السبت، 4 مارس 2017

بسم الله الرحمن الرحيم
Godiya ta tabbata ga Allah; Ubangijin qasa da sama, Mai amsa addu'a, Wanda yake faran bayi da ni'imomi, Kuma yake yaye mummuna da bala'i, Ina yabon Ubangijina kuma ina godiya a gare shi, Ina tuba zuwa gare shi, ina neman gafararSa, Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai yake bashi da abokan tarayya,  Ma'abucin buwaya da girma.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawansa ne manzonsa ne wanda aka turo shi da shrai'a cikakkiya, mai haske.
Ya Allah ka yi daxin salati da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka Muhammadu,    da iyalansa da sahabbansa masu rigaye zuwa ga aiyukan biyayya ababen godiya.
Bayan haka:
Ku kiyaye dokokin Allah da taqawa, iyakar kiyayewa, saboda duk wanda yayi riqo da taqawa to sai Allah ya haxa masa alkhairi a duniyarsa da lahirarsa. Wanda kuma ya nisanci taqawa to sai ya tave a qarshen lamuransa, ko da kuwa duniyarsa ta fiskance shi.

Ya ku Musulmai!!
Lallai Allah ya qaddara sabbuban alkhairori, da samun rabo a duniya da lahira, Kuma ya qaddara sabbuban sharrukan duniya da lahira, saboda haka; Duk wanda ya yi riqo da sabbuban alkhairi da rabauta to sai Allah ya lamunce masa samun gyaruwan rayuwarsa ta duniya, A lahira kuma zai kasance yana da kyakkyawan makoma, yana mai dawwama cikin aljannonin ni'imah, tare da rabauta da samun yardar Ubangiji Mai rahama. Allah (تعالى) yana cewa:
"Ba komai ba ne sakamakon kyautatawa face kyautatawa" [Suratur Rahman: 60].
            Wanda kuma yayi aiki da sabbuban sharri, to sai ya girbe sakamakon aikinsa, a rayuwarsa ta duniya, da kuma bayan mutuwa. Allah yana cewa:
 "Wanda ya aikata mummunan aiki za a saka masa da shi, Kuma ba zai sami wani masoyi ba, baicin Allah, kuma ba zai sami mataimaki ba" [Suratun Nisa'i: 123].

            Ku saurara!
            [Yin addu'a] Lallai yana daga cikin sabbuban gyaruwa da kawo gyara, da rabauta, da yawaitar samuwan alkhairori, da tunkuxe fitintinun da suke sauka, da uqubobi, da xauke musibun da ake cikinsu, da baqin ciki: YIN ADDU'Ada ikhlasi, da zuciya da take halarce, tare da yin naci, Saboda Ubangiji Mabuwayi da xaukaka yana son a riqa yin addu'a, kuma yayi umurni da shi. Shi kuma addu'a yana yin amfani akan abinda ya sauka, da wanda bai sauka ba (na musibobi), Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma Ubangijinku ya ce: Ku roqe ni zan amsa muku, Lallai waxannan da suke kangarewa daga bauta mini, za su shiga jahannama qasqantattu" [Ghafir: 60].
            Kuma addu'a shine Bauta, kamar yadda ya zo a cikin hadisin Annu'uman xan Bashir (رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), Ya ce:
"Addu'a shine bauta (ibada)", Abu-dawud ya ruwaito shi da Attirmiziy, kuma yace: Hadisi ne mai kyau ingantacce.
Kuma an ruwaito daga Abu-hurairah (رضي الله عنه), yace: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Babu wani abu wanda yafi matsayi a wurin Allah fiye da addu'a", Attirmiziy ya ruwaito shi, da Ibnu-Hibbana a cikin sahihinsa, da Alhakim, kuma yace: Isnadinsa ingantacce ne.
            Kuma Addu'a abun kwaxaitarwa ne akansa a kowani lokaci, kuma ibada ne wanda Allah ya ke bada sakayya akansa da mafi girman sakamako, Kuma addu'a yana tabbatar da ababen nema gabaxayansu; kevantattu, da waxanda suka game, na addini, da na duniya, a cikin wannan rayuwar da bayan mutuwa.
Kuma saboda amfanin da addu'a yake da su masu girma Allah ta'alah ya shar'anta yinsa a cikin ibadodin da aka farlanta, a matsayin wajibi ko mustahabbi, saboda rahamar Ubangijinmu da karramawa da yin baiwa, domin bayi muyi aiki da wannan sababin; da Allah ya sanar da mu Shi. Kuma lallai da Allah bai sanar da mu yin addu'a ba, to da kwakwalenmu basu shiryu izuwa gare shi ba, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma aka ilmantar da ku, abinda Ku da ubanninku baku sani ba" [Suratul An'am: 91].
Don haka; Yabo da godiya na Allah ne, yabo mai yawa, mai daxi, mai albarka, kamar yadda Ubangijinmu yake so, kuma kamar yadda Ubangiji ya yarda.

            Kuma buqatar yin addu'a a ko-da-yaushe ta kan yi tsanani, Musamman a wannan zamanin, Wanda fitintinu suka bayyana, kuma suka yawaita, tare da saukar bala'oi da annoba masu halakarwa, da kuma saukar ababen baqanta rai, ga Musulmai, da bayyanar qungiyoyin bidi'a; waxannan da suke rarrabe kan Musulmai, kuma suke halatta zubar da katangaggen jini da kwasar dukiya ta haramaun, suke kuma kyamar ilimi da ma'abutansa, kuma suke yin fatawa da jahilci, da kuma vata. A lokacin da maqiyan Musulunci suke taruwa don murqushe shi, suke kuma shisshirya makirce-makirce akan masu Imani, su kuma Musulman suke tavar da junansu, suke rarrabewa, suke savani, a tsakaninsu. A kuma lokacin da dangogin cutuwa suka riski kowanne daga cikin xaixaikun Musulman da aka fitar da su, daga gidajensu, da zalunci, kuma cutuka suka shafe su, buqatunsu suka zama da wahala, Lallai a irin waxannan halaye masu tsanani; waxanda Musulmai suke quna da wutansu a garurrukan da fitintinu suka kunnuBuqatuwar yin addu'a tana yawaita.

            Kuma lallai haqiqa Allah yayi yabo akan waxanda suke roqonSa, suke kuma qanqan-da kai izuwa gare shi Mabuwayi da xaukaka; IDAN har manyan lamura  ko tsanani suka sauka akansu, Allah (تعالى) yana cewa dangane da iyayenMu guda biyu (Adamu da Hauwa'u عليهما السلام):
 "Su biyun, suka ce: Ya Ubangijinmu! lallai ne Mu mun zalunci kayukanmu, idan har baka gafarta mana kayi rahama a gare mu ba, zamu kasance daga cikin masu hasara" [Suratul A'araf: 23]. Kuma Allah (تعالى) yace:
"Kuma tabbas zamu jarrabe ku da wani abu na tsoro da yunwa da tawaya cikin dukiya da rayuka da 'ya'yan itatuwa, Kuma ka yi bishara ga masu haquri * Waxannan da idan musiba ta same su, sai su ce: Lallai Mu daga Allah muke, kuma lallai Mu zuwa gare shi masu komawa ne * Waxannan akansu akwai albarku daga Ubangijinsu, da wata rahama, Kuma waxannan sune shiryayyu" [Suratul Baqarah: 155].kuma Allah mabuwayi da xaukaka ya faxa dangane da annabi Yunus s(عليه السلام):
"Kuma annabi Yunus sa'ad da ya tafi yana mai fushi, sai yayi zaton cewa ba za mu quntata masa ba, sai yayi kira a cikin duffai, cewa: babu abin bautawa face kai, tsarki ya tabbata a gare ka, lallai Ni kasance daga azzalumai" [Suratul Anbiya'i: 87].
Hadisi ya zo daga Sa'ad xan Abiy-Waqqas (رضي الله عنه) yace, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Addu'ar annabi Yunus wanda kifi ya haxiye, a lokacin da ya roqi Allah alhalin yana cikin kifi, babu wani Mutum Musulmai da zai yi roqo da shi, face Allah ya amsa masa addu'ah", Ahmad ya ruwaito shi, da Attirmiziy, da Alhakim, kuma yace: Isnadinsa ingantacce ne.
            Kuma a yayin da Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya kirayi qabilar Saqifu zuwa ga Musulunci, sai suka qi karvar da'awarsa, sannan suka jefe shi da duwatsu, sai ya roqi Ubangijinsa yana mai cewa:
"Ya Allah ina koka raunin qarfina zuwa gare ka, da qarancin dabarata, da qasqancin da nake da shi a wurin Mutane, Ya mafi rahamar masu rahama; izuwa ga Wa; zaka jivintar da Ni; zuwa ga maqiyin da yake xaure min fiska, ko kuma izuwa ga wani maqiyin da ka mallaka masa lamarina, Idan baka yi fushi da ni, ba; to bani da damuwa, Saidai kuma  lafiyarka ita tafi yalwa a gare ni. Ina neman tsari da hasken fiskarka wanda ya haskaka duffai, kuma lamarin duniya da lahira suka gyaru da shi, kada fushinka ya sauka akaina, Komawa naka ne, har sai ka yarda, Babu dabara babu qarfi face daga wurinka".

            Da yin addu'oi ne, ake fiskantar tsanani da ababen vacin rai, na abubuwan da Mutum ba zai iya tunkuxe maka su ba; saboda Yazo daga Sauban (رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Babu abinda ke tunkuxe qaddara sai addu'a, kuma babu abinda yake qara tsawon rai sai xa'a ga iyaye da sada zumunci, Kuma lallai mutum ana haramta masa arziqi saboda wani zunubin da ya aikata", Ibnu-Hibbana ya rawaito shi a cikin sahihinsa, da Alhakim, kuma yace: Isnadinsa ingantacce ne.
An ruwaito daga Abdullahi xan Umar (رضي الله عنهما), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), yace:
"Lallai addu'a yana amfani daga abinda ya sauka, da kuma wanda bai sauka ba, Ya ku bayin Allah; Sai ku lazimci yin addu'a", Attirmiziy ya ruwaito shi, da Alhakim.
An ruwaito daga Abu-Hurairata (رضي الله عنه) yace: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: Lallai Allah (تعالى) yana cewa:
"Ni, Ina yadda bawana ke zatona, kuma Ni ina tare da shi idan ya roqe ne", Bukhariy ya ruwaito shi, da Muslim.
Kuma lallai wannan lada da falala ya kai yadda ya kai (A ce, Allah yana tare da bawansa; idan ya roqe shi!).

            Kamar yadda Allah yayi zargi ga waxanda  suke barin roqon Allah ko addu'a a lokacin da uqubobi suka sauka, ko bayyanar fitintinu; Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma haqiqa mun kama su, da azaba, saidai basu qanqan da kai ga Ubangijinsu ba, kuma ba sa yin tawali'u" [Suratul Muminuna: 76]. Kuma Allah mabuwayi da xaukaka yace:
"Kuma lallai mun aika zuwa ga al'ummai daga gabaninka, sai muka kama su da tsanani da cuta, tsammaninsu za su qanqan da kai * To, don me lokacin da tsananinmu ya je musu basu yi tawali'u ba, Sai zukatansu suka qaiqashe, kuma Shexan ya qawata musu abinda suka kasance suke aikatawa" [Suratul An'am: 42-43]. Kuma Allah (تعالى) yace:
"Kuma ba mu aika wani annabi a cikin wata alqarya (sai suka qaryata shi) ba, face mun kama mutanenta da azaba, da cuta, tsammaninsu za su qasqantar da kai" [Suratul A'araf: 94].
            Kuma lallai qin yin addu'a, a lokacin tsanani dogewa ne, akan zunubai, da kuma raina lamarin kamu ko damqar Ubangiji mai tsanani, Allah (سبحانه) yana cewa:
"Lallai damqar Ubangijinka mai tsanani ce" [Suratul Buruj: 12].
            Kuma lallai shi addu'a sababi ne mai girma na sauqar alkhairori da albarkoki, da tunkuxe sharri, ko xauke shi, daga mai yin addu'ar.
            Kuma yin addu'a shine sababin da ya fi qarfi domin fita daga sharrin da ya auku, da mummunan yanayin da ake ciki, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma da Ayyuba a lokacin da ya kirayi Ubangijinsa lallai ne Ni, cuta ta shafe ni, kuma kai ne mafi rahamar masu tausayi * Sai muka amsa masa, sa'annan muka kwaranye abinda ke a tare da shi na cuta, Kuma muka kawo masa iyalansa da kwatankwacinsu tare da su, saboda rahama daga gare mu, da tunatarwa ga masu ibada" [Suratul Anbiya'i: 83-84]. Kuma Allah (تعالى) yace:
"Ko, Wane ne ya ke amsawa mai buqata, idan ya roqe shi, kuma ya kwaranye mummuna" [Suratun Naqml: 62]. Ai, Babu wani da yake aikata hakan, sai Allah (تعالى).
Kuma Allah (سبحانه) yace:
"Ka ce Wane ne yake tsirar da ku daga duffan tudu da ruwa, kuna roqonsa bisa ga qanqan da kai, kuma a voye; Lallai ne idan ka tsiratar da mu daga wannan (masifa), zamu kasance masu godiya * Ka ce: Allah ne, yake tseratar da ku daga gare ta, da kuma dukan baqin ciki, Sa'annan sai ku kuma ku ci-gaba da yin shirka" [Suratul An'am: 62-63].
            Shi Musulmi wajibi ne akansa ya riqa addu'a da kwaxayin Allah (تعالى) ya gyara masa sha'anoninsa, gabaxaya, yana mai xaga buqatunsa zuwa ga UbangijinSa gabaxayansu, ya riqa roqonSa kowani abu. Kuma mafi girman abin nema shine aljannah, da kuvuta daga aukawa wuta, Allah (تعالى) yana faxa a cikin hadisin Qudusiy:
"Ya ku bayina! dukkaniku vatattu ne, sai wanda na shiryar da shi; ku nemi shiryarwata; in shiryar da ku. Ya ku bayina! dukkaninku mayunwata ne sai wanda na ciyar da shi; sai ku nemi ciyarwata; in ciyar da ku. Ya ku bayina! kowanenku tsirara ya ke; babu tufafi sai wanda na tufatar da shi; sai ku nemi tufatarwata, in tufatar da ku. Ya ku bayina ! lallai kuna yin laifi dare da rana, ni kuma ina gafarta zunubai gabaxaya; sai ku nemi gafarata; in yi muku gafara", Muslim ya ruwaito shi daga hadisin Abu-zarri (رضي الله عنه). Ma'anar hadisin kuma shine: Ku roqe ni shiriya, da ciyarwa, da tufatarwa da gafara.
Kuma y azo a cikin hadisi cewa:
"Xayanku ya riqa roqon UbangijinSa koda akan igiyar takalminsa ne (da ya tsinke), da gishirin abincinsa".

          Kuma dayawa, addu'a ta kan canza abinda yake gudana a tarihi daga sharri zuwa ga alheri, ko kuma daga abu mai kyau zuwa wanda yafi shi kyau, Allah (تعالى) yana cewa dangane da Babanmu annabi Ibrahim (عليه الصلاة والسلام):
"Ya Ubangijinmu! Ka aiko a cikinsu, wani manzo, daga gare su, yana karanta musu ayoyinka, kuma yana karantar da su wannan littafin da hikima, kuma yana tsarkake su, lallai ne kai, kai ne Mabuwayi Mai hikima" [Suratul Baqara: 129]. Kuma an ruwaito daga Abu-Umamah (رضي الله عنه), yace: Na ce: Ya ma'aikin Allah! Menene farkon lamarinka? Sai yace: Ni addu'ar babana ne annabi Ibrahim, kuma busharar annabi Isah, Sai mamata ta gani a mafarki cewa wani haske ya fita daga gare ta, wanda har ya haskaka benayen qasar Sham", Ahmad ya ruwaito shi. 
Kuma saboda wannan addu'ar ta annabi Ibrahima; Musulmai suka kasance cikin alheri madawwami, kai, dukkan dumiya itama wannan addu'ar ta shafe su.
            Haka, addu'ar da annabi Nuhu (عليه الصلاة والسلام) itama ta kasance alheri ga muminai masu tauhidi, sharri ga mushirkai.
            Haka addu'ar da annabi Isah (صلى الله عليه وسلم) zai yi; shi da sahabbansa waxanda za a killace su a jikin dutsen AXXUR, a qarshen zamani itama zata kasance nasara ce ga muminai, sa'annan halaka ga YAJUJU da MAJUJU, waxanda suke kamar farar da za ta game dukkan qasa (duniya), Mafi sharrin halitta, masu tsananin varna da qetare iyaka da qirman kai,  saboda Ya zo cikin hadisin Annawas xan Sam'an (رضي الله عنه) bayan annabi Isa ya kashe MASIHU AD-DAJJAL:
"Sai Allah (تعالى) yayi wahayi ga annabi Isah (صلى الله عليه وسلم) cewa: Lallai ni na fitar da wassu bayi, waxanda wani bashi da ikon yaqarsu, Sai ka killace bayina a wajen dutsen Ax-xur. Sai Allah ya tayar da Ya'ajuju da ma'ajuju alhalin suna gaggawa daga kowani tudun qasa; Sai na farkonsu su shige ta jikin wani qaramin teku na xabariya, sai su shanye dukkan ruwan da ke cikinsa, Sai na qarshensu su zo shigewa sai su ce: Lallai wannan, da akwai ruwa a cikinsa, To, sai a killace annabin Allah Isah (صلى الله عليه وسلم)shi da sahabbansa; har sai ya kasance kan Saniya yafi alheri ga xayansu, fiye da dinari xari ga xayanku a yau, to daga nan, sai annabin Allah; Isah ya bayyanar da kwaxayinsa shida sahabbansa (رضي الله عنهم) wa Ubangijinsu maxaukaki; ta hanyar roqonsa, Sai Allah (تعالى) ya saukar da tsutsotsi a wuyan Ya'ajuju da Ma'ajuju, sai su wayi gari sun mutu, kamar mutuwar rai guda xaya. Sa'annan sai annabin Allah; Isah da sahabbansa su sauka kan qasa, saidai kuma ba za su sami daidai da taqi xaya ba, a doron qasa face gawar Ja'ajuju da ma'ajuju da warinsu ya cike shi; Sai annabin Allah; Isah ya bayyanar da kwaxayinsa shida sahabbansa (رضي الله عنهم) wa Ubangijinsu maxaukaki; ta hanyar roqonsa, Sai Allah (تعالى) ya turo da wassu tsuntsaye, waxanda suke kama da wuyan raqumi, sai su tattare su; su kai su, su jefa, a wurin da Allah (تعالى) ya nufa", Muslim ya ruwaito shi.

            Kuma addu'ar da annabi (صلى الله عليه وسلم) shugaban halitta,  yayi; shi da sahabbansa, a yaqin badar, itama ta kasance wata nasara ce ga Musulunci, har abada, kuma tavewa ce, ga kafirci har abada; Allah (تعالى) yana cewa:
"A lokacin da kuke neman agajin Ubangijiku sai ya amsa muku; da cewa: lallai ne Ni zan taimaka muku da dubu daga cikin Mala'iku, a jere" [Suratul Anfal: 9]. Sai Annabi (صلى الله عليه وسلم) yayi ta yin addu'a, kuma ya nace, wajen yin addu'ar, har sai da mayafinsa ya faxi, A nan ne, Abubakar (رضي الله عنه) ya rungume shi, sa'annan ya ce:  Yadda kake yin magiya wa Ubangijinka, ya isa, ya ma'aikin Allah! Kuma lallai Allah zai cika maka abinda ya yi maka alkawari.

            Kuma lallai yin addu'ar taimakon gaskiya, da ruguje varna, yana daga nasiha ga Allah da littafinSa, da ManzonSa, da jagororin Musulmai, da kuma sauran Mutanensu.
            Kuma babu wanda zai guje wa yin addu'a, yana mai qaurace masa face wanda ya tozarta rabonsa a duniya da lahira, sa'annan ya tozarta abinda ya wajaba akansa na haqqin Musulunci da Musulmai. Ya zo a cikin hadisi cewa:
"Duk wanda bai himmatu da lamarin Musulmai ba to baya cikinsu".
            Kuma da a ce, za mu yi ta bibiyar fa'idodin addu'a da albarkokinsa, da alherorinsa, da natijojinsa, daxaxa, kuma ababen mamaki, to da, ambaton hakan yayi tsayi. Saidai abinda muka riga muka yi ishara, a baya, ya isar.
           
            Kuma lallai addu'a yana da SHARRUXA, DA LADDUBA;
Kuma yana daga cikin sharruxan addu'aCin abinci na halal, da sanya tufar halal, Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace wasahabinsa Sa'ad xan Abiy-Waqqas (رضي الله عنه):
"Ka kyautata abincinka; sai a amsa maka addu'arka".
Kuma yana daga cikin sharruxansa: Riqo da Sunnah, da kuma amsawa Allah (تعالى) ; ta hanyar aikata abubuwan da ya yi umurni, da nisantar abubuwan da yayi hani, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma idan bayina suka tambaye ka dangane da ni, ka ce: Lallai ni, a kusa nake, ina amsa addu'ar mai addu'a idan ya roqe ni, Sai su nemi amsawata, kuma su yi Imani da ni, tsammaninsu za su shiryu" [Suratul Baqara:186]. Kuma Allah (تعالى) yace:
"Kuma yana amsawa wadannan da suka yi imani,  suka kuma aikata aiyukan kwarai, kuma yana qara musu sakamako daga falalarsa" [Suratush Shurah: 26]. Mutumin da aka zalunce shi, shi kuma ana amsa masa, idan yayi addu'a; koda kuwa kafiri ne, ko xan bidi'a.
            Kuma yana daga cikin sharruxansa: Yin ikhlasi da halarto da zuciya, da yin naci, wa Allah, da yin gaskiya cikin neman mafaka, daga Ubangiji (تعالى), Allah ta'alah yana cewa:
"Sai ku roqi Allah kuna masu tsarkake addini a gare shi, ko da kuwa kafirai sun qi" [Suratul gafir: 15].
Ya zo cikin hadisi cewa, "Allah baya karvar addu'a daga zuciya rafkananniya mai wargi".
            Kuma yana daga cikin sharruxansa: Kada ya yi, addu'a da savo, ko yanke zumunta, kuma kada ya qetare iyaka, cikin addu'a.
            Kuma yana daga cikin sabbuban amsa addu'a: Yin yabo wa Allah (تعالىda sunayensa mafiya kyau, da sifofinsa maxaukaka, tare da yin salati wa annabi (صلى الله عليه وسلم); Ya zo cikin wani hadisi cewa; Lallai annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ji wani Mutum yana cewa:
"Ya Allah, lallai ne Ni ina roqonka , da shaidawata cewa babu abin bautawa da gaskiya sai kai, Makaxaici, Wanda ake nufi da biyan buqata, wanda bai haifu ba, kuma ba a haife shi ba, kuma bashi da wani wanda yake daidai da shi, Sai yace: Lallai ne, ka roqi Allah da sunanSa da yafi girma; wanda idan aka roqe shi da shi ya kan bayar, idan kuma aka yi addu'a da shi, ya kan amsa", Abu-dawud ya ruwaito shi, da Attirmiziy, kuma yace: Hadisi ne mai kyau (hasan).
Da kuma Ibnu-Majah da Ibnu-Hibbana, da Alhakim, daga hadisin Buraidah (رضي الله عنه).
An kuma ruwaito daga Fadalah (رضي الله عنه), yace: Wata-rana Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana zaune, sai wani Mutum ya shigo yayi sallah, Sa'annan ya ce:
"Ya Allah, ka gafarta mini, ka yi mini rahama, Sai Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace: Ka yi gaggawa ya kai mai sallah, Idan ka zo sallah; sai ka zauna, to ka yi godiya wa Allah da abinda ya cancance shi, San'annan sai ka yi min salati, Sa'annan sai ka roqi Allah", Ahmad ya ruwaito shi, da Abu-dawud, da Attirmiziy, kuma yace: Hadisi ne hasan.
A cikin wani hadisin kuma:
"Lallai addu'a yana rataye tsakanin sama da qasa har sai ya yi salati wa Annabi (صلى الله عليه وسلم)".
            Kuma yana daga cikin ladduban addu'a da sharruxan karvarsa: Kada ya yi gaggawar amsawa, A'a yayi haquri, Ya zo a cikin hadisi cewa:
"Za a amsa wa xayanku matuqar bai yi gaggawa ba; yace: Na roqa, na roqa, amma ba a amsa mini ba", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi, daga hadisin Abu-hurairah (رضي الله عنه).
            Kuma lallai, dawwama kan addu'a (da yawaita yinsa), a tare da shi akwai amsawa, Ya zo cikin hadisi cewa:
"Babu wani Musulmi a bayan qasa, wanda zai roqi Allah da wata addu'ar face, Allah ya bashi ita, ko kuma ya tunkuxe masa wani mummunan kwatankwacinta, matuqar bai roqi sabo, ko yanke zumunta ba. Sai wani Mutum yace: To, lallai za mu yawaita! Sai yace: Allah zai fi ku yawaitawa", Attirmiziy ya ruwaito shi, kuma yace: Hadisi ne, hasan sahih, kuma Alhakim ya ruwaito shi daga riwayar Abiy-Sa'id, sa'annan ya yi qari a cikinsa: Ko kuma, a ijiye masa kwatankwacin addu'arsa.

            Kuma ya dace, Musulmi ya yi kirdadon lokutan amsa addu'a, An ce wa Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم):
Wace addu'a ce, aka fi amsawa? Sai yace: "Ta qarshe dare, da bayan sallolin farilla", Attirmiziy ya ruwaito shi, yace: Hadisi ne, hasan, daga hadisin Abiy-Umamah. Kuma ya zo cikin wani hadisin cewa:
"Ubangijinmu yana sauka zuwa ga saman duniya, a cikin xaya bisu ukun dare na qarshe; Sai ya ce: Wa zai yi roqo sai na amsa masa, Wa zai tambaye ni sai na bashi, Wa zai nemi gafarata sai na gafarta masa", Bukhariy ya ruwaito shi, da Muslim daga hadisin Abu-hurairah.
            Da kuma tsakanin kiran sallah da yin iqamah, Nan ma ba a mayar da addu'a: Ya zo cikin hadisi cewa:
"Lokacin da bawa yafi kasancewa kusa da UbangijinSa shine a lokacin sujjada; Sai ku yawaita addu'a", Muslim ya ruwaito shi daga hadisin Abu-hurairah.
            Da kuma lokacin ganin ka'abah, da lokacin saukan ruwa, da hali na buqatuwa, da bayan khatamar alqur'ani gabadaya, da bayan yin sadaka.

            Ka yi mamakin girman rabauta, da nasara, da samun ladan Mutumin da ya killace zuciyarsa, ga Allah (تعالى); yana roqonSa, yana fatanSa, yana kuma dogara akanSa, yana neman taimakonSa.
            Da kuma tavewa, da girman shirka ko kafircin wanda yake roqon kabari, ko yake neman agaji daga Annabawa (عليهم الصلاة والسلام), da waliyyai, ko yake roqonsu koma bayan Allah (تعالى), ko yake xaga buqatunsa zuwa ga wani mala'ika makusanci, ko wani annabi mursali; saboda Annabawan Allah (عليهم الصلاة والسلام) sun zo ne, don kiran Mutane, cewa su keve Allah (تعالى) da yin roqo a gare shi, sa'annan su kaxaita shi da bauta shi kaxai. Su kuma waliyyai an umurce mu da mu riqa yin aiki irin nasu, sa'annan mu so, su, kuma aka hane mu, kan roqonsu, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma lallai masallatai na Allah ne, kada ku roqi wani tare da Allah"[suratul Jinn: 18]. Kuma Allah (تعالى) ya ce:
"Kuma ka ce: Kawai ni, ina roqon Ubangijina ne, kuma ba zan tara kowa da shi ba" [Jinn: 20].       
Kuma wanda baya halarce, da matattu babu wani daga cikinsu da yake amsa addu'a; saboda addu'a babu mai amsa shi idan ba Allah Mabuwayi da daukaka ba, Allah (سبحانه) yana cewa:
"Kiran gaskiya nasa ne, Wadanda kuma suke roqon waninshi basa amsa musu da komai, face kamar mai shumfuda tafukansa zuwa ga ruwa domin ya kai ga bakinsa, kuma shi ba mai kaiwa gare shi ba ne, Kuma kiran kafirai (ga wanin Allah) bai zama ba, face a cikin bata" [Suratur Ra'ad: 14]. Kuma Allah (تعالى) yace:
"Babu wanda ya fi bata fiye da wanda ke roqon wanin Allah, wanda ba zai amsa masa ba, har ranar qiyama, alhalin (wadanda ake roqan) sun gafala da kiran masu kiran * Kuma idan aka tattara mutane, za su kasance abokan gaba a gare su, kuma za su kasance masu kafircewa ga bautan da suka yi a gare su" [Ahqaf: 5-6].
Kuma Allah (تعالى) yace, alhalin yana bada labarin aiyukanSa:
"Yana shigar da dare a cikin yini, kuma yana shigar da yini cikin dare, kuma ya hore wata da rana; kowannensu yana gudana zuwa ga ajali ambatacce. Wannan shine Allah Ubangijinku, mulki nasa ne, kuma waxanda kuke roqa waninSa basa mallakar ko da fatar kwallon dabino * Idan kuka roqe su, to ba za su ji kiranku ba, koda sun ji to ba za su amsa muku ba, kuma a ranar qiyama za su kafirce wa shirkarku, kuma babu mai baka labari, kamar wanda ya sani", [Fadir: 13-14].
            Kuma lallai Allah bai yi izinin a roqi waninSa ba, duk irin kusancin da yake da shi, Allah (تعالى) yana cewa:
"Almasihu ya ce: Ya ku 'ya'yan Isra'ila, Ku bauta wa Allah; Ubangijina, kuma Ubangijinku; lallai ne duk wanda ya yi shirka da Allah to, lallai Allah ya haramta masa aljanna, kuma makomarsa itace wuta, kuma babu wassu mataimaka ga azzalumai" [Ma'idah: 72]. Kuma me tsarki da daukaka (Allah) ya ce ''kuma baya umurninku da ku riki mala'iku da annabawa iyayengiji . shin ze umarceku da kafirci ne bayan kun riga kun zama masu sallamawa (musulmi)
Ya zo cikin hadisi cewa: "Wanda ya mutu alhalin yana roqon wani koma bayan Allah ya shiga wuta", Bukhariy ya ruwaito shi daga hadisin Abdullahi dan Mas'ud (رضي الله عنه).

            Ya kai Musulmi!!
            Wannan shine littafin Allah, da hadisan ManzonSa (صلى الله عليه وسلم) suna bayyana maka cewa, lallai ADDU'A shine BAUTA, kuma lallai Allah mabuwayi da xaukaka shine kawai ya kevanta da addu'a, ba a yinsa sai ga Allah maxaukaki, kuma duk wanda ya haxa wani da Allah a cikin addu'a to wannan mushirki ne mai babbar shirka.
Kuma kada wani ya yi koyi da wani cikin vata da shirka; saboda shirka da kafirci basu auku a cikin 'ya'yan Adam ba face, da sababin taqalidanci, da bin mutane vatattu, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma shin wancan, shine mafi zama alheri ga liyafa, ko kuma itaciyar zaqummi * Lallai Mu mun sanya ta fitina ga azzalumai * Lallai ita wata bishiya ce, wadda take fita daga asalin wutar jahima * Fudarta, kai kace kayukan shexanu ne * Lallai su haqiqa masu ci ne daga gare ta, sa'annan masu cika cikinsu ne daga gare ta * Sa'annan suna da wani gauraye a kanta, daga ruwan zafi * Sa'annan lallai makomarsu izuwa ga wutar jahimu take * Lallai su, sun iske Ubanninsu suna datattu *  Sai suka kasance akan gurabansu suke ta yin gaggawa" [As-safat: 62-70].
Kuma Allah (ta'alah) yana cewa:
"Kuma ku roqi Ubangijinku da qanqan da kai, da kuma a boye, Lallai ne shi, baya son masu qetare iyaka kuma kada kuyi barna a cikin kasa bayan gyaranta kuma ku kirayeshi saboda tsoro da tsammani : lallai ne rahamar Allah makusanciya ce daga masu kyautatawa" [A'araf: 55].

            ALLAH YAYI MINI ALBARKA, NI DA KU A CIKIN ALQUR'ANI MAI GIRMA.

HUXUBA TA BIYU
            Yabo da godiya sun tabbata ga Allah Mai rahama, Mai jin qai, Mabuwayi Mai hikima, Ma'abucin sunaye da suka fi kyau, da sifofi maxaukaka.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya, Maxaukakin da Yafi xaukaka.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawansa ne manzonsa ne Zavavve.
Ya Allah ka yi daxin salati da sallama da albarka, ga bawanka kuma manzonka Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa Masu taqawa.
Bayan haka:

Ku kiyaye dokokin Allah, sai ya gyara muku aikyukanku, sa'annan ya sanya ku daga cikin masu rabauta a yanzu, da kuma bayan komawa izuwa ga makoma.

Ya ku Bayin Allah!
            Ku kasance, masu bayyanar da kwaxayi zuwa ga Allah, masu dawwamar da yin roqo a gare shi (da yawaitawa); saboda Duk wanda ya roqi Allah baya tavewa, wanda kuma ya yi fatan samun Allah ba a hana shi.
Umar Allah kara yarda a gare shi yace : Lalle ni ba na dorawa kai na damuwar amsa adua sai dai na kan damu da yin aduar, in har an min dacen yin adua to Allah ya lamunce amsa aduar.
Kuma kowani Mutum yana da buqatun da suke sabuntuwa, da ababen nema a kowani lokaci masu yawa; Don haka; Sai kowa ya roqi UbangijinSa, duk abinda ya san alheri ne. kuma ya yi wa Musulmai da aka zalunta a addini adu'a, ya kuma nemi tsarin Allah daga  duk abinda ya san sharri ne.
Kuma mafi girman abin roqo shine neman samun yardar Allah, da kuma aljannah.
Shi kuma mafi girman abinda ake neman tsari daga gare shi, shine wuta da sabubanta.
Kuma Mutum Musulmi ya yi naciyar roqon abinda ya dame shi, daga wajen Ubangijinsa; saboda Allah Mawadaci ne, Mai karimci, Abun godiya, Mai yawan baiwa, Mai girma, Mai iko, Allah maxaukaki yana cewa:
"Ya ku bayina! Da, na-farkonku da na-qarshenku, da mutanenku da aljanunku zasu tsaya a bigire xaya, sai kowanne ya roqe ni, sai in bada kowanne xaya abinda ya roqa; to ba zai rage komai daga cikin abinda ke wurina ba sai kamar gwargwadon abinda allura ta rage; idan aka tsoma ta a cikin ruwan teku", Muslim ya ruwaito shi/ ya zo a hadisi :Wanda bai roki Allah ba zai yi fushi da shi,

            Kuma mustahabbi ne, Musulmi ya riqi addu'oi masu gamewa, waxanda suka zo daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), kamar faxinsa maxaukakin sarki:
"Ya Ubangijinmu ka bamu mai kyau a Duniya, a lahira ma mai kyau, ka kare mu daga azabar wuta" [Baqara: 201].
Da kuma misalin
"Ya Allah, lallai ne Ni ina roqonka aljanna da abinda ya kusantar zuwa gare ta na zance ko aiki, Kuma ina neman tsarinka daga wuta da kuma abinda ya kusantar zuwa gare ta na zance, ko aiki".

            Ya ku bayin Allah!
             "Lallai Allah da Mala'ikunSa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi imani ku yi salati a gare shi domin amintarwa" [Ahzab: 56].

Addu'a ….
……………….
……………….

……………….


الخميس، 9 فبراير 2017

HUDUBAR JUMA'A A MASALLACIN ANNABI  13/05/1438AH, NA SHAIKH SALAH BIN MUHAMMAD AL-BUDAIR.
HUDUBAR FARKO:
Ya ku Musulmai:
Hakkoki tsakanin ma'aurata biyu ya ta'allaka ne da Kulla aure, wanda kuma ke lazimta kyakkyawar muamala  da juna, kada  ya jinkirta bashi hakkin shi ko ya ki  bada abin da ke kan shi. Kyautata muamalarsa ga abokin zamansa da tausaya masa da juriya bisa ga cutarwarsa sabo da fadin Allah (su matayen suna da hakki akan maza irin wanda mazan suke da shi akansu, da abin sani.)
Ita kyakkyawar mu'amala da kyakkyawan zama ya fi kawo sanyin ido, da kwanciyan hankali da daddadan rayuwa, Allah madaukakin sarki ya ce :- ( ku yi mu'amala da su da kyakkyawa)  ma'ana ku yi cakudedeniya da abota da su, da bishara da kuma sakin fiska , da bada hakkoki da aka farlanta, kamar na daga sadaki da ciyarwa da raba kwana, da barin cutar da ita da kakkausar magana , da bijire mata,  da karkata zuwa ga watanta,  da rashin hada mata fiska, da turmuke mata ba tare da wani laifi ba , sa'annan Allah na ladabtar da bayinsa da fadin sa (  sa'annan kuma idan kun ki su , to, akwai tsammanin ku ki wani abu, alhali kuwa  Allah ya sanya wani alheri a cikinsa mai yawa)  a cikin ayan kwai kwadaitarwa bisa rike su da kyautata zamantakewa da su, ko da mijin ya tsani wani abu daga cikin halayen su, domin rai ya ki abu ba ya nuni da kore alheri da wannan abu, ta iya yuwuwa  abinda rai taki ya zama shi ya fi maslaha a addini, kuma ya fi zamewa abun godiya a karshe , so da yawa abin ki kan komawa abin yabo, kuma abin yabo kan koma wa abin zargi,  miji kan tsani mata  sabo da wata sifa daga cikin sifofinta, amma kuma a rike ta din akwai wani alheri da yawa da bai sani ba,   kuma ba zai gane hakan ba, Abdullahi dan Abbas  Allah ya yarda da shi da mahaifin shi ya ce: ta iya yiwuwa Allah  zai azurta shi da Da daga gare ta , sai Allah ya sanya alheri mai yawa acikinsa .
Ya ku musulmai:
Lallai mutum yana da wahala ya samu wanda ya ke kauna  wanda bai da wani abu da ya ki tare da shi  ,  to yayi hakuri da abin  da ya ki sabo da abin da ya ke so,  yana da wahala ka samu mutane biyu  suna mu'amala ko wannensu ya yarda da dukkan dabi'un junansu, ba wasu mutane biyu da za su yi mu'amala  da junan su fa ce daya na kawaici dan uwansa an karbo daga Abu huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:-  ( Kada mumini ya tsani mumina, idan yaki wani hali na ta idan ya ki wani hali na ta to zai so wani hali nata Muslim ne ya rawaito) .
Wato kada  mutum ya ki matar sa ki na gaba daya wanda zai sanya shi ya rabu da ita ya sake ta ya warware kullin aure, to idan ya tsani wani hali nata mara kyau to kuwa zai samu wani hali nata abin yarda.
To  ya ku mazaje  ku riki matayenku kar ku yi gaggawan kosawa da sa'insa kar ku yi gaggawan rabuwa   kada ku yi gaggawa zuwa ga cika , kar ku kambama abu wurin nuna tsana da kiyayya  so dewa mutum rauni na hankali  yaka yi galaba a kanshi  fushi ya rinjaye shi  sai ya yi aiki na wauta ya yi gaggawa  ya yi cika sannan daga baya kuma ya dawo yana nadama a halin kuma wato kome ya tsere mishi  ya wuyata a gare shi,  ta koma gare ta daga cikin wadanda suka saki matan su  sannan rayin kuma tabi ta shiga damuwa akwai Qais Dan zarih in da yayi waka yana mai nuna hasara  cewa:-
Wayyo zuciyata da ta saki ginina  £ Rabuwa da abin ginina kamar wani yaudara ne
Masu kai komo a tsakani su suka kewaye ni su suka ruda ni £ kaito da mutanen da za su yiwa masu shiga tsakani biyayya  £  ga shi na wayi gari  cikin zargin zuciya ta ga wani al'amarin da ba ni da kuma yanda zan yi ba yanda na iya £
Kamar mutumin da  abu ya boyu a gare shi yana cizon yatsa  £ kamar mutumin da ya yi faduwa yayi asara yana ciza yaza £ sa annan kuma sai bayan ya  riga ya saida abinne sai ya gane ase faduwa yayi.
Ya ke mata mumina , kar ki zama cikin masu ci don tarawa, kuma ki zama kina yawaita zargi, mai yawan hayaniya da saurin fushi, wacce bata bin umarnin mijinta , kuma in ya yi rantsuwa bata biye mishi  , ki kyautatawa mijinki , ki kasance kusa da kaunarsa, mai taimaka masa yayin bukatarsa  mai amsa kiransa,  mai sauka zuwa ga bukatarsa  mai tuna falalarsa da   kyautatawansa, kar ki zama mai munana mishi mu'amala  , kar ki yi musu da shi yayin fushin shi da fusatan shi,  kar ki tsauwala mishi  yayin da ya cije ko ya harzuka , Mu'awiya Allah ya kara mishi yarda ya ce da Sa'asa'atu dan sauhan cikin mata wacce tafi soyuwa a gareka ? sai ya ce :- mai biyewa  abinda kake so, waccece kuma ka fi ki acikinsu ? wacce tafi nesa da abinda kake so , sai Mu'awiya ya ce :- wannan cin gyara na duniya kenan, sai Sa'a'sa'atu  ya ce:-Da  ma'auni na  adalci .
 An karbo daga abu Uzaina Assadafi    Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:- (  masu tsananin kauna masu  yawan haihuwa , mai aikta  (abinda ka ke so) , muddin suka ji tsoron Allah , mafi sharrin matayen ku kuma sune masu bayyana tsiraici , masu alfahari sune munafukai, ba wanda zai shiga aljanna a cikin su, face kamar bakin hankaka.  Nasa'I ne ya fito da shi
 An karbo daga Abdullahi Dan  Mihsan daga wata gogon  shi cewa ta shiga wurin Manzon Allah sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata  agare shi  sai ya tashi don wata bukata ,  sai ya biya mata bukatar tata , sai manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce mata ko ke  kina  da miji ? sai  ta  ce e,  sai ya ce   yaya kike da shi sai ta ce bana gajartawa ( a hakkinsa) sai abinda ya gagareni  sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:- to,  ki duba matsayinki a gunshi domin shi ne aljannan ki kuma wutanki)  . Nasa'I ne ya rawaito shi
Idan rayuwa ta kasance ana rayatacike  da  kyawawan halaye ba kiyayya ba gaba, to ya haramta akan mace ta nemi cika , ko kuma ta nemi kul'i a daya daga cikin zantuttuka mafi inganci a magan ganun malamai an karbo daga saubana Allah ya kara mishi yarda ya ce:- Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi  ya ce  ( Dukkan matan da ta tambayi mijinta saki ba tare da wani laifi ba to, kamshin aljanna ya haramta a gare ta ) Ahmad ne ya rawaito.
An karbo daga Ukubata dan Amir Allah ya kara yarda a gare shi ya ce :-( Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:-  lallai mataye wadanda suke wofantattu ,  masu  yin khil'I masu warware auren su sune muna fukai ) Dabarani ne ya rawaito shi    Ibnu kudama ya ce :- wannan yana nuni cewa haramunne  yin khul'I ba tare da bukata ba sabo da akwai cutarwa ga ita da kuma mijin nata ,  da kuma  gusar da maslahohin aure ba tare da bukata ba  , sabo da haka aka haramta.
Mustahabbi ne  a sulhu tsakanin ma'aurata  biyu wanda suke rikici da junansu an karbo daga Abdullahi dan Abbas Allah ya kara yarda a gare su shi da mahaifinshi  cewa mijin  barira ya kasance bawa ana ce da shi  Mugithu kai kai  ka ce ina kallo zuwa gare shi ina dubi yanda yake shawagi a bayanta yana kuka  hawaye na zuba  a gemun sa  sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya ce ga Abbas :-  (  Ya Abbas baka mamaki irin kaunar da mugithu yake yiwa barira da kuma irin kin da barira take yiwa shi Mugith sai ya ce da ita da kin koma mishi sai ta ce ya Manzon Allah umarni ne ka ke min  sai ya ce a'a  sai dai kawai ina nema mishi shawara sai ta ce bani da bukata  zuwa gare shi  ).Buhari ne ya fito da shi. …       

Yana nuni cewa idan mace ta ki miji bai kasancewa ga waliyinta da ya tilasta mata kan zama da shi. Idan ta so shi kuma bai kasance wa ga waliyinta da ya raba su, Allah ya amfanar da mu da Alkur'ani da sunna da abin da ke cikin su na daga ayoyi da shiriya bayyanannu da wazi da hikima .
Ina neman gafaran Allah ku nemi gafararsa shi Ubangiji na mai gafara ne Mai kauna.
 HUDUBA TA BIYU
Ya ku Musulmai ! Allah ya sanya shika da warware igiyar da aka kulla tsakanin ma'aurata biyu a hanun miji, sai dai  ya haramta ya munana amfani da hakkin nasa cikin sakin da rikon sa wata hanya don ribatar ita matar da firgita ta, ya sanya shi kamar wata bulala ce a fiskar ta don ya bautar da ita da tsorata ta, da walakanta ta, Allah madaukakin sarki ya ce : ( To ku rike su da kyautata wa ko ku sake su da kyautata wa.) An karbo daga ASSUDI  kan fadinsa  (ko a sake su da kyautata wa) Da ya bata cikakken hakkinta kada ya cutar da ita, ko ya zage ta, wanda ya katange matarsa bai sake ba bai kuma barta ta yi aure ba idan iddarta ya kare, ya cutar da ita da duka, da kuntata mata, ko ya hana ta hakkokinta na daga ciyarwa da kason kwana, da makamancinsau don ta fanshi kanta daga gare ta sai ta yi to khulin ya baci kuma zaa maida mata abin da ta bada don fansan.    
(ba ya halatta a gare ku ku gaji mata a kan tilas kuma kada ku hanasu aure domin ku tafi da sashen  abin  da kuka basu ).
Idan ta zo da alfahasha sai ya hana ta aure don ta fanshi kanta daga gare shi sai ta yi hakan to khul'in ya inganta. Sabo da fadin Allah Madaukaki: (kuma kada ku hana su aure domin ku tafi da sashin abin da ku ka ba su, face idan suka zo da wata alfahasha bayyananniya.)
Ba ya dace wa rike wacce ba ta kamun kai, sabo da tawaya ne ga mijin a addinin shi da dabiunsa da bata sunansa da zubar da mutuncinsa, bai da amincin kada ta bata mishi shimfidinsa da jingina mishi wani da da ba nashi ba, kuma mace mai sakaci da hakkokin Allah na wajibi kamar sallah da makamancinta, wacce ba ta jin nasiha  Mustahabbi ne a sake ta.
Kuma rantsuwar shika na cikin rantsuwa na fasikai, wadanda ke rikan ayoyin Allah da izgilanci, Ibnul Arabi yace a cikin Ahkamul Kur'an : (Na daga cikin rikan ayoyin Allah da izgilanci abin da aka rawaito daga Abdullahi dan Abbas kan cewa an tambaye shi game da mutumin da yace da matarsa : Ke sakakkiya ce sau dari, sai yace : Ukun ya isan maka a gare ta, sauran casain da bakwai ka riki ayoyin Allah da su bisa izgili ).
Daga cikin mazaje akwai wanda  ya sanya furta shika da yawaita shi abin ambato a bakinsa kuma abin sabon shi da al'adan shi,da abu mafi soyuwa a gare shi a abu mai kima da mara kima da babba da karami da mai girma da abin da bai taka kara ya karya ba,sai yace : In kiyi magana da wane to mata ta ta saku,ko saku ya tabbata a gare ni idan na ci abincin wane. Ko shika ya tabbata  a gare ni muddin kika tafiya da wane, ko shika ta tabbata a gare ni muddin mata ta ta shiga gidan wane, ko yace wa bako: Shika ta tabbata a gare ni muddin baka ci abincin rana a gu na ba, wannan dare , ko kuma in gobe baka ci abincin dare a guna ba, amma ba shikan yake nufi ba, ko rabuwa ba, sai dai ya yi hakan ne kamar rantsuwa, don yana nufin kwadaitarwa ko hanawa,ko tilastawa, wadannan lafuza ne haramtattu da ayyuka ne na laifi, da walakanta rayuwan zamantakewa da rena hakkokin mace da yara da wasa da shika  da hukunce – hukuncenta.
Ya wajaba ga miji ya kiyaye harshensa daga yawaita furucin shika, da tsoratarwa da ita da jirwaye da kamar ruwa game da  aukar da shi.
Ku ji tsoron Allah ya ku Musulmai kada ku riki ayoyin Allah abin izgili kar ku ketare iyakokin Allah madaukaki duk wanda ke ketare dokokin Allah to ya zalunci kansa, kuma dun wanda ke katare dokokin Allah to wannan yana cikin azzalumai.
Ya kare.