الجمعة، 18 أكتوبر 2019

BADA KARIYA GA AKIDAR MUSULUNCI DAGA SIHIRI DA BOKANCI


Hudubar Masallacin Annabi  na shaikh Abdullah Bin Abdurrahman Albuaijan 19 safar 1441Ah.
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya shiryar da mu ga imani. Ya bayyana mana manyan ginshikai na gaskiya da hujja, ya turo manzanni ya saukar da littafi a gare su tare da mizani.
Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya, shaidawa ta gaskiya da imani, Na shaida Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, an turo shi zuwa ga mutane da aljanu.sai Allah ya tseratar da mu daga dulmuya cikin bata.ya kuma kubutar da mu daga gangarawa cikin kafurci da hasara.tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabbanSa da wanda ya bi su da kyautatawa.
Bayan haka :
Lalle mafi alherin zance shine maganar Allah, mafi alherin shiriya ita ce shiriyar Muhammad dan Abdullah, kuma mafi sharrin al'amura shine fararrunta, kuma dukkan fararrun al'amura bid'a ce kuma dukkan bid'ah bata ce, kuma dukkan bata na wuta.
Ya ku bayin Allah! Ina muku wasiyya da ni kai na da tsoron Allah,Mabuwayi da daukaka,domin shine wasiyyar Allah ga mutanen farko da na karshe (Hakika mun yi wasiyya ga wadanda aka bawa littafi gabaninku da ku kanku da ku ji tsoron Allah).
Ya jamaar musulmi!
Allah ya bawa mutum hanyoyi masu yawa na samun ilimi.ya bashi hankali da fahimta, ya mishi umarni da neman ilimi sai ya ce : (ka yi karatu da sunan Ubangijinka mafi karamci. Wanda ya koyar da alkalami. Ya sanar da mutum abin da bai sani ba).
Allah ya zabi mutum don ya khalifantar da shi a doron kasa kuma ya bashi ilimi don aiki da samun daukaka, ya bashi hankali don a fiskantar da magana gare shi a kuma dora mishi nauyi na sharia sai yace : (A yayin da  Ubangijinka yace ga Malaiku lalle Ni zan sanya mamayi a doron kasa, sai suka ce :zaka sanya a cikinta wanda zai yi barna kuma ya zubar da jini alhali mu muna tasbihi da godiya a gare ka kuma muna tsarkake ka,sai yace lalle ni na san abin da baku sani ba).
  Sai Allah Madaukakin sarki  ya bayyana cewa samun daukaka da daraja na ga ilimi sai yace :( Allah na daukaka darajan wadanda suka yi imani daga cikin ku da wadanda aka bawa ilimi darajoji).

Ya ku bayin Allah!
Lalle mutum ana haifansa jahili ne bai san komai ba, Allah Madaukakin sarki  yace : ( Allah ya fitar da ku daga cikunan uwayenku baku san komai ba).
Hakika Allah ya dauke shamaki na kadan daga cikin ilmomi sai ya bada dama ga bayi da zasu iya riskan su, amma mafi yawan ilimi ya boyu daga riskar mutum. Allah ya ce :  ( Kuma ba a baku wani abu na ilimi ba face dan kadan)  Allah ya kebanta da ilimin gaibi ya boye shi, ya sanya ba wanda ya san hakikanin tawilin shi sai shi kadai. ( A gare shi mabudan gaibi suke, ba wanda ya san su sai shi).
An karbo daga Abdullahi dan Umar Allah ya kara yarda a gare su ya ce daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : (Mabudan gaibi guda biyar ne. ba wanda ya san su sai Allah, Ba wanda ya san abin da mahaifa zata rage sai Allah, ba wanda ya san gobe sai Allah,ba wanda ya san yaushe ruwa zai zo sai Allah,ba wanda ya san rai a wace kasa zai mutu sai Allah, ba wanda ya san yaushe Alkiyama zata tashi sai Allah, sai ya karanta fadin Allah ( A gare shi mabudan gaibi suke, ba wanda ya san su sai shi ya san abin da ke cikin tudu da kogi, ba wani ganye da zai fado face ya san da shi, ko kwaya cikin duhun kasa ko danye ko busasshe face yana cikin littafi bayyananne).Bukhari ne ya rawaito.
Na daga cikin hikima da sunnar Allah ya sanya shamaki tsakanin gaibi da halittunSa har ma da mafi soyuwan mutum cikin bayinSa, Ba wani mala'ika na kusa ko Annabi Manzo, ( Kace ba wanda ya san gaibi cikin sammai da kasa face Allah) kuma ya umarci Manzon Allah da ya maida al'amura zuwa ga Allah, kuma ya bada labari game da kansa cewa bai san gaibi ba, kuma ko tsinkayar wani abu na hakan, face abin da Allah ya sanar da shi, sai yace :  ( Kace ban mallakawa kai na wani abu na amfani ba ko cuta face abin da Allah ya so, da ace na san gaibi da na nemi yawaitawa daga alheri kuma wani abu mummuna bai shafe ni ba.).
 Ya jamaar musulmi!
Zukata na neman sanin gaibi, kuma dukkan boyayyen abu ana kwadayin shi, a cikin su akwai wanda shaidanu kan kaskantar da su da mataimakansu makaryata, da bokanci da duba da masu duba da taurari da sihiri suna kage da karerayi suna fadin abin da ba su sani ba game da Allah,  ( Kace Ubangiji na ya haramta alfahasha ne kawai wanda ya bayyana ko ya boyu daga cikin su da laifi da zalunci ba tare da gaskiya ba kokuma ayi shirka a hada Allah da wani cikin abin da bai saukar ba da shi na hujja ko ku fadi abin da baku sani ba game da Allah .)  kuma hakika shaidanu sun kasance  suna haurawa zuwa sama sai su saci ji don su labartawa mataimakansu na daga bokaye su kuma sai su gayawa mutane labarin to ku saurara lallai shaidanu an hana su satan  ji kuma an yi shamaki tsakaninsu da shi tun lokacin da aka turo Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  hakika alkura'ni ya bada labarin hakan game da su sai ya ce :( lallai mun nemi satar ji daga  sama sai muka sami an cika ta  da matsara masu karfi da taurari masu konewa. Hakika mun kasance gabanta don sauraru, duk wanda yake neman saurara to wanda ya yi sauraru a yanzu ya saci ji to  zai sami tauraru mai dako gare shi da aka dakatar da shi don a jefe shi da shi  (lalle mu bamu sani ba sharri ake nufa da wanda ke doron kasa ko kuma Ubangijinsu ya na nufinsu da shiriya ne) Allah Madaukakin sarki ya ce :  shaidanu ba su sauka da wannan alkura'n  ba  kuma ba zai kamata gare su su saukar da shi ba, kuma baza su samu ikon saukar da shi ba hakika su ababan nesantarwa ne game da  barin jin zancen mala'iku )
Hakika Allah ya hana su zuwa sauraro zuwa ga duniyan sama ya sanya taurari abin jifa ga su ta kowani jiha da suka  fiskanci sama Allah Madaukakin sarki ya ce (Hakika mun kawata saman duniya da adon taurari , Mun kiyaye ta daga kowani shaidani mai taurin kai , ba za su yi sauraro zuwa ga mala'ikun sama ba ana jefesu daga kowace nahiya, ababan korewa suna da azaba madawwamiya a lahira , sai wanda ya fauta guda daya daga mala'iku kuma tauraru mai tsananin haske ya bi shi)  
 ya ku bayin Allah imani da alkura'ni mai girma ba ya haduwa a zuciya da gaskata wadan nan bokaye (dujjalai) sabo da haka ne Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (Duk wanda ya zo ga boka ko dan duba ya gaskata shi cikin abin da ya ke fadi to hakika ya kafurta da abin da aka saukar wa Muhammadu,)
Ku yi katanga da akidar ku kuma ku yi riko da alkura'ninku kuma ku sani lallai Allah shi ne masanin gaibi ba ya bayyana saninSa ga wani .
                                                                             Huduba ta biyu

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai  kyakkyawan karshe  na ga masu tsoron Allah babu gaba sai ga azzalumai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabinmu Muhammad da iyalansa da sahabbansa baki daya ya ku bayin Allah
Hakika an yi jarabawa ga mutane ta hanyar shigowan bokaye da matsafa da masu duba da 'yan tsubbu sai suka yi galaba akan masu rauninsu suna musu dako da wasa da hankulansu dukkan isgilanci har sai sun komo zuwa gare su a lokacin sauki da lokacin cuta suka gaskata su a sha'nin ilimin gaibi da labarin sama, hakika kuma ya tabbata daga Annabi Muhammad an karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce :Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (duk wanda ya zo ga mai duba ko boka sa'nnan kuma ya gaskata shi cikin abin da ya fadi to hakika ya kafurce da abin da aka saukar ga Muhammadu)
An kuma karbo daga Imrana dan Husaini ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (baya tare da mu duk mutumin da yake camfi ko ake mishi camfi kokuma ya ke bokanci ko ake mishi bokanci ko ya ke sihiri ko ake mishi sihiri).
Lallai shaidanu kayan hajansu shi ne karya da kirkira kage Allah Madaukakin sarki ya ce (shin bazan baku labari ba bisa ga wanda shaidanu ke sauka a gare shi , suna sauka ne a bisa dukkan mai yawan karya ko mai kage mai zunubi , su shaidanu suna jefa saurara daga mala'iku ga bokaye yawancin su makaryata ne).
An karbo daga A'isha Allah ya kara yarda a gare ta ta ce: wasu mutane sun tambayi Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi game da masu bokanci sai ya ce :lallai su din nan ba kome bane sai suka ce ya Manzon Allah lallai fa suna bamu labarin a wasu lokutan abin da zai kasance kuma sai ya kasance gaskiya, sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : lallai mala'iku suna sauka zuwa sama a wurin gajimare sai su ambaci abubuwanda za a hukunta a sama sai shaidanu su sauraresu sai su dauki wannan sakon su kai shi zuwa ga  bokaye sai su kara musu karairayi akan abin da suka ji guda dari daga garesu) . A wata riwayan (wancan kalma ce guda daya na gaskiya wanda aljani zai fizgota sai sautin ya fada kunnen masoyansa kamar yanda kukan kaza yake tabbatuwa a kunne sai ya . cakuda shi da karerayi sama da karya dari) Bukari da muslim ne suka rawaito
Ya ku jama'n musulmi
Lallai shaidanun mutane da aljanu abokan juna ne kuma makiya ne a gare ku Allah ya ce( sashinsu na wahayi zuwa ga sashi suna masu kawata zance na rudi ) kuma hakika Allah ya musu alkawarin narkon azaba gaba daya sai ya ce (A ranar da za a tada su gaba daya ya tawagar aljanu gashi kun yawaita akan mutane sai masoyansu na daga mutane suka ce : ya Ubangijinmu sashinmu sun ji dadi da sashi kuma gashi mun kai lokacin da ka sanya mana sai ya ce ai wuta ne makoman ku kuna masu dawwama a cikinta sai inda Allah ya so lallai Ubangijinka mai hikima ne kuma masani)
Bayan haka: ya jama'r musulmai lallai Allah shi ne wanda ya kebanta shi kadan shi da sanin gaibi duk wanda ya ikirarin tarayya da Allah a cikin wani abu na wannan to hakika ya sanya wa Allah abokin tarayya kuma ya yi karya ga Allah da Manzo lallai ku saurara duk wanda ya bar da'a wa Allah zuwa da'a ga waninSa ya biye mishi cikin ala'marin addininsa to hakika ya yi shirka ga Allah Madaukakin sarki, Allah Madaukakin sarki ya ce (lallai shaidanu suna yin wahayi zuwa ga masoyansu domin su yi jayayya da ku, muddin kuka musu da'a to lallai ku din nan kuna cikin masu shirka) ku yi riko da addininku da akidar ku domin ku kuna kan hanya mai haske darenta kaman wuninta ne ba mai zamewa sai wanda ya ke halakakke.