|


ترجمة خطبة الشيخ أحمد بن طالب
المترجم : أمين سعد
اللغة : الهوسا
التاريخ :24-5-1442هـ
Hudubar Masallacin Annabi, shaikh Ahmad Bin Dalib
24-5-1442 AH 8-1-2021AD
HUDUBAR
FARKO
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah muna gode masa kuma muna neman taimkonSa kuma
muna neman gafararSa, muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu, da
munanan ayukanmu duk wanda Allah y
shiryar da shi babu mai batar da shi
kuma duk wanda ya batar da shi babu mai shiryar da shi .
Kuma na
shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah ba shi kadai yake bashi da abokin tarayya , kuma na
shiada Annabi Muhammadu bawansa ne kum ManzonSa ne , kuma zababbenSa ne cikin
halittunSa, kuma badadayinSa ne,
ya isar da sako kuma ya bada amana
ya yi nasiha wa al'uma ya yaye
bakin ciki ya yi jahadi don Allah cancancin jahadi , har mutuwa ta zo mi shi ,tsira da amincin
Allah su tabbata agare shi da iyalan
gidansa tsarkaka da kuma matayen sa uwayen muminai da sahabbansa
masu hasken hannaye da kuma wanda
ya bisu da kyautatawa zuwa ranar sakayya .
BAYAN HAKA:
Lallai mafi
gaskiyan zance shi ne littafin Allah , mafi alherin shiriya shi ne shiryarwan
Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi , mafi sharrin
al'amura kuma su ne fararrun ta, kuma
dukkan fararrun abu bidi'a ne dukkan bidi'a bata ne, dukkan bata na
wuta.
Ya ku mutane!
Ku yi wa kanku hisabi kafin a yi muku hisabi, kuma ku auna ayyukan
ku kafin a aunaku,
To, idan an yi busa a cikin kaho, busa daya.
14; Kuma aka dauki kasa da duwatsu, kuma aka nika su nikawa daya.
15; A ran nan, mai aukuwa za ta auku.
16; Kuma sama za ta tsage, domin ita a ran nan, mai rauni ce.
17; Kuma mala´iku (su bayyana) a kan sasanninta, kuma wasu (mala´iku) takwas na
dauke da Al´arshin Ubangijinka, a sama da su, a wannan ranar.
18; A ranar nan za a bijira ku (domin hisabi), babu wani rai, mai boyewa, daga
cikinku, wanda zai iya boyewa.
19; To, amma wanda aka bai wa littafinsa a damansa, sai ya ce wa
(makusantansa), "Ku karba, ku karanta littafina."
20; "Lalle ne ni, na tabbata cewa ni mai haduwa da hisabina ne."
21; Saboda haka, shi yana cikin wata rayuwa yardadda.
22; A cikin Aljanna madaukakiya.
23; Nunannun ´ya´yan itacenta makusanta ne (ga mai son diba),
24; (Ana ce musu) "Ku ci, kuma ku sha a cikin ni´ima, saboda abin da kuka
gabatar a cikin kwanukan da suka shige."
25; Kuma wanda aka bai wa littafinsa ga hagunsa, sai ya ce: "Kaitona, ba a
kawo mini littafina ba!"
26; "Kuma ban san abin da (ke sakamakon) hisabina ba!"
27; "In da dai ita, ta kasance mai halaka ni gaba daya ce!
28; "Dukiyata ba ta wadatar da ni ba!"
29; "ikona ya bace mini!"
30; (Sai a ce wa mala´iku) "Ku kama shi, sa´an nan ku sanya shi a cikin
kukumi."
31; "Sa´an nan, a cikin Jahim, ku kona shi."
32; "Sa´an nan, acikin sarka, tsawonta zira´i saba´in, sai ku sanya
shi."
33; "Lalle ne, shi ya kasance ba ya yin imani da Allah, Mai girma!"
34; "Kuma ba ya kwadaitarwa ga (bayar da) abincin matalauci!"
35; "Saboda haka, a yau, a nan, ba ya da masoyi."
36; "Kuma babu wani abinci, sai daga (itacen) gislin."
37; "Babu mai cin sa sai masu ganganci."
Ranar sakayya
da idon yakini, da kuma kamunga, da fayyacewa da nesatan juna,
"Aranar da zaku juya kuna masu bada baya (gudane) ba ku da wani
mai tsaro a daga Allah, kuma wanda Allah ya batar to ba shi da wani mai
shiryarwa)
(Baku da wata mafaka a ranar nan kuma baku iya yin wani musu)
1. Idan aka girgiza ƙasa, girgizawarta.
2. Kuma ƙasa ta fitar da kayanta, masu nauyi.
3. Kuma mutum ya ce « Mẽ neya same ta? »
4. A rãnar nan, zã ta faɗi lãbãrinta.
5. cewa Ubangijinka Ya yi umurni zuwa gare ta.
6. A rãnar nan mutane za su fito dabam- dabam
domin a nuna musu ayyukansu.
7. To, wanda ya aikata ( wani aiki )
gwargwadon nauyin zarra, na alheri, zai gan shi.
8. Kuma wanda ya aikata gwargwadon nauyin
zarra na sharri, zai gan shi.
(Shin, bã ya da sanin lõkacin da aka
tõne abin da yake cikin kaburbura.
Aka
bayyana abin da yake cikin zukata, lalle ne Ubangijinsu game da su a ranar nan
Mai kididdigewa ne)
Mai
kwankwasar (zukata da tsoro ) Me ne mai
kwankwasr kuma mai ya sanar da kai abin da aki ce wa mai kwansar
ranar da mutane za su kasance kamar ya yan fari masu watswa kuma duwatsu
za su kasance kamar gashin sufin da aka sabe to ama wanda ma aunrsa su kai
naauyi to shi ya na cekn wata rayuwa
yardadda kuma ama wanda ma aunarsa
babu nauyi to uwarsa hawiya ce kuma mai ya sanar da kai me ne ita? Wata wuta ce mai zafi
Alfahari
da yawan dangi ya shagaltar da ko da ga
ibada mai amfaninku har kuka ziyar ce kaburbura A aha nan gaba za ku sani sa an nan tabas za ko sani hkika da kuna da sani sani nan yakini lalle ne da kuna da ganin jhim sa an nan lalle ne za ku ganta da edanu
bayyane sa an nan lalle ne za
atambaye ku a ranar nan labarin ni imar
da aka yi muku
Awanan ranar
Allaha zai dunkule kasa ya nade sammai
da damanSa sai ya ce nini me mulki ina
masarautar kasan?
10; Lalle
wadanda suka kafirta, ana kiran su, "Hakika, kin Allah (a gare ku) shi ne
mafi girma daga kinku ga kanku a lokacin da ake kiran ku zuwa ga imani, sai
kuna ta kafircewa."
11; Suka ce: "Ya Ubangijinmu! Ka matar da mu sau biyu, kuma Ka rayar da mu
sau biyu, saboda haka mun yarda da laifuffukan mu. To, shin, akwai wata hanya
zuwa ga fita?"
12; Wancan sababinsa, lalle (shi ne) idan an kirayi Allah Shi kadai, sai ku
kafirta, kuma idan aka yi shirki game da Shi, sai ku yi imani. To, hukuncin fa,
na Allah Madaukaki, Mai girma ne.
13; Shi ne Wanda ke nuna muku ayoyinSa, kuma Ya saukar da arziki daga sama
saboda ku, kuma babu mai yin tunani face mai mayar da al´amari ga Allah.
14; Saboda haka ku kirayi Allah, kuna masu tsarkake addini a gare Shi, kuma ko
da kafirai sun ki.
15 ; Mai daukaka darajoji (domin muminai), Mai Al´arshi, Yana jefa ruhi daga
al´amarinSa a kan wanda Ya so daga bayinSa, domin ya yi gargadi kan ranar
gamuwa.
16; Ranar da suke bayyanannu, babu wani abu daga gare su wanda yake iya boyuwa
ga Allah. "Mulki ga wa ya ke a yau?" Yana ga Allah, Makadaici, Mai
tilastawa.
17; Yau ana saka wa kowane rai a game da abin da ya aikata, babu zalunci a yau.
Lalle Allah Mai gaggawar hisabi ne.
18; Kuma ka yi musu gargadi kan ranar (Sa´a) makusanciya, a lokacin da zukata
suke masu cika da bakin ciki, ga makosansu. Babu wani masoyi ga azzalumai, kuma
babu wani mai ceto da za a yi wa da´a (ga cetonsu).
19; (Allah) Ya san yaudarar idanu da abin da kiraza ke boyewa.
20; Kuma Allah Shi ke yin hukunci da gaskiya, wadannan da kuke kira, waninSa,ba
su yin hukunci da kome. Lalle Allah, Shi ne Mai ji, Mai gani.
21; Ashe, ba su yi tafiya ba, a cikin kasa, domin su duba ga yadda akibar
wadanda suka kasance a gabaninsu ta zama? Sun kasance su ne mafi tsananin karfi
daga gare su, da kufaifan aiki a cikin kasa, sai Allah Ya kama su da
laifuffukansu. Kuma ba su da wani mai tsarewa daga Allah.
22; Wancan sababinsa, domin su Manzanninsu sun kasance suna zuwa gare su da
hujjoji bayyanannu, sai suka kafirta, sai Allah Ya kama su. Lalle Shi Mai karfi
ne, Mai tsananin azaba.
42;
"Kuma kada ka yi zaton Allah Mai shagala ne daga abin da azzalumai suke
aikatawa. Abin sani kawai, Yana jinkirta musu ne zuwa ga wani wuni, wanda
idanuwa suke fita turu-turu a cikinsa."
43; "Suna masu gaggawa, masu daukaka kawunansu zuwa sama kiftawar ganinsu
ba ta komawa gare su. Kuma zukatansu wofintattu."
44; Kuma ka yi gargadi ga mutane ga ranar da azaba take je musu, sai wadanda
suka yi zalunci su ce: "Ya Ubangijinmu! Ka yi mana jinkiri zuwa ga wani
ajali makusanci, mu karba wa kiranKa, kuma mu bi Manzanni."(Allah Ya ce
musu) "Ashe, ba ku kasance kun yi rantsuwa ba daga gabani, cewa ba ku da
wata gushewa?
45; "Kuma kuka zauna a cikin gidajen wadanda suka zalunci kansu, kuma ya
bayyana a gare ku yadda Muka aikata game da su, kuma Muka buga muku
misalai."
46; Kuma lalle sun yi makirci irin makircinSu kuma a wurin Allah makircinsu,
yake, kuma lalle ne makircinsu ya kasance, hakika, duwatsu suna gushewa saboda
shi.
47; Saboda haka, kada ka karfafa zaton Allah Mai saba wa´adinSa ne ga ManzanninSa.
Lalle ne Allah ne Mabuwayi, Ma´abucin azabar ramuwa.
48; A ranar da ake musanya kasa ba kasar nan ba, da sammai kuma su bayyana ga
Allah Makadaici, Mai tankwasawa.
49; Kuma kana ganin masu laifi, a ranar nan, suna wadanda aka yi wa ciri daidai
a cikin maruruwa.
50; Rigunansu daga farar wuta ne, kuma wuta ta rufe fuskokinsu.
51; Domin Allah Ya saka wa kowane rai da abin da ya tsuwurwurta. Lalle ne,
Allah Mai gaggawar hisabi ne.
52; Wannan iyarwa ce ga mutane, kuma domin a yi musu gargadi da shi, kuma domin
su sani cewa, abin sani kawai, shi ne abin bautawa guda. Kuma domin masu
hankali su rika tunawa.
Allah ya sa mini albarka ni da ku.
Huduba ta
biyu
Dukkan yabo
da godiya sun tabbata ga Allah Tilo Marinjayi, Mabuwayi Mai gafara Mai juya
dare da rana da kuma rana a kan dare, tsira da amincin Allah su tabbata ga
Annabi zababbe da iyalansa tsarkaka da muhajirai da ansar,da sauran sahabbai
ma'abota biyayya, da wanda ya bi hanyar su ya haskaka da hasken su,
Bayan haka Ya
ku mutane ku bi Ubangi-jinku (Ya ku mutane ku bi
Ubangi-jinku da takawa lalle ne girgizar kasa ta tsayuwar Sa,a wata aba ce mai
girma Aranar da kuke ganin ta du
–kan mai shayar da mama tana sha-gala daga a da ta shayar, kuma dukan mai ciki
tana haihuwar cikinta kuma kana ganin mutane suna masu maye alhali
kuwa su ba masu maye ba amma azabar Allah ce mai tsanani)
Ku yi salati
da sallama ya ku bayin Allah!