السبت، 1 فبراير 2020

FALALAN MUSULUNCI DA WAJABCIN SHIGANSA


Hudubar Masllacin Annabi na Sheikh Ahmad Bin Dalib 6-6-1441Ah 31-01-2020AC
Hudubar farko
 Ya ku musulmai!
Ku sani ba wani abu da ya ke mafi kamala da cika kamar abin da Allah  tsarki ya tabbata a gare shi  ya cika mana ya kammala mana shi ya kuma jingina shi mabuwayi da daukaka ga kansa kuma ya yarda da shi ga masu karamci, Allah Mabuwayi da Daukaka ya ce :  (A yau na cika muku addininku kuma na cika muku ni'imata a gare ku ni na yardar muku musulunci addini gare ku)
Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bayyana shi cikakken bayani, ya jinginta shi ga kansa mai daraja,  ya kafa tushensa da asasinsa, ya fifita abin da ya ke na dole da abin da ke biye da shi, da abin da ke tawaye shi, da abin da ke warware shi, kuma lalle shi gaskiya ne bayyananniya, kuma hanya mikakkiya da tafarki madaidaici, kuma shiryarwa ne mabayyaniya,kuma shi ya fi cancanta da bi a yi hakuri a kansa har zuwa gamuwa da Mafi iya mahukunta zartar da hukunci, Allah Tabaraka wa Ta'ala ya ce :  (Ya ku wadannan mutane in kun kasance cikin shakku daga addini na to ni ba zan bautawa wadanda ku ke bautawa ba, ba Allah ba,sai dai ni ina bautawa Allah wanda ya ke karbar rayukanku, kuma an umarce ni da na kasance cikin muminai.ka tsayar da kanka ga addinin totar kada ka kasance cikin mushrikai. Kada ka bautawa wani ba Allah ba, abin da ba zai amfane ka ba, ba zai cutar da kai ba, to muddin ka yi haka to lallai kana cikin azzalumai.Idan Allah ya sa ma cuta to ba mai yaye ma sai Shi, in ya nufe ka da alheri ba mai ije falalarSa rahamarSa na samun wanda ya ga dama daga bayinSa, Shi Mai gafara ne Mai jinkai. Ka ce ya ku mutane hakika gaskiya ta zo muku daga Ubangijinku, to duk wanda ya shiryu don kansa, kuma duk wanda ya bata to hakika ya bata ne ga kansa kawai.Ni ban kasance wakili ba a kanku. Ka bi abin da aka yi wahayi a gare ka kuma ka yi hakuri har Allah ya yi hukunci shi ne, mafi alherin  mahukunta.

        Allah ya riki alkawarin annabawa da mabiyansu bisa imani da shugabanmu  Muhammad  cikamakin Annabawa da manzanni da imani da abin da ya zo da shi daga Ubangijin talikai, Allah Matsarkaki ya ce :  ( Kuma alokacin da Allah ya riki alkawarin annabawa :"Lalle ne ban baku wani abu ba daga littafi da hikima, sa'an nan wani manzo ya je muku, mai gaskatawa ga abin da yake tare da ku, lalle ne za ku gaskata shi, kuma lalle ne za ku taimake shi," ya ce : shin kun tabbatar, kuma kun riki alkawari Na a kan wannan a gare ku?" suka ce : " mun tabbatar" ya ce : "To ku yi shaida, kuma Ni a tare da ku ina daga masu shaida. To wadanda suka juya baya a bayan wannan, to, wadannan su ne fasikai.Shin wanin Addinin Allah suke nema, alhali kuwa a gare shi ne wadanda ke cikin sama da kasa suka sallamawa, a kan so da ki, kuma zuwa gare shi ake mayar da su.)
To duk wanda ya cika yana da sakayya mafi cika, kuma a bashi rabo biyu daga rahamar Allah Daukakakke Mafi daukaka, Allah Madaukakin sarki ya ce : ( Ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah, ku yi imani da ManzonSa zai baku rabo biyu daga rahamarSa, kuma ya sanya muku wani haske wanda ku ke yin tafiya da shi, kuma ya gafarta muku, kuma Allah Mai gafara ne Mai rahama.Domin kada ma'abota littafi su san cewa lalle basu da ikon yin  komai ga falalar Allah, kuma ita falalar ga hannun Allah kawai take, yana bayar da ita ga wanda ya so, kuma Allah Mai falala ne Mai girma.)
        Musulmai su suka fi dacewa da wannan ribanyawar da haske da gafara, sabo da su ne suka yi imani da dukkan Annabawan Allah da manzanninSa, kamar yadda Ubangiji Mabuwayi da daukaka ya bada labari game da su, a fadinSa : ( Manzo Allah ya yi imani da abin da aka saukar zuwa gare shi daga Ubangijinsa da muminai, kowannensu ya yi imani da Allah da mala'ikunSa da littatafanSa da manzanninSa, ba mu rarrabewa a tsakanin daya daga manzanninSa, kuma suka ce :Mun ji mun yi da'a, (muna neman) gafararka ya Ubangijinmu, kuma zuwa a gare ka makoma take).
Wannan al'uma ita ta fi karancin al'umu ajali kuma ta fi su lada, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Misalinku da misalin ahlul kitabi kamar mutum ne ya dauki 'yan kodago ijara yace : wa zai mini aiki daga safiya zuwa rabin wuni na bashi kiradi guda? Sai yace : wa zai min aikin daga rabin wuni zuwa lokacin la'asar akan kiradi? sai  nasara suka yi, sannan sai yace :Wa zai min aiki daga la'asar zuwa faduwar rana a kan kiradi biyu? To sai ku kuka amsa  sai yahudawa da nasara suka yi fushi suka ce : yaya mu da muka fi aiki kuma ladanmu ya fi karanta ? sai Allah ya ce : shin ko na tawaye muku hakkinku? Sai suka ce : a'a, sai yace : to wannan falala ce na kan bawa wanda na so,)
Wannan al'uma ita ce ta zo karshe a zamani a duniya, amma kuma ita  tafi daukaka a duniya da lahira, kamar yadda Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Allah ya batar da wadanda suke kafin mu daga rabauta da juma'a, sai ranar asabat ta zama ga yahudawa, ranar lahadi kuma ta nasara,  sai mu Allah ya shiryar da mu ga ranar juma'a, ya kuma sanya juma'a sannan asabat sai lahadi, to haka nan zasu zama su suke baya gare mu ranar alkiyama, mu ne na karshe a duniya amma na farko a ranar alkiyama).
Sai Allah ya hada mana a wannan Addini na tafarkin masoyin shi Ibrahim da sunnar zababbanSa Muhammad tsakanin kamalar fiskantar Allah da sauki gurin bautawa Allah, shine Addini mafi soyuwa a gurin Allah,  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Mafi soyuwan Addini a gurin Allah shine Addinin hanifiyya mai sauki,)
     To dadi ya tabbata ga mutumin da Allah ya hada masa tsakanin tafarki na musulunci da daidaituwa akan sunnan mafificin halittu, mafificin tsira da aminci su tabbata a gare shi, Ubayyu bin Ka'ab ya ce : "ku riki tafarki da sunna, sabo da ba wani bawa da zai zama kan tafarki da sunna da zai  ambaci Allah to sai idanuwansa su cika da hawaye sabo da tsoron Allah, sannan wuta ta taba shi,to haka nan ba wani bawa da zai zama kan tafarki da sunna da zai  ambaci Allah Mai rahama to sai tsikan jikinsa ya tashi sabo da tsoron Allah face ya kasance tamkar itaciya ce da ganyenta sun bushe, to haka zunubansa zai rika karkadewa kamar yadda ganyen wannan itaciyar kekarkadewa ya  zube. Kuma lalle tsakaitawa a kan sunna ya fi alheri bisa ijtihadi bisa sabanin tafarki da sunna,"  
To duk wanda ya kasance kamar haka kuma Allah ya tseratar da shi daga alfahari da girman kai da jiji da kai da riya to zai cinma buri ko da kuwa aikinsa kadan ne,
Abu Darda'u ya ce : (Ina ma da barcin masu hankali da wayo da shan ruwansu za su yi kamunga ga kwana ba barci  da azumi na wawaye, misalin kwayar zarra na ibada na mai da'a ya fi daraja a kan ibadan masu ruduwa da aikinsu).
   Allah ya sa min albarka ni da ku a cikin Alkur'ani mai girma Allah ya amfane ni da ku da abin da ke ciki na daga ayoyi da ambato mai hikima.
Ina fadin magana ta wannan kuma ina nema wa kai na da ku gafarar Allah, to ku ma ku nemi gafararSa lalle shi mai gafara ne mai jinkai.

Huduba ta biyu

     Allah Mabuwayi da Daukaka ya ce :  (Allah ya shaida ba abin bautawa da face shi, mala'iku da ma'abota ilimi sun shaida yana tsaye da adalci, ba abin bautawa face shi, Mabuwayi Mai hikima. Lalle ne addini a wurin Allah shine musulunci, kuma wadanda aka bai wa littafi basu saba ba face a bayan ilimi ya zo musu, bisa zalunci a tsakaninsu, kuma wanda ya kafirta da ayoyin Allah to lalle ne Allah Mai gaugawar sakamako ne. To idan sun yi musu da kai sai ka ce : Na sallama fiska ta ga Allah kuma wanda ya bi ni (haka) kuma ka ce ga wadanda aka baiwa littafi da ummiyai, "shin kun sallama"? to idan sun sallama, hakika sun shiryu, kuma idan sun juya to kawai abin da ke kan ka shine isarwa, kuma Allah mai gani ne ga bayinSa. Lalle ne wadanda suke kafirta da ayoyin Allah, kuma suna kashe annabawa  ba da wani hakki ba, kuma suna kashe wadanda ke umarni da yin adalci daga mutane to, ka yi musu bushara da azaba mai radadi.wadannan ne wadanda ayyukansu suka baci a cikin duniya da lahira, kuma basu da wasu mataimaka.