda  daga gare shi,   kuma   bai cutar da shi  wanda ya tsananta wurin gaba da shi ba zai cutar da shi ba ,  sanin Allah game da makiya addinin sa ba a maida shi .
         Duk wanda ya nemi shiriya a wanin musulunci to ya bata ,  duk wanda kuma ya nemi kawo gyara ba tare da musulunci ba to zai zame, wanda ya nemi daukaka a wajen musulunci  to zai kaskanta, duk wanda ya  nemi aminci da wanin musulunci to amincin shi zai saraya ya ma rasa shi    .
     ( ALLAHU AKBAR  ALLAHU AKBAR      ALLAHU AKBAR   ALLAHU AKBAR  ALLAHU AKBAR  ALLAHU AKBAR ) Allah mai girma Allah mai girma  Allah mai girma  Allah mai girma Allah mai girma Allah mai girma. Ba abin bautawa da gaskiya sai Allah .
   YA KU MUSULMAI:
Zage –zage shi ke kunna fitina  ,  zagi baya dawo da wanda ya guje baya kuma janyo  mai musu  sai ma ya shuka gaba a tsakani da tsanan juna  shi kuma abokin fada sai ya kara dogewa da musu    abubuwa na ta faruwa cikin al'uma   mutane ba za su ji wata kara  ko  wani abu ba da ya faru na kusa ko na nesa face sun garzaya ga yanar giza  suna rikar wannan abin da ya faru  suna masu zagin junan su da shi   suna gaggawa zuwa ga shafin sada zumunta na facebook  tsakanin mai jifa da mai kazafi  da mai suka da mai tsinuwa  da mai zagi da mai cin zarafi   sai wanda Allah ya jikan shi  wadanda ba su da yawa 'yan kadan ne .
  Ya wadanda suke zana tsinuwa da zagi  suke jefa tuhumce-tuhumce   da hukunce-hukunce  to fa lallai za a tambaye ku game da abin da kuke rubutawa  a ranar da  halittu za su taru a cikin shi  a kuma auna ayuka a cikin shi   har abubuwa  da suke kanana  ko wani rayi za ta zo tare da ita akwai mai  shaida da mai korawa.
      Ya wanda yake  fakewa a bayan gilashin na'urarsa  , ya wanda yake buya da sunan aro   ya yi nesa daga idanuwa  ya rinka auna zagi da cin zarafi ga wanin sa ! Shin    ka  manta cewa Allah yana ganin ka ne   ?!  Kuma shi yana tsinkayan sirrinka da ganawarka   .
       Mumini bai zama mai yawan suka ko tsinuwa ko mai alfasha ko mai batsa ba .
To ka tuba daga abin da hannayen ka suka rubuta  ka share zagin ka da cutarwarka   ka tuna da fadin mahaliccin ka kuma  majibincin ta ( KA CE DA BAYI NA   SU FADA ABIN DA TAKE KEKKEWA  LALLAI SHAIDAN    SHAIDAN YA KASANCE YANA BARNA A TSAKANIN SU KUMA HAKIKA SHAIDAN YA KASANCE MABAYYANIN  KIYAYYA NE GA MUTUM ).
        Allah mai girma Allah mai girma ba abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Allah mai girma Allah mai girma  dukkan yabo da godiya sun tabbata gare shi
YA KU MUSULMAI :
Ku rayu da  musulunci da aminci da kauna da hadin kai  kar ku warware  cakudedeniya  face da kekkewan mu'amala  da sauke hakkoki na mu'ashara  da kuma tabbatar da adalci   awurin mu'amala  wanda ya cika  wani abu da ya kasance na mu'amala a kan shi  , haka shi ma za a kiyaye mishi abin da ya kasance na shi a kan wani  to wanda ya yi haka ya yi adalci a alkalanci  ya yi hukunci kuma na dai-dai   neman kwalkwalewa  cikin hakkoki   yana haifar da bijirewa, haka tsanantawa na bata zamantakewa,
Wanda ya kuskuren hanyar kauda kai da kawaici da yafiya  to makiyansa zasu yawaita, wadanda zasu yi zaman lafiya da shi 'yan kadan ne.   Masoyan sa za su kaurace mi shi   masu mu'amala da shi za su guje shi  wanda ya jahilci guraben shiriyar sa    wanda ya tsunduma cikin kogin jahilci  to zai haura jirgin fajirci  da kiraye – kiraye da cece ku ce  da karya a wurin koke – koke  da musu  sai ya zabi jafa'i  akan 'yan uwantaka   da kiyayya a kan soyayya  da kaushi akan taushi   in aka yi mu'amala da shi sai ya yi tsanani  in an kusanto shi sai ya yi fada da mutum idan ka nemi ku game da shi sai ya saba  kana neman riskan shi yana neman darewa  ya zo a cikin sahihul muslim Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce : ( Kada ku yankewa  juna  kar ku juya baya wa juna  kada ku yi gaba  kada ku yi hasada  ku kasance bayin Allah 'yan uwan juna ).
    Duk wanda ya shimfidawa mutane taburman girmamawa  ya fadada musu shimfidi na kimantawa   ya nema musu hujjoji da uzurori , ko da ya musguna a gare shi ya gajarta :- To zai rayu ne a cikin zukata abin girmamawa  kuma a harshe abin mutuntawa .
   Na kasance idan na kulla alaka da  mutane*** sai na abokance su  kuma dabi'una shi ne wafa'i 
to ka kyautatawa lokacin da masu kyautatawansu suka kyautata***  to ku nisaci munanawa in sun musguna
 ina son sabanin abin da suke so amma sai na zo *** Da abin da suke so na bar abin da nake so
  '' Hakika ance  cikin kauda kanka akwai hutu ga gabbanka''    ''kuma ance  mai ladabi mai hankali  shi ne mai wayo mai kawaici '' to ku yi yafiya  a tskanin ku  ku dauke kai daga wanda ya musguna muku  ku fita daga kunci na tattaunawa  zuwa ga  hutu na yafiya  , ku fita daga tsanani na tsauri zuawa ga saukin mu'amala  ku nade tabarmar yankewa  a tsakanin ku  da kewa  ku sada  zumunci na 'yan uwantaka da  kauna  ku karbi uzuri ,  domin karban uzuri  na daga cikin kyawawan halaye idan kun iya ,  idan ku ka samu iko akan mai musgunawa to ku sanya yafiya a gare shi  godiya ga Allah  sabo da kudura da kuka samu akan shi .

   Allah mai girma Allah mai girma ba abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Allah mai girma Allah mai girma  dukkan yabo da godiya sun tabbata gare shi
YA KU MUSULMAI :-
 Babu dauwama a duniya ga wanda yake fata  hakanan babu wanzuwa a cikinta ga mai fata  kuma mutane ba kowa ba ne sai matafiyi dan matafiyi  zamani kuma ba wani abu ba ne face  daci ne na yini da dare  mutuwa kuma ba wani abu bane face mai saukowa makusanci  ba wani numfashi face yana nisatar da haifaffe  kuma yana kusanto da mutuwa zuwa ga zukata don su fita  abin mamaki da irin saurin ranaku wurin nadewa  tana tafiya gare mu  sannan ta tafiyar da mu  , to, ku farkar da zukata daga bacci irin na  gafalanta  ku kauda zukata daga guraben sha'awe-sha'awen ta , ku kiyaye salloli biyar na wajibabbu da aka farlanta  kada ku yi sakaci wurin farillu da wajibabbu  kar ku rena  haramtattun abubuwa kar ku bayyana munanan abubuwa,  ku sani cewa kuna cikin ranaku da ana muku daku  bayan su akwai  lokaci , gaggawa na ingiza su  duk wanda  yau din shi bai amfanar da shi ba  to kuma  abun da bai tare da shi , shi ya fi wahala a gare shi , wanda baya kusa da shi kuma shi ne zai gagare shi  kuma lallai babu baccin da ya fi nauyi kaman  na  gafala , babu kuma bauta irin na gafala  babu bauta da yafi mallaka irin na sha'awa  babu musiba kuma da takai mutuwan zuciya   babu abu mai gargadi  da ya kai kololuwa sama da hurhura babu makoma mafi muni da ya kai  wuta .
   Allah mai girma Allah mai girma ba abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Allah mai girma Allah mai girma  dukkan yabo da godiya sun tabbata gare shi
Ina fadin abin da kuke ji  ina neman gafaran Allah  to ku nemi gafarar sa  lallai shi ya kasance mai gafara ne ga masu komawa gare shi.
 HUDUBA TA BIYU

     ( ALLAHU AKBAR  ALLAHU AKBAR      ALLAHU AKBAR   ALLAHU AKBAR  ALLAHU AKBAR  ALLAHU AKBAR  ALLAH MAI GIRMA  ALLAH MAI GIRMA  ALLAH MAI GIRMA WALLAHU AKBAR  ALLAHU AKBAR WA LILLAHIL HAMDU )
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah madaukaki mai girma   mai tausayi goni  na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya    ya halicci dukkan komai ya kyautata kaddara shi  ya gudanar da halittu ya kyutata gudanarwa na shada Annabin mu  kuma shugaban mu Muhammadu bawan sa ne  kuma manzon sa ne  mai albishir mai gargadi  kuma fitila ne mai haske  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi  da sahabban shi  tsira  abun ribanyawa na madauwamiya  har zuwa ranar sakayya  .
BAYAN HAKA:-
YA KU MUSULMAI:
Ku ji tsoron Allah  ku yi murakabar sa kuma ku yi mishi biyayya  kar ku saba mishi  ,(Yaku wadan da suka yi imani ku  ji tsoron Allah ku kasance tare da masu gaskiya )
YA KU MUSULMAI :
 Laiha kusanci ne madauwami  kuma ibada ce mai girma kuma wani alama ne daga cikin manyan alamomi na addini  ita laiha sunna ce mai karfi ba wajiba ba,  ba kuma mustahabbi ba ne barin ta ga wanda ke da iko  baya isarwa  ga laiha sai dabbobin gida  mafificin su shi ne rakumi sai tumaki   sannan sai tarayya a rakumi  sai kuma tarayya a saniya  shi kuma tarayya a rakumi  da tarayya a saniya  da tinkiya guda  yana isar ma duk wani mutum guda da iyalan gidan  shi  baya isarwa ga laiha sai jaza'in rago   koma bayan shi kuma dan shekara biyu  rakumi shekara biyar saniya shekara biyu akuya shekara guda rago wata shida  mafificin su  shi ne wanda ya fi kyau kuma ya fi kiba  mafi girman su  kuma mafi cika  mafi dadi  kuma wanda ya fi tsada , ku kiyaye laifuka da suke  hana isarwa ga laiha   mai aibi bayyananne  ba zai isar ba  na daga rashin lafiya ne ko ido daya  ko gurguntaka  ko rama  ko makanci na ido .
       ku lura da idanuwa, da kunnuwa , kar ku yi laiha da  laiha da mai kececcen kunne   ko mai tsagaggen kunne  ko mukabila ko mudabara wato su ne masu aibi  a kunnuwan su ta hanyar kecewa ko buli ko tsagu ku kyautata yanka   ku wasa abin yanka    don ya kasance ya kai kuma ya yi sauki .
   Ku fiskantar da abin yankan ku zuwa ga  alkibla   ku ambaci Allah ku yi kabbara  ku ci ku yi kyauta ku yi sadaka  wanda ya yi yanka kafin sallah to  ya sake laihar sa  wanda ba haka ba kuma to ya yi yanka bisa sunan Allah .
Allah ya karbi laihan ku ya yarda da ku kuma ya  yardar da ku   ya tabbatar muku cikin alheri  bukatun ku  kuma ya sanya ku walwala kar ya sanya ku cikin  tsiya   sannan kuma ya sake maimaita  muku sa'ada  , muddin idi ya sake maimaitowa, itaciya kuma ta yi koriya        
  Allah mai girma Allah mai girma ba abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Allah mai girma Allah mai girma  dukkan yabo da godiya sun tabbata gare shi 
YA KU MUSULMI:-
Wannan rana ce na yafiya da rangwami  ku yi rangwami ku yi yafiya ku yi rahama  ku kasance bayin Allah 'yan uwan juna  wanda ya sammaka  ya bi ta wata hanya to ya dawo ta wata hanyar ba ita ba  in hakan ta yiwu a gare shi don koyi da sunnan  shugaban manzonni  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi .
   Allah ya maimaita mana da ku wadan nan ranaku masu albarka  na shekaru masu yawa  da zamuna  daban-daban  masu yawa  a hali muna cikin koshin lafiya da daddadan   rayuwa .
    Ya Allah ka daukaka musulunci da musulmai ka kaskantar da shirka da mushrikai  ka rusa makiya addini  ka sanya kasan mu cikin aminci da natsuwa da sauran garuruwan musulmai .
    Ya Allah ka datar da jagoran mu kuma shugaban mu  shi mai hidima wa harami biyu masu alfarma da daukaka cikin abin da kake so kuma ka yarda da shi  kuma ka riki makwarkwadan sa  zuwa ga da'a da takawa    ,    
  Ya Allah ka datar da mataimakin shi cikin abinda  akwai daukakan musulunci da gyaruwan musulmai ya Ubangijin talikai  .
    Ya Allah ka taimaki sojojin mu masu dako a bakin daga  da iyakoki  ya Ubangijin talikai  ya Allah ka kiyaye jami'an tsaron mu ka saka musu da alheri mafi cika   ya Ubangijin talikai .
   Ya Allah ka warkar da mara lafiyan mu   ka bada lafiya ga wanda ka jarabce shi   a cikin mu  ka tausayawa matattun mu  ka taimake mu akan wanda ya yi gaba da mu .
Mafificin salati da aminci *** Bisa ga Annabi Musdafa mai girma .
Muhammadu mafi alherin talikai al akibu *** kuma lallai shi dinnan  shi ne mai haske a goshi ma'aboci falaloli.
Da sahabbansa masu girma masu da'a *** manya zababbu
Ya Allah ka yi dadin tsira da aminci bisa ga Annabin mu kuma shugaban mu  Muhammadu da iyalan sa da sahabban sa  salatin da za ta wanzu da aminci da zai bibiyi juna har zuwa ranar sakayya .
Allah mai girma Allah mai girma ba abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Allah mai girma Allah mai girma  dukkan yabo da godiya sun tabbata gare shi .

السبت، 18 أغسطس 2018

laduban Hajji


Hudubar  Juma'a  a Masllacin Annabi  6-12-1439AH
Sheikh Salah bin Muhammad Al- Budair
Hudubar farko:
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah , godiyar da ta dace da ni'imarsa da kyautarsa, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya, ba abi bauta bisa cancanci koma bayansa.Na shaida cewa Annabinmu  kuma shugabanmu Muhammad bawansa ne kuma Manzonsa ne , Annabinsa ne zababbensa  abin kaunarsa ,Majibincinsa yardajjensa, abin kulawarsa, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  da Iyalan shi da sahabban shi salati madawwami  muddin gari na waye wa haske na bayya
Bayan haka ya ku musulmai!  Ku ji tsoron Allah ta hanyar aiki zuwa ga neman yardarsa da nesatan saba masa .
( ya ku wadan da suka yi  imani ku ji tsoron Allah cancancin tsoronsa kar ku mutu face kuna musulmai)
Ya ku musulmai!
Hakika iska kakkamsa ta kada tsarkakakka  daddada  wacce ke dauke da kamshin ayyukan Hajji da ruhinsa, da labaransa da manyan alamominsa da farillansa, da Haramin Allah mai aminci  da ya cika shi  da karama  da kawa da kaye da  tsarkaka da daukaka,
Ga tawagar Alhazai suna nufan  Dakin Ka'aba suna (talbiyya  ) amsa kira daga kowane sako mai zurfi suna cike da farin-ciki  da dadin rai da washewar zuciya.
     Wannan tawagar Allah din wanda ta fiskanto zuwa ga Ubangijinta cikin gaggawa ta shimfida tafukan kaskanci tana mai rusunawa ,  sai ga idanuwanta na cika da hawaye , adu'o'in ta na daguwa zuwa sama 
     Gare ka na zo ya Ubangiji ina mai amsa kira *** Ka albarkaci hajjina da adu'o'I  na ya Ubangiji
Na zo  babu guzuri fatana ne kyautar ka  *** Baya hasara duk wanda ya  nemi kyautan ka
   Alhazan dakin Allah  ku girmama harami  kuma ku ga  girmar alfarmar sa  ku kiyaye matsayin sa  ku bada kariya ga kwarjinin sa ,  ku kiyaye bin doka da oda , ku yi nesa da abin da zai kawo matsala a aikin haji  ko kuma zai sabawa manufofin shi  ko kuma zai ci karo  da hadafin shi   haji ba wuri ne na husuma da cece ku ce ba       da musu  ba kuma gune na  taron gangami ko zanga-zanga ba  ba kuma gu ne na daga tutoti na ta'assubanci  ba ko  na  kungiyanci ba   Hajji  girman shi ya fi a ce wuri ne  na bajekolin sabani da kungiyanci   da mazhabanci  ko guri ne na bangaranci na siyasa ba .
     Ya ku Alhazai   da masu Umra ku nemi fahimtar fikhun Hajji  da sharudan isan  sa da siffan aiwatar da shi   kafin ku sanya ihrami  ku nufi dakin ka'aba mai alfarma  sau dayawa Alhaji  kan  aikata wani babban al'amari  har sai ya kai gari mai tsarki sannan ya kama aikin shi na hajj  sannan gashi bai san hukunce-hukuncen shi ba  bai kyautata cika shi ba  sai ya koma zuwa garin shi yana mai halin ya bar wani  rukuni    ko ya yada wani sharadi  ko kuma ya yi sakaci da wani abu na wajibi ko ya aikata wani  abin da aka hana mai ihrami ya aikata ,    ko ya zo da wani abu da aka yi gargadi a kai    .
 YA TAWAGAN   ALHAZAI DA MAZU UMRA DA MAZIYAR TA :
Akidar musulunci   ta hada ku , farillan hajji ya sa ku  a tsari  dankon zumuncin addini ya hada  ku  to, ku tausayawa juna    ku yi  ludufi  , ku yi taimakekeniya    kada ku yi tunkudedeniya  kar ku yi cunkoso kar ku yi fada  ku tausayawa masu rauni   ku shiryar da wanda suka bace   ku taimaki gajiyayye mabukaci  .
    Wajibi ne a gare ku ku tausaya   ku yi dako  da saukin lamari da  yafiya da barin cunkoso   da kuma janyo natsuwa  da kuma jin tsoron Allah a cikin zuciya  da lazimtar     mutuntawa da tausasawa , .
    Na hore ku da ku yi nesa daga jidali da musu   da dadin baki  da kiyaye cece ku ce  da jayayya  da kuma wasa irin na magana  ku nisaci fadin batsa da alfasha  da yasassar magana  da kauracewa juna  da zage-zage da  suka  lakuba marasa kyau, ku kiyaye Hajjin ku  daga kazantar shirka , da najasar bidi'o'I da fararrun abubuwa .
           Ku nisanci ketare iyaka   ku jefi  jamra da kananan duwatsu wanda girman su bai fi na gujjiya ba  ko kuma  kwallan dabino ,   ko kuma  kan yasu    ku kiyaye ketare iyaka na shari'a  ku yi koyi da masoyi abin kauna zababbe   tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ,  a  ibadodin ku da ayukan ku na hajji  ku yawaita tuba da istigfari    ku bayyana kankan da kai da marairaicewa da nadama da nuna bukatuwa ,  da nuna talauci da nuna bukata ga Allah     domin ku dinnan ku na wurin da rahama ke zuba  kuma kuna bigire da wurin karba  da wurin da ake sa ran karban adu'a  da gafara da 'yantawa daga wuta  ku tuna girman wurin da darajan zamanin Allah na karban adu'o'in ku da amsawa da neman gafarar ku da yarda da karban Hajjin ku  da sanya  aikin ku ya zama abin  godiya zunuban ya zama abi gafartawa  Hajjin ku ya zama   wadda aka yi da'a ne a cikinta , wanda ya yi hajji baiyi batsa ba bai yi fasikanci ba  zai koma kamar yanda mahaifiyar  shi ta haifiyar shi ta haife shi, shi hajjin da aka yi da 'a a cikin shi bai da sakayya sai aljanna ina fadin abin da kuke ji kuma ina neman gafaran Allah  , ku nemi gafaran Allah  domin shi mai yawan gafara ne  ga masu komawa gare shi da tuba.
HUDUBA  TA BIYU
Dukkan yabo da godiya sun tabbata  ga  Allah wanda bisa ludifin sa   ya tattara wanda ya tattaro    na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah wanda shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya  ya warkar da ni'imar sa da mutumin da ciwon sa ya sa ya yanke tsammani daga magani   na shaida cewa Annabin mu kuma shugaban mu Muhammad bawan sa ne kuma Manzon sa ne tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabban shi , tsira mai wanzuwa da aminci mai bibiyan juna .
BAYAN HAKA:
YA KU MUSULMAI:- ku ji tsoron Allah ku yi murakabarsa , ku mishi biyayya kada ku saba masa,    (ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah   ku kasance tare da masu gaskiya  )
YA KU MUSULMAI :
Ranar arfa rana  ne mai daraja  da daukaka  kuma idi ne mai girma  ga ma'abota maukif   rana ne da ake 'yanta  wuyaye a cikin shi  ana sauraron adu'o'i kuma a amsa  rana ne wanda alherin Ubangijin mu ya yawaita kuma ya dadada,  ba wani rana da Allah ya fi 'yanta bawa daga wuta  kamar ranar arfa  lallai yana kusanta sannan ya yi alfahari da su gaban mala'iku sannan ya ce mai wadannan suke so .
   Adu'an da ya fi ko wanne albarka  da yalwa  a wurin lada   da saurin amsawa shi ne Aduar Arfa, to ku yi kokari da kankan da kai da kyautata yabo , da Adu'a , kuma mustahabbi ne yin azumin ranar Arfa ga wanda bai hajji, azumtar ta na kankare  zunuban shekarar da ta gabata, da shekara da ta biyo ta.
Mustahabbi ne yin kabbarori a karshen sallolin farillah, tun daga asuban ranar Arafa har zuwa ranar karshe na ayyamu al-Tashrik, wanda aka tsere wa a  wani sashe na sallah to zai kawo su kabbarorin ne bayan ya rama sallarsa,  Alhazai za su fara kabbarorin ne daga azahar na ranar Babbar sallah.
Ya ku Musulmai!
Ku yi kabbarori a sassa da nahiyoyi,ku yi kabbarori a gine gine da sarari, ku yi kabbarori a gidaje da jeji, ku yi kabbarori a safiya da maraice, ku yi ta kabbarori har ya cika sama,
Allahu Akbar Allahu Akbar  la'ilaha illal lahu Allahu Akbar walillahil Hamd
Ku yi salati da aminci ga Ahmadu mai shiryarwa  mai ceto ga dukka halittu, wanda ya mishi salati guda Allah zai mishi guda goma.
Ya Allah ka yi dadin tsira ga bawan ka kuma manzonka  Muhammad, ya Allah ka yarda da iyalanshi da sahabbai da mu  ya mai karamci mai kyauta.
Ya Allah ka daukaka Musulunci da Musulmai ka kaskantar da shirka da mushrikai, ka rusa makiya Addini, ka sanya garuruwan musulmai cikin aminci da natsuwa da kwanciyan hankali da zaman lafiya ya Ubangijin talikai             

الاثنين، 30 يوليو 2018

'YAN UWANTAKA A MUSULUNCI


HUDUBAR  JUMA'A NA MASALLACIN ANNABI NA  SHAIK ALIYU AL-HUZAIFI  14\11\1439
HUDUBAR FARKO
Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Mabuwayi mai hikima , mai rahama mai jin kai ina kyautata yabo ga  Ubangijina  ina kuma gode masa bisa  ni'imomin sa wadanda muka sani da wadan da ba mu sani ba  to shi din nan ahli ne na  a ambace shi ba za a manta shi ba a kuma gode mishi ba za a saba mishi ba ,  shi ne mawadaci mai karamci , na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kaadai yake bashi da abokin tarayya , madaukaki mai girma  na shaida Annabin mu kuma shugaban mu Muhammad  bawan sa ne kuma Manzon sa ne  wanda Allah ya fifita shi akan bayin sa ga dukkan dabi'u na karamci , ya Allah ka yi dadin tsira da  aminci bisa ga bawan ka kuma Manzonka   Muhammad da iyalan sa da sahabban sa  masu shiryarwa zuwa ga tafarki mikakke  bayan haka ku ji tsoron Allah  ta hanyar neman kusanci zuwa gare shi da neman yardan shi da barin abubuwan da ya haramta su  ba masu rabauta sai masu tsoron Allah    ba masu hasara sai masu sabon  Allah mabarnata  .
             Ya ku musulmai  :
Mumini  shi  mai karfi ne da imanin sa  sa'annan kuma mai karfi ne da 'yan uwan sa,   Mumini yana karkata ne zuwa ga imanin sa da  Ubangijin sa a lokacin tsanani  da bakin ciki  kuma yana riko da  imanin sa  da Ubangijin sa a lokacin da wasu shubuhohi suka bulla    da kuma sha'awe –sha'awe   kuma yana ganin haske ne da imanin sa a lokacin duhun fitintinu da musibu Allah sai ya kare shi da imanin sa lokacin sauki da lafiya da faraga  domin kar ya fada ya halaka  cikin jin dadin abubuwan da aka haramta .
      Allah yakan raya shi da imanin sa a duniya irin rayuwa mai albarka  mai walwala  abin yarda  mai amfani   kyakkyawa mai kyakkyawan karshe  da imanin sa da Ubangijin sa ne zai riski daraja madaukakiya  bayan mutuwa  Allah madaukakin sarki yake cewa: (  lallai wadan da suka yi imani suka yi aiki na kwarai Ubangijin su zai shirye su   dalilin imanin su  kwaraimai na gudana a karkashin su  a cikin lambuna masu ni'ima  adu'a an su a cikinta shi ne  tsarki ya tabbata a gare ka ya Allah  gaisuwan su kuma a cikinta aminci   , karshen da'awar su shi ne dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai  , ).
                      An karbo daga salman Allah ya kara yarda a gare shi  daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Abin mamaki da al'amarin mumini lallai dukkan al'amarin sa alheri ne  ba wanda yake da wannan face mumini  idan abin jin dadi ya same shi sai ya gode to sai hakan ya zama alheri a gare shi idan kuma cuta ya same shi sai ya yi hakuri sai hakan ya zama alheri a gare shi  ) Muslim ne ya rawaito
              To shi mumini  madaukaki ne  mai walwala ne kuma wanda ya yi dace ne da imanin sa  kamar yanda mumini  yana da karfi ta hanyar 'yan uwan sa   domin 'yan uwantaka na musulunci ya fi karfi akan 'yan uwantaka na jini sabo da haka ne ma    gado ke datsewa tsakanin musulmi da kafiri, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Musulmi baya gadan kafiri haka kafiri baya gadan musulmi) Buhari da Muslim ne suka rawaito   daga hadisin Usama dan Zaid Allah ya kara yarda a gare su , to, 'yan uwantaka na Musulunci ya fi girma  akan alaka  da zumunci  da dunkulewa  Allah madaukakin sarki ya ce : ( muminai maza da muminai mata sashin su waliyyai ne ga sashi    suna umarni  da kyakkyawa kuma suna hani ga mummuna  suna kuma tsaida sallah suna kuma bada zakka kuma suna yiwa Allah da'a da Manzon sa wadan nan Allah zai jikan su , lallai Allah mabuwayi ne mai hikima) . Allah madaukakin sarki ya ce : ( Lallai muminai 'yan uwan juna ne)     Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Musulmi dan uwan musulmi ne ba zai zalunce shi ba ba zai tabar da shi ba) .  muslim ne ya rawaito shi
                To 'yan uwantaka na musulunci yana kasancewa ta hanyar taimakekeniya  a addini da karfin hadin kai  Allah madaukakin sarki ya ce  ga Annabin shi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi : (  Shi ne wanda ya karfafe ka da taimakon shi  da kuma muminai ya kuma hada zukatan su  da ka ciyar da duk abin da ke doron kasa gaba daya da ba ka iya hada zukatan su ba sai dai Allah shi ya hada zukatan su, lallai shi din nan mabuwayi ne  mai hikima ) kuma Allah madaukakin sarki ya ce : ( Ya ku wadanda kuka yi imani  ku ji tsoron Allah cancancin tsoron shi  kada ku mutu face kuna musulmai , ku yi riko da igiyan Allah  baki daya  kar ku rarraba  ku ambaci ni'imar Ubangiji a gare ku zamanin da kuka kasance makiya juna   sai kuka zama 'yan uwa sabo da ni'imar Allah  ,   a da kun kasance a gabar rami  na wuta   ya tsamo ku daga gare ta  )
          'Yan uwantakan addini yana kasancewa ne   ta hanyar taimakekeniya  wurin tabbatar da maslahohi  da tunkude barna  da bada kariya  ga al'umma  daga masu ketare iyaka  Allah madaukaakin sarki ya ce: ( ku yi taimakekeniya akan da'a da kuma tsoron Allah , kada ku yi taimakekeniya akan laifi da kiyayya ) Allah madaukakin sarki ya ce : ( Ya kasance a cikin ku akwai wata al'uma da tana kira zuwa  ga alheri, kuma suna  umarni da kyakkyawa  , kuma  suna hani da  mummuna  wadannan sune masu rabauta ).
     'Yan uwantaka na musulunci  yana kasancewa ta hanyar jin kai da tausayawa juna  da kuma  taimakekeniya  , da kuma  hadin guiwa  wurin samar da abin da al'uma ke bukata  da kyakkyawan tsarin rayuwa  Annabi  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya ce : ( Misalin muminai cikin kaunar su da son junan su da tausayawa junan su kamar  gangan jiki ne guda     idan wani gaba ya tabu da rashin lafiya  sai sauran jikin ya amsa  da zugi da rashin bacci ) Buhari ne ya rawaito da muslim daga Hadisin Abu Musa Al-ash'ari  
       Na daga cikin abin da ke kawo dadin rayuwa akwai wanzuwar kauna a tsakanin  musulmai   Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (   Na rantse da wanda raina yake hanun shi  ba za ku taba shiga aljanna ba har sai kun yi imani  , ba za ku yi imani ba kuma har sai kun so junan ku  , ase ba zan nusar da ku  bisa ga aabin da idan kun aikata shi za ku kaunaci junan ku ba  to ku yada  sallama a tsakanin ku .,
    YA JAMA'AR MUSULMI:
     Rayuwa fa ba za ta daidaita ba har sai kun tashi da hakkoki na 'yan uwantaka na musulunci   ,  to abubuwan da suke na wajibi akwai wanda suke  na Ubangiji madaukakin sarki , wannan shi ne wajibi mafi girma  da kadaita Allah da bauta mishi ,  daga ciki kuma akwai abin da yake hakki ne na  halittu  ,   kuma hakkokin musulmai iri uku ne :-
            Mafi girman su shi ne fifita wani akan kai (isar) wato gabatar da bukatar musulmi   da hakkin shi akan hakkin kai  wannan ita ce daraja da muhajirun suka rabauta da ita da kuma ansar Allah ya kara yarda a gare su  Allah madaukakin sarki ya ce: (Wadanda suke zaune a madina suka kudure imani tun gabanin su  suna son wanda yayi hijira gare su ya yi kaura  basa hasada da abinda ya basu   suna fifitawa 'yan uwan su a kan kansu  koda akwai wani bukata a gare su izuwa  abinda suka fifita   wani da shi , wanda aka kiyashe shi kwadayin kansa   wadancannin ka   su ne hakikanin marabauta ).
        Wannan na maimaituwa a ko wani zamani   da ko wani wuri  idan imani ya cika  tarihi ya kiyaye mana   wasu sifofi na fifita wani akan kai masu yawa a lokuta daban-daban  
 Daraja  na tsakatsakiya kuma daga cikin darajoji na 'yan uwantaka  shi ne mutum musulmi ya    so wa dan uwansa abin da ya so wa kan sa an karbo daga Anas Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (     Imanin dayan ku ba zai cika  ba har sai ya so wa dan uwan shi abin da yake so wa kanshi) Buhari da Muslim ne suka rawaito
         Mafi daraja na kasa kuma  wanda musulmi zai tashi da shi game da hakkin dan uwan shi musulmi shi ne ka kame sharrin ka daga gare shi ,  ba za ka zalunce shi ba a jini ne ko dukiya ko mutunci  , ba za ka zare harshen ka ba akan shi   ko hanun ka  ko kuma ka tawaye mishi wani hakkin  da yake na shi ne  ,  ko ka hana shi hakkin sa  tare da yin kokari  yin abin da Allah zai datar da kai zuwa gare shi na alheri, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce da Abu zarri (kuma ka kame sharrinka daga mutane, domin hakan sadaka ne gare ka a kan ka,)
Ya ku musulmai!
Lallai abin da ya fi cutar da 'yan uwantaka na musulunci shine bidi'a mai batarwa, don dan bidi'a yana kiyayya ga duk wanda  bai aminta da bidi'arsa, ba abin da zai hada zukatar musulmai sai akidar Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da sahabbansa da wadanda suka bi su da kyautatawa , su ne masu son juna don Allah, na karshen su na son na farkonsu, Allah Madaukakin sarki ya ce: ( Wadan da suka zo bayansu suna cewa  :Ya Ubangijinmu ka gafarta mana  da 'yan uwan mu da suka gabace mu da imani kar ka sanya kulli cikin zuciyarmu game da wadan da suka yi imani ya Ubangijinmu kai mai tausayi ne mai jinkai)
Na daga cikin abin da ke cutar da 'yan uwantaka ta musulunci akwai fifita duniya akan lahira, da mutuwa don ita. Har ya zama  mafi yawan mutane kan haka suke 'yan uwantakarsu, da gina kiyayya kan kawar duniya da jin dadinta.
Na daga cikin abin da ke cutar da 'yan uwantaka  zalunci da yaduwar wannan zalunci ta hanyar hana mutane hakkokinsu, ko kwace hakki, don rayin dan adam na tsanan duk wanda ya zalunce ta, kuma tana neman daukar fansa, daga gare shi,
Na daga cikin abin da ke cutar da 'yan uwantaka  na musulunci akwai hasada, domin yana janyo gaba da kiyayya.
Na daga cikin abin da ke haifar da illa ga 'yan uwantaka na musulunci mutum ya rika ganin kansa  a matsayin kamili  ya ke  ganin waninsa  da reni da tawaya. To ga ku jama'ar musulmi jikunanku sun hadu a farillu  na musulunci, a hajji da juma'a da  sallar jam'i da sallolin idi, to ku hada zukatanku a kan akidar magabata na kwarai, da kur'ani da sunna , ku tuna cew za ku koma ga Allah Madaukaki, ku bar duk wani abu da ke kange ku daga gaskiya, ku tsaya gaba ga Ubangijinku huntaye tsirara, ba kaciya, ba wani abu tare da ku sai kyawawan ayyukanku da munana, to ku zo wa kyawawan ayyuka ku kiyayi munanan ayyuka,Allah Madaukakin sarki ya ce : (ku yi gaggawa zuwa ga gafara daga Ubangijinku  da Aljanna fadinta ya kai sammai da kasa an tanade ta don masu tsoron Allah. Wadan da suke ciyarwa a lokacin sauki da tsanani, da masu hadiye fushi da masu yafiya ga mutane, Allah na son masu kyautatawa,)
Allah sanya mini albarka ni da ku cikin Alkur'ani mai girma,
Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah a kowane hali, muna neman tsarin shi daga hali irin na 'yan wuta, wadan da ayyukansu ya jefa su cikin wulakanci da azaba, ina gode wa Ubangiji na bisa ga kyauta mai girma,Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya Mai girma Maabocin daukaka, Na shaida Annabin mu kuma shugabanmu Muhammad bawansa ne kuma Manzonsa ne.
Allah ka yi dadin tsira a gare shi da sahabbansa da iyalai, bayan haka ku ji tsoron Allah ku mishi biyayya, ku kiyayi fushinsa  da bushewar ido cikin saba masa, ya ku bayin Allah hakika hujja fa ta tsayu a kanku, hanya ta bayyana a gare ku, kuma duk wasu uzurori sun yanke, to ku fiskanci aiki kada buri ya rude ku, Allah Madaukakin sarki na cewa : (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijin ku ku kiyayi wata rana da Mahaifi ba zai fanshi dansa ba ko shi  da ya fanshi mahaifinsa  da wani abu ba, Alkawarin Allah gaskiya ne kada rayuwar duniya ta rude ku, kada kuma wani abin rudi ya rude ku daga Allah)
To ku tuna mutuwa da abin da ke bi mata na daga azaba  da ba mai kubutar da mutum daga shi sai ayyuka na kwarai, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce ku yawaita ambato mai datse jin dadi, wato mutuwa ,
Ya ku bayin Allah lale Allah da Mala'ikunsa su na  salati ga Annabi ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi da aminci tabbatacce,
Har karshen Adua.