الخميس، 13 يوليو 2017

JIN DADIN RAYUWAR DUNIYA GA MUSULMI

Hudubar  Juma'a  a Masallacin Annabi 20 shawwal 1438 AH Na Sheikh Abdul-Bari Bin Awad Al- subaiti
Allah ya sanya kasa ga mutum  shimfida da makwanci ,ya sanya a cikin shi Matabbata da kuma jin dadi zuwa wani lokaci, sannan ya sa albarka kuma ya kaddara abin cinta a ciki  Allah ya hore  abin da ke cikin sammai da kasa, ya sanya dare da wuni da rana da wata da   sauran halittu don amfanin bayi da kuma nau'uka na  maslahohinsu.
Na daga cikin hikimar   samar da amfani shine a bawa musulmi  daman jin dadi  da abin da Allah ya halatta, mutun ya ji dadi  da rayuwa ta duniya da jin dadinta, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Lalle Ubangijinka yana da hakki a gare ka haka nan jikinka na da hakki a gare ka kuma iyalan ka na da hakki a gare ka haka nan shi ma mai ziyaranka  yana da  hakki a gare ka to ka bawa kowanne hakkinsa.)
  Allah Madaukakin sarki yana cewa : (ka ce: wa ya haramta kawa na Allah wanda ya fitar ga bayinSa da dadada  na daga arziki? ka ce : su din nan  ga wadanda suka yi imani ne a wannan rayuwa ta duniya sannan kuma yana  kebanta a gare su ranar alkiyama haka nan ne muke bayanin ayoyi daki daki  ga mutanen da suke sani).
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi kira da bayyana abin da ke cikin addinin Allah na hutu da shakatawa ta rayuwar duniya don jin dadi da ke kawo karsashi ga rai da ingizawa zuwa ga aiki, a lokacin da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya ga  mutanen Habashawa suna wasa sai ya ce: (Domin ku sani a cikin Addininmu akwai sauki da sassauci, domin ni an turo ni ne da addini mai sauki wato Alhanifiyya Assamha)
Aliyu Dan Abu Dalib Allah ya kara yarda a gareshi ya ce: (Lalle zukata na kosawa kamar yanda jiki ke kosawa to ku nema mata abubuwa da kalaman hikima  na jin dadi )
kuma yake cewa : (ku hutar da zukatanku na wani lokaci bayan lokaci domin zuciya idan an takura mata sai ta makance).
Abu darda' Allah ya kara yarda a gareshi yana cewa (lalle ni ina dan zuwa yawo na shakatawa da zuciyata da wasa na halal domin ya dada  samun karfi don tsayuwa a kan gaskiya.
Manzon mu tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi mai karamci yana cewa  ya kai  Hanzala haba dan lokaci  bayan  lokaci mana )(Wato a huta)
Umar dan kaddab yace:( mutanen (sahabbai) sun kasance suna dariya a halin  imani a cikin zukatansu  yafi karfi da kafuwa  akan dutse.)
To wan nan wasan da jin dadin baya raunana imaninsu kuma baya bata dabiunsu sannan  kuma ba ya sa su ketare lokaci na sallarsu da ambaton Allah da karatun alkur,ani.
Jin dadin musulmi daga cikin abin da Allah ya samar madaukakin sarki na daga abubuwa na amfani da alheri ana gina shi ne akan daidaito tare da saiti, sai mutum ya rayu da fidira irin wanda Allah ya halicci dan adam akai sannan mutum yaji dadin abin da Allah ya halatta a gare shi tare da yalwata jin dadi da annashawa musamman alokacin idi wato da kuma bukukuwa ana bawa mutum lada alokacin da yake jin dadi a rayuwarsa na duniya in bai fita cikin dokoki na sharia ba da ka'idoji na addini ba Manzo Allah tsira da aminci Allah su tabbata a gare shi yace: (A cikin tsokan dayanku akwai sadaka (wato agurin tarawa da iyali) sai suka ce ya Manzon Allah mutum zai  biya bukatarsa ya more shaawarsa kuma kasance yana da lada? Annabi yace: E  yanzu in da zina ya yi  shin bai da alhaki? sai suka ce e yana da shi.  yace to haka ne idan ya sanya shi ahalal to shima yanada lada.
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: ( An sanya min kaunar turare da mata, sannan an sanya sanyin  idanuwana acikin  sallah).
   Dadin rayuwan duniya da ni'marta na daga cikin nau'uka na gabatar da lada da Allah ke yi wa bayinsa mu'minai kari a kan abin da ya tattala musu a ranar sakayya  na daga ni'ma na madawwamiya,  Allah Madaukakin sarki ya ce :(To domin men wata alkarya bata kasance ta yi imani ba har  imaninta ya amfane ta, face mutanen Yunus?  A lokacin da suka yi imani mun janye azabar wulakanci daga gare su a cikin rayuwar duniya kuma muka jiyar da su dadi zuwa wani lokaci )
A duk lokacin da bawa ya  dada kusantan majibincin shi  ya kuma koma zuwa gareshi to zai yi rayuwa na jin dadi da morewa kuma abin da ke wurin Allah yafi alheri kuma yafi wanzuwa : shi jin dadi da morewa na daga cikin amfanin  ne ayyuka na kawarai,  Allah madaukakin sarki ya ce :(wanda ya yi aiki na kawarai na daga na miji ko mace  yana mumini to zamu raya shi rayuwa na jin dadi  kuma mu sakanya mishi da mafi kyan abin da suka kasance suna aikatawa ) mafi girman abu mai kawo  jin dadi shi ne lazimtan istigfari wanda da shi ne alheri ke tabbatuwa da albarkoki kuma da shi a ke tunkude bala'i kuma a duddulo da arziki sannan muna sha daga albarkatun sama a  fitar mana kuma da albarkatun kasa kuma a taimaka mana  da dukiya da y'ay'a  sai na ce ku nemi gafara daga ubangijinku lalle ya kasance mai gafara ne0 ya sako (girgijen) sama a kanku da ruwa mai bubbuga . kuma ya yalwata muku game da dukiya da diya ,( kuma ya sanya muku albarka  kuma ya sanya muku gonaki kuma ya sanya muku koguna )
walwala da jin dadi a rayuwan mutun  musulmi abu ne mai fadi da yalwar ma'ana ya taso ne daga wasu manufofi masu daraja kuma ya ta'allaka da sako na wannan addini da halayensa da ladubansa , kai lalle jin dadi wani hanya ne na sauke sako  ba ita ce ma kura ba  da ake so a nemi jin dadin ta,   to idan ba haka ba kuma to sai mutun ya dulmuye ya samu rauni da fandarewa.    
jin dadi a rayuwan musulmi be  iyakance shi a  kyalakyalan  rayuwan duniya ba bai kuma tsakaita a kantaba, sai dai ma ya zarce zuwa ga ni'ma na aljanna wanda ke mantar da dukkan gajiya da wahalhalu na duniya  :to shi musulmi yana riskan cewa wannan rayuwan na duniya duk yadda ta tsawaita to zata gushe kuma jin dadinta duk yadda ya girmama to na dan wani lokaci ne, Allah madaukakin sarki ya ce ( ka ce jin dadin duniya dan kadan ne )
kuma Allah ya ce:(kuma  alhali kuwa rayuwan duniya bata zama ba dangane da duniya face jin dadi kadan ) (kuma kuna da a cikin kasa matabbata da kuma jin dadi zuwa wani lokaci )
Aduk lokacin da  musulmi ya dandani dadi na rayuwan duniya da walwalanta )
zai yi gaggawan faduwa a tunaninshi jin dadi na aljanna da ni'mar lahira sai ya yi gaggawa saboda kwadayi da shawki zuwa gareta da kuma fatan samun daraja mafi kololuwa
 Allah madaukakin sarki ya ce: (sabo da haka  abin da aka ba ku, ko mene ne,  to, jin dadin rayuwan duniya ne kuma abin da ke wurin Allah shi ne mafifici kuma shi ne mafi wanzuwa ga wanda suka yi imani kuma suna dogara a kan ubangijinsu kawai )
imani da Allah da dogaro a gare shi tsarki ya tabbata a gare shi rangwame da afuwa da yafiya da sa farin ciki a zukatan masu rauni da sanya musu hoton shi a fiskan su da idanuwan su da tsayuwa don biyawa mutane bukatunsu shine dukkan jin dadi,
wani mutumi ya zo gun Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi sai ya ce ya manzon Allah wani aiki ne yafi soyuwa a wurin Allah? sai ya ce farin ciki da zaka jefa wa musulmi  ko kuma ka yaye mishi bakin ciki, ko kuma wani bashi da zaka biya masa  ko ka kore mishi yunwa ,da na tashi na tafi ga dan uwana musulmi da bukata yafi soyuwa a gare ni  a kan na yi itikafi a wannan masallaci :yana nufi masallacin madina .
Na daga cikin jindadin duniya akwai ni'ima ta 'ya'ya da 'yan Uwa maza da mata, don samuwarsu akwai debe kewa, gyaruwarsu kamar wata ganima ce da karfi, su kawa ce ta rayuwar duniya da kyalakyalanta, da kuma cikar walwala da annashawa ne,su ne ma tushenta, Farinciki da walwala na karuwa a lokacin da ka yi shi tare da 'yan Uwanka da wadanda ke kewaye da kai, ka yi farin ciki da farincikinsu, kuma ka samu walwala da debe kewa a dalilin nasu walwalar,ka yi tarayya da su a jin dadi da annashawa,
Rayi na kara samun jin dadi a lokacin da mutum ya cinma wata manufa ya yi nasara a aiki ya tsinkayi daukaka  da fa'idojinta, kamar yadda ya ke shiga rayuwa mafi  sa'ida idan ya kammala wata ibada,zai yi murna da azumi yayin da ya sha ruwa, zai yi murna da sallah yayin da ya ya yi ta, haka kuma da hajji bayan ya sauke ayyukanta.
Dadi na kai wa makura idan mutum ya yarda da  kaddara ta Ubangiji, ya zama ya samu yakini da Allah Madaukaki a dukkan  abin da ya hukunta na al'amari, Abu Addarda ya ce : ( Lalle Idan Allah ya kaddara hukunci to yana so bayi su yarda da shi)
Ibnu Mas'ud ya ce : (Allah cikin adalcinsa ya sanya hutu da farinciki a yakini da yarda, ya kuma sanya bakin ciki da bacin rai a shakku.)
Umar dan Abdul'Aziz Allah ya masa rahama ya ce :( Na wayi gari ba abin da ya rage na ke jin dadinsa sai cikin yarda da abin da Allah ya hukunta)
Huduba ta biyu
Mai hankali ya na baiwa rayuwar duniya matsayinta, bai kwace wa a tunanin sa alkawarin Allah duk yadda kyala kyalan duniya da kawannta  ke ci da habaka, Allah  Madaukakin sarki ya ce :( kuma wannan rayuwa ta duniya ba ta zamo ba face abar shagala da wasa, kuma lalle lahira tabbas ita ce rayuwa, da sun kasance suna sani,)
Mai hankali zai yi taka tsantsan da jindadi na boge, wanda ke haifar da hasara da nadama, domin sabo karshen sa kaskanci ne da bakin ciki da radadi, ba wata ni'ima da zata gushe wa mutum face sabo da shu'umci irin na sabonsa, domin idan Allah ya yi ni'ima ga bawansa  sai ya kiyaye ta gare shi ba zai sauya ta gare shi ba har sai idan shin ne da kansa ya yi aiki don canja ta, (Lalle ne Allah bai canja abin da ya ke ga mutane sai sun canja abin da ya ke ga zukatansu kuma idan Allah ya yi nufin wata azaba game da mutane to babu mai mayar da ita kuma ba su da wani majibinci baicin shi ).
Wace hasara ce ta fi jin dadin da zai haifar da fushin Allah da azabarsa? Allah madaukakin sarki ya ce :(wancan domin abin da ku ka kasance ne kuna farin ciki da shi a cikin kasa ba da hakki ba kuma da abin da kuka kasance kuna yi na nishadi).
                                                                                                                                                                                        









الخميس، 29 يونيو 2017

CI GABA DA AYYUKAN DAA BAYAN WATAN AZUMI

Hudubar masallacin Annabi  6-shawwal 1438AH na sheikh Abdullah bin Abdurrahman Albuaijan
Dukkan yabo da godiya  sun tabbata ga Alllah, wanda da ni'marsa ce ayyuka na  kwarai ke kammala, na shaida babu abin bawtawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya, Ubangijin kasa da sammai na shaida lalle Annabin mu Muhammadu bawansa ne kuma manzonsane, shine mafi darajan wadanda su ka yi gaggawa zuwa ga alkin alheri,
 Allah ka yi dadin tsira da aminci da albarka a gare shi da iyalansa da sahabbansa masu tsoron Allah da ayyuka na kwarai.
 Baya haka:
lalle mafi alherin zance shine littafin Allah kuma mafi alherin koyarwa shine koyarwan Annabi muhammadu tsira da  amincin Allah su tabbata a gareshi,  mafi sharrin al'amura shine fararrunsu dukkan bidi' a kuma bata ce dukkan bata kuma yana wuta .
ya ku bayin Allah ina muku wasiyya da ni kaina da tsoron Allah Mabuwayi da daukaka domin ita ce wasiyyan Allah ga mutanen farko da na karshe (kuma lalle ne hakika mun yi wasiyya daga wanda aka baiwa littafi a gabaninku da ku cewa kubi Allah da takawa
ya jama'r musulmi:
cikin shudewan zamanunnuka akwai abin lura mafi girma haka  cikin jujjuyawar ranaku akwai gargadi mafi girma (lalle ne a cikin sabawan dare da yini da abin da Allah ya halitta a cikin sammai da kasa akwai ayoyi ga mutane wadanda su ke yin takawa).
Ya ku bayin  Allah!  hakika munyi bankwana da wata mai girma kamin wasu yan kawana ki kadan kum wani lokaci ne mai girma daga cikin lokutan alheri da albarka ya kasance yana cike da riba da kyawtuttuka da gafara da rahama wanda ke ratsa zuciya ga idanuwa kuma na zubar da hawaye ga zukata sun  rusunawa Ubangijinsu kuma suna cikin tsoro, da gabbai sun himmatu suna fiskantan Allah da wurin ambaton shi kuma ana raya masallatai da ambaton Allah da karatun alkura'ni ga natsuwa ta sauko kuma rahama ta lullube.
Allah ya karrama mu da azumi a wuninsa da abin da ya sawwaka na  tsayuwa a darensa, ya kuma  datar da mu a cikinsa da da yawa daga nau'uka  na da'a da ibadoji da zikiri da adduao'i da sadakoki, to dukkan yabo da godiya da baiwa na Allah ne to muna godiya a gare shi bisa wadannan ni'momi to   ya Allah ka karba .
Ba wani abu bane face wasu ranaku kididdigaggu da awowi iyakantattu da wasu  'yan lokuta da ke shudewa hakika gajiyansu da wahalansu sun tafi saura ladarsu da ribarsu in Allah ya yarda .
Watan ramadana ya kare kuma ya nade tabarmarsa wanda ya rabauta a cikinsa ya rabauta wanda aka haramtawa kuma an haramta mishi Allah sarki wanene aka karbi aikin shi a cikin mu yi mishi murna! kuma wanene aka maida mishi mu mishi jaje! .



 Ya ku bayin Allah
Ibada na da tasiri a halayen ma'abotanta Allah madaukakin sarki ya ce:
 (lalle salla tana hani ga alfahasha da munkari ).
Na daga cikin alamomin karban ayyuka akawai gyaruwan halaye daga wani halin zuwa halin da yafi kyau  (lalle da'a  na shiryarwa zuwa ga aljanna )
Ta daya bangaren kuma na daga cikin alamomin  tsiya da kuma rashin karban aiki akwai komawa baya zuwa ga munanan ayyuka bayan shudewan ramadana  da canjawan hali zuwa mafi muni domin shi sabo sashinsa na jan sashi (madalla da aikata kyakkyawa bayan mummuna don zata gogeta wanda yafi kyau kuma shine mutum  ya aikata kyakkyawa bayan kyakyawa,  mafi muni kuma aikata mummuna bayan kyakkyawa domin zata shafe albarkanta kuma ta gogeta . zunubi guda daya bayan tuba yafi muni akan zunubai da yawa kafin  tuba, juyawa zuwa ga munanan halaye yafi wuyan  sha'ani akan cuta watakila ma ta halakar, roki Allah tabbatuwa akan da'a har zuwa mutuwa , kuma mu nemi  tsarinsa daga juyawan zukata  da kuma lalacewa bayan gyaruwa, abin mamaki da dabbancin kaskancin sabo bayan daukaka irin na da'a, abin mamaki kuma da abkawa cikin talaucin kwadayi bayan wadatan zuci).
Ya ku musulmai
Lalle hanyoyin alheri na da yawa ina masu binsa haka kuma kofofin nasa a bude suke ina masu shigansu  lalle gaskiya a bayyane take ba mai baude wa daga gare ta sai halakakku,  to ku yi riko ya ku bayin Allah da kaso dagsa dukkan biyayya  (ya ku wadanda suka yi imani ku yi rukui kuma ku yi sujjada kuma ku bautawa ubangijinku kuma ku aikata alheri saboda ku samu babban rabo )
Kuma lalle hakuri a kan dimantan da'a da tsayuwa a kan tafarki da tabbatuwa na daga cikin mafi girman ayyukan da'a, tabbatuwa da dogewa dalili ne na ikhlasi  da  karban aiki , (mafi soyuwan  ayyuka a wurin Allah su ne wadanda aka dawwama a kansu )
(aikin manzon Allah ya kasance dimamme )
To ku tabbatu akan  da'a, ku tabbatu a kan da'a  kuma  ku tsayu a kan biyayya, to ku tsayu a kan biyayya kuma ku dawwama a kan ayyuka .
Ya ku bayin Allah !
Ku yi kwadayin karban ayyuka kuma ku kiyayi talauci da gushewa ,lalle mafi girman hasara   shine ka bawa waninka mafi girman abinda ka samu na daga lada, to wannan shi ne talauci na gaskiya.
An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara masa yarda ya ce manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :( shin kun san wanene matalauci ?  sai suka ce matalauci shine wanda bai da dirhami ko kaya sai ya ce: matalauci daga alumma ta  shine wanda zai zo ranar alkiyama da salla da azumi da zakka, ya zo ya zagi wannan kuma ya yi wa wannan kazafi kuma ya ci dukiyan wannan kuma ya zubar da jinin wannan kuma ya daki wannan  sai abawa wannan daga ayyukan shi  kyawawa  wannan ma daga ayyukan shi kyawawa in ayyukansa  kyawawa sun  kare kafin a gama masa hisabi  Sai a dauki  zunuban wannan sai a dora mishi sai a hurgashi cikin wuta )muslim ne ya rawaito

Bayin Allah!
Kuma rena sabon Allah da bushewar ido wurin keta alhurmarsa na daga cikin sababi mafi girma na tsiyacewa da hasara  da bata da tabewa, an karbo daga Sauban  Allah ya kara yarda  a gare shi cewa Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Lallai zan san wasu mutane acikin al'umata za su zo ranar alkiyama da ayuka misalin duwatsun Tihama farare  sai Allah ya maishe su  tarwatsatssen kura ,  Sauban ya ce: ya Manzon Allah siffanta mana su don kar mu kasance cikin su a halin ba mu sani ba ,  sai ya ce  ai su dinnan lalle 'yan uwan ku ne  kuma wadanda fatar ku iri daya, kuma suna riko cikin dare  kamar yadda ku ke riko,  sai dai su din wasu mutane ne da idan sun kebanta da ababen da Allah ya haramta sai su keta alfarmarsa,  sun kasance suna azumi kuma suna salla kuma suna rikan wani lokaci cikin dare  sai dai basa murakabar Allah  a lokacin yalwa,  to idan sun kebanta da abin da Allah  ya haramta sai su keta alfarmarsu  sai Allah ya ruguza ayukan su ( Kuma abin da  ba su kasance suna  zato ba daga Allah ya bayyana a gare su) .
 Idan ka kadaita a wani zamanin wata rana  to kar ka ce *
                                                     Na kadaita sai dai ka ce ina da mai mini murakaba
Kada ka zaci Allah yana gafala na wani lokaci  * 
                                                    ko kuma abin da ake boyewa   yana fakuwa a gare shi.
ku saurara  ku tsayu akan da'a wa Ubangijinku ku  amsa kiransa ku bi umarnin sa  a dukkan  matakan rayuwanku za ku samu rabauta da ganima   da walwala da tsira   ( Lalle ne wadan da suka ce '' Ubangijin mu Allah ne''     sa'annan suka daidaitu to, babu wani tsoro a kan su , kuma baza su yi bakin ciki ba  . to wadannan su ne ma'abota aljanna suna masu dauwama a cikinta sakayyan abin da suka kasance suna aikatawa  ).


                            HUDUBA NA BIYU
Lalle dukkan yabo da godiya sun tabata ga Allah  muna gode mishi kuma muna neman taimakonsa , muna neman shiriyarsa , kuma muna neman gafararsa , muna tuba zuwa gare shi , muna neman tsarin Allah daga kawunan mu da kuma munanan ayukanmu   wanda Allah ya shiryar da shi ba mai batar da shi  wanda kuma Allah ya  batar da shi babu mai shiryar da shi , na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai  yake bashi da abokin tarayya , na shaida Annabi Muhammadu bawansa ne  kuma Manzon sa ne , tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa da sahabansa  , da  wadanda suka bisu da kyautatawa har zuwa ranar sakayya da aminci tabbatacce mai yawa.

 Ya ku Musulmai  ku ji tsoron Allah   ku  gaggauta  ribatan ayukanku kafin karewar rayuwarku   ku tabbatar da maganganun ku ta hanyar ayukan ku   domin lalle hakika  rayuwar mutum  shi ne abinda  ya tafiyar da shi a cikin da'a  wa  Allah ,  lalle mai wayo shi ne wanda  ya yi hisabi  da kansa ya yi aiki don bayan mutuwarsa   shi kuma  wanda ya gajiya  shi ne wanda ya bi son ran shi ya yi ta gurace – gurace  a wurin Allah .
 Ya ku bayin Allah      watanni dukkan su lokuta ne na ibada  ko da sun  saba a wurin falala.  rayuwa dukkanin ta dama ce ta aiki da kuma da'a , ko wanne yana wayan gari  yana mai saida kansa, wani ya 'yanta ta wani kuma  ya halakata , sannan kowa ana saukake mishi abinda a ka halicce shi don shi   .
 To ya wanda ya cika a ramadana ya kyautata   bisa mafi kyawun kyautatawa , maganganun shi da ayukan shi suka    kawata,  to ka tabbatu kada ka canza a bayan shi a cikin shauwal.
 Ya wanda mutane suka tsere maka   aka barka a baya mafi yawan rayuwa ya tafi   sai zanyi , bai yin ba , dama ta Ramadan ta tsere maka baka ci riba ba , taho  , to, kofofin basu gushe ba suna bude ,  kuma tuba ana karbanta   Allah madaukakin sarki ya ce :( Ka ce , (Allah ya ce) '' ya ku bayi Na  wadan da suka yi barna  akan rayukansu ! kada ku yanke kauna   daga rahamar Allah . Lallai Allah na gafarta zunubai  gaba daya .  Lallai shi ,  shi ne mai gafara , mai jin kai .
  Ya ku  jama'ar Musulmai :
Lallai na daga  cikin hanyoyi na shiriya da kuma aikin Musdafa  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  akwai azumtar   azumi shida na watan shauwal,  an karbo daga Abu Ayuba Al'ansari Allah ya kara yarda a gare shi Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata gare shi ya ce : ( Wanda ya yi azumin Ramadana ya bi shi da guda shida a shauwal  yana dai-dai  da ya yi azumin shekara)
 Hakika Allah ya sanya  lada goma ga kyakkyawa   daya wato wata  daya na da ladan watanni goma ,   ranaku shida kuma na bayan salla na da ribin su sau goma wato kwana sittin wannan shi ne shekara guda cikakkiya .
Ba laifi , a yi azumin su a jere ko a rarrabe  kada dayan ku yayiwa kanshi rowa  na wannan kwanaki shidan ta iya yiwuwa a rubuta  shi  cikin wadanda suka yi azumin shekara,  lallai kuwa wannan babban ganima ce wanda ke sa mutum yayi kokari don ya same shi.
  Ya ku Musulmai :
  Lallai abin da 'yan ta'adda suka tashi da shi a cikin azumi kuma  a makka  a kusa da ka'aba  na daga cikin ayyuka na ta'addanci   wanda shari'a da hankali duka zai kyamace shi ,  basu kiyaye alfarmar Ramadana ba  ko alfarmar daki mai alhurma ba  ,  ko kuma alhurmar jinin muminai ba ,  ma su azumi , lallai wannan na daga cikin kaidi na makiya musulunci  da kuma bushewar ran mahara  wanda suke aikin barna a doron kasa  .
 Lallai dakin na da Ubangijin da zai kiyaye shi , hakika Allah yayi alkawarin narkon azaba   ga wanda ya keta alhurmar sa, Allah ya ce : (Lallai wadanda suka kafurta kuma suka taushe''  mutane'' daga hanyar Allah da masallaci mai alhurma     wanda muka sanya shi ga mutane alhali kuwa` mazauni a ciki da bakauye dai-dai suke kuma wanda ya yi nufin karkatar da gaskiya a cikinsa da zalunci  za mu dandana masa daga wata azaba mai radadi).
Allah  ya kiyaye  shi daga dukkan mai ketare iyaka azzalumi , maha'inci , mai laifi , shaidani abin jefewa , mai girman kai la'imi (mai dakon mummunan abu)  ya faru da musulunci ,  to, mugunyan musifa  mai kewayewa ta tabbata akansa ,Allah ya maida mishi kaidinsa a mokoshinsa , ya sanya mummunan shirinsa  ya zama  halakarwa a gare shi , kuma Allah ya yanke karshensa .
Ya ku bayin Allah:
 Lallai Allah mabuwayi da daukakaa ya umarce mu da al'amari mai girma , ku saurara! Wanda shi ne salati da aminci ga Annabi mai girma ya Allah ka yi dadin tsira da aminci da  albarka bisa  ga shugabanmu Annabin mu Muhammad.
 Ya Allah ka yarda da kalifofi shiryayyu Abubakar da Umar  da Usman da Ali da iyalai baki daya da wanda ya bi su da kyautatawa  har zuwa ranar sakayya .
 Ya Allah ka sanya mu cikin wadanda ka karbi azuminsu  da tsayuwansu da sauran ayukan su .
 Ya Allah ka maimaita mana Ramadan shekaru masu yawa   muna cikin lafiya da aminci da imani    .
Ya Allah ka tsawaita rayuwarmu ka kyautata ayukanmu  ka bamu kyakkyawan karshe .
Ya Allah ka gyara halayen Musulmai a ko ina  ya Ubangijin talikai  .
Ya Allah ka kiyaye shugabanmu kadimul haramaini sharifaini da kiyayewan ka ka ba shi kulawa da kulawarka .
 Ya Allah ka datar da mataimakin shi cikin abin da kake so kuma ka yarda da shi , ka riki makwarkwadan su  da da'a da takawa .
 Ya Allah ka datar da su cikin abinda akwai alheri ga Musulunci da musulmai  , da kuma abin da cikin shi a kwai gyaruwar gari da bayi .
Ya Allah ka azurta shi da abokan sirri na kwarai, masu nasiha wanda za su  nusar da su zuwa ga alheri kuma su taimaka musu a kanshi , ya Ubangijin talikai.
 


الخميس، 25 مايو 2017

GODIYA GA ALLAH



Hudubar juma'a na masallacin Annabi tare da sheikh Salah Bin Muhammad Al Budair
16/sha'aban/ 1438 AH
Ya ku musulmai!
Godiya hanya ce ta kari da takawa da dace.
Rabiu dan Anas yace: lallai  Allah na ambaton wanda ya ambace shi kuma yana kari ga wanda ya gode mishi kuma yana azabtar da wanda ya kafurce mishi
Na gode maka lalle godiya wata igiyace ta takawa* kuma ba dukkan wanda ka yiwa ni'ma bane yake biya.
Allah madaukakin sarki yace (kuyi godewa ni'mar Allah in kun kasance shi kadai kuke bawtawa ) 
(ku godemini kada ku kafurce mini).
An karbo daga Mu'azu dan Jabal Allah yakara yarda a gare shi yace lalle manzon Allah yayi riko  da hanun shi sai yace ya Mu'azu  wallahi ni lalle ina sonka wallahi lalle ni ina sonka, sai yace ;ina ma wasiyya ya kai Mu'az kar ka bar fadin cewa bayan kowani sallah : ya Allah ka taimakeni bisa ambatonka da godiya a gare ka da kyautata bauta a gare ka) Abu dauda ne ya fitar da shi.
Dukkan yabo da godiya naka ne ya ubangiji sa'annan dukkan yabo naka ne muddin baki na furuci, falalarka ta kebance ni kuma ta game, daga gun ka ne gani da ji da dandano,  da shakan ga wuni ma haske ga dare mai duhu ga kuma dutse mai tudu da tsirrai wanda suke tsaye akan makyangamansu da wadanda suke akasin haka.
Yaku musulmai
Lalle ku kuna rayuwa a cikin aminci mai yawa da arziki mai yalwa da rayuwa na jin dadi da ci da sha, ga wasu a kewayenku matsanancin yunwa na kashe su ga mutuwa na bi ta kansu a kashe   akamasu amasayin bayi a riki matayensu kuyangi suna kuma fama da bala'i da annoba suna kuma fiskanta tsadan abinci ga kuma fitar da su da aka yi daga gidajensu ba abin da za kagani sai uwa cikin yunwa yara cikin  kuka ga alummu raunuka  ya illantasu to ku kiyaye wasa da ni'mar da Allah ya yi muku kar ni'man ya mantar da ku godiyan Allah a gare ku, ku  yi dubi da abin da Ubangijinku ya yalwata a gareku na daga ni'momi ku san hakkin shi ne mai muku ni'man
Ku kasan ce daga cikin wadanda suka jawu gare shi ta hanyar godiya bisa ga ni'imominsa,
Kar kuyi amfani da kyauta  da ya muku cikin saba masa kada shaidanu su rudekukada makiyanku su yaudareku da bata ,karku bayyana sabo bayan samuwan arziki da aminci da bayani da baiwa,ku kyautata muamala da ni'imomi, ku kiyaye ni'imomin da ke tare da ku, sai kuma ku nemi ni'imomin da kuka rasa ,ku nemi dawwamar kyautar Allah da karamcinsa ni'ima ba ta juya baya idan ta fiskanto, ba a dauke ta bayan ta sauka ba a dauke wata karama bayan an bada ta ,sai dai  kasancewarta kyauta da ba a gode ba ,ko sakamakon kusakurai da aka aikata kuma ita ni'ima idan an yi godiya sai ta tabbata, idan an butulce saita guje.
ya wanda ke tafiya akan koyin kafirci ya sanya kafarsa cikin tawagar matafiya na kafirci da fasikanci da sharri, abin da ya rudeka shine hakurin Allah sararawarsa harka juya baya da fiskanka ka yi watsi da hakkin Allah.
Ya kai dan' adam lallai ka gafala,  sai  kace ba zaka kare ba ko ba zaka halaka, ba ya wanda yayi sharri da dagawa da sabo da fasikanci da fajirci ,shin ko kana zaton kyautar bata halake ba ne, ko ni'imar ba a amsarta ne,dako da jinkiri da rashin gajiyawa ukuba ke diban ka, ka gajarta daga barnarka Allah bai taba kama mutane ba face a yayin da suke mayensu suka shagaltu cikin rudunsu da walwalansu, sau da yawa Allah kan bawa mutane arziki da yalwa da ni'ima, sai suka riki ni'imar Allah tamkar wani tsani ne da zasu haura su tsallaka zuwa ga saba mishi suka rike shi matakala zuwaga abin da Allah ya hana sai suka zaci wannan kyautar da ni'ima wata girmamawa ce da daukaka da darajanta su kan saura da fifitasu da zabansu basu san hakan ba wani abu bane sai daurin talala, sau barkatai akan yiwa wasu daurin talala ta hanyar ihsani, sau da yawa wani kan fitinu in an yabe shi, wani kuma ya rudu in Allah suturce shi bai tona masa asiri ba.
 Ya ku musulmi!
 ka kiyaye fadawa cikin sabon Allah da nuta a cikinsa, da kwankwada daga gare shi da yin sakaci gurin keta laduba, da yin karan tsaye ga tauhidi da sharia da addini, ku kiyaye daga mataimakan shaidan da abokansa dake kokarin batar da ku ta hanyar yaudara kuyi nesa da mummunar fahimtarsu da bataccen tafarkinsu, ku kauda kai daga kiranye kiranyesu, ku kaurace wa tawagarsu, ku wofantar da hanyarsu  ku shakala yinsu, kar kubi soye soyen rayu kansu da sha'awe sha'awensu, kar kuyi biyayya ga mai zunubi ko mai yawan sabo mai yawan kafurci, (kada ka bi wanda muka rabkanar da zuciyarsa ga barin  ambatonmu,alhali kuwa al'amarinsa ya kasance yin barna)
( ku kauda kai daga wanda ya juya bayadaga ambatommu bai nufin komai sai rayuwar duniya)
Makhlad dan Husain yace: An kasance ana cewa : (Godiya shi ne barin sabo)
Mai lura mai hankali yakan banbance tsakanin tsaki da tsakuwa, kuma ya rabe tsakanin zare da abawa domin rogo ba kitse bane.
Yaku musulmai!
 ku janyowa kanku kari ta hanyar  godiya daga kyauta kuyi nesa daga sifa ta butulci da afkawa ga sabo, kuyi nesa daga abin da aka haramta, kar kuyi sabuban da za su kai ku ga fadawa cikinta, don godiya ga Allah bisa ga ni'imominsa masu yawa  da ya baku, duk wanda ya tsallaka halall ya fada ga haram to ya ketare iyaka kuma yayi zalunci,
 Allah yace:(wadancan iyakokin Allah ne, sabo da haka kada ku ketare su, to duk wanda ke ketare iyakokin Allah wadan nan sune azzalumai)
 yaku musulmai ku kiyaye yin dabaru don bata hukunce- hukunce na sharia don ku isa zuwa ga abubuwa da aka haramta munana, don aikata hakan baya cikin aikin masu tauhidi masu godiya, aa yana cikin sifofi na fasikai batattu ) Al hiyal wato dabaru jam'i ne na dabara hanya ce ta boye da zata isar dakai ga manufa.
Imamun Nasafi yace acikin Al kafi daga Muhammad dan Alhasan yace: Baya cikin dabi'ar mumini gujewa hukunce- hukuncen Allah ta hanyar dabaru da zasu kai mutum ga bata gaskiya .
 Allah ya sanya ni da ku cikin masu godiya a halin yalwa ya tabbatar da mu akan addininsa  ba tare da baudewa ba .
HUDUBA TA BIYU:-
Ya ku Musulmai :  Yarda da kadan sifa ce ta masu godiya,  ba sa rena ni'imar Allah  ko da ta karanta,  a duk yayin da wani abu na al'amarin duniya ya wuyata a gare su,  sai su wadatu da abin da ya ke koma bayansa , kuma su yarda ,  hakika ya daukaka duk wanda ya yi wadatan zuci ,  kuma ya kaskanta duk wanda ya sa kwadayi,   daga cikin mutane akwai wanda baya yarda da abin da Allah ya kasa mishi na  arziki ,  za ka ganshi  yana fushi yana raki  yana kuma fatan abin da ke hanun wanin shi na daga matsayi da  dukiya da hali ,  

Yaro na neman girma  *   tsoho kuwa na neman  ya koma yaro
 Me zaman banza na neman aiki   *  Ma'abocin aiki kuma ya kosa
Ma'aboci dukiya kuma na cikin gajiya  *  Matalauci kuma na cikin wahala
Mai yara kuma na cikin bacin rai   *  mai neman su kuma gashinan ya jikkata
 Mutumin da aka yi galaba akan shi kuma yana cikin  tsiya  *  wanda  kuma ya yi nasara shi kuma bai da  hutu
Zai rika neman daukaka  cikin tsoron hasara   *  idan ya yi nasara da ita kuma  sai jikin sa ya mutu .
Arziki kaso ne daga Allah  wanda ya fito bisa hikima  da gudanarwa da ilimi game da halin bayi,  kada ku yi hasada, kada ku yi fatan abin da Allah ya fifita wasunku akan wasu da shi  , kada dayanku ya yi burin  dukiyan wanin shi  da iyalan shi,   ku roka mishi Allah albarka , kuma  ku roki Allah daga taskar sa da bata karewa , a cikin mutane akwai wanda yake rokan mutane don ya bunkasa dukiyan shi, zai rika bijiro musu a masallatayya da kuma wuraren tarurruka  ,   da kuma lokuta masu daraja  kamar juma'a  da ramadan,  watakila ma ya rike dan yaro  ya koya mishi kaskanci da roko  domin neman tausayin mutane   da kuma neman yawaita kyautan su .
An karbo daga Abu Huraira  Allah ya kara yarda a gare  shi ya ce :  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :''  Wanda ya roki mutane dukiyan su  don neman ya yi kudi  to hakika garwashin wuta yake rokan su  to ya roki dan kadan ko da yawa  '' . Muslim ne ya rawaito shi.
 Ya ku Musulmai :
 Almabazzaranci da dukiya  da ciyar da shi a gurin da ba hakkinsa ba   hakanan a wurin alfahari da neman suna,  da tinkaho  da shi   kishiyan godiya ne .
Mujahid ya ce:  da mutum zai ciyar da dukiyan shi gaba daya a cikin hakki , to, da bai zama  almabazzaranci ba  .
 Ciyar da abinci  falala ne mai girma  da kuma ciyar da masu azumi abincin buda baki   a Ramadan  kusanci ne mai daraja , kuma  ibada ne mai girma  da ya dace  duk wani  wanda ya yi dace   ya yi kwadayin ta,
 Muna gargadi game da barna cikin fadada  shinfidar cin abinci  ba tare da bukata ba      da zuba dabino da biredi da abinci ba tare da iyaka ba,  wanda karshe makomansu ya zama abin jefarwa a wurin tara shara , ku tuna 'yan uwanku talakawa da wadanda suke cikin jarabawa a kasar fari   , da tsananin talauci  da yunwa  da  yake -yake  .
Ku nemi abin da yake dai-dai, ku kusanto , ku yi bishara, kuma ku yi fatan alheri, lallai Allah baya sarayar da ladan wanda ya kyautata aiki,
 lalle Allah bai lalata ladan masu kyautatawa.            

MARABA DA RAMADAN

HUDUBAR  JUMA'A NA MASALLACIN  ANNABI TARE DA SHAIKH ALIYU DAN  ABDURRAHMAN AL, HUZAIFI  NA 30/8/ 1438
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai
  Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Mabuwayi mai yawan gafara yana halittan abin da ya so kuma ya zaba abin da ya so , mai juya dare da rana   lallai  cikin haka  akwai abun lura  ga masu basira, ina kyautata  yabo ga Ubangiji na kuma ina gode mishi  ina tuba zuwa gare shi  ina nemar   gafarar sa   na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya  tilo  mai rinjaye   na shaida Annabin mu  kuma shugabanmu Muhammad bawansa ne kuma Manzon sa ne zababbe  ya Allah ka yi dadin tsira da aminci da albarka  bisa ga bawanka kuma Manzon ka Muhammad da iyalansa  da sahabbansa masu biyayya .
Bayan haka ku ji tsoron Allah Madaukaki  ku mishi biyayya   ba wanda  zai tsiyata ta hanyar   yiwa Allah da'a  ,  haka kuma ba wanda zai rabauta ta hanyar sabawa Allah  .
 Ya ku bayin Allah !  
Ku aminta da alkawarin Allah   bisa ga kyawawan ayyuka , ku yi kokari  don samun kyakkyawan karshe da makoma   to,  Ubangijinku mai yawan godiya ne  kuma masani   mawadaci ne kuma mai karamci  yana kira don a nemi kusanci zuwa gare shi   da abinda  ya ke so ,  kuma shi mawadaci ne  ga barin da'an bayi   yana muku gargadi daga sabo  a halin kuwa ba zai cutar da shi ba,   wanda ya tsayu akan zunubai masu halakarwa  Allah madaukakin sarki ya ce :  (  Wanda ya yi aiki na kwarai to, don kansa wanda  ya yi munana to, (alhaki)  a kansa Ubangijinka ba mai zalunci ba ne ga bayi  ).
 Kuma Allah madaukakin sarki ya ce : (  Kuma duk wanda ya juya baya akan diga-digansa  to, ba zai cutar da Allah da komai ba  kuma Allah yana sakanyawa masu godiya  ).
 Ku kasance ya ku mutane cikin tsoron azaban Allah domin baya sauka ga wani face ya halaka shi , haka kuma baya kewaya wani wanda ya gafala face ya azabtar da shi   ya tsiyata shi  Allah madaukakin sarki ya ce :  ( Kuma wanda hushi na ya sauka akansa to lallai ne ya fadi )
 Abun mamaki ga mutumin da yake aiki don duniya ya manta da lahira , to, duniya akan same ta ta hanyar  aiki hakanan akan same ta ba ta hanyar  aiki ba ga wanda ya gaza yin aikin,  amma ita lahira da  ni'imarta   ba a riskanta sai da aiki,  Allah madaukakin sarki ya ce :
( Kuma wancan ita ce  Aljannar  wannan da aka  gadar da ku ita   sabo da abin da ku ka kasance kuna aikatawa).
Ya ku Musulmai :
 Ga wani lokaci mai girma ya sauka a gare ku , kuma wata  mai karamci  ,  albarkatu na sauka a cikinta da alheri , kuma ana kankare zunubai a cikinta  watan ramadana wanda Allah ya sanya mishi falala    . An karbo daga Abu Sa'id Allah ya kara mishi yarda ya  ce: daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Jagoran watanni shi ne watan Ramadana  mafi girman al'hurma kuma shi ne watan zulhijja ) Albazzar ne ya rawaito shi .
  Allah madaukakin sarki ya ce : ( watan ramadana da aka saukar da alkur'ani a cikinta shiriya ne ga mutane da hujjoji bayyanannu  na shiriya  da kuma rarrabewa )  lokaci na Ramadan lokaci ne mai albarka da Allah ya tattaro a cikinsa  ibadoji na azumi tare da salla da zakka  ga wanda ya ke yin zakka a cikinsa  , ga kuma karamin hajji acikinta , wanda  shi ne umra  da kuma yawaita karatun Alkur'ani da nau'uka  daban –daban    na ambaton Allah  da umarni da kyakkyawa da hani da mummuna    da sauran ayuka na da'a ga wanda ya ke son yawaita  neman  kusanci   to, sabuba na alherin cikin sa na da yawa kuma a bayyane suke  sabuban sharri kuma a ramadana dan kadanne  ,  ana shiga tsakanin shaidanu da  abin da suke so na barna  da batar da  Musulmi  da  kange shi daga da'a.  An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi daga Annabi  tisra da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya ce : (  Idan Ramadana ya zo ana bubbude kofofin Aljanna a rurrufe  kofofin jahannama a daure shaidanu cikin mari ) Buhari ne ya rawaito da  Muslim
Daga cikin nau'uka na lada da  ni'ima a cikin Aljanna,  akwai irin nau'ukan da'a da ibada da suka dace da su anan duniya    , to dukkan da'a na  da ladan shi kuma  da ni'ima da ya dace da shi, Allah madaukakin sarki ya ce: Ana ce musu ( Ku ci  kuma ku sha a cikin ni'ima sabo da abin da ku ka gabatar  a cikin kwanukan da suka shige )
An karbo daga sahal Dan Sa'ad  Allah ya kara yarda  a gare shi  ya ce : Daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbat a gare  shi ya ce : (  A cikin aljanna a kwai kofan da ake kira arrayanu za a kira masu azumi ta gun shi , duk wanda ya kasance acikin masu azumi zai shige shi, wanda ya shige shi ba zai ji kishi ba har abada ,  ) Buhari ne ya rawaito shi
  Mafi girman girmamawa ga wanda ya shiga aljanna shi ne dubi zuwa ga fiskan Ubangiji mai girma    wanda shi din sakayya ne ga kyautatawa  da musulmi ya yi na bautawa Allah kamar yana ganin shi , Allah Madaukakin sarki yace :( Wadanda suka kyautata yi suna da abu mai kyau kuma suna da kari) Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya fassara kari da kallo zuwa ga fiskar Allah Mai girma, kamar yadda ya zo a hadisin salman Allah kara yarda a gare shi, wanda Muslim ya rawaito, To sakayyar na daga irin jinsin aikin da mutum ya yi, kamar yadda nau'i na azaba ma ya ta'allaka ne da irin sabo da aka yi, To cin itaciyar zakkumi  da shan tafasasshen ruwa sakayya ne ga cin riba da haram, da shan abubuwan maye da hodar iblis, kwarara ruwan zafi a kai sakayya ne na girman kai da jiji da kai daga bin shariar Allah da kin jawuwa a tafarkinsa,   Allah Madaukakin sarki yace: ( Lalle itaciyar zakkum. Ita ce abincin mai laifi. Kamar narkakken kwalta, yana tafasa a cikin cikuna. Kamar tafasar ruwan zafi.ku kama shi sa'annan ku fizge shi zuwa ga tsakiyar jahim. Sa'annan ku zuba a kansa daga azabar ruwan zafi. Ka dandana lalle kai ne! kai ne mabuwayi mai girma ) to sakayya na daga ginsin aiki  a duniya da lahira.
Albishirinku ya ku musulmai da albishirin manzon Allah ya yi ga sahabbansa game da ramadana domin hakika yakasance yana musu albishir da shi a karshen sha'ban don su shirya, to ku fiskanci wannan wata da dukkan alheri  kuma ku mishi dukkan tattali, ku fiskance shi da neman lada da farin ciki mai tsanani , Allah ya kai ku zuwa gareshi Allah madaukakin sarki yace :(ka ce da falalar Allah da rahamansa sai su yi farin ciki da wannan shi ne mafi alheri daga abin da suke tarawa ) ku fiskance shi da tuba daga dukka zunubai don Allah ya goge muku abin da ya gabata na daga zunubai da shi ku fiskance shi da maida abinda aka zalunta ga ma'botansa  don  Ubangiginka ya kiyaye maka kyawawa ya kankare maka munana ka tuna akwai ranar da zai zo ba zaka riski ramadan ba, ka kasance mai shirya wa mutuwa da kuma  musibunta,  ka kiyaye azumin ka daga wasa da batsa  da cin nama dayanku da annamimanci da magana mara kyau da ayyukan sabo da kallo zuwa ga abubuwan da aka haramta ka kiyaye zuciyarka daga munanan sake- sake,  An karbo daga Ibnu umar Allah ya kara yarda a gare su  daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a ga re shi ya ce :( Ta iya yiyuwa wani mai azumin kason shi daga azumin sa shine yunwa da kishin ruwa, ta iya yiwuwa wani mai tsayuwan dare rabonshi na tsayuwansa shine hana idonshi barci ) Addabarani ya rawaito shi a cikin littafinshi Alkabir, Imamu Al munziri  ya ce isnadin ba shi da laifi,
An karbo daga Abu huraira  Allah ya kara yarda a gare shi ya ce:Manzon Allah tsira da  amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(Duk wanda bai bar fadin karya ba da aiki da shi to Allah bai da bukatan barin  abincinsa  da abin shan sa ) Bukhari ne ya rawaito da Abu Dawuda da Tirmizi.
 An karbo daga Abu Ubaida Allah ya kara yarda a gare shi Annabi tsira da  amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce  (Azumi garkuwa ne) wato kariya ne muddin ba' keta shi ba  )Nasa'I ne ya rawaito da dabrani a Al-ausad  ya kara da :sai aka ce me ya  ke keta ta  sai ya ce da karya da cin naman wani ,
Musulmi yayi kokarin  girmama ladan azumin shi  ta hanyar yawaita ayyukan da'a da neman kusanci a ramadan, na daga tilawan alkura'ani da yawan zikiri da istigfari da yin  salati ga Annabi  tsira da  amincin Allah su tabbata a gare shi da sadaka da kyauta don neman yardan Allah da nau'uka na kyautata wa kamar ilmantarwa da umarni da kyakkyawa da kwadaitar wa zuwa gare shi da hani daga sharri da gargadi game da shi .don yawan da'a tare da yin azumi, yana kara ladar azumi, wanda ya shayar da mai azumi yana da lada kwatan kwacin ladansa ba tare da an tawaye wani abu ba na daga ladansa ba.
 kada ka yi sakaci ya kai musulmi  game da sallan tarawihi da tsayuwan dare musamman kokari na neman lailatul  kadri a goman karshe,  azumin ramadana kankara ne ga zunubai  an karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce manzon Allah tsira da  amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(Duk wanda ya yi azumin ramadana cikin imani da neman lada to za a gafarta  masa abin da ya gabata daga zunubansa  )Buhari da Muslim ne suka rawaito.
  An karbo daga Ubada dan Samit Allah ya kara yarda a gare shi Annabi  tsira da  amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce game da lailatu al kadri (ku neme shi a goman karshe wanda yayi tsayuwan shi yana mai imani da neman lada sannan yayi dace da shi za a gafarta mishi abin da ya gabata na daga zunuban shi da abin da ya jinkirta ) Ahmad ne ya rawaito da Addabarani a Al kabir.
Ka kirdadi  salla cikin jam'i , kai musulmi  Allah zai kiyaye bawa kuma ya jibinci alamarin shi  kuma ya datar da shi a alamuran shi, wanda ya daidaitar da sallah to duniyarsa za ta tafi hakanan kuma  da  lahirarsa  zai ji dadi a duniya jin dadi irin na dabbobi sannan kuma a ce da shi ranar alkiyama shiga wuta tare da masu shiga.Ya zo a hadisi wanda yayi sallar ishai acikin jama' kamar  ya yi tsayuwan rabin  dare ne, sannan kuma wanda yayi sallar asuba acikin jama'a  kamar wanda yayi tsayuwan dare ne dukaninsa. )Muslim ne ya rawaito a hadisin Usmana dan affan Allah ya kara masa yarda,
Na daga cikin abin da ke girmama hasara kuma yake haramta wa bawa alheri yin azumi da barin salla  ko kuma barin wani sashi daga gare ta.
Na daga cikin tafiyar da rayuwa da bata shi  kwana  da hana ido barci akan wasa ko kuma bibiyan yanar gizo na  barna da kuma bin fina finai masu cutarwa  da zubar da mutunci da bata tarbiyya da halaye,hasara da tabewa na girmama idan mutun ya rinka shagaltuwa da wadannan abubuwa a wannan wata, daga ayyuka na alheri Allah madaukakin sarki ya ce (ku yi gaggawa zuwa ga meman gafara daga ubangijinku da wata aljanna wanda fadinta (daidaida ) sammai da kasa ne an yi tattalinta domin masu takawa )*(wadanda suke ciyarwa a cikin sauki da tsanani kuma suke masu hadiyewar fushi kuma masu yafewa mutane laifi ,kuma Allah yana son masu kyautatawa  ) Allah ya sa mini albarka ni da ku a alkura'ni mai girma   
Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah mai shiryarwa zuwa ga hanya madaidaiciya. Ma'aboci falala mai girma, yana baiwarsa ga wanda ya so da falalarsa, ya kuma  hana wanda ya so bisa adalcinsa, shi mabuwayi ne Mai hikima ina kyawtata yabo ga ubangiji na kuma ina gode mishi  ina mai tuba zuwa gare shi ina neman gafararsa na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya Mai iko kuma masani na shaida cewa    Annabinmu kuma shugabanmu  muhammad bawansa ne kuma manzonsa ne,  ma'abocin sharia' mai haske da shiriya mikakkiya ya Allah ka yi salati da sallama da albarka bisa ga bawanka kuma manzonka muhammad da iyalansa da sahabbansa wanda suka siffantu da dukkan dabiu na karamci.
Bayan haka :
    Ku ji tsoron Allah yadda ya dace a ji tsoronsa kuma kuyi riko da igiya mai karfi na musulunci, Ya ku bayin Allah  ko sanya wa kowani zunubi  tuba hakika masu tuba sun rabauta masu dogewa a kan zunubai sun  yi hasara Allah madaukaki ya ce: (ku tuba zuwa ga Allah ya ku mu'minai  ko za ku za ku rabauta).  wannan wata lokaci ne na tuba kuma na daga cikin  mafi girman zunubai da ya  wajaba atuba daga gareshi akwai shan taba  ka tsarkake bakinka ya kai musulmi daga shan shi,  ka tsarkake bakinka daga gare shi don ambaton Allah da karatun alkura'ni ka dadada kamshinka ga salihai masu zama da kai da mala'ku masu rubutu domin shan taba yana kusanto da shaidanu kuma yana lalata jini kuma yana jawo  cututtuka masu halakarwa, kuma yana gajarta rayuwa, kuma  ka'idoji na shari' na  haramta shi,  ka sani ya kai musulmi ya wajaba ka kwana  da niya tun daga dare, An karbo daga Hafsa Allah ya kara yarda agareta daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yace :  (  wanda bai kulla niyarsaba tun daga dare na azumi  to babu azumi agareshi ) Abu dawda da tirmizi da nasa'I  da ibnu majah su ka rawaito shi. Ya zo a hadisi dukk wanda ya sha azumi na ramadana ba tare da uzuri ba ba zai iya biyansa ba ko da ya azumci zamani baki daya.To Allah ya tsare mu. lalle Allah da mala'kunsa na yin salati ga Annabi ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi da aminci tabbatacce .
  


الخميس، 27 أبريل 2017

MIKA WUYA GA ALLAH

HUDUBAR JUMA'A TA MASALLACIN ANNABI  2 GA SHA'ABAN 1438 AH NA SHAIKH HUSAINI AL- ASSHAIK.
HUDUBAR FARKO
A LOKACIN DA DUNIYA KE KUSA TA ZAMA TA HADE GU GUDA SAKAMAKON BUNKASA NA ILIMI DA CI GABA DA DAN ADAM KE SAMU,SAI GA FANDAREWA NA MANHAJA NA YAWAITA DA FITINTINU MASU HADARI,WADANDA KE SHAFAR ADDINI  NA GASKIYA DA KYAWAWAN DABIU, HAKA NE DAN ADAM YAKE DA ZARAN YA SAMU WATA DAMA DON FADIN ALBARKACIN BAKINSA DA TUNANINSA DA MANHAJARSA.
KU SAURARA! LALLE MUSULMAI A YAU SUNA CIKIN BUKATAR LAFIYAYYEN MA'AUNI DA ZASU BANBANCE TSAKANIN ABU MAI INGANCI DA MARA KYAU, TO AI SUNA DA WASU TABBATATUN ABUBUWA DAGA UBANGIJI DA WA SU KA'IDOJI DAGA ALLAH WADANDA ZAI TSALLAKA DASU ZUWA BAKIN GABA NA TSIRA DAGA DUKKAN WATA FIKIRA MAI ILLA DA KUMA FANDARARREN TSARI,WANDA ZAI HASKAKA MUSU HANYA TA MUSULUNCI DA MIKAKKAR MANHAJI (YA KU MUTANE HAKIKA WATA HUJJA TA ZO MUKU DAGA UBANGIJINKU, MUN SAUKAR MUKU DA HASKE BAYYANANNE, TO AMMA WADANDA SUKA YI IMANI DA ALLAH KUMA SUKA KANKAME SHI,TO ZAI SHIGAR DA SU CIKIN WATA RAHAMA DAGA GARE SHI DA FALALA YA SHIRYAR DA SU ZUWA GARE SHI TAFARKI MIKAKKE.)
RAYUWA TA TSIYATA BAZA TA KAU BA, HAKA BA ZAA FITA DAGA WAHALHALU BA A DUNIYA DA LAHIRA  HAR SAI MUTANE SUN MIKA WUYA GA MANHAJIN LITTAFIN UBANGIJINSU,SU KUMA MIKA WUYA GA KOYARWAR ANNABINSU DA AKA TURO MUSU.
 LALLE BABBAN GINSHIKI NA GYARUWA DA RABAUTAR AL'UMAR MUSULMAI, DAIDAIKUN SU DA GABADAYANSU, SHI NE MIKA WUYA NA GABADAYA GA SHARIAR ALLAH MABUWAYI DA DAUKAKA.A KYALE DUK WANI ABU DA KAI KOMO A MIKA WUYA GA HUKUNCIN ALLAH MAI GIRMA DA DAUKAKA DA NA MANZONSA TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI.
LALLE WAJIBIN MUSULMAI SHINE GIRMAMA UMARNIN ALLAH MAI GIRMA DA DAUKAKA, DA MURAKABARSA A BOYE DA BAYYANE, CIKIN TSANANI DA SAUKI, CIKIN ABIN DA RAI KE SO DA WANDA BAI SO. CIKIN YANAYI NA CUTA DA AKASINTA, DA LOKACIN YALWA DA LOKACIN KUNCI, ALLAH MADAUKAKIN SARKI YA CE, (BAI DACEWA GA MUMINI KO MUMINA IN ALLAH YA YI HUKUNCI DA MANZONSA NA WANI UMARNI DA SU KASANCE SUNA DA ZABI CIKIN UMARNINSU, DUK MAI SABA WA ALLAH DA MANZONSA TO YA BATA BATA BAYYANANNE).
WANNAN AYAR MAI GIRMA TANA KAFA MANA WATA KA'IDA NA ASALI WANDA YA WAJABA TA KASANCE TSARI NE GA RAYUWAR MUSULMAI, KUMA YA ZAUNA CIKIN ZUKATARSU, KUMA SU ZARTAR DA SHI A WAKI'INSU, LALLE SHI DIN NAN TUSHE NE MAI GIRMA WANDA KE WAJABTAWA MAI KIWO DA WANDA AKE KIWATA, GA DAIDAIKU DA KUMA AL'UMA DA SU AMSA KIRAN UMARNIN ALLAH MAI GIRMA DA DAUKAKA, DA NA MANZON ALLAH TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI, A DUKKAN YANAYI  DA SAURAN BANGARORI,DA FAGAGE NA RAYUWA DA KAI KOMO NA YAU DA KULLUM.
WANNAN AYAR TANA TABBATAR DA WATA KA'IDA MAI GIRMA, DA KE NUNA NA DAGA CIKIN ABIN DA KE HUKUNTA IMANI, DA SIFFARSA DA RUKUNANSA AKWAI GAGGAWA ZUWA GA NEMAN YARDAR ALLAH MABUWAYI DA DAUKAKA,DA NEMAN SHIRIYA DAGA KOYARWAR MANZON ALLAH TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI,DA RUSUNAWA DA SALLAMAWA DA MIKA WUYA GA HUKUNCIN ALLAH DA HUKUNCIN MANZON ALLAH TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI A DUKKAN WANI SHA'ANI NA DUNIYA DA ADDINI, HAR YA ZAMA BAWA BAI DA WANI ZABI KO GANIN DAMA WURIN ZARTAR DA UMARNIN ALLAH MAI GIRMA DA DAUKAKA DA UMARNIN MANZONSA DUK YANDA RAI DA SHA'AWE SHA'AWE SUKA KARKATA ZUWA GA WANINSA, NA DAGA CIKIN ABIN DA IMANI KE LIZIMTAWA AL'UMA MUSULMAI SU RAYU KARKASHIN INUWA NA SHARI'A MAI TSARKI, KUMA YA ZAME ABIN DA RANSA KE SO DA ABIN DA ZAI FISKANTA SHI NE BIYE WA ABIN DA YA ZO A LITTAFIN ALLAH MAI TSARKI DA SUNNAR MANZONSA  A HARKOKINSA NA YAU DA KULLUM DA DUK WANI KAI KOMO NASHI.
WANNAN SHI NE TAFARKIN MUTANEN KWARAI MASU RABAUTA, KUMA TAFARKIN MASU TAKAWA DA CIN NASARA.
IMAMU AHMAD YA RAWAITO CEWA ANNABI TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI YA NEMAWA JULAIBIB WATA MACE DAGA CIKIN ANSAR A GUN MAHAIFINTA, YA ZO A KISSAR MAHAIFIYARTA TACE; ANNABI YA RASA WANDA ZAI NEMAWA SAI JULAIBIB TO NA RANTSE DA ALLAH BA ZA MU AURA MISHI BA, SAI YARINYAR TA CE :SO KU KE KU KI BIN UMARNIN ANNABI BAYAN  SHI YA YARDA DA SHI GARE KU TO KU AURA MISHI, SAI ANNABI YA MATA ADU'A YANA CEWA :YA ALLAH KA KWARARA ALHERI GARE TA KWARARAWA, KADA KA SANYA MUSU WAHALA A RAYUWA, TO SAI TA ZAMA BA WATA MACE CIKIN ANSAR DA TA KAI TA CIYARWA.
YA KU MUSULMAI!
LALLE NA DAGA CIKIN ALAMOMI NA IMANI INGANTACCE: TSAYAWA KAN DOKOKI NA ALLAH DA LAZIMTAR BIN SUNNAR MANZON ALLAH TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI DA GIRMAMA TARIHINSA DA TAFIYA AKAN KOYARWARSA, YA ZO DAGA DA'WUS KAN CEWA YA TAMBAYI ABDULLAHI DAN ABBAS GAME DA RAKA'OI BIYU BAYAN LA'ASAR SAI YA HANE SHI, SAI IBNU ABBAS YA KARANTA WANNAN AYAR (BAI DACE BA GA MUMINI KO MUMINA BA). AN KARBO DAGA SALIM DAN ABDULLAH KAN ABDULLAHI DAN UMAR YA CE: NA JI MANZON ALLAH TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI YANA CEWA : (KAR KU HANA MATAYENKU ZUWA MASALLACI IDAN SUN NEMI IZININKU, SAI BILAL DAN ABDULLAHI YA CE ; ( WALLAHI ZA MU HANA SU. SAI ABDULLAHI YA FISKANTO YA MISHI MUMMUNAR ZAGI BAN TABA JI YA YI WA WANI IRIN SHI BA. YA CE INA BAKA LABARIN ANNABI YA CE KANA CEWA ZAMU HANA SU). MUSLIM NE YA RAWAITO.
A RAYUWAR SAHABBAI DA TABI'AI AKWAI IRIN WANNAN  DA YAWA WURIN GIRMAMA UMARNIN ALLAH DA UMARNIN MANZON ALLAH TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI DA KUMA DIMANTAR BIN UMARNINSU DA KIYAYE SABA MUSU.
YA 'YANUWA MUSULMAI!
LALLE MAGABATA NA WANNAN AL'UMA SUN FI KOWA TSANANIN TSAYUWA DON TUNKUDE DUNIYA DA KYALA KYALANTA DA RABAUTANTA DA NASARARTA, DA AMINCINTA DA ZAMAN LAFIYARTA.
AMMA LOKACIN DA SUKA TSAYA INDA ALLAH YA YI UMARNI, SUKA ZABA WA KANSU ABIN DA SHARIAR ALLAH TA ZABA MUSU SAI SUKA RABAUTA DA ALHERIN DUNIYA DA WALWALARTA DA YARDAN ALLAH A LAHIRA.
AN KARBO DAGA A'ISHA ALLAH KARA YARDA A GARE TA TA CE:( ALLAH YA JIKAN MATAYEN MUHAJIRAN FARKO YAYIN DA ALLAH YA SAUKAR DA :( KUMA SU YI LULLUBI DA MAYAFANSU AKAN ALJIHOHINSU) SAI SUKA TSAGA SAMAN MAYAFANSU SUKA YI HIJABI DA SU.) BUHARI NE YA RAWAITO SHI MUALLAKI DA ABU DAUDA DA SANADINSA INGANTACCE.  
IBNU HAJAR YACE : KWARJALLAYENSU, JAM'I NE NA KWARJALLE WATO ZANI DA SUKE DAURAWA, FADINSA : SUKA SA HIJABI WATO SUKA RUFE FISKANSU.
ABIN DA YAKE WAJIBI GA DUKKAN MUSULMI YA TSAYA GA SHARIAR ALLAH, KUMA YA HAKIMANTAR DA DOKOKIN ALLAH MADAUKAKI DA BUWAYA CIKIN ABINDA RAI KE SO KO YAKE SHA'AWA KO YAKE KWADAYINSA, IDAN RANSA YA KIRAYE SHI ZUWA GA NEMAN WANI ABU NA NEMAN DUNIYA KO WATA SHA'AWA TA JIKI TO YA YI DUBI ZUWA GA HUKUNCIN HAKAN KO YA TAFI DAIDAI DA MANHAJI NA SHARIA MAI INGANCI, KUMA YA YI GARGADI GA RANSA MAI YAWAN UMARNI DA MUMMUNA, YA NESACI RUDUWA DA WANNAN DUNIYA MAI KAREWA MAI GUSHEWA, (ABIN DA KE GUN ALLAH YA FI ALHERI KUMA YA FI WANZUWA, ASE BA ZAKU HANKALTA BA).
YAYIN DA AKA HARAMTA GIYA HARAMTAWA NA KARSHE KWATA KWATA DA FADIN SA MADAUKAKI (TO SHIN KU MASU HANUWA NE?)  A KA KARANTA WA UMAR SAI YA CE: MUN HANU MUN HANU, SAHABBAI SUKA RINKA SHEKAR DA GIYA A KWARARO SUKA FASA TUKWANENTA SUKA HANU DAGA GARE TA.
TO YA KU JAMA'AR MUSULMAI!
KU YI RIKO DA ADDININKU, KU GABATAR DA SHI AKA KO WANI ABU MAI TSADA DA KIMA SAI KU SAMU RIBA DA WALWALA KU RABAUTA (DUK WANDA KE YI WA ALLAH  DA MANZONSA BIYAYYA TO HAKIKA YA RABAUTA RABAUTA MAI GIRMA).
HUDUBA TA BIYU
YA JAMA'AR MUSULMAI!
DUK MUTUMIN DA BAI BI SHARIAR ALLAH BA KUMA YA BI SON RANSA TO HAKIKA YA ZAME DAGA HANYA YA FANDARE DAGA TAFARKIN DAIDAI MIKAKKE YA  KUMA FADA CIKIN BATA NA NESA, KUMA YA BAUDE BAUDEWA MAI ZURFI.
ALLAH MADAUKAKIN SARKI YA CE BAYAN YA AMBACI SHANIN MUMINAI  (BAI DACEWA GA MUMINI KO MUMINA IN ALLAH YA YI HUKUNCI DA MANZONSA NA WANI UMARNI DA SU KASANCE SUNA DA ZABI CIKIN UMARNINSU, DUK MAI SABA WA ALLAH DA MANZONSA TO YA BATA BATA BAYYANANNE).
GA MANZONSA TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI YA NA MAGANA DA AL'UMARSA YANA KIRAN SU ZUWA GA TAFARKIN WALWALA DA JIRGIN  TSIRA, YANA MAI CEWA : (KOWANNENKU ZAI SHIGA ALJANNA SAI WANDA YA KI, SAI SUKA CE WA YE ZAI KI YA MANZON ALLAH? SAI YA CE : WANDA YA MIN BIYAYYA ZAI SHIGA ALJANNA, WANDA YA SABA MIN TO HAKIKA SHI YA KI.)
KU KIYAYE BIN SON RAI DA BIN SHAIDAN, KU NESANCI MUNANAN ABUBUWA DA DA SABON ALLAH, ZAKU SHIGA ALJANNAR MAI RAHAMA ZAKU RABAUTA DA YARDAR MAI KYAUTA.
   
  
  



الجمعة، 14 أبريل 2017

LURA DA DAUKAN IZINA

HUDUBAR JUMA'A NA  MASALLACIN ANNABI NA SHEIKH ALIYU ABDURRAHMAN ALHUZAIFI  17 RAJAB 1438 AH
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Masanin gaibi, mai juya zukata, Mai yawan gafarar zunubai, ina yabon Ubangijina da godiya a gare shi bisa ni'imominsa da ba mai iya kididdige su sai shi, Na shaida ba abin bauta wa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya, mulki da kyakyawan yabo na shi ne, kuma shi ne mai iko ga dukkan komai,
Na shaida Annabinmu kuma shugabanmu Muhammad bawansa ne, kuma Manzonsa ne, Mai albishir kuma Mai gargadi, ya Allah ka yi dadin tsira da aminci da albarka bisa ga bawanka kuma Manzonka  Muhammad da iyalansa da sahabbansa  wadanda Allah ya jibince su, to madallah da majibinci kuma madalla da mai taimako,
Bayan haka ku ji tsoron Allah Mai tsarki, a sirracenku da a bayyanenku, don ya jibinci al'amuranku ya kuma gyara halayenku, domin takawa hanya ce ta mutanen kwarai da masu rabauta, rashin takawa shi ne  bayyanannen hasara, ya ku bayin Allah ku kasance daga cikin ma'abota lura da imani, ku bi tafarkin masu hankula da kyautatawa, ma'abuta lura su ne masu lafiyayyen hankali mikakke, kuma  masu lafiyayyen fidira, kuma suke amfana da wahayi,  suna fahimtar ma'anonin abin da Allah ya saukar bisa manufar Allah da Manzonsa, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, suna aiki da maganar Allah don  fatan ladarsa da tsoron ukubarsa, Allah Madaukakin Sarki ya ce : (kuma wadanda suka nisanci shaidanu ga bauta musu, kuma suka maida al'amari ga Allah, suna da bushara ,to, ka bayar da bushara ga bayi na . wadanda ke sauraron magana sa'annan su bi mafi kyaunta . wadancan sune Allah ya shiryar da su  , kuma wadancan su ne masu hankali)
Lura  na daga ayukan masu hankali   mai haskakawa      kuma yana daga cikin ayyukan masu basira masu gogewa  lura yana shiryarwa zuwa ga rabauta da tsira daga ayuka masu halakarwa, kuma yana datar da ma'abocin shi zuwa ga ayuka na kworai , kuma ya shiryar da shi zuwa ga hanyar mutanen kirki masu  neman  kawo gyara  kuma karshen shi yana zamewa zuwa ga alheri , wanda ya rasa lura  tunatarwa bazai mishi amfani ba  zai fada cikin halaka kuma zai bi sha'awe-sha'awen rayuka, kuma ya bi ta hanyar mabarnata sai ya zame cikin masu nadama ,  lura shi ne kaura daga wani hali da ya shude  ma'abocin ukuba da azaba  zuwa ga kyakkyawan yanayi ta hanyar nisantar sabuban ukuba da azaba  ko kuma kaura daga tarihin mutanen kworai  da abinda Allah ya karrama su da shi , zuwa da aiki da ayukan su da bin sawun su , ko kuma tunani cikin abin halittu da sanin tsirrin da suka kunsa da sifofin su da hikimar samar da su don bautawa mahaliccin su  da kebance shi da tauhidi da biyayya  albarka da daukaka ya tabbata agare shi  .
Hakika Allah mabuwayi da daukaka ya halicci halittu  kuma ya sanyawa duniya hanyoyin da suke tafiya a kai sai ya sanya da'a sababi ne na dukkan alheri a duniya  da lahira  ya sanya sabo sababi ne na dukkan sharri a duniya da lahira  shin akwai wanda ya taba zama shakiyyi sabo da biyayya ga Allah?  Ko kuma akwai wanda ya rabauta  sabo da sabawa Allah? Hakika Allah mai tsarki ya bamu kissa a littafinsa haka ma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bamu kissoshi  da wasu halaye  na Annabawa da Manzanni da muminai wanda a cikin shi akwai abin lura  da kuma abu na koyi ga wanda ke bayan su , da abinda akwai tsira daga ukubobi a cikin shi  da kuma rabauta da alheri  ,  da abinda akwai kyakkyawan karshe tare da shi da daga darajoji  Allah madaukakin sarki ya ce: (Lallai ne hakika abin kula ya kasance ne acikin kissoshin su  , ga masu hankali. Bai kasance kirkirarren labari ba, kuma amma shi gaskatawa ne ga abin da yake a gaba gare shi, da rarrabewar dukkan abubuwa , da shiriya da rahama ga mutane wadanda suka yi imani)  Allah madaukakin sarki ya ce  :( Sa'annan kuma muna kubutar da manzanninmu da wadanda suka yi imani  , kamar wannanne, tabbatacce ne a gare mu mu kubutar da masu imani )  Allah mai tsarki ya ce game da masu karyatawa :( Kuma suka kulla makirci, kuma muka kulla sakamakon makirci alhali su ba su sani ba . ka duba yadda akibar makircin su ta kasance  lallai mu mun darkake su da mutanen su gaba daya  . wadancan gidajen su ne wofintattu sabo da zalunci da suka yi   lallai ne a wancan akwai aya ga mutane da  suke sani).Muka  tsirar  da wadanda suka yi imani ,  kuma sun kasance suna  takawa).
Yayin da Allah ya ambaci dewa daga cikin kissoshin Annabawa tsira da amincin Allah su tabbata a gare su  a cikin suratul Shu'ara'I  ya ciken kissan  da fadin sa madaukakin sarki , bayan tsiran Manzannin sa da muminai tare da su :(  Hakika  lallai  akwai aya a cikin wancannanka, yawancin su ba su kasance muminai ba . Hakika Ubangijinka lallai shi ne mabuwayi mai jinkai )
Ibn kasir Allah ya mishi rahama ya ce: Hakika  lallai  akwai aya a cikin wancannanka.
Ai a wannan kissan da abunda ke cikinta na ban al'ajabi da taimako da karfafa ga  bayin Allah muminai akwai nuni da hujja na yanke  da hikima na kololuwa ( lallai Ubangijinka shi ne mabuwayi  )  wato wanda ya buwayi dukkan komai  kuma yayi galaba a kansa kuma ya fi karfinsa mai jinkai da halittunsa baya gaggawa ga wanda ya saba mishi sai dai ma yana sarara mishi kuma ya jinkirta mishi , sa'annan ya damke shi damka irin na mabuwayi mai iko,  Sa'id Dan Jubair  Allah ya kara mishi rahama ya ce  mai jinkai ga duk wanda ya tuba zuwa gare shi , maganan ta tike  a fadin Allah madaukakin sarki a kissan mutanen Ludu  amincin Allah ya tabbata a gare shi  lallai a cikin hakan a kwai ayoyi ga masu lura  katada yake cewa  ga masu lura Bagawi ya ambaci haka a cikin tafsirin sa mafi amfana da  abubuwan da suke faruwa na tarihi , da hikimomi na yanayi ,sai masu lura masu tunani wadanda suke koyi da  mutane na kwarai   masu neman gyara , kuma sukan bar ma'abota barna da fasadi amma shi wanda baya lura baya wa'azantuwa !  baya wa kanshi hisabi baya aiki don lahiransa addinin shi baya hanashi aikata komai , ko hankalin shi baya hana shi aikata munanan aiyuka  da laifuka wannan kamar fa dabba ne  Allah madaukakin sarki ya ce: (  ko kana zaton cewa ,  mafi yawansu suna ji , ko kuwa suna hankali ?  su ba su zama ba  face dabbobin gida  suke . A'a, su ne mafi bacewa ga hanya.)
A cikin Hadisi daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gashi : (Lallai ne idan mumini yayi rashin lafiya sai cutar ta buge shi har ya mutu ,to zai zama  kaffara ne ga  zunubansa da suka shude, idan Allah ya sauwaka mishi to zai zama kankara ne ga zunubansa da suka shude, kuma wazi ne ga lokaci mai fiskantowa. Idan kuma munafuki ya yi rashin lafiya, sannan ya samu sauki to zai zama kaman rakumi ne da masu shi suka daure shi sannan suka sake shi, to bai san don me aka daure shi ba kuma don me aka sake shi ba.)  Nasa'I ne bya rawaito



 Allah bai ambaci tarihin Annabawa ba da Manzanni  da cikamakin su  Annabinmu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  face don  ayi izina da tarihin su  a yi kuma koyi da shiryarwar su da halayen su  mku bi tafarkin su  hakika Allah ya umarci Annabinsa Muhammada tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  da yayi koyi da su  sai mai tsarki ya ce :(  Wadancanne Allah ya shiryar sabo da haka  ka yi koyi da shiryarwar su . )  Allah madaukakin sarki ya ce :( Sabo da haka ka yi hakuri kamar yadda masu karfin niyya daga Manzannai suka yi hakuri).
 Allah madaukakin sarki ya ce game da  muminin yasin  :( Ya mutane na ku bi Manzannin nan ,  ku bi wadanda  ba su tambayarku wata ijara  , kuma su shiryayyu ne ).  Cikamakin su Annabin mu Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi wanda  Allah ya goge sauran shari'u da shi  kuma ya aiko shi da   shari'a mafi kamala   da addini , Allah ya dauki nauyi ga duk wanda ya yi riko da shi zai shiryar da shi ya bashi  kyakkyawar rayuwa  a duniya da lahira ya shigar tare da shi mafificin halitta gidan aminci  Allah madaukakin sarki ya ce : (Kuma wadannan da suka yi da'a ga Allah da Manzon sa , to wadannan suna tare da wadanda Allah ya yi ni'ima a kansu , daga Annabawa da masu yawan gaskatawa , da masu shahada da saliha  kuma wadannan nan sun kyautatu da zama abokan tafiya )  
To wani girmamawa ne ya fi wannan , to wani daukakane ya ke kusa da wannan  matsayi?, kamar yanda Allah  ya kissanta mana  kissoshin Annabawa amincin Allah ya tabbata a gare su da wadanda suka yi imani da su don muyi  koyi da su  kuma mu bi tafarkin tsira tare da su  muyi lura da tarihinsu mu kuma san halayen su  ,Allah ya kuma bamu kissan labaran masu karyata su kuma masu  musu da  gaskiya kuma masu girman kai daga binsu  wanda  suka fifita rayuwan duniya akan na lahira  masu bin sha'awe – sha'awen su da jin dadi , don fa mu yi izina da ukubar su, kuma mu wa'azantu da abinda ya faru da su  na walakacin duniya da azabar lahira kuma mu gargadu daga tsinuwan da aka tabbatar a gare su .
Allah madaukakin sarki ya ce :(Da Adawa da Samudawa ,  alhali kuwa lallai alamun azaba sun bayyana a gare su , daga gidajen su  kuma sahidan ya kawata musu ayukan su . sabo da haka ya kange su daga hanyar Allah  kuma sun kasance masu basira  .
Kuma Karuna da Fir'auna da Hamana . kuma lallai Musa ya zo musu da hujjoji, sai suka yi girman kai acikin kasa kuma ba su kasance masu tserewa ba , sabo da haka ko wannan su mun kama shi da  laifinsa: wato daga cikin su akwai wanda muka aika iskar tsakuwa a kansa ,  kuma daga cikin su akwai wanda tsawa ta kama , kuma daga cikin su akwai wanda muka birkice kasa da shi , kuma daga cikin su akwai wanda muka nutsar, ba ya yiwuwa ga Allah ya zalunce su , amma sun kasance kansu suke zalunta .
Allah madaukakin sarki ya ce :( ko wannan su ya karyata Manzanni  sai narko ya tabbata a gare su )  Allah madaukakin sarki ya ce a kissan Banu ndir :( To ku lura fa ya masu basirori,)  tarihin manzanni tsra da amincin Allah su tabbata a gare su tare da masu karyatawa na daga masu sabawa Allah da  Manzanni  mutane sun san su zamani bayan zamani , na karshe ya karba a gun na farko , wannan na daga cikin manyan hujjojin Allah akan bayinsa wurin karfafan gaskiya da sanin tauhidi  da taimakawa masu kadaita Allah  a cikin bata da shirka da gargadi daga gare  shi  amma lura da dabi'un halittu  da gano hikimanta da siffofinta  da tunani akan kirkiran da Allah ya mata da  tunani cikin  aikin  Ubangiji gayarsa da kuma fa'idansa shi ne kadaita Allah madaukakin sarki mabuwayi da daukaka da kuma bauta masa da mishi da'a , to wanda ya kebanta da halitta shi ne abin bautawa bisa cancanci . Allah madaukakin sarki ya ce : (  Kuma lallai ne da abin lura a cikin dabbobin ni'ima; muna shayar da ku daga   abinda yake a cikin cikunansu  daga tsakanin tukar tumbi da jini, nono tsantsan mai saukin hadiya ga masu sha ) Aallah madaukakin sarki ya ce :( Allah yana juyar da dare da yini , lallai ne a cikin wannan akwai abin kula da ma'abota gannai)
  "ka ce ku yi dubi me ke cikin sammai da kasa, kuma ayoyi da gargadi ba za su yi amfani ba ga mutanen da basu ba da gaskiya da Allah ba "
To shi tuntuntuni cikin halittu ibada ne ga musulmi, amma daukan izina cikin wadannan halittu yana kara wa musulmi imani, kuma yana kara mishi zurfi cikin yakini, Allah Madaukakin sarki ya ke cewa :( Lalle ne a cikin sammai da kasa akwai ayoyi ga masu imani)
Tunani da lura na tabbatar da mai shakku, yana kuma raya zukata, yana haskaka gannai, yana mikar da halaye, shi kuma kauda kai daga tunani da lura yana kekasar da zukata, yana haifar da gafala,yana ja zuwa ga nadama, yana kuma jefa mutum cikin sabo    An karbo daga Abu Huraira Allah kara yarda a gare shi ya ce : ( Lalle Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce a isra'I : yayin da na sauko zuwa sama ta duniya sai na dubi kasa ta, to sai ga wata iska da kara da hayaki, sai na ce : me ye wannan ya kai Jibrilu? Sai yace : wadannan shaidanu ne ake kona su a gaban dan Adan basu tunani ga mulkin sammai da kasa ba don haka ba da sun ga abin mamaki) Ahmad ne ya rawaito
Aallah madaukakin sarki ya ce :( Lalle ne wadanda suka yi takawa idan wani tashin hankali daga shaidan ya shafe su, sai su tuna (Allah) sai ga su sun zama masu basira. Kuma 'yan uwansu (shaidanu ) suna taimakon su a cikin bata  sa'anan kuma ba su takaitawa).
Allah sanya albarka a gare ni da gare ku cikin Alkur'ani.
 Huduba ta biyu :
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya haskaka zukatan masoyansa da Alkur'ani, ya haskaka gannansu da imani, ya kawata ayyukansu da kyautatawa,
Ina kyautata yabo ga Ubangiji na kuma ina gode mishi, bisa ga ni'imominsa da ba mai iyakance su koma bayansa,
Na shaida ba abin bauta wa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya, mulki da yabo duka na shi ne, Mai rahama mai jinkai.
Na shaida cewa Annabinmu kuma shugabanmu bawansa ne kuma manzonsa ne, wanda aka kebantar da shi da dunkulallun kalmomi masu kamalar ma'ana da cikan bayani, Ya Allah ka yi salati da aminci da albarka bisa ga bawanka kuma manzonka  Muhammad da iyalansa da sahabbansa, da wadanda suka bi su da kyautatawa
Bayan haka. Ku ji tsoron Allah Madaukaki zai gafarta muku,zai tattaro muku dukkan alheri a rayuwanku da bayan mutuwarku,
Ya ku bayin Allah ! Ku yi wa kan ku hisabi kafin a yi muku hisabi, kowannen ku ya duba game da karshen al'amari, da karewar ajali, to wanda ya yawaita lura to kurakuransa za su karanta, wanda duk ya kiyaye sabawa Allah da zunubai to zai rayu cikin aminci, kuma a datar da shi zuwa ga kyakkyawan karshe, mai samun sa'ada shi ne wanda ya waazantu da waninsa, mai hasara kuwa shi ne wanda waninsa ya waazantu da shi.
Hakika Allah ya  yi zambo ga masu bin son rai wadanda basu yi lura ba suka wa'azantu da abin da Allah ya basu na labarai, Allah Madaukakin sarki ya ce :( Kuma suka karyata kuma suka bi son zuciyarsu, alhali kuwa kowane al'amari (wanda suke son su tare daga Annabi ) an tabbatar da shi.  Kuma lalle abin da yake  akwai tsawatarwa a cikinsa na labarai ya zo musu.)
Ku saurara Allah Madaukakin sarki na da wasu hanyoyin da ya saba bada lada da alhaki akan su to duk wanda ya ci karo da sunnar Allah to za ta tambadar da shi ta tarwatsa shi ya fado ya kaskanta, Allah Madaukaki ya ce : (A kan hanyar Allah (ta gyaran jama'a) a cikin wadanda suka shude gabaninka , kuma ba za ka sami musanya wa ba ga hanyar Allah.)
Ya zo a hadisi (ku yawaita ambaton mai katse jin dadi mutuwa)

Ya ku bayin Allah : Lalle Allah da Mala'iku na salati ga Annabi ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi kuma ku yi sallama domin amintarwa a gare shi.
  
  

 vv